UWAR AGOLA

Chapter 7

by @mamanafrah3028

*UWAR AGOLA* 

         🅿️7️⃣


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya Slsai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo Zamzam tamkar yar budurwa.*

*Tasirin magani Idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga Amare, uwargida ,zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*


*UWAR AGOLA*

                
                 NA
 
     MAMAN AFRAH
 
    *Daga marubuciyar* 
 *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
   ***


             🅿️7️⃣

  Hudu ne a gaba lokacin da za su fito daga cikin gidan Malam yana biye da shi, gabaɗaya idanunsa kafe a jikin kayan Hudu ba don kar Hudu ya ce bashi da godiyar Allah ba, kuma bai gode ƙoƙarinsa ba kawo masa yadin da ya yi ba da sai ya ce ya tuɓe kayan jikinsa ya bashi ya saka, don ya hango tsantsae tazara mai yawa tsakanin kyan da ya yi da kuma kyan da Hudun ya yi. A zahiri ma dai sai dai a ce kyan da Hudu ya yi amma Malam Nura ba za a ce ya yi kyau ba za dai a kira abin da ya yi da suna, ba yabo ba fallasa. 

  Suna fitowa ƙofar gidan inda jama,a suke jiransu, saboda Malam ya yi gayya sosai, ga kuma wanda Hudu ma ya gayyato, tun da ya ga Malam yana ji da auren nan nasa da Hadiza.

  Kunya ce ta kama Malam Nura ganin duk kamar ma ido ba ya kansa, sai hannu ake ba Hudu ana gaisawa da shi, sai sun fara bashi hannu sannan ake ba Malam, wannan wai wanda ma suka san shi ne angon bare baƙi kamar makaɗa da maroƙa da suke ta wasa Malam Nura amma kuma Hudu suke kallo alamu sun nuna cewa sun ɗauka shi ne angon. Hudu ganin wannan kara da ake musu ya sanya hannu a aljihu ya ciro yan naira ashirin sabbi yake liƙawa maroƙan kamar wanda suke jira suka shiga ƙara ƙaimi wajen ƙarawa kiɗan nasu da wasawar armashi, shi kuma sai gyaɗa kai yake alamar yana taya Malam Nura farinciki. Malam Nura da bai fito da ko sisi ba, takaici ya hana shi magana sai hannu yake sakawa a kai- a kai yana gyara zaman hularsa, wacce tun lotsewar da ta yi lokacin da Hudu ya bi ta kanta bata dawo daidai ba sai yake jin kamar an kifa masa kwano a kan. Wato ta ƙi zama daidai.

  Kabiru da Lawwali ƴaƴan Malam Nura ne suke musu da wasu yara abokansu wanda musun ya sauka a kunnen Malam Nura inda abokin nasu yake cewa.

"Ashe daman ƙarya kuke da kuka ce babanku ne ango, ashe bashi ba ne baban su Ya,u ne(Hudu) Kallu shi ne ya sanya sabon kaya amma babanku tsoho ya saka, ai ango ba ya saka tsohon kaya" 

Kabiru ne ya ce

"Wallahi muna babanmu ranar nan ya siyo sabon kaya mai kyau aka masa ɗinki, kayan sun fi na baban su Ya,u kyau" 

Yaron ya ce

"Ai dai tun da bai saka ba bashi ne ango ba" Malan da yake jin tamkar ya kwaɗawa yaron nan mari musamman da yake jaddada cewar Hudu ne ango sai tsumin Malam Nura na kishi ya motsa nan ya ci gaba da cika yana batsewa.

  Ayari suka yi don zuwa can gidan matan inda za a ɗaura auren, hakan ya sa aka fara tafiya masu kiɗa suna yi. Malam Nura ne ya ji duk hankalinsa ya tashi domin yana tsoron haɗuwarsa da Hadiza ba ya ma fatan ta gan shi da kayan jikinsa. Hadiza kuwa kamar ta san tunanin da yake ta doko masa waya, jin wayarsa tana ƙara ya ciro ta daga aljihu kamar ya san ita ce kuwa domin a ransa ita ya ƙiyasta za ta kira shi a daidai wannan lokacin.

  Wani gumi ne ya karyo masa amma ya yi ta maza ya maze ya ɗaga wayar suna tafiya, yana karawa a kunne ta ce

"Ni fa na ƙosa in ganka wallahi, don tun da ka ambata min cewar ka yi kyau na ban mamaki, gabaɗaya sai na ji ka kwaɗaita min son ganinka, don na san yadda shaddar ta karɓe ni kai ɗin ma haka ne a naka ɓangaren" Hannu ya kai goshinsa ya sharce gumi, ya mayar da idonsa jikin kayan jikinsa ya haɗiye wani yawu muƙut ya ce

"Yanzu dai gamu nan za mu je wajen ɗaurin auren" Sautin dariyarta ya ji har cikin kunnensa ta ce

"Ka ce yau zan yi kwalli, don kafin ka ƙarasa wajen ɗaurin auren ka fara zuwa mu ga juna" Ƙulululuuuu cikinsa ya bada wani sauti don ya san tana son ɓallo masa ruwa  ne, matuƙar ta ganshi da kayan nan ya san sai dai wani angon amma ba shi ba.

Yana ƙirƙirar dariyar yake tamkar wani sabon mahaukaci ya ce

"Haba Hadizatuwata, ni yanzu duk na matsu in ga an ɗaure mu da igiyoyin nan guda uku ki jira ni idan aka ɗaura sai in zo yau sai kin gaji da ganina don kanki" Ya faɗa yana aikawa Hudu harara wanda yake ƙunshe dariyarsa.

Ta yi ɗan shiru, Malam Nura yana ta addu,ar ka ta ƙi amincewa ko kuma ya masa masifar nan tata, kamar daga sama ya ji ta ce

"To shikenan sai an ɗaura ɗin ka zo, mai hoton ma yana nan yana yi a cikin gidan amma ni na ƙi yi na fi so sai mun yi tare kar kwalliyata ta ƙoƙe" Yana godewa Allah a zuciyarsa da cin nasarar da ya yi ya ce

"Yawwa haka nake so, ai ana shafa fatiha zan garzayo nan" Ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya ya san dai duk tsiya in aka ɗaura aure ba za ta ce a warware ba, ko ta ce sai ya sake ta ai dai ganin damarsa ne tun da sakin a hannunsa yake.

  Yana yin wannan tunanin ya ji ta ce

"Ai ba zan jure ba, tahowa zan yi in tsaya ta windown gidanmu in hango ka, ka ga na yi kwalli kenan" Malam Nura wata wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauke, jin wata lukutar masifar.

  Bai gama tunani ba da ya ji ta sake cewa

"Dan Allah idan kun zo wucewa ka ɗago min hannu" Cike da ƙoƙarin danne damuwarsa ya amsa mata, amma a ransa yana raya cewa ba zai taɓa yin abin da ta ce ɗin ba saboda kar ta je ta ganshi komai ya caɓe.

  Yana shirin datse kiran ta ce

"Ni yau duk kishin ka ma nake ba na so ake gani min kai, domin ko matanja ba don matanka ba ne da basu fara gane min kwalliyar ɗaurin aurena da kai ba" Dariya ya yi amma a zahiri ta ji sautin a baɗini kuwa dariyar yaƙe ce ya ce

"Daman na yaga buhu na rufa a kaina yadda babu kowacce mace za ta gane miki ni, ko wajen ɗaurin auren sai na je da buhun rufe a kina" Dariya take sosai ta katse wayar bayan ta faɗa masa tana jiran wulgawarsa.


  Tana katse wayar ya kalli Hudu bayan ya sanya hannu ya goge gumi, ya ciro hularsa ya shiga fifitawa a kansa da shi ma tuni ya jiƙe da gumin yana ƙasa da murya ya ce


"Hudu ina cikin talatainin masifa, Kuluwa ta cuceni, yanzu ga Hadiza can a windon gidansu in za mu wuce in ɗago mata hannu ta ga kwalliyata" Hudu ya bushe da dariya ganin gabaɗaya jama,ar fa suka taho tare kowa sabgar gabansa yake ya ce

"To mene ne abin tashin hankalin sai ka ɗaga mata hannun ai" Harara ya aikawa Hudu bai sake cewa komai ba, har suka kusa shiga layin gidan su Hadiza gaban Malam Nura yana dakan lugude.

  Tun da aka shiga layin ya kutsa tsakiyar mutanen da suke tafiya, ya dunƙufar da kansa yake kallon ƙasa, Hudu ne yake faɗa masa cewar ya hango ta tana leƙowa daga windown, suna zuwa Malam Nura ya nannaɗe hannun rigar jikinsa sai da ya kai wajen kafaɗa yadda ba za a hango kalar yadin jikinsa ba, yana ɗan sunkuyawa kamar mai ƙusumbi ya shiga ɗaga hannu saitin ƙofar gidan nasu, don shi dai kawai ɗaga hannu yake yana bye-bye yi yake babu ƙaƙƙautawa.

  Hadiza wacce ta kira ƙawayenta guda biyu take shirga musu ƙaryar kuɗin shaddar da Malam Nura ya ɗinka musu ita da shi da yaranta, don dai da ta linka kuɗin ta faɗa musu, su kuma suka yarda suna fasa mata kai a kan cewar lallai ta tsinci dami a kala tun da dai gashi har ƴaƴanta ya yi ws kayan fitar biki ba su san cewar dai da aka kai ruwa rana ba ya ɗinka.

 Tsaye suke sun zubawa hanyar ido har dai suka fara jiyo tashin kiɗa, Hadiza ta ji kanta ya fashe, ƙawayenta suka ci gaba da wasa ta, musamman da suka ga mutane sun shawo kwanar sai kiɗa ake ana wasa ango, kowa ya gyara tsayuwa don ganin angon Hadiza don ta ce musu ya fi tsohon mijinta komai, gashi da kuɗi kuma ba ya jin ciwon fitar da kuɗi, hakan ya sa suka sake ganin girmanta.

  Tun da suka hango mazan suka zuba na mujiya, kasancewar ma su mazan da suka taho tawagar angon daga can tsallaken hanyar suke ba daga saitin inda gidan su Hadizar yake ba, wato daga tsallen dama suke tafiya, gidan su Hadiza daga ɓangaren hagun.


  Ɗaya daga cikinsu har ɗaɗɗage take tana son hango angon, Hadiza tana hararta tana cewa za ta gane mata ango. Amma maimakon ango ya fito fili a ganshi tamkar wata ɗan daren goma sha huɗu, sai ya ɓace a cikin mutane tamkar kifin da ya nutse a ruwa, hannunsa kawai ake hangowa, a haka yake tafiya a dudduƙe tsoronsa ɗaya ma kar ya yi tuntuɓe ya je ya faɗi a shiga uku don idan ya faɗi ya san dole Hadiza ta ganshi don daga ya faɗi za a fara cewa ango ya faɗi dole a ganshi kuwa. Hudu ztsabar dariya har da hawaye, mutane kuwa babu wanda ya lura da abin da yake faruwa.


Ƙawayen Hadiza ne suka ce


"Kin ce mu zo mu ga ango zai ɗago hannu, amma mu babu wani ango da muka gani bare mu ga kwalliyarsa, kawai iya wancan hannun da ake ɗago daga cikin jama,a tamkar shamuwa tana ɗaga fiffike shi kaɗai muke gani"

  Ɗayar ta ce


"Ni hannun ma kamar wanda ya ji uwar wuya, duk kawai kamar dai ana rauda hannun ne ba wai ana ɗagoshi ba"

 
  Ɗayar ta ce

"Ni fa yadda ta ce ya saka shadda irin tata kawai zatona zan hango haɗaɗɗan hannu ake hango shadda a jikin hannun, amma wannan babu abin da ake gani na shaddar fa, kawai sangalalin hannun ne ake gani tamkar wanda singileti ce sanye a jikin mai ɗago hannnun babu kaya" Ran Hadiza ne ya ɓaci da tsiyar da suke mata ta fara tunanin ko dai sun ɗauka ma ƙarya take bai ɗinka musu tare da ganin hakan ya sa a zuciye ta ce


"Wallahi duk cikin ku kun san na fi ƙarfin in muku ƙarya, idan har ba shi ya saya mana ba babu dalilin da zan sa in ce shi ya saya, kuma har shi ya siyo ya ɗinka, amma tun da har kuka musa bari na kira shi ya fito gefe guda daga cikin ayar mutanen, ku hango shi" Ta faɗa tana doka masa waya.

  Malam Nura da ya kusa tsallake rijiya da baya wato gani yake an kusa wuce saitin gidan su Hadiza ya huta da wannan jarabar ta ɗaga hannu, ya san dai idan an je an ɗaura aure in ta ganshi kowacce jaraba za ta yi sai dai ta yi tun da an ɗaura. Amma me yana cikin wannan halin wayarsa ta fara neman ɗauki, saboda tsoron abin da zia biyo baya ƙin ɗagawa ya yi da ya ga sunan Hadiza hannunsa ne kawai yake karkarwa domin hatta hularsa da ya cire yakw riƙe da ita a ɗaya hannun neman suɓucewa take amma har lokacin bai daina ɗaga hannun ba.

  Hudu ne ya kalle shi ya ce

"Dan Allah ka daina ɗaga hannun nan, kamar wani mai ɗaga tutar nigeri,a"

 
Malam Nura ya ce

"Wallahi wanda yake ɗaga tutar ma ya fini ƴanci nidai wanna aure na Hadiza ya wahalar da ni" Hudu ko tausaya masa bai yi ba ya shiga masa dariya don shi kaɗai ya san waye abokinsa da irin tsiyar da ya shuka, ya san yanzu kawai abin da ya shuka ne bai ma fara girba ba.

 
 Ran Hadiza ne ya ɓaci ganin ɗaga daga cikin ƙawayen nata ta yi tsaki ta ce


"Ƙaryar banza" Tana faɗar hakan ta tafi, ɗagar ta tsaya tana mata dariya, Hadiza tana kallon aminiyar tata ta ce

"Kema Bintu baki yarda da ni ba?" Bintu tana dariya ta ce.


"Ina fa zan yarda sai na ganshi ido da ido, wannan mazan na yanzu masu shegen son kuɗin tsiya har zai tsaya kashe miki kuɗi a kayan fitar biki ke da shi da ƴaƴan da ba ma nashi ba, bayan kuɗin da kika ce ya baki" Ƙwafa Hadiza ta yi ta bar wajen cike da haushin Malam Nura da bai ɗauki waya ba, tana saƙawa a ranta cewar zai zo ya same ta.

   Sai da ya ga sun gota wajen yadda ba za a iya gane shi ba tun da sun ɗan yi nisa ya ɗago yana sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ce

."Haba ina dalili gabaɗaya wuyana ya ƙage a sunkuyon nan, hannuna ma da nake ɗagawa haka" Ya faɗa yana mayar da hularsa ya ɗora a kansa ya danna ta sai kuwa ya zama kamar wani maroƙi!.

 
  A haka suka ƙarasa wajen da aka tanada don ɗaura auren, Malam Nura yana ta sauke ajiyar zuciya, ana ta kaɗe-kaɗe har dai aka saurara aka yi abin da aka taru dominsa, wato aka ƙulla aure tsakanin Hadiza da Malam Nura!. Maroƙa suna ta cewa
...."Aure ya ɗauru, Allah bada zaman lafiya"

 
 Malam Nura ya ce


"Hudu babu pure water a nan wajen ne?" Ya faɗa yana waige-waige.

 Hudu ya ce


"Mai za ka yi da pure water?"

 
Malam ya ce


"A ƙasa zan zuba in tsotse, wallahi ƙirjina tun da na fito daga gida kamar ana bubbuga kalangu, har sai yanzu da auren nan ya ɗauru duk da har yanzu ina jin tamkar mafarki ne" Tsaki Hudu ya yi ya shiga gaisawa da jama,ar da suke musu Allah sanya alkairi, bakin Malam Nura har kunne yana ta washe bakin murna.

  Ana ta raba alewa da goro, sai hotuna ake ɗauka tsakanin abokan ango da ango, Malam Nura duk lokacin da aka ƙyalla hoton sai yake tuno haɗuwarsa da Hadiza maganar hoton nan amma idan ya tuna cewa an ɗaura auren sai ya ji da dama-dama wai kibiya a ido!.

 
    Wani saurayi da yake maƙotan su Hadiza wanda ya ji Hadiza tana faɗawa mai hoton da ta kirawo cewar zai musu hoto na kata,i, wanda zai ɗauki hankali a wanko musu na bango za ta liƙa a ɗaki, shi ma angon hakan, har rana cewa ita da shi tamkar an biyun sarari suke kayan nasu iri ɗaya ne, ana ta fasa mata kai, ganin Malam Nura da wani shegen yadi wanda yake tsohon yayi ne an jima da gama yayinsa, ga wata uwar hula da ya kifa sai wani uban maiƙon mai yake ga wani gumi yana kwaranyo masa, da sauri ya saita wayarsa ya ƙyalla hoto guda biyu, wato ya ɗauki Malam Nura gabaɗaya biyun kuwa yana dariya haƙoran nan a waje tamkar an bashi kyautar kujerar makka, duk da shi a wajensa Hadiza babbar kyauta ce .


  Yana gama hoton ya saka wayar a aljihunsa ya hau mashin ɗinsa ya bar wajen taron ya nufi gidan su Hadiza. Yana zuwa ya faka mashin ɗina a waje har neman tuntuɓe yake saboda tsabar gulma.

  
    Yana shiga da ƙaran guɗar mata kunnuwansa suka fara cin karo, ana ta murnar an ɗaura aure. Kiran Hadiza ya yi gefe tana ta washe baki tana wani farfari  da iyayi tana zuwa ya ce


"Wai Hadiza ba Malam Nura ne kika aura ba, mijin Haule da Kuluwa?" Harara ta dalla masa ta ɓata rai ta ce

"Ba na son gulma da rainin wayo, ni ina ruwana da matansa da zan ɓatawa kaina lokacin wajen sanin sunansa, na san dai Malam Nura sunansa, kuma mijin Hadiza don ni yanzu kaina kawai na sani, ba ruwana da kowacce shegiya ta yi ta kanta su shiryawa zuwana gidan!"


Yana mata hararar wasa ya ce


"Bakya cin ribar zance, ni fa kawai so nake na tabbatar don ni dai na ga shi ake ta tayawa murna a wajen ɗaurin auren, kuma na san shi kika ce za ki aura"


Tana zare ido ta ce.

",To uban mai kake son sani, eyeh masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, ku fa ko kashi mutum yake idan ya ganku ya tashi" 


  Ganin tana neman ja masa lokaci ya ciro wayarsa daga aljihu ya kamo hoton Malam Nura ya miƙa mata wayar, tana karɓa ta sauke idanunta a kan Malam Nura da ya hangame baki yana dariya, hular nan tasa da ta masa wani iri tamkar tashi da ƙwawa ta mayar da shi kamar wani tsoho, yadin jikinsa ta kalla gaba ɗaya a ɗaya hoton ma mazan da aka ɗauke su tare ne suka cinye hoton shi yadda idanunta suka nuna mata ma duk a firgice yake, can ta sauke idanunta a inda ya tattare hannunsa lokacin da zai ɗaga mata hannu, kasancewar a firgice take da ya gyara hannun ma bai gama gyaruwa ba ya bar shi a hakan, shi kuma Hudu bai lura ba bare ya sanar da shi.


  Wani uban ashar ta ɗura ta ce

"Sallamanu kuma an ɗaura auren? Ka tabbatar an ɗaura mana auren da shi????"



     *A page 10 zan gama free pages, wanda yake so zai iya saya mu ƙarasa har ƙarshe, wanda bashi da ra,ayi babu dole kar ma ki zo ki min ƙananun maganganu ba ɗauka zan yi ba a toh*


      MAMAN AFRAH
       ***