HADIN KADDARA

Chapter 8

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                    By 

        AyshaNalado



Page 8


“Yawwa to bari ina zuwa na ba su saƙo.” Hajiya Turai ta faɗa tana miƙewa zuciyarta cike da mamakin Ammar, saboda  yadda ya yi saurin amsawa babu wani jan aji ko ƙorafin da ya saba, gashi ta lura tun ɗazu sai bin ƴan matan   da kallo ya ke yi kamar zai haɗiye su da ido, murmushin manya ta yi zuciyarta cike da zargin wani abu, tasan dai banza ba ta kai zomo kasuwa, ta fi kowa sanin Ammar da ƙyuyar masifa, ko yanzu ma ta faɗa ne kawai don ta ji bakinsa, ba don ta saka rai da  amincewarsa ba. Shigewar Hajiya ya bashi damar samun waje ya zauna a kujerar da ke kallon nasu, ya zuba musu shanyayyun idanunsa masu kyau da kwarjini. Duk sun taƙura musamman Aysha da ba ta cika son kallo ba, dauke kai ta yi daga gefen shi, amma duk da haka tana jin idanunshi na yawo a jikinta. Salmah ya shiga ja da hira yana mata tambayoyi akan karatu da mutanen gida, tana bashi amsa. Sosai haushin  Salmah ya cika ta jin yadda ta sake tana bashi labarin gidansu, har da wanda ba a tambaye ta ba, abinka da mai bakin tsiya. Shi kuma  bini bini ya sako ta cikin hirar tasu, basar da shi ta dinga yi tana amsawa a takaice, wani kuma ta share ta yi kamar ba ta ji ba. Gajiya ya yi ya ce "Salmah hala Sistar ki bata magana?" Kallon ta Salmah ta yi ta ce "Tana yi, amma ba sosai ba, kuma ba a ko ina ba." Gyada kai yayi tare da ce wa "Very good." Yarinyar ta  birge shi jan class ɗin ta ya ƙayatar da shi uwa uba kyaulwunta ya matukar fusgar shi, cikin son ta kula shi ya ce "Ki saki jiki dani fa Aysha ni yayan ki ne, nasan baki waye ni sosai ba kamar Salmah, amma abinda yayi Anas shi yayi ni ki dauka cewa ni Anas ne." Rasa yadda za ta yi da wannan nataccen mutumin ta yi, kafin ta tattaro amsar da zata bashi, Hajiya Turai ta dawo falon hakan ko ba ƙaramin dadi ya mata ba, karasowa Hajiya ta yi tana ce wa "Ayya daughters ku yi hakuri na barku jira, wlh kunnen nawa ne da shegen mantuwa, manta indai na ajiye abin na yi." Ta ƙarkare maganar tana miƙawa Salmah wani leda mai dan girma mai dauke da rubutun Arabic da tambarin wani kamfani da ke nuni da cewar ta kasashen larabawa ce. Bayan Salmah ta amsa, sai taci gaba da ce wa "ƴan kayan kwalliya ce ta mata nace bari na baku kwa ƙara." A tare suka shiga godiya, magana Ammar ne ya katse su,  "Hajiya ai da kinbar shi, yanzu in mun fita sai na biya dasu na siya musu." "Nawa dabam, naka dabam ko yanzu ma bata baci ba ƙari ai yafi ƙara." Murmushin ya yi ya ce "To shikenan yau zan fanshi abokina." "Ai kuwa dai da ka kyauta, Salmah, Aisha ku tashi ku je yamma na yi nagode Allah ya muku albarka ku gaishe ta da kyau." Kusan a tare suka miƙe Ammar yayi waje suka rufa mishi baya har gurin motarsa, suna zuwa Aysha ta yi saurin buɗe baya ta shige, don karma tsautsayi zama a gefen shi ya kama ta, don kwarai ta takura da mayen kallon shi. Fuskar shi ta gwada rashin jin dadin hakan, amma ba yadda ya iya, Salmah kam bata fahimci abinda ke faruwa  ba ta buɗe gidan gaba ta zauna shima ya shiga ya ja motar suka bar farfajiyar gidan.

Ko a hanya shiru ta yi ta maida hankalinta kan wayarta, ta na dai jiyo sautin hirar shi da Salmah sama sama , amma kai tsaye ba za ta iya cewa ga abin suke cewa ba, jin motar ta yi parking yasa ta dago da sauri,tasan dai a ƴar tafiyar nan da su ka yi bai ci ace sun iso gida ba, tasha mamakin ganin ya faka ne a farfajiyar babba katafaren sabon gurin cin abinci da makulashen nan dake tashe wanda babu kamarsa duk faɗin garin, *Dausayi food's & snack's* a ruɗe tace "Salmah me ya kawo mu nan?" Salmah ta ce "ki tambayi, Ya Ammar." Juyawa ta yi ta banƙawa keyarsa harara, caraf idanunshi ya haɗu ta mirror, murmushi ya sakar mata da sauri ta dauke kanta, ya ce "Oh sorry Aysha ban gaya miki ba, na ɗan biyo daku ta nan ne, ku sai abin kwalama." Cike da jin haushinsa  tace "Bama jin yunwa kuma a gida ance karmu daɗe Ammi za ta yi mana faɗa idan muka koma." Ƙarara muryarta ya nuna ɓacin ranta, duk shiru su ka yi kafin Ammar ya sauke numfashi ya ce "karki damu ni da kaina zan kai ku har gaban Ammi na kuma gaya mata nine na daɗar daku." Share shi ta yi dan har ga Allah ranta bai ya so, kuma ga wani tsitsinkewa da take ji zuciyar ta na yi haka kawai, gabanta ya shiga faɗuwa. Buɗe motar ya yi ya fita Salmah ma ta fita, ita kam gyara zamanta ta yi ta haɗe kanta da kujera tana ambaton sunan Allah saboda bakon yanayin da ya risketa nan take, ganin shiru shiru bata fito ba yasa Salmah dan leƙawa ta window ta ce "Sister fito mana." Ba tare da ta dago ba ta ce "ku shiga kawai, zan jira a nan." Muryar ta kadai ya shaidawa Salmah cewa ba wasa take yi ba, jiki a sanyaye Salmah ta kalli Ammar ta ce "Yaya Ammar wai mu shiga kawai." Shi karan kanshi jikin shi ya fara sanyi da lamarin yarinyar da alamar dai ko zai samu kanta sai ya sha baƙar wuya,amma ba komai zai jure, don ba zai wasa ya rasa wannan zukekiyar ba. ba dan yaso ba suka barta a mota suka shiga ciki shida Salmah.

Jin sun tafi yasa ta dago ta maka wa bayan shi harara tare jan tsuki, ta riga ta gama fahimtar takun shi tsaf, ,so yake ya samu fuskarta ta yadda zai iya gaya mata wani shirmen bazan shi, ta sha haɗuwa da maza kala kala da suka nuna muradansu a kanta, ta riga ta lashi takobin cewa har ta mutu baza ta taɓa ba wani ɗa namiji dama ya shiga zuciyarta ba, ta riga ta yi na farko, kuma na karshe, indai soyayya ce wannan alkawari ne.

Tana cikin wannan saƙe saƙen wata jar mota mai matsakaicin tsada amma sabuwa ce dal tayi parking a kusa da motar Ammar, bata san mai yasa ba amma haka kawai ta tsinci kanta da son ganin su wanene a cikin motar, ƙurawa motar idanu ta yi ba tare da ita ma tasan dalilin yin hakan ba amma koma mai tayi umarnin zuciyarta ne, anfi minti goma kafin a buɗe murfin motar, sai da aka kuma kwashe minti biyu , kafin da sauri taga wani mutum dogo ya fito daga motar, fuskar shi sanye da facemask idanunshi toshe da bakin gilashi kanshi sanye da face cap, ya jawo cap ɗin kasa sosai ya kare fuskar shi, hannun shi kuma rike da dan ƙaramin jaka mai zubin akwati, da wani irin sauri ya fito daga motar yana waige waige kamar mara gaskiya  kafin ya yi wuf ya shige cikin wurin kamar  walkiya  cikin takun shi na majiya karfi. 

Dam dam dam zuciyarta ya ci gaba da bugawa da sauri, haka kurum ta ji bata yarda da mutumin nan ba domin ta tabbatar bugun zuciyarta yana da nasaba da shi, ya yi kama da mugun, duk alamun rashin gaskiya sun bayyana a tare da shi,  ‘ko dai irin masu dasa bom ne a cikin al'umma don su hallaka muminai waɗan da ba su ji ba ba su gani ba? Zuciyarta ya yi mata wannan tambayar cikin firgici, zumbur ta dago kai tana zare ido, tabbas zai iya kasancewa musamman yadda taga yana ta kaffa kaffa da akwatin nan tasan ba abin arziki bane a ciki, kuma hakan ba wani abu bane a wannan karni da suke ciki na yanayin rashin tsaro, ko sati ba a rufa ba da irin hakan ya kasance a tsakiyar kasuwar tudu har yanzu cikin jimami da alhinin abin jama'a suke.

Innalillahi wainnailaihi rajiun! Ta shiga maimaitawa a bayyane, yanzu ya za ta y?, ba za ta iya tafiya tabar salmah a cikin wurin nan ba, dole ta shiga ta ceto rayuwarta koda hakan na nufin zasu rasa rayuwar su baki ɗaya ne, lokaci guda ta fice daga cikin hayyacinta, musamman  da zuciyarta  ta ci gaba da hasaso mata hoton mutumin har  ya riga ya dasa bom ɗin, da wani irin mahaukacin gudu ta balle murfin motar ta fito, waige waige ta shiga yi babu salmah babu alamar ta a farfajiyar wurin, da alama har zuwa yanzu basu fito daga ciki ba, da  gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin wurin, hankali a tashe kallo ɗaya zaka san bata cikin hayyacinta ita kadai tasan halin tashin hankali da take ciki, sai bangaje mutane take yi ba tare da ta tsaya ta saurare su ba, security dake bakin ƙofa ne suka rufa mata baya suna “Hee heee! Amma , ko su ɗin bata saurara ba taci gaba da kutsawa tana waige waige, wuri ne babba don gidan sama ne me hawa biyu yadda saman yake haka exactly ƙasan yake, kuma cike yake da mutane , tuni hankalin mutane ya fara dawowa kanta, take wasu daga cikin mutanen dake wajen suka shiga binta, don duk tunanin su sata tayi shi yasa security ke binta tana gudu, duk bata san su na yi ba, burinta bai wuce tayi tozali da salmah ta jata subar gurin , sai dai duk iya waige waige da duɓe duɓenta bata ga salmah a ƙasa ba,da alama suna sama kenan, da mugun gudu ta nufi saman, ganin haka yasa wasu daga cikin masu binta suka zagaya ta daya hanyar don yi mata zobe su ritsa ta.

Ya juya baya yana tafiyar shi cikin sassarfa sauri yake yabar gurin kafin mutane su ankara da shi so yake yayi ya gabatar da abin da ya kawo shi wajen, cikin gaggawa ya tafi domin yana da wani meeting da zai shiga immediately 6pm yanzu gashi 5:40 hawa stairs ɗin yake yi cikin sassarfa, yayin da ita kuma take bin bayan shi a guje ba tare da ta lura da cewa mutumin da dakewa gudu bane a gaban ta,don idanunta ya rufe bata ko ganin gabanta, burinta ta ja salmah su bar wajen kafin mai afkuwa ya afku. Ta iso daf dashi ba tare da ta san shi bane ta dai san a kwai mutum a gabanta wanda burinta idan ta cimmi shi bai kauce ba ta bangaje shi ta wuce kamar yadda take wa duk wanda ya tsaya mata a hanya , shi kuma jin alamar ana biye da shi da gudu, yasa ya dakata tare da juyowa a shirye don duk tunanin shi daya daga cikin masu harin rayuwar shi ne da basu rabi da bibiyarshi duk in da yasa ƙafa, dan sun sha  kawo mishi irin waɗan nan harirrukan duk da futa ce yayi ta sirri cikin ɓadda kama.

Ba ta san wanda ke gabanta ya tsaya har ya juyo ba sai da ta ji ta gwabza wani irin mugun karo dashi, wanda saida yayi saniyar cirewar glass ɗin idon shi da face cap ɗin kan shi a lokacin guda,ita kam taga taga tayi baya zata fadi da sauri yayi wurgi da box ɗin hannunshi ya taro ta da gaba ɗaya hannayenshi, yayi haka ne kuma ganin idan har ya bari ta faɗi a gurin zata raunata sosai, duk da baisan wacece ba hasalima bai san shi take ma gudu ba, dai dai kuma lokacin masu binta suka ƙaraso wajen ciki harda salmah da Ammar, duk cirko cirko mutane suka tsatstsaya ganin abin da ke faruwa, ita kam idanunta a rintse yake don ta sadakar ta fadi, jin an taro ta yasa ta shiga sauke ajiyar zuciya da sauri da sauri, sun kwashe kusan 1 minute a haka, bata gama dawowa cikin hayyacinta ba.

Tunda idanun shi suka sauka akan fuskarta ya kafe ta da su, bai san me yasa ya kasa dauke idanu daga fuskarta ba. Tuna abin da ke gabanta yasa ta zabura da sauri ta ware idanunta, fuskar data gani ne ya saka ta sauri zaro sauran dukkannin girman idanunta,  "baa ba ba ba Babagida.” Ta furta cikin rawar laɓɓa zuciyarta na tsintsinkewa.." .............



Please ku dinge react ta haka ne zan gane yadda kuka karɓi labarin na samu gwarin  gwiwar ci gaba da typing, tunda comment ya gagara.😏