TALES OF THE WAZEERIS

the death

by @surayyahms

*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms

#Royal hate-love

#Forbidden bloodline

#Obsession

#royal politics

#Sisters love hate

Bismillah rahmanir raheem.

4. The Death..

acikin sauri sauri nana A tafito daga cikin sashen uwar jini sanye da bajajjen doguwar riga irin original hand woven ghanian kante print din nan da aka mata sakakken dinkin doguwar riga wanda jelarsa take da tsayi har yana jan kasa.

daga farfajiyar gidan bayine da masu aiki suka tsaya a jejere cikin tashin hnkli, kowannensu ya dan sunkuyar da kansa kasa babu wanda ya kuskura ya iya daga idonunsa sama bare yagane meke shirin faruwa da shugaba khaleefa wazeeri.. har nana A ta wucesu babu wani cikakken motsi face sai karar ƙararrawar securities da yariga ya karade sararin wajen.

gaban wani katafaren golden gate me tsayi daya killace babban sashen da khaleefa shugaban Tharim Vale yake nana atiqar ta dosa cikin nitsuwar data tattaro makanta daqyar nan da nan baiwarta me suna sabuwa ta rufa mata baya dan bakasafai ake bari kowa ya shigo cikin killatecn sashen da chamber shugaba khaleefa wazeeri vale yake ba.

masu tsaron kofar wajen suna ganinta aka bude musu gate din farko, wanda duniya ne daban agabansu dan kuwa girman muhallin yayi girman bangaren da uwarjini take zama sau biyu inma bei fi ba..

tsaftatacciyar iska me sanyi me gauraye da original qamshin frankincence ke ratsawa taramin hancinsu ayayinda beautiful decorative vegatation of dark green umbrella nd palm trees suka jeru sukayi liff kamar da hannu aka jejjera su, colourful shrubby fresh flowers dake zagaye da dogon shararren streets din yanamai bada atrctive straigh layout mei triangular countour dazai bi dakai harta cikin round water splash fountain wanda yakedada fallasa irin tsafta da kwanciyar hankali dake muhallin wajen..

anan bangaren ma kowani ma'aikaci na yawone cikin specific tsarin uniform din aikin sa, dake akwai katoton mega orchid da horse stalls da ake yawan musu kiwon kosashun dokunansu wanda zallan masu lura da su ne kawai ke shawagi anan wajen.

suna wuce gaban wata mahaukaciyar multi estate car Garage da ta cinye huge space that fits major luxury cars wanda tundaga nesa ma zakaga yadda aka wani irin jerasu a layi into sections kamr daily cars, luxury, SUVs sann aka kara bude musu yar madaidaiciyr golden gate kurkusa da home garden me fidda qamshin furanni suka shige ciki..

saidai wann environmt din daban yake, dan kuwa is calmer nd quieter babu yawan masu tsaro a fili...

amma kana tafiya ne boyayyun camera da snippers suna kallonka a boye batare da snnin ka ba..

kai tsaye nana A ta wuce cikin huge building din da babban private chamber shugaba khaleefa waxeeri vale yake, a detached greek style royal bungalow, wani boyayyr ajiyar zuciya nana A din ta sauke snn suka ratsa tacikin kofar da already masu tsaron kofar sun riga sun wangale musu shi kafin su karaso..

Katafaren Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji Lumtsattsun royal chairs golden and wine red colour. dogayen labulaye da luxury chandelliers suma golden colour sai baza qyalli suke snn duk wani abu daya ƙawata falon ya zamto shima golden nd red colour dinne da wasu irin royal caperts sai incence burners suna aikin bada Daddan Qamshin turarruka na alfarma da kuma iskan Airmores mai sanyi wanda already sanyin ma yakama falon takoina sabida wata irin dukiyace ta musmn aka narkashi acikin wnn falon.

Babu kowa acikin falon tasu ta farko wanda shine zai sadaka da babban falo na biyu wanda ya kasance falon zaman iko ne daga nan kuma har zuwa turakar meigirma khaleefa

Ratsa dogon Falon tayi baiwarta sabuwa na biye a bayanta har tanufi kofar da zai kaita ainihin bedroom dinsa na musamman..

tana isa dede wajen wanda ke tsaron kofar ya bude matashi, cikin takunta mai sanyi da aji ahankali tashige ciki baiwarta sabuwa ta koma gefe ta tsaya daga nan itama tana jiran fitowar uwar gijiyar tata.

Katafaren dakine na alfarma anmasa kwalliya me daukar hankli wanda shirun da wajen yay tamkar babu kowa aciki yasaka tsikar jikinta ya dada tashi.....

Ajiyar zuciya ta sauke ayayin data sauƙe ruwan idanuwanta akansa nan da nan dukkan masu tsaronsa atake sukafara darewa suna masu basu waje

...

ginannen mutum ne sosai da hutu da jinin iko tareda dukiya ya gama ratsasa, Kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa taso rudewa tayi saurin daidaita kanta cikin tattaro nutsuwa da qarfin hali.

Qarasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kalle yanayinsa cikin runtse idanuwanta da suka fara canxawa murya na rawa tace,

Allah yataimakeka rankashi shi dade.....

gajiyayyun Idanuwan daya sake watso matane yasa tayi saurin gyara murya cikin nutsuwa ta dauke idanuwanta daga kallonsa dayakeyi ta tsaya cak atake dakin ya cika da wani irin nutsuwa mai nauyi…

ba irin nauyin nan na kwanciyar hankali ba, sai wanda yake dauke da tsoron mutuwarsa dake nuna alama ajikin sa da numfashinsa

duk da wani irin ƙamshin turaren wuta mai sanyi dake yawo a iskar dake yawo a sararin daki bazai hanaka jin raunin ganinsa akan gadon sa na iko da aka mayar masa wajen jinya ba…

atsakiyar dakin a kan babban gadon da aka lullubesa da lallausar bargo marar nauyi

shugaban Tharim Vale khaleefa wazeeri vale the true pure blood of the wazeeris clan ya kwanta amma kamar bashi ba dan gabaki daya ginannen jikinsa yashanye ya dan jeme numfashinsa na fita ahnkali kamar ana ja da igiya…

kusan idanunsa ne kadai suke da rai a jikinsa dan harynxu baya iya furta magana a fili

nana A ta dada matsowa kansa a hankali ta tsaya nesa kadan daga gadon ta dan sunkuyar da kanta cikin girmamawa iduk da kasancewarta ‘yar uwar jini ga mhifiyarsa

muryarta ta fita kasa kasa da natsuwa tace

“ranka shi dade…ya jikin?

idanunsa suka motsa akanta a hankali da alamar amsawa nan

tadan ja numfashi kafin ta cigaba…

“...agarface ni, uwarjini ba zata samu damar zuwa nan ba.

shiru ne ya ratsa dakin yana dan kallonta sai wahallen numfashinsa mairauni da yake kan saukewa yana kuma karantar yanayinta da nutsuwa da alaman yana sauraro..

kanta akasa ahankli tace "akwai abu mai muhimmanci da ya zama dole ka sani kafin…..

sai kuma ta kasa karasa maganar, ta dan gyara zaman mafayin kanta cikin dauriya tace “ranka shi dade..uwar jini ta riga tatsayar da yarjejeniyar haɗa aure tsakanin zuriyarka da Zamkora…

dede nan idanunsa suka dan budu sosai kamar wanda yake kokarin tabbatar da abinda ya ke ji. sai kuma ya gyada mata kai alaman tacigaba da magana

kanta na kasa tace “doka ce da aka riga aka karbota daga wajen ruhi me tsarki dan akare martaban zuriar nan… kuma uwar jini ta riga ta amince da ita a karkashin ikonka tana so ahade yarjejnyr aure da kuma jini da jikanka shamsan.

tana gama furta hakan ya dauke kai bai kara kallonta ba sai wani dan karamin motsi da yatsunsa sukahauyi ajikin farin zanin gadon

.

nana A da ta lura da sauri sauri ta dan matsa kusa ta durkusa agabansa kadan.

kusan da dukkan karfin da yarage masa ya daga kwayar idonsa sama snn ya motsasu zuwa kofar ficewa da

alamar yana son ganin wani.

daqayr ta fahimta nan take tace“..matarka…?”

a hankali ya lumshe idonsa da alamar eh. ya sake mata alama da ido, tana kallonsa tace da danka Abdallah ko…?

anan ma ya dan motsa idanunsa da sauri sauri kuma ahankli

nana A ta mike tsaye da agaggauce ba tare da bata lokaci ba ta doshi hanyar fita tana mai furta“toh ranka shi dade yanxu za a kirawo su.

tana ficewa ta bawa baiwarta sabuwa dake tsaye a kofar farko saqo cikin gaggawa sabuwa ta fice ta doshi dayan huge chamber da matar khaleefa din take wato Uwarjini Nana hafsa wacce take musu tamkar gimbiya a wann ahali, dan itadin ma pure jinin zuriar wazeeris vale ne, anan sashenta kawai take rayuwarta sbd babban sashene wnda ratarsa baida wani yawa dana mijinta khaleefan sosai.

bai wuce mintuna ba sabuwa takai sako…

after like 7 mins kofar dakin ya sake budewa a hankali nana hafsat din ta shigo tasaka wani irin bakin kaya mai kamar sakekken luxury egyptian abaya bamai tarkacen design ba kusan koinanta a killace, kai tsaye ta shigo dakin tare da babban danta Abdallah da jikarsu shamsan dake biye da su a baya

Nana hafsa farace soll irin fari na zabiiya me dauke idon nan saidai kyakkwan tsiririn fuskarta a dusashe yake da tsananin baqin ciki kullum musmn tunda ciwon nan ya kwantar da mijinta shugaba khaleefa

tun da aka sanar da ita yanayin jikinsa nayau kwayar idanunta suka rika suka kumbura da kuka… tana tafe da babban dansu kwalli daya abdallah wanda shikansa harynxu bai gama fahimtar abinda ke shirin faruwa da mahaifinsa ba sai dai tsoron yanayin wajen yagama cika shi taciki

duk gidan babu ahalin da ake ji dasu kmr na shugaba khaleefa wazeeri vale sbd an haiho ƴaya maza masu lafya da kyau a tsatsonsa ga babban dansa abdallah ga kuma jikarsa shamsan.

Nana hafsa tana karasowa ta tsaya cak ganin halin da mijinta ya ke ciki. suna hade ido muryanta a karye ta rusuna da hawaye taf a idonta, ahnkli ta rusuna agabnsa da matsanancin rauni a voice inta tace...“ya jikin??

kallonsu yake duka baiy alamar amsa maganar ba har saida nana atiqa tasha jinin jikinta ta dan janye ta fice musu a dakin ta basu sarari sabida dukansu basu sanma yana iya magana ba.

tana ficewa baiyi wata wata ba ya dan motsa kansa da kyar ruwan idanunsa suka tsaya a kansu dukansu ukun yanamai jin tsananin tausayinsu har ransa

ayayinda yake musu kallo na karshe.

his only beloveth wife nd his only son ga kuma jiknsa dayake bala'in kama dasu kamar an tsaga kara.

jin numfashinsa na dan tsanantawa yay sauri sauro ya riko hannunsu duka ya dan bude baki akaro na farko muryar sa ta fito sarari da rauni mai saka karayar zuciya cos he made sure dat su kadai suke iya jin muryansa dake fita almost in a whisper

atakaice ya fayyace musu abunda nana A tazo tagaya masa game da hadin jini da za'ayi da ahalin su na zamkora.

sosai hankalin dansa Abdallah ya tashi jin mahaifinsa yana masa harsashen xama akan kujerar mulkin garin kano amatsayin sarki...

sann yay masa wasiha akan ya tabbatar da cewa zuriar sarauta da zai shinfida a kano na addini da gaskiya ne bana biyayyar tsafi wa uwarjini ba...

shugaba khaleefa yafi kowa sanin irin zuciyar mahaifyarsa duk dama

nana A bata wani fayyace masa duka shirinsu akan hadin auren jini ba saidai basirarsa ya riga ya warwaro masa kan zancen.

yasan idan ya yau rasu yan uwansa maza ne kawai zasu cigaba da gaje kujerar iko a tharim vale, dukan su kuma Allah bai basu haihuwar ɗa namiji ba

dan haka wnn alaqar yarjejiniyar aure yasan dole dazuriar dansa abdallah ne kadai za'a iya hada shi wanda hakan yana nuni da cewa cigaban asalin zuriar wazeeri vale na daga jininsa ne...

hawayen nana hafsa nakan zuba kmr ruwa tafara bankwana da mijinta cikin kalamai masu sanyi da taushi..

sai can ya dan motsa yatsunsa yamata alamar ta yi shiru...

tareda juyo idanunsa da kyau kanta tareda dansa abdallah ahnkli yana murmushi me sanyi yace "musu bayan namutu kuyi kokari ku kauda jikana shamsan acikin gidan nan da gaggawa kar ku barsa ya shaqu da ita ko kadan...

yana maganan cikin nishi duka suna kallo juna

cikin jan numfashinsa dake fita kmr na karshe yace" na aje rubutattun littafn dabara da qa'idodi da zasu taimaka maka wajen zama akan kujerar sarauta, ka riqesu dakyau, kay amfani dasu, har ka bayar ma jikoki na suma su bayar ma nasu..

ya sake cewa "...akai jikana shamsan dahrul zarah dake can qasar moroco abashi ilimin addini mekarfi dan ya samu yana kare kansa snn agargadesa, kar ya fada cikin tarkon da mahaifyata take kan shiryawa wajen maida shi yarimar da zai cika mata burikanta na tsafi da zalunci akan ahalin zamkora....na baku amanar junanku..

nan ya sakesu ya riko hannun matarsa ita daya ahnkli yace ranki shi dade nana hafsat na baki amanar zuria ta da jinina..ki karesu

ahnkli nana hafsa ta lumshe idanuwanta dake zubar da ruwa sosai, akaro na farko da jikansa shamsan din ya sunkuyar dakai slowly yanamai share hawayensa tsilli daya daya sauko dan tun da suka xo wajen bai wani nuna emotion ba

dansa Abdallah ne kawai ya kara riko hannunsa da karfi idonsa yay jaawuuur gabobin jikinsa cikin rauni yana jin wani irin tsananin zafi aransa bana kadan ba.

shugana khaleefa ya musu kallo na karshe nan take shima ruwan idanunsa suka lafa

kmr wanda ya gama sauke nauyi aransa yace" Alhamdullhi.

a fili kuma ya furta la ilaha illah...

yanamai lumshe ido numfashinsa ya tsaya cak wani irin shiru mai sanyi da kuma karya zuciya ya mamayesu atake nana hafsa ta saki kuka mai masifar rauni ta fado bisa jikin gadon rungume da mijinta

salati da Abdallah yay da karfi kuma cikin rauni yasaka nana atiqa kasa hakuri agaggauce ta bude kofar kawai ta shigo ciki da gaggawa kirjin ta na bugawa kusan

idanuwanta a rufe…

akaro na farko data ta kalli gawar shugaba khaleefa wazeeri taji kamar ruwan wuta ake narkawa ajikinta sbida akwaisu da son jininsu

duk dama ba itace ta tsuguna ta haifesa ba amma dataga gawan sa akwance saida taji kamar zuciyrta kawai aka cinnawa wuta.

tabbas maganan ruhi ya zamto gaskiya...

zunubin uwarjini yay sanadiyar mutuwar shugaba khaleefa waxeeri of tharim vale

hawaye kawai ta zubar batare da tay kuka me sauti agaban dansu da jikarsu da kuma surkuwan sun ba sai can har saida ta tattaro makanta nitsuwa sann ta juya ahnkli tafice a sashen agaggauce ta nufo waje dan taje ta sanar da uwarjini cewa ɗanta khaleefa ya rasu

bayan ficewarta kusn Abdallah ne kawai yay karfin halin miqewa ya kira amintaccen likitar su Dr haladu maruwa within few mins likitan ya shigo nan ne aka asalin tabbatar da cewa Tharim Vale rasa shugabansa a karancin shekarun da baifi 48 ba for the first time in deir history dan zuriarsu kaf basu taɓa binne wani jininsu wanda yay kasa da shekaru 120yrs a duniya ba....

daga bangaren nana A kuwa kusan ba acikin hayyacinta ba ta isa chambern uwarjini maqboola dan sanar da ita wnn mummunan saqo, lkcin ana neman karfe 8 ne na dare, dan haka ta boye hawayen ta bata sake tayi wani kuka a fili ba har saida takai kanta gabanta yar uwarta uwarjini maqboola data sameta a uwar dakintan har yanxu a tsaye tabi ta kura ma bango idanu..

gabaki daya kaganta kasan ba acikin hayyacinta take ba kwayar idanunta sun kada sunyi jajir, tayi nisa sosai cikin zurfin tunani, kusan sautin durkusuwa tare da fashewa da kuka me karfi da nana A tay ne yasaka ta farga ta juyo agaggauce cikin lura da ita.....

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025