UWAR AGOLA

Chapter 9

by @mamanafrah3028

*UWAR AGOLA*

                
                 NA
 
     MAMAN AFRAH
 
    *Daga marubuciyar* 
 *Ruwa cikin cokali, ci ma zaune, malamin bogi, ƙazamin miji, Bonono ƴar zaman wanka, ruɓaɓɓiyar igiya ƴan adaidaita sahu, ƙara,in inna delu, jalli joga, Beelal, ungozoma da sauransu.*
   ***


             🅿️9️⃣


   Tun da Malam  Nura ya fara bayanin facin wando Ibra yake ta dariya, har ya gama faɗa masa amma bai tsagaita dariyar ba sai da abin ya ishi Malam Nura ya kalli Ibra cike da takaici ya ce

"Dalla Malam ba kyauta za ka yi ba kuɗinka zan cake na baka" Dariyar ta tsagaita ya ce

"Zan yi maka mana ai ka san ni da kai bata ɓaci, kawai dai lamarin ne ya bani dariya, yanzu duk kuɗinka abin ka sake ɗinka sabuwa ka zauna kana ta wannan lissafin, ka yarda mace ta maka aika-aika har burinta yake neman cika" Malam ya ce

 "Burin Kuluwa in tozarta ni kuma ba zan tozarta ba kuma sai na yi bikin nan yadda ba ta so, kai dai ka yi ƙoƙarin fito mini da shaddar nan kawai" Amsa masa ya yi ya ajiye aikin da yake ya shiga yi masa nasan kamar yadda ya buƙata. Malam yana zaune a gefe aka yanki ƙasan rigarsa aka yi ƙasan wandon aka yanke ƙasan wandon yadin aka jona na shaddar. Bakin Malam Nura har kunne ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu yana kallon Ibra cike da girmamawa ya ce

"Ba gashi ba, ai wallahi da na san za a iya yin wannan dabarar da ko wajen ɗaurin auren ba zan je a haka ba" Ya faɗa yana karɓar wandon ya kara a jikinsa ganin ya masa yadda yake so ya biya Ibra kuɗin gyara har da ƙari. Ibra yana ta tsokanarsa ya ɗauki ledarsa ya nufi gida, lokacin gar an fara kiran sallar la,asar, Hadiza kuwa ya kira ta ya fi sau goma amma bata ɗauka ba, da ya gaji sai ya ƙyale ta. Babu abin da ya saka a cikinsa wuni guda, haka ya wuni a shagon ana masa gyaran sai da ya ga ya kammala sallah ce kawai take fito da shi daga shagon, ko da suka haɗu da Hudu a masallaci ma ya sanar da shi cewa yana can ana masa ƴan dabaru dariya ya masa saboda ya san kawai wandon nan ba zai saku ba.

  Lokacin da ya shigo gidan, matan nan duk sun watse sai kaɗan, bai ga Kuluwa ba, shi ma bai nemi inda take ba saboda daman ba nemanta yake ba, a cewarsa tauraruwa mai wutsiyaci ganin ta ma ba alkairi ba ne. Ɗakinsa ya nufa ya rufo ƙofar cike da hanzari ya cire kayan jikinsa ya saka wandon ya ɗora rigar ya kalli jikinsa ya fashe da dariya a fili ya furta

"Hadiza daman rashin wando ne ya mini cikas yanzu za ki tabbatar da cewa wanka iya wanka Malam Nura ya iya" Ya faɗa yana sake kallon wandon tabbas ba a ganin saman yadin da aka haɗa daga sama, sannan waje da aka yi ɗinke-ɗinken ma ba a gani sai dai wanda ya yi kallon ƙurilla. Kayan ya cire ya linke, ya ɗakko wani kayansa ya saka don bai mayar da yadin Hudun ba saboda haushin yadin ma yake ji.


  Ya gama kenan, Haule ta zo ta buga ƙofar ya ce

"Waye?" 

Ta ce

"Ni ce fa ango na amarya Hadiza" Wani daɗi ne ya baibaye shi jin kiran da ta masa, duk da yana jin haushin yadda Hadiza ta masa a gaban mutane amma kuma da yake bahaushe ya ce, so hana ganin laifi, sai ya fara ganin laifinsa ne ba laifin Hadizar ba.

  Yana washe baki ya buɗe ƙofar yana faɗin

".Na baki ɗan mutum da uwarsa" Dariya ta saki tana faɗin

"Ai ka cancanta ne ango, Allah dai ya sa an ɗaura a sa,a ya bada zaman lafiya" Da amin ya amsa har ya yi shiru ya ce

"Haule anya kina sona?"

,Haule ta ce

"Mai ya kawo wannan maganar?" ,

Malam ya ce

"To ai ke ɗin ce sai kike ta nuna kamar dai bakya kishina, amma ko kaɗan ne ai kya ɗan gwada min kishi" A fili ta ce


"Ai ka san ka so abin da mutum yake so ma yana cikin so"


  A zuciyarta ta ce
 
'Ku maza mace ma ta yi kishin ku ta haɗa kanta da wahala, yanzu ba ga Kuluwa nan daga yin kishi kake neman nakasta ta ba, haka kawai ai gwara ma mace kar ta ɗora namiji a ranta hakan zai sa ta zauna lafiya'

  Malam ya ɗan yi shiru ya ce

"Kuma fa haka ne"


 Haule ta ce

"Yawwa, daman na ce ko a kawo maka abinci na ga baka zauna ba ma bare ka saka wani abu a cikin ka, ni kuma duk na damu" Dariya ya yi ya ce a zuciyarsa

'Namiji ɗan gatan mata, wato dai kai idan matarka ɗaya ce shikenan ba kowacce mace ce take bada kulawa ba, amma idan sun haura ɗaya sai abin da ka gani kowacce sonka take' ,A fili ya ce


"Barni Haule ai no yau ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, babu batun cin abinci har sai na je na yi hoto da Hadiza kin san ranta ne ya ɓaci da bamu yi hoto tare ba da ta ganni da wannan yadin" Haule ta ce

"Ba dole ya ɓaci ba wataƙila ta shiryawa ranar ne"

 Malam ya ce

"Shiri ma ai in kin ji ɗaya kenan, in banda wannan Kuluwar ƴar wahala ta kawo mini cikas har akwai wanda zai kaini wanka" Shiru ta yi bata ce masa komai ba, saboda ba ɗabi,arta ba ne yi da kishiya a bayan idanunta.

  Sallama ta masa ta ce sai ya fito. Tana fita ya fito ya ga wani bokiti cike da ruwa, lokacin tsakar gidan ma babu kowa sai su Alawiyya suna cin abinci. Yana ɗaukan bokitin ya yo hanyar banɗaki, ya shiga ya rufo, Kuluwa tana kallonsa kuma ruwanta ne amma sanin akwai wata wutae tsakaninsu ya sa bata fito ba, domin ita hankalin ta kwance an yi ɗaurin aure ya je da tsohon kaya, kuma yanzu ma don zai je ya yi wanaka ta san sai dai ya saka wasu kayan aron.


  Yana shiga ya yi wanka ya fito, ya shiga ɗakinsa ya saka sakata, yana goge jikinsa ya saka singlet, ya ɗakko rigar shaddar nan ransa fari ƙal ya saka ta ya saka wandon da ya zo ɗauree mazugin sai ya ga ƙarami ne Ibra ya saka masa, ɗazu ma da ya gwada saboda a ruɗe yake shi ya sa bai lura ba, wata zuciyar tana faɗa masa ya cire ya saka wani wata tana faɗa masa kawai kar ya ɓatawa kansa lokaci ya bari.

  Maɓallin ya ɓalle ya ɗakko hularsa ya gyara karin ya goga mata turare ya saka, ya sanya turare a kayansa sosai ƙamshi ya cika ɗakin ya saka takalmansa ya je gaban madubi, ba ƙaramin kyau ya yi ba sosai ya yaba yana fatan Hadiza ta yaba fiye da shi a fili ya ce


"Ashe dai ina da fasahar da zan saka shaddar nan a ranar nan amma na zauna na je ɗaurin aure da tsohon kaya" Ya faɗa yana ɗaukan wani tsumma ya sake goge takalmin sa.  Ƙaramar ledar da magungunan mazan sa suke ciki ya ɗakko, wanda Hudu ya faɗa masa sai ranar da amarya za tare zai sha, sannan ya ce masa a huɗu zai raba maganin, wata ƙaramar kwalba ce kamar ta magani, a jikinta an sake laulaye ta da leda a cikin ledar kuma wata ƙwayar magani ce guda ɗaya, ita ƙwayar Hudu ya ce masa a biyu zai raba, ita kuma na kwalbar a huɗu. Yana ɗaga kwalbar bayan ya buɗe sai da ya sha ya fi rabi, wanda ya bari bai fi kwata ba, ya ɗauki ƙwayar da aka ce ya raba a biyu ya saka a baki ya tsotse ita ma ya tsotse ta duka, ya mayar da komai cikin ledar ya ɓoye.
 
  A fili ya ce


"Ba a bori da sanyin jiki, ai tun da dai amarya yau za ta tare ina na ga ta zama, ai gwara na shanye duka, shi ma na kwalbar da na rage saura da daddare kafin a kawo ta zan shanye tasss, don ba zan zauna ta raina ni ba gwara ta san babu raini a lamarin"


   Ƙofar ya buɗe ya fito yana cikin kullewa Haule ya fito daga ɗaki, wata uwar guɗa ta carara tana faɗin


"Kai ma sha Allah, kyau iya kyau ango, wanka iya wanka, na Hadiza jan gwarzo, na Hadiza mai kyan mamaki" Ɗari biyar ya ciro ya miƙa mata ya ce

"Ki ba su Alawiyya hamsin-hamsin ki riƙe canjin" Karɓa ta yi tana masa godiya, sannan ta ce

"Malam idan an yi sallar magriba zan je gida, baba zan dubo bai ji daɗi ba duk da dai an ce jikinsa da sauƙi amma dai zan dubo shi"

 Malam ya ce

"Subhanallahi, a ki je kya masa sannu kafin in samu in ɓulla" Amsa masa ta yi ya yi gaba abin sa. 
  
Kuluwa wacce take ɗakinta jin guɗar da Haule ta yi ya sa gabanta faɗuwa, musamman kirarin da Haulen ta masa ya ƙonawa Kuluwa rai, amma haka ta taso domin ganewa idonta tun da dai bahaushe ya ce baba bori da sanyin jiki, tana leƙowa daga window abin da ya gani ne ya ɗaga mata hankali sa sauri ta dafe ƙirji tana zaro idanunta don su tabbayar mata da abin da ta gani zahiri ne ko kuwa gizo ne. Tabbas shaddar da ya ƙona wandon ta ce sanye a jikin Malam, kuma wandon ne take gani sannan shaddar sak ce a wandon daga gani ba haɗawa aka yi ba wato ba wata kalar shaddar ce aka samu wacce zanen ba ɗaya ba ne.

 
  Ranta ne ya ɓaci sai dai bata da damar amayar da abin da yake cikin ta, tun da ta san yanzu ma da sauran rina a kaba tun da ba yafe mata ya yi ba. 


Malam kuwa fita ya yi hannunsa ɗaya a aljuhu ɗaya yana riƙe da wayarsa da take ta ƙara. Yana fita Kuluwa ta fito tana huci kamar zakanya wani uban ƙamshin turare ne ta jo ya ziyarci hancin ta,  ko ma ta ce ya buɗaɗe tsakar gidan, tsayawa ta yi ta kama ƙugu tana wani karkaɗa kai ta taɓe baki ta ce


"Oh ni Kuluwa duniya sabuwa Malam Nura sanye da sabuwar shadda mai tsada yana ƙamshi tamkar an yi ɓarin turare" Haule ta yi dariya ta ce

"Wallahi kuwa wai wajen amarya Hadiza zai je su yi hoto... Tun bata ƙarasa ba Kuluwa ta tari numfashin ta da faɗin


"Ke kam Haule Allah yaye miki, yanzu a gabanki mijinki ya fita ya tafi wajen wata banza, amma har kike wasa shi kina ce masa wani na wata can banza, bayan kin san a cikin gidan gani ga kuma ke, ai ko da me -da me biyu ta fi ɗaya ko a rabon gado!" Haule ta tsura mata ido ta ce
..."To ina ruwana ita ma ta yi ta kanta, kuma ai na ga matarsa ce, to ya ma kike so na yi cakumarsa kike so in yi mu yi dambe saboda zai je wajen matarsa, to wallahi ni ko wajen bazawara zai je ba zan wahalar da kaina ba"


Kuluwa ta ce


"Ke dai na lura wannan ɗan kuɗin da yake baki ne suke rufe miki ido sho ya sa bakya samun damar nuna kishin naki"

Haule ta yi wata ƴar bazawarar dariya ta ce


"Ai ko da me da me kurna ta fi magarya zaƙi, inaso ki sani ba wai ba na son Malam ba ne kuma ba wai ba na kishin sa ba ne, a,a kaina dai na shafawa lafiya game da lamarin maza, sannan abu na gaa kin san da neman kuɗi nake kaina da ƙafata ina sana,a to kuɗin na  nasho da bai taka kara ya karya ba maganin matsalata zai min? Kin ga kenan kawai dai a bar kaza a gashin ta, ke da kika ɗorawa kanki kishin da mai kika tsira, ba don Allah ya rufa asiri ba da yanzu ƙafafun ki biyu ba sa jikin ki" Tana faɗar haka ta juya ta bar wajen.

  Ran Kuluwa ya ɓaci jin Haule ta faɗa mata magana, tana yin ƙwafa ta ce

"Hummm ba Hadiza ba ko Hadizo ce ta zo ina nan ina jiranta, tun da dole a ci kasuwa da maƙiyi, kuma hangen dala ba shiga birni ne ba, in da Malam Nura ne kaska ne raɓi mai jini ki bar shi da gashi, ai mai kashe miciji sai ya yi niyya zai ɗauji sanda, a yi dai mu gani idan tusa tana hura wuta, mu dai mazaunai ne ko dan zama za a neme mu, mu zuba mu gani, matuƙar ta shigo gidan na  ƴar kallo za ta zama, don ni ce da ragamar mijina, an aure min miji maimakon ta koma gidan mijin ta shi ne aka ƙi cin biri aka ci dila" Duk wannan karin magaanar da take Haule tana jin ta bata taka mata ba.


 
 Malam Nura yana fita ya amsa kiran Hudu nan ya faɗa masa gasu nan zuwa, haka suka zo da wasu abokan nasa guda biyu suka ɗunguma zuwa gidan su Hadiza suna ta zuzuta irin kyan da ya yi.


    Malam Nura ya murmusa ya ce


"Ni fa daman na faɗa maka Hudu sai na daka shaddar nan, amma dai har yanzu ina kan bakana idan ka samu mai saye ya zo na fansar masa" Hudu ya yi ƙasa da tashi muryar kamar yadda Malam ya yi lokacin da zai faɗa masa ya ce

"Waye zai sayi wannan shaddar wando da ɗori ɗori" Shiru ya yi sai kuma ya ce


"Ai idan aka samu mai son banza tsaf zai saya yake maleji, tun da nima ai sauƙi zan masa tun da na san wandon haɗi-haɗi ne wato yadi da shadda, wa ya ga haɗin gambiza" Ya ƙarasa faɗa yana dariya.

   A ɓangaren Hadiza ita kaɗai ta san irin ɓacin ran da ta ƙunsa, ranta ya sosu game da abin da Malam Nura ya mata abin ya fi mata ciwo ma da ya kunyatata a gaban ƙawayen ta bayan ta gama shirga musu ƙarya. Ta san ko ƙaramar hauka za ta yi Malam Nura ba zai sake ta ba amma dai ta ƙudurta a ranta cewar ba za ta tare yau ba ko ana muzuru ana shaho,a ƙalla sai ta shafa satika ba ta tare a gidansa ba sai ta gama bashi wuju-wuju sai ya san ita ya tozarta.

 
    Haka ta wuni suƙuƙu ranta a ɓace, don Zainaba ma sai da ta ce mata


"Inna wai ya na ga angon bai saka sabon kaya ba, kika ce tare ya siyo mana shaddar, wallahi ko kaɗan bai yi kyau ba kamar dai ba ango ba, sauran abokan nasa duk sun fishi yin kyau, ai daman babana ya fishi iya gayu shi ya sa na ce ki koma amma kika ƙi" Harara ta zabgawa Zainaba kamar idanun ta za su faɗi, da sauri Zainabar ta bar wajen tana ƙunshe dariyar ta.


    Da yamma kasancewar ta yi gayyata hakan ya sa ta sake sabon ɗauri inda aka mata kwalliya da ɗaurin ɗankwali, haka suka fito ana ta gaisawa da muyane da suke Allah sanya alkairi. Kamar an ce ta waiwaya idanunta suka sauka a kan su Hudu da sukw tahowa, tabbas ta gane su Hudu domin Hudu bai sauya kayana jikinsa ba, sannan sauran abokan ma duk ta gane su tun da da su aka zo ɗazu, wato ta shaida kayan jikinsu duk da cewar daga ɗan nesa ne ta hango su. Na huɗun ne bata gane ba, mai kalar shaddar irin ta jikin ta, wani ɗan gayu ta gani amma da yake ta san Malam Nura bai zo ɗaurin aure da shadda ba ma, shi ya sa bata ma yi tunanin shi ba ne. Ranta ne ya ɓaci domin ta san abokansa ne ya aiko su zo su bata haƙuri a kan yana ya kiranta bata ɗauka, kuma ta san dai zancen gizo ba ya wuce na ƙoƙi, ma,ana duk a kan maganar tarewar ta ce yau, za a kafa mata ƙahon zuƙa, ita kuma ta saka a ranta daidai da zamanin su take, wato sai ta musu tatasss sannan ta faɗa musu ba za ta tare ba sai nan da sati biyu kuma sai idan ya cika sharuɗɗan da za ta gindaya masa, juyawa ma ta yi daga kallon nasu ta ci gaba da gaisawa da mutane don ma kar su ga fuska su yi zaton za su samu sassauci daga gare ta.



Malam Nura ganin an kusa zuwa wajen da sahibar tasa take sai wani bubbuɗawa yake shi ala dole yana son kashe ta da mamakin wankan da ya yi. Sai da suka zo dab da su Hadizar ya mayar da wayarsa aljihu ya sanya hannayensa duka biyu a aljihun rigar ya tsaya daga gefe irin tsayuwar nigogin nan yana son ya mata ba zata don ya san ranta a ɓace yake tun daga batun shaddar nan. Shi kuma yanzu so yake a daidaita ta tare a yau domin ya gama shiryawa yau a matsayin ranar tariyar ta, kuma ranar amarci. 

  Ko da suka zo su Hudu ne ya yi musu sallama, suka je gaban su Hadiza, shi kuma ta bashi baya don haka bata ganshi ba. Hudun yana mata magana amma ta kauda kai gefe sai su Bintu ne suka amsa sallamar, yana dariya ya ce

"Ni da ba ni na kai zomon ba rataya aka bani" Cike da masifa ta ce

"Malam Hudu to na ga dai aure ne an ɗaura, to yanzun mai zan muku da kuka zo kuka tsaya mini, baka ga ina tare da mutane ba? Idan ma batun jere kuka zo ku koma ku faɗawa Malam Nuran ni Hadiza gayu na ce tariya ba yau ba, sai nan da sati biyu zan tare!!!" Malam Nura da yake bayan ta tsaye bai san lokacin da ya gyara tsayuwar nigogin da ya yi ba, gabansa yana faɗuwa ya haɗiye wani yawu muƙut, ba komai ne ya sanya shi wannan fargabar ba sai tunawa da ya yi da cewar ya shanye maganinsa da zai fito wanda aka ce kuma sai ranar da amarya za ta tare zai sha, daɗin daɗawa ma maganin kaf cikin magungunan Hudu ya ce masa ya fi kowanne tsada ya fi kowanne aiki.

  Su Bintu da suke kusa da ita su biyu ɗaya tana   bata baki, da yake sauran matan da suke wajen ganin zuwan mazan sai suka ɗan basu waje, amma Bintu da yake tafiyarsu ɗaya daman kamar yadda hausawa suke cewa sai hali ya zo ɗaya ake abota, Bintu ta ce

"Ina bayan ki ƙawata, ai kina da ƴancin ki yi yadda kike so, auren zawarci ne fa ba wai na budurci ba, kin ga kenan ko wata biyu kika ɗauka ba sati biyu ba kin da fiye da wannan damar...

  Kafin wani ya sake furta komai Malam Nura ya yi taku ɗaya biyu sai gashi a gaban amarya, yana zuwa ya ja ya tsaya hannuwan nan biyu a aljihu yana kashe ta da wani murmushi, don ba zai tsaya a masa sakiyar da ba ruwa ba, yana kallon ruwa kwaɗo ya masa ƙafa gwara dai ya yi duk yadda zai yi ganin bai yi asarar wannan ranar ba, bai yi asarar kuɗin maganinsa da ya bankamawa cikinsa ɗazu ba.

  Tsayuwarsa ta dakatar da su Hadiza da maganar ka ce na ce idanu ta zaro baki sake ita kanta ganin irin kan da ya mata bata san bakin ta ya furta

"Angina malam Nura?" Kansa ne ya ji ya masa gingirim daman kuma ya san a rina wai an saci zanen mahaukaciya, ya san in har ta ga wankan nan nasa ƙarya take ta ce bai yi mata kyau ba, shi ya san wanka iya wanka.

 Yana murmushi ya ce

"Na,am amaryata Hadiza" Daɗi ne ya baibaye mata zuciya musamman da ya zo a wannan daidai gaɓar da wurin yake a cike, kowa dai zai ganshi ya san ba ƙarya ta yi ba.

  Tana kallonsa ta ce

"Wannan kyau haka" Ya gyara tsayuwa ya ce

"Ai daman na faɗa miki zan baki mamaki"

 Bakin ta har kunne ta ce

"Ai kuwa ka bani ina sonka Malam Nura" 

Allah ne kaɗai ya san daɗin da Malam Nura ya ji musamman da ya ga ta mayar masa lulluɓin da ta cire masa ɗazu a gaban ƙawayenta da abokansa, amma yanzu gashi ta sake rufa masa bargon mutunci.

  Da kanta ta matsa kusa da shi suka jeru, a take abokansa suke musu kirarin sun dace, ƙawayen nesa sukaa matso kusa ana ta sakin guda Malam Nura a zuciyarsa ya ce

'Ai Kuluwa ba ƙaramin cutata kika yi da kika ƙona wandon nan ba, Allah ma ya taimakaeni an mini dibara da yanzu kin jaza mini tsiya, to amarya tana ba za ta tare yau ba ai ɗan jijjiɓin bala,i kenan" 

  Hadiza ta fito da wayarta daga jaka ta shiga kiran mai hoto yana ɗauka Malam Nura ya ji tana faɗin

"Ka zo yanzu ango da abokansa sun ƙaraso za ka mana hoto" Malam Nura ya ciro hannayensa daga aljuhu ya shiga gyara hularsa, suka haɗa ido da Hudu da yake ta faman doka murmushi ganin sun samu karɓuwa.

  Daga ɗaya ɓangaren mai hoto ya ce

"Ba kin ce shikenan ba?"

 Kamar ta falla masa mari haka ta ji da ya yi wannan furucin ta ce

"Na faɗa maka ka zo yanzu" Da to ya amsa mata, nan ta kashe wayar tana aikawa Malam Nura kallon soyayya shi kuma gogan sai wani kashe mata ido yake ransa fari ƙal.

   Shi Malam Nura yanzu maganar hoto ce a gabansa, shi dai a musu hoton nan da amarya wanda za su kafe a ɗakunan su. Yanzu babu batun ya yi maganar tariya a nasa ganin tun da daman fushin rashin saka kaya mai kyau ne ya janyi cecw ku ce ɗin da ta ce ba za ta tare ba yanzu kuwa ai babu wanna batun.

   Mai hoto aka sauke a mashin nan ya shiga aikin sa babu ƙaƙɗautawa don su Hudu gefe suka koma suka zubawa sarautar Allah ido, mai hoto yana ta basu style ɗin yadda za su yi, yana ta walla musu hoto, ya musu ya fi kala goma sha biyar, nan suka nuna masa wanda za a musu na bango.

 Malam Nura sai ya tsinkayi muryar amarya tana faɗin a kirawo  Zainaba da Shafi,i nan fa aka kira su, amma Zainaba dakyar ta zo tana ta kumbure-kumbure don ta tsani Malam Nura babanta take tayawa kishi, shi ma Malam Nura a nasa ɓangaren haka ne, burinsa kawai ya ɗauke Hadizarsa a bar waɗannan ƴaƴan musamman ma Zainaba. Ko da aka jeru za a musu hoton da yaran kowa yana ta washe baki amma Zainaba ta cukule fuska ban da harara da take aika musu babu abin da take, sai za a ɗauki hoton ango da amarya suna kallon juna cike da soyayya shi kuma Shafi,i shi ma dariyarsa yake amma Zainaba sai ta shiga banka musu harara kamar idanunta za su faɗo!. 

  A hakan ne cike da rashin sa,a Malam Nura ya ji tazugen wandon jikinsa ya cire daga cikin wandon. A take ya ji tsantsar wandon ta masa yawa, daman ya san ya yi kaɗan tazugen dakyar ma ya ɗauru saboda ƙanƙantarsa, shi kuma garin sauri bai tsaya ya canza wani ba, idanu ya ɗan zaro a ɓoye yana ɗan yatsina fuska kamar mai jin kashi a zuciyarsa ya ce

"Innahu min sulaimana wa innahu bismillahir rahmanir rahima, li,ilafi ƙuraish, ilafihim rihlatash shita,i wassaif fal,ya,abudu rabba hazal bait allazi aɗ, amahum min ju,in wa aamanahum min kauf" Ya faɗa wani gumi yana karyo masa. Da sauri ya saka hannunsa a cikin aljihun rigarsa, ya riƙe saitin ƙugun nasa ta yadda wandon ba zai zame ya faɗi ba, tun da yanzu babu inda yake a riƙe sai hannunsa da ya riƙe shi.

  A zuciyarsa ya ce

'Allah ka taimakeni kar wandon nan ya faɗi, kar ya tsinkani a idon jama,a, ya Allah yadda aka taru ake kallonmu ni da amaryata muna birge mutane Allah kar ka saka wandon nan ya rusa farincikin nanu, Allah kar ka ba wandon nan ikon ya kunyatani, yadda kowa yake kallona kamar wata ɗan daren goma sha uku ka sa abun nan ya ɗore' Ya faɗa yana sake bada ƙaimi wajen damƙe tsantsar wandon.

  Mai hoto cike da bada umarni ya ce

 ",Amarya kama hannun angon" Amarya tana murmushi ta miƙa hannu ta riƙo hannun Malam Nura da yake cikin aljihu yana riƙe da wandon, ta riƙe tana faɗin

"Cire hannun mana ya ka saka shi a aljihu?" Malam Nura idanu ya shiga rabawa a zuciyarsa yana faɗin

'Shikenan asirina a tonu, ya zan yi idan wandon nan ya zame Hadiza ta ga haɗe yake da tsohon wandona na yadi aka yi faci' A fili ya ce

"Ai na fi ganin kyauna idan hannuna yana cikin aljihu" Ya faɗa cike da ganin vata kunyata shi ba. Bata kawo komai a ranta ba ta riƙe hannun ana ta musu hoto shi kuma ya riƙe wajen gagam, don Hudu yana lura da shi ya ga hatta wajen da ya riƙe ƙafar wandon har tattarewa ta yi, shi kaɗai yake dariya a ransa duk da bai san mene ne ba amma banya raba ɗayan biyu matsala ce domin ya lura gabaɗaya abokin nasa ya fita hayyacinsa ba kamar lokacin da ake hoton ba duk ba a nutse yake ba.


  Dabara ce ta faɗo masa yana cikin tunanin yadda zai yi ne wayarsa ta shiga ƙara, ya fito da ita ko gama ganin waye bai yi ba ya raɗawa amarya cewar Goggo Ramma ce take kiransa, haka ya ɗan ja gefe yana wayar ƙarya, da ta faki ido sai ya sha wata ƴar kwanar lungu, a kan wani dogon tsumma ya yi wa idanunsa masauki, da sauri bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ɗauka ya ɗage rigar ya zare mazugin cikin, ya gyara wandon ya saka tsumman da ya tsinta ya ɗaurew wandon daga sama wato daga ƙugunsa wandon ya tsaya ya saki rigar yana sakin wani gauron numfashi. Fitowa ya yi daga lungun ya dawo yana ta jin daɗin ya tsira da mutuncinsa, amma dai alla-alla yake ya bar wajen tun kafin a yi abin da zai kunyata.


 Haka dai aka sha hoto sai wajen ƙarfe shida saura ango za su tafi, abokan sun ɗan yi gaba sun tsaya shi zai yi sallama da amarya, yana tsaye yana washe baki ya ce

"To mu za mu tafi"

Amarya ta ce
"Tohm kuɗin karin nawa fa" Yawun bakinsa ne ya ƙafe ya ce

"Wane kuɗin kari kuma, ke da za ki kwana a gidana ai akwai su Haule a gida sai abin sa ranki yake so za a girka da safe" Ranta ne ya ɓaci ta ce

"Ai na faɗa maka ba yau zan tare ba ko?" Idanu Malam Nura ya zaro a zuciyarsa ya ce

 'Ashe kuwa wanda ya mutu zai falko, duk wannan wankan da na yi don kin raina mini hankali, to ai kuwa ba zai taɓa yiwuwa ba mai kaza ya tashi da fifike' A fili kuma ya ce

"Amma dai wasa kike ko Hadiza?"

Farrrr ta yi da ido sai da bakin idon ya ɓace ɓat sai farin sannan ta dawo da idanunta daidai ya ce

"Wai wasa an faɗa maka a komai ake wasa ne, wallahi da gaske ba zan rare yau ba, kaima da wata magana yanzu fa batun ƙarfe shida na yamma ake yi ko jere ba a je an yi ba, kuma a yaushe zan tare?"

  Malam Nura ya kalle ta ya ce

"To mene ne abin wahala a wani jere, yanzu wasu ƴanmatan ma sai da isha,i ake tafiya da kayan a jera ai ba wahala ba ne gado ne fa kawai za a ajiye yanzu da gabaɗaya ma jeren maza ne suke yi"

Hadiza ta ce

"To bari ka ji ni wallahi kayana suna wajen kafinta da na saya daman sai za a jera za a ɗauke su daga can a wuce gidanka da su, ka ga a yanzu kuwa lokaci ya ƙure"

Malam ya ce

"Ni yanzu daga nan sai na je wajen kafinta a ɗoro kayan a baro wallahi ina iya jerasu duka ke kuma in aka yi isha,i sai a kai ki"

 Baki ta taɓe ta ɓata rai ta ce

"Kamar wata amaryar kunkuru, to wallahi ba zai yiwu ba so kake ake gulmata ana faɗin ango ne ya mini jere, yadda kowace mace ake zuwa a jera mata kaya haka za a mini, kuma in tafi a tsanake, duk ka hana kanka sakat kamar dai baka da mata a gida, ni wanna auren jin sa nake kamar auren farko don haka a tsanake zan tafi"

 Malam ya tari numfashin ta da faɗin

"To ko amaryar buzuzu ce ba dole a yi ɗokin ta ba, kuma da kike batun matana ai na san da zaman su, ke fa na ce miki wata guda za ki yi kina amarci, babu wacce za ta karɓi bakin kwananki" Fuska ta yatsina ta ce

"Wllahi ko shekara za ka bani ba zan tare yau ba!" Su Hudu ne suka matso ganin abin yana neman wuce makaɗi da rawa, Bintu ma suka matso na  aka shiga basu baki, a ƙarshe dai an shawo kan amarya ta ce za ta tare amma sai gobe, nan su Hudu suka shiga lallashin Malam a kan ya haƙura yau da goben ai duk ɗaya ne!. Ba dan ransa ya so ba sai don ba yadda zai yi haka ya haƙura, cikin ransa tsanar Kuluwa ce fal don ya san ita ta haddasa komai, da tun farko ya zo da shaddar a jikinsa daga wajen ɗaurin aure da tuni an jera kayan amarya ta tare a yau, amma da yake ta yi fushi tun da aka ɗaura auren shi ya sa ko shirin tarewa yau bata yi ba.




Haka ya bata 5k don ta ce yau kuɗin ba iya na kari zai bata ba har da na abincin dare!.

 Ko da suka taho a hanya suna ta zolayarsa amma shi kaɗai ya san halin da yake ciki, banza ya musu kawai so yake ya samu abin da zai yi wa Kuluwa sanadiyyar daren amarcin da ta masa yau!.

    A can gida kuwa da magriba Haule ta fito da shirin fita tana faɗaw Kuluwa za ta je gidansu duba babanta, har tana cewa Kuluwar ko ita ma za ta je su fita tare. Buɗae bakin Kuluwa ta ce

"Ni in fita yanzu haba Haule ai ban ga ta zama ba an saci ɗan ɓarawo, in ban da ma ke ina za ki samu damar fita ana jimawa fa ƴan kawo amarya za su yi wa gidan nan kutse" Baki ta taɓe ta ce

"To wa ya aikeni bare ya ga na daɗe, ai dubiyar dai ta fiye mini, amarya kuma da ba a kaina za a ɗora ta ba ina ni ina su, kafin dai su kawo ta zan dawo don ba zama zan yi ba, kar a zo a ce kishi ne ya sa na ƙi zama a gidan basu san ni auren Malam Nura ko a gefen takalmina ba"

 Kuluwa ta ce
"Ai ni ina nan na kasa na tsare, na je na yi wa baban naki sannu idan ƙura ta lafa don yanzu ba zan iya nisa da gidan nan a mini sakiya  da ba ruwa" Da mamaki Haule take kallon ta ta ce

"Ban gane ba, wace ƙura kuma sai ka ce wanda guguwa ta taso, wai ke Kuluwa ba za ki sauƙaƙawa kanki kishin wanda bai damu da ke ba, yanzu ban da Allah ya takaita da ba tuni ya lahanta ki va" Baki ta taɓe ta ce

"Na ga alama idan ina biya ki hawan ruwa sai ya kama ni, ai ni da wuya ta karni ai gwara daɗi ya karni, ai abin alfahri ne ma a ce miji ya nakastaka a kan kishin sa soyayya kenan, kuma ni ina nan ko sama da ƙasa za ta haɗe yau kwanane idan amarya ta isa ta yi kwanan turaka yau Allah tsine mini don wallahi ko a ni ko a ita domin sai ta jira na famshe gabaɗaya kwanankin da Malam ya haramta mini shiga turaka, sannan zan bata dama ta yi kwana ukun da kowacce bazawara take yi" Baki sake Haule take kallon Kuluwa tana mamakin ƙarfin hali irin nata, ta san yau ko gawa za ta yi Malam ba zai bari ta kwana a turaka ba!. In ban da ma rashin zuciya mutumin da ya haramta mata shiga turaka kusan kwana shida yau, shi ne zai bari ta shigar masa turaka a ranar da yake jin sa zai ɓarji amarci da amaryar da ya gama yi wa tanadi a cewarsa. 

  Fatan samun sa,a ta yi wa Kuluwar ta ja su Kabiru suka tafi. Suna fita Kuluwa ta rufe nata ɗakin ta tafi gidan mai maganin mata magunguna ta lodo ta biya kuɗin ta dawo gida. Tana zuwa ta kai ruwa banɗaki ta salsala wankanta, ɗaki ta dawo ta shafa wani turare mai suna MU JONE turare ne na jan hankalin mai gida da ta siyo an faɗa mata yana da kyau kuma matukar miji ya shaƙi ƙamshin shikenan  sai yadda hali ya yi shiga motar mahaukaci!. Wando da riga ta saka domin mai maganin ta ce ta saka kaya na jan hankali,  dan haka wani wandon Malam Nura da yake ajiye a ɗakin ta ta ɗauka ta saka sannan ta saka rigarta tshirt kasancewar bata da wanduna.Magani mai suna maƙale mata ta ɗauka ta zuba a nono ta dama ta shanye ta shafa humra.

    Wani kwalli idonka idona shi ma duk yana cikin kayan da ta siyo ta ɗauka ta rambaɗa a idanunta. Kanta da yake a tsefe ta shiga tajewa.

  A can kuwa su Malam Nura masallacin magriba suka wuce, bayan an yi sallah ya musu sallama duk ransa babu daɗi domin har ya hango zai kwashi amarci amma gashi an samu akasin lissafi. Hudu cikinsa har ciwo ya yi wajen tsokanar Malam Nura yana faɗin

"Wai da gaske abokina duka ka shanye maganin nan kaɗan ka rage, gashi kuma mai maganin ya ce a ranar maganin yake barin amfani, to Allah ya sa ma kai ba gwauro ba ne, ga Haule nan ga kuma amarya Kuluwa sai wacce ka zaɓa" Ko amsa bai bashi ba saboda takaici.

  Shago ya wuce yana zuwa ya ce mai shagon ya bashi sufagilu guda huɗu, haka aka ɗakko masa ya bashi kuɗin ya saka a aljihu ya nufi gida.

  Kuluwa da ta gama shiryawa tsaf sai kuma ta ce

"Ni da zan je turaka yau, gashi na gama haɗa bom wato na sha kayan gyara, gwara dai in shiga banɗaki in tsugunna don na ji taushen da ta sha ya saka mini ciki" Ta faɗa tana ɗaukan buta ta shige banɗaki ta rufo, a ranta tana ta saƙa yadda idonka idona kwallin da ta saka zai ruɗi Malam, da MU JONE da sauran abubuwan da ta yi amfani zai sanya idan har ta je turaka amarya za ta ƙufula ta ce an wulaƙantata a ranar amarci, in ya so da safe a yi badaƙala a sake ta shikenan ƙurunƙus.

  Malam Nura a hanya suka haɗu da Haule da za ta je gidan nasu, take faɗa masa sai Kuluwa kaɗai a gidan ita ma ba yanzu za ta dawo. Da sanɗa ya shigo zaure  gidan, yana zuwa ya cire takalmansa ya shigo saɗaf-saɗaf motsin da ya ji a banɗaki ya tabbatar Kuluwa tana banɗaki bokiti ya ɗauka ya koma zaure da sauri.

  Yana zuwa zauren ya fito da gabaɗaya sufagilu yana buɗewa yna tatsewa a cikin bokitin wato can ƙasan bokitin amma daga cikin bokitin ba wai daga waje ba. Sai da ya gama tatsewa duka ya saka wani ƙaramin icce ya gyara shi ko ina.

  Kuluwa wacce fitowarta kenan daga banɗaki ta cika ruwa a buta za ta yi alwala, tana ƴar waƙarta. Alwala ta zauna a kan ɗan dutsi tana yi amma ta ba ƙofar gida baya. Da ta zo shafar kai ta cire hularta ta ɗora a cinya daman kan a taje yake bata ɗaure ba. Malam Nura ya taso da sanɗa yana zuwa ya kifa mata bokitin nan a kanta, a take kan ya shige cikin bokitin, ya saka hannu biyu ya danna saman kan ta cikin bokitin a take sufagilu da bokiti suka ce sun ga wurin zama a kan Kuluwa, domin babu ɓata lokacin gashin nan ya yi nutso a  sufagilu.

 Kuluwa da bata ankara ba ta ji wani abu kamar roba a kanta, kafin ta ankara ta ga ya rufe mata har fuskarta, tana shirin yin magana ta ji an buga abun, abu na farko da ya fara zuwa ranta shi ne aljannu, don ta san dai gidan babu kowa, kuma daman wataran Haule tana cewa idan ta fito fitsari cikin dare tana ganin kamar gilmawar mutum, amma saboda ƙi faɗi irin na Kuluwa da ƙaryata mutum sai tw ce ita bata taɓa gani ba don haka ba za ta yar da ba. Baki yana rawa ta ce

"Subhanallahi waye, mene ne haka, mai na yi muku? Ni ce fa Hauwa Kulu, da aka fi sani da Kuluwa don girman Allah ku yi haƙuri" Ta faɗa jikin ta yana karkarwa idan akwai abin da take tsoro shi ne aljannu. Shiru ta ji hakan ya sa ta saka hannu biyu domin ta cire abun ta cece ranta tun da bata gani bokitin ya rufe mata ido, am a tana ja ta ji gabaɗaya a manne yake da gashin ta, gabanta ne ya faɗi ta tabbatar da wannan aikin aljani ne. A take ta shiga lalume kwaraf ta buge butar alwalar ta, butar ta tuntsura ruwan ya zube, kasancewar wajen alwala ne duk a jiƙe yake kuma har ya yi laka a wajen irin tsantsin nan da ƙasa take idan ruwa yana jiƙa wuri. Da hannu biyu ta dafa ƙasa ta miƙe tana ta salatin da bata iya ƙarasawa take dawowa farko, a zuciyarta tana jin daman ta raka Haule dubiyar babanta. Malam Nura ransa fari rass cike da mugunta yana tuno irin ɗiban albarka da ta yi wa wandon sa ya kai wani ɗan icce ya ɗan soka mata a jikin hannunta, a take Kuluwa ta tabbatar da cewa ta faɗa hannun aljannu domin zaton ta farcen aljani ne aka caka mata a hannun.

  Salati take yi kafin ta ƙarasa sai ta kamo hailala, bata gama hailalar take kamo a,uziyya, a haka ta samu nasarar miƙewa tsaye tana baza hannu kamar makauniya ƙafafun ta ta yi wa masauki a wajen santsin lakar nan, a take santsin ya kwashe ta suuuuuu ƙafarta da babu takalmi ta tafi, domin gabaɗaya ta sille takalman wani ya yo kudancin Nigeri,a wani arewacin Nigeri,a ya nufa. Ji ta yi kamar an yi sama da ita sai gata ta faɗi jirif, duk da ta ji faɗuwar amma yanzu ba wai ta faɗuwar take yi ba batun ceton rai ake daga hannun mutanen da su suke ganinmu ba mu muke ganinsu ba. Da sauri ta tashi ta muskuta ta shiga rarrafe domin ta san matuƙar ta sake tashi to faɗuwa za ta yi tun da ba gani take yi ba bare ta taka inda babu laka. 

  Wata zuciyar tana bata shawarar ta kama hanyar waje a nan ne za ta samu a rabata da abin da aljannu suka kifa mata ya manne mata a gashi, wata kuma tana faɗa mata ta koma ta shige ɗaki ta kulle duk da ta san aljannu har bango suna shiga. A zaton ta ko Haule ko ƴan kawo amarya sa kawo mata ɗauki. Tana sunkuye tana rarrafawa Malam Nura ya lallaɓa ya naɗe hannun rigarsa ya jimƙe ya sakar mata ƙulli a baya saboda bokitin iyakarsa wuya da kafaɗarta. Jin saukar ƙulli rididif har sau biyu ta ji dukan da bambanci da na mutane a take faɗuwar gabanta ta yawaita Malam kuma a zuciyarsa ya ce

',Yadda kika salwantar mini da daren amarcina da Hadiza, da yadda na yi asarar maganin da na ɗaɗɗaka yau, wallahi sai na baki wuju-wuju sai kin gwammace kiɗa da karatu, har da wani saka wandona ke kika san jarabar da kika taka, amma yau yadda zan tsurar da ke sai kin ji daman ƙafafun na guntule miki don har suma sai kin yi Kuluwa, za ki san ni kika yi wa rashin mutunci, kika barni ina yawo da wando kwambileshin (Combination)"  

  Muryarsa ya shaƙe ta zama kamar ta yara kamar ta tsoho ya ce

"Kuluwaaaaaa" Kuluwa da daman a tsorace take ga kuma bokitin da ya rufe mata kunne wani irin sauti ta ji da wata murya a take a tsure gudawar da take matsewa ta fara ƙoƙarin fitowa!!!.

    *Saura page 1 mu gama free pages daman na ce muku a 10 za mu gama masu son karantawa har ƙarshe za su biya 700 domin shiga group ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay shaidar biya ta ***, *mutanena na Niger ga* 
 *naku acc ɗin da za ku saka 88630104 nita ko* *amana* 
 *Issaka issoufou.* 

   MAMAN AFRAH
   ***