Episode Sixty Three: Save The Date
by @mamanmaama
Yace "eh nasan tana da dalilin ta shi yasa ni kuma na kasa zuwa in tuna mata. Am just scared Diyam, tsoro nake yi kar a sake hana ni ke a karo na biyu. Bansan me zanyi ba wannan karon" tace "babu wanda zai hana mu juna Aliyu. In har kaga ba'ayi ba to kuwa tabbas Allah bai rubuta za'ayi ba. Waliyai na ne su amma basu kadai bane waliyai na in sunki zamu iya zuwa Kollere mu......" Yace "no, no Diyam. Ba su kadai ne waliyan ki ba amma sune shakikan Baffa, kamar yadda kika fada haka ne Baffa zaiji dadi idan muka sasanta tsakanin mu da su. Kuma ni ba zanso in zama sanadiyyar rabuwarki da yanuwanki ba but am not going to give you up, not now not ever. Dan haka zamu jira in ta kai ga cewa ni zan kuma durkusawa Alhaji Babba zan durkusa din" sai ya ɗan yi dariya yace "the table have been turning so past yanzu kuma na dawo ni nake nema a gurinsa" ta taya shi dariyar sannan tace "in lokacin durkusawar yazo, call me sai mu durkusa tare ni da kai because we are in this together". Washegari sai ga wayar Mama. Ta gayawa Diyam duk abinda sukayi da Alhaji Babba tace "na bashi wannan damar ne saboda naga yadda yayi nadamar abinda yayi, so nake ya nemi Sadauki da kansa ya gyara kuskuren da yayi da kansa. Yanzu yace yana so kizo gari dan yana son neman yafiyarki, sannan kuma yace kice da Sadauki ya turo, in yaso sai a hada dana su Fati ayi gabadaya" Diyam ta lumshe idonta tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa a zuciyarta wanda har sai daya saka hawaye ya taru a idon ta. Mama tace "kinyi shiru kuma, me zance masa?" Ta dan goge hawayen idonta tana jin zuciyarta fari kal kamar takarda, rabon data ji wannan feeling din tun Baffa yana da rai, tun tana carefree teenager, tun lokacin da Sadauki yake zuwa gurinta a school suyi ta bayyana wa junansu abinda yake zukatan su. Amma sai taji kunyar Mama tace "mun kusa fara exams yanzu Mama, ba zan iya tahowa gida ba amma muna yin hutu zan taho sai in samu alhajin, duk da dai ni na riga na yafe masa tuntuni" Mama tace "to Allah ya bada sa'a. Maganar Sadaukin fa?" Diyam tace "duk yadda akayi Mama" Mama tace "ki gaya masa ya tura gurin Alhaji Babba, sai asa rana tare dana su Fatin. Yaushe kuke so a saka?" Diyam ta sake yin shiru sai da Mama ta maimaita sannan tace "duk sanda aka ce dai dai ne" Mama tace "in aka saka lokacin hutun ku ai yayi ko?" Diyam ta sake yin shiru tana murmushi amma a ranta tana lissafa kwana nawa ya rage ayi hutun. Mama tace "shikenan tunda ba zakiyi magana ba, shi bara in kira shi in tambayeshi" Suna yin sallama Diyam tayi saurin kiran Sadauki ta gaya masa yadda sukayi da Mama, yace "tare dana su Fati kika ce?" Tace "eh, haka tace min" ya girgiza kai yace "I don't like that. Nafi son ranar bikin ki ya kasance all about you not you and someone else, nafi son in an ganki ace 'ga amaryar can' kar ace 'ga daya daga cikin amaren nan' nafi son ki samu cikakkiyar kulawa daga kowa ba wai ki samu divided attention ba. Dan haka zan gaya mata ayi nasu first, later in an huta sai ayi namu" Tun da ya fara magana take murmushi har sai daya gama sannan tace "I don't need attention din mutane, attention din ka nake so, in nayi kwalliya ban damu da a yaba ko ayi comparing dina da w asu ba as long as kai ka yaba as long as a gurinka babu wadda ta kai ni. Besides, ni ba biki zanyi ba, daurin aure kawai za'a hada da nasu, ni a gida zanyi zamana kawai sai wanda ya shigo aka gaisa kawai shikenan. Ban damu da having a big wedding ba as long as kaine angon that's all that matters, tunda nasan a gurinka zan samu more than abinda na samu a wancan auren" a can kasan makogwaron sa yace "more of what?" Tace "everything" yace "like?" Tace "caring" yace "and?" Tace "tunda nace everything ai ina nufin everything ko? Sai na lissafa maka?" Yayi dariya yace "so nake ki fada da bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke kika nema da kanki" ta bata rai tace "abinda kake nufi fa ni ba shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing" yace "zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake nufi" tace "ni ban san me kake nufi ba fa" yace "to in baki sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke ba?" Tayi rolling eyes dinta tace "good night Aliyu" yace "ashe tsoro ma kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana" tace "ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school gobe" yace "hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I will still demand to know that 'everything' da kika fada, ko ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you". Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma school, sai ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar su school yana neman weekend mai perfect date for their wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday. Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to have a perfect birthday gift for his 30th birthday. Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata abinda Diyam tace mata "duk sanda aka saka dai-dai ne Mama" ta tabe baki tace "ai shikenan, idan manyan sunzo ayi magana dasu". Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu Alhaji Babagana wanda yake kani ne a guri n Papa kuma shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan'uwa suje su hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi "kana ganin ba za'a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon" Sadauki yace "babu matsala in sha Allah, tunda wannan karon ai sune da kansu suka nemi azo din". Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun gurin yaya Ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace "Diyam din dai Aliyu?" Ya dago kai yana kallon ta yace "Diyam din dai. Ko kina kishi ne?" Ta tabe baki tace "ni dai daka hakura da Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar da yan'uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?" Ya daga kafada yace "ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in anyi auren da ita zan zauna bada yan'uwanta ba" Hajiya Dije, cousin din Yaya Ladi tace "amma duk da haka Aliyu, ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka kara da ita" sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a hannu fuskarsa da murmushi yace "kar ku damu, bayan anyi auren da sati daya zan dawo nan sai in aure ku duk ku biyun a rana daya". Yaya ladi ta tabe baki dan tasan shirishitar da maganar yake yi, tace "to ai shikenan, uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura" ya durkusa a gabanta yace "kisa mana albarka kawai ke dai. Kiyi mana fatan alheri" ta dafa kansa tace "Allah ya sanya alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri'a mai albarka" yayi kyakykyawan murmushi yace "yanzu kika yi magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina, ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata". A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa? Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace "dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar". Alhaji Babba yace "mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana" Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace "kamar yadda yake a al'adar kanawa cewa ana kawo kuɗin sa rana, shi yasa muka taho a shirye. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema" sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace "lokacin yarinyar tana hutu" babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa. Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace "ga abinda suka kawo" Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace "wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba" Kawu Isa yace "nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru" Inna tace "ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba" Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace "tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu'a shikenan". Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi. Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message "save the date. 25th August" [1/12, 20:44] ***: *🎶 Diyam🎶* *2nd Edition* *Maman Maama*