Chapter 20
by @khairatup01
ADNAN
BOOK 1
COMPLETED
20
Ya faka motarsa ya bawa security mukulli ya gyara mata zama sannan ya shiga ciki. Bai ci karo da kowa ba a falon haka ya saka ya shiga falo na biyu. Gidan shiru kamar duk ba sa nan bayan ya san suna nan al'adar gidan ce a haka.
Wayarsa ya Zara ya kira Mimi.
"Ke ina falo na biyu ki aiko wanann yarinyar meye ma sunan ta?"
Da sauri tace "Yaya Bilkisu."
"Koma meye send her sauri nake."
"To Ya Artist."
Mimi ta kalli Bilkisu tace "Maza ki shirya ki je Ya Artist na falo na biyu yana jiran ki amma fa ki hanzarta baya son jira zai iya tafiyarsa."
"Haba don Allah ni Artist ya zo gani da gaske?"
"Eh mana kina ɓata lokaci dai."
"To! To! Bara na sauya shiga da sauri."
A gefen tagar falon ya tsaya ,hannunsa cikin aljihun wandon sa, hasken farinwata na ratsowa ta cikin labule yana shiga ciki. Zuciyarsa cike take da nauyi amma ba na tsoro ba, abubuwa biyu yake tunani abubuwan da suke tskanin gaskiya da kuma tilas.
Ƙofar falon aka ɗan yi knocking a hankali.
Ba tare da juya ba yace "Shigo. Amma ko don gaba sallama ake yi."
Ta koma a hankali sanann tayi sallamar
"Salamu alaikum!"
"Wa'alaikum Salam."
Ta buɗe ƙofar da kyau sanann ta shiga ciki. Ta gefen ido ya kalle ta tana sanye da atampa mai kyau ,ba ta da hayaniya.
"Sannu da zuwa Ya Artist."
Ya juya ya ɗan kalle ta saboda Muryar ta da ya ji kallon yan sakanni ya mata sanann yace "Zauna."
Ta samu wuri ta zauna tana daidaita zaman rigar ta.
Shi kuma ya zauna daga nesa da ita sosai kamar yana ƙoƙarin kiyaye wata tazara mai girma a tsakanin su.
Falon ya yi tsit ya yi shiru ba irin shiru na rashin magana ba sai dai irin shirun nan da ke ɗauke da tambayoyi da amsoshin da babu wanda ya furta a tsakaninsu.
A ƙarshe Adnan ya ja numfashi a hankali yace "Bilkisu."
Ta ɗago kai,idanunta suka haɗu da nasa.
"Bamu saba da juna ba, hatta wannan zaman da muka yi ni da ke abu ne da bamu taɓa kawo shi a ran mu ba."
Ta ɗan murmusa kaɗan kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta sanann tace da shi "Haka ne ,komai ya zo ne a bazata."
Ya ɗan sunkuyar da kansa ya fara gajiya amma yana son ya yi wa iyayensa biyayya.
"Zamu yi magana a buɗe ba wani ɓoye-ɓoye ."
Ta gyaɗa kai a hankali.
"Bilkisu wannan auren da ake shirin yi ra'ayin mahaifina ne. Kuma bana son ki shiga cikin abu ba tare da kin san inda kike tsayawa ba."
Bata ce komai ba amma kakansa suna shiga jikinta.
Bata san yadda aka yi ba ta tambaye shi "To kai fa kana son auren?" Ta tambaye shi a hankali.
Tambayar ta tsaya a tsakaninsu.
Bai bata amsa kaitsaye ba ya juya ya kalli gefe ,kamar yana son tattara gaskiyarsa.
"Bana ƙarya don na burge mutum gaskiyar ita ce ban shirya ba, ba don kuma akwai wadda nake so ba ko wadda take cikin rayuwata ba sai saboda bana son auren rashin fahimta."
Bilkisu ta gyara zama,zuciyarta na bugawa a hankali.
"Ni dai Yaya Artist ina son ka, tun kan na san iyayen mu zasu iya haɗani aure da kai ina son ka ina son waƙoƙin ka tuni ka shiga cikin zuciyata.Amma duk da haka ba na son na shiga rayuwar ka kamar wata baƙuwa."
Adnan ya gyaɗa kai.
"Shi ya sa na ce zan zo muyi magana ba don ban gamsu da zaɓin Daddy ba ko kuma wai kin fito daga tsantsan Ammi ba amma ina son mu fahimci juna ina son inji daga gare ki me kike so?"
Ta ɗan yi shiru,tana kallon hannuwanta.
"Gaskiya kake son ji?"
"Gaskiya nake so."
Ta ɗaga kai,idanunta sun ɗan nuna damuwa.
"Ina son auren da zan samu nutsuwa. Auren da zan zauna cikin kwanciyar hankali bana son na rayu ina ƙoƙarin faranta ran mutum amma zuciyata tana kuka."
Kalaman sun tsaya mai a rai.
"Ba zan so haka ya faru da ke ba amma ba zan ɓoye miki ba bana son ki amma ban sani ba ko a gaba."
Ta kalle shi da ɗan mamaki ba ta zaci yana da sauƙin kai haka ba.
"Kai me kake tsoro a auren nan?"
Ya ɗan yi wani kalar murmushi yana kallon agogo yayi magana sama da mintuna goma.
"Bana tsoron komai, amma bana son rashin gaskiya a zamantakewa ,ina tsoron mu zama kamar mutane biyu da aka haɗa su amma ba sun san juna ba, ina tsoron ki ji kamar an ɗaura miki rayuwa ne ta dole."
Ta ɗan sauke numfashi.
"To yanzu fa, yaya zamu yi?"
Ya ɗan jingina bayansa da kujera yana kallon sama na yan sakanni sannan yace "Ba zan ce mu ƙi auren ba kuma ba zan ce miki zan iya miki komai ba amma ko da anyi auren mu bawa kan mu lokaci tukunna."
"Lokaci?" Ta maimaita.
"Eh ba kamar ma'aurata ba kamar mutane biyu masu son fahimtar junansu idan muka ga zai yiwu sai mu zauna idan muka ga ba zai yiwu ba sai mu fawallawa Allah."
Bilkisu tayi shiru tana nazartar kalamansa "Amma ka san hakan ba abu ne mai sauƙi ba."
"Na sani, kuma na san hakan zai fi mana sauƙi fiye da rayuwa cikin rashin jindaɗi."
Shiru mai cike da nutsuwa ya ratsa falon can kuma Bilkisu tayi wani murmushi,murmushin da ya ratsa har cikin zuciyarta.
"Ya Artist ban zata zaka ma iya zama dani har kayi magana dani har haka ba ban san ma zaka iya min magana ba."
Ya ɗan ɗaga girar sa kaɗan.
"Yaya kika zata to?" Ya tambaye ta yana rungume hannu a ƙirji.
"Na zata zaka kasance mai taurarin kai ne da faɗa."
Ya yi murmushi kawai suka kalli juna wani abu ya tsarga a tsakanin su ba soyayya ba ce tukunna,amma akwai wata irin fahimta mai zurfi da ta shiga tsakaninsu.
Adnan ya gyara zamansa yace "Gaya min wace ce ke?"
"Wane ɓangare?"
"Duk ta inda zan san ki."
"Ni mutum ce mai son nutsuwa ,bani da son hayaniya,ina daraja iyayena,shi ya sa ma na ke cikin wannan halin a yanzu."
Ya gyada mata kai yana sauraron ta.
"Kina da wani buri?"
"Buruka kai."
"Zan so ki cika burukakan ki."
"Da gaske?"
"Eh. Amma fa ki sani bana son mace mara kamun kai ,ballagaza,wadda ya saida mutuncinta."
Ta gane me yake nufi
Sannan bana son ya zamana kin rasa wacce ke saboda kawai kina aure na kiyi rayuwar ki sharaɗin kawai shi ne kar ki matsa min, kar ki ce zaki zama uwata,kar ki ce zaki kuma rusa darajar aure. Idan kika kiyaye wannan zamu zauna lafiya babu wata miskila.
"Haƙiƙa ka zame min wani haske wanda ya haska min duhu a kan ka. A da ina tsoron yadda rayuwata zata sauya amma a yau bana tsoron komai sai fatan alheri ga junan mu."
Da biyu ya zauna na farko jiran Sahib na biyu kuma yarinyar ta burge shi. Suka cigaba da magana a tsakaninsu suna tambayoyi da amsa har mamakin kansa yake yi.
Daga karshe Sahib ya kira shi yace ya zo. Ya kalle ta yace "Zan tafi."
"Na gode."
"Saboda me?"
"Saboda ka bani damar na zama ni."
"Mu duka muna da bukatar hakan. Ki karbi lambar waya ta a gun Mimi ki min text kice kece in ba haka ba za kiyi ta kira ban ɗauka ba."
Tayi dariya sannan tace "An gama Yallaɓai." Ta fita daga falon shi ma.
*
Daga motarsa ya fito suka tafa yace "Blaze."
"Sahib."
"Meke damun ka?"
Adnan ya ɗaga kai a hankali,murya ƙasa-ƙasa kamar wanda bakinsa ke ciwo.
"Wallahi Sahib... bana jin daɗin kaina."
"Baka jindaɗi? Kana da lafiya kuwa? Ko asibiti zamu?"
Ya girgiza masa kai.
"Ba ciwon jiki ba ne wani abu ne na daban.Duk lokacin da na gan ta zuciyata daban take bugawa kamar zata hudo ta fito waje ko ta fashe."
"Wace ce?" Sahib ya tambaya yana ɗaga gira.
Adnan ya yi shiru na ɗan lokaci kamar yana jin nauyin furta sunan. Can ya kumshe idanu ya kuma buɗe su a hankali yace "Blue eyes."
Sahib ya ce "Kuma na san ta? Ko ta mafarkin nan da ke zuwar maka?"
Tsaki ya yi ya fincike hannunsa zai bar wurin ya kamo shi yace "Yi haƙuri gaya min sunan ta."
"Lamrat."
Ya kuwa sake kecewa da dariya.
"Ahhhh! Wannan ne ciwon naka?"
Bai yi dariya ba amma cike da nutsuwa ya cigaba da magana yace "Ba wasa nake ba fa...idan ta kalle ni da waɗancan idanun nata...na azure...kamar ina mantawa da komai. Ina jin haushi,amma lokaci guda...ina son sake ganin ta."
Sahib ya dafa kafaɗarsa yana girgiza kai yace "Guy ka rikice ne."
Adnan ya ɗan ja gaba kamar wanda yake ƙoƙarin tserewa daga tunanin kansa.
"Ban san me ke faruwa da ni ba.Ni da na sa a raina babu wata mace da za ta iya shigowa rayuwata haka ba...amma yanzu...idan ban gan ta ba,ina jin kamar wani abu ya ɓace a rayuwata."
Sahib ya yi masa wani kallo cike da dariya da Allah Ya ƙara ya na tafa hannu yace "Congratulations Blaze...You are in love...."
Adnan ya tsaya cak kalmar ya bugi zuciyarsa ya MAIMAITA kalmar "Love" kamar bai taɓa jin kalmar ba.
Sahib ya matsa kusa da shi yace "Eh mana. Wannan ciwon da kake ji ba ciwo bane soyayya ce."
Adnan ya yi shiru ,ya sauke numfashi mai nauyi.Idanunsa sun ɗan sauya,kamar ya shiga wani sabon yanayi.
"Idan wannan soyayya ce to Wallahi Sahib tana iya hallaka ni."
Me Sahib zai yi in ba dariya ba ya fashe masa da dariya yace "Ko kuma ta gina ka ba."
Adnan ya juya bayan sa ya bar kallon Sahib Wallahi da gaske yake zuciyarsa cike take da rikici.
Ya dafa kafaɗarsa ta baya.
"Ba zaka fahimta ba kana min kallon wawa ko ban san me nake yi ba bayan ni ina da bukatar kwanciyar hankali."
Sahib yace "Afuwa! Abin ne dole ya bani dariya kuma ya bani mamaki.Ban taɓa ganin ka a haka ba."
"Ba wai ina son ta bane kawai ina jin kamar tana da iko a kaina. Kamar duk wani abu da nake ƙoƙarin ɓoyewa a kaina tana gani."
Ya ɗaga gira yace "Wannan kuma wani sabon level ne."
Adnan ya matsa kusa cike da murya ƙasa-ƙasa sosai kamar yana tsoron a ji shi.
"Idan ta kalle ni...ba jin kaina kamar Adnan Blaze ,bana ganin kaina a matsayin mutumin da duniya ta sani. Daban nake jin kaina."
"To ka gaya mata mana ,me kake tsoro?"
"Ina tsoron kaina ne.Ni ba mutumin kirki bane."
"Kai dalla wannan drama ce taka kuma ka daina kawai ka faɗa soyayya ne You are in love."
"Na rantse maka idan ta cigaba da kusantata ko dai na lalace ko kuma ta lalace duk abinda ya kusanto ni baya kai labari."
"Kai! Guy cool mana ba gani ba ina tare da kai tsahon shekaru me ya same ni? Ga su Daddy, ga su Mami Ga Hamma Deen..."
"Ishaq fa?"
Sai ya yi shiru.
Ya sa hannu biyu ya dafe kan sa yace "Ban taɓa jin irin haka a rayuwata ba Sahib ban taɓa ba zan haukace the feelings is killing me deep inside me. Ba fushi ba ne, ba sha'awa ba ce wani abu ne na daban,wani abu da na kasa sarrafa kaina."
"Tana jin haka a kan ka?"
Tambayar ta tsaya masa a rai,Lamrat yadda take kallonsa yadda take tsoron sa yadda idanunta ke cike da wani abu da ya kasa fassara su.
Numfashin sa ya tsaya.
"Ban sani ba, idan ma tana ji hakan zai zama hadari gare ta."
"Ko kuma hakan ya zama alheri ba."
"A rayuwata abubuwa masu kyau ba sa jimawa."
"To wannan karon ka gwada bari ka amshi soyayyar da zuciya ɗaya."
Ya sauke numfashi ya kalli wata a sararin samaniya sai dai shi ba watan yake gani ba Lamrat yake gani a fuskar watan a ransa yace "Wannan wani irin abu ne mai kama da kaffara kamar kuma masifa."
Sahib ya tsura masa ido ,yana ƙolarin karantar wani abu daga fuskar Adnan.
"Ka yi shiru."
Ya sauke wani irin numfashi mai zurfi, ya shafa fuskarsa kamar wanda yake ƙoƙarin dawo da nutsuwarsa.sai ya gyara tsayuwarsa a hankali,yana kallon gefe kamar yana kauce wa gaskiyar da ke gabansa.
"Akwai wani da zan yanke."
"Me kenan?"
Ya yi shiru kafin ya ba shi amsa.
"Wani satin....ran asabar.."
"Me za ayi wani satin?"
"Ina ganin zan haɗa aurenta da na Bilkisu a rana ɗaya."
Kamar an jefa wuta a tsakar gidan Sahib ya buɗe baki,idanunsa suka yi waje don tashin hankali yace "Wait...what?"
Adnan bai kalle shi ba ya ci gaba da kallon gefe ɗaya.
"Abinda ya kamata nayi kenan."
Sahib ya kama kansa da hannu biyu yana zagaye farfajiyar gidan.
"Guy! Lallai kana cikin soyayya mahaukaciya..za ka haɗa auren mata biyu a lokaci ɗaya? Ka san Daddy ba zai taɓa bari ba kar fa ka mata yarinyar ma bata san kana yi ba kaima ba ka sani ba dai yau ya haka ne Artist?"
"Meye? Na ce maka ban da lafiya ne?"
"Kai! Ba zai yiwu ba."
"Zai yiwu ni ne mijin ,ni ne kuma ikon me zai hana na iya?"
"Daddy yana daraja martabarsa ba zai taɓa karɓar ta a matsayin suruka ba ko ka manta ma yar aikin gidan ku ce?"
"Shi ne me?"
"Ka ce shi ne me?"
"Yes shi ne me?"
"Adnan kana wasa da wuta."
"Sunan nawa ai Blaze ko ka manta ne?"
"Ka yi magana da yarinyar."
"Bana buƙatar yardar ta ni ai tunda na yarda shi kenan."
"Adnan...."
"Kai wanann ce mafitar zuciyata."
"Wani lokacin zuciya bata bada mafita mai kyau."
"Zaku rasani in kuka hana ni burin zuciyata."
"Ka sake shawara."
"Na riga na yanke hukunci."
"Blaze..."
"Sahib shiga mota sai da safe."
Yana kaiwa nan ya shige cikin motar sa ya yi gaba.
Sahib ya bi bayan motarsa da kallo Adnan ya taro yaƙin da bai shirya masa ba kuma abu mafi muni shi ne Lamrat bata ma san an yanke mata hukunci ba.
*
Ƙyauren ɗakin nasu ta tura da hannunta tayi ƙara kaɗan, duk da haka sai da ƙarar ya cika gidan saboda ta ƙarfe ce.Tabarmar da aka shimfiɗa a ƙasa ta ɗan murɗe alamun ta jima ana amfani da ita,duk ta koɗe. Ta tsaya a jikin ƙyauren na yan daƙiƙu. Yau gidan nasu tsit ga dukan alamu ba sa nan sun tafi sana'o'insu. Amma tana jin ƙarar tukunya wataƙila Umman ke girki yau.
Cikin ranta kuwa amo kawai ke tashi ta sauke mayafin kanta a hankali ga rataya shi jikin ƙugiyar dake tsakar ɗakin ta ma kusan faɗuwa.
Ta zauna a gefen tabarmar hannun ta na rawa.
"Aure zai yi?" Ta tambayi kanta a hankali kamar tana tsoron kalaman na ta.Sai kuma ta girgiza kai da sauri tace "A'a ba zai yiwu ba." Wata zuciyar tace mata "Me zai hana ya yi ke wace ce a gun sa ? Mutum kamar shi da duniya ta sani ga ilimi ,ga aji,ga dukiya, ga kyau, ke yar aiki ,yar talakawa yar aikin gidansu taya ma za ki yi tunanin yana son ki? " Ta ɗaga kanta ta kalli ɗakin yadda bangon ɗakin ma ya tsare ,ga tsohon kwano a sama da wata ƙaramar fanka ta gwan-gwan na juyawa tana fitas da ƙara saboda gajiyar da ta yi.
Zuciyarta ta buga da ƙarfi ta sa hannu ta dafe ƙirjinta a fili tace "Kar ki manta matsayin ki Lamrat."
Ta jingina da bango hawayen da take ta maƙalewa suka zubo mata bana farinciki ba kuma bana baƙinciki ba illa na ruɗani ,tsantsar ruɗani.
Daga can ɗakin girki Umma ta kira ta.
"Lamrat."
Ta firgita,ta goge idonta da sauri.
"Na'am Umma ina zuwa." Ta faɗa haɗe da miƙewa da sauri tana share hawayen fuskar ta da bayan hannu kar Umma ta gane.
"Na'am ɗin uban wa? Ki dawo kin shige ɗaka bayan kin gan ni ina ta kici-kici da girki.kin bar ni da aiki kamar wata sarauniya kin ƙule a ɗaka."
"Maza ki wanke kwanukan can." Ta nuna mata wasu kayan wanke-wanke himili guda kamar cikin dare bata wanke wasu ba da gayya aka ɓata su. Ita kanta yanzu mamakin yadda tayi sanyi take yi don da da ne sai ta bata amsa kuma ba zata yi aikin ba amma zaman ta da Mami duk ta sauya tayi laushi.
"To."
"Shegiya ai amfanin ki aiki uwar ki ta mutu ta bar min ke kamar wata kaddara."
Lamrat taji ranta ya ɓaci. Ta tsani a taɓo mahaifiyarta ita kuwa Umma bata da wani aiki sai na sako marigayiya.
Sai dai ta danne komai. Ta dinga ambaton sunan Allah a ranta.
Ta durƙusa ta soma ɗaukar kwanukan dake wajen ba tare da ta ce komai ba.. Ita kanta Umma sai da ta sha jinin jikinta ta kuma cika da mamakin sauyin da take gani a tare da Lamrat kwana biyu.
Duk zagi da kwashe daraja Umma ta mata kuma ta jefe ta da su amma da ta ji hawaye na neman zubo mata sai ta kulle idanunta fuskar Adnan ta hanga yana mata kallon mutunci yana mata kallon mai daraja a karon farko suka so su fito daga bakinta amma ta danne su don idan tayi magana komai zai rikice a gidan ta tattara komai ta soma wankewa tana jin ƙananun mitocin Umma amma ta baiwa banza ajiyar ta.
"Munafuka kawai mai idon mayu,kina ji yanzu ke wata aba ce mai daraja ko? Da ina da hali da tuni na watsar da ke daga gidan nan."
*
Adnan ya tura ƙofar ɗakin Mami da ɗan ƙarfi ya shiga ciki. Fuskarsa a ɗaure idanunsa cike da gajiya sai dai cikin su akwai ƙuduri. Ba tare da ya tsaya ba ya shiga ciki kaitsaye inda Mami ke linkin kaya.
Ta ɗago ta kalle shi,ta ɗan murmusa sannan tace "Adnan ,yaushe ka shigo,amma ya na gan ka haka ko yunwa kake ji?"
"Mami...ba wanann ba ne." Ya ja kujera ya zauna ya kamo hannun Mamin.
Mami ta lura da yanayin sa kamar ba lafiya ba.
"Lafiya dai?"
"Mami i want to get married."
"Na sani ba shi za ayi maka ba wani satin?"
"Mami ba haka bane i have other plans."
"Wanne plans kuma ? Ba ga Bilkisu ba? Me kake nufi ne kai?"
"Mami zan aure ta mana ...amma ba ita kaɗai ba."
Kalaman Adnan suka saka Mami gyara zaman ta tace "Me kake nufi?"
Adnan ya jingina bayansa kaɗan,yana kallon Mami bakinsa har rawa yake yi ya rintse ido sannan yace "Ina son Lamrat."
Shiru ya ratsa ɗakin gabaɗa sai sautin bugun zuciyoyinsu kawai su biyu. Mami ta nemi duk wata kalma ta rasa tana kallonsa kawai kamar tana ƙoƙarin fahimtar ko wasa yake yi. Kamar an zabure ta kuma sai tace "Wacce Lamrat ɗin?" Ta tambaye shi da murya mai sanyi.
"Wacce ke miki aiki a gidan nan. Wacce kike wa kallon ya."ya faɗa kaitsaye.
Mami ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Babana ka san abinda kake faɗa kuwa?"
"Mami ba tambaya nake ba fa."
Tayi masa wani irin kallo saboda yadda kalaman sa suka yi mata nauyi a kunne. Ya ci gaba da magana.
"Ina sanarwa ne."
Ta kuma kallon shi da mamaki. "Kana nufin..."
"Zan aure su duk su biyun a rana ɗaya."
"Ka san mahaifin ka ba zai yarda ba ka ...."
"Mami in har ba za ayi min hakan ba to ita ma Bilkisu ba zan aure ta ba."
"Ba fa abin wasa bane Babana."
"Mami nima ba wasa nake yi ba rayuwata ce."
"Adnan ba zan iya wannan fitinar ba kai ka sani mahaifin ka ba zai taɓa yarda ba ka sani mutuncinsa shi ne gaba a gun sa."
Ya tashi tsaye ya gyara hannun rigarsa yace "Ki taimake ni ki shawo kan Daddy. Ina son a haɗa auren lokaci guda ran asabar." Ya juya zai fita yana kai wa ƙofa ya tsaya amma bai juya ba yace "Idan kuma kina ganin hakan ba zai samu ba to ku bar ni da rayuwata a yadda nake amma kar a tilasta min abinda zuciyata bata so." Ya sa kai ya fice.
Ya bar Mami da jimami da tunani tsakanin son ɗan ta da kuma tsoron abinda zai biyo baya domin wannan yaƙi ne da ba zai zo da sauƙi ba.
Ta zauna shiru cike da tunani iri-iri ba komai ke damunta ba kamar tsoron karon su da Daddy da yadda za su yi fama da shi.
Lamrat yarinyar kirki ce, tun zuwan Lamrat ta gane cewa akwai wani abu a tattare da ita, akwai wani abu a fuskar ta,akwai kammani da take gani a tare da ita ,Mami ta ɗan lumshe idanu,kamar tana ƙoƙarin tuna wani abu da ya ɓace a baya.
Na san fuskar yarinyar amma a ina?"
Ta sani Daddy ba zai yarda ba, ba don Lamrat bata da kyau ba ,ko bata da tarbiya ba a'a sai don a wurinsa matsayin ta bai kai ba saboda ita yar aikin gidan ce.Mutuncinsa ,sunan sa,matsayinsa cikin al'umma waɗanan abubuwa ne da ba ya wasa da su.Take a fili tace "Ba ma zai saurare ni ba."
Nan Mami ta zauna tana juya zoben hannunta. Deen ya shiga ciki da sauri yace "Mami gani meya ya faru kika kira ni cikin gaggawa?"
"Waye in ba Adnan ba?"
"Me ya yi yanzu kuma?"
"Fitina , rigima yake son ya tada min tsakaninsa da ubansa."
"Ta me?"
"Wai mata biyu zai aura."
"Mata biyu? Dama yana soyayya da wata ne?"
"Ban sani ba ban san komai ba Deen."
"Wacce ce yake so?"
"Lamrat."
"Wace...ba dai wanann yarinyar ba me blue eyes?"
"Ita mana."
"Mami ba shi da hankali? Magana zai ɗauko mana?"
"Ka san halin shi da naci ya saka abin a zuciyarsa in yace sai ya samu abu sai ya samu."
"Mami Daddy fa?"
"Shi ne matsalar. Daddy ba zai taɓa yarda ba. Bana son wannan maganar ta zama rikici tsakaninsu. Idan kuma aka matsawa Adnan ka sani zai aikata abinda ba a taba tunani ba don ya sanar min ba fa wai tambaya yake ba sanar mana yake yi."
"Mami me kike so ayi yanzu?"
"Ko dai a shawo kan Adnan ya sauke fitinarsa ko kuma a shawo kan Daddy."
"A'a Mami a shawo kan Adnan. A nuna masa cewa ba kowanne abu da zuciya ke so bane take dacewa da rayuwa ba."
"Kash! Deen ka san soyayya ba ta jin magana idan ta makantar da mai yin ta."
Washegari!
Iskar sanyin safiya na ratsowa ta labulen ɗakin Adnan. Bai yi bacci sosai ba tun da ya gane cewa yana son Lamrat.
Ƙofar ɗakin aka buga. Ya ziro ƙafafunsa ƙasa don ya ga waye a ƙofa wataƙila ma Lamrat ce zuciyar sa ta raya masa.
Yana buɗewa ya ga Mami da Deen a bakin ƙofar.
Ya juya ba tare da yace musu komai ba.
Suka shiga ciki. Ya zauna a kan gado ya ce "Mami ina kwana."
"Lafiya."
"Hamma Deen."
"Uhm lover boy."
Ya kalle shi amma bai ce komai ba.
Mami ta ce "Adnan." Cike da nutsuwa ya kalle ta kallo ɗaya ta mai ta gane bai samu baccin kirki ba.
"Bro ka gaya mana gaskiya.Tun yaushe kake soyayya da ita?"
Adnan ya yi shiru na ɗan lokaci yana tattara kalmomin da zai yi amfani da su ya saki numfashi mai nauyi sannan yace "Ban san tun yaushe ba amma maganar gaskiya jiya na soma ji.
Kalmar "jiya." Ta tsaya a iska kamar wani sirri mai nauyi yana neman ya fallasa.
Daga waje bakin ɗakin hannun Lamrat ya soma rawa shayi ne da ta saba kawo mai ta kawo masa.
Tsoro,mamaki duk suka ratsa ta. "Ni kaina jiya na ji ina son ga..."
Kalmar ta sake dawo mata kunnen ta.
"Kaf!" Kofin shayin ya faɗi ya fashe shayin ya malale kamar wani sirri. Su uku suka juyo a lokaci guda.
Mamakin ganinta suka yi. Da sauri ya sauko ya fito ya tsaya a gaban ta ya soma tambayar ta da zafi-zafi.
"Baki ji ciwo ba ko? Ba ki ƙone ba ko. Mami zo ki gani don Allah shayin fa da zafi."
Mami ta kalli kafar Adnan ba ko takalmi a ƙafar shi kuma yana cikin shayin da tangaran ɗin da ya fashe.
Lamrat kuwa ko motsi ta kasa yi idanunta sun ƙara girma ta kasa magana.
A wannan dakiƙar duk abinda ke ɓiye ya fito fili ba tare da an furta shi ba.
Amma tambaya ɗaya ta tsaya a tsakaninsu,shin abinda ta ji zai haɗa su ko kuma raba su zai yi na har abada?
Lamrat ta juya a hankali ba tare da tace komai ba ta fara tafiya matakanta suna da sauƙi,amma kowanne yana ɗayke da nauyin da zuciya ba zai iya ɗauka ba.
Mami da Deen suka matsa kusa da shi amma suka kasa cewa komai don sun san wannan ba ƙarshen labarin ba ne wannan farkon rikici ne da zai iya canja komai......