12
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*12*
Hamma Abdullahi ya ɗauko Ummin ikki a mazaunin gaba na motarsa sai Baɗɗo da Ummu dake zaune a gidan baya akan hanyar su ta zuwa gidan Baffa. Baɗɗo ne ke ta kuka saboda in ta kalli Ummu sai ta ji rauni ya dabaibaye ta, ita ma Ummin ikki hawayen take yi tana sake rantsuwan ba za su yafe ba sai Allah ya yi ma Ummu sakayya akan tozarcin da Habib ya yi mata.
Hamma Abdullahi ko baya magana tuƙinsa kawai yake yi amma in da za a tona zuciyarsa da wataƙila an fahimci halin baƙincikin da yake ciki, takardan sakin tana cikin aljihun jallabiyan jikinsa har wani ɗaci yake ji a ran shi na tozarcin kalaman Habib yanzu ya ya Baffa da Amma za su ji? Ummu ma ba a maganar ta, tana zaune kawai ta ƙura ma gabanta idanuwana sai ta daɗe ba ta kyafta idanuwana ba kamar wacce ta zama gunki ba ta kuka ba ta motsi sannan babu hawaye sai dai ido kawai yana kallonta, ta cikin madubin motarsa na gaba gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi kamar an masa wanka da ruwan sanyi, addu'a kawai yake yi mata Allah ya ba ta ikon cin wannan jarabawan domin jarabawan mai zafi ne sai wanda ubangiji ya so zai iya tsallakewa.
Har suka isa gidan Baffa dake Zone 3 suna cikin wannan yanayin har cikin haraba Hamma Abdullahi ya shiga da motar Baɗɗo ta kama Ummu ita da Ummin ikki suka shiga da ita cikin gida yayin da Hamma Abdullahi ya buɗe boot ya kwaso akwatin Ummun guda huɗu ya bi bayan su da shi. Amma na zaune a falonta tun bayan fitowarta daga wajen Baffa ba ta koma ba, ba ta so ya fahimci tana cikin gigita shima kamar ya sani sai ya bata lokaci tunda suka gama waya da Aminiya take zaune cikin mutuwar jiki da na zuciya na tsawon lokaci kafin ta ji sallama a tsakar gida zumbur ta miƙe jikinta ba in da ba ya rawa ɗago labulen da aka yi ne yasa Amma ta yi saurin komawa ta zauna tana ɗan daidaita yanayin ta.
Lokacin da suka shigo da Ummu a riƙe kallo ɗaya Amma ta yi mata ta ji ta sare, kafafunta sun yi mata nauyi da ta kasa ma miƙewa Ummu ce ta koma haka! Idanuwa sun kumbura fuskarta ta yi wani irin jajir, tana zaune kawai tana kallon su, suka zaunar da ita a saman kujera Baɗɗo ta zauna a gefenta ta jawo ta a gefen kafaɗanta tana ɗan tapping bayanta alamun lallashi, duk in da aka bi da ita can take bi kamar wata doluwa ko yarinya ƙarama.
Ummin ikki ta ƙarisa kusa da Amma ta zauna tana faɗin" Aminiya yau mun tashi cikin jarabawar Ubangiji."
Amma ta kalleta kafin ta ɗan motsa bakinta a hankali tana faɗin" Allah ya sa hakan ya zame mana alheri gabaɗaya"
Ummu ikki ta amsa da Amin kafin ta fara goge ƙwalla tana cigaba da faɗin" Wannan yaro ya cuce mu. Da ikon Allah sai Allah ya saka mana."
Ta faɗa tana kallon Ummu har a lokacin kawai waje ɗaya take kallo ko kiftawa babu, kafin ta sake cewa wani abu Hamma Abdullahi ya yi sallama ya shigo cikin gida sun amsa sannan ya shigo falon Ammah, sanda suka taho da su Ummin ikki Hamma Jibo ne ya kira wayarsa shi ya sa ya ɗan dakata suka yi magana ya sanar da shi ya kawo su gida yanzu. Akwatin hannunsa ya jera anan tsakiyar falon Ammah ko zama bai yi ba ya kalli Ummu na wani lokaci kafin ya ɗan girgiza kansa.
"Ina kwana Ammah."
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Lafiya lau Baba ya iyalan naka?
Ta amsa masa amma ba ta kalle shi ba kanta na ƙasa ba ta so shima ya fahimci halin da take ciki, ko ba ta fito ta nuna ba ko ta ɓoye Ammah fa uwa ce ga Ummu Salma yadda lamarin nan zai daki kowa barin ita ne.
"Suna lafiya."
Ya faɗa sai kuma ya yi shuru, Ummin ikki na ta sharan ƙwalla Baɗɗo ko hawaye ne wasu na zuba wasu na sake tunkuɗowa.
"Ba komai in sha Allah zai wuce."
Hamma Abdullahi ya faɗa domin a lokacin shima ya rasa kalaman da zai faɗi falon ya yi shuru kamar mutuwa ta gifta tun ballanta shessheƙan kukan Baɗɗo da na Ummin ikki. Ummu dai ba ta kuka da man an ce wani baƙin ciki in ka yi kukan daga baya in kukan ya ɗauke shike nan sai dai zuciya ta dinga ƙuna da raɗaɗi to hakan ce take faruwa da Ummu tunani take yi kamar ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa gani take yi kamar komai a mafarki ne in ta farka za ta ganta a cikin ɗakin auren ta, tare da Habib amma ina duk lokacin da ta kifta idanuwanta a falon Ammah take sake ganin ta.
"Ammah Baffa fa?
Ya faɗa ganin Ammah ta yi shuru kanta na kallon ƙasa.
"Yana cikin ɗakin sa."
Ammah ta amsa masa cikin ajiyar zuciya.
Ya kama hanyar barin falon ne sai ga Baffa ya shigo da sallama daidai lokacin da Hamma Abdullahi ya ɗaga labulen falon Ammah sai ya koma da baya ya ba ma Baffa waje domin ya shigo.
Baffa ya shigo har falon Ammah ya yi tsaye kawai yana kallon Ummu Salma sanye yake da manyan kaya tun da ya saka ne zai je masallaci da asuba.
Tun ɗazu ya ji shigowarsu amma ya kasa tashi ne, bai san adadin hawayen da ya share a ciki kafin ya fito ba. Bai san a wani hali zai ga Ummu ba! Abin da ya faru da ƙanwarsa Fatima ya dawo masa sabo, shi kaɗai ya san dararan da ya ɓata idanuwan shi biyu yana kukan tausayin Fatima tausayin jarabawan rayuwan da ta faɗa sai ga shi kwatan kwacin haka ya sake faruwa da gudan jininsa Ummu Salma, amma bai yi butulci ba sai ya yi ma Allah godiya domin ba wai ba ya son bayin shi ba ne don ya sake jarabtansu, ya yi haka ne domin ya sake jaraba imaninsu, yana fata da tunanin in Habib ya zama mafarin Ummu Allah ya kawo mata wanda zai wanke mata duk wani dattin zuciya da Habib ya sanya mata.
Ko da yake tsaye a gaban ta, ba ta nuna alamun ta san ma yana wajen ba, kawai gabanta take kallo babu ko ƙyaftawa. Falon ya sake yin shuru kamar ba kowa a ciki Baffa ya duƙa a gaban Ummu yana kallon ta amma ita ba shi take kallo ba kawai gabanta ta ƙura ma idanuwa ba ta ko motsi daga in da take zaune Baɗɗo na rumgume da ita.
"Ummu Salma."
Baffa ya kira sunan ta cikin kulawa na musamman.
Shuru ita ba ta amsa ba sannan ba ta kalle shi ba, ya sake kiranta a karo na biyu nan ma ba ta ɗago ta kalle shi ba sannan ba ta amsa ba.
"Ummu Salma."
Shuru falon ya sake ɗauka kowa hankalin shi na wajen Ummu cikin tausayi.
"Kalle ni nan Ummu Salma."
Baffa ya sake faɗa lokaci ɗaya yana riƙo hannunta guda ɗaya, abin mamaki haka ya riƙe hannunta da ya ji sa ya yi sanyi sosai amma Ummu ta kasa iya rike Baffa sai ta ji kamar duka kasusuwan hannun nata ba sa aiki, daƙyar ta iya ɗago idanuwanta ta kalli Baffa. ta ƙura masa ido ba ko kiftawa tana ta kallon shi.
"Ummu Salma."
Baffa ya sake kiranta yana mai matse hannunta a cikin na shi hannun, yana ji kamar ya fashe da kukan tausayin ta amma in ya yi kuka ita za ta sare a yanzu a wannan kadamin su ne ƙarfin gwiwanta in suka rushe itama za ta rushe.
"Ummu Salma."
Ya sake kiran sunan ta, sai ta motsa idanuwanta. Ta kifta ta sake kiftawa sai ga hawaye sharr sun kwaranyo mata a saman kumatun ta.
Ganin Baffa kawai da ta yi ya duƙa a gabanta yana kiran sunan ta ya sa hawaye ya kawo mata. Ya Baffa zai ji? Wani hali zuciyarsa take ciki? Ta yi aure ta tafi ita kaɗai sai gashi ta dawo musu da ciki a cikin jikinta, Ammah ma ta san tana cikin firgici kawai tana ɓoyewa ne. Kuka fa ake yi saboda abin da ya same ta. Ita ko in ba ta ce tana cikin bala'i ba me za ta ce?
"Allah ya ba ki dangana Ummu Salma. Sannun kin ji ko?
Baffa ya faɗa yana sake jinjina hannanunta dake cikin na shi. Sai ta sake kifta idanuwanta hawaye suka sake zubo mata.
"Ai gwara ta yi kukan ko za ta samu sauki. Tunda muka je yarinyar nan ke cikin wannan yanayin."
Ummin ikki ta faɗa cikin rawan murya. Baffa ya yi shuru kansa na ƙasa kafin ya saki hannun Ummu ya miƙe yana kallon Baɗɗo na saka tafukan hannayenta tana mai share ma Ummu hawaye.
Hamma Abdullahi da tausayin Ummu ya kama shi sai ya ji kamar ya yi mata ƙwalla amma duk da haka idanuwansa sun kala sun yi jajir kamar gwarwashi saboda bacin rai.
"Baffa ina kwana? Ya muka ji da wannan al'amarin kuma da muka tashi da shi yau?
Ummin ikki ta faɗa tana faman goge ƙwallah.
Baffa ya sauke numfashi kafin ya amsa mata.
"Lafiya lau. Ya za a yi da sanin Allah komai zai wuce in sha Allahu."
Baffa ya faɗa cikin karfin hali kafin ya sake kallonta yana faɗin" Sannu da kokari mun gode sosai Allah ya bar zumunci."
"Amin yiwa kai ne Baffa. Allah ya saka ma wannan yarinyar."
Kowa ya yi shuru bai ce komai ba, sai da Baffa ya sake jan numfashi kafin ya ce" Ba komai. Komai zai wuce."
"In sha Allahu."
Hamma Abdullahi ya faɗa cikin damuwa.
Ammah dake zaune tun ɗazu ba ta ce komai ba ta ɗago tana kallon Baffa kafin ta ce" Baffa ko za ka kira waliyin Habibun. Watakila su shiga ciki su iya gyara al'amarin."
Hamma Abdullahi na shirin magana Ummin ikki ta yi saurin cewa" Tab wani gyara kuma Aminiya?
Ammah ta kalleta cikin mamaki ba ita ba har Baffa ma.
"Saki uku fa ya yi mata."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
Baffa ya yi saurin faɗa cikin fitan hayyaci, Ammah kuma sai ta kasa magana amma bakin ta na motsi.
"Wallahi tozarcin da yaron nan ya yi mana kenan. Takardan sakin ma tana hannun Baba."
Ummin ikki ta gama faɗa tana nuna Hamma Abdullahi shi ko bai yi magana ba ya zaro takardan sakin cikin aljihun wandon sa ya mika ma Baffa, hannunsa na rawa ya karɓa haka fa ya karɓi na Fatima shekaru talatin baya yau ma gashi zai sake karɓan na Ummu Salma, Allah kana gani.
Nan take Baffa ya warware takardan ya fara karantawa a bayyana ne, kafin ya gama ya jiƙe da zufa kafafuwansa sun gaza ɗaukansa sai da ya yi ɗan baya ya samu damar jingina da bangon ɗakin Ammah.
Ummi ikki sai ta hau kuka tana jero ma Habib addu'an Allah ya sa, Ammah ko wani nauyi ta ji daga ƙasan zuciyan ta. Ganin ta ya yi duhu sai kawai ta dafe kanta ta kasa mgana.
"Lalle wannan yaron ba shi da mutumci."
Ummin ikki ta faɗa cikin cizon yatsa, Ummu na zaune a yadda take amma abin da Baffa ya karanta ya yi mata fami a gyambon ta wataƙila da Baffa ya san ba ta san abin dake cikin takardan ba da bai karanta kowa ya ji ba, ita ba kanta take ji ba su Baffa ya za su ji? Ita ta riga ta gama Haddace kalaman Habib na baya son ta sannan ta daɗe da fahimtar manufar auran ta zuwa gare shi, su ne suka rage su sani duk kuma yadda ta kai ga yi ma maganar rufa rufa Habib ya fallasa komai.
Baffa ya yi shuru kawai da takarda a hannunsa ya kasa magana. Zuciyarsa na wani tafarfasa in da a ce zai iya wallahi da sai ya yi shari'a da Habibu amma kuma ba zai kai shi kara a kotun duniya ba sai dai ya kai shi a kara a kotun Allah. Ya gama cutar su ya cuce Ummu Salma ya gama da rayuwarta ko da sun yi ƙaran shi a gaban hukuma wani ɓata lokaci ne, sannan tonuwar asirin auran Ummu ne ga duniya amma a ƙotun Allah ne kaɗai zai karɓi sakamakon abin da ya aikata.
"Baffa bai kamata a bar yaron nan ya tafi haka ba gaskiya."
Hamma Abdullahi ya faɗa cikin jin haushi.
"In ya saki Ummu ba mu yi jayayya ba, amma maganar ya bar mata ciki ba shi da alaqa da shi bai ta so ba, tunda har shi ya yi cikin nan bai isa ya ce babu ruwan shi ba in ya yi taurin kai ai akwai hukuma sai mu yi ƙaran shi "
Ya faɗa yana kallon Baffa da ya yi shuru ya kasa mgana.
"Gaskiya magana, ita in mun ƙarbeta tamu ce amma ai cikin na shi ne bai isa ya ce babu ruwan shi ba"
Ummin ikki ta faɗa Baffa dai ya yi shuru bai yi magana ba sai kawai ya zura hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro wayarsa.
"Wa za ka kira Baffa?
Hamma Abdullahi ya tambaya sai kawai Baffa ya ɗaga masa hannu ba tare da ya yi magana ba. Lambar Alhaji Sheriff ya nemo lokaci ɗaya ya kira shi ya kara a kunne tana ta ringing bai ɗaga kiran ba sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗaga wayar daga can bangaren da sallama, Baffa ya amsa cikin dattakon sa ran shi a ɓace yake shi ya sa bai tsaya ma wata doguwar gaisuwa ba.
"Alhaji kana da labarin ɗan ku Habibu ya saki Ummu Salma saki uku?
Daga can bangaren Alhaji Sheriff dake zaune a ɗakin da mahaifin Habib ke jinya a cikin gidan su ya miƙe a razane cikin firgici ya ce" Innalillahi yaushe? Wallahi tallahi Alhaji ban sani ba."
Ya faɗa cikin tashin hankali to da man ai ba zai sanar da kowa in zai aikata abu mara kyau ba a yanayin maganar Alhaji Sheriff za ka fahimci bai sani ba sannan maganar kuma ta dake shi matuƙa.
"To ya sake ta saki uku gata nan ma na saka an je an taho da ita."
"Hasbunallahi wa'imal wakel. Alhaji wallahi bamu sani ba. Ba mu da labarin wannan hukuncin da Habibu ya yanke"
Alhaji Sheriff ya sake faɗa cikin ɗimuwa da tashin hankali tare da nadamar yadda ya shiga lamarin Habibu, da yau bai shiga ba tuni bai ji kunyar da ya ji yau ba.
"Ba komai Alhaji kar ka damu na san da man ba ka sani ba, da man dalilin da ya sa na kira ka wani saƙo zan ba ka zuwa ga Habibu sannan na kafa shaidata akan maganata da kai "
Alhaji Sheriff ya ma kasa magana Gwaggo ma ta dawo ɗakin da man ta ɗan fita ne, jin wayar da Alhajin yake yi yana rantsuwan bai sani ba sannan yana ambaton sunan Habibu ya sa ta tsaya ta kasa fita cikin zullumin abin da kuma ya sake faruwa.
"A cikin takardan sakin ya rubuta cewa da man ba son Ummu Salma yake yi ba, jikinta ne ya sa ya aurete kuma yanzu tunda ya gama moran abin da ya aura domin shi, shiyasa ya sake ta."
Baffa ya faɗa yana jin ƙuna a ƙasan zuciyarsa.
"Lailahaillallah."
Alhaji Sheriff ya faɗa cikin tsorata da lamarin Habibu.
"Sannan kuma ya ce cikin dake jikinta ba ya so, shi ya sa ya ce ta zubar amma ta yi taurin kai. To saboda haka ya bar mata cikin kar wata rana a danganta shi da cikin har abada"
"Wannan ne kuma bai isa ba ƙarya yake yi. Tunda har ya amince da cikin na shi ne to ko ya mutu ne sai an danganta shi da wannan cikin."
Alhaji Sheriff ya faɗa cikin fushi mai tsanani saboda ya fahimci Habibu ya raina musu wayau yana wasa da hankalin su.
"Ai ba a dole Alhaji tun da har ya ce ba ya so to ba wanda zai masa dole akan haka. Tunda har da kansa ya yi ikirarin cewa har abada kar mu danganta shi da cikin jikin Ummu, to nima Alhaji Hadi Baaba a matsayina na mahaifin Ummu Salma na yi alƙawarin ko bayan raina kar Habibu ya kusanto ni ko ya kusanto Ummu Salma ko abin da za ta haifa nan gaba kamar yadda ya haramta ma kansa dangantakar shi da cikin jikinta nima na haramta masa ya danganta kan shi da Ummu Salma ballanta cikin dake jikinta, ni da man uba na ke ga Ummu Salma har abada sannan zan sake zama uban abin da za ta haifa. Har abada bana son na sake ganin fuskar Habibu."
Baffa ya gama faɗa yana jin zuciyarsa na tsalle saboda ɓacin rai da baƙin ciki.
Alhaji Sheriff daga can bangaren ya ruɗe yana ƙoƙarin magana amma tuni Baffa ya katse wayarsa ya bar shi tsaye cikin mutuwar jiki da nadama mai yawa.
"Alhaji me ya faru ne?
Gwaggo ta tambaya cikin tashin hankali.
"Habibu ne ya saki matarsa saki uku."
Ya ba ta amsa kai tsaye ai sai ta saka salati tana ɗauka tana direwa.
"Wai ko Habibu ya fara shaye-Shaye ne?
"Babu abin da yake sha, kawai yaron ba shi da mutumci ne."
Ya faɗa yana ta neman lambar Habibu amma sai dai ta yi ta ɗif ɗif ba ta shiga.
Mahaifin Habibu na kwance yana jin duk abin da ke faruwa ba mgana amma hawaye sun taru a idanuwansa har suna kwaranya ta gefe da gefen idanuwansa.
"Uhm wallahi na yi nadamar shiga maganar auren Habibu. Ba ki ji kunyar da na ji ba, yau na ji kunyar Uba, nima fa uba ne ya zan ji in aka yi ma ƴata abin da Habib ya yi ma ta su ƴar?
Ya faɗa cikin bayyana takaicinsa lokaci ɗaya yana saka wayarsa cikin aljihun rigansa.
"Bai kyauta ba, sam ba daɗi kai innalillahi ga shi saki uku ne ballanta a gyara lamarin."
"Ai ko saki ɗaya ne ni da kaina zan ba ma mahaifinta shawaran kar ya mai da ma Habibu ita. Ballanta ya cika gudirinsa tunda da man ya ce ba sonta yake yi ba jikinta ya aura kuma ya gama mora shi ya sa ya sake ta."
"Eyye."
Gwaggo ta faɗa tana zare ido cikin mamakin Habibu.
"Haka mahaifinta ya ce ya rubuta a cikin takardan sakin. Sannan ya ƙara da cewa ba ya son cikin jikinta. Su kuma sun ce tunda ba ya so to su sun karɓa amma ya sani har abada ba shi da hurumin sake danganta kan shi da abin da ke cikin yarinyar."
"Ba za a yi haka ba Alhaji."
Gwaggo ta faɗa har ta fara hawaye.
"An ma yi. Domin hukuncin ya yi mini daidai ko ni ne a matsayin su wallahi tallahi abin da zan yi kenan."
"Alhaji k.."
"Ba sai kin roke ni ba, ai magana ta kare Aina'u Habibu ya fara komai kuma ya ƙarƙare komai. Saƙon da mahaifinta ya bani ne na sanar miki, in ya zo gidan ki isar masa."
Yana gama faɗin haka ya saɓa babbar rigansa zai fice daga ɗakin.
"Alhaji ka tsaya ka ji don Allah.'
"Har abada in dai maganar Habibu ne na fita daga cikin ta, amma ba wai ina nufin na fita daga sha'anin ɗan'uwa na ba ne, ba Habibu ne ya haɗamu ba. Ubangiji ne ya kawo mu duniya a mahaifa ɗaya. Zan shiga sha'anin duka yaran gidan amma ban da Habibu ai ya isa kan shi saboda haka ya je ya yi rayuwarsa Allah ya ba da sa'a."
Yana gama faɗin haka ya saka takalminsa ya bar gidan ya bar Gwaggo na hawaye. Haka ma mahaifin shi ke kuka daga in da yake kwance, an ya Habib zai ga daidai a rayuwasa kuwa?
***
*ZONE 3.*
2:30PM.
Har zuwa lokacin su Ummin ikki na gidan ba su tafi ba, ita Baɗɗo tana tare da Ummu a ɗayan bedroom ɗin dake kusa da na Ammah nan aka sanya mata kayanta. Daman kuma nan ne ɗakin da ta yi ƴanmatancinta kafin ta yi aure, komai yana nan Ammah ba ta kauda shi ba ko baƙi ta yi ba ta cika sauke su anan ba duk wasu littafan makarantan Ummu Salma da tarkacenta duk suna ɗakin Ammah ba ta kauda su ba. Sai ga shi Ummu Salma ta sake dawowa cikin shi a karo na biyu.
Ammah kuma suna tare da Ummin ikki tana ta ɗan jan ta da magana saboda ta kwantar mata da hankali, duk da tana nuna mata ba komai. Baffa kuma tun da ya gama waya da Alhaji Sheriff ya shige ɗakin sa Hamma Abdullahi ya bi shi ya ɗan jima a ciki kafin ya fito ya yi musu sallama ya tafi gidan shi. Tun kuma daga lokacin Baffa bai sake fitowa ba sai da zai je sallan azahar.
Ammah kuma aikinta ta fita tana yi kamar ma ba ta damu ba, ba wanda ma ya tsaya bi ta kan ba ta damu ba domin an san ta damun. Aminan junan tare suka share gidan suka yi girki shinkafa da wake jallop mai allayahu Ammah ta kai ma Baffa na shi amma ya ce mata ba zai iya ci yanzu ba. Na su Ummu ma yadda ta shiga da shi ciki haka ta koma ta gan shi daga Ummu har Baɗɗon ba su taɓa ba.
Ummu Salma na zaune a in da ta yi salla a saman darduman tana nan dai a yadda take. Ba ta magana sai dai kallon waje ɗaya kawai tunda suka zo ko tari ba ta yi ba. Baɗɗo ma ta kasa iya shan ko ruwa ne tana zaune a gefen gado ta yi tagumi kawai tana kallon Ummu cikin tausayawa. Ummin ikki ta zo tana ta yi ma Baɗɗo fada akan cewa ta matsa ma Ummu ta ci abinci.
"Ummi tun ɗazu na ke yi mata mgana ba ta kalle ni ba."
Baɗɗo ta faɗa idanuwanta na tara ƙwalla.
"Ummu daure ki ci abinci kin ji ko? Kar ki manta ba ke kaɗai ba ne ko domin abin da ke cikin ki."
Ummu Salma ba ta ko kalleta ba sannan ba ta motsa ba,har tea Ummin ikki ta haɗo mata mai zafi tana ta lallashinta da nasihan cewa ta sha ruwan zafi ya ɗan jiƙa mata maƙoshi kafin ta ci abinci amma kamar da dutse ake magana.
"Haba Ummu Salma kar ki ja da hukuncin Allah, Ubangiji yana sane dake, ki yi haƙuri ki sha ruwan zafin nan kin ji ko?
Har bakinta ta kai mata kofin amma ta kauda kai ba ta yi magana ba.
"Me ya sa kike haka ne Ummu? Ba fa ƙarshen rayuwarki ba ne ya zo domin Habibu ya sake ki. Ki yi haƙuri ki yi hakuri ki daure ko domin abin da ke cikin ki Ummu Salma ki sha wani abun don Allah."
Sai a lokacin ta kalli Ummin ikki da luhu luhun idanuwanta.
Ƙarshen rayuwanta ne ya zo mana. Me ya rage mata? Habib ya sake ta me kuma ya yi mata sauran ita Ummu Salma a wannan duniyan babu shi.
Duk magiya da lallashin Ummin ikki bai saka Ummu ta kurɓi ko ruwan tea ɗin ba Ammah ce da ke ƙofar ɗakin tun ɗazu tana jin duk magiyan da Ummin ke yi mata amma ba ta karɓa ta sha ba.
"Aminiya ƙyale ta. ."
Haka kawai ta faɗa ta juya ta koma cikin ɗakin ta. In ta ce Habibu zai ga daidai a rayuwarsa ta yi ƙarya tana so Allah ya wulaƙanta rayuwarsa ya farraƙa jin daɗinsa kamar yadda ya farraƙa jin daɗin ɗiyarta mace ƙwara ɗaya da Allah ya bata, ji Ummu Salma cikin kwana ɗaya ta fita kammaninta da Hayyacinta. Ita ko a matsayinta na uwa wani fata ko addu'a za ta yi ma Habibu face na Allah ya ɗanɗana masa ƙwatanƙwacin irin zafi da raɗaɗin da Ummu Salma ta ɗanɗana a dalilin shi, Allah ya haɗa shi da firgici da baƙin ciki irin kwatanƙwacin yadda ya haifar musu tare da duk wani masoyan su.
Har Ummin ikki ta shigo ta zauna kusa da ita ba ta sani ba sai da ta yi magana.
"Ta ƙi shan ruwan zafin abincin ma haka."
"Barta in ta gaji za ta sha ai ba za ta zauna ta mutu ba."
Ammah ta faɗa tana cije bakinta saboda ɓacin rai.
"Aa Aminiya ko saboda abin da ke tare da ita ya kamata ta ci wani abu. Yanzu haka tun jiya rabon ta da wani abu."
"To ba kin faɗa mata ba ta ji ba Aminiya? Ai tafi ki sanin ba ta ita kaɗai ba ce. "
Ammah ta sake faɗa har tana girgiza ƙafa, ji take yi kamar ta rufe Ummu da duƙa ko ta huce baƙin cikin ta. Akan wannan ɗan iskan yaron da ya tozarta ta koma haka? Kawai ta yi shuru ne ba ta so ta yi magana ace ba ta tausayin Ummu. Ita a yadda take jin zuciyarta bai kamata Ummu ta sake kuka saboda Habib ya sake ta ba. Godiya ya kamata ta yi ma Ubangijinta domin bai kaddara mata rabon wahala anan gaba ba. Tunda Baffa ya karanta takardan sakin nan da kalaman dake ciki ta ji nan duniya ba wanda ta tsana sama da Habibu ta yi masa addu'an bala'ai kala kala a cikin zuciyarta da fatan ya tozarta kamar yadda ya tozarta su.
"Aminiya sai fa haƙuri yanzu sabon reno ne za ki yi Ummu kafin ta warware har ta cire abin a cikin zuciyarta "
Ummin ikki ta faɗa sanin halin Aminiyarta ta, ba ta ɗaukan reni da ɓata lokaci akan abu ko kaɗan.
"Aminiya."
Ammah ta kirata ta amsa tana kallon ta.
"Ba zan lalace akan lallashin Ummu Salma ba. Ita ba yarinya ba ce ta san illan yunwa da abin da damuwa ke haifarma gangan jikin ɗan adam."
"Ba za a yi haka ba Aminiya."
Ummin ikki ta faɗa da sauri, kafin ta ɗora da maganarta Ammah ta miƙe da sauri za ta bar ɗakin Ummin ikki ta riƙo hannunta amma taƙi juyowa saboda kuka take yi ba ta so ta ganta tana kuka.
"Ki yi kuka Aminiya ko za ki samu sauƙi na fi kowa sanin ki na san yadda zuciyarki ke ciki a halin yanzu."
Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta isa ga Ammah wacce tana ganin ta sai ta juyo ta ɗora kafaɗanta a saman na Ummin ikki ta fashe da kuka.
"Me ya sa za ta damu don ya sake ta? Da man bai dace da rayuwarta ba. Tana so ta kashe kanta saboda wanda bai san darajan ta ba? Ko so take yi wani abu ya same ta muma zullumi ya kashe mu a tsaye Aminiya?
Amma take faɗa cikin kuka Ummin ikki na bubbuga bayanta alamun lallashi sai da ta yi kukan ta fidda hawaye sannan ta ɗago ta share hawayenta.
"Ki kalli yadda Ummu ta koma Aminiya? In ta cigaba da zama a haka wata cutar za ta kama ta."
Ammah ta faɗa cikin rawan murya.
"Lallashi ba zai sa ta ji ba. Ki yi mata faɗa ne ki zare mata ido in ba haka ba za ta cutar da kanta sannan ta cutar da abin da ke cikin ta."
"Zan yi mata, kar ki damu ba abin da zai same ta "
Ta faɗa tana kallon Ammah da duk ta yi zuru zuru a yini ɗaya kawai ta faɗa, lamarin nan ya dake ta sosai.
"Haka na riƙa yi ma Fatima a wancan lokacin. Tunda duk lallashin Baffa ba ta ji, amma da ta ga na buɗe mata wuta na fara masifa za ta yi shuru ta ɗau abinci tana ci."
Ta faɗa tana kallon Ummin ikki, kai ta gyaɗa mata kafin ta ce" Za ta warware sai a hankali Aminiya."
Kafin Ammah ta ce wani abu suka ji muryam Saddam ya shigo cikin ƙaraji yana kiran sunan Amma.
"Ammah"
"Amma kina ina ne?
Da sauri Amma da Ummin ikki suka fito falo, ita Ammah ta ma manta da yana gidan kwata-kwata.
"Saddam? Da man kana gidan?
Ummin ikki ta faɗa cikin mamakin ganinsa.
Bai ko damu da tambayanta ba ya kalle su ita da Ammah yadda suka ƙura masa ido da yanayin Amnma kawai ya sa ya samu tabbacin abin da Hamma Jibo ya faɗa.
"Da gaske ne kenan?
Ya tambayana yana kallon su.
"Me fa?
In ji Ammah tana kallon shi.
"Yanzu na buɗe data kawai sai ga saƙon Hamma Jibo a Family group namu wai mijin Ummu Salma ya sake ta saki uku."
Ammah ta wucesa zuwa kan kujera ta zauna ba tare da ta yi magana ba.
"Da gaske ne Saddam kai dai bari "
Ummin ikki ta faɗa cikin sanyin murya.
Zaro ido ya yi kafin ya ce" Da gaske ne? To ni duk ina ina hakan ta faru ban sani ba, kuma yau ne abin ya faru?
Ya tambaya cikin ɗimuwa da mamaki
"E yau ne da asuba nan."
Ummin ikki ta faɗa kafin ta cigaba da faɗin" To kai kana ina ne duk ba ka ji zuwan mu ba."?
"Ummi ina can cikin ɗaki mun gama exams ina biyan bashin barci, tashi na kenan na yi salla sai na ga saƙo a group ina shiga kawai na ga Hamma Jibo na faɗin wai mijin Ummu Salma ya sake ta "
Ya gama faɗa yana sake duba wayarsa.
Abin da ma yasa ya saurin duba saƙon a group ɗin sai a yi wata uku ba wanda ya yi ko sallama a ciki kwata-kwata group ɗin ba ya active kuma duk suna ciki hatta da Hamma Lamiɗo, kuma shi da kan shi ya buɗe group ɗin shekaru biyu da suka gabata ya sanya masa suna AMMAH AND BAFFA HAPPINESS. su takwas ɗin su cur ƴa'ƴan Ammah da Baffa suna ciki da Hamma Lamiɗo cikon na tara domin ba wanda ya isa ya cire shi a cikin jerin ƴa'yan Amma da Baffa.
Ba su fita ba amma ba mai magana farko farkon ma buɗewa Saddam na raya group ɗin da ɗan turo jumma'at mubarak, ko irin short-short vedio haka na ban dariya kawai ranar Hamma Kabiru ya fito ya yi Viocenote na kusan sakwan hamsin a ciki yana yi ma Saddam faɗa da jan kunnen cewa daman ya buɗe group ɗin ne ya tara su domin ya riƙa turo musu Vedios ɗin ban dariya! Hala yara ne su irin shi ko marasa aikin yi kamarsa! To in dai abin da ya sa ya buɗe group ɗin kenan gwara ya gaggauta cire su ya rufe group ɗin su suna da abin yi.
Wannan maganar ta ɗan muzanta Saddam ya ji zafi, tun ballanta yadda Ummu Salma ta kira shi tana masa dariya da ya so ya cire kowa ya rufe group ɗin ne amma sai bai yi haka ba da Hamma Jibo ya kira shi ya lallasheshi da cewa ya san halin Hamma Kabiru da gwasala ya ƙyale shi kawai. Dalilin da ya sa bai rufe ba kenan amma ya kama kan shi, bai sake tura komai a ciki ba, ko addu'an jumma'at mubarak ya daina turawa kuma ba wanda ya yi cigiyarsa tun daga ranar ya san ba su damu da turowan nashi da rashin shi ba, tun daga lokacin sai group ɗin ya yi wata sama da uku ko sallama ba wanda ya yi wasu ma mantawa suke yi da shi, akwai ma waɗanda ba su taɓa magana ba irin su Hamma Lamiɗo, shi wataƙila ma ba lalle ya san an buɗe ba mutumin da sai ka yi masa mgana a chart sai ya yi sama da sati biyu yake dubawa ba kuma lalle ne in ya duba ya baka amsa a lokacin ba sai a lokacin da ya samu dama.
Hamma Jibo ne daman ko Hamma Mustapha kan ɗan sanar da wani ƙaruwa ko jaje in ya samu ɗaya daga cikin su, suma ɗin suna dai yi ne kawai saƙon da sai su tura ya yi sama da sati ba wanda ya nuna ma ya gani ballanta ya tanka alhalin akwai waɗanda suka gani ɗin amma su yi magana suna ganin ɓata lokaci ne.
Shi ya sa yau yana ganin saƙon ya shiga da sauri sai ya ciro karo da labarin da ya razana shi.
"To wai me ta yi masa ya yi mata wannan sakin a lokaci ɗaya?
Ya faɗa saboda mamaki shi abin yake ba shi.
Ummin ikki ce ke bashi labarin yadda lamarin ya fara har zuwa yau Ammah ba ta yi maagaana.
"Kai innalillahi."
Ya faɗa yana mai zaro ido.
"Wallahi ai yaron nan ya gama cutar mu."
Hamma Saddam ya yi shuru kafin ya ce" Ni gabaɗaya ma na rasa abin cewa. Kamar ba zaai aikata ba sumu sumu da shi munafuki.".
Shuru ba wanda ya tanka shi.
"To yanzu ina ita Ummun?
"Tana cikin ɗakin ta."
Ummin ikki ta faɗa tana nuna masa ɗakin da hannunta da sauri ya wuce ya shiga a bakin kofa ya tsaya yana kallon Ummu na zaune kawai tana kallon waje ɗaya.
Baɗɗo na gefenta ta yi tagumi ɗakin shuru ba ka jin motsin kowa kamar an yi mutuwa.
Sai jikinsa ya sake yin sanyi jiki a sanyaye ya ƙariso ɗakin.
"Baɗɗo."
Ya kira sunan ta cikin sanyin murya. Kallon shi ta yi kafin ta amsa itama a sanyaye.
"Naam Hamma Saddam yanzu ka dawo?
"Tun jiya fa na dawo"
Ya bata amsa yana kallon Ummu da ya ga ba ta ko motsi
"Ta ƙame ne?
Ya faɗa yana ɗan ware ido.
"Ko ta suma ne a zaune?
Ya sake faɗa yana ɗan yawo da hannunsa a wajen idanuwanta sai ya ga ta ɗan kifta ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Ummu sorry amma don Allah ki daina damuwa kin ji ko?
Shege mara mutumci kawai "
Ya faɗa yana kallon ta, kallon shi ta yi da luhu luhun idanuwanta na wani lokaci kafin ta ɗauke ba tare da ta yi magana ba
"Ummu"
Shuru ba ta amsa shi ba ya saka hannu ya dafa kafaɗanta nan ma ba ta sake kallon shi ba, Baɗɗo ya kalla cikin mamaki da sauri ta ce" Tunda muka je muka ɗaukota haka take ba ta yi kuma magana ba."
Hamma Saddam ya ware ido kafin ya ce" Kar fa shock ya kamata zuciyarta ta buga ba a sani ba."
Baɗɗo ta yi shuru tana kallon shi, hannun Ummu ya kama ya riƙe yana kallon ta.
"Ke Ummu kina jina?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana saka ɗayan hannunsa ya ɗan taɓa kumatunta sai ta runtse idanuwanta na wani lokaci kafin ta buɗe sai ga hawaye sharr, ajiyar zuciya ya saki kafin ya ce" Gwara dai a dinga ganin alamu zuciyarta na tafiya."
Ya faɗa yana share mata hawaye da gefen jallabiyan jikinsa
"Ki daina kuka kin ji, a matsayina na yayanki sai na rama miki abin da ya yi miki."
Yake faɗa yana sake share mata hawaye.
"Shi ne zai ce ba ya son ki? Kaf duniyan nan akwai wacce ta kai ki kyau ne da zati?
Sai da ta kalle shi, hawaye suka sake kwaranyo mata. Duk da kyan da zatin shi Habib ba shi yake so ba jikinta yake so kuma tunda ya gama amfana shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda kamar yadda ya faɗa sannan ya jaddada mata.
"Wallahi sai mun rama miki. Mugu kawai."
Ya sake faɗa yana kallon ta yana yi ne domin ta ji sanyi a zuciyarta bai san a lokacin ma jin wani irin zafi take yi yana ta so mata ba ta so ana zagin shi domin har yanzu tana jin soyayyarsa a cikin zuciyarta
"Ta ci abinci?
Ya faɗa yana kallon kulan abincin dake gefe.
Da kai Baɗɗo ta amsa masa da Aa ba ta ci ba
"To ya za a yi ta zauna da yunwa"
Ya faɗa yana jawo abincin.
"Ta ƙi ci Ummi har tea ta haɗo mata ta zauna tana lallashin ta amma ba ta karɓa ba. Ga shi kuma ina jin tun jiya ba ta ci komai ba."
Ta faɗa hawaye suna kawo mata, Hamma Saddam ya kalle ta kafin ya ce" To ke ma kina kuka ita wa zai lallashe ta?
"Wallahi ina tausayin Ummu. Ina tausayin halin da za ta shiga."
Baɗɗo ta faɗa tana kecewa da kuka, shi ma ba domin yana namiji da shima ya kece da kukan tausayin Ummu amma shi namiji ne ya kamata ya daure.
"To ki yi haƙuri ki daina kuka. Ke za ki zama ƙarfin gwiwanta."
Shuru ta yi tana cigaba da kukanta mai sauti yayin da na Ummu sai dai kawai zuɓar ƙwalla.
"Ummu ya kamata ki ci wani abu."
Ya faɗa yana kallon ta, sai ta kalle shi amma ba ta yi magana ba.
"In haɗo miki tea ɗin?
Shuru ta yi masa amma tana kallon shi.
"Kina da juna biyu Ummu kar wani abu ya same ki"
Ya faɗa yana sake kallon ta.
Sai ta lumshe ido hawaye na kwanranyo mata.
"Na kawo miki tea ɗin?
Karo na farko ta girgiza masa kai.
"Me ya sa Ummu? Za ki zauna ki mutu da yunwa ne. Mai faruwa fa ta faru sai dai mu yi haƙuri kawai.".
Ya faɗa cikin sigan lallashi duk dai ta samu ta jiƙa maƙoshin ta.
"Na kawo miki?
Ya faɗa cikin sanyin murya.
Sai ta sake girgiza masa kai a karo na biyu.
"Haba mana Ummu."
Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
"Bari na je na haɗo miki, ki sha ko kaɗan ne."
Yana shirin barin ɗakin a karon farko Ummu ta yi magana.
"Ba z.. zan sha ba."
Ta faɗa cikin dashewar murya.
"Ko kaɗan ki sha Ummu"
Baɗɗo ta faɗa tana kallon ta.
"E ko kaɗan kin ji?
Hamma Saddam ya sake faɗa domin a yadda bakin ta ya bushe ya tabbata ma cikin ta a bushe yake.
"Na ce ba zan sha ba. Ba zan sha ba don Allah ku ƙyale ni."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kecewa da wani irin kukan, muryanta ma baya fita sosai.
"Zan mutu, ina ji kamar zan mutu zuciyata ke zafi ciwo take yi.."
Haka ta faɗa tana nuna saitin zuciyarta cikin kuka.
"Zuciyata na zafi, ji nake yi kamar na kashe kaina."
Ta faɗa cikin kuka kafin ta fara buga saitin zuciyanta da hannu tana wani irin kuka da gudu Baɗɗo da Hamma Saddam suka yi kanta suna riƙe ta amma kamar an ƙara mata karfi tana fizge kanta tana kuka tana faɗin su bari ta kashe kanta, hayaniyarsu ya kawo su Ammah ɗakin ganin abin da ke faruwa ya sa ke raunana Ummin ikki ta fara kuka ita kuma Ammah ta fita tsakar gida da sauri domin ta kira Baffa sai suka ci karo da juna
"Me ke faruwa ne! Na ji kuka?
Ya faɗa cikin tashin hankali.
"Ummu ce ke kuka tana faɗin za ta kashe kanta."
Ammah ta faɗa cikin rawan murya.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ya faɗa da gudu yana faɗawa falon Ammah. Daidai lokacin da Hamma Abdulrrahman ya shigo tsakar gidan da sallama. Lokacin da ya ga saƙon Hamma Jibo fitowar shi kenan daga wata sharia da ya jagoranta. Shi da man ya san sai an zo wannan matakin.
"Ammah"
Ya kira sunanta ganin ta cikin wani yanayi.
Tana ganin shi ta nufe shi da sauri.
"Abdulrrahman."
"Ammah"
Ya amsa yana kallon ta cikin mamakin ganin yanayin ta.
"Ummu Salma ce."
Ido kawai ya sakar mata yana kallon ta.
"Tana ciki tana kuka wai za ta kashe kan ta."
"Za ta kashe kanta?
Ya maimaita cikin mamaki.
Sai Ammah ta gyaɗa masa kai, goshinta har yana tara zufa saboda damuwa da firgici.
"Mu je na ganta. In ta fasa kashe kanta saboda wani banza ta ci ubanta."
Ya faɗa yana yin gaba zuwa cikin falon Ammah cikin fushi da fusata. Saboda wani banza sakarai ne za ta zo tana yi ma mutane sakarci in ta fasa kashe kanta ta ci bura uban ta in ji shi Abdulrrahman Hadi Baba, in ba ta kashe kanta ba ta ci uban ta.
*Janafty*