BAYAN AURE

11

by @rahmakabir13

*BAYAN AURE*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 11.

Sarac Stars R Pen...✍️


Bacci ne mai nauyi ya ɗauke ta wanda bata farka ba sai kiran sallar azahar ne ya tashe ta saboda akwai masallaci a kusa da su, ta tashi zaune tana salati kafin daga bisani ta sauko daga gadon ta shiga bayi ta ɗauro alwala kafin ta fito ta gabatar da Sallah, bayan ta idar ta fito zuwa kitchen dan ta haɗawa kanta abunda zata ci, tana shiga ta duba sauran Irish ɗin safe taga yana nan sai ta buɗe fridge ta ɗauko sauran kazarta na jiya, ta cire tsokar daga jikin ƙashi ta haɗa miyar albasa ta zuba kazar a ciki ta bashi minti biyu a wuta kafin ta zuba wannan Irish ɗin a ciki, nan take ƙamshi ya cika kitchen ɗin ta haɗa ƙwarya ƙwaryar kayan daɗi, tun kafin ta gama ta soma haɗiyar miyau, ta rage wuta, ya ƙarasa fitar da mai yadda take so sai ta juye shi a plate ta kashe gas, sai ta ɗauki ruwa da drink ta fito zuwa ɗakinta, ta zauna dirshen akan dadduma ta soma ci tana lumshe ido tana korawa da ruwa, sai taji kamar duk Duniya ba wacce ta kai ta sa'ar aure, ta bar miyar kuka ta dawo aswaki da kaza, ita ba abunda zata ce banda ta yi wa Allah godiya da ya bata Hafiz a matsayin miji, dan haka zata yi masa komai dan faranta masa domin tasan ba zata taɓa biyansa alkhairin da ya yi mata ba daya tsamo ta daga talauci zuwa gidan alfarma, haka ta dinga saƙa zance a zuciyarta har ta gama cinyewa kafin ta fito dai-dai lokacin Laila ta sauko zata amsa saƙon shawarma, tana ganin Hamida ta saki murmushi.

Amarya wai girki kike yi ne.? naji gidan ya buɗe da ƙamshi.

Sauran Irish da kazata na jiya na ɗumama na ci yanzu.

Oho na zata ai girki ne nace ba sai kin yi abincin rana ba. Nima na saka shi yayi mini oder ɗin shawarma ne saboda bana sha'awar cin komai sai shi.

Laila ta ƙare maganar cikin dan yamutse fuska, Hamida ta ce.

Eh ya faɗa mini bazan yi girkin rana ba shiyasa na sama wa kaina abunda zanci.

Ta ƙare maganar tana wuce wa zuwa kitchen, Laila kuma ta fita waje ta amsa saƙonta ta dawo da sauri dan ta cimma Hamida, ta yi sa'a tana kitchen tana ɗauraye plate ɗin data yi amfani da shi da tukunya, bayan ta gama ta fito sai ta tadda Laila tana cin Shawarma, sai ta ce mata.

Hamida kin ko iya cin Shawarma.?

Haba anty ai idan ban iya ci ba na zama 'yar ƙauye, na iya ci saboda wasu lokuta Hafiz yasha siyo min in zai zo hira.

Tayi maganarta a iya gaskiyarta amma kuma sai Laila ta dauka kamar cin fuska tayi mata dan ranta ya so su, amma sai ta dake.

To Allah yasa kin iya haɗa shi dan gaskiya gidan nan muna son shawarma da duk abinda ya shafi snack.

Taf aiko ban iya komai ba banda cincin da fish pie, suma saboda nayi sana'ar su ne.

Cewar Hamida tana samawa kanta wajen zama a Cushing dan ta kula Laila tana son suyi hira, sai Laila tace.

Ya kamata ki iya dan muna so sosai, kamar su Samosa, meat pie, burger, pizza kai komai ma muna so da natural drink, kin san me zai faru.?

A'a anty sai kin faɗa.

Kina yin WhatsApp ai.?

Ina yi sosai ma har da su tiktok ina hawa.

Yauwa, to zan niman miki online class na girki dan ina so ki kware sosai ta yadda zaki riƙa fitar damu kunya, kinga ni ban fiye zama ba balle nace zan samu shiga kitchen kullun, shiyasa baki ji daɗi da farin cikin dana ji ba da zuwan ki, kuma kin nuna mini kin fito daga gidan tarbiyya dan ban zaci kina da sauƙin kai haka ba wlh.

Kai anty, ai kema naga kina da sauƙin kai, ba kamar wasu matan ba da basa iya ɓoye kishinsu. Kuma ina godiya dan wlh ina so na iya girki kala-kala ko dan na riƙa burge Hafiz.

Hamida ta faɗa cikin murmushi tana sunne kai, Laila ta banka mata harara, amma kuma sai ta dake tace cikin yaƙe.

Amma dai bakya kiran sunansa a gabansa ko.? Haba Hamida ya kike abu kamar ba tashin birni ba, ga irin su love, soulmate, sweetheart, ai ya dace ki kira shi da sunan soyayya, ni kinga beb ko love nake ce masa.

Laila ta ƙare maganar cikin murmushi, Hamida ma murmushi tayi tana cewa.

Nima zuciyata nake kiransa, yanzu ne dai na kira sunansa.

Haba keko wani irin zuciyata, ina kika bar my heart, ai yafi daɗi, kinga kema kin zama 'yar gayu.

Allah ko Anty.?

Hamida ta faɗa cikin guntun dariya, Laila ma ta dara tana cewa.

Eh mana so nake ki waye. Yanzu dai maganar shiga ajin girki ni zan biya miki da kuɗina zan bada number ɗinki a saka ki, sannan idan a gabana zaki kira Hafiz to gwara ki ce masa Dadyn Khalil ko Afrah.

To Anty nagode sosai Allah ya saka da alkhairi.

Haba mun zama ɗaya fa. Yauwa idan ba takura akwai Uniform ɗin bokonsu khalil an wanke ba a samu yin guga ba ko zaki danne musu, ni zan yi aiki ne yanzu a system kin san aiki nake a companyn Abbanmu, wai ma kin taɓa cin Zadeen bread ko Lipton ɗinmu.

Laaa Anty babanku keda gidan biredin.? kamar ma har da youghurt ko.?

Eh na Abbanmu ne bari zan sa a kawo mana biredin mu karya ma da shi gobe In Allah ya kaimu.

Ikon Allah, to Allah ya sa albarka ya ƙaro kasuwa.

Cewar Hamida cike da jin daɗi, Laila ta amsa da Amin sai ta miƙe.

To ya batun gugan.? zaki samu yi.?

Haba zan yi mana ai bana aikin komai.

Hamida ta faɗa tana miƙewa sai Laila tace ta jira ta zata kawo mata sai ta haura sama riƙe da sauran Shawarman a hannunta, ba jimawa sai gata ta sauko da uniform ɗin kala uku-uku ta bata, sannan ta nuna mata ɗakin da suke yin guga a ɗaya daga cikin ɗakunan falon ƙasa, sai ta koma sama, Hamida kuma ta wuce cikin zumuɗi ta fara aikin, tayi mamaki na yadda aka kashe ɗaki guda a gidan saboda guga, babu komai a ciki sai ƙaton tebur da aka shimfiɗa wani zani mai kauri, sai kuma akwai washing machine daga can gefe kusa da bayin dake ɗakin har guda biyu, ta gane ɗakin an barshi ne musamman dan wanki da guga, sai ta fara tunanin kamar ma ita kaɗai ce ke rayuwa a ƙasa su suna sama, dan gidan sama ne babba ƙasa akwai ɗaki uku nata ne farko daga hannun dama, sai wanda suka bar shi a matsayin ɗakin wanki sai kuma wani ɗaki dake hannun hagu kusa da kitchen wanda yake a rufe bata san meke ciki ba, a sama kuma ɗaki huɗu ne ɗaya na Hafiz sai ɗaya na Laila suna kusa da juna, sai ɗayan gefen hagu ɗakin Afra ne da kuma na Khalil, kenan ita tana rayuwa a kasa ita kaɗai, ƙila in ta haihu ɗaya ɗakin dake rufe ya zama na yaranta, abunda ta ƙissima kenan a ranta wanda ya saka ta sakin murmushi. Bayan ta gama ta ɗauki kayan ta haura dasu sama ta aje a Cushing ganin Laila bata nan, sai ta fito ta koma ɗakinta ta kwanta ta ɗauko wayarta taga misscall da yawa, Mamansu ta kirata kusan sau uku sai Haulat ƙawarta sannan Inna Jamila ta kira sai kakarsu, wayar tana silent shiyasa bata ji kiran ba, dan haka ta duba balance ɗin kuɗin wayar taga akwai kati sosai, saboda lokacin saura sati ɗaya aurensu Hafiz ya tura mata katin dubu biyar saboda kiran mutane. Mama ta fara kira bugu ɗaya ta ɗauka da sallama, cikin farin ciki Hamida ta gaisheta, ita kanta mama yadda taji muryar Hamida cikin annashuwa ya faranta mata rai, sai ta amsa ta shiga tambayarta me yasa ana ta kiranta ba ta ɗagawa, kuma su Hadiza yayyinta ɗazun sun zo gidan amma mai gadi yace bata nan, Hamida ta shiga mamaki amma sai ta samu kanta da cewa eh kawai saboda bata san dalilin mai gadi na faɗan bata nan ba, dole zata bincika taji. Sai ya kawar da zancen ta shiga bawa mama labarin abubuwan da suka faru, bata ɓoye mata komai ba, hatta yadda Laila ta rufe gida ta kwana gidansu Hafiz, ta ɗaura da bata labarin abunda ya faru jiya na tarban da Laila tayi mata har zuwa yau da safe, Mama ta saki guntuwar guɗa tana cewa.

Alhamdulillahi Hamida kin dace, dan haka saiki mayar da hankalinki kiyi musu biyayya dan gaskiya matarsa tana da hali mai kyau duk da abunda tayi shekaran jiya, amma munyi mata uzuri dan kishi wajibi ne balle miji irin nata da 'yan mata suke mafarkin samu, Hamida dan Allah da son Ma'aikin Allah S.A.W karki bani kunya, kinga dai yadda suka nuna miki yarda suka fara sakar miki ragamar gidan, nan gaba kaɗan In Sha Allah zaki mallaki kadarori ta dalilin biyayyarki. Dan babu mamaki kiga tana yi miki kyautar kuɗi masu kauri in kina mutuntata tunda ubanta hamshaƙin mai kuɗi ne. To ba ke ba nuna kishi da ita, dan abun alfaharinki ne ma ace kina auren mijinta.

Wlh mama nima fa nayi mamakin sauƙin kan da ta nuna min, tace ma zata saka ni a makarantar koyon girkin Zamani, da kuɗin ta zata biya min. 

Cewar Hamida cikin dariya, sai mama ta fashe da kukan murna. 

Allahu Akbar Hamida, Allah ya duba maraicinki ne ya haɗa ki da mutanen arziki, kinga dai duk gidan nan babu wanda Allah ya ɗaga darajarsa sai ke, dan Allah karki bani kunya, yi nayi bari na bari. 

Kai mama to miye na kuka, in kina haka zan daina faɗa miki komai, ke dai addu'ar ki kawai nake buƙata na cigaba da kasancewa a farin cikin dana samu. 

To ba dole nayi kuka ba na wannan bazata da muka riski kanmu a ciki, ban taɓa mafarkin ganin ki a gidan hutu ba duba da irin tsatson talaucin da muka samu kanmu a ciki. 

Haba mama Allah Allah ne! shi ke wanzar da komai, ya bayar da komai a inda yake so, dan haka wannan tsarinsa ne, babu wanda ya isa ya yi wa bawa komai face abunda Allah ya ƙaddara. 

Hakane kuma.

Cewar Mama, haka suka cigaba da hira mama ta cigaba da bata shawarwarin yadda zata zamu kujerar zama a gidan.

******

Hafsah.

Shuru-shuru ta zuba idon dawowar Bilal amma ba amo ba labari, har sai da aka shafe awa guda, duk yadda taso ta daure ta kasa, sai ta fashe da kuka mara sauti tana yi tana share hawaye dan kar yaranta su ganta, haka ta daure ta soya ƙosai ta zubawa yaran suka karya ita kuma ta adana sauran ta saka hijab da niyyar bin bayan Bilal dan zuciyarta ta kasa natsuwa, tasan 'yan ƙato da gora wasu ba Imani suka da shi ba, kamar jira suke a kawo musu karar yaro su karairayashi dan basa yin duka na hankali, ta fito tsakar gida riƙe da fos tana cewa yaran su jirata zata je ta dawo, Yazeed yace. 

Mama zan biki muje gurin yaya Bilal. 

Bai rufe baki ba sai ga Bilal ɗin ya shigo gidan da ɗingishi fuskarsa a kumbura alamun yasha mari, ga kuma zanen bulala a gefen fuskarsa har ya fashe yana tsatso jini, Hafsa ta dafa ƙirji tana salati tsabar kaɗuwar data yi, Bilal ya ƙaraso ciki ya tsaya idanunsa suna ƙara fitar da hawaye, cikin kuka yace. 

Mama ki yafe min bazan iya cigaba da zama a gidan nan ba, zan tafi na shiga duniya saboda ina so na nimo asalin mahaifina. 

Yana gama faɗar haka ya rushe da sabon kuka sai ya yi hanyar ɗakinsu cikin ɗingishi, Hafsa ta ce cikin sanyin murya dan ta kasa kuka saboda tashin hankali hawayen sun ƙafe. 

Bilal ashe baka yarda da ƙaddara ba. Ka sani yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau shima cikar imani ne. Sannan Allah yana jarabtar bayinsa wanda ya fi so domin ya gwada Imaninsu, kuma wasu iyayensu sune jarabarsu kamar yadda wasu 'ya'yan sune suke zama jarabawa ga iyayensu. Bilal ba kada wani uban daya wuce mahafinka kuma da shi zaka yi ado, yanzu idan ka tafi saboda halin Abbanmu ni kuma a wani hali kake so ka jefa ni.? Ba Abbanku kaɗai ne yake da haƙƙi akanka ba nima ina da haƙƙi akan ka, kuma wannan ba tarbiyyar dana baku bane, dan haka ka dawo cikin hankalinka. 

Tana gama faɗar haka ta wuce kitchen ta juye ruwan zafin data dafa dan dama tun ɗazu ta dafa idan ya dawo ya gasa jiki tunda tasan sai sun duke shi, ta fito ta sirka masa ta kai masa bayi, tace yaje yayi wanka ya fito tana jiransa, ba musu yaje yayi wankan kuma yaji daɗin jikinsa sosai, ya fito ya shiga ɗaki ya shirya cikin farar Jallabiya da dogon wando ya fito ya zauna a tabarman dake tsakar gida, sai ta saka Yazeed ya kawo masa abin kari, ba musu ya karya, kaɗan ma yaci saboda bakinsa babu daɗi, Hafsa ta zauna tana dubanta fuskarta cike da murmushi amma cikin kwayar idonta hawaye ne kwance sai tace. 

Ni jarumi na haifa ba lusari ba, Bilal ɗina mai juriya da haƙuri ne, ba yi da riƙo balle yin faɗa, har gobe a haka nake kallon ɗana. Kune sanyin idanuna, kune nake kallo a matsayin bangon jingina na, yanzu idan ka tafi kana tunanin zan yi farin ciki. Bilal Saboda ku na kasance har gobe tare da mahafinku, me yasa ni ba zaku yi mini wannan sadaukarwar ba mu kasance a tare mu raya farin cikin dana ke ƙoƙarin gina mana. 

Mamaaa! 

Bilal ya faɗa cikin dakatar da ita yana kuka mai cin rai, sai ya cigaba da cewa. 

Na tuba nabi Allah na biki, bazan sake irin wannan furucin ba, duk wuya duk runtsi muna tare dake. 

Ya ƙare maganar yana kamo hannunta jikinsa yana rawa, Hafsa ta matse hannunsa cikin nata tana danne wutar dake ruruwa a zuciyarta, sai sauran yaran suma suka zo suka rungumeta suna kuka mai cin rai haka ta haɗosu duka ta rungume tsam tana murmushi ga siraran hawaye suna bin kuncinta.

*Uwa kenan, uwa uwa ce Allah ya bamu ikon faranta wa iyayenmu Ameen.*

Rahma ce.