11
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*11*
*TUSHE, MAFARI*.
Mafarin ya fara daga Abdullahi(AUDU BABA) bafillace haifaffan garin Mubi. ita kuma Mubi ƙaramar hukuma ce daga cikin Jahar Adamawa Yola. Garin Yola nan ne maƙyanƙyasan sa tun daga kakkannin shi dai bai san wani asalin tarihin iyayen shi ba sai da ya san su a haifaffun jahar Adamawa, wasu suna cikin yankunan dake zagaye da Adamawa kamar irin su girai, funfore, ganye da dai sauran su amma shi asalin iyayen iyayen shi a garin Mubi sukai rayuwa shima anan aka haife shi anan kuma ya yi rayuwarsa har zuwa auran shi na fari da bafillatan matarsa mai suna Asma'u.
A matsayin shi na bafillace tsantsan na gaba da baya, kamar wajibi ne ya auri bafillatana yar'uwansa sannan da yake ba karatun boko matan suke yi da wasu mazan ba to ana yi musu aure ne suna da ƙananun shekaru, in har ka ga namiji ya yi karatu to sai in har fita ya yi cirani daga nan sai ya faɗa harkan neman ilimi , shima hakan ne ta kasan ce da shi yana da ƙarancin shekaru ya yi auran shi na fari kafin ya sake yin wani auren na gani ina so.
Lokacin ya fara shiga jahohin Nigeria domin fatauci ya faɗa garin Daura na Jahar Katsina a can Allah ya haɗa shi Ummu Salma(Gwaggo) ita ɗin haifaffiyar baƙar bafillata ce yar nan garin Daura ce ta uwa da ta uba, tunda Audu Baba ya ƙyalla ido ya ga Ummu Salma ya ji duk duniya ba wacce yake so irin ta a lokacin itama shekarunta ba su wuce sha biyar ba yarinya ce ƙarama ya ɗauka zai sha wahala kafin ya same ta amma sai ga shi cikin lokaci ya samu abin da yake so, tun ballanta da Ummu Salman take son shi ta ga dogon bafillace jajir tas a tsaye jarumi kuma Sadauki tuni ta ce shi take so, su kuma iyayenta ganin duk tushe ɗaya ne sai suka aura ma Audu baƙo Ummu Salma ya tafi da ita can garin su Mubi.
A lokacin ƴa'ƴan shi da Asma'u huɗu Hamza, sai Umaru, Salihu da Sha'aibu. Zuwan Ummu Salma ya sanya suka haɗe kansu suna zaune lafiya Ummu Salma ta ɗan jima ba ta haihu ba sai da aka yi ta karɓa mata taimako wajen shekaru biyar da auran su sannan ta haifi babban ɗan ta namiji wanda Audu Baba ya yi ma huɗuba da Hadi bayan shi kuma ba ta sake haihuwa ba har sun cire rai ma gabaɗayan su sannan ta samu Fatima wanda tsakanin su da Hadi shekaru sha bakwai ne. A lokacin da aka kawo Ummu Salma wacce kowa ke kiran ta da Gwaggo akwai wata maƙociyarsu da aka yi ma Gwaggo uwar ɗaki da ita tun lokacin da aka kawo ta Daura wacce ake kira Nenne tsada saboda hasken fatan ta duk yankin a lokacin ba mai jan ta, shi ya sa ake kiran ta Nenne tsada ita ta zama kamar uwa ga Gwaggo tun kawo ta garin zuwa yanzu komai nata da na ƴa'yanta Nenne take shigewa gaba ita Nenne Allah bai ba ta ɗa Namiji ba duka ya'ƴanta mata ne sannan in ta haihu sai su yi wabi a cikin yara goma da ta haifa huɗu kawai suka tsaya mata, Balki ce babba sai Salamatu sai A'i, sannan autar ta Jamila wacce a lokacin yar shekaru goma ce to bayan Jamilan ma ta sake haihuwa sau uku suma suna yin wabi su kaɗai ne ta samu suka tsaya mata, tunda da daɗewa megidanta ya rasu ita kaɗai ce ke gwagwarmayan riƙe marayun ƴaƴan nata.
A lokacin Gwaggo tana cewa ta kama ma Hadin ta Jamila matsayin mata, tun ana ɗaukan maganar wasa har dai Gwaggo ta tabbatar da ita ba wasa take yi ba. Tun Jamila na ganin Hadi tana gudunsa har ta daina domin shi bai taɓa ɗaukan maganar Gwaggo da muhimmamci ba tun ballatana a lokacin shi ɗan gayu ne tunda yana makarantan boko, Jamila kuma karatun allo suke yi a lokacin sannan tana da wata Aminiya da suke tare tun suna yara mai suna Aisha. Gida uku ne ya raba tsakaninsu duk in da za su je tare ne sannan makarantan allo ɗaya suke zuwa iyayensu su san juna, ko kaya ne in za a yi ma Jamila sai an yi ma Aisha haka itama gidan su Aisha ba sa nuna cewa Jamila bare ce, Aminci ne mai karfi a tsakanin su tun suna yara har kuma girman su sai da Ubangiji ya saka aminta da yarda har a tsakanin ƴaƴan su.
Jamila na da shekara sha shidda a duniya bayan ta yi saukan Allo aka saka ta a lallen aure ita da Hadi. Shi a lokacin yana da shekaru ashirin da shidda ne, kuma yana gama sakandiri amma bai cigaba da karatu ba sai dai yana yin noma sannan yana kiwo. Auren gata aka yi musu auran da har bayan shekaru masu yawa suke zaune a ƙarƙashin kulawan iyayen su a garin Mubi suka fara gudanar da kyakyawan rayuwarsu a farkon auran su Hadi ba ya son Jamila amma da tafiya ta yi tafiya sai ya ji ya gode ma zaɓin Gwaggo har bayan ranta in ya tuna da abin alherin da ta yi ma rayuwarsa sai ya gode ma ta sannan ya yi mata addu'an samun haske a cikin kabarin ta.
A shekaran auran su Jamila ta haifi yaron ta na farko mai suna Jibril ana haihuwan shi Gwaggo ta ce an samu Jibo shikenan sunan ya bi shi har girman shi, Jibo ya taso tsakanin iyaye da kakanni ne shi ya sa Jamila(Ammah) ba ta sha wahalan renon shi ita kaɗai ba sunan da Hadi(Baffa) Ammah ce ta fara kiran shi da Baffa har ya kama bakin yaran gabaɗaya, bayan Jibo ta sake haihuwan Mustapha tana da cikin Mustapha suka saka Aminiyarta a lalle Aisha ta yi aure a garin Girai duk da ba ta son auren amma hakan nan aka kaita kuma ta zauna sai ya kasance ba a gari ɗaya suke aure da Jamila(Amma) ba.
Haka dai rayuwa ta cigaba da gudana cikin farinciki, Nenne ta fara rasuwa maciji ne ya sare ta a makewayi sai dai gawarta aka iske a kwance shike nan su Ammah sun zama marayu Allah ya sa ma dukkansu sun yi aure a cikin garin Mubi shi ya sa sai maraicin ya zo musu cikin gata Ammah ta fi kowa jin mutuwar Nenne amma samun Baffa kusa da ita ya sa ba ta daɗe ba ta warware uwa uba ga Gwaggo ga Baba ita yar gata ce gaba da baya ba sa barinta ta yi kukan rashin wani abu saboda soyayya da gata. Ga ƙanwar Baffa Fatima da kusan a tare suke rayuwa tun da ba wani tserayan shekaru ne a tsakanin su ba.
Ta haifi Mustapha ko shekara bai yi ba suka sake samun wani rashin na rasuwar Audu Baba shima lafiya lau ya kwanta da asuba rai ya yi halin shi tsakanin shi da Gwaggo kwana arba'in, da man tun rasuwar Baba ba ta da lafiya ashe itama ajali ne Baffa da Ammah sun fi kowa shiga cikin tashin hankali gaba da baya maraici ya sarƙe rayuwarsu yanzu ba su da mai kula da su, Ammah ta rasa mai duba ta, mai kula da ya'yanta da duka rayuwarta sun yi kuka kamar ba za su daina ba. Ga Fatima da take ƙarama a lokacin abin tausayi da Baffa ya so ya karɓi riƙon tilon ƙanwarsa amma sai dangin Gwaggo da suka taho daga Daura suka ce za su tafi da ita saboda ita mace ce sannan Baffa kuma ba kai girman da zai iya rike wani ba shima yana da iyalansa tunda Baba baya raye yana ji yana gani suka tafi da Fatima Daura ko gadon su na Baba da Gwaggo da aka raba su suka tafi da shi, shi kuma ganin ba Gwaggo ba Baba sai ya fara tunanin barin Mubi duk da akwai Umma(Asma'u) da sauran ƴan'uwansa maza amma duk da haka sai garin ya yi masa ƙunci Ammah ma duk ba ta cikin walwalarta tun ballantana da Fatima ta bar Mubi zuwa Daura rashin ta dameta sosai tana kuka tana cewa za ta iya riƙe Fatima me ya sa Baffa ya bari aka tafi da ita? Lallashinta ya yi ta yi saboda shima bashi da tacewa a lokacin a matsayin sa na ƙarami sannan su Hamma Hamza a lokacin ba su hana ba to shi ma bai isa ya ce komai ba.
Da kuɗin da aka raba musu gado Baffa ya fara bin matasa garin da sukan shiga cikin birnin Yola kasuwanci yana ɗan taba harkoki a can farko ya ɗan faɗa harkan siyar da siyarwa ne daga baya kuma ya fara haɗawa har da cinikiyar dabobbi irin su shanaye da raguna, duk abubuwan dai ba su tafi daidai ba sai ya faɗa harkan siyan tsoffin ƙarafan motoci ya fara daga ƙananun karafa ne sanadiyar wani abokin kasuwancin sa da suka haɗu a garin Yola shi ya ba shi tabbacin harkan ana samu sosai kawai sai ya faɗa kuma bai rufe shekara ba ya ga haske a cikin lamarin, yana daɗewa baya gida tunda ba iya Yola yake harkokinsa ba ko'ina har Lagos da ibadan suna haurawa neman ƙarafa sai dai in ya ga mai zuwa gida ya tura ma Ammah da su Umma saƙo wani lokacin sai ya yi wattani biyar ba ya gida amma duk da haka bai manta da tilon ƙanwarsa ba yana tura kuɗi can gida Mubi ya ce in an samu mai zuwa Daura akai ma Fatima sannan duk salla yana yi mata sutura tunda suna kawo ta salla ƙarama in kuma sallar layya ce Baffa da Amma ke zuwa can Dauran saboda dai kar Fatima ta yi maraicin rashin iyaye da ƴan'uwa.
Kuma Alhamdulillah Fatima ta samu iyayen riƙo na gari. Wanda ke riƙon ta ƴaya maza suke da Gwaggo Madibbo shi Allah bai ba shi haihuwa ba ne har sun fara tsufa shi da mai ɗakin sa, sannan yana aiki a gidan Sarkin Daura shi ke kula da bargan dawakai na cikin masarautan gabaɗaya. Fatima ba ta yi karatun boko ba amma tana yin karatun addini. Shekaran su Gwaggo uku da rasuwa Baffa da Ammah da yaran su biyu suka yi ƙaura daga mubi zuwa garin Yola acan Baffa ya kama musu haya suka fara zama saboda harkokinsa suna daɗewa a can shi ya sa ya ga gwara ya ɗauko ta, ta dawo kusa da shi amma in salla ne ko aka yi wani abu ba su manta da mafarin su ba suna zuwa Mubi tunda can ne gabaɗayan yan'uwan suke Ammah ma duka yan'uwanta suna Mubi ga Aminiyarta dake aure a Girai sai dai har lokacin ba ta haihu ba amma in dai Amma ta je Mubi ta kan karisa can Girai su zumunci da amincewar Baffa kamar yadda ya saba bata dukkan wata dama ba ya tauye mata haƙƙin ta na aure ta kowani bangare godiya take yi ma Allah da ba ta auri Baffa ba da ta zama mai asara a cikin mata.
Baffa da kansa ya je Daura ya taho da Fatima ya kawo ta Yola ta ga in da suke da zama ta yi kwanaki da su kafin ta koma kuma lokaci bayan lokaci tana zuwa duba su musamman Baffa zai tura mata kuɗin mota domin ta zo, yana ƙaunar ƙanwar shi, itama tana son yayan ta guda ɗaya da suka haɗa uwa saboda yana kula da ita sosai. Tana da shekaru sha bakwai kwatsam mariƙinta Madibbo ya aiko masa da cewa ya zo Daura yana son ganin shi akan Fatima ne ba ɓata lokaci ya shirya ya tafi yana zuwa sai ya ji labarin da ya girgiza shi wai Fatima ta samu miji, amma mijin ba kowa ba ne sai yaron Sarkin Daura. Sarkin Daura a lokacin Alhaji Muhammad Shitu Daura ne sarki na 49 a lokacin.
Kuma ɗa ne ga sarki Alhaji Bashar Daura sarki na 39 a wancan zamanin, Sarki Alhaji Muhammad Shitu yana da tarin ƴa'ƴa amma duka duka yaran shi maza guda biyu ne Babban ba shi da lafiya ana ta raɗen raɗen an haife shi da ɗan matsalan ƙwaƙwalwa, sai kuma na biyun Muhammad Nasiru(Hakimin Daura kuma Yarima mai jiran gado) domin tun a lokacin ana tunanin shi ne zai gaji sarauta daga mahaifinsa saboda zamowarsa tushen masauratan Daura. Mahaifiyarsa Hajiya Ruƙayya(Fulanin Daura) duk da fa a wancan lokacin ba ita ce uwargidan Maimartaba Alhaji Muhammad Shitu ba, Hajiya Rakiya Muhammad Shitu ce(Magiyar Yamman Daura) amma ita ce mafi soyuwa a gare shi tunda ita ce mahaifiyar Hakimin Daura sannan Yarima mai jiran gado.
Labarin ga shi dai mai daɗi ne amma kuma ba shi da daɗi a mahanga da yanayin tsarin rayuwarsu na talakawa, ina Fatima ina Yarima mai jiran gado! Ai haɗin ma bai yi ba akwai tazara mai yawa su da ba kowa ba, sai talakawan gari ina su ina haɗa kafaɗa da masu garin gabaɗaya nan da nan Baffa ya nuna bai amince ba shi bai ma yarda son Fatima yake yi ba domin bai ga ta in da suka haɗu ba, ballanta har rayuwarsu ta haɗu waje ɗaya. Amma mariƙinta ya dage da cewa Yariman Daura mutumi ne na gari mai taimakon talakawa, mai alheri ga matasa mai son talakawaa kuma mutanen garin Daura suna son shi kamar yadda ake son mahaifin shi.
Sai dai duk da haka Baffa bai amince ba duk sun faɗa masa a gidan Sarkin Yariman Daura ya ga Fatima lokacin da ta je kai ma Madobbi abinci kuma ya ji nan duniya ita yake so ya kuma je ya yi magana da mahaifinsa. Shi kuma Sarkin Daura a lokacin Marigayi Alhaji Muhammad shitu ya sa aka kira Maddibo mariƙin Fatima ya yi magana da shi a cewarsa da talaka da mai kuɗi da mai sarauta duk Allah ne ya yi su, sannan tunda dai Muhammad Nasiru ya ce yana son ta shi kuma ya yi alƙawarin samar masa da duk abin da yake so amma duk da haka Baffa bai amince ba haka ya dawo Yola cikin damuwa da Amma ta tambaye shi sai ya sanar da ita abin da ke faruwa itama ta ce gaskiya abin ma bai haɗu ba ta ina Fatima za ta kai kanta a matsayin auran ɗan sarkin? Sarkin gobe itama ta goya masa baya kan hukuncinsa saboda haka ma ya ce zai ɗauko Fatima ta dawo hannun shi ya saka ta a makaranta ta yi karatu nan gaba Allah zai kawo mata mijinta ta yi aurenta amma ba ya jin zai yi kasadan wasa da rayuwarta wajen kai ta in da ya fi karfin zuwan ire-iren su.
Ba ƙwace Fatima ya yi daga hannun mariƙanta Modibbo ba amma dai ya nuna zai karɓe ta riƙon ta ya dawo hannun shi tunda Allah ya rufa masa asiri shi kuma Madibbo sai ran shi ya ɓaci da ganin kamar Baffa ya raina masa ne sai ya tara yan'uwansu dangin Gwaggo ya faɗa musu halin da ake ciki nan aka ba ma Baffa rashin gaskiya suka kuma hana shi ɗaukan Fatima daga ƙarshe suka yanke shawaran tura wakilan Sarki can Mubi wajen su Baffa Hamza domin su yi mgana tunda suma suna da haƙƙi, Baffa ba da yawun shi aka aminta da auran Fatima da Yarinman Daura ba lamarin bai yi mishi ba tun ballanta da yaji auren a matsayin auren sirri ba wanda zai ji labarin auran daga Daura a cewar Maimartaba saboda mahaifiyar Muhammad Nasiru in ta ji labari ba za ta bari hakan ya faru ba, hankalin Baffa dai bai kwanta ba sai da ya je har garin Daura ya yi kyakyawan bincike akan Masarautar Daura ya samu kyakyawan shaida akan Maimartaba da Hakimin Daura amma sam bai samu shaida mai kyau kan Fulanin Daura ba, mace ce mai ji da kanta da sarauta, ita ɗin babanta ya yi sarki kakanta ma Sarki ne sannan mijinta ma Sarki ne kuma ɗan ta ma zai yi sarauta, shi ya sa ba ta ƙaumar talaka ko mara arziƙi tana harkokinta da masu asali ne da sarauta a labarin da ya ji ma tana nema ma ɗan ta auren ɗiyar wazirin Daura ne a lokacin.
Ba yadda Baffa bai yi da kar a yi auren ba amma ba wanda ya saurare shi, dangin Gwaggo suna ganin wata dama suka samu guda tak a kaf zuru'an su, suma su Baffa Hamza haka suke gani musamman shi da yake Babba mulki da kwaɗayi sun rufe masa idanuwa ganin irin dukiyar da Sarki yasa aka aiko wasu amintatttunsa da shi a matsayin Sadakin Fatima har da gwala-gwalai, Umma(Asma'u) a lokacin itama ta goyo bayan Baffa amma Baffa Hamza bai saurare ta ba, yana ji yana gani aka ɗaura ma Fatima aure da Hakimin Daura daddare domin sirrinta auren. Auren da aka ɗaura a garin Mubi sannan anan aka saka Fatima a lalle tana kuka tunda ko sau ɗaya bata taɓa sanin mijin ba, ta dai san Hakimin Daura a saman doki kansa da rawani idanuwansa kawai ta taɓa gani tunda suna zuwa kallon hawan salla lokacin shagulgulan salla a lokacin mace ba ta ikon cewa ba ta son wanda aka bata ko ba ta so dole za ta yi hakuri ta zauna kowa faɗa mata yake yi ta yi dace a dangin su kaf daga asalin tushen su ba wacce ta taɓa samu sa'ar da ta samu, Baffa ne kaɗai bai yi farinciki ba Ammah daga baya ta saduda ta riƙa lallashin Baffa da ya yi hakuri ya yi ma ƙanwarsa addu'an samun dacewa. Da za a tafi da Fatima Daura a wani kebantttacen gidan Maimartaba da ba wanda ya san da shi za a ajiye Fatima cikin sirri, Baffa ya yi magana da ƙanwarsa ya yi mata nasihan ta yi ma mijinta biyayya amma shi dai a ƙasan zuciyarsa yana ta jin tsoro, tsoron faruwan abin da yake gudu kuma daga ƙarshe sai da ya faru ɗin
Tun Baffa na tunanin nan da wata ɗaya zai ji wani abu game da Fatima har dai aka kwarari wattani bai ji komai ba sannan tana yi masa saƙo da cewa tana nan lafiya lau. Sai hankalin shi ya kwanta ya ɗan samu natsuwa bai sake jin ya natsu ya samu kwanciyar hankali ba sai da Fatima ta zo ganin su a Yola tare da wani dogari amintattacen Hakimin Daura ya kawo ta Fatima ta yi kyau ta yi kiba har da wayar nan ta zamani a hannunta Handset sannan ta tabbatar ma da su Amma da Baffa cewa mijinta na son ta Sarki ma na zuwa dubata amma dai ba ta zuwa ko'ina itama ba mai zuwa wajenta daga ita sai wata amintattaciyar Baiwa mai suna Zulai tare ma suka zo sai dogarai guda biyu masu gadin ta da direba, irin kayan alfarman da ta zo da su kawai ya isa ya ba su tabbacin abin da ta faɗa gaskiya ne sannan ta zo ma da Baffa da kuɗi da suturu shi da Ammah da yara ta ce daga Hakimin Daura. Baffa dai ba abin duniya ba ne a gaban shi, shi dai fatan shi da burin shi Fatima ta samu farincikin da zai dauwama. Bayan zuwan Fatima sun sake dawowa tare da Hakimin Daura mijinta sun zo yi musu sallama zai tafi wani cos na wattani biyar kasar waje kuma tare da Fatima zai tafi, Hakimin Daura har ƙasa ya duka ya gaishe da Baffa ya kuma ba shi tabbacin har iya numfashinsa na ƙarshe zai kare Fatima. A lokacin da suka bar kasar Fatima ta bar Ammah da cikin Kabiru ne itama acan ƙasar da suka je ta samu ciki kuma suna garin ba su dawo ba maganar auren Hakimin Daura ya tabbata da Ɗiyar Wazirin mai ci a lokacin dalilin haka ya sa Fulanin Daura ta tsara bikin da yana dawowa za a ɗaura aure a yi shagulgula.
Auren da ya zagaya duniya, amma Baffa bai damu ba tunda Fatima ta tabbatar masa tana lafiya babu abin da auren nan ya rage ta ko shafe ta. Ita tunda auren sirri ne yanzu ne duniya ta shaida Hakimin Daura ya yi aure suka kuma tare a wani katon bangare a cikin masarauta. Fatima ta zo taron sunan Kabiru da tsohon cikin ta in da suka haɗu da dangi daga Mubi, kowa ya ga Fatima sai ya rike baki ta yi wata kiba sannan duk in ta taka kunyanga na biye da ita riƙe da jakarta ta zama abar sha'awa a wajen dangi, tana ma Yolan ne ta samu labarin Maimartaba Sarki Muhammad Shitu ba lafiya an fita da shi ƙasar waje domin nema masa lafiya kuma tare da mijinta aka tafi, dalilin da ya turo direba ya ɗauke ta ya ma yar da ita Daura ta koma da kwana uku Allah ya yi ma Maimartaba rasuwa, mutuwar da ta saka ma suna da mutuwa mai tonon asiri, domin sanadiyar mutuwar maimartaba sirrin auran ta ya bayyana a masarautar Daura. Ranar da Hakimin Daura ya zo hankali tashe yana sanar da ita mahaifiyarsa Fulanin Daura ta saka ana bibiyansa ta gano komai saboda haka ta shirya zai saka a zo a ɗauke ta zuwa can Mubi har zuwa komai ya lafa ya fita ya barta cikin tashin hankalin da ya jawo mata gajeruwar naguda.
Daga ita sai Zulai ta haifi kyakyawan ɗanta namiji mai kama da uban shi, tana ma nishin haihuwan Fulanin Daura ta dira gidan a daran tare da Mijinta Hakimin Daura.
Fatima na kwance a cikin jinin Haihuwa Fulanin Daura ta umarci ɗanta da ya sake ta a cewarta zama da Fatima zai iya yi masa cikas da hawa karagan mulki ita kuma nan duniya ba abin da take muradi da fata kamar ta gan shi ya gaji mahaifinsa Fatima na kuka yana kuma yana roƙon ta amma Fulani ta ce ya zaɓa ko daraja da ƙimar masarautan Daura, Ko auren Fatima
Ba shi da yadda zai yi anan take ya yi ma Fatima saki ɗaya sannan ko ɗan da aka haifa masa Fulanin Daura ba ta bashi damar ɗaukan gudun jininsa ba a daran ta saka aka ɗauki Fatima a mota ita da abin da ta haifa, a cikin jinin haihuwa ita kanta da tsamin naguda da jinin haihuwa a jikinta ta kamo hanyar Yola a daran ba ta je ga gidan mariƙanta ba , sannan ba ta je mubi ba Sai ta je ga Baffa da Ammah ƙarfe uku na dare Fatima ta isa ita da Zulai da wani dogari Baffa sai da ya yi hawayen tausayin Fatima. Suna kuma kawo ta ba su tsaya ba suka juya daga Umarnin Fulanin Daura bayan an basu kuɗaɗe da gwala'gwalai da cewa kar Fatima da abin da ta haifa su sake dawowa Daura har abada. Sannan su Madibbo ma sai da Fulani ta saka a ka sauya musu gari suka koma cikin garin kurfi a cewar ta, ba ta son duk wani da ya danganci Fatima ya zauna a garin Daura ba ta fatan nan gaba labarin Fatima ya fito har ya yi ma ɗanta cikas ɗin zamowar Sarki. Waɗanda ma suka sani a lokacin duk ta rufe bakin su, ta haramta musu ambaton labarin.
Tabbas burinta ya cika, Hakimin Daura Muhammad Nasiru ya gaji mahaifinsa ya hau ƙaragan mulkin Daura bayan matarsa Gimbiya Shahida ya sake auran mata uku ya cike kofa a halin yanzu mata huɗu gare shi, ita kuma Fatima tana wajen Baffa tana rayuwa cikin kunci da baƙin ciki, dalilin Fatima domin ta samu kwanciyar hankali ya so da a ce shi mai kuɗi ne da zai yi nesa da garin Yola na har abada saboda Fatima ta samu kwanciyar hankali amma duk da haka sai da suka bar Yola suka koma cikin Jimeta da zama, kuma dawowar Fatima gida bai sa ya je Mubi ya faɗa musu abin da ya faru ba daga can ne Midibbo ya sanar da su ga abin da ya faru Baffa Hamza ya dawo yana wallahi tallahi, duk dai bayan an gama jajantawa ba wanda ya sake bi ta kan Fatima ballanta halin data ke ciki.
Fatima ba ta mgana sai kuka sai damuwa ba ta cin abinci sai Baffa ya zaunar da ita yana ba ta baki da lallashi da nasiha kamar ta ji amma da ya bar wajen sai ta koma gidan Jiya. Muhammad Lamiɗo da Baffa ya yi ma shaƙika da huɗuba wajen ma bashi Nono ma sai Baffan ya tsaya mata ba domin Ammah ba sai dai Lamiɗo ya mutu ba mai kula da shi, itace ta haɗa shi da Kabiru a lokacin mutane da dama suna tunanin ko y'an biyu ta haifa tunda tsakanin su bai fi kwana arba'in ba. Ammah ta sha wahala sosai ga Fatima ita kanta kula da ita ake yi Aminiyarta Aisha ce auren ta ya mutu a can Mubi kuma ana ta magana sai Amma ta yi ma Baffa mgana ya ce ta taho ta zauna da su na wani lokaci, ko domin ta riƙa taimaka ma Amma da kula da su Lamido ga Fatima.
Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya a wajen su Ammah ta samu miji ta yi auren ta da Babansu Baɗɗo Malam Sani, mutumin Jada ne shima kasuwancin siyar da hatsi ne ya kawo sa Jimeta ba jimawa suka yi aure anan kuma cikin Jimeta suke zaune Amma ta fi kowa murna Aminiyarta ta dawo kusa da ita. Haihuwan ta na fari mace ta haifa mai suna iklima shi ne dalilin da ya sa ake kiran ta da Ummin ikki.
Fatima ta sha gwargwarmaya kafin ta dawo daidai. Daga lokacin ta tsani duk wani abu da ya shafi sarauta, ta tsani har garin Daura gabaɗaya. A daddafe ta yaye Lamiɗo ta sakar ma Ammah ita kuma da taimakon Baffa ta koma makaranta a zaman ta a gidan Baffa har deperession sai da ya kamata Allah ne ya taimake ta tana da sauran kwana a gaba, zuciya da takaicin abin da aka yi mata ya sa ta ji tana so ta tashi daga Fatima yar ƙauyen Mubi zuwa Fatima mai ilimi wacce za ta nemi ilimi domin gobenta ta yi kyau.
Daga SS1 ta fara karatu sannan tana zuwa lesson haka saboda taimakon kanta tunda daga sama ta faro karatun kamar ba za ta iya ba domin ta sha wahala kafin ta fara ganewa ko za ta sare sai ta ba ma kanta ƙwarin gwiwa ta cigaba. Ta zana jarabawa kuma ta ci sai ga ta da taimakon Baffa ta samu gurbi a Federal Collage of Education Yola Jimeta. Saboda ma ta yi karatun a cikin makaranta take zama sai bayan wata ɗaya take zuwa ganin su Baffa Lamiɗo ko tun da ta yaye shi ta sakar ma Ammah ta ce ta bar mata shi halak makal a matsayin ɗan ta. Shikenan ta koma kamar ba ita ta haife shi ba shi ma yadda ba ta ta kansa shima Ammah ya sani a matsayin uwa tun yana ƙarami. Fatima ta mayar da hankalinta a kan karatunta da taimakon Baffa.
Bayan ta gama NCE ba ta zauna ba ta nemi gurbi a jami'ar Maddibo Adama University, tun a lokacin tana Federal University of Tecnology.
Shima saboda nisa a garin Girai jami'ar take can take zama a hostel sai ta samu hutu take zuwa gida kuma tana karantar Biology ne. Fatima ta saka kanta da cewa za ta iya ta yi dakiya ta yi naci kuma Allah ya taimaketa ta cika burin ta.
****
SHEKARU TALATIN DA SUKA SHUƊE A BAYA.
Bayan shuɗewar wasu shekaru Talatin a baya Rayuwa ta daidaita. Tunda Baffa harkokinsa sun buɗe ya yi arziƙi da kasuwancin sa na siyan tsoffin ƙarafa yana siyarwa sannan shekaru goma a baya ya fara haɗawa da siyar da motoci tun haɗuwarsa da Alhaji Isa Ɗan marke bazamanfare mai siyar da motoci wanda ke da kamfani a garin Kaduna sun daɗe suna kasuwanci kuma dalilin shi Baffa ya samu alheri masu yawan gaske. Baffa ya gina katon gida a anguwan Zone 3 in da iyalansa ke zaune har yanzu.
Shima Alhaji Isa Ɗanmarke a dalilin Baffa ya samu matar aure. Ya auri Fatima tana da shekaru talatin da biyar mai kwalin karatun Degree da masters a lokacin. Matarsa ta rasu kuma ba su taɓa haihuwa ba yana ganin Fatima a gidan Baffa ya ce ya yi mata Baffan kuma ya bashi domin a lokacin shi ke da alhakin aurar da Fatima da duk itama tana da haƙƙi tun da ita bazawara ce. Fatima ta auri Alhaji Isa ta kuma tare a gidan shi dake Kaduna. Suna kuma yin auran ta ɗora karatun ta na PHD a jami'ar Amadu Bello dake Zaria wato ABU ZARIA.
Tana cikin kuma karatun ne ta samu ciki ta haifi yarta mace Islam(Fatima) bayan ita sai da ta gama karatu da shekaru biyar sannan ta haifi Faruk(Umar). Tun bayan barowan ta Daura ba ta sake komawa ba amma su mutanen Dauran sun neme ta daga baya saboda Lamiɗo.
Baffa kuma ya tara zuru'a sai son barka. Hamma Jibo ne babba wanda ya yi karatu har matakin Master mazaunin Abuja da iyalansa shekarunsa na haihuwa 40.
Sunan matarsa Nauwara da yaran su huɗu, Saudat, Jamila(Amma) sai yan biyu Hassan da Hussaini sai Isma'il.
Sai Hamma Mustapha shima ya yi karatun boko har matakin Degree yana garin Gombe tare da iyalansa yana aiki da hukumar ruwa(Water resourses) shekarunsa na haihuwa 38.
Sunan matarsa Aisha(Momi) ya'yansu uku Fatima(Mahma) Zainab sai Hadi(Baffa).
Sai Hamma Kabiru shima ya yi degree a kan medical lap, yana aiki da asibitin Federal hospital Jalingo. Shi kuma shi da Lamiɗo suna cikin shekaru na 35 ne.
Sunan matarsa Safinatu yaran su biyu, Muhammad da Yusra, kuma a can Jalingon yake zaune da iyalansa.
Sai Hamma Abdulrrahman lauya ne mai zaman kansa yana zaune a garin Jimeta shekarunsa 33. Matarsa Ummu Sulaim da ya'yan shi biyu duka mata. Mariya da Jamila(Mimi) sai Hamma Abdullahi tare suke kasuwanci da Baffa shima ya yi karatun Boko ya karanta harkan kasuwanci shekarunsa 31 babu nisan haihuwa tsakanin a duka yaran Amma.
shima yana zaune da matarsa Suwaiba da ɗansa ɗaya Umar(Maddibo) sai Hamma Abdulrahim shi kuma yana can ƙasar singphore yana karatun likitan ci, ɗan kimanin shekaru 29.
Wanda Hamma Lamiɗo ya ɗauki nauyin karatun na shi.
Sai Hamma Saddam wanda ke karatun mass com a jami'ar ATBU BAUCHI yana aji uku, tsakanin Saddam da Auta Ummu wata ashirin ne.
Shi yana cikin shekaru na 27 ne. Sai Auta Ummu Salma wacce iyakar ta sakandiri ta tsaya aka yi mata aure.
Zuwa lokacin rayuwa duk ta yi kyau, a can Mubi ma Baffa Hamza ya rasu haka ma Umma(Asma'u) a gidan su Baffa yanzu Baffa Umaru ne Babba duka kuma a gidan su ke zaune da ƴa'ƴansu da iyalansu, su dai ba su bar Mubi ba suna nan a cikin ta amma dai Baffa da iyalan shi suna zuwa Mubi akai akai in an yi wani abu Amma ma tana da zuru'a a can tun da su Umma Balki sun tara iyalai masu yawa a can Mubi ɗin. A nan kuma ita da Ummin ikki ne suka tara iyalai, sai son barka Ummin ikki ta aurar da matan ta huɗu, iklima, Saratu, mai sunan Amma Jamila, sai Binta sannan kaltume da Baɗɗo(Aisha) su ne yanzu a gabanta ita Allah bai ba ta namiji ba amma Mallam Sani ya kara aure amaryan ta haifa masa maza uku. Amintansu da Ammah sai ma abin da ya yi gaba sai dai duk amintan dake tsakanin Ammah da Ummin ikki Baffa da Mallam Sani ba sa Aminta sosai amma suna da kyakyawan alaqa da juna sai dai ba kamar Aminta da shakuwa irin na matan su ba
Abin da Mami(Fatima) ba ta sani ba shi ne tun Lamiɗo na ƙarami Mahaifin shi Maimartaba Sarkin Daura Alhaji Dr Muhammad Nasiru na tura kudaɗe duk wata domin hidimarsa a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba sannan duk in da Baffa suke yana sakawa ana bibiyan su
Da shawaran ƙanwarsa mai bi masa Hajiya Zaliha(Magajiyar Sanda Mata) kuma ita ke auran Madakin masarautan Zazzau, tun faruwan lamarin ita ce kawai ta nuna rashin kyautawar Fulanin kan abin da aka yi ma Fatima. Amma sauran duk sun goyo bayan Fulani a wancan lokacin. Ita ce ta bashi shawaran ya nemi in da Fatima take domin gudan jinin dake tsakanin su, ya sani Fulani ba yadda za ta yi domin Ubangiji mai haɗawa ya riga ya haɗa danganta a tsakanin shi da Fatima ta sanadiyar Lamiɗo.
Tunda ga haihuwar Lamiɗo har girman shi da komai da komai Marmartaba yana da labarin komai sannan shi ya saka a ka samo masa lambar asusun bakin Baffa yana tura masa kuɗi, a saƙon da ya taɓa tura masa na farko ne ya yi bayanin kan shi sannan ya roƙi Baffa da cewa kar ya ce ba zai karɓi kuɗin ba, har abada ba zai taba karɓan Lamido daga hannun su ba, shi ko Baffa daman ko bai roƙe sa ba, ina shi ina ma yar ma da sarki kuɗi kuma ko ya ce zai karɓi Lamiɗo ai ba shi da ta cewa ba zai iya ja da masu mulki ba, shi ya daɗe da yafe komai da man sanadin Fatima ne, yanzu kuma Fatima ta samu komai na rayuwa kuma yawancin mutanen da suka yi ruwa da tsaki a kan auran ba sa raye. Hatta mariƙan Fatima na Daura sun rasu da daɗewa amma dai har yau akwai wasu daga cikin ahalin Gwaggo a garin Daura Baffa dai kan tura musu saƙo amma shima ba zuwa yake yi kamar yadda Fatima ta tsani garin haka shima ya ji ya fita kan shi gabaɗaya.
Mami ba ta san Maimartaba ke ɗauke da nauyin Lamido ba sai da ya tafi ƙasar Malesia karatu a lokacin Baffa ya sanar da ita komai saboda ta san ba shi da kuɗin da zai kai Lamiɗo waje domin ya yi karatu kuma kaf cikin yaran ba a kai kowa ba sai shi. Ta sha kuka tana faɗin ita har abada ba ta da alaqa da waɗanan mutanen Baffa ya nuna mata ita ko ke da alaqa da su, tunda akwai jininsu a tare da ita. Da ta yi bore Ammah ta ce ba ruwanta tunda daman tuntuni ta ce ta bar mata ɗan, jin haka yasa ta cire bakin ta akan Lamiɗo da man kuma ba saka bakin take yi ba.
Rayuwa ta gangara har Lamiɗo ya gama karatun shi na degree da Master akan Nautical Sceinces a jami'ar Akademi laut Malaysia. Ya samu ƙwarewa da horo kan tuƙin jirgin ruwa kuma lokacin ne Fulanin Daura ta buƙaci Jikan da ta juya ma baya tun a farko. Saboda duka ƴa'yan sarakunan da ta aura ma Maimartaba ba su ba ta jika namiji ba sai mata ita kuma tana so zuru'an ta su ƙare a zamowa sarakuna ne shi ya sa ta ɓullo da maganar nemo Fatima da abin da ta haifa shi kuma da man Maimartaba yana neman dama ne sai ga Fulanin Daura har falon Ammah tare da manyan ƴa'ƴanta mata
ta duka tana ba ma su Baffa haƙuri, Baffa ya ce shi ya daɗe da yafewa Fatima za ta roƙa gafara. Mami kuwa ta ƙi yafe musu har sai da Fulanin Daura ta je har falonta a gidan mijinta dake garin Kaduna. Dalilin mijinta Alhaji isa ya sa ta yafe ma Fulani da ɗanta amma game da Lamiɗo ta ce ba ruwanta a ciki ta nemi Baffa da Ammah sune iyayen Lamido. To shima dai Lamiɗon ya yi taurin kai duk da daman ya san ba Baffa da Ammah ba ne suka haife shi ba. Maimartaba na zuwa Jimeta a ɓoye Baffa ya kai masa Lamiɗo ya gansa sannan da yana Malaysia yana zuwa ganinsa tare da Hajiya Zaliha(Mahma)
A haka ne sabo ya shiga tsakanin su kuma Maimartaba da kansa ya zaunar da Lamiɗo ya bashi labarin duk abin da ya faru shi ya sa ya fi jin haushin Fulanin Daura.
Bai amince da komawa Daura ba sai da Ammah ta saka baki sannan ya koma Daura da zama a cikin Masaurata. Gari ya ɗauka domin waɗanda suka san da auran aminttun sarkin a wancan zamanin duk sun rasu sai mutum ɗaya ne ya rage a lokacin shi ne ya ba da shaidan Lamiɗo ɗan Masaurata ne balle ma kamanninsa da kowa ya gani ba sai ya yi magana ba, kamar Maimartaba yana tashen ƙuruciyarsa.
Bai daɗe da komawa Daura ba ya kama aiki gadan gadan da kamfanin Nigerian Port Authority a matsayin matuƙin jirginsu Captain bayan ya karɓi licence ɗinsa a matsayin pilot matuƙin jirgin ruwa By Nigerian Maritime Administration and Safety Agency (NIMASA)
Sai ya zamana baya samun zama sosai amma duk salla a Daura yake yin ta saboda za a gudanar da hawan salla tare da shi, kuma uwa uba yana da wasu yan'uwan da suke uba ɗaya duk da ba su tashi a gida ɗaya ba amma dai yana son su tunda su ɗin jininsa ne.
Sai da ya auri ƴar Sarkin Kano sannan aka na ɗa shi Yariman Daura mai jiran gado duk da abubuwan sarauta ba su dame shi ba amma Muhammad Lamiɗo mutum ne nagari mai kirki kamar mahaifinsa. In dai ya na Daura talakawa da matasa na cikin alheri yana da alheri sannan ga ƙokarin samo ma matasa ayyukan yi.
Duk da shi miskili ne mara sakewa amma kuma mutanen garin Daura suna son shi saboda yana da kyautawa. In dai ya zo Daura to tare da shi ake zaman Fada a dole sai an koya masa abubuwan da suka shafi sarauta, abin da ba su sani ba shi bai taɓa sha'awar Sarauta duk da ko bai faɗa ba mutane da dama in suka gan shi da yanayin shi sai sun ce yana da jinin sarauta a jikin shi. Sannan in dai ya zauna da Maimartaba to ba su da hira sai hiran sarauta da tarihin masaurata da sarakunan da suka gabata. Haka ma Hajiya Zaliha ko da wani lokaci suka haɗu girman matsayin shi take nuna masa, da lissafinta na cewa wata rana shi ne a kan ƙaragan da mahaifinsa ke zaune yanzu. Shi sai dai ya ji su kawai kwata-kwata baya son mulki kuma ba zai taɓa sha'awa ba, saboda mulki hayaniya ne da damuwa tare da nauyi shi kuma ba ya so.
Hajiya Zaliha(Mahma) tana son Lamiɗo sosai saboda ba ta taɓa haihuwa ba shima yana son ta ko domin yadda take ji da shi ya sakata cikin jerin mata masu muhimmanci a rayuwarsa.
Fulanin Daura da ta tsufa yanzu ba ta da abin so kamar Lamiɗo tana ji da shi kamar tsoka ɗaya a miya. Shi ko ba ya wani ta kanta amma dai yana zuwa wajenta ya zauna na wani lokaci in dai ya zo garin.
Itama in ya je wajenta haka za ta zaunar da shi tana ta yi masa hira da labarin Masarautar Daura har ya gaji da ji ya haddace. Da yana jin haushin ta akan abin da ya faru amma daga baya ya daina tun da ita kanta Mami ta na can tana wata sabuwar rayuwar da shi da Ahalin na shi duk ba sa gabanta shi ya sa ya bar komai ya wuce ya kuma rumgumi ahalinsa. Ba a sauya ma tuwo suna duk a je a dawo abin faharin shi da asalin shi garin Daura ne.
Dalilin abin da Fulani Daura ta aikata ne daga baya Fargar Jaji ya kamata ta yi nadama. Saboda haka ya sa duk wani abu da zai faru a Masarautan Daura za a sanar ma da Ammah da Baffa saboda Lamiɗo zumunci mai karfi ne a tsakanin Ammah da Gimbiya Shahida uwar gidan Maimartaba da man duka sauran matan na shi.
Sannan Fulanin Daura yadda ta dauki Lamiɗo da muhimmanci haka ta dauƙi Ammah da Baffa. Mami ce tun da ta ce ba ta da alaqa da su haka ɗin take ba ta ma nuna ma ita ta haifi Lamiɗo ballanta wani abu ya sa a sako ta a ciki. Shima kuma ba ya taɓa nuna Mami a matsayin mahaifiyarsa Ammah ce uwar sa har gaban abada.
Lamiɗo kawai suka sani da marikan shi da suke tamkar iyayen shi, shima Lamiɗon ba ya ɗaukan kowa a matsayin iyayen shi sai Ammah da Baffa Mami dai kawai sunan ta uwa ne amma babu shaƙuwar ɗa da uwa a tsakanin su. Dalilin Lamiɗo har Hajji Masarauta ta kai Ammah da Baffa suka je suka sauke farali.
***
Ummu Salma ta kasance a wajen Ammah da Baffa a matsayin yar Auta. Ta taso cikin zaratan yayyen ta maza bakwai ko na ce takwas ga Lamiɗo sannan ita mace, shi ya sa in dai ana maganar gata sai dai a yi kwataance da Ummu Salma.
Tun tasowar Ummu ta tsani karatun boko, domin kanta gaskiya ba ya ja, kusan na kusa da na ƙarshe take ɗaukowa a makaranta. Duk gori da zagin da su Hamma Kabiru ke yi mata bai sa ta gyara ba. Kuma makaranta mai tsada take yi ta Ahmadu Ribaɗo Collage a garin Yola. Amma sai a saran kuɗi ake yi kwaƙwalwar Ummi ba ta fahimtar komai har gwara ma bangaren islamiya shi ba laifi amma na bokon nan ne sai a hankali. Ita kawai karatun boko na wahalar da ita ne, duk ko yadda ba ta iya shan inuwa ɗaya da su Hamma Kabiru a cewar su daƙikiya ce ita kar Hamma Lamiɗo ya ji labari ita tun zaman shi a gidan su jininsu bai taɓa haɗuwa ba, wata maganar arziƙi ba ta taɓa haɗa su ba shi ba ya magana ma. In ka gan shi yana mgana to da Ammah ne ko Hamma Kabiru, tun tana yarinya ta san shi ba ɗan Ammah da Baffa ba ne saboda su suna kama da juna amma shi kamininsa na dabam ne, duk da ba ta son shi amma kuma akwai shakuwa a tsakaninta da mahaifiyar shi Mami, wacce ita ta yi renon ta bayan Ammah ta haifeta kafin auranta sannan bayan ta yi aure tana yawan zuwa Kaduna gidan Mami ta yi hutu, Mami mace ce mai fara'a sannan ita da mijinta suna ji da ita in suka je kasashen waje haka Mami za ta ciko mata jaka cike da kayan sawa na alfarma sai wanda ya gani. Ta sha zama ta yi ta mamakin yadda Mami ta iya haihuwan Hamma Lamiɗo ita ba ta ga ta in da ma suka haɗu ba, shi dabam ita dabam ita mai fara'a ce mai kirki da son Jama'a saɓanin Lamiɗo da ba shi da fara'a ba shi da son mutane sannan ba shi da kyakyawan mu'amala.
Ummu Salma ta taso ta ga Aminci tsakanin Amma da Ummin ikki shi ya sa itama Aminta ya haɗa ta da Aisha(Baɗɗo) a yayin da makaranta ya haɗa ta da Shamsiya(Bestie) su suna da son karatu kuma suna ganewa ba kamar ita ba tun da kuma ta fahimci ba ta gane karatu ta ce ba za ta ci a karatun boko ba, daga lokacin ta saka ma kanta tunanin daga sakandiri ba za ta cigaba da karatu ba.
Kuma haka aka yi ba yadda ba a yi ba amma Ummu Salma ta ce ta gama Baffa kuma da Ammah suka goya mata baya. Abu ɗaya Ummu ta fi mayar da hankali shi ne girken-girken zamani, ta bakin Hamma Kabiru ya ce shi kaɗai take ganewa.
Bayan ta gama sakandiri ta je Kaduna ta yi wattani huɗu a wajen Mami saboda tsangwaman su Hamma Kabiru akan sai ta cigaba da makaranta tun ballanta ganin kawayenta Baɗɗo da Shamsiya sun cigaba.
A can kaduna ta yi ta shiga catering School tana samun ƙwarewa bayan ta dawo Jimeta ma ba ta zauna ba yayyenta sun gaji da magana sun ƙyale ta tun da Baffa yace boko ba dole ba ne, shi bai yi ba Ammah ma ba ta yi ba amma ba su mutu ba sun rayu saboda haka a bar Auta ta sarara. Kadunan ma da ta gudo saboda Mami ta fara zaunar da ita tana kwatance a kanta na amfanin karatu tunda ta ji haka tace za ta koma gida saboda Mami za ta iya jan Ra'ayin ta in kuma hakan ya faru ko ta shiga ba za ta iya ba gwara maganin ayi kar a fara.
Sai da ta yi zaman shekaru uku a gida ba makaranta ba ta da aiki sai girke girken zamani a gida duk abin da ta koya sai ta gwada shi tun ballantana abubuwan da take gani a waya tunda Mami ta siya mata waya Samsumg babba ta zamani, ko da yaushe tana cikin kwabin fulawa ita ce Cake ita ce donot wani abun ta yi ya yi daɗi wani kuma ya lalace Amma ta yi ta masifa Baffa ne mai supporting ɗin ta.
Ummu Salma Bata taɓa tunanin za ta haɗu da Habib ba sai ga shi Allah ya haɗa su, wata rana ta dawo daga gidan su Baɗɗo ya biyo ta. Duk da a ganin farko ta ji ya yi mata ba ta ɗauka soyayyar da ya nema a wajenta zai kai su ga aure ba sai ga shi komai ya faru cikin lokaci. Ummu Salma da Habib sun yi soyayya kamar su lashe juna kafin aure ya nuna mata duk duniya bai so wata mace sama da ita ba, yayyenta suka yi ta mganganun cewa bai kamata a yi mata aure a lokacin ba, amma Baffa ya ce tunda ta samu miji kuma ya bincika yaron nagari ne zai aurar da Ummu sun yi adawa sosai amma kuma sun haƙura daga karshe. Cikin wattani biyar aka yi auran Ummu Salma da Habib auran ya zama abin kwatance kowa na ganin Ummu ta gama yin dace, ko bayan auran Habib ya nuna ma Duniya Ummu Salma ce duniyarsa, zaman lafiya da soyayya da ƙauna shi ya rike su a cikin wattani takwas ɗin da suka yi da aure. Duk masu adawan auren ta sun haƙura ganin tana zaune lafiya da mijinta.
Ummu Salma ta ɗauka ta gama dacewa. Ta ɗauka bayan ita da wahala a samu mace irin ta a cikin tsara. Sai ga shi cikin wattani uku Habib ya yi ma rayuwarta juyin waina daga sama ta koma kasa. Cikin wattani tara zuwa goma da auran su ya yi ma rayuwarta katon taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta manta ba.
*Janafty*