BAYAN AURE

10

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 10.

Sarac Stars R Pen...✍️


Wajen ƙarfe takwas saura na safe Hamid ya zo ɗakin Hamida ya turo ƙofa ya shigo da sallama, wanda sallamarsa ne ya farkad da ita dan ba tada nauyin bacci, cikin jin kunyarsa ta tashi ta zauna kanta a sunkuye ta gaishe shi, ya amsa yana cewa. 

Amarya 'yar shagali da fatan babu wata matsala ko.? 

Eh babu Alhamdulillahi. 

Yauwa idan kin karya sai ki sha paracetamol zaki ji daɗi a jikin ki sosai. Amma kin yi wanka da ruwa mai zafi ko.

Eh nayi.

Yauwa nasan kin samu ƙarfi a jikinki.

Ya ƙare maganar yana tsura mata ido, ita kuma ta gyaɗa masa kai alamar eh, sai ya ɗan ja fasali kamar mai jin shakkar abunda zai furta yace. 

Emmm ko zaki iya shiga kitchen kiyi mana breakfast.? Ko da yake ai nasan Amaryar tawa jaruma ce nima na shaida haka. 

Ya ƙare maganar cike da zaulaya, ita kuma ta sunne kai cikin jin kunya tana murmushi, sai ya zauna gefen gadon yana mai ƙara sausauta muryarsa.

Ina son fara cin girkin matata naji ya yanayin hannunta yake, duk da ina tunanin kin iya, dan haka muje na taya ki haɗa mana breakfast, Kuma kin ga su Afrah zasu tafi hadda ƙarfe tara, to zaki haɗa musu abunda zasu tafi da shi makaranta, kuma naga time ya tafi amma ko doya da kwai sai kiyi musu.

To tace masa cikin farin ciki domin taji daɗin yadda yayi mata magana cikin sigar rarrashi, Kuma ita abun alfaharinta ne ace mijinta yana ɗokin yaci girkinta, dan haka dole zata baje basirarta wajen faranta masa, balle yau da ya zama rana ta farko da zata fara girki a gidan mijinta, sai ta yunƙura zata sauko amma sai taji zafi daga ƙasanta, ta ɗan cije leɓenta tare da nuna dauriya ta tsaya akan ƙafafunta. Hafiz ya miƙe ya buɗe mata ƙofa yana nuna mata hanya. 

Takawarki lafiya yau ke ce zaki ja ragamar abincin gidan nan, In Sha Allah nasan ba zaki bani kunya ba. 

Ya ƙare maganar cikin murmushi, itama murmushi tayi sosai har haƙoranta suna bayyana, lamarin yayi mata daɗi dan bata zaci zasu sakar mata ragamar gidan ba daga zuwanta, amma kuma tunawa data yi da tarban da Laila tayi mata jiya sai ta ƙara samun nutsuwa da tunanin komai yana tafiya akan dai-dai. Haka yayi mata jagora zuwa kitchen zuciyarta cike da tunanin itama yanzu ta zama cikakkiyar matar gida, sai wani farin ciki ya lulluɓeta, duk wani nauyi da jikinta yayi ya fara saki ta aro jarumta ta fara aikin girki dan kawai ta burge Hafiz, shi kuma sai ya shiga nuna mata kayan amfani, dangin kayan wuta da yadda zata riƙa amfani da su, hatta gas sai da ya gwada mata yadda zata kunna dan bata taɓa amfani da cooker gas ba, ya buɗe mata store ɗinsu taga kayan abinci iya kallon mutum komai akwai a ciki, sai ta ɗauko doya babba guda ɗaya ta fito ta fara ferewa, data gama ta ɗaura a wuta tare da saka masa curry, maggi da gishiri, Hafiz yana tsaye yana kallonta, shi aikinsa sai dai ya miƙa mata abu in tana buƙata. A hankali take aikin har ta haɗa doya da kwai ta yi miyar albasa na yaran, ta zuba musu a Lunchbox ɗinsu sannan ta dama musu custard wanda zasu karya da shi, Hafiz kuma ta dama masa kunun tsamiya tare da ita kanta dan tace shi zata sha, sai ta dafa ruwan tea da kayan kamshi tasa a flask na Laila, ta kuma sake soya irish da kwai wanda zasu karya da shi har da Laila, Hafiz ya fitar da abincin zuwa dinning ya shiryasu, sai ta sakawa yaran drink da ruwa a Lunchbox ɗinsu da biscuit data gani a store kafin ta fito da su falon ta aje a center table, har tayi hanyar ɗakin ta dan ta watsa ruwa sai ta tsinkayi muryar Hafiz yana cewa.

Hamida zoki ɗiba naki kije ki karya karya huce. 

Da wanka zanyi kafin na karya. 

Ta bashi amsa a gajarce, sai ya rausayar da kai yana murmushi. 

Amma da kin gama aikinki gabaɗaya, kinga in mun gama zaki yi wanke-wanke da gyaran gidan, nasan zaki iya ai tunda gashi kin yi mana girki. 

Ya ƙare maganar da murmushi a fuskarsa, Hamida tayi jim ta kasa bashi amsa dan kanta ya kulle, kenan bayan abincin da ta yi itace zata yi gyaran gida. 

Koda yake ai nice da miji dole ni ce zanyi tunda basu da mai aiki. 

Tayi maganar a cikin ranta, kamar Hafiz ya karanceta sai yace. 

Idan ba zaki iya aikin ba ki barshi, aima kin yi ƙoƙari, dama kawai bana so gidan namu ya zama babu gyara kamar babu matan aure a ciki, kinga ita Laila tana sama to ita zata kula da abunda ya shafi can ke kuma kina ƙasa, kin ga alhakin kula da nan yana wuyanki, amma zan yi miki uzuri duba da baƙuwa ce ke ga shi kuma jiya na tara miki gajiya. 

Ya ƙare maganar yana kanne mata ido ɗaya, wanda ya sata sunne kai ƙasa tana ƙunshe bakinta cikin murmushi, suna a haka Khalil ya sauko yana cewa. 

Barka da Safiya Dady. 

Yauwa harka shirya.? 

Umm Khalil yace kafin ya isa dinning ya fara karyawa da custard dan dama kafin Hafiz ya sauko wajen Hamida sai da ya tashesu ya tambayi me suke so a girka musu, kafin yaje ya sameta da zancen girki, Hafiz ya isa dinning ɗin ya ja kujera yana cewa. 

Khalil baka ga Antynku bane. 

Wace kuma Anty.?

Khalil ya faɗa yana ɗage gira da taɓe fuska. Hafiz yace cikin murmushi. 

Ba na gaya muku zan auro muku Anty ba, itace ta yi mana abinci yau, ya kaji custard ɗin.?

Hmmm ba laifi yayi daɗi. Hey anty sannu.

Khalil ya faɗa yana ɗaga mata hannu, Hamida ta amsa da yauwa ta samu Cushing ta zauna dan ƙafarta ta fara gajiya da tsayuwa, daga haka ta mayar da hankalinta kan tv har Afrah ta fito cikin shirin uniform, ta ga Hamida amma bata kula ta ba ta samu guri ta zauna a dinning, itama sai da Hafiz yasa ta gaishe da Hamida, ganin sun fara karyawa har Hafiz ɗin sai Hamida ta miƙe ta isa gurin da niyyar ta zauna itama ta karya, duk da Hafiz bai gayyace ta ba amma tasan itama tana ɗaya daga cikin alhalin gidan a yanzu, tana shirin zama Hafiz ya dakatar da ita. 

Ki ɗiba naki ki je ɗaki kici, ina ga zaki fi sakewa. 

To, tace masa a gajarce tana mamakin ba zai barta ta karya da su ba, sai ta ɗiba komai iya yadda zata ci ta koma kitchen ta ɗauko wannan farantin na jiya da aka ɗaura mata abinci akai ta dawo, ta saka abunda ta zuba ta wuce zuwa ɗakinta cike da mamakin abunda Hafiz ya yi, haka ta ture tunanin komai ta karya dan ba zata haɗa yunwa da komai ba bata wasa da cikinta. Bayan ta kammala ta shiga toilet ta yi wanka tana shirin fitowa taji Hafiz ya shigo mata dan ya ambaci sunanta, sai da ta kimtsa kafin ta fito, ya dubeta yana wannan murmushi. 

Kin manta nace karki yi wanka sai kin gama aiki, ko da yake zaki ƙara jin daɗin jikinki, dama magani na kawo miki ki sha, ni zan fita karki yi abincin rana, na dare kuma zan kira ki na faɗa miki abunda zaki girka. 

To a dawo lafiya. 

Hamida ta faɗa cikin sanyin murya, ya amsa da to kafin ya juya zai fita sai kuma ya tsaya yana juyowa tare da wannan murmushin da ya fara sabar mata da shi. 

Na manta idan kin shirya kije ki gaishe da Laila zata ji daɗi idan kin girmamata, kuma zaku samu fahimtar juna a dalilin haka, sannan ɗazu karki ga na hana ki zama a dinning, kawai ina guje miki cin fuska daga Laila ce saboda bani na siya dinning ɗin ba itace tasa kuɗinta ta siya, kinga ko zaki fara amfani da shi dole sai ta nuna amincewarta. 

Haba Zuciyata ai babu matsala kuma ban kawo ma tunanin komai ba, ka manta ni baƙuwa ce dole sai a hankali zan fahimci komai.

Good girl shiyasa nake sonki saboda kina da saurin fahimta. 

Ya ƙare maganar cikin jinjina mata babbar yatsa kafin ya juya ya fita ita kuma ta rakashi da murmushi, har ga Allah ta gamsu da abunda ya faɗa mata, sai ta cire komai a ranta ta ɗaura niyyar yi masa duk abunda zai faranta masa domin da zuciya ɗaya ta aure shi take kuma fatan zama da shi.

A ɓangaren Hafiz kuwa abunda ya faɗa mata shi ne kaɗai hanyar da zai bi cikin sauƙi ya ɓatar da tunanin Hamida, domin so yake ya kauce duk abunda zai ɓata ran Laila akan sharuɗɗan data kafa masa na zaman Hamida a gidan tun kafin ya aure ta, a ciki tace bata yarda su zauna da ita a guri ɗaya ba suci abinci dan bata karɓeta a matsayin family ɗinta ba, kuma shi kansa ɗazun abunda yayi wa Hamida bai ji daɗi ba dan yaga sauyawar fuskarta akan dakatar da ita zama a dinning ɗin, shiyasa yayi wannan tunanin ya sanar da ita abunda ya faɗa mata dan wanke kansa ba tare da ta zargi Laila ba, sannan batun taje ta gaishe da Laila shima yana cikin dokar data shimfiɗa masa akan dole ta bita tayi mata biyayya, shi kuma ya yarda ya amince da duk wacce zai kawo dole sai ta kasance mai bin Laila sau da ƙafa, shiyasa yake yin amfani da wannan murmushin wanda a bayansa na yaƙene ba har zuci ba, yana amfani da shi ne wajen karya zuciyar Hamida ta yadda zata yi saurin amincewa da duk abunda zai faɗa mata. Koda ya fito daga ɗakin Hamida sama ya hau ya sanar da Laila zai wuce kuma Hamida ta gama breakfast ta sauko ta karya, ya kuma tabbatar mata da duk doka da sharuɗɗan data gindaya yana tafiya akan yanda take so, kallonsa kawai tayi ta taɓe baki tace. 

Ba yanzu ba, ka bari muga yadda tafiyar zai ɗaure. Anjima kayi min oder ɗin shawarma shi zanci da rana, abincin dare kuma zan faɗa maka abunda nake so matarka ta girka mana. 

Ok ba matsala zata girka abunda kike so, Nima zata yi min nawa, sannan zata yi wa yara abunda suke so Hamida tanada sauƙin kai, amma in ba damuwa zan iya yin oder ɗin shawarmar har da ita.?

A'a ban yarda ba, ka sanar da ita idan tana so taci shawarma tayi a gida nan dan muna da komai na yinsa. 

Tayi maganar cikin gatsali, Hafiz ya girgiza kai yana murmushi dan yasan fushin jiya ne bata sauka ba, shi kuma zai yi duk me yuwuwa ta sauko su dawo kamar da, amma har yanzu yana akan bakansa zai iya mata komai amma bata isa ta hana shi tarawa da Hamida ba. Sai ya fice yana farin ciki dan sosai yaga alfanun aurensa da Hamida, zai huta da wulaƙancin da Laila take yi masa a shimfiɗa, sannan ya samu matar da zata yi masa komai ba tare da musu ba, kuma zai huta da yawan siyan abinci a rastuarant ya shiga adana 'yan kuɗinsa, sannan Laila zata sakar masa mara da ƙorafinta na rashin mai kula mata da gida, sai ya kunna mota ya wuce yana ƙara jin kansa a sabon ango. 

....

Hamida. 

Ta zauna ta shafa mai sai ta kuma mayar da rigar da ta cire domin bata gama aikin gidan ba, ta fesa turare kafin ta ɗauki ɗankwalin kayan ta yane kanta da shi sai ta fito ta haura sama wajen Laila dan ta gaisheta kamar yadda Hafiz ya umarce ta, koda ta hau bata shiga kai tsaye ba sai da ta tsaya ta yi sallama tare da nocking kafin ta jira na mintuna, ba jimawa Laila ta zo ta buɗe suka yi ido biyu da juna, Laila ta saki wani faɗaɗɗen murmushi. 

Aaa Amarya ina shirin na zo naji ya kwananki amma kin riga ni, sannu da zuwa, shigo ciki. 

Ta ƙare maganar tana juyawa ciki, Hamida tabi bayanta suka zauna a cushing mai fuskantar juna, Hamida ta gaisheta cikin girmamawa, Laila ta amsa fuska sake.

Ya baƙunta, sannu da aiki fa, Dadynsu ya faɗa mini kin yi mana breakfast, ke da kike baƙuwa mun fara saka ki aiki, kiyi haƙuri yau na tashi bana jin daɗi kin ga ban iya gyara gidan ba. 

Allah sarki Allah ya ƙara afuwa. Dama na zo na gaishe ki ne, bari na sauka saboda zanyi gyaran falo ne. 

Ok in ba damuwa ki haɗa mini breakfast ki hawo min dashi, sannan in ba takura ki zo nan ma ki gyara min. 

To Hamida ta faɗa kafin ta miƙe ta sauko zuwa dinning, ta haɗa wa Laila komai a babban tire kafin ta kai mata sama sannan ta tsaya ta fara gyara mata nan, Laila ta dinga janta da hira tana tambayarta makarantar da ta yi itama tana bata labarin rayuwarta na makaranta, tana yi tana dariya, sai nan da nan Hamida ta saki jiki da Laila wanda har cikin zuciyarta ta yarda da cewar Laila mutumiyar kirki ce, wancan abunda ta yi na rufe gidan da aka kawota kishi ne yasa tayi haka kuma ko wace mace zata iya yin haka matsawar tana ƙaunar mijinta. Da jan hira Laila ta saka Hamida ta gyara mata falo da ɗakunansu har da na Hafiz, daga bisani da ta gama sai ta sauko da kayan da Laila ta gama amfani na breakfast. Laila da murmushi a fuskarta ta rakata da harara ranta fes, kamar yadda Hafiz ya faɗa cewar zata fi kowa morar Hamida domin tana da sauƙin kai, to a yanzu ta shaida ta kuma yarda da maganarsa, sannan ya iya zaɓen amaryar da ta dace da zaman gidansu. 

A ɓangaren Hamida ta mayar da kayan breakfast ɗin Laila kitchen sannan ta fito ta kwashe kayan kan dinning zuwa kitchen, sai ta dawo ta fara mopping ɗin falo dan babu datti bata tsaya yin shara ba. Bayan ta gama sai ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke ta goge ko ina kafin ta fito ta koma ɗakinta, sai a lokacin gajiyar aikin data yi ya saukar mata, ta kwanta a gado rigingine tana mayar da numfashi, sauƙinta ma ta saba da yawan yin aiki a gidansu shiyasa bata galabaita sosai ba, amma kuma a cikin jikinta tana jin yayi mata ɗumi kamar zazzaɓi ke shirin kamata. 

Rahma ce.