10
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*10*
*10:12pm*
Ƙarfe goma da mintina sha biyu Habib ya shiga falon gidan shi, da ƙishin ruwa ya dawo shi ya sa yana shigowa falon bayan ya kunna hasken wuta.
Da yake Ummu ta kashe komai kafin ta kwanta Kitchen ya zarce yana neman ruwa a firiza amma babu ruwa sai wani guda ɗaya pure water da ya gani a saman kantan kitchen ya ɗauka sha, ya manta bai bar komai a gidan ba, ruwan bai ishe shi ba amma haka nan ya haƙura har zai fita sai ya leƙa store bai yi mamakin ganin kayan abinci ba, daman dalilin da ya sa ta nace ta ƙi tafiya saboda iyayenta sun kawo mata kayan abinci ne tunda daman ta ji daɗin kai shi ƙara wajen iyayenta.
Da gangan ya kwashe kayan abincin shi ya kai gidan su, a tunanin shi ai ba za ta zauna ta mutu da yunwa ba, in ta ga babu komai za ta koma gida ta sanar ma da iyayenta halin da ta ke ciki, su kuma kafin ma su kira shi zai aika mata da takardan sakinta, amma saboda maita da rashin zuciya ba ta tafi ba sai ma aka kawo mata kayan abincin saboda dole ne sai ta zauna a gidan shi, to ya gaji shima zai sauwaƙe ma kan shi ne, gida da man na haya ne kuma shekara ɗaya ne kuɗin hayar kuma na shekaran ya kama gidan saboda biyan buƙatan shi ya kuma samu biyan buƙatan shi to ba zai damu domin ya bar musu ragowan kuɗin hayar ba. A gidan kansa zai gina wata sabuwar rayuwar da ya tanada shi da abar ƙaunarsa.
A fusace ya fito daga kitchen ɗin ya shiga ɗakin da ya ke kwana ya nemo takarda da biro, yana fitowa ƙofar ɗakin da Ummu ke ciki ya shiga bugawa cikin sauri sannan da ƙarfi kamar zai ɓalla ƙofar sannan lokaci ɗaya yana kiran sunan ta.
"Ummu Salma."
"Ke Ummu Salma."
Ya ke faɗa da muryansa a sama lokaci ɗaya yana cigaba da buga ƙofar da karfi.
Kamar a mafarki ta ji bugun ƙofar domin har ta fara barci kanta ke ciwo saboda kukan da ta sha, sai ta sha pracetamol tana idar da sallar isha'i ta kwanta cikin ikon Allah barci ya kwashe ta da man wani lokacin tana samun yin barci a farkon dare amma in ta farka ne yake da matukar wahala ta samu nasaran komawa, wata rana ta tashi ta yi salla wata rana kuma ta yi karatun Qur'ani wata rana kuma ta yi kuka. Yau ma da wuri ta samu barcin amma bugun ƙofar da Habib yake yi ya katse mata barcin nata kuma a daidai lokacin daman mafarkin Habib ɗin take yi wai ya kira ta yana yi mata mgana ita kuma ta ɗuka har ƙasa tana bashi haƙuri har ya tashi zai tafi ta riƙo kafarsa amma ya juya ya ture ta a cikinta ta faɗi, sai ga jini na bin ƙafarta shi ya sa bugun ƙofar da mafarkin da ta yi suka samar mata da tashi a firgice tare da fargaba mai tsanani.
"Ba za ki buɗe ba! Ke Ummu Salma."
Ta ji muryan Habib yana magana, ta sake figicewa cikin gigita ta sauko daga kan gadon da take kwance, ta ma manta da hulan kanta da ya saɓule bayan ta kwanta sai da ta nufi ƙofar sannan ta shafa kanta ta ji ba ɗankwali ga shi kan ya yi datti goron kitso har ya ɓace saboda daɗewa, saboda ba ta kitso take yi ba.
"Wai ba za ki buɗe ba? Na san fa kina jina."
Habib ya sake faɗa kuma yana cigaba da buga ƙofar, yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke rawa domin ba ta san da abin da Habib ya zo a daran nan ba amma dai tafi tunanin abin da ke kawo shi wajenta ya zo nema jikinta, in shi ne kuma ya zo ga shi nan har sai ya gaji.
Saboda saurin ta buɗe kofar har tana neman faɗuwa rigar jikinta ce ta harɗeta ta kusa kaiwa ƙasa sai da ta riƙe gefen wardrope ɗin dake ɗakin. Hannnunta na rawa ta murza key ɗin dake jikin ƙofar ta buɗe ɗakin, Habib ya tsaya yana kallon ta cikin bacin rai.
"Ni za ki mayar ɗan iska kina ji ina kiran ki kina yi mini shuru?
Kanta na ƙasa ta ce" Ka yi haƙuri ban ji ba ne"
Ta ɗauka abin da ya saba kawo shi yau ma shi ya kawo shi ya sa tana gama bashi haƙuri ta juya za ta koma ciki.
"Ki same ni a falo."
Ta ji ya faɗa ta juya cikin mamaki shi kuma tuni ya bar wajen, zuciyar ta amsa na rashin sanin dalilin kiran Habib amma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta bi bayan shi zuwa falon, jikinta ya yi wani irin sanyi ne lokacin da ta ga Habib zaune kan kujera mai zaman mutum biyu ya harɗe kafafunsa kamar wani basarake ga littafi da takarda a hannun shi har da biron rubutu.
Kasa ƙarisowa ta yi ta tsaya cak daga nesa tana kallon shi cikin bugawar zuciya, me Habib zai yi da takarda da biro? Allah ya sa ba abin da zuciyarta ke saƙa mata ba ne, in ko haka ne da ta ce ita yau Ummu Salma ta shiga uku ta lalace rayuwarta ta faɗa cikin mawuyacin garari, gararin da har abada ba za ta iya fita daga cikin sa ba.
"Malama ki ƙariso kin tsaya mini a saman kaina "
Salau-salau haka ta ƙarisa gaban shi, ta zauna a kasan cafet tana mai ƙura ma kwalliyan cafet ɗin idanuwanta, amma hankalinta ba ya wajen in da zai lura ma kafafunta da hannayenta ma rawa suke yi tsabar firgici.
"Kin gama na ki aikin saura nawa aikin kuma Ummu Salma."
Sai ta ɗago tana kallon shi amma ba ta yi magana ba.
"Kin je kin haɗa ni da iyayena, kin yi ƙoƙarin ɓata mini gobe na sai dai burin ki bai cika ba."
Ya sake fada yana mai kallon ta fuskar nan ba fara'a kamar bai taɓa dariya ba.
"Me kuma na yi?
Ummu ta faɗa muryanta na karyewa kamar ta fashe da kuka.
"Ni kike tambaya abin da kika yi! Kin manta kin sake kai ƙarana wajen iyayen ki? Ke a tunanin ki za su iya sauya komai ne?
Ta ma kasa mgana bakinta na rawa, shi ya sa kawai ta yi shuru amma har hawaye sun kece mata maganarsa ya ba ta tabbacin Baffa ya ji labarin halin da take ciki, magana ta kai kunnen iyayen Habib.
"Ummu Salma ba ke kaɗai ne ba ki da tunani ba har da iyayenki ma."
Da sauri ta ɗago ta kalle shi cikin mamakin kalaman shi, iyayenta ne marasa tunani? Yau ita Habib ke faɗa ma iyayenta ne ba su da tunani?
"E haka na ce ba su da tunani, in har suna da tunani ai ya ci ace zuwa yanzu sun fahimci bana ra'ayin ki, na nuna bana son ki a aikace duk domin su fahimta su sauƙaƙa mini aiki amma sun kasa fahimta ban sani ba ko a wajen su ne kika gado wannan kidahumancin na ki ba"
Habib ya gama faɗa har yana nuna kanta cikin izgili.
Ummu Salma ta yi ma Habib ƙuru da ido ta kasa mgana, domin sai ta ji kamar an zare mata duka lakkan jikinta.
Yau iyayenta ne kidahumai a bakin Habib? Iyayenta fa? In ita ya zageta ta shanye, to ai bai kama ta ya taɓo bangaren iyayenta ba, domin ya san duk ɗa na gari ba zai zura ido ana cikin zarafin iyayenshi kuma ya yi shuru ba.
"Na gaji da ke, na gaji da auren ki wallahi, ke kika fara cutar da iyayen ki tun da kika ɓoye musu gaskiyan manufata akan ki, su kuma rashin tunanin su da lissafin su yasa suke tunanin ina son ki, sannan iyayena suna da ikon sarrafa rayuwata ne? Ina, rayuwata ce ni ke da ikon zaɓa ma kaina yau n da gobe na ba wani ba, ba kuma wanda ya isa ya saka ni na zauna da abin da bana so, a farko ni ne na yi ra'ayin zama dake saboda ina son cimma burina, yanzu kuma na gama amfana dake, na cimma burina akan ki me kuma ya yi saura a tsakanina da ke?
Ya faɗa yana zare mata ido.
Ummu na hawaye har da majina, ta ce" Iyayena ba su yi maka komai ba Habib ka daina zagin su don Allah."
Ta faɗa kukanta har yana fitar da sauti.
Sai ya kwashe da dariya kafin ya ce"Oh kina jin zafi ne? To na dai na cewa basu da tunani suna da shi, amma dai ba zan fasa faɗa miki kin turo bagidajen tsohon ki wajen iyayena ba kuma ya zo, sannan kuma har ya bar mini saƙo "
"Haba Habib."
Ummu ta sake faɗa cikin kuka tana sakin shessheka domin ji take yi kamar ta shiɗe yadda maganganun Habib suke kassra tunaninta da sauran kuzarinta gabaɗaya.
"Na faɗa wannan bagidajen uban naki ne, wai shi ne yake da zarran zuwa ya faɗa ma Abba cewa in na gaji dake ne na dawo masa dake gida"
Ya gama faɗa yana wata dariya ta reni da wulakanci.
"Shi yana ɗauka ya yi gwanin ta ne, ko kuma me ya ke takama da shi? Lauyan yayanki? Ko mai aikin filin jirgi? Ko mai fama da gwajin kashi da fitsari ko mai aiki da hukumar ruwa? Ko wannan yayan na ki mai bin tsohon ku saro tsoffin injina? Ko kuma wannan yayan naki mai karatun jami'a? Ko wanda ya tafi ƙasar waje da kuɗin tallafi?
"Habibb.."
Ta faɗa muryanta baya fita saboda kuka.
Bai saurareta ba ya cigaba da faɗin.
"Oh na tuna ko yana takama da wannan ɗan da bai haifa ba ne? Lamiɗon da dangin ku ke ji dashi, Yariman Daura ko? Wanda uwarki ke zuwa maula gidan sarki ko? Da shi yake taƙama da har zai zo wajen ƙanin mahaifina ya bar mini wannan saƙon? To in ma gatse yake yi ya yi kuskure, a yau ba sai gobe ba zan cika umarninsa zan mayar masa dake kamar yadda na ɗauko ki daga gidan shi."
"Habib ka bari, ka daina zagin iyayena."
Ummu Salma ta faɗa tana kuka zuciyarta na ƙuna tana wani irin soya da irin wannan cin mutumcin da Habib ya zaunar da ita yana yi ma iyayenta da yan'uwanta.
"Na faɗa ko za ki rama musu ne?
Ya faɗa yana taso mata kamar zai dake ta sai ta yi shuru ban da kuka ba abin da take yi, yi take yi kamar zuciyarta zai fita, wani ɗaci na taso mata ɗacin an ci zarafin iyayenka a gaban idanuwanka amma ba ka da hurumin da za ka hana faruwan haka, miyan bakinta har kafewa ya yi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa.
"Ni ce na yi maka laifi ba iyayena ba. Ni ce baka so ba su ba, to kuma su me suka yi maka da za ka ci zarafin su?
Ummu ta faɗa cikin kuka mai ƙarfin da sautin shi yake fita sosai.
"Ka yi mini abin da za ka yi mini zan jure Habib, ka tozartani iya tozartawa ba zan taba mgana ba, amma ba zan jure jin maganganun cin fuska ko na ɓatanci ga iyayena ba, kar ka sake ban zagi naka iyayen ba kai ma ba ka da hurumin da za ka zagi nawa iyayen."
Tana magana yana mata dariya kamar ya ga wata mahaukaciya.
"Me suka yi mini kike tambaya na?
Tasowa ya yi zuwa gabanta ya durƙusa saitin kunnuwanta ya yi magana.
"Saboda sun haife ki, laifin su kenan a wajena."
Ya faɗa yana yi mata dariya, Ummu na tsiyayan hawaye tana kallon Habib tana jin son ta ji ta tsane shi, tana so ta daina jin ko da ɓurɓushin son shi a cikin zuciyarta amma ina, tunda ba ita ke da alhalin sarrafa zuciyarta ba har yau ba ta daina jin son Habib a ƙasan zuciyarta ba.
Miƙewa ya yi ya koma in da ya tashi ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda har tsohon ki ya bar mini sallahun in na gaji dake ne na dawo masa dake shi bai gaji dake ba, to a matsayin shi na Surukina mahaifin matar da na aura na more albarkatun jikinta ya zame mini kamar wajibi na cika umarninsa."
Kallon ban fahimce ka ba Ummu ke yi masa kamar idanuwanta za su faɗo kasa, ga shi suna masu zubar da hawaye.
Takardan ya jawo a gefen shi ya ɗora saman cinyarsa ya ɗora biron a kai lokaci ɗaya yana faɗin" Zan sake ki kamar yadda mahaifinki ya ɓukata, duk da ya ɗan yi gaggawa, da a ce ya jira da ni da kaina zan sako masa ke ba sai ya wahalar da kansa wajen zuwa ya bar mini saƙo ba."
Ummu Salma ta ji kanta ya sara, har ɗan dake cikinta sai da ta ji ya motsa saboda firgici da tashin hankali.
"Yanzu Habib sakina za ka yi?
Ummu ta tambaya muryanta cikin kuka kamar za ta shiɗe.
"Kina tantama ne? Bari na rubuta na ba ki ki karanta sai ki samu tabbaci "
Kawai sai ta ga ya fara rubutu da sauri ta rarrafa gaban shi cikin kuka tana faɗin" Don Allah Habib ka yi hakuri kar ka sake ni, don Allah ka taimaka mini ka rufa mini asiri ka da ka sake ni."
Take faɗa tana wani irin gunjin kuka, ga ta duke kan gwiyoyinta tana mai zubar da hawaye tana haɗa shi da Allah akan kar ya sake ta.
"Ai abin da tsohon ki ya bukata ne, duk da nima ina da niyyar yin haka amma ba yau ba."
Ya faɗa yana nuna halin ko in kula, yana ma ƙoƙarin cigaba da rubuta abin da ya fara.
Da sauri Ummu ta faɗa kan kafafun Habib ta riƙe shi gam tana wani gunjin kuka.
"Ke miye haka?
Ya faɗa yana fizge kafarsa har tana yin gefe amma ba ta haƙura ba sai da ta sake riƙo kafafunsa da karfi ta rumgume a ƙirjinta lokaci ɗaya tana faɗin.
"Na tuba, don Allah ka yi haƙuri Habib kar ka sake ni."
"Wallahi sai na sake ki, mutuwa ce kawai za ta hana na sake ki, itama sai in yanzu ta zo ta ɗau raina amma in dai ina raye a yau zan yada ƙwallon mangwaro na huta da guda."
Ya gama faɗa yana sake fizge kafafuwanshi ya ɗora saman kujera ya bar Ummu duƙe a gaban shi tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe.
"Habib in ka sake ni ina zan je? Wa zai sake kwasa ta? Wa ye zai iya aurena bayan ba ni da komai. Don Allah ka rufa mini asiri kar ka sake ni, kar ka manta da gudan jinin mu dake rayuwa yanzu haka a cikin jikina, kar ka bari ɗan mu ya rayu ba tare da kai ba, ka yi haƙuri don Allah ka rufa mini asiri "
Majina har zuba take yi a ƙasan cafet saboda kukan da Ummu ke rusawa amma ina Habib ba ya sauraranta rubutu kawai yake yi.
"To na ji , wallahi zan yi duk abin da kake so. Na ji zan. Zan zubar da cikin."
Ta faɗa cikin fitan hayyaci, har muryanta na dishewa saboda kuka.
Ganin ya ɗago yana kallon ta, ya sa da sauri ta sake rarrafawa gaban shi tana rawan bakin faɗin " Da gaske na ji zan zubar da cikin in har zan tsira da aurena."
Take faɗa cikin fitan hayyaci, domin ba ta ji ba ta gani, tunanin ta hangenta shi ne in Habib ya sake ta ya gama lalata mata goben ta, ya cuceta ya mai da ita ƙaramar bazawara, sannan tana son shi tana son aurenta za ta yi komai domin ta ga ta tsira da aurenta.
"Kika ce me?
Ya tambaya yana mata wani kallo
"Na ce, e zan zubar da cikin wallahi na yarda."
Ta faɗa hawaye na kwaranyo mata yadda ya ga ta ruɗe ne tana roƙon shi har tana cewa ta yarda za ta zubar da ciki ya sanya shi nishaɗi ya kwashe da wata dariyan jin daɗi.
"Na yarda ko yanzu ne ma mu je a zubar amma don Allah kar ka sake ni "
Ta sake faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun roƙo.
"Yarinya kin makara."
Ya faɗa yana dariya sannan ya cigaba da rubutun sa.
"Wataƙila da wata ɗaya kafin yanzu ne kika ce mini haka da zan iya sauraran ki, amma yanzu lokaci ya kure miki, da man ai na sha faɗa miki sai kin yi nadama, a ranar da nadamar ba za ta yi miki amfani ba lokacin da na ke bin ki, kina mini yadda kike so ai ba ki yi tunanin rana irin ta yau za ta zo ba, duk ɗaukan maganganuna kike yi a wasa?
Ummu ta kasa magana ban da kuka ba ta komai.
Ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya cigaba da faɗin" Ni yanzu ban damu da ki zubar da cikin jikin ki , ko ki zubar ba ko ki haife shi duk wannan ya rage na ki, dake da cikin duka bana so, ba na kuma buƙatar ku a cikin rayuwata "
Ya ƙarishe faɗa yana nuna ta da yatsa daga sama har ƙasa cikin ƙyama.
Ummu ta gigice ta sake fashewa da kuka tana faɗin" To ba ka ce jikina kake so ba? To ai ga jikin nawa ai ba na hana ko?
Ta faɗa tana yi kamar za ta haura a saman kujeran da yake zaune.
"Ke kar ki hauro mini nan"
Ya faɗa yana zare mata ido.
"To to na zauna "
Ta faɗa lokaci ɗaya tana zaman dirshan a gaban shi yanayinta kawai za ka gani ka fahimci ta rasa natsuwarta ba ta ma san abin da take yi ba, ballantana abin da take furtawa.
Ganin ta cikin wannan yanayin yafi masa komai daɗi, nishaɗi da farinciki yake ji da man ya ce sai ta yi nadama to kaɗan ta gani.
"Ai ni gama moran duk wani albarkatun jikin ki, babu wani sauran maiƙon da ya rage da ban gama lashewa ba."
Ya faɗa yana dariya ƙasa-ƙasa har yana kashe mata ido ɗaya.
Ummu na kuka tana kallon Habib kamar zai yi mata gafara tana rokon shi Allah da Annabinsa kar ya sake ta, amma ina bai ƙara sauraran ta sai da ya gama rubuta abin da ya yi niyya sannan ya miƙa mata , ta kasa karɓa lokaci ɗaya tana girgiza kanta cikin kuka.
"Karɓi mana "
Ya faɗa yana mai sake miƙa mata takardan.
"Don Allah Habib. Kar ka. Sa ke ni."
Ta ƙarishe faɗa kamar za ta shiɗe domin har numfashinta ya fara ɗaukewa.
"Ai na ma riga na sake ki Ummu Salma."
Zuciyarta ta tsinke, idanuwanta suka fara rawa, hannaunta ɗaya ya kama ya tusa mata takardan lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda dare ya yi na yi miki alfarman ki kwana amma gobe da safe ki tattara kayanki ki koma gidan ku, kayan ɗaki kuma suma ki zo ki kwashe kafin masu gidan su bukaci dakin su."
Yana gama faɗin haka ya kwashi takardansa da biron sa ya wuce yana sake faɗin" Alhamdulillah."
Har yana wani harba ƙafafuwansa, Ummu ta bi shi da kallo cikin zubar ƙwalla takardan ta matse a hannunta tana sakin kuka da ƙarfin iyawanta, kuka ta fashe da shi da duka muryanta da ubangiji ya ba ta, kanta a ƙasa kamar tana sujudda take rusa kuka kamar ranta zai fita Habib ya gama tozarta, irin tozarcin da bata taɓa jin labarin an yi ma wata mace ba, Habib ya sake ta da ƙaramin ciki bayan ya gama lalata mata rayuwa ya mayar da ita ƙaramar bazawara, ya kunya ta iyayenta ya cutar da ita sannan ya cutar da zuciyan ta.
Koda ta ɗago daga durkushen da ta yi ruwan hawaye da majina ya gama jiƙa cafet ɗin gabanta sannan fuskarta har ta jirkice tsabar kuka da tashin hankali, a hankali ta miƙe tana jin jiri na ɗiban ta, kanta na sara mata da ƙarfi, cikinta ya cure waje ɗaya daƙyar ta iya jan kafafunta tana dafe bango ta koma ɗakinta tana matsanacin kuka takardan sakin na matse a hannunta ta kasa dubawa, ba ta son gani ba ta son ganin wannan baƙin rubutun Habib a gare ta, kukan ta kawai take yi da karfi ba ma tunanin ta yi shi a cikin zuciyarta, yi take yi tana shessheƙa, tana fidda sauti ga majina na shatata, ga ruwan hawaye kafin kace me gaban riganta ya jiƙe da hawaye, fuskarta ta kumbura saboda kuka idanuwanta sun tasa sun yi jajir kamar gawarshi, daga karshe ma da ta gaji da kukan dole ta haƙura ta koma ajiyar zuciya tana faman sauke numfashi a jejjere kamar wacce ta yi gudun tsere tana zaune a ƙasan tayels a gefen gado kanta na gefen gadon ta ɗora saman hannayenta lokaci ɗaya hawaye na kwaranya har a saman hannayen ta amma ta daina kuka da sauti sai dai a cikin zuciyanta take jin wani ɗaci da raɗaɗin da ba za ta iya misalta yanayin ba.
Takardan sakin na jimƙe a hannunta ganin zufan hannunta ya fara jiƙa takardan ya sa ta ɗan ɗage zanin gado ta tura takardan ta koma ta kwantar da kanta tana ta tsiyayan hawaye yadda ta ga rana haka ta ga dare barci ko ɓarawo bai sace ta ba a cikin kunnuwanta aka fara kiran sallan asuba, duk kuma tana zaunen har wasu masallatan suja tayar da salla amma ta ƙasa tashi saboda kuka ga jikinta duk ya yi tsami kanta saboda ciwo ba ta ma san ma ɗago shi, sannan ga idanuwanta sun kumbura sumtum ko iya buɗe su ma ba ta yi, ko'ina na jikinta ya yi tsami saboda kwanan da ta yi a zaune cikin yanayi mara daɗi, da rarrafe kamar yar koyo ta shiga tiolet ta kama ruwa sannan ta wanke fuskarta da ruwan zafi ta ɗauro alwala haka ta fito da rarrafe nan domin ba za ta iya tashi ba ji take yi kamar kafafunta ba za su iya ɗaukan gangan jikinta ba.
Salla ma a zaunen ta yi, ta daina zubar ƙwalla amma raɗaɗin dake cikin zuciyarta kaɗai ya isa ya yi ajalinta. Domin zuciyarta wani zafi take yi ga wani abu mai ɗaci da ya tokare mata a ƙirji tun jiya ya kasa wuce miyan bakinta ya daɗe da kafewa sannan bakin nata ya yi ɗaci kamar maɗaciya, sannan ga ciwon kai mai tsanani yunwa take ji amma a bakinta ba ta bukatar cin komai maranta ya cure waje ɗaya da ya haifar ma gangan jikinta rawa, bayan ta idar da sallan ta kura ma waje ɗaya ido tana ma rasa abin da take tunani, yanzu fa wata sabuwar rayuwa ce ta tunkaro ta bayan barin ta gida na wattani takwas a matsayin matar aure yanzu kuma za ta koma gida a matsayin bazawara har da ƙaramin yaron ciki, yanzu a wannan kadamin wa za ta kira? Ina za ta nufa? Rayuwarta ta gama lalacewa ba ta da sauran wani abu na mamora a tare da ita.
Tuna gargaɗin da Habib ya yi mata ajiya ne ya sa ta rarrafa ta ɗauko wayarta dake saman side drower ɗin gadon. Gwara ta bar gidan tun kafin ya fahimci ba ta tafi ba ya yi mata wulaƙanci, agogon wayarta ta duba sai ta ga shidda ne da mintina biyu na safe wataƙila Baffa na masallaci sai ta kira wayar Ammah amma tana ta ringing ba ta ɗauka ba ta kira ta kamar sau uku amma shuru, sai ta mayar da akalan kiran zuwa ga Baffa, domin nan duniya su ne kaɗai ne suka rage ba za su guje ta ba, amma ta rasa komai na ta. zuciyarta na sake yin duhu in ta tuna yadda Habib ya zaunar da ita yana cin zarafin iyayenta da ƴan 'uwanta.
****
*6:13am*
Shidda da mintina sha uku Baffa da Hamma Saddam suka shigo gidan daga masallaci, jiya da yamma Saddam ya dawo daga makaranta can Bauchi. sun gama jarabawa za su yi hutun sati uku kafin su koma.
Ɗakinsa ya wuce shi kuma Baffa ya ƙarisa cikin gida, ɗakinsa ya wuce kai tsaye yana shiga ya iske Ammah na zaune saman darduma da casbaha a hannunta bakinta na motsi, yana takawa zuwa gefen gado wayarsa dake cikin aljihun rigan jikinsa ta ɗau ruruwan kira, bai duba ba sai da ya zauna sannan ya fiddo wayar yana duba sunan mai kiran..
"Auta."
Ya faɗa a sarari cikin mamaki, Ammah na lazimi sai da ta kalle shi cikin mamaki.
"Auta kuma! Ummu Salma?
Amma ta faɗa cikin ƙarin mamakin gabanta na faɗuwa, shima ita yake kallo amma sai ya aro jarumta a matsayin shi na namiji.
"Bari na ji Allah ya sa lafiya."
Ya faɗa shima cikin ƙarfin hali, kafin ya ɗaga kiran ma ya katse hannunsa na rawa yana ƙokarin sake kiran ta sai ga kiranta ya sake shigowa da sauri ya ɗaga kiran yana mai kiran sunan ta.
"Auta"
Ya faɗa yana jin bugawar zuciyarsa na ƙaruwa da sauri da sauri.
Ummu Salma daga can bangaren jin muryan Baffa ya sa rauninta ya karu, hawaye ya kece mata mai hade da kuka Baffa sai jin sautin kukan kawai ya yi ta cikin wayar.
"Ummu Salma."
Baffa ya faɗa cikin tashin hankali, Ammah na jin yadda ya kira sunanta cikin sauri ya sa ta bar saman darduman ta dawo gefensa ta zauna ta kafe shi da idanuwanta cikin damuwa tana faɗin.
"Baffa me ya faru da Auta?
Ta faɗa tana jin jikinta na yin wani sanyi, haka kurum take jin faɗuwar gaba tun jiya da man kawai Autan ke faɗo mata arai ta so ma kiranta sai ta ga dare ya yi tana shirin da man yau ta kirata a waya ta ji lafiyan ta ne.
Baffa ya kasa mgana jin yadda Ummu ke rusa masa kuka a waya gabaɗaya jikinsa ya gama yin sanyi amma sai ya yi jarumta komai ya faru daga gare ka ne Ya Ubangijin mu.
"Ki bar kukan nan ki yi mini bayanin abin da ya faru Auta."
Ya faɗa cikin lallashi a muryan sa Amma ta sake tsurewa a cikin zuciyanta tana maimaita kalmar kukan da ta ji Baffa ya ambata.
"Baffa."
Ummu Salma ta kira sunan Baffa muryanta a shaƙe da ƙyar ma take fita.
"Naam Auta me ya faru ne?
Ya faɗa cikin sauri domin ya kosa ya ji abin da ya faru duk da yana zargin wani abu amma bai yanke hukunci ba.
"Baffa."
Ta sake kiran sunan shi cikin matsannacin kuka duk ta ruɗar da Baffa, ga Ammah ma a gefen shi kamar za ta kwace wayan idanuwanta kawai ya kalla ya ga tsoro da firgici a cikin su.
"Na'am ina jin ki Auta, ki daina kuka maza ki sanar da ni abin da ke faruwa bar kuka Auta kin ji ko?
Ya ƙarishe faɗa muryansa na karyewa shima jin irin kukan da Ummu Salma ke yi a waya kamar ranta zai fita.
"Baffa Habib."
"Me ya samu Habib ɗin?
Baffa ya katse da sauri kafin zullumi ya kashe shi.
"Ya sa ke ni..."
Ta faɗa tana sarƙewa cikin matsanancin kuka.
Sai da Baffa ya miƙe da sauri kansa ya sara, idanuwansa suka ciko da ƙwalla hannunsa na rawa haka ƙafafuwansa shuru ya yi yana kiran sunan Allah a cikin zuciyarsa domin ya samu ya tattaro natsuwarsa.
Ammah ta biyo shi a tsayen tana tambayan shi jin ya yi shuru sannan ba su yanke wayar ba, ta san waye Baffa shurun sa na nufin damuwa mai yawa ko a fuskarsa ma ya bayyana haka.
Tana so ta yi magana amma sai ta kasa ta dai tsura masa ido kawai tana bin shi da kallo.
"Baffa Habib ya sake ni, ya sake ni jiya da daddare."
Ummu Salma ta sake faɗa cikin kuka jin Baffa ya yi shuru, bai ce komai ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
Baffa ya samu bakin shi da furtawa cikin wata murya mai cike da tausayin Ummu.
"Allahumma ajirni fimusibatihi. Daga gare ka muke Allah kuma a gare ka za mu koma."
Baffa ya sake faɗa cikin yaƙinin da cewa akwai Allah da sanin sa komai ya faru kuma shi zai kawo sauƙin lamarin cikin gaggawa.
Ummu kuka kawai take rusawa kamar ranta zai fita Baffa ya kasa jure jin kukan ta kawai sai ya kashe wayar, ya ma kasa kallon Ammah wacce ke bin shi da kallo, kansa ya juyar kawai ya koma ya zauna a gefen gado ya dukar da kansa lokaci ɗaya ya saka hannayensa duka biyu ya dafe kansa yana sake maimaita salati da muryansa cikin rauni da tausayi.
"Allah ya ba ki ikon cinye wannan jarabar mai zafi da raɗaɗi Ummu Salma."
Muryansa ta karye da man Baffa akwai rauni ko ciwo mutun yake yi sai ya yi kuka lokacin da Ammah ke haihuwa haka zai yi ta kuka asibiti in tana naguda, ganin yanayin shi kawai ya ba ta tabbacin wani abu ya faru mara daɗi amma ba ta tambaya ba, sai ta bishi ta zauna a gefen shi ta ɗora hannayenta saman kafaɗan shi tana ɗan matsawa alamun lallashi duk da itama ƙarfin hali take yi amma zuciyarta ta yi rauni ba ta so ta nuna ne.
Shuru na wani lokaci kafin Baffa ya fesar da numfashi cikin hikima ya share ƙwallar da ta ɗan siraro masa ta gefen idanuwansa saboda kar Ammah ta gani abin da bai sani ba, ta riga ta gan shi, kukan sa kawai ya sake ba ta tabbacin Ummu ta fsɗa cikin kaddaran aure, kaddaran da take ta yi mata fatan kar Allah ya sa ta faɗa a cikinsa, domin ba ko wacce mace ba ce jaruma, ba ko wacce mace ba ce take iya tsallake wannan jarabawar sai jaruma sai sadaukiya amma Ummu ba za ta iya ba zuciyarta karama ce tana da rauni ba lalle ne ta fuskanci girman jarabawan da ya faɗa mata ba.
Baffa ya ɗago kanshi suka haɗa ido da Ammaj sai kawai ta yi masa mirmishi, ita wai a dole ta nuna masa ba ta damu ba, fillanci na cin ta amma duk wanda ya kalleta ya san a cikin zuciyarta tsoro ne da fargaba ba ta tambaye shi ba shima sai ya kasa faɗa mata, illah hannayenta da ya jimƙe cikin nashi yana kallon ta amma ya kasa mgana a cikin zuciyarsa salati kawai yake yi da kiran sunan Allah.
Itama sai ta jimƙe hannayen na shi cikin nata cikin karfin hali ta kira sunan shi.
"Baffa."
Bai amsa ba amma yana ta kallon ta.
Sai kuma ta yi shuru ta kasa mgana tana so ne ta tambaye shi amma ta kasa, shi kuma ya san halinta ba za ta sake tambaya ba saboda kawaicin ta sai kawai ya yi kumdulan fada mata ita uwa ce ya kamata ta sani ko domin su yi tunanin mafita.
"Jamila."
Tunda ta ji wannan sunan a bakin Baffa ta san maganar da zai faɗa mata mai girma ne.
"Habibu ne ya saki Auta jiya da daddare."
Ya faɗa yana kallonta hannayenta na cikin na shi yana matsawa, shuru na wani lokaci yana kallon ta duk da ta tsammaci haka amma ai zato ne ba gaskiya ba yanzu da ta samu tabbacin sai ta ji zuciyarta ta yi duhu wani abu kamar ya sare daga kirjinta kwata-ƙwacin abin da ta ji a lokacin da Fatima ta zo gare su da tsohon dare ɗauke da jaririn da ko jinin haihuwa ba a wanke masa ba, a lokacin da ta ba ma Baffa takardan saki, abin da ta ji a lokacin a wannan lokacin ma shi ta sake ji.
"Ta kira ni tana ta kuka Jamila. Gwanin ban tausayi "
Ya sake faɗa muryansa har tana sauyawa, Ammah ta yi ajiyar zuciya kafin ta tattaro kalaman bakinta ta furta." Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabadaya "
"Amin "
Ya amsa yana kallon ta.
Shuru na wani lokaci kafin Amma ta yi ƙarfin halin cewa" Baffa wa zai je ya taho da Ummu?
Ta faɗa tana kallon shi, sai yanzu ya tuna ya kamata wani ya je ya ɗauko ta zuwa gida a yanayin da ta ke ciki tana bukatar wani a kusa da ita.
"Bari na yi ma Saddam magana ya tuka ni muje mu taho da ita."
Baffa ys faɗa yana miƙewa da sauri Amma ta mike ta riko shi ganin duk ya daburce kallon ta ya yi yana cigaba da faɗin" tana ta kuka gwara na je da kaina "
Ya faɗa yana laluban aljihun jikinsa
"Ammah ina key ɗin mota ta?
Ya faɗa yana waige-waige Baffa fa ba ya cikin natsuwarsa shi ya sa ta sake riko shi tana kiran sunan shi.
"Baffa."
Sai kawai ya tsaya yana kallonta
"Jamila Auta tana can tana kuka ba ki ji muryan ta ba."
Ya faɗa cikin karyewan sauti, kawai sai ta faɗa jikin shi, domin itama in ta cigaba da jin sautin Baffa cikin rauni za ta iya fashewa da kuka ba ta sani ba, jin ta a jikinsa ya sa ya yi shuru kawai yana sauke ajiyar zuciya, bayansa take ɗan tapping da hannunta alamun lallashi, kuma ta yi nasara domin sai ya ɗan samu natsuwar zuciya.
"Ba kai za ka je ba Baffa."
Ya ji Ammah ta faɗa da sauri ya dago ta kafin ya yi magana ta yi saurin cewa" ka kira Abdullahi ka sanar da shi abin da ke faruwa ka ce ya ɗau mota ya je ya ɗauko Aminiya zan kira ta yanzu na sanar da ita abin da ke faruwa, ita in suka je za ta shiga ciki ta taho da Ummu gida."
Tabbas ya aminta da shawaran ta, gwara mace ta je zai fi akan namiji.
"Hakan ya yi, amma ko na kira Abdulrrahman ne?
"Aa gwara dai Abdullahi ka san halin Abdulrrahman fusattace ne."
Shi saboda tashin hankali duk ya manta da halin ƴa'yan na shi, wayarsa ya fara laluba Ammah ta ɗauko masa ita a gefen gado ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Ka kira shi yanzu, bari na je na kira Aminiya"
Tana gama faɗin haka ta wuce ta fita daga ɗakin, falon ta yana sakaye ne ta tura ta shiga wayarta a chaji ta sakata tun daran jiya hannanunta na rawa kamar yadda zuciyarta ke bugawa.
Tana duba wayar sai ta ga ma Ummu ta kirata sau uku a lokacin da ta kira Baffa kenan, lambar Ummin ikki ta nemo wacce ta yi ma saving da Aminiya, duk da Ammah ba ta yi karatun boko ba amma sun yi yaki da jahilci shi ya sa ta iya karanta hausa, wani lokacin ma da fillanci take yi saving din lambobin wayarta.
Sai dai tana kiran wayar sai ta ji a kashe, har sau biyu ba ta shiga ba sai kawai ta laluɓo lambar wayar Aisha(Baɗɗo). Tana kiranta ita sai ta shiga.
Baɗɗo na kwance a ɗakin su bayan ta idar da sallar asuba gajiya ne a jikinta jiya wajen takwas na dare ta iso gida daga Mubi, tana idar da salla sai ta ɗan kishigiɗa barcin ya ɗan ɗauke ta kenan ta ji ringing ɗin wayarta dake gefen filon data ke kwance da barci-barci ma a idanuwanta ta zaro wayar sai dai ta wattsake ganin sunan Ammah tana kiranta, ido ta waro tana sake duban sunan mai kiran da gaske dai Ammah ce.
"Wa ke kira hala ?
Adda Kaltume ke tambaya ganin yadda Baɗɗon ta zaro ido kamar ta ga wani abun tsoro.
"Ammah ce fa."
Ta faɗa tana kallon ƙaramin agogon bangon dake ɗakin barcin na su, ƙarfe 6:32am na safe to ba lafiya.
"Topha, ɗaga mu ji Allah ya sa dai lafiya"
Adda Kaltume ta faɗa, daidai lokacin da Baɗɗo ta ɗaga kiran Ammah bayan ta sake kiran ta a karo na biyu.
"Ammah ina kwana."
Daga can bangaren Ammah ba ta tsaya amsa gaisuwar Baɗɗo ba da sauri ta ce" Aisha ina Aminiya?
"Tana ɗakin ta "
"Kai mata wayar zan yi magana da ita."
Amma ta faɗa muryanta cunkushe, Baɗɗo ta mike tana amsawa da to Adda Kaltume tana ta mata tambaya me ya faru da hannu, ita kuma Baɗɗo tana ɗaga mata hannu alamun ba ta sani ba.
Ummin ikki na cikin ɗakinta, itama da carbi a hannunta tana ja ne barci ya ɗan sace ta tana zaune tana ta gyangaɗi sai ta ji Baɗɗo a saman kanta tana faɗa mata ga Amma na son magana da ita.
"To Allah ya sa lafiya "
Ta faɗa tana leken waje ganin har lokacin gari bai ida sa wayewa ba.
Tana karɓan wayan ta saka a kunnenta lokaci ɗaya tana faɗin" Aminiya Allah ya sa lafiya."
Ummi ikki ta faɗa cikin fargaba kira da sassafe haka ba na lafiya ba ne.
"Wayarki a kashe Aminiya ?
Ammah ta faɗa, da sauri Ummin ikki ta ce" Tun jiya ban ga wayar ba, waya sani ma ko ta mace ba chaji ne."
Amma tace" To ƙila."
"Lafiya Aminiya? Na ji muryan ki wani iri ne"
Amma ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce" Ki shirya ga Abdullahi nan zai zo ya ɗauke ki zuwa gidan Ummu"
"Me ya faru da Ummun?
Ummin ikki ta tambaya har tana waro ido, Baɗɗo na gefe tun da taji an ambaci sunan Ummu ta matso kusa da sauri tana son jin abin da ya faru.
"Ya sake ta ne."
Ammah ta faɗa tana runtse ido, kafafunta sun fara rawa da ya sa dole ta lalubi gefen kujeran dake gefenta ta zauna tana ƙoƙarin daidaita yanayin ta.
"Ya sake ta fa ta kika ce Aminiya! Shi Habibun ne ya saki Ummu Salma?
Ummin ikki ta faɗa da karfi da ya sa Baɗɗo ta yi zaman yan bori a gaban Ummin tana faɗin" Habib ya saki Ummu?
Ta sake maimaitawa hannunta a saman ka cikin tashin hankali.
"Ya sake ta Aminiya, Abdullahi na hanya za ku je ku taho da ita "
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un amma dai Habibu ya cuce mu Allah ya isa tsakanin mu da shi."
Ummin ikki ta fada sai ga hawaye Ammah kashe wayarta kawai ta yi ta bar Ummin tana ta salati da tsine ma Habibu.
Baɗɗo ta fashe da kuka tana faɗin" Innalillahi Ummi Habib ne ya saki Ummun? Ummun tawa?
Take faɗa tana kuka, Ummin ikki ta ce" Wannan yaron ya gama cutar mu Allah sarki Ummu."
Da man kuma Ammah ta sanar da ita zaman da aka yi na farko ta dinga zagin shi tana cewa mara albarka, to amma daga baya Ammah ta ce mata an daidaita ashe bai hakura ba sai da ya mayar da ƙaramar yarinya bazawara.
Kukan Baɗɗo da hargagin Ummi ya fiddo da duka yaran gidan har mahaifin su Baɗɗo duk wanda ya tambaya aka faɗa masa abin da ya faru sai ya girgiza.
"Subhanallah lamarin bai yi daɗi ba me ya faru ne?
Baban su Baɗɗo na tambaya Ummi ba ma tsaya masa bayani ba ta miƙe tana faɗin Abdullahi na hanya zai zo ya dauketa za ta je ta taho da Ummu zuwa gida Baɗɗo na jin haka ta ce itama za ta je Ummi ta ce ba za ta je ba.
"Ummi ki je da ita in Ummu ta gan ta za ta ji daɗi "
Adda Kaltume ta faɗa cikin damuwa ta girgiza da jin wai Habib ya saki Ummu Salma, duk wanda ke gidan nan ya san waye Habib domin zuwa goma in Ummu za ta yi shi zai kawo ta ya kuma zo ya ɗauke ta kuma duk zuwa sai ya shigo ya gaida Ummi da Baba, tun kafin auren su ma bayan auren ma sai ya zama ɗan gida nan zai zo ɗaukan Ummu su zauna a falon Ummi da shi da Baɗɗo da Ummun suna ta hira suna dariya.
Kowa sai jinjina lamarin yake yi, abin mamaki abin tausayi ga rayuwar Ummu, da wayar da Ammah ta yi da Ummin ikki ko minti talatin ba a yi ba sai ga Hamma Abdullahi bakwai saura mintina ya iso gidan yadda ya shigo kawai za ka san shima labarin ya dake shi, jallabiya ce a jikinshi a baibai ya sako ta ma domin yana barcin nan na bayan asuba ya samu wayar Baffa labarin da ya faɗa masa ne ya sa ya diro daga kan gado bai shirya ba, ya razana da jin wai mijin Ummu ya sake ta! Har ya kariso gidan Ummin ikki yana tunanin to me ya sa zai sake ta? To ta yi masa wani abu ne?
Daga Ummin har Baɗɗo da hijaban jikinsu suka bi Abdullahi takalma kawai suka saka, suna tafe a mota Ummin ikki na sake kwashe ma Habib albarka Baɗɗo na daga baya tana ta sharan ƙwalla tausayin halin da Ummu take ciki a daidai wannan lokacin.
"Ummi to wai me ya sa zai sake ta? Ko ta yi masa wani abu ne?
Abdullahi ya tambaya jin yadda Ummin ke mgana da alamu ta san wani abu.
"Ba ka san abin da ya faru kwanaki ba ne Abdullahi?
"Ban sani ba Ummi, Baffa bai faɗa mini ba, haka ma Ammah."
Nan fa ta warware masa komai mamaki ya kama shi sai ma ya kasa mgana wato shi ya sa kenan ya ga Baffa Umaru ya zo har da mijin Ummu da ita kanta ashe lokacin duk matsalan ne ya ta so.
"Wai ba ya son ciki ka ji fa, sai ka ce shi uwarsa ba cikin ta yi ta haife shi ba wataƙila daga sama ya faɗo"
Ummin ikki ta faɗa cikin takaici da haushi.
"Allah ya kyauta."
Kawai Abdullahi ya ce amma maganganu na yawo a cikin ranshi, ta ya ya mutum zai auri macen da yake so kuma ya ce ba ya son ciki? Cikin kuma na shi ne, daga karshe hadda saki? Kai gaskiya yana tamtama an ya mijin nan na Ummu Salma yana son ta kuwa? Domin wanda ke son ka ba zai yi maka wannan tozarcin ba.
Bai sake magana ba har suka isa gidan, a bakin flat ɗin Ummu suka yi parking ɗin motar, dukkansu kuma suka firfito, abin mamaki ƙofar falon Ummu ma a buɗe take har ga labule nan a waje shi ya sa kawai suka faɗa, Baɗɗo ce ta shige gaba da sauri Ummi a bayanta Abdullahi kuma sai ya tsaya daga waje bai shiga ba, a tunanin shi ko Habib ɗin na gidan abin da ba su sani ba tun wajen shidda da rabi ya tattara kayan shi kaf ya bar gidan a motar shi baya son ma wani cikin yanuwan Ummu su gan shi tun da abin da ya haɗa su ya raba baya fata ko son sake haɗuwa da duk wani abu da ya shafi Ummu Salma. Tunda ya ce ya gama da ita, to har abada ya gama da shafin ta.
Yadda Baɗɗo ta ga Ummu Salma ya sake tsinke mata zuciya tana zaune a in da ta yi salla kanta jingine da wardrope, ta yi kuri kawai ba ta magana ba ta kuma kuka amma fuskarta da idanuwanta sun kunbura babu kyan gani.
Rumgumeta ta yi ta fashe da kuka tana faɗin" Allah ya saka miki Ummu, da ikon Allah Habib sai ya ga sakamakon shi."
Ummu ba ta mgana tana dai kallon Baɗɗo kawai, Ummin ikki ta kasa mgana saboda tausayin Ummu har tana ƙwalla.
"Baɗɗo kamata ta tashi, ki kaita falo ki zo ki ɗan haɗa mata kayan sawan ta."
Da to Baɗɗo ta amsa, ta taimaka ta miƙar da Ummu tsaye ta riƙe ta zuwa falo, ta zaunar da ita a saman kujera ta zauna kawai tana kallon ta, bakin ma ya ɗinke ba mgana sai dai kawai ido.
Baɗɗo na kuka ta juya ta koma ciki tare da Ummin ikki suka cika akwatin Ummu huɗu da kayan sawan ta, Ummin ikki ta ce duk a cire zannuwan gadon kar su yi ƙura a tusa su cikin wardrope kafin a ga abin da Ubangiji zai yi, Baɗɗo ce ta yaye zanin gado sai ga takarda ta faɗo ta ɗauka ta buɗe ta karanta.
"Ummi."
Ta faɗa cikin ƙaraji lokacin da ta gama karanta takardan sakin Ummu Salma.
"Mene ne ya faru?
Ummin ikki ta faɗa cikin tashin hankali tana kallon Baɗɗo..
"Ummi saki uku fa Habib ya yi ma Ummu."
Ta faɗa tana nuna mata takardan hannunta
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ummin ikki ta faɗa kanta har yana sarawa.
"Wannan wani irin sakin wulakanci ne da tozarci?
Ta faɗa tana hawaye, Baɗɗo ba saki ukun take yi ma kuka ba illa maganganun da Habib ya rubuta masu alamu da tozarci da wulakanci bayan sakin
Karɓan takardan Ummin ikki ta yi ta ce bari ta kai ma Abdullahi bayan ta umarci Baɗɗo da ta yi sauri ta naɗe zanin gado ta kuma jawo akwatunan Ummu zuwa falo.
Abdullahi na tsaye jikin motar shi yana waya da Hamma Jibo.
Jiya sai wajen goma na dare suka isa, yana shirin zuwa wajen aiki ne Abdullahi ya kira shi yana sanar da shi mugun labari, shi ne suke tattaunawa yana ba shi labarin halin da ya je gidan Ummu ya same ta a ciki har zuwan da suka yi shi da Baffa gidan waliyin Habibun ashe duk bai ji ba shi ne ya yi mata sakin wulakanci, sai a lokacin Abdullahi ya tuna wato ranar da ya ga Baffa da Hamma Jibo sun tafi ashe can suka je.
"Ni fa Hamma duk ban san abin da ke faruwa ba, kwanaki dai na ganta a gida duk ta rame to ni ban kawo cewa mata matsala ba ce."
Abdullahi ya faɗa yana nusar da hannunsa a cikin sumar kansa.
"An ɗauka za a iya gyara lamarin ne ashe bai zai gyaru ba."
Hamma Jibo ya faɗa daga can bangaren cikin damuwa da tausayin ƙanwar tasu.
Kafin Hamma Abdullahi ya sake magana Ummin ikki ta fito wajensa tana mika masa takardan hannun ta.
"Abdullahi ka ji tozarcin da wannan yaron ya yi mana? Saki uku fa ya yi ma Ummu?
Har Hamma Jibo ya ji abin da Ummi ikki ke faɗa a tare shi da Abdullahi suka saki salati cikin firgici.
Kashe wayarsa Abdullahi ya yi yana mai karɓan takardan hannun Ummi ya fara karantawa a bayyane.
"Ni Habib Idris Mai Imani na saki matata Ummu Salma Hadi Baba saki uku, da ita da cikin jikinta bana ɓukatar su a rayuwata. Na sake ta ne saboda ni ban aure ta domin ina son ba, saboda jikinta na aure ta kuma na samu abin da nake so, shi ya sa na rabu da ƙwallon mangwaro na huta da kuda. Maganar ciki kuma sai da na ce ta zubar da shi ta yi taurin kai da a ce ta ji magana ta da ba haka ba, to ina so ku sani abin dake cikin Ummu Salma ba ni da alaqa da dashi har abada ba ni da danganta da abin da za ta haifa ballanta wata rana a neme ni saboda shi. Ni da Ummu mun rabu,rabuwa ta har abada ku ɗauka ma kamar ba mu taɓa sanin juna ba."
"Hasbunallahi wa'imal wakeel"
Ummi ikki ta faɗa tana mai riƙe kanta cikin baƙin ciki da takaici.
Abdullahi ya ma kasa mgana ji ya yi lamarin ya yi masa nauyi wannan wani irin tozarci ne, lalle wannan yaron bashi da mutumci duk yadda Abdullahi ke da saukin kai sai da ya fusata ya harzuka da wannan sakin wulaƙancin da Habib ya yi ma ƙanwarsu.
"Lalle wannan yaron ba shi da mutumci ba ɗan arziƙi ba ne. "
Ya faɗa yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa. Baffa da Ammah kawai yake tunawa, in ya tuna da Ummu sai ya ji ya karaya, ya take ji yanzu? A wani hali zuciyarta take ciki, ya cuceta, ya cuce su sai dai Allah ya saka musu kawai.
*Janafty*