the witching hour
by @surayyahms
*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms
#Royal hate-love
#Forbidden bloodline
#Obsession
#royal politics
#Sisters love hate
Bismillah rahmanir raheem.
3: The witching hour.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tanamai sake shanye tsanananin damuwarta Kamar yanda ta Saba akan al'amarinsu da ahalin zamkora dankuwa hada alaqar aure da jinin zamkora a gareta babbar matsalace da zai sakokai tsakaninta da ababen bautarta muddin bata amince hakan ya yuwa ba.
Abun baqin cikin ma shine sanin cewa pure jinin ahalinta na wazeeris basu taɓa zama akan kujerar sarauta ba saidai su su daura sarki, amma sbd wnn kuskurentan ya jawo dolene ynxu sai taware wani bbn yanki guda dake karkashin ikon tharim vale domin sudora wann aure da jininsu dana ahalin zamkora.
qarasowa tayi ahankali cikin nutsuwa wadda zallar mulki da wayewarta tareda ajin datake dashine yasa komai nata yake cikin izza da nutsuwa.
ahnkli ta doso wani irin katafaren gida wanda gaba daya tsarin ginin sa is just like that of a huge royal kingdom sai dai daga ka matso kusa zakaga tsantsar tarin narkakken dukiya ce kawai take ambaliya aciki, gidan babba ne sosai wanda fadi da girmansa zai iya kaiwa rabin anguwa guda daga ciki an rabashi estate estate slightly nesa da mutane but surrounded by pure silence nd cold breeze of harmattan.
sanyin iskar hamadar dake ƙadawa aciki da wajen gidan na ɗauke ne da ƙamshin original turaren frankincense..
Ganuwar gidan nasu yanada matukar tsayi anshafeshi da launin white nd grey paint mai maiqo a ido da laushi tareda manyan steel golden colour gates na shigewa ciki.
akowani kusurwar ganuwar yanamai daukene da wani irin sassaƙaɓɓiyar rubutun Alƙur’ani da tsofaffin karin magana game da mulki da adalci.
babban golden gate na farko uwarjini ta dosa wanda tun daga tsarin wnn katoton golden gate zaka iya gane cewa gidan acike yake da tarihi, dukiya, da matsanancin tsaro.
yalwataccun trained security armed forces da parol uniform insu baqaqe sune suke kare gidan ta kowani fuska sai domestic staff da kala kalan unform dinsu kowa na aikin dake gabansa.
wasu irin tsayayyun huge buildings ne guda biyu irin grand Imperial design din nan Inspired by Greek nd Roman architecture.
...kowane babban sashe na gidan yana da personal gate dinsa amma dake dare yafara yi sosai iyaka ma'aikatan gidan da suke musu tamkar bayi da kuma masinjoji ne a kowane kusurwa kowa da kalar aikin daya duqufa yanayi dukka nin su kalar kayansu ne kawai yake iya bambamcesu
jin iskar gidan ya dauke cak yayi nauyi Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana raɓewa gefe tareda sunkuyarda kai qasa sbd sautin tahowar uwarjini Wanda sautin sarqa dake qafarta shine ya sanar musu isowarta tun daganesa atake lokacin kowa ya zuɓe kasa cikin nuna biyayya da girmamwa
personal servants dinta ne kaÉ—ai suka nufota babban cikinsu tasaka hannu ta amshi fitilar suka hau binta abaya dashi..
tana qarasowa hanyar dazai shigarda ita bangarenta ta tsaya cak batareda tace komi ba tajuyo ahnkali tadan kalli gefenta ganin yar uwarta na jini kuma amintacciyar jakadiyarta nana Atiqa tayi saurin matsowa kusa dan su shige cikitare, tareda juyawa takalli personal servants din dake take musu baya kusan su hudu wani mugun kallo tayi musu suka ja baya ahankali suka tsaya agefe tareda sunkuyarda kai.
idanu ta zuba wa uwarjini amma bata fahimce komi ko ta gano alamar nasara gameda amsar data je neman musu a wajen ruhi ba face tashin hankali da tsananin fargaba datafara hangowa..
Boyayyar ajiyar zuciya uwarjini tasauke ahankali batare da sun cewa juna komi ba ta shiga qofar sashenta da akajima da bude mata jakadiya nana Atiqa nan tabita abaya aka rufo musu qofar.
hall ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon ottaman royal chairs dark green nd golden sai qyalli suke sai komai daya qawata palon yazamto shima green and golden sanyi yakama palon takoina sbd wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a hall din.
Babu kowa awajen sbd hall din farkone dazai sadaka da main huge falon uwarjini harzuwa turakarta
sunakaiwa falo na biyu tatsaya cak tareda sake sakin wata iriyar sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na biyu jin zuciyarta na harbawa da ƙarfi, batareda tajuyo ba murya a karye kuma a hankli tace
Atiqa!! saqonnin da ruhi me tsarki ya bani ya matuqar girgixa zuciyata sbd saqone daya zamto na baqin ciki da qasqantarwa
ayau inda ace wani masinja ko bawa ne na aika yaje yakawo min iwannan mummunan saqon da babu tantama ko shakku a bakacin rayuwarsane shiyasa tun farko na zabi naje jejin na ji komi dakaina.
Ajiyar zuciya mai masifar nauyi nana Atiqa ta sauke tareda kallon uwarjini cikin zaquwa da taushin murya tace..
Allah yakara miki tsawon rai uwarjini yakuma sanyaya ranki koma minene nasan kin sha gabansa..kece ginshiƙin wannan gida na mulki, kece jarumar da kikagina mana duk wani darajar da ahalin Wazeeris ke tinkaho dashi, kece hasken da yake jagorantar Tharim Vale… babu wani abu da zai zo na qaddara ya girgiza ki bare har ya rusa ki.
tanakaiwa nan ta ƙara matsowa kusa da ita cikin nutsuwa, tanamai rage sautin muryarta kasa kasa kamar mai tsoron kada kalamanta nagaba su fito ba dede ba a zuciyar uwarjini…
“…ranki shi dade meya faru...
wani irin shiru ne ya mamaye wajen na ɗan lokaci sautin sauƙar numfashin uwarjini ne kaɗai ke fita a hankali tareda nauyi tanaji kmr zuciyarta na ɗaure da wani abu mai girma fiye da yadda kalmomi zasu iya fassarawa.
ahankali uwarjini ta lumshe idanuwanta…
wani irin baqin ciki da tsnananin zafi atake suka gauraya a jikinta lokaci guda… sannan ta buɗe idanunta a hankali tamkakken fuskarta namai bayyana wani irin ƙarfin iko da kuma ɓoyayyen rauni da take ƙoƙarin ɓoyewa.
“Atiqa…”.... ta kira sunanta a hankali. shiru dakin ya kara dauka kafin nan tace"
“…wannan ba irin musibar da muka saba fuskanta bane…
dede nan ta juyo a hankali idanunta suka sauka akan na nana Atiqa…
“ruhi mai tsarki ya bayyana min cewa babban ɗana khaleefa zai mutu snn kafin ahali na bazasu warke daga wnn cutar sai na hada wata yarjejeniya na hada alaqar aure..
tana furta hakan taɗan tsaya, zuciyarta na bugawa da ƙarfi har ana iya jinsa.
“…ƙaddara ce da aka riga aka rubuta…wadda idan na ƙi amincewa da ita to ba ni kaɗai ba… gaba ɗaya zuriyar Wazeeris ce zata shiga cikin wani duhu da ba mu taɓa gani ba…
atake numfashin nana Atiqa ya tsaya cak na ɗan wani lokaci ruwan idanunta suka cika da firgici amma ta danne shi da ƙarfin hali kai tsaye tace "wani irin qaddara ce haka da sai har ta bukaci alaqar jini?….
murmushin da babu farin ciki a cikinsa uwarjini tay kafin nan
ta ɗan matso kusa da ita sannan ta furta mta kalmar da ta karya duk wani ƙarfin zuciyarta a cikin falon…
…jinin da muka rantse ba zai taɓa haɗuwa da namu ba…”
nana atiqa tay shiru mai nauyi mai cike da tashin hankali…sai can ta ja numfashi ahankali
tace“kina nufin ahalin…
suna hade ido kuma sai taji ta kasa ƙarasa maganar…
nan take uwarjini ta juya mata baya a hankali tanamai ɗaga kanta sama muryanta kasa kasa tace“eh…jinin da muka haramta
…jinin da na la’anta shine yau qaddararsu ya haɗu da nawa…
zuciyar nana Atiqa kmr zai fashe da zafi tafaɗi ƙasa bisa gwiwarta tareda riqe saman kirjinta domin a karo na farko kenan cikin shekaru masu yawa taga tsantsar fushi da bacin rai a cikin idanuwan uwarjini saidai kafin ta dawo hayyacinta ta furta wani abu taji magana na fitowa ahnkli...
dan uwar ko ranta a ɓace ne bata daga murya, bata son yin tsawa bata kuma iya nuna fushi da damuwa a fili yawanci saidai ta shanyesu. cikin muryan ta dake fita kasa kasa take cewa
"bazan taɓa aminta ƴaya na da suka zauna acikina sukasha nonona su hada jini da ahalin bayi na zamkora ba. Ruhi me tsarki ya saka sharadinsa, nima Dole nasaka sharadu na. babu wanda ya isa yasakamin wani tsari ko doka snn inbishi..
...na amince babban dana khaleefa zai mutu amma kannensa imran da zafar da ummu salma sune zasu cigaba da shugabntar wannan ahali bazan gurbata jinina dana bayi ba. na riga na yanke hukunci, jikana Abdallah dan khaleefa shine zan daura abisa kujerar mulkin dala (kano), inyaso babban dansa shamsan da zai zamo yarima a karkashin mulkinsa shine zamu zaɓa a matsayin wnda zaikawo mana karshen wannan jarabawa.
da wani irin ƙarfin izza da babu jayayya a cikinsa take maganan cikin ikon da ya wuce na jinin mulki kaɗai dan power ne da ya haɗu da jini me qarfi da kuma wani abu mai zurfi fiye da fahimtar me fahimta dan itadin matsafiyace na karshe.
ahankali ta juyo gaba ɗaya tanakan fuskntar nana Atiqa…
ruwan idanunta duk sun sauya dan ba tsoro bane a cikinsu yanzu iko ne tsantsa.
ita ce uwarjinin zuriar nan dan haka ba a rubuta qaddararta a cikin waɗanda ake nakasasu da igiyar dokoki da tsoro…
dede nan ta ɗaga kanta kaɗan, sarƙar dake ƙafarta ta yi ƙara mai sanyi…
ta matsa gaba kaɗan, hannunta ya ɗan taɓa wata kujera mai adon zinare tadafashi da sanyin ikon data san tanadashi ahnkli ta ɗan lumshe ido snn ta buɗe su da cikakken ƙarfi…
“…ni nake saka iyaka… ni nake karya duk wata ƙaddara idan har ta kuskura ta wuce gona da iri…
Nana A ta tsaya tana kallonta na É—an lokaci zuciyarta cike da tsoro da kuma girmamawa mai zurfi.
ahankali ta sunkuyar da kanta ƙasa cikin nitsuwa tace “hakika… wannan itace uwarjini da na sani..tana fadin haka taɗaga kai sama kaɗan, ruwan idanunta sun cika da tsayayyen imani. tace “ba wanda ya isa ya ketare tunaninki, kuma ba wanda zai tilasta ki, amma uwarjini… dolenen mu ne fa mu yi taka-tsantsan,saboda wannan alaƙar… idan aka barta ta ɓaci zata iya zamowa babban ƙofa ga maƙiya
uwarjini ta É—an kalle ta da gefen ido ba tare da ta katse ta ba.
Atiqa ta ci gaba da cewa" yara maza goma kika shafesu acikin tarihin zuriarsu dan haka laanannen ahalin nan na Zamkora ba za su taɓa mantawa dake arayuwarsu ba, saidai yau idan suka ji an ƙirasu akan batun hada alaqar aure…to za su so su juya wnnan al’amari ya zamo mana tamkr gadar zare, dan haka dole ne mu juya wnan alaƙar ta zama wani abu daban
ahnkli uwarjini ta ɗan karkatar da kai tace… "Nasani...amma zan saka musu tarko da tsaruka wanda ba za su iya fita daga ciki ba…zamu maida rayuwarsu ta zama tamkr bacci acikin wutar jahannama amma ahankali..kin fara fahimtata Atiqa…?
wan irin shuumamnn murmushi nana atiqar tay snn ta juya gaba kaɗa cikin kyabe baki tace "....Allah ya taimakeki..nan bada jimawa ba zasu fahimta cewa ba acin yaƙi da ƙarfi wani lokacin ana cin sa ne da jinkiri da kuma tsari har sai abokin gaba ya fahimci cewa ya riga ya shiga cikin tarkon da ba zai taɓa iya fita ba..
Murmushi uwarjini tay cikin nitsuwa wanda zallar iko da mulki da ke ratsa jinin jikinta yasaka komi nata yake cikin izza da kamiya
saidai kafin ta budi baki sukaji karar tahowar mutum da sauri wani irin shiru wajen ya dauƙa ayayin da daya daga cikin personal servant na uwarjinin ta tsaya daga bakin kofa jikinta na rawa rawa ta rusuna.
uwarjini batace uffan ba dan atake jikinta ya bata wani abu...
fuskar nana atiqa a murtuke tana bin maid din da harara tace "ke kuma Laure menene haka zaki fado mana gatsau...
kanta na qasa muryanta na rawa sosai tace "Ku gafarce ni ranki shi dade...jikin me girma khaleefa ne ya tashi ana buqatar uwar jini a shashensa da gaggawa.
wani irin cold silence ne ya gauraye cikin falon basuce mata uffan ba kuma basuyi motsi ba harta gaji da rusunawarta ta miqe da sauri ta fita ta basu waje..
nan nana atiqa ta daga ido takalle uwarjini suka hade idonsu waje guda da sanyin murya tace.."kina bukatar naje tare da ke ne???
jin uwar jini bata amsata ba da tausayi tace "mutuwar É—a na da zafi, gashi shine mana mutum na farko a zuria da xai mutu da karancin shekaru
cikin katseta da hannu ahnkli uwarjini tace ba mutuwar wuri zaiy ba atiqa, kasheshi ruhi zaiyi da sunan daukar mataki wajen wanke zunubai na..wani rauni kawai ake so acusa min. amma bazai taɓa yuwa ba. cikin hadiye qulluton baqin ciki dake cinta arai tace "nabaki umarni atiqa...kije ki tsaya acan a shashensa ynxu, dan idan naje dakaina zan iya harzuka indauki mummunan mataki akn maqiya na cikin daren nan na shafesu
..idan khaleefa yamutu yau ke kadai nakeso kizo nan ki gayamin...
hawaye ya cike idon Nana atiqa da sanyin murya da na jiki tace"
Angama..uwar jini.. daga nan ta juya da sauri sauri ta fita a sashen tare da barin uwarjini dake tsaye cikin jin tsananin baqin ciki da radadin rasa babban danta da zatayi...
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
AREWABOOKS
@SURAYYAHMS
WATTAPAD @SURAYYAHMS
WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025