Episode Sixty Nine: Karma
by @mamanmaama
A ranar da yamma su Diyam suka dawo Kano. Da kyar Diyam take iya bude idanunta a jirgi saboda baccin da yayi yawa a cikin su, ganin haka ya sa Sadauki ya daga armrest din tsakanin kujerun su ya jawo ta ta kwanta a kan cinyarsa ya zagaye ta da hannayensa tayi ta baccin ta tana jin daɗin dumin jikinsa. Sai da zasu sauka sannan ya tashe ta, suna fitowa already daya daga cikin office drivers dinsa yana jiransu ya dauke su ya kaisu gida. A gidan ma Diyam sallar magrib kawai tayi ta hau gado ta cigaba da baccin ta, Sadauki shima yana dawowa daga masallaci yayi musu order dinner sannan yayi joining dinta a gado suka yi ta baccin su. Bacci yi mai nauyi, ba su suka tashi ba sai after 10pm. Sadauki ne ya fara farkawa, yayi juyi sannan ya bude idonsa yana kallon dakin yana kokarin dawo da tunanin sa guri daya, sai kuma yayi murmushi irin murmushin nan mai shiga har cikin zuciya, ya saka hannunsa yana shafa hannunta da yake zagaye da ruwan cikinsa, assuring himself cewa ba daya daga cikin mafarkan sa bane ba, Diyam din ce dai a kwance a tare da shi a matsayin matarsa ta sunna. Ya juya sosai yana kokarin daidaita fuskarsa da tata, ta dan motsa kadan tana kara shigewa jikinsa tare da kara karfin rikon da tayi masa, ya ɗan yi murmushi mai sauti yana jin dadin love languages din ta, idan da akwai abinda yake da tabbas akan sa bayan cewa zai mutu shine Diyam tana son sa, ya sani dama tun can amma a cikin kwana biyun nan ya kara tabbatar wa da kansa hakan. And one of the greatest pleasure in life is to love someone who equally loves you back. Ya saka hannu yana gyara mata gashin ta da ya zubo ya rufe kusan rabin fuskarta. Ta bude idonta a hankali ta sauke su akan fuskarsa da har lokacin take cike da murmushi, ta bata rai amma fuskarta ta kasa boye farin cikin da ganinsa ya saka ta a ciki "ni bacci....." Ya hura mata iska a ido, "shi baccin nan ba zai kare ba ne?" Ta sake bude idon murmushin yana karasa replacing bata ran da tayi "to ai baka bari na inyi baccin sosai shi yasa na kasa gamawa" ya bude ido "ni ɗin? Baiwar Allah yaushe na hana ki bacci?" Ta fara lissafawa da yatsun hannunta, "shekaran jiya, da jiya, da yau ma gashi ina bacci na ka tashe ni" yace "shekaran jiya gaisawa muka yi, irin zumuncin nan na tsakanin yan uwa, jiya kuma na kula da ke ne a matsayin ki na bakuwa a garin da baki san kowa ba, I was only showing you around, y anzu kuma ba tashin ki nayi ba juyo wa nayi in kalli fuskarki and assure myself cewa you are mine, ba wai imagining these two days nayi ba. These two days Diyam, are the greatest days of my life" ta sunkuyar da idonta kasa sannan ta jawo hannunta daya daga bayansa ta dora shi akan bare chest dinsa tana wasa da gashin da yake kwance a kai sannan tace "they are the greatest days of my life too" ya sake sunkuyo da kansa yana kokarin kallon idonta yace "and?" Bata kalli idonsa ba tace "and I love you too" ya kuma cewa "and?" Tace "and yunwa nake ji, duk an bi an zuƙe min duk wani energy na jikina" Sai ta ja gashin da take wasa da shi da karfi ta kuma mike da sauri tana dariya, amma kafin ta bar gadon sai jinta tayi ta dawo kan kirjinsa sannan ya saka hannayensa duk biyun ya matse ta kamar zai saka ta a cikin kirjin, tayi ƙara tana kokarin kwatar kanta amma sai ya kara karfin rikon da yayi mata yana dariya manly yace "wa kike wa rashin kunya?"ta marairaice murya "ba da kai nake ba fa, da gado nake" yace "to ki baw a gadon hakuri, kinsan dai ya fiki girma ya kuma fiki karfi, in yace zai zane ki kuma ba zan tare miki ba" tace "Gado Allah ya baka hakuri wallahi ba zan sake ba" still yana dariya yace "kice masa yaya gado na tuba ba zan sake ba" sai ta saka hannayenta duk biyun tayi masa chakulkuli a gefen cikin sa, ya cika ta da sauri yana kyalkyala dariya tare da matsawa gefe, wannan ya bata damar mikewa da sauri ta sauka daga kan gadon itama tana dariya, sai kuma ta kalleshi tayi masa gwalo tace "anki ace maka yaya din, sholoki" ya mike da sauri amma kafin yazo inda take tayi sauri ta shige toilet ta rufe kofa. Sanda ta fito baya dakin, tayi sallar isha sannan ta shafa mai da turaruka masu daɗin kamshi ta kuma saka kayan bacci amma kuma tana jin kamar ba zata iya yin bacci yanzu ba dan tayi bacci mai nauyi dazu, tana shiryawa a ranta tana tunanin abinda zasu ci dan tana jin yunwa ta san kuma shima haka. Sai dai tana kokarin fita kenan shi kuma ya shigo hannayensa rike da tray mai dauke da abinci da drinks a kai, shorts ne a jikinsa kamshin da yake yi shi ya tabbatar mata da cewa shima wankan yayi, gashin kansa yana kyalli kamar yadda fuskarsa take fitar da annuri. Ta bude ido tana kallonsa sannan tayi sauri ta karba ta ajiye tace "don't tell me......" Yayi saurin cewa "bani na dafa ba. Na riga na amince cewa ban iya dafa abinci ba. Na san kin gaji ba zaki iya girki ba and we are yet to hire a cook shine na aika a kawo mana a gurin da nake siya sanda ina........" Bai karasa ba ganin yadda take kokarin rike dariya sai kuma yace "don't laugh!" da dariya shima a muryarsa, ta saki dariyar da take rikewa sannan tace "sanda kana gwauro" ya harare ta "in na kama ki ko?" Ta zauna a gaban abincin ta fara bubbudewa, wainar shinkafa ce da farfesun naman rago, sai white rice da wani hadin gas meat na musamman. Ya zauna shima a gefenta yana kallon ta tana zuba abincin sai tace "tell me about it. About been gwauro. How do you cope". Farko kamar ba zaiyi magana ba, sai da ta dauko abincin da hannunta ta saka masa a bakin sa sannan yace "it was easy, taking care of myself was easy, though I missed Umma and Baffa alot, I still do. The hardest part was the constant feeling of emptyness in the heart, accepting that I could never have what I wanted" sai kuma ya danyi murmushi tare da rike hannunta da ya kai abinci bakinsa yace "yanzu gashi I am having it all and more" Tana kallon sa tace "ko scratch baka samu ba daga cikin abinda kayi deserving, ina da burin treating dinka as the king that you are, ba wai king din gari bane ba kai na zuciyar Halima ne, king ne a cikin gidan ka. Ina da burin mu zame wa junan mu duk abinda muka rasa, da duk abinda bamu da shi" ya ɗaga gira yace "da gaske? Da gaske ko scratch ban samu ba na daga abinda aka tanadar min?" Ta juya ido, "we are not talking about the same thing" ya gyara zama "what are we talking about?" Tace "I am not talking about what you are talking about" yana murmushi yace "ni me nake magana akai to? Haka ranar nan ma fa a waya muna magana sai kika juya maganar kika ce ba ita muke yi ba" ta ajiye abincin hannunta da ta debo da niyyar bashi ta fara bayani "ni kulawa nake magana akai da nuna soyayya da kuma tarairaya da biyayya da sauran su" still yana murmushi yace "sauran su.... Su menene sauransu?" Ta bata rai "mu bar maganar, kana sane ai" ta sake saka masa abinci a baki, yana taunawa idonsa yana kanta yace "dama lokacin nayi wani alkawari, cewa zan fito da maganar daga bakin ki complete dinta, kuma so far har yanzu banji ta ba. Yau kam I will get it out of you dan kin san bana saba alkawari idan nayi shi". Ta sunkuyar da kanta tana jin kunyar kallon da yake mata, sai ya kasa dogayen yatsunsa guda biyu ya dago fuskarta yana kallon cikin idonta yace "feed me". Ta dauke idonta daga cikin nasa tana jin hannunta yana dan rawa kadan, ta zuba lemo a cup ta kai bakinsa, sai ya hada har hannun nata ya rike yana shafa hannun. Tayi kokarin zame hannun amma ya hana tace "in baka saki hannuna ba bani da wanda zan baka abincin dashi, tunda dai babu kyau cin abinci da hannun hagu" ya saki hannun yace "to gashi nan na baki aro, only because ni zaiyi wa amfani" tayi murmushi ta cigaba da bashi abincin itama tana ci dan tana tsoron kar ya karasa rikice mata ya hana ta cin abincin, kuma tana kokarin yi masa hirar da zata dauke hankalin sa daga kan abinda yake ransa for the mean time, sai kuma ta samu sukayi hirar sosai, hirar sanda yana gwauro da kuma yasha wahala kafin ya kafa Abatcha motors da yadda har yau yake shugabancin gurin with iron fist, a lokacin ne tasan how much Abatcha motors was worth, da kuma plans dinsa for the future of the company. Sai ta samu ta jejjefa shawarwarin da take ganin zasu taimaka masa duk kuwa da cewa ita ba ilimi ne da ita akan harkan business ko managing company ba, amma daga yadda taga yana gyada kai sai ta fahimci akan dai dai take. A haka har suka gama cin abincin, suna ta hirar su kamar su biyu ne kadai a duniya, basu damu da lokacin da yake ta wucewa ba kamar yadda basu damu da duk wasu abubuwan da suka faru a baya ba, abinda yake a lokacin shi suka fuskanta da kuma abinda suke saka rai tare da fatan zai faru nan gaba. A cikin hirar ne Diyam ta kwanta a kasa ta dora kanta akan cinyarsa, shi kuma sai ya jawo ta ta zauna sosai akan cinyarsa fuskarta akan kirjinsa yace "much better" amma kuma haduwar jikin su sai ta saka hirar ta tsaya, maganganun suka kare, a dole suka hakura suka mayar da hankulan su gurin biyan bukatun jukkunan su da zuciyoyin su. Bukatun da zuwa lokacin sun tabbatar wa da kansu cewa ba masu karewa bane ba kamar yadda soyayyar su ba mai karewa ba ce ba. Sai da suka yi sati biyu a gida babu wanda yaje ko gate a cikin su in banda masallaci da Sadauki yake zuwa, babu abinda sukeyi sai karba da kuma bayar da soyayya ga junan su, in suka zauna hira sukan yi kamar best friends din da suka shekara basu hadu ba, idan kuma suna wasa da junansu zaka dauka siblings ne sa'annin juna, and then there was that constant insatiable desire for each other, duk wata magana da Sadauki yace zai fitar daga bakin Diyam sai da ya jita, kamar yadda itama taji maganganu daga nasa bakin da suka saka ta ji a ranta kamar tafi duk sauran mata, ko ba a gurin duk maza ba to kuwa tabbas a gurin mijinta. Duk irin tanadin da Diyam tayi wa Sadauki sai da ta fahimci ya wuce duk inda take tunani, sai ta kasa tantance a tsakanin su waye yafi ɗokin ɗanuwansa dan sosai itama take kokarin cire kunyarta ta tari duk bukatar da yazo da ita. Wannan yasa ranar nan ta dauki wayar ta ta kira Maman Iman, bayan sun gaisa tace "uhmmm. Dama cewa nayi bara in tambaye ki wannan bita zai zai din da kika bani ranar nan, har yanzu yana nan?" Maman Iman tayi dariya sosai kamar yadda itama Diyam din tayi dariya sannan tace "ke da kika ce min ba kya so? Me ya chanja kuma yanzu?" Ta tambaya cikin tsokana dan duk ta fahimci rashin soyayyar da aka samu a wancan auren na Diyam da kuma soyayyar da take cikin wannan auren. Diyam ta daina dariyar da take sannan tace from the bottom of her heart "komai Maman Iman, komai ya chanja, komai ba daya bane ba. Yanzu ina so ya manne min kamar super glue" Maman Iman ta sake dariya tana jin d adi a ranta sannan tace "to alhamdulillah, yanzu zaki fahimci duk hanyar da nayi ta kokarin nuna miki kina rintse ido, kar ki damu kafin ku koma england zan kawo miki ba bita zai zai kadai ba har da manta uwa zan hado miki" suka sake dariya tare sannan suka cigaba da hirar su akan hanyoyin faranta ran juna a cikin aure. Sai da Diyam ta kwana 15 da tarewa sannan Inna ta bar Asma'u tazo ita da Subay'a, shima dan Sadauki ne da kansa ya aika da mota aka dauko su, ranar Subay'a kamar zata zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman saboda ganin dakin da aka ware a gidan saboda ita. Diyam kuma sai ta dauko gifts din data samu a Maiduguri ta ware wadanda take so sannan sauran ta hada da wasu daga cikin kayan lefen ta ta bawa Asma'u tace ta kaiwa Inna a raba wa yan'uwa, cousins dinta duk kowa sai daya samu wani abu. Asma'u kam sai data debi rabonta dama tun kafin ta bar gidan. A lokacin ne Diyam ta fahimci cewa Asma'u suna waya da Bassam, she did not comment, idan hakan suke so to ita kam sai dai ta taya su da fatan alkhairi. Sati uku bayan bikinsu hutun su Diyam ya kare, ta dauka zasu yi drama da Sadauki akan komawarta amma sai taga shine ma mai taya ta lissafi. Da lokaci ya matso sai taga ya fara hada nasa kayan shima. Tace "aikin fa? In ka bini wa zai kular maka da companyn ka?" Yace "my dear Halima. Kin manta I managed my company for the five years din da nake karatu? Ko kin dauka zan bar ki ki tafi ki barni ne?" Tayi dariyar yadda ya fadi maganar kamar wani yaro. Amma kuma ta ji dadi a ranta dan ba karamin faduwar gaba take yi ba a duk lokacin da ta tuna cewa zata koma England school ta bar Sadauki a Nigeria. Dan ba karamin sabawa tayi da shi a kusa da ita ba. Ta zo ta zauna akan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta ta saka fuskarta a wuyansa tana dan bubbaga bayansa tace "kar kayi kuka, bazan tafi in barka ba kaji habibi" ya shafa mararta yace "habibi yana cikin nan gurin a kwance" ta zaro ido tace "ba wani nan" yace "to ni dai banga kinyi period ba" tace "sati uku ne fa kadai" yace "koma kwana uku ne, ni ai nasan irin shukar da nayi kuma nake yi so nake inga na fara girbi" ta boye fuskarta a wuyansa tace "kai dan Allah, sai kace wata gona? Ni bani da komai Allah. Kuma ma ai kaga karatu nake yi yanzu ko? Ko so kake in ke faduwa exams dina?" Ya dago fuskarta yace "tare zamuyi karatun ai, muna yi kuma muna cigaba da planting seeds din mu, kafin mu gama karatun in Allah ya taimake mu sai mu girbi ko da biyar ne" ta zaro ido "biyar fa kace? Sai kace kaza?" Sukayi dariya tare. Yace "biyar din ma rage miki nayi ai dan kar ki sha wahala da yawa, in za'a bani zabi twins nake so duk shekara. In akayi twin boys sai ayi girls, sai a sake boys a sake girls, kinga a shekara hudu anyi takwas kenan" ta mike da sauri tana cewa "in yaso a shekara ta biyar sai inga an shigo min da amarya ko" ya jawo ta ta fado jikinsa, ya gyara mata zama tana facing dinsa yana tracing jawline dinta da finger dinsa yace "you my dear have no idea how much son ki ya cika zuciyar Aliyu ko? Shin ina gurin da zan saka wata a cikin zuciyar da bani ne mamallakin ta ba?" Ta turo baki duk kuwa da cewa taji dadin maganar tace "daɗin baki. So kake kayi min daɗin baki" yace "au baki na yana da dadi dama? Ai ban sani ba nasan dai naki yana da mugun dadi" ta murguda masa baki sannan tana kallon lips dinsa tace "Let's taste and find out na waye yafi dadi". Tafiyar su tazo dai dai da hutun su Subay'a. Dan haka Sadauki yace zasu tafi da ita da Asma'u suyi musu hutu a can kuma su taimaka musu gurin settling a sabon gidan su. Murna gurin Asma'u kamar zata tashi sama dan dadi, Diyam tana kallonta tace "kina murnar zaki je England ne ko kuma kina murnar zaki je gurinsa?" Asma'u tayi saurin yi mata signing akan tayi shiru kar Sadauki yaji. Diyam ta daga murya tace "eh, Bassam da kuke waya dashi Asma'u nace kinga kuwa a can yake karatu, nasan zaku ke haduwa in kinje" Sadauki yayi saurin juyowa daga kallon news yana kallon su yace "Bassam, menene hadin Yar asama da Bassam?" Diyam ta nuna ta tace "gata nan, tayi maka bayani". Asma'u ta fara kame kame tana rarraba ido, ya kalle ta strictly yace "bana son shashanci, idan yana sonki da gaske yazo ya same ni first kafin ya cigaba da neman ki. I know his family, amma shi din zan saka a bincika min halayensa in kuma basu yi min ba kin gama ganin sa kenan. Kinji abinda nace?" da sauri Asma'u ta gyada kai. Ranar dasu Diyam suka sauka a ranar ne suma su Fanna suka zo. Sun taho gabaki dayansu da sisters dinta dan su taya su Diyam tarewa a sabon gidan su. Gidan da Diyam taga kamar yayi musu girma dan haka ta saka aka rufe part din matar gida suka zuba kayansu a part din maigida ita da Sadauki. Sai bangaren yara kuma anan Fanna zata zauna tare da Judith din da Diyam ta kuma gayyatowa. Daga nan kuma sai gurin ma'aikatan gidan wadanda dama suna nan already, mai kula da tsaftar gidan, mai abinci da mai gadi. Sadauki yana shafa cikin Diyam yace "saura Nanny, kinsan guda biyu ne sai mun nemi taimako" Diyam ta juyo ta harare shi amma kuma itama ta fara zargin shukar sa ta fara tsiro dan babu period babu labarin ta. A cikin kwana biyu aka gama settling komai tunda dama anyi sabon penti tun kafin su zo, a ranar suna zaune gabaki dayansu matan a sitting room suna hira sai Sa'adatu take basu labarin abinda Papa ya gaya musu kafin su taho daga Canada, cikin kwaikwayon muryarsa tace "ke Sa'adatu da ke Falmata, ku fito da miji ayi muku aure hakanan, tunda naga karatun nan naku ba karewa zaiyi ba" duk suka kwashe da dariyar yadda tayi maganar, Diyam ta harare ta tace "yanzu haka baban nawa yake magana?" Falmata ta bude hannu tace "yanzu fi sabilillahi ni ina naga mijin da zan fitar? Ni ina naga saurayin ma? Samari fa basa kula mu" Fanna ta gyara zama tace "basa kula ku dai, ku da kuke musu girman kai, ki zo in koya miki yadda ake jawo hankalin namiji komai girman sa komai ji da kansa". Anan Sadauki ya bude kofar bedroom ya fito ya tsaya yana kallon su, duk suka yi tsuru-tsuru saboda basu san yana cikin daki ba sai Diyam ce kawai ta sani. Bai ce musu komai ba sai ya dauko wayarsa yayi dialing sannan yace "hello Papa" ya gaishe shi yace "maganar nan da ka yiwa su Sa'adatu, ina ganin a hada harda Fanna itama. Okay. Insha Allah. Thank you Papa. Love you too" ya juyo yana kallon Fanna yace "ke ma ki fito da naki. Gaba daya guri na zasu fara zuwa first, sai nayi approving sannan zasu je gida" bai sake cewa komai ba ya saka hannayensa a aljihu yayi tafiyar sa. Fanna ta zamo daga kan kujera ta fado kasa tana birgima dramatically, tace "wallahi yau na kara tabbatar wa yaya Aliyu baya so na" su kuma duk suna tayi mata dariya. Diyam tace "Alhamdulillah. Zuciya ta fess yau. Karyar tara samari ta kare. Satin su Sa'adatu daya suka koma. Su kuma su Asma'u sai da sukayi wata daya sai da hutun su ya kare sannan suka koma gida. Washegarin da suka tafi ne da assuba Diyam tana karatun Alkur'ani akan sallaya sai ga Sadauki ya dawo daga masjid. Ya zauna akan gado yana kallonta har ta idar sannan ta mike ta hawo kan gadon ta kwanta ta lulluba yace "ni fa har yanzu banga tazo ba" bata kalle shi ba tace "wacece zata zo? Bakuwa zaka yi?" Ya yaye rufar yace "yau ba zaki yi baccin nan ba sai kin gaya min akwai ko babu" ta fara yi masa shagwaba "ni me zan gaya maka. Ni babu abinda zan gaya maka" ya cire rigar da yaje masjid da ita yayi astriding dinta yace "ko ki gaya min ta lallami da lumana ko kuma ki gaya min in kinji wuya" ta fara dariya, ya sakar mata nauyinsa shima yana dariya, tayi kokarin ture shi ta kasa sai ya rike hannayenta duk biyun da hannunsa daya, yace "akwai ko babu?" Tace "to ni yanzu me kake so ince maka" yace "cewa zaki yi 'sadauki kayi min ciki" ta kwace hannunta da sauri ta rufe fuskarta tace "la ila, wai kai baka jin kunya ne?" Yana dariya yace "ina ji mana, ina jin kunyar mutane amma bana jin kunyar matata" tace "ni dai bazan iya fada ba" yace "to kinga, in akwai ki gyada kanki, in babu ki girgiza kanki" tayi shiru, yace "akwai ko babu?" Ta bude ido tana kwallon sa ta miko masa hannu tace "kawo tukuici" yace "say it, duk abinda kike so, anything" ta rufe hannun tace "in ka kawo tukuici sai kazo a gaya maka" yace "a bani bashi zan biya" ta turo baki "har yau fa baka biya ni bashin kaza ta ba kuma kake neman a kara maka wani bashin?" Ya dafe kai "wannan kaza, wannan kaza. Yanzu duk kajin gidan nan amma ban biya ba?" Tace "waccan special ce" Ya mike ya saka rigarsa. "Zan siyo miki kaza yanzu, zan kuma kawo miki tukuicin ki". Sai daya loda rigunan sanyi a jikinsa saboda sanyin da ake yi a waje, gashi kuma gari bai ko gama wayewa ba amma haka ya fita, da kyar ya samu kazar saboda duk eateries din kusa dasu basu fito ba sai da ya shiga cikin gari sosai sannan ya samu, ya siyo mata chocolates duk wadanda yasan tana so leda guda sannan ya dawo gida. A gado ya same ta har lokacin ta lulluba tana baccinta. Ya zauna a gaban gadon ya bude ledar gasassun kajin ya yanko cinya daya ya bude fuskarta ya kai naman kusada fuskata, ta motsa idonta sannan ta bude idon cikin nauyin bacci tana kallon naman sai kuma ta kai hannu da sauri zata karba sai ya janye yace "kwadayayyiya. In kina so sai kin fada min abinda nake son ji, akwai ko babu?" Ta tashi zaune ta leko tana kallon naman kajin daya bude ya cika dakin da kamshi ga kuma chocolates din daya zube a kasa suma. Sai ta kalleshi ta gyada kai da sauri ta koma ta kwanta ta rufe fuskarta. Wannan ciki na Diyam ya sha gata, gayu da soyayya a gurin sabon shiga Sadauki. Rigimar da tayi tunanin zasu yi akan komawarta school basu yi ba sai yanzu akan zuwa school da ciki. "Idan kuma kika fara rashin lafiya a can fa? Ko kuma in kina son ki kwanta ki huta babu gurin kwanciya? In zaki yi amai fa? Ko kuma kina sauri kin makara ki gurde ki fadi" tana dariya tace "baban baby kenan" yace "babies, kar ki rage min daraja mana" tace "okay baban babies. Wannan cikin fa ba me laulayi bane ba, dame laulayi ne da ni da kaina zan nemi hutu. Ka barni in cigaba da zuwa please kaga yafi inyi ta zama a gida ko?" Sai da tasha fama da kyar sannan ya barta ta cigaba da zuwa, dan da farko cewa yayi sai dai ta koma online classes. Bayan ya barta ma kuma sai da ya jera mata dokoki. "Banda unnecessary yawo, daga kinji kuma the slightest something ki kira ni, don't act the hero" tayi murmushi tana gyada kai "an gama ranka ya dade". Driving ma Fanna ce take yi, wata rana kuma judith tayi tunda lokacin duk sun iya motar, shima kuma sai Sadauki ya buga musu warning banda gudu "na karanta cewa bumpy ride yana kawo miscarriage ko premature labor" ya fada wa Fanna yana jaddada muhimmanci maganar sa. Suna daukan hanya Fanna ta maimaita abinda yace tana kwaikwayon maganar sa "bumpy ride yana kawo miscarriage" duk suka kwashe da dariyar yadda ta bude makogwaro wai tana so tayi irin muryarsa. Ta juya idonta tace "wannan baby in aka haife shi ina jin ko daukan sa ba za'a bar mu muyi ba dan kar mu shafa masa rashin jin magana or something like that". Bayan karatu babu abinda Diyam take yi sai dai taci ta sha ta kwanta tayi bacci sannan ta kula da mijinta, wanda sun rasa gane a cikinsu waye yafi kula da danuwansa. Kullum tamkar kara musu kaunar junansu ake yi. A lokacin ne kuma ya bayyana mata abinda yake shiryawa. "Branch nake so in bude na Abatcha Motors anan kasar. Tunda muka zo nake processing abin amma saboda kasancewar ni ba dan kasa bane ba sai na kasa samun permit na bude Company, but alhamdulillah yanzu na samu" ya dauko takardar ya nuna mata, ta karba tana karantawa yace "har na sayi fili ma a yanzu zan fara gina gurin tukunna sai in dauki ma'aikata insha Allah" ta rungume shi cikin jin dadi tace "congratulations King. Allah ya cigaba dayi maka jagora" ya zagayo da ita gabansa yace "ameen Queen. Yanzu problem din shine, bana son harkar bude wannan branch din ta saka ni in kasa saka ido akan wancan, though lafiya lau komai yake tafiya a can din but I need an assistant, someone that I can trust to help me manage there". Tayi shiru tana tunani sai tace "Alhaji Bukar bashi da ya'ya? Kayi masa magana mana ya hada ka da mafi aminci a cikin yayansa kaga shima zaiji dadin ka karrama shi" yayi murmushi mai kyau sannan yayi kissing forehead dinta yace "that is one of the reasons I love you, saboda kina da tunani mai kyau. You know what? Kema na baki aiki" ta bata rai tace "wanne aiki kuma bayan wanda already nake dashi?, na matarka?" Yace "you are now my special advisor" tace "duk dai part of my job ne as your wife". Koda yaushe Diyam tana lissafin Saghir a ranta, amma bata taba yiwa Sadauki maganar ba saboda bata son taba masa zuciya, duk kuma sanda suka yi waya da Subay'a sai tayi mata maganar sa, duk da cewa Inna tana yawan kaita ta ganshi. Shima Sadauki bai taba yiwa Diyam maganar Saghir din ba amma shima Subay'a bata barshi gurin tambaya ba. A lokacin dasu Diyam suka kammala second semester dinsu a lokacin cikinta yana da watanni biyar, a lokacin kuma Sadauki har ya kammala ginin sabon branch din Abatcha Motors. Cikin Diyam ya dan fito kadan amma baiyi girma sosai ba, abinda ya fito sosai shine kyawunta, dan sanda suka fito daga jirgi a malam Aminu Kano international airport ita da Sadauki hannayensu rike dana juna, duk wanda ya kalle su sai ya sake kalla. Gidan Inna suka fara zuwa, a can suka ci abinci suka huta Diyam tana ta jin kunyar cikin jikinta, anan Sadauki ya barta sai dare yazo zai dauke ta amma sai tayi ta rokonsa ya barta ta kwana biyu a nan. Da kyar ya barta bada son ransa ba sai dai yana fita Inna ta kora ta ta bishi, tace "mijinki yan a garin zaki kwana gida? Ki bari in yayi tafiya sai ki zauna ko kwana nawa ne kiyi mana" amma sai ta dauki Subay'a ta tafi da ita. A week after that, ya dawo daga office sai taga mood dinsa ba shi da kyau, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya zauna akan kujera tare da lunshe idonsa. Ta zauna a hannun kujerar tana shafa fuskarsa tace "wanka ko abinci?" Ya dan bude ido ya kalleta yace "bara in dan huta tukunna" sai ta sauka ta durkusa a gabansa ta cire masa takalmi ta hada da briefcase dinsa ta kai sama ta dawo ta sake zama a gabansa ta cire masa safar kafa ta dora kafafun a kan cinyarta tana mammatsa masa su a hankali tare da jan yatsun kafar. Ya dan janye kafar yana cewa "ke! Chakulkuli fa kike min" ta sake jawo kafar tace "tausa fa nake yi maka, haka ake chakulkulin?" Sai tayi masa chakulkulin gaskiya a tafin kafarsa, Yayi dariya yana tashi zaune sosai ya janye kafarsa, sai ta mike tayi kneel down tana murmushi ta faki idonsa ta saka hannunta cikin rigarsa tayi masa chakulkuli tana cewa "gana gaskiyar nan nayi maka to" ya fara kokarin cire hannunta daga rigarsa yana dariya har da zamowa kasa, ya jawo ta suka fadi tare, sai shima ya yi mata yana cewa "sai na rama wallahi" ta kama kyalkyata dariya tace "wayyo zan mutu, ka bari wallahi, chakulkuli fa kanin mutuwa ne" ya sake ta ta janye daga jikinsa da sauri tana dariya, yace "kinci sa'a bake kadai bace ba" Ta murguda masa baki sannan ta dawo kusa da fuskarsa tace "wanne mai tsautsayin ne ya taba min King dina" ya danyi tsaki yace "mutane, yanayin rayuwa, cin amana. Babu abinda wasu mutanen ba zasuyi ba saboda kudi. Babu wanda ba zasu ci amana ba akan kudi. I don't know mai mutanen mu suka mayar da kudi, abinda zaka iya samu yau gobe ka rasa, abinda zakayi bayani a lahira dalla dallar yadda akayi ka samu. Abinda zaka kare rayuwarka kana tara wa kuma ka mutu ka barshi". Tace "me ya faru?" Yace "Saghir zai fito next week insha Allah" taji dadi har cikin ranta amma sai ta boye ta danyi murmushi tace "alhamdulillah. An samu Kabir din kenan?". Yace "tun kafin ku koma school ake neman Kabir an kasa kama shi, iyayensa sunki bada hadin kai dan haka ba'a san sanda yake shigowa gari ba ballantana sanda yake fita, nayi nayi abu ya gagara, daga baya ma sai na samu labarin wai ya kwashe iyalansa daga kano sun koma kaduna da zama baki daya. I told Ahmad amma sai yace ba zai iya kama shi a kaduna ba saboda kaduna ba a ikonsa take ba, in dai zai kama shi a can sai yana da arrest motive da zai nuna wa commissioner of police na kaduna, kuma a lokacin babu wani motive na kama Kabir tunda zargi kawai akeyi babu shaida. Sai nayi tunani a kan wani abu, nayi tunanin yadda son kudi ya kai Saghir inda yake a yanzu, na kuma tuna yadda son kudi ya saka abokinsa yayi framing dinsa, sai na tuna maganar hausawa da suke cewa sai hali yazo daya ake abota, da kuma maganar bature da yace birds of the same feathers flock together, sai na saka aka bincika min wanene next friend dinsu su biyun, sai aka hada ni da wani Bashir, kin sanshi?" Diyam ta gyada kai, yace "ranar da muka zo gari na kira shi nace ya same ni a office dina, and he came, na gaya masa abinda Kabir yayi wa Saghir na kuma nemi ya taimaka mana mu kama Kabir din, farko sai yaki, but then as I expected sai ya fara bargaining, ya fadi kudin da yake so in bashi in ina so ya fada mana sanda Kabir zai shigo gari da kuma inda za'a same shi. I told him in yana so in bashi kudi sai dai yayi making Kabir yayi confessing cewa shi yayi framing Saghir and he agreed. I gave him some money and promised him some in na samu abinda nake so. Yau sai gashi ya dawo, can you believe he got Kabir drunk ya ringa yi masa questions yana amsawa shi kuma yana recording? It hurts me cewa duniya tayi lalacewar da friend zai iya yiwa friend dinsa haka, but considering abinda shima Kabir din yayi sai naga yayi deserving shima ayi betraying dinsa" "Nayi submitting record din to Ahmad shi kuma ya bawa NDLEA copy, yanzu zasu iya shiga har Kaduna su kama Kabir, and Saghir is coming out latest next week". [1/12, 20:44] ***: *🎶 Diyam🎶* *2nd Edition* *Maman Maama*