17
*Page 17*
Koda na shiga cikin room d'in ban bi ta kan komi ba ,domin hankalina gabad'aya na kan laptop d'ita kawai,connecting d'in na'urar da na gani a cikin teddyna da system d'in na fara yi,bayan na dakatar da duk wata camera dake cikin Room d'in don gudun kar Elder ya fahimci wani abun, idanuwa na zubawa laptop d'in a lokacin da komi na cikin na'urar ke loading ma'ana yana k'ok'arin sauka akan system d'in yanda zan sami damar ganin abinda ke ciki, na zak'u ,na k'agara in ga abinda ke ciki, babban burina da kuma fatana in samu key wanda zai zamemin warwarar bak'in ciki, tashin hankali, damuwa gami da k'unci rayuwar da nake a ciki........... sosai na mai da hankalina kan laptop d'in na ga still processing.
Duk wata ga'ba da ke jikina sai da tayi sanyi sakamakon cin k'aro da nayi da abin da ke cikin na'urar ,ba komi bane a ciki face record Video guda d'aya sai wani rubutu da na rasa gane kansa da kuma kalar yaren da aka yi sa,tattara kayan dake wurin nayi domin barin secret room d'in gabad'aya sai kuma zuciyata ta rinjaye ni akan in saurara,in kalli Video duk da dai inajin ba lalle ace inji kalar yaren ba,duba da wancan rubutun da na gani.
Wata k'ara kawai na ke ji ko da na kunna Video,amma dishi-dishi nake ganin sa da kuma wata k'ara da ta cika min kunne, har na tsawon wani lokaci nama fara fidda rai gami da sarewa da wannan lamarin sai na fara jin magana can k'asa-k'asa,amma ko dawa bana iya ganin fuskokin Mutanen dake ciki,abu d'aya dana fahimta shine suna zaune kamar a parlour ne,da sauri na dawo gami da jawo headphone nasa domin samun damar jin abin da ke ciki yadda ya kamata,muryoyin mata guda biyu nake ji amma ko da wasa na kasa fahimtar abinda suke cewa saboda wata irin k'ara da nake ji ,da alama dai na'urar ta samu wata matsala ko kuma setting d'in ta ya goce,sai can daga bisani kuma naji muryar ta dai-daita d'aya daga cikin su na cewa,"Haba Nabeelah bai kamata ki rik'a fad'in wad'annan kalmomin ba,in sha Allah Komi zai koma dai-dai,zuwa anjima zan yi ma Zain magana in ya so sai ya tare shi Zaid d'in suyi magana ko za'a samu sauk'in al'amuran dake faruwa".
"Hmmmmm a'a da kin kyale shi ,don na fahimci suma tsakaninsu da akwai abinda yake faruwa".
"Subahanallahi abun har ya kai haka,to ni duk ina-ina haka ta faru ban sani ba kuma ban ta'ba fahimtar hakan ba?".
"Bazaki gane ba Aunty Nasema amma wlh Abban Naheed ya canja hali fiye da yanda baki tunani".
"Kai ni wannan lamarin gaskiya bai min dad'i ba ko Daddyn Irfan za'a fadamawa,wata k'ila in aka yi sa'a in ya shiga cikin maganar ko a samu sauk'i".
"Ni wlh na gaji da saka Yayah a cikin lamarin Gidana tunda abun ya k'i ci ya k'i cinyewa".
"Oh ni ya Allah wannan lamarin ta ina zamu fuskance shi har mu kai ga samun maslahar?".
"Kin ga kar ki tada hankalinki in sha ALLAHU komi zai dai-daita da izininsa ,harma muci nasarar ganin k'arshen abin".
"Ameenn suma Ameenn,Nabeelah".
"Kin ga bari in tashi in tafi Gida kar yamma tayi,amma har zan tafi banga d'iyata ba?".
"Tana can tana barci,da kin zo mata da abokinta Naheed ai da ta fito".
"Yana can shi da Irfan da yike ya zo mana weakened,to shine fa ya d'auke masa hankali bai biyo ni ba, nasan da yanzu sunanan sun ishemu da bari-bari,don ni na rasa cikinsu waye yafi rashin ji",da haka suka gama hirar su ta yi mata bankwana ta tafi,k'arar da na fara ji tun farko ce ta sake maye gurbi a cikin kunnuwana,kwakwalwata sai faman had'a tunaninta wuri guda take ,don son gano wani abu mai muhimmanci acikin labarin da na saurara,duk a tunanina gami da haikace na ko akwai wani abu wanda ya shafe ni a cikin sa,a bad'ini da kuma zahiri na wannan labari ba wata alak'a tsakanina da duk wani wanda yake cikin wannan labarin.
Ihun k'aramar yarinya ne ya karad'e min kunnuwana tana faman kwala ma Momynta kira,wanda har hakan ya firgitani saboda ban yi tsanmani jin sa a dai-dai wannan lokacin ba,duk a tunanina record d'in ya k'are sosai hakan ya tsoratar da ni,kawarta kawai nake iya jiyowa sai daga bisani na jiyo muryar d'aya daga cikin matannan tana magana cikin yanayin jigata da wahalarwa,"Zain .....mun shiga ukku.....gashi can sun tafi da ita.... wayyooooo Allahna....Dan Allah kayi wani abu kar su tafi da ita.....ka dakatar da su".
"Kiyi hakuri Nasema...bazan iya ta'buka komi ba don sun rigada sun illatani in sha ALLAHU ba abinda zasu iya yi mata".
"Inalillahi wa'innan illaihirraju'una wlh bazan kyale su ba",alamun tafiyar,cikon yanayin han k'afa da alama ita ta raunatar,karfin haline kawai take dashi amma ta na ji a jikinta,sai dai tun kafin tayi nisa naji wata k'ara da ta firgitani,alamu kamar an kai mata duka da wani mabugi,k'ara ta saki mai k'arfin gaske,amma duk da haka ranta da zuciyarta na kan yarinyarta , yunk'uri take gami da ambaton sunanta tana cewa,"My Baby....Dan Allah kubar min ita kar ku tafi da ita...*MAHNOOR....MAHNOOR....... MAHNOOR*",daga haka sai naji d'if record d'in ya k'are,wanda daukewarsa yai dai-dai da daukewar wutar jikina sannan kuma kwakwalwata ta d'auke na wucin gadi haka ma duk wasu jijiyoyin jikina sun daina gudanar da aiki na wucin gadi,sai dana shafe Sama da sa'a guda ba tare da na iya yin kwakkwaran motsi ko tunanin guda d'aya ba mai amfani ba,sai can daga bisani na jawo wani littafi da biro da ke kusa da ni,na fara rubutu a hanzarce kamar wacce a ke jira ko makamancin haka sunayen duk wanda aka anbata a cikin Video record d'in na fara rubutawa da manyan bak'i gami da tsura masu idanu ,tamkar wacce aka tsikara haka na mik'e tsaye ina karanta sunayen da k'arfi tamkar mai shirin haddace su baki d'aya,karar bud'e k'ofar shigowa d'akin ne ya d'an jawo hankalina har na kai ga d'ago kaina domin in ga mai ke shirin faruwa,Nanny na ci karo da ita idanuwanta cike da barci,da sauri ta idasa shigo ciki tana mai cewa,"Subahanallahi Mahnoor me yake faruwa?".
Idanuwana da sukayi jajajur kawai na iya zuba mata ba tare da nayi yunk'urin iya ce mata komi ba, saboda na riga dana zama speechless,komi nawa ya d'auke na wucin gadi.
"Ki amsamin tambayata mana ,naje d'akinki na ga bakinan shine hankalina ya tashi na zo nan sai kuma gaki a cikin wannan halin,ki fad'a min wai me yake faruwa?".
Lura tayi da yanda jikina ke kyarma yasa ta tabbatar da ba lafiya ba,da sauri tayo kaina gami da jawoni jikinta,hankalinta gabad'aya tashi yayi bata k'ara cewa komi ba sai janyo ni tayi muka bar cikin d'akin,kai tsaye d'akinta ta kai ni, kusan yanda naga rana haka na ga dare don ko da wasa na kasa rintsawa Nanny ce ma ta tirsasa ni akan sai na kwanta wai hakan zai iya taimaka min don in samu inyi barci amma ina sai itace yake d'an sata lokaci zuwa lokaci........✍✍✍✍