HADIN KADDARA

Chapter 9

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                    By 

        AyshaNalado


Page 9


"Baa... Ba.... bangida." Haka ta dinga maimaita sunan a rarrabe idanunta Æ™em cikin nashi. Sake ta yayi ta tsaya kan kafafunta kallon cikin idanunta yayi kafin a hankali da t muryarshi mara hayaniya ya ce "Ki dinga kallon gabanki idan kina tafiya Miss." Jin sautin muryar shi yasa ta Æ™ara gwalalo idanu waje, a ruÉ—e ta sake ce wa"Baban gi daa." Girgiza kai yayi ya ce "Not Babangida, I'm Ahmad Kangiwa." Kafin ta sake cewa wani abu ta ga ya É—uka da sauri ya  dauki face cap da box É—in shi dake Æ™asa kafin tayi wani yunkuri ya bace É“at a wurin kamar walkiya, daidai time É—in kuma salmah ta iso ta da sauri ta rirriÆ™eta hankali tashe take ce wa "Sister me ya same ki, meke faruwa waye ya biyo ki garin yaya kika fito daga ciki mota?" Duk wannan tambayoyin da Salmah ke jero mata babu guda É—aya da ya shiga kunnenta, hanyar da ya bi Kawai ta Æ™urawa idanu babu abin da ke amsa kuwa a kunnenta sai muryar shi da ya ke  cewa "Not babangida, I'm Ahmad Kangiwa." Can kuma kamar zautacciya  ta  shiga cewa "shine, wlh shine Salmah Babangida ne."  Kafin Salmah ta kai ga tambayarta wani Babangidan wanene  ma Babangida, taga ta zabura tabi hanyar da yabi da mugun gudu, bata saurari kiran da Salmah ke mata ba ganin haka yasa ta rufa mata baya ita ma a guje tana ce wa  "Ya Ammar pls help me, na shiga ukuna." Jin haka yasa Ammar security da sauran maza je biyu da suka biyo ta É—azu suka sake rufa mata baya a guje.

Tana fitowa daga cikin wajen,  motar shi na barin compound É—in  wajen da mahaukacin gudu, zubewa ta yi akan gwiwowinta ta fashe da wani irin matsanancin kuka, tuni hankalin mutane ya dawo kanta wasu duk sun bar abinda suke yi sun zubo mata idanu, wasu ma har sun fara kwashewa a samu na yaÉ—awa a duniya, dai dai nan, su salmah suka Æ™araso inda take, da sauri Salmah da ke kuka ita ma hawaye bibbiyu ta tsuguna tare da rungume ta a jikinta,  cikin kuka take ce wa "Na haÉ—a ki da wanda rai da numfashin ki yake hannunsa ki tashi Aysha, duka idanun mutane yana kanki." A hankali take maganar amma kuma Cikin matsanancin kuka, rintse idanu Aysha ta yi ta tsayar da nata kuka tana sauraren na Salmah wanda take jin shi har cikin bangon zuciyarta, gaba É—aya jikinta yayi sanyi, a ranta taji babu daÉ—i yadda ta saka Salmah kuka bata ji ba bata gani ba, to ya zata yi itama abin ne yazo mata a bazata,  daure wa tayi ta saka dukkan karfinta ta danne zuciyarta, ta zare Salmah daga jikinta ta miÆ™e tsaye tare da miÆ™ar da ita, share mata hawaye tayi da hannunta, suka kalli juna, murmushin yake ta sakar mata don son kwantar mata da hankali, cikin muryarta irin na wanda yaci kuka ya gaji, ta ce "ki daina yi min asarar hawayenki masu daraja kinji salamatuna  mai..." Kafin ta kwai ga karashewa Salmah ta katseta da cewa " ta yaya kike tunanin hawaye zasu daina kwaranya a idanuna idan har zaki ringa shiga ciki irin wannan halin,wannan ba shine karon farko da kika taba yin irin hakan ba,na tambayeki sau babu adadi wanene shi kin ki ki gaya min ya kike so nayi da rayuwata ne A'isha."ta karashe maganar tare da fashewa da matsanancin kuka  hawaye na kwaranya a idanunta, kama hannayenta Aysha  ta yi, ba tare da ta tanka mata ba ta ja ta  suka nufi gurin da Ammar ya faka motar shi, mutane sai kallon ikon Allah suke, security ne suka shiga yima Ammar faÉ—a wai me yasa yake yawo da mai larurar hauka, yanzu da ta jima wani a gurin fa, shidai hakuri ya ringa basu don shima harga Allah ya tsorata, kuma ya yarda da maganar security É—in da suka ce ita É—in mai lalurar hauka ce, to idan ba hauka ba ta yaya mutum zai kama gudu shi kaÉ—ai.

A mota ya same su dukan su a gidan baya fuskokin kowacce su babu alamar fara'a salmah ta haÉ—a kai da kujera sai shehshekar kuka takeyi yayinda A'ishatu ta daga kanta tana kallon saman motar bayanta jingine da kujera, hawaye sai gudu suke a fuskarta a gefe guda kuma sheshshekar kukan Salmah na taÉ“a mata zuciya.   Jiki a sanyaye ya buÉ—e gaban ya shiga yaja motar suka bar wajen, har suka isa kofar gida babu wanda yace uffan, a cikin motar, a bakin get ya ajiye su, shiga cikin da yayi niyya ma tuni ya fasa don jikin shi ya mutu muruss, yana yin parking suka buÉ—e kofar suka fito Salmah ce tayi karfin halin zuwa wajen windo ta daidai saitin da yake ta ce "mungode yaya Ammar." Æ™aÆ™alo murmushi yayi ya sakar mata tare da cewa "ba komai Salmah ki gaida Ammi bazan samu shigowa ciki ba yanzu, naji anata kiraye kirayen sallah amma zan dawo ko gobe ko jibi na gaisheta." Gyada kai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba Koda ta É—ago A'ishatu har ta buÉ—e get ta shige, bin bayanta tayi jiki a sanyaye, har suka isa entrance  din part din Ammi babu wacce ta ce wa yar uwarta uffan, Salmah ce ta miÆ™a hannun zata dannan doorbell da sauri Aisha  ta riÆ™o mata hannun kallon juna sukayi cikin ido kowacce idanu jajur anci kuka an Æ™oshi, girgiza mata kai A'isha tayi, kafin kuma taja hannunta da sauri sauri suka nufi wajen bakin famfo dake daga gefe, wanda anyi shi ne don bama flowers ruwa, gane abin da take nufi yasa Salmah kwace hannunta, ta juya mata baya da sauri ta ce "Akan me kike so mu boye wannan maganar ga Ammi, ki sani anyi na farko kuma na karshe in dai  ni  baza ki iya gaya min wanene wannan mutumin nan ba,  ai ita nasan idan ta tuhumeki zaki gaya mata." Da sauri ta riÆ™o hannunta ta baya cikin yanayin tashin hankali tace "A'a Salmah A'a A'a don  Allah da manzonsa karki min haka." "Zan iya rufe wannan maganar akan maslaha  É—aya, idan kin amince yau zaki gaya min wanene *Babangida*." Shiri tayi tana sauke ajiyar zuciya, bata ce uffan ba kuma É“ata saki hannunta ba, ganin haka yasa ta fisge hannunta zata yi wucewarta da sauri ta sake riÆ™o hannun, cikin sanyin murya tace "Salmah bazan sanar dake wanenen Babangida domin sanin wanene shi bashi da amfani a gareki, babu abin da zai haifar miki sai bakin ciki da bacin rai da Æ™uncin zuciya." Ajiyar zuciya Salmah ta sauke tare da juyowa ta rungume ta, suka ci gaba da kuka,  cikin kukan Salmah ke cewa "saboda meye baza ki gaya min ba, shin bakyaso ki raba damuwarki da nine, a she har yanzu baki dauke ni Æ´ar uwa ba? ba wai na damu da son sani wani boyayyen sirrinki saboda komai bane sai don saboda soyayyar da nake miki, ina sonki soyayya irin ta jini , ina jinki a rai na har fiye da yadda nake jin Salman É—an uwan tagwaitakana, idan har ina miki irin wannan soyayyar ta yaya bazan so ganin farin cikin ki ba, ta yaya damuwarki bazai dameni ba, ina son na ganki watarana kina dariya mai amsa sunan dariya bawai wannan kalar dariyar da kike mana kullum ba wanda ni ce kadai na fahimci na yaÆ™e ne wanda yafi kuka ciwo, na fahimci rashin walwala da farin cikin ki  nada nasaba da Babangida tun ranar da kika faÉ—o hannun iyayena, ko kin san sau da yawa nasha laÉ“ewa na saurare ki kina kuka a toilet kina ambatan wasu maganganu da wani yare wanda bana iya ji, abinda Kawai nake iya ji a cikin zancenki shine Babangida, haka ma ciki barcin ki, kusan kullum a cikin barcin ki sai kin ambaci sunan Babangida ba tare da kema ki a sani ba, abin da ya faru rannan a green land har yau yana rai na bawai na manta bane shirya ta yadda zan tunkareki da zancen nake shine yauma kika sake maimaita abin da yafi wanda ya faru ranar kuma duk a silar Babangida, to na gaji ina son sanin wanenen Babangida."  Tana gama faÉ—in haka ta É—uka ta tari ruwa ta wanke fuskarta ba tare da ta jira Aisha ba ta wuce abinta.

Girgiza kai tayi tana jin wani irin abu na sukarta a zuciya, ta fi minti biyu a tsaye tana bin hanyar da Salmah tabi da idanu kafin ta duÆ™a itama ta tari ruwa ta wanke nata fuskar, ta bi bayan ta , a falo  ta samu Ammi da  Salmah, tana shiga duk suka zuba mata idanu hakan yasa gabanta ya yanke ya shiga faduwa, duk da bata tunanin  Salmah ta gaya wa Ammi wani abu gama da abin da ya faru. Cikin sanyin muryata wanda yadan dashe saboda kuka ta ce "Ammi mun dawo." bata amsata ba sai cewa da tayi, "zo nan kema." Zuwa  tayi gabanta, ta tsuguna, cikin ido Ammi ta kalleta kafin tace "shin ina kuka tsaya bayan hajiya turai tace min tun tuni kuna hanya kuma mai ya samu idanunku kukan me kuka yi." Rasss gaban A'ishatu ya faÉ—i koda wasa baza taso  Ammi tasan abin da ya faru ba, kuma ita baza ta iya ma Ammi karya ba, ta yaya zata yi karya bayan ga Salmah a wajen  É—agowa tayi ta kalli Salmah cikin sa'a itama Salmah ta kalleta  haÉ—a idanu sukayi,  da idanu tayi mata alamar roko akan karta gayawa Ammi komai, dauke kai Salmah tayi tace "Ammi na riga na gaya miki accident muka samu me napep dinmu ya buge wata yarinya, duk taji ciwo gwanin tausayin shine ma abin da ya saka mu kuka, Ammi naga kamar baki yarda dani ba to A'ishatu ke da ta fi yarda da ke ki mata bayani." Da sauri A'ishatu tace "eh haka ne Ammi yarinya karama abin tausayi Ammi sai da muka jira ya kaita asibiti mafi kusa a ka yi mata magani  sannan ya karaso damu gida." Cikin tausayawa Ammi tace "Allah sarki yanzu ina yarinyar?" Salmah tace "tana gurin iyayenta ciwon da sauki Æ™ujewa ne, a hannun da gefen fuska." Ammi tace "Allah ya bata lafiya Allah ya kiyaye na gaba." Har suna hada baki wurin amsawa da amin  , ta ce "ku tashi kuje kuyi sallah gashi nan har an kusa idarwa a masallatai." Ita ce ta fara mikewa ta nufi É—akinta, sai da ta kulewa ganin su Salmah ta mike ba tare da ta kalli inda A'ishatu take ba ta bar wajen, sauke ajiyar zuciya tayi, kafin itama jiki a sanyaye ta mike tabi bayan Salmah.

Haka suka karkare cinye dan sauran yinin ba tare da Kalmar A ta kuma shiga tsakanin su ba, fushi sosai Salmah take yi da ita wanda ko haÉ—a ido taki bata damar suyi, maganar duniya Aysha ta mata amma ta danne zuciyarta taki tankawa, damuwa goma da ishirin suka taru suka mata caa, kan kace koba zazzabi na neman rufeta, Salmah tsab ta fahimci ce ta, tausayinta ya riga ya gama karshe zuciyarta amma dole  ta danne na É—an wani lokacin idan tayi da fushin taga babu  riba zata sauko ta koma da rarrashi wata kila ta dace, har Ammi da Salman sai da suka so fahimtar yau kamar da matsala a tsakaninsu ko wani abu na  damun su, Salman ne ya kasa hakuri ya jeho musu tambayar "wai yau meke damun ku ne, Æ´an mata, naga kunyi wani irin kamar Baku cikin walwala." Ammi ce ta bashi labari haÉ—arin da suka samu yau, shima ya tausayawa kwarai yayi jimami, koda suka zo kwanciya baya Salmah ta juya mata tare da daukar wani bargo dabam bata shiga wanda suke amfani dashi tare ba, abin yayi wa Aysha  ciwo, gefe daya ga tunanin  Ahmad kangiwa daya ke ta azalzalan zuciyarta nan kuma ga Salmah na kokarin haifar mata da ciwon kai, duk shuru sukayi a kwance babu wacce ta iya rintsawa a cikin su  abu ne da bai taÉ“a faruwa ba tun tasowar su, samun sabani a tsakanin su, daren yau yazo musu a baibai, kasa daurewa Aysha tayi duk kuwa dauriya da jarumtarta, a hankali shehshekar kukanta ya fara karaÉ—e É—akin nasu,  Salmah na jinta amma ta share ta bata tanka ba, don ta fahimci ta fara laushi, tana da tabbacin idan ta daure zataci galaba akan ta,  tayi kuka yafi na 30 minute kafin kuma a hankali ta kira sunan Salmah, shareta ta yi wannan karon ma, cikin dasasshiyar murya tace "nasan kina jina Salmah kiyi hakuri ki fahimce ni." Yaye zanin rufa Salmah tayi ta  miÆ™e daga kwancen da take ta zauna bakin gado tare da   sauke kafafun ta kasa, cikin  yanayin nuna fushi da bacin rai tace "hakurin me kike bani A'ishatu, babu komai ai rayuwa ce, yau kin nuna min cewa ke ba yar uwata ta jini bane ashe ni kadai nake haukana ke baki dauke ni a yadda na dauke ki ba, zanyi kokari na cireki a zuciyata zanyi kokarin na sauke ki daga matsayin da na daura ki a cikin zuciyata." A hankali ta tashi daga kwance ita ma, ta bayan ta ta tsaya ta miÆ™a hannunta ta daura akan kafadar ta, cikin dasassiyar murya tace "ban ki gaya miki tarihin rayuwata saboda wata manufa ba sai dan kuje miki shiga damuwa, da tarwatsa miki zuciya da cusa miki tsanar  Kalmar so, da duk wani abin da ya shafi  soyayya a rayuwarki, labarina zai saka miki tsanar duk wani É—a namiji a rayuwar duniyar nan." Shuru tayi ta É—an  nisa kafin ta ci gaba da cewa "cikakken sunana A'ishatu Muhammad Lawal........"