ALIYU HAYDAR

Chapter 9

by @nieemartullah

Kamar yadda ya saba yau ma kafin ya fita masallaci sai da ya tabbatar duk sun tashi sannan ya tafi masallaci suna idar da sallah duk suka tafi part din dad suka zauna bayan ya dawo suka gaisa sannan ya wuce don shiryawa saboda jirgin bakwai zai bi zuwa qasar Russia bayan ya gama shiryawa cikin wani tsadadden yadi anyi masa dinkin riga three quarter da wando na maza,sosai shekarunsa suka qara buya don idan ka kalle shi baza kace yayi shekaru sittin a duniya ba za ka dauka irin magidan tan nan ne masu ji da lokaci irin yan shekaru arba'in din nan,mom da tun lokacin da ya gama shiryawa ta kafe shi da ido tana ta kallon shi kamar yau ne rana ta farko da ta fara ganin shi har ya qaraso inda take taba daina kallon shi ba duqawa yayi dai dai saitin fuskarta ya hura mata iska a ido murmushi tayi sannan tace anya zan bari ka fita a haka kuwa murmushi yayi ya zame hular kanshi tare da shafa kanshi sannan yace da wannan furfurar ta kaina wacece zata kalleni ma ai ni naki ne ke kadai tace hmmmm na sani kasan fa matan yanxu sun fi son sugar daddy dariyar da bai shirya ba yayi yace toh ki sha kurumin ki ni naki ne ke kadai yanxu tashi mu je kar kisa na rasa jirgi,parlour suka fito inda JAY da hajiya mama suke jiran su addu'a sosai hajiya mama tayi ma tilon dan nata na kariya da fatan nasara sannan duk suka dunguma zuwa parking lot din gidan back seat driver ya bude mashi ya shiga sannan JAY ma ta shiga zata yi masa rakiya zuwa airport bayan sun dai daita zaman su driver ya rufe motar ya bude driver seat ya zauna ya tada motar suka bar gidan har suka fita daga gate din gidan mom da hajiya mama na daga masu hannu sai bayan sun fita daga gidan baki daya sannan suka koma cikin gida,bayan sun shiga cikin gida kitchen mom ta shiga don duba abinda suke yi tana shiga ta tarar suna gyara waken da zasuyi qosai da shi bayan ta gama duba duk abinda zata duba ta wuce dakinta............................

Dawowar shi daga masallaci kenan yaji wayar shi ya fara vibrating alamar shigowar saqo,cire ta daga jikin charge yayi ya zauna gefen gadon dakin aunty ce ta turo mashi saqo idan babu inda zaije zai kaita unguwa da qarfe goma reply yayi mata da tohm Allah ya kaimu sannan ya hau gado ya koma bacci kasancewar yau sunday baya fita aiki...............................

Yau da kanta ta shiga kitchen tana hada breakfast abinda bata taba yi ba tun da aka auro ta gidan barira sai binta take da kallon mamaki don gani take kamar ma mafarki take gashi yadda take magana babu wannan izzar da gadara kamar dai an canja ta tana dai biye da ita har ta gama hada kayan breakfast din ta juyo ta kalli barira da tayi saurin sunkuyar da kai qasa tace mata barira ki kai kayan nan dining bari naje nayi wanka a fito lpia tace mata ta juya ta tafi dakin ta ita kuma ta fara daukar food flasks din tana kaiwa dining.........................

Qarfe tara da minti bakwai ya tashi daga baccin da ya koma bayan ya dawo daga masallaci da addu'ar tashi daga bacci a bakin shi miqewa yayi ya shiga toilet don yin wanka,bayan kusan minti goma ya fito daure da towel a qugunshi gaban madubi ya wuce yana shafawa cream a murdaddan jikin shi da yake yi ma gym,bayan ya gama shafe shafen shi kamar wata mace ya dauka body spray ya fesa sannan ya wuce wurin wardrobe din shi dake cike maqil da Kaya ya bude wani farin T-shirt ya dakko na company Ralph Lauren sannan ya dakko black jeans shima na company Ralph Lauren ya saka komawa yayi gaban madubin shi yana fesa turarukan shi na GUCCI BLOOM,INSTINCT NIOR and OUD NIOR bayan ya gama fesa turaren ya dauki waya da makullin motar shi da suke kan madubin ya nufi part din mahaifiyar shi,bai sami kowa a parlour ba hakan yasa ya wuce bedroom dinta direct,knocking yayi a bakin qofar aka bashi ixinin shiga sannan ya shiga da sallama a bakin shi ta amsa gefen gadon ya zauna yana gaishe da ita ta amsa tana tambayar shi fita zai yi yace eh daxu bayan na dawo daga masallaci nake ganin text din aunty zan kai ta anguwa toh shikenan Allah ya dawo daku lpia yace ameen yace bari naje na gaishe da abbah kafin mu tafi,kayi tafiyar ka kawai ka kaita don abban ku ya fita gidan gona tun da sassafe toh bari naje na kaita a dawo lpia tace mashi ya wuce part din aunty,a parlour ya same ta ta gama shiryawa tana jiran shi ya tsugunna ya gaishe ta ta amsa da fara'a a fuskar ta tana cewa yanxu nake shirin kiranka doctor dan murmushi yayi yace na shiga ne mun gaisa da mama yawwa koda naji ai na dauka ko bacci ne ya dauke ka ta fada tana dariya murmushi yayi bai dai ce komai ba,fitowa suka yi daga parlour ta suka nufi parking lot inda motar tashi take back seat ya bude mata tace kaga ni bana son iyayi haka kawai inyi wani qwam a baya,ta zagaya ta bude front seat ta zauna,shi dai murmushi kawai yayi ya bude driver ya zauna ya tada motar suka bar gidan bayan sun dau hanya tace doctor jiya yaya da daddare yaya ke fada man wani abun farin ciki,ka samu matar Allah ya sa alkhairi ya kaimu lokacin yace ameen dai dai lokacin da yayi horn a bakin gate din wani gida leqowa mai gadi yayi sannan ya wangale masu gate ya shiga ciki,sauka tayi daga motar ganin yana zaune baya da niyyar sakkowa yasa tace doctor baza ka shiga ba ku gaisa da hajiya?da bari nayi idan na dawo zan dauke ki da dare sai na shiga don nasan yanxu gidan a cike yake,kaji da shi in zaka sakko ma ka sakko don gidan yama fi cika in dare yayi,ba yadda ya iya ya kashe motar ya bi bayan ta sallama yayi a qofar parlour da ake ta hayaniya aka amsa masa sannan ya shiga ciki durqusawa yayi ya gaishe da mutanen da ke parlour yan matan ma suka hada baki suka ce ya sadeeq ina kwana ya amsa da lafiya qlau aunty ta kalli Nafeesah tace jeki dakin hajiya ki ce ga doctor ta fito su gaisa da toh ta amsa  sannan ta nufi hanyar dakin hajiya bayan wani dan lokaci suka dawo tare da hajiya zama tayi Akan daya daga kujerun tace sannu da zuwa sadeeq yace yawwa hajiya ina kwana,lafiya lau ya aiki? Alhamdulillah masha Allah ya wajen su hadixa tace a gaishe da ku ina amsawa miqewa yayi yace ni zan koma sai anjima tace toh Allah yayi maka albarka yace ameen sannan yayi wa mutanen parlour sallama ya wuce.............................

Tsaye take a kitchen tana ta tunanin abinda zata yi,yau tun bayan da ta dawo daga raka dad daga airport ta koma bacci,bayan ta tashi take jinta wani iri breakfast ma kasa yi tayi,yanxu ma don taga mom duk ta damu ne yasa ta shigo kitchen don ta samar ma kanta wani abu da zata ci,haka nan taji tana son shan tapioca drawer din dake gefenta ta bude ta dakko tapioca bowl ta dakko ta qara wanke shi sannan ta zuba tapioca din a ciki ta dakko tukunya itama ta qara wankewa sannan ta zuba ruwa a ciki ta kunna gas ta dora fridge ta bude ta dakko apple da grape sai banana ta saka su a wani bowl din ta qarasa wurin sink ta kunna sai kuma ta dakko gishiri da vinegar ta zuba ciki ta fara wanke su bayan ta gama ta yankasu qanana sannan ta koma wurin ruwan da ta dora ta tarar ya tafasa bowl din da zuba tapioca ta dakko ta matsa kusa da tukunyar ta saka butter da vanilla flavour da sugar sannan ta fara zuba tapioca din a ciki tana zuba wa tana juyawa har ta gama wani bowl din ta dakko ta zuba wanda zata sha sannan ta zuba peak milk tana juyawa sai kuma ta dakko wannan cupped fruit din ta zuba akai,bayan ta gama komai ta dauki bowl din ta fito ta zauna a dining tana sha a hankali saboda zafi mom da fitowar ta daga daki kenan ta tarar tana shan tapioca tace haba ko ke fa amma da kin zauna da yunwa sai wani ciwon ma ya kama ki murmushi tayi tace ai bai kama ni ba gashi ina ci yanxu,yawwa JAY ki shirya anjima sai ku fita ke da ayaanah ku sha iska tayi hakan ne ganin har yanxu akwai sauran damuwa akan fuskar ta amma ko yaya idan ta fita zata manta da wani abun toh mom wucewa tayi ta koma dakinta ita ma bayan ta gama shan tapioca din ta wuce kitchen ta wanke duk abubuwan da ta bata sannan ta gyara kitchen din da bai yi wani datti ba,sama ta wuce ta tafi dakinta,tana shiga  ta wuce bathroom don lokacin azahar yayi al'wala tayi ta fito ta shimfida prayer mat ta tada sallah bayan ta idar ta kwanta don wani bacci taji take ji.........................................

Bude flasks din da ta aje ta shiga yi ganin bai taba komai ba yadda ta aje haka ta dawo ta tarar da su,ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tattara komai ta fita da shi a kitchen ta samu barira tana shirya abincin rana ajiye flasks din tayi ta fita har tayi hanyar dakin ta sai kuma ta fasa ta wuce part din shi sallama tayi a parlour sannan ta shiga ganin baya parlour sai qamshin turaren shi da cika ko ina yasa ta wuce bedroom din shi kai tsaye ta tura ta shiga babu kowa a dakin ta kara kunnenta jikin qofar bathroom nan ma shiru babu alamun da mutum a ciki hakan yasa ta gane baya gidan fita tayi daga part din nashi ta wuce bedroom dinta ta zauna a gefen gado tunani kala kala na yawo a kanta....................................

Ana ta kiraye kirayen sallar la'asar ta farka daga baccin da ya dauketa,toilet ta wuce direct tayi wanka sannan ta yi al'wala ta fito bayan tayi yan shafe shafenta ta saka hijab tayi sallah bayan ta idar ta wuce walk in closet dinta ta na duba kayan da zata sa wani A-line maxi skirt flared hem with drawstring waist black colour ta dakko sannan ta hada da wata white T-shirt wadda hannun ta ya kasance long sleeve bayan ta gama saka kayan ta dakko vintage scarf shima baqi ta daura akanta,shigowar mom hannunta riqe da na ayaanah yasa ta juyawa ta kalli bakin qofa ita ma an shirya ta cikin wasu English wears farar riga da baqin jeans sai jacket baqa itama da ta saka mata amma sai ta barta a bude,ta gyara mata gashinta wanda ya ke baqiqqirin sai sheqi yake yi ga tsayi sannan ta saka mata band a fili ta furta masha Allah Allahummah barèèkh feekhum kunyi kyau sosai dan murmushi JAY tayi wanda iyakar sa kan leben ta tace thanks mom wayarta da mukullin sabuwar motar da dad ya siya mata bata taba hawa ba qirar Lexus LX 600 ta dauka tare da riqe hannun ayaanah suna daga ma mom hannu alamar bye bye da addu'a ta raka su har sai da taji fitar su sannan ta sauke ajiyar zuciya ta koma nata dakin.............................

Yau lectures din nasu na yamma ne tunda  suka fito daga lectures suka nemi daya daga cikin gossip chairs suka zauna,magana suke ta yi mata amma ina tayi nisa cikin tunanin da take yi Meenah ce ta sa qafa ta zungureta firgigit ta juyo ta kalleta da manyan manyan idanun ta wanda suka dan koma ciki saboda damuwa Laylah anya Lpia kike kuwa ina lura da ke yau gabaki daya bakya cikin walwala ajiyar zuciya ta sauke sannan tace Meenah ina cikin tashin hankali ne na rasa yadda zanyi,nabi duk irin shawarar da hafsa ta bani but to no avail,me yake faruwa ne kina qara sa ni a duhu,labari ta bata tun daga zargin da ta fara akan Sooraj na neman aure har zuwan su gidan su Jaiyana tana rufe bakinta Meenah ta fara dariya har da riqe ciki a qule tace wani irin rashin mutunci ne zan fada maki matsala ta kina man dariya dena dariyar tayi tace sorry amma kin matuqar bani mamaki ke yanxu a 21st century ki tsaya namiji yana zaman maki ciwon kai,kyakyawa da ke you just turn 22 last month,you are too young for all this,yanxu duk wayewar ki ki kasa daukewa mijin ki hankali daga matan waje gaskiya I'm really disappointed in you hafsat ce ta karbi maganar da fadin kar ki damu idan har na rakaki wani guri damuwar ki ta qare,Sooraj kuwa ko kara kika aje bazai tsallake ba ke ko uwarsa bazai ji maganar ta kamar taki ba,Meenah ce hafsat wannan ba shawarar kirki kike bata ba wallahi kinga duk rashin ji na bana harka da mushirikai shiyasa nake baya baya da ke,ke kuma Laylah idan har kin yadda zaki bita gurin mushiriki toh gaskiya zan ja baya da ku Laylah ce ta dago ta kalleta tace gaskiya Meenah kiyi haquri ni mafita kawai nake nema i can go to any lengths don ganin RAJ bai man kishiya ba,dan murmushin takaici Meenah tayi sannan tace ba baki zanyi maku ba amma ku sani akwai ranar qin dillanci this is all i can say ta dauki handbag dinta tayi gaba miqewa Laylah tayi zata bita Hafsat ta riqe mata hannu tace kar ki damu da ita,mu fara kawar da matsalar dake gaban mu,ba don ranta ya so ba ta koma ta zauna,gobe bamu da lectures don haka ki shirya da wuri zan zo sai mu je gyada mata kai kawai tayi suka tashi kowa ta wuce inda tayi parking motar ta suka wuce gidajen su........................................

Tuqi take yi cikin nutsuwa da qwarewa tana bin waqar badman binladin ta You for me har suka qaraso millennium park,tunda ayaanah ta kalli gate din park din ta washe haqoranta tana dariya cikin maganar yara tace laaa aunty kema kin san wurin nan? daddy na yana kawo ni nan Idan ya dawo gida murmushi tayi tace yau kuma gashi aunty ta kawo ki ko?tana murmushi ta daga mata kai bayan ta dai daita parking ta fito sannan ta zagaya side din ayaanah ta bude mata sannan ta kashe motar baki daya suka wuce cikin park din,Idan ka kallesu sai ka qara kallon su saboda yadda suka yi kyau,kama hannun ta tayi ta riqe suna tafiya ta cikin walkway din dake gurin suna kallon yadda aka qawata wurin da korayen shuke shuke masu daukar hankali,sunyi tafiya mai nisa sannan suka qaraso wurin wani fountain,wuri ta samu ta zauna tana jin wata nutsuwa na shigar ta kasancewar wurin babu hayaniya sai yan dai-dai kun mutane dake wucewa jefi-jefi,ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi,tun bayan da suka yi magana da sadeeq sai yanxu ta samu nutsuwar yin tunanin rayuwar ta tun daga farko ta tashi cikin qauna da kulawa daga ahalinta har zuwa lokacin da rayuwar ta ta juya ta koma upside down har zuwa yau,tunani ta farayi anya bata yi gaggawa ba meyasa baza ta qara mashi lokaci ba kar ta yanke hukuncin da daga baya zai qarasa tarwatsa zuciyoyin su,kiyi addu'a sannan ki bawa sadeeq dama duk abinda yake alkhairi tabbas zai same ki duk ita kadai take ta saqa da warwara ganin Idan tayi shiru zata ci gaba da tunani daban-daban yasa ta dau wayar ta ta fara yi musu hotuna ita da ayaanah...................................

Sallama tayi qofar dakin hajiya mama sannan ta shiga,samun ta tayi akan dadduma tana azkhar gefen gado ta samu ta zauna,sai da ta gama sannan ta juyo ta kalleta ganin kamar tana cikin damuwa,ajiyar zuciya mom ta sauke sannan tace barka da hutawa hajiya bata amsa ba tace Bilkisu mom tace Na'am me yake damunki ko umar yayi maki wani abu? Da sauri ta girgiza kanta tace ko kadan beyi man komai ba dama akan JAY ne,wani abu ya samu Jaiyana ne ban sani ba?A'a babu abinda ya same ta amma ina lura da ita kwana biyu bata cika walwala ba kamar da kuma kin san ta da zurfin ciki wasu lokutan shiyasa nazo naji ko ta fada maki abunda ke damunta dan murmushin manya hajiya mama tayi sannan tace kar kisa damuwa a ranki ki kwantar da hankalin ki munyi magana JAY and it's not something serious stress din aiki ne dan murmushi itama tayi duk da a qasan ranta tasan ba stress din aiki bane da akwai abinda suke boye mata,tace toh shikenan bari na koma dama ina aiki ne a daki tace toh haka ake so Allah ya bada sa'a tace ameen sannan ta fita...................................

Meemarh I'm bored,no one is saying anything to me in the house that why i decided to go out and have some fresh air ta fada a shagwabe,ta cikin wayar wadda aka kira da meemarh tace but you should have told me before going out sweetie,dariya tayi sannan ta kama kunnenta kamar tana gaban ta tace I'm sorry meemarh it's ok sweetie take care of yourself,ok meemarh byeeeeeeee,tana yin ending wayar kamar ance ta kalli gefenta ta hangi JAY da ayaanah suna ta daukar pictures abin su cikin farin ciki what a happy family ta furta a cikin ranta da murmushi akan fuskarta ta qarasa inda suke tace Hii martanin murmushin ita ta mayar mata sannan tace hello cikin yan sakannin da basu wuce ashirin ba ta qare mata kallo tana sanye cikin T-shirt sapphire blue da white rubber jeans sai sapphire blue jacket kasancewar garin akwai sanyi ba fara bace amma kuma baza a saka ta a sahun baqaqe ba,tace as you can see i don't have friends can i be your friend? ta miqa mata hannu kallon hannun JAY tayi sannan ta miqa mata nata tayi shaking hannun tace why not,I would love that dariya tayi sosai tace thank you so much 😊 you are such an angel tayi murmushi tace thank you,would you mind sharing your number with me wayar ta ta dakko ta miqa ma JAY ta saka mata number kira tayi tace this is my number save it kamar an tsikareta ta juya ta tafi har ta tafi kuma ta juyo ta dawo tace my bad I forgot to tell you my name ta fada tana zaro ido kamar wadda tayi ma sarki qarya dariya sosai JAY ke yi,haka nan taji tana qaunar yarinyar oya tell me what your name is,my name is Bilkisu but my mom calls me sweetie and you can call me that too dariya tayi tace ok sweetie I'm Jaiyana,but everyone calls me JAY,ok auntie JAY byeeee,kallon ayaanah da ta  tsaya  tana ta kallon su tayi tace it's getting dark let's go home gyada mata kai tayi suka fara tafiya inda tayi parking motar ta ................

Tun a parlour ta fara kwala mata kira Meemarh Meemarh Meemarh bibbiyu ta rinqa haura steps din ta sakko parlourn kasa ta tarar da ita zaune a kan daya daga cikin kujerun parlour what happened,sweetie? You scared the heck out of me dariya tayi tace it's nothing fah dungurin ta tayi tace Allahummah yahadhiki sweetie dariya tayi tace Ameen and one more thing i now have a friend ta fada cikin farin ciki daga bayan su suka ji ance with this your character who will be your friend?bata ce masa komai ba tace good evening bro ta dauki jacket dinta tayi hanyar da zai kaita dakinta,gefen qafar ta ya zauna ya daura kanshi kan qafar ta sannan yace good evening meemarh,evening son ya aiki yace Alhamdulillah cike da damuwa tace faruq har yanxu babu wani clue da aka samu wanda zai taimaka mana sunkuyar da kanshi yayi don har kunyar fada mata yake bai samu komai ba kayi shiru faruq baka ce komai ba hannun shi ya dora akan nata yace i assure you mom,we will get a clue that will help us find them and in shaa Allah this time around i will be the one going to kano to investigate but before that please meemarh ki rage yawan damuwar nan kin sani is not good for your health gyada mashi kai kawai tayi ta jinginar da kanta da kujera,maganganu ya fada mata na kwantar da hankali sannan ya tashi ya fita,yana fita ta tafi hanyar dakinta saboda ana ta kiran sallar isha'i..................................