MENE NE ABIN YI..?

Page 10

by @cwtsumiey19988


        *Page 10*

"Brr Junaid dan Allah kasa baki ko Mom zata fahimce ni,Allah ba wata manufa ko niyya tasa nace mukoma wancan garin ba , Ina son yin hakan ne dan k'ok'arin wajen tsaran lafiyar Nadeen ne kawai".
       "Shawara d'aya zan iya baki a yanzu shine ki dakata ma'ana ki aro natsuwa kisa ma ranki har zuwa sanda Dad zai dawo sai ki sake tada maganar".
      "Taya haka zata kasance bayan Mom itace k'ashin bayan da zata taimaka min wajen convincing d'in Dad,gashi ta ce min a'a tunda farko ,to taya zaka ce in yi shiru har sai ya dawo?".
    "Kin fi kowa sanin halin Mom,idan tace zatayi abu tom ba shakka zatayi shi haka ma idan tace a'a to fa a'a d'in ne,to dalili da me zai sa mu damu ko takura kan mu akan abin da munsan ba zamu samu ba ko kuma mu iya canza shi ba?".
    "Eh to na yarda kana da gaskiya amma kuma ya kamata ace nayi wani abu ko d'an ya yake,wanda zai k'ara taimaka min wajen cin nasarar abin da nake so".
    "Kamar me kenan?".
    "Zan kira Dad ne yanzu tun kafin yadawo mu fara maganar da shi".
     "Kina ganin hakan ba zai haifar da wata matsala ba ?".
"In sha ALLAH haka nake fata,but amma ina zuwa just a minute's",ta k'are maganar tana nufar hanyar bedroom d'in ta da sauri .
Kamar wanda aka tsikara haka ya mik'e tsaye yana mai kaiwa da kawowa gami da kaiwa d'ayan hannunsa bugu ,zarya ya fara a cikin parlour cikin k'ank'ani lokaci duk ya rikice har ta kai ga ya fara fad'in abin da ke cikin zuciyarsa a bayyane yana mai cewa,"taya haka zata kasance? ,ba zan ta'ba barin hakan ta faru ba gaskiya,tsawon shekara nawa na kwashe ina lalla'ba yarinyar nan domin in samu in shawo kanta ko na samu wurin zama a cikin zuciyarta amma ina hakan ta gagara,har sai da na kai ga'bar da na ke saran cimma nasara sannan wani sha-sha ya shigo yace zai lalatamin komi kuma sannan a ce in tsaya in zuba ido ina kallon sa,wannan ba mai yiwuwa bane don haka duk wata shawara da zata k'ara rikirkita wannan lamarin ita zan bada har sai nayi nasarar fidda wannan mutumin mai siffar kwanciyar mage mai d'aukar rai daga cikin gidanan",duk wannan surutun yana yin sa ne yana me kai komo a cikin parlour d'in ba tare da ya zauna ba.
   K'arar motsin tafiyar da yaji ne yasa shi waigawa da sauri,domin ganin waye jikinsa har rawa yake abun ka da mara gaskiya,fuskar da ya yi tozali da ita ne yasa shi ya mutsa fuskarsa tamkar wanda yaga wani abun kana gami da d'aurewa.
  Nadeen ne ya fito wanda tun bayan dawowar su shi da Shuraimah bai k'ara fitowa ba sai yanzu da k'ishir ruwa ya dame sa ya fito domin ya d'auka a kchine,ganin yanda ya nuna halin ko in kula game da wanzuwar Brr Junaid a cikin parlour d'in yasa shi kuma ya k'ara harzuka,ya bi bayansa a fusace,kusan a tare suka shiga cikin kchine d'in saboda saurin da Brr. Junaid yayi, lura Brr Junaid ya yi da Nadeen ruwa yake san d'auka yasa yaje saitin inda Fridge d'in yake ya tare hanyar,cikin hargagi yake masa magana gami da nuni da hannu(alamun yaren kurame) yanda zai fi ganewa akan ya bashi guri yayi abinda yazo yi,shi kam tsuru yai masa da idanuwa ba tare da ya iya yunk'urin komai ba balle har ya sa ran zai ce masa wani abu,shigowar Mom cikin kchine d'in ne ta dakatar da komi.
     "Kai! lafiya kuwa,kuke tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru?".
Mara gaskiya ko a cikin ruwa ji'bi yake, da k'yar Barr Junaid ya tattara y'ar sauran natsuwar sa duk da dai ba zata iseshi ba, ya ce,"uhm..... dama .... kawai ba komi zan dai tafi ne na dawo zuwa gobe in Allah ya kaimu".ya k'are maganarsa yana mai nufa hanyar da zata Sada shi da gate d'in gida.
   Dukansu da idanuwa kawai suka bishi da shi har da ita Shuraimah dake fitowa daga nata bedroom d'in cikin mamaki ba tare da wani ya iya yunk'urin cewa komi ba,wani abun Allah ba wanda ya k'ara bi ta kanshi da kuma abin da ya aikata,saboda kowa da akwai abin da ya dame sa a cikin ransa.
    A tak'aice dai sai da muka kwashe tsawon kwana ukku a gidan ba tare da walwala ko sukuni ba,duk nabi na takura ma rayuwarmu ni da Nadeen,ba shiga ba fita ba inda muke zuwa ko chamber na daina zuwa,duk wasu case's dana kar'ba sai Barr Junaid ne ya ji da lamarin, harta da wayoyinmu ma na had'a su duka na kashe don gani nake sune hanya ta farko da zaai saurin gano mu,yanda kasan wad'anda suka aikata wani mugun laifi wa k'asa da k'asa haka nake 'boyenmu,a ta d'ayan 'bangaren kuma na hana Mom zaman tsaf kullum cikin magiya nake da ban baki akan ta amince da buk'atata,tun tana kulani har ta koma sai dai ta zuba min idanu kawai,lokacin da Dad ya dawo daga tafiyar da suka yi ba k'aramin farin ciki nayi ba sai da ata wani 'bangaren na zuciyata cike take da fargaba da kuma zullumi yanda zata kasance tsakanin mu in har ya samu labarin abin da na zo da shi.
   Ilai kuwa hakan ce ta kasance,don ba k'aramin firgita nayi ba da ganin reaction d'in sa sanda na tare shi da zancen.
   "Ya isa haka Shuraimah!",ya fad'i sunana kai tsaye ba tare da ya 'boye ba kamar yanda ya saba,"baki da hankali ne, mai yakawo irin wannan munmunan zancen a bakin ki?".
     "Dad wlh kuskure ne aka samu, kuma duk na aikata hakan ne don gujewa fad'awa cikin halaka,nice silar cutar da Nadeen,bazan so wani abun ya k'ara samunsa a ta dalilina ba kuma "......dakatar dani yayi cikin fushi da hargagi"ya isa haka bana buk'atar dogon zance daga wajen ki,abu d'aya na sani shine bazan koma Doha State da zama ba,ruwanki ne ki zauna ki sake tunanin wata mafitar ko akasin haka".
     A firgice ta d'ago kanta tana mai tattara natsuwar jikinta gami da ta zuciyarta domin samun damar da zata yi masa magana yanda zai fahimta,"Dad dan Allah ka fahimceni ban san wani abu da ya kamata inyi baya ga haka ba,wannan itace kad'ai mafitata".
    "Naga alamar ba so kike ki ceci rayuwarsa ba ,nema kike ki k'ara kai shi ga wata babba kasadar a rayuwarsa, wacce zata iya zama ajalinsa ma gaba d'aya bawai raunatar da shi ko wani abu makamancin haka ba ,in ba haka ba mai zai sa ba za ki shirya ke da shi ku fita wata k'asar ba ko other state,sai kice sai Doha State,sai kace shine kad'ai gari a Nigeria?".
    Hawaye kwance sha'be-sha'be a saman fuskata na ba shi amsa,"Allah Dad nima nayi irin wannan tunanin,amma na fahimci hakan k'ara dagula komi zai yi,saboda kai tsaye za'a gane bani da gaskiya tunda har nagudu zuwa wani country d'in ".
    "Da'alama dai ba zaki ta'ba gane ko fahimtar abun da ne ki so in sanar da ke ba,so get out of my side!",ya k'are maganarsa yana mai nuna min hanyar da zata sada ni da d'akina.
    "Dan Allah Dad"...... dakatar da ni yayi a k'aro na biyu yana mai cewa,"da'alama sai na nuna miki asalin true colour d'ina sannan zaki shiga taitayinki",gadan-gadan ya yo kai na wanda hakan yasa na kwasa da gudu ba tare da na yi la'akari da hanyar da zan nufa ba ko da na fita ba hak'ura ya yi ba ci gaba yayi da fad'an Inda kacokan ya mai da laifin a kan Mom.
    "Idanuwanta a rufe tana ta faman share k'ollar da ke zubowa daga cikin su,ta bud'e k'ofar d'akin da ke kusa da ita ,ba tare da ta fahimci komai ba ta danna kanta ciki,sassanyar iskar dake kad'awa tare da daddad'en kamshin turarensa ne suka bigi fuskarta hakan ne ya nusar da ita cewa ba d'akin ta ta shigo ba,da sauri ta fara rarraba idanuwanta don son yin tozali da shi,can gefan gado ta hangesa kwance yana ta sharar barci abinsa hankalinsa kwance,rausarya da kai tayi gefe guda gami da nufar inda yake kwance,tana mai k'are masa kallo,ko da ta k'arasa kusa da shi kan bedside drawer ta samu ta zauna tana mai k'ara tsaresa da kyawawan idanuwanta.
    Ban san sanda bak'in cikin dake raina da kuma saman fuskata suka fara yayewa ba,naji wani farin ciki,natsuwa gami da nishad'i suna sauka a jikina da zuciyata, inama da'ace nice nake kwancennan haka, barcinsa yake haik'an cikin natsuwa da kuma dad'in rai ba abun da ya damesa,don ita kanta ta manta yaushe rabon da tasamu damar yin barci peacefully irin haka,ko da ta kwanta a tsorace take yinsa tunaninta a kullum shine da wanne irin k'alubale zata farka a gobe in Allah ya kaimu.
    Motsi ya fara alamun yana son farkawa,wanda kaifin idanuwan da ta tsura masa ne yasa yaji kamar mutum na tsaye a saman kansa yana kallonsa,a d'an diririce na tashi da zumar barin d'akin tun kafin ya gama wartsakewa daga barcin da yafarka,caraf naji an rik'o hannuna wanda hakan yasa na waigo cikin sauri tare da fiddo idanuwana waje alamun mamaki,ido biyu mukayi da shi, kai tsaye rashin gaskiya da rauni suka bayyana a kan fuskata,kuma na kasa aikata komi domin ganin na 'boye hakan ,sai dai zuba ma juna idanu da mu kai har na tsawon wasu dak'ik'u daga k'arshe kuma na fara kiciniyar kwace hannuna a cikin nasa,sai dai ko kusa ko alama na kasa aikata hakan,ganin da gaske wahalal da kaina kawai zanyi yasa na far yi masa magiya a kan ya sake ni in tafi d'akina,jawoni ya yi baya ya zaunar dani kan bedside drawer dana tashi akanta,shi kuma ya tashi zaune a kan bed d'in yanda zai fuskanceni sosai, har yanzu hannuna na cikin nasa daga k'arshe ma duka biyun ya had'a ya rik'e,ban san a taya zan iya yi maku bayanin halin da na tsinci kaina a wannan d'an lokacin ba wani irin tsam gami da y'ar naje ji tun daga yatsansa kafata har zuwa saman kaina,babban burina shine in 'boye asalin gaskiyar da take binne a cikin zuciyata,girgizanin da naji an yimin ne ya dawo da ni cikin hayyacina.
     "Shuraimah wai me yake faruwa ne,naga kwana biyu komi na gidannan ya canza?".
    A diririce nake kallon fuskarsa ba tare da nasan amsar da zan ba shi ba,domin har ga Allah ba na son ya fahimci abun da yake faruwa don gudun afkawarsa cikin wani halin,kasa ce masa komi nayi har ya mai-maita hakan kusan so ukku.
    Cikin yanayin fushi yake magana ta sigar su ta kurame,"kiyi min bayani mana ko idanu zaki zuba min kawai ba tare da kin yimin bayanin abun da yake faruwa ba?".
    "Am.....uhmmmm.......dama....ohhhh... laifi nayi ma Dad shine nake ta faman ba shi hakuri,amma yak'i hakura".
     "Laifi kuma wa Dad d'in,mutumin da ko wani kika yi ma laifi baya gani balle shi karan kansa kuma har kice kin basa hakuri ya k'i ya hakura,anya kuwa Shuraimah ba akwai abun da kike son 'boye min ba?".
    "Allah iya abun da na sani ke nan".
    "To amma duk da ba yawan shiga cikin irin wannan zantuttukan nake ba sai dai na fahimci cewar  kamar ba iyakar abun da ke faruwa a cikin gidanan kenan ba?".
    "Ni dai iyakar abun da na sani kenan,inma akwai wani abun to ni ban san da shi ba",na k'are maganata ina mai sharce hawayen da suke rige-rigen sauka a saman fuskata.
    "To shikenan ya isa haka share hawayen,koma mene ne zan je in samu Dad d'in nima da kaina in basa hakuri in sha ALLAH zai hak'ura,kawai abun da nake so dake shine ki daina takura kan ki,komi zai zama normal okay?".
    "Shikenan in sha Allah zan fidda damuwar da ke raina kaji my big brother".
    "Yauwa that's my sis,yanzu maza share hawayen ban san na dinga ganinsu".
    Da kai kawai na amsa masa tare da sa hannu ina goge hayen dake saman fuskata.
    "To ko ke fa, har kin k'ara kyau abunki".
    Murmushi ne ya kwace man ba tare da na shirya masa ba kana na ce da shi,"yanzu barcin ka zaka koma ko?,tunda dama nice na ta da ka".
    Yamutsa fuska yayi gami da kishingid'a a jikin allon gado yace da ni,"barcin ba wani dad'i ne da shi ba,saboda mafarkin da nake yawan yi kwananna baya min dad'i ko kad'an biside ma ciwon kai suke saka ni sosai".
    A firgice na waigo Ina kallonsa bakina har rawa yake amma na kasa iya ce masa komi ,da k'yar na samu na aro natsuwa gami da jarumta na tambaye shi,"Mafarki kuma dama har yanzu kana yinsa amma baka ta'ba fad'a min ba?".
    "Eh lokaci zuwa lokaci dai,sai dai wannan karan abun ya na d'an takuramin sosai,kusan kullum sai naga wata dattijuwa tana mik'o min hannu ko ta kira sunana wai in zo gareta kar in tafi in barta ni kad'ai kawai take da shi a rayuwata kuma ita d'in mahaifiyatace.......da dai sauran makamantan irin wannan zance".
    Hannayena na d'ora saman kai na bakina d'auke da kalmar Inalillahi wa'innan ilaihirraju'una,ba tare da na k'ara ko second d'aya a d'akin ba na kwasa waje da da gudu,wanda ni kaina ban san ina ne zan nufa ba............✍✍✍✍✍✍