Bayan Murmushi

67

by @zahrabmrs02

67

Komawar su Massachusetts a wannan karon ta zo da wani irin salo mai dadi wanda Farhana ba ta taba tsammani ba. Tun a cikin jirgi, AK ya nuna mata cewa "New AK" ya dawo. Kulawar da yake ba ta, da yadda yake damuwa da jin dadinta, ya sanya ta fara jin cewa kaddarar su ta sauya.

Satin su na farko, AK ya ki komawa ofis. "Ina bukatar hutu da iyalina," abin da ya fada wa Sakatarensa kenan a waya. Farhana tana kallo, AK ya koma tamkar wani bawan su .Kullum da safe, shi ne yake tayar da yaran, ya yi musu wanka, sannan su fito falo don su karya tare. Farhana ta zama tamkar sarauniya; babu Hanadi, babu Yaya Ramla, babu bacin rai.

Ranar Laraba, AK ya bukaci su shirya su nufi wani babban Park dake yankin Boston ,rabon su da zuwa park din tun tana amarya Farhana ta sanya wasu tattausan kaya na sanyi (sweaters) masu kyan gaske, ta yi wa yaran ado na alfarma. Suna isa, AK ya koma tamkar wani yaro; ya rinka guje-guje da Lamido da Sultana a kan ciyawa, yana tura su a jikin swings.

Farhana tana zaune a kan benci tana kallon su, tana murmushi wanda ya fito daga asalin zuciyarta. AK ya nufo ta, fuskarsa cike da gumi amma yana dariya. Ya zauna kusa da ita, ya kamo hannunta.

"Wifey , na gano cewa babu abinda ya kai zaman lafiya dadi. Na yi kuskure a baya, amma ina so mu fara sabon babi a nan USA ," ya fada yana kallon cikin idanunta.

A ranta, Farhana ta ji wani irin sanyi. Ta dade tana jiran wannan

Murna ta kara ninkuwa lokacin da Hailey ta kira Farhana tana sanar da ita bikin zagayowar ranar haihuwar danta, Kevin. Wannan rana ta kasance ranar haduwar abokai. Su Isabella duk sun hallara a gidan Hailey.

Sultana da Lamido sun yi kyau sosae a cikin sabbin kayan da Farhana ta siyo musu. A wajen taron, AK ya ba kowa mamaki. Ya taya Hailey shirya wasu abubuwan, kuma ya rinka wasa da yara kamar shi ne ya haifi kowa a wajen. Hailey ta kalli Farhana, ta rada mata a kunne:

"Farhana, your husband has changed! Gaskiya kinyi sa'ar miji."

Farhana ta gyada kai, tana jin wani irin alfahari. Gidan ya cika da dariya da nishadi, inda yara suka ci cake suka yi wasa har suka gaji. Wannan daren, Farhana ta kwanta da babban kwarin gwiwa cewa rayuwar su ta kusa zama abin. Ranar Litinin ta zo, ranar da AK dole ya koma ofis. Ya shirya tsaf cikin shigar sa ta alfarma, ya sumbaci kowa ya fice.

Farhana ta fara shirye-shiryen ta na karshe domin ta tafi Flight School ta karasa rajista, tunda mako na gaba ya kamata su fara karatu gadan-gadan. Tana tsaka da hada takardu, ta ji kukan Lamido ya canza sauti. Ta nufi dakin da sauri, ta same shi ya lafe a gefen gado, yana wani irin nishi. Taba fuskarsa da za ta yi, ta ji tamkar ta taba garwashin wuta.

"Innalillahi wa Inna Ilaihir Raji'un!" Farhana ta kira sunan Allah cikin razana.


Cikin kankanin lokaci, numfashin Lamido ya fara sarkafe wa. Farhana ba ta tsaya wata-wata ba, ta kira Briana suka nufi babban asibitin dake kusa da Massachusetts General Hospital. Suna isa, likitoci suka karbe shi da gaggawa domin yanayinsa ya riga ya tsananta.

Farhana na zaune a corridor din asibiti, Sultana na kuka a hannunta, zuciyarta na bugawa. Ta kira AK a waya, muryarta na rawa.

"Papa Twins... Lamido ba shi da lafiya. Muna asibiti yanzu haka!"

AK bai tsaya tambayar me ya faru ba, ya bar taron da yake yi ya nufo asibiti a guje. Yana isa, ya iske Farhana ta zabge, fuskarta tayi jawur saboda kuka. Ganin guda daya tilon dansa  da yake takama da shi a matsayin magaji yana cikin wannan yanayin, ya sanya AK jin kamar jikinsa zai dauki zafi shi ma.


A wannan ranar ne kuma ya kamata Farhana ta karasa takardun ta na karshe a Flight School (makarantar koyon tuka jirgi). Ta kalli wayarta, tana ganin kiran Isabella dake jiran ta a makarantar, sannan ta kalli dakin da aka kwantar da Lamido.

"Ina son zama Pilot, amma Dana  ya riga komai," ta fada a ranta yayin da take kashe wayar.

Dole ta hakura, ta ajiye burinta a gefe guda domin ta kula da babban amanar dake gabanta. Wasa-wasa, zazzabin Lamido ya ki ci, ya ki cinyewa. Gwaje-gwaje sun nuna cewa jikin yaron ya dauki wata irin infection wadda ba a gane asalin ta ba nan take.


Zaman asibiti ya kusa kwashe wata guda. Farhana ta zabge, idanunta sun yi luhu-luhu saboda rashin barci. AK ma ya daina komawa ofis, duk wani taro na kasuwanci ya soke shi domin ya zauna kusa da Lamido. Wayoyinsu ba su daina ƙara ba tun daga 

Su Isabella ma kullum suna cikin zarya ,su da Briana ke kula da sultana ,suna gefen ta a asibiti ,ba abinda zata ce masu sai godiya 


Abbi a kullum sai ya kira  Farhana . "Maryama, kiyi haƙuri, jarrabawa ce daga Allah. Mun sa an muku saukar Kur'ani a nan gida."

Farhana ta share hawaye, "Nagode Abbi, don Allah ku taya mu da addu'a."

Nene kuma ta kira AK, muryarta cike da fada da tausayi. "Abdulkadir, na ce maka ka kula da yaron nan. Hassada ce ta biyo ku har can. Ga maganin zan  turo  a gwada na gida ko zaa dace 

Mahaifin AK shi ma baa barshi a  baya ba. "Abdulkadir, yaya mai jiki? Na yi magana da likitocin asibitin, sun ce ana samun cigaba. Ka kwantar da hankalinka, komai zai wuce."



Diddi ta kira Farhana tana kuka. "Maryam kiyi haƙuri, inshaAllah Lamido zai tashi."

Yayyen Farhana gaba dayansu kiran su na ƙarfafa gwiwa ne. "Maryama, ki daina kuka. Ke uwa ce, idan kika karaya yaran ma za su karaya.

Fadila ma ta kira AK tana kuka, "Yaya, don Allah ya mai jiki? Mun kasa barci a gidan nan."Khalil Akwai shiga rai,Allah ya tashi kafadun sa 

Halima ma ta kira Farhana, "Anty Farhana, Allah ya ba shi lafiya. Muna sa ran ganin hotonsa yana murmushi nan ba da daɗewa ba."

Sai ga  kiran fateeha , muryarta na nuna damuwa. "Farhana, kin ga abin da nake gaya miki ko? Rayuwa ba ta da tabbas. Ki dage da addu'a, kuma ki sani ina tare da ke. Karki bari wannan ya dakile miki lissafi."the next day 

Precious ma ta biyo baya da kiran Skype don ta nuna wa Farhana yadda suke addu'a a coci domin samun sauƙin sauki Khalil 

Abdulkadir, ka kwantar da hankalin Ka cewar mummy suna FaceTime da Ak Inda tace a bata farhana Karon farko mummy tayi magana da farhana cikin tsausaywa, ba abin da zai same shi inshaAllah."daga nan ta juya screen din fuskar yaya Safiyya ta bayyana 

Yaya  Safiya ta ba  Farhana shawarar yadda za ta rinka lallashin AK don kada ya faɗi ganin yadda taga Ak ya Koma wani daban yaba yaya Safiyya mamaki ,Nima mai Neman rarrashin nawa nake yaya Safiyya ,farhana ta ayyana a ranta .


Akwai wani kira da ya ba Farhana mamaki—kiran Hanadi. Ranar da Lamido ya shiga mawuyacin hali, sai ga kiran Hanadi ya shigo wayar Farhana.

"Farhana... ya mai jiki?" Hanadi ta faɗa, muryarta ba ta da wani amo na nuna farin ciki ko baƙin ciki.

Farhana ta ja numfashi, "Yana samun sauƙi Hanadi, muna addu'a."

"Allah ya ba shi lafiya. Na kira papa ma ya ce yana tare da ke," Hanadi ta faɗa a taƙaice ta kashe wayar.

Farhana ta kalli wayar, ta san kiran Hanadi ba na ƙauna ba ne, kiran "girma" ne kawai don kada a ce ba ta kira ba.

Amma babban abin da ya fi ci wa AK da Farhana tuwo a ƙwarya shi ne Yaya Ramla. Har aka kusa wata ɗaya, ba ta ɗaga waya ta kira ba, bare ta turo saƙo. Wannan halin nata ya sanya AK ya gane cewa, lallai ashe ba kowa ne yake son ka ba idan kana cikin jarrabawa.