TURMIN DANYA
by @hilfat
Ruwan da suka sheƙa mata ne a jikinta ya sanya ta farkawa a gigice tana sauke wata wawuyar ajiyar zuciya. Take jikinta ya hau kakkarwa kamar mazari sakamakon ruwan na da azabar sanyi ga kuma muƙu-muƙun da ake yi, sai ta fara ƙoƙarin miƙewa tsaye sai dai ta ji ko gezau bata yi ba domin ko ɗan yatsanta ba za ta iya motsawa ba sakamakon ɗaurin huhun goron da ta sha jikin kujerar da take kai, ta hau kici-kici amma a banza man kare. Sai lokacin ne ta shiga ƙarewa inda take kallo, kafin idanunta suka sauka a kan basamudan mutanen da suke tsaye ƙiƙam a kanta sun zubo mata maganansu, dukkan su sun murtuƙe fuska tamkar magribar ɗinya babu alamun ɗigon imani a tattare da su.
Sai lokacin ƙwaƙwalwarta ta shiga dawo mata da dalilin wanzuwarta a wurin daki-daki. Ta runtse idanunta da ƙarfi. 'Tabbas na san dama a rina an saci zanin mahaukaciya, amma alƙawari ne na ɗauka wa kaina kuma duk wuya duk rintsi na yi zaman turmin dinya a bisa bigiren da aka dasa shi kan cimma abin da na saka a gaba koda za a daddatsa naman jikina' Ta raya a ran ta.
Fincike baƙin gam ɗin da yake liƙe a bakinta da aka yi shi ya dawo da ita daga taƙaitaccen tunanin da ta tafi. Ta yi 'yar ƙarar azaba domin ba a yi mata a hankali ba. "Ki gaggauta ba mu duk wasu bayanai da shaidu da kika tattara idan ba haka ba sai na lahira ya fi ki jin daɗi." Cewar babbansu, babu alamun wasa a fuskarsa, ta masa wani irin kallo kafin ta buɗi baki ta ce "Ban gane a kan me kake magana ba."
Bai tanka mata ba ya kalli na kusa da shi. Bata yi aune ba sai ji ta yi ya damƙi gashin kainta kafin ya sa ƙarfi ya fara dukan bakinta. Azaba ta sanya ta rintse ido ta fara ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ta kasa, ji take yi kamar ba a duniyar take ba. Shi kam bakin nata kamar ba a jikinta yake ba haka take ji. Take jiri ya fara kwasarta, jini kuwa tuni ya gama wanke mata gaban doguwar riga ruwan madara da take jikinta.
"Har yanzu ba ki fahimci me nake magana a kai ba ko? Wannan ba iya tunaninki ba ne, ke da su waye ke shirin tono sirrin da muka ɗauki lokaci muna binnewa a doron ƙasa? Ina mai tabbatar miki za ki yi dana sani mai girma, domin allura ce za ta tono garma, wuƙa ce kike shirin daɓa wa kanki da kan ki, da ma kaza garin tone-tone take tono wuƙar yanka ta."
Numfashinta na fita da ƙyar ta fara ƙoƙarin magana "Ko za ku kashe ni ba zan taɓa ba ku bayanan da na ɗau lokaci mai tsayi ina ƙoƙarin haɗawa ba, domin ni ba raguwa ba ce ballantana barazanarku ta tsorata ni, kuma ni kaɗai nake gudanar da aikina ba tare da taimakon kowa ba, aikina na saida rai ne na yarda na mutu ko na rayu domin kawo ƙarshen matsalar da ta addabi al'ummar ƙasata."
"Hahhhhh ba ki daku ba ne, idan kin ji wahala ai za ki magantu." Ya kuma faɗa, ba ta san ya iso gabanta ba sai ji ta yi an ɗaga fuskarta kafin aka buɗe bakinta ta ƙarfi, wani irin ƙarfe ne a hannunsa ya zura cikin bakinta sai ji ta yi yana ƙoƙarin cizgo mata haƙori, tun daga jijiyar idonta zuwa kanta ne ya amsa take jikinta ya ɗau karkarwa, jin fincike mata haƙori daga bakinta ya yi silar ɗaukewar jinta da ganinta, daga nan ba ta kuma sanin a duniyar
da take ciki ba....
*** *** ***
Zaune take ta barbaza takaddu a gabanta tana bin su ɗaya bayan ɗaya tana dubawa. Littafin da take rubutu ta janyo ta haɗa da wata takadda sannan ta fara tattare takaddun. Kwashe su ta yi zuwa inda ta ciro su sannan ta mayar da hankali tana kwafar rubutu daga jikin takaddar zuwa cikin littafin.
Jin motsin shigowa ya sanya ta kai kallonta bakin ƙofar. Sai ta miƙe da sauri bayan ta ajiye abubuwan hannunta ta nufe shi, tana zuwa ta rungume shi cike da jin daɗin ganin shi. "Barka da dawowa daddyna"
Shi ma murmushin ya saki yana dafa kanta kafin ya ce "Yawwa maman daddy ana nan ana ta fama ko?"
Ya ƙarasa yana murmushi, itama murmushin ta yi ba ta ce komai ba.
"To Allah ya taimaka"
"Amin daddyna"
Ina Mamyn naki ban ji ɗuriyarta ba" Ya ce yana leƙen fuskarta, sakin shi ta yi ta juya ta kalli bayanta, kafin ta nuna masa ita da hannu, shi ma wurin ya kalla sai kuwa karaf suka haɗa ido da ita tsaye a ƙafar bene ta biyun ƙarshe ta harɗe hannunwanta a ƙirji tana murmushi itama.
"Au yo ai ni ko motsin sakkowarki ban ji ba, balle na gan ki" Ya faɗa yana ƙarasa wa cikin falon ya tallaɓo ta a jikin shi. Itama ta ƙarasa sakkowa ta zauna tana faɗin "Yo ai kai Alhaji indai kana tare da Nuratu baka ji ba ka gani."
Murmushi ya yi kafin ya ce "To kin ga laifina Iyami? Uwar masu gida take fa, ko ba haka ba mamana?" Sunkuyar da kai kawai ta yi tana cigaba da murmushin.
"Alhaji abincin ne ko wankan?" Hajiya Iyami ta tambaya fuskarta a kan shi. "A'a wankan dai, idan na yi sai mu ci abincin. Ina yaron nan ne Nura ko bai shigo ba?" Cewar Alhajin. "Bai shigo ba tukunna duk inda yake dai yana hanya yanzu tunda magriba ta yi." Ta ba shi amsa, bai kuma magana ba ya miƙe ya haura saman, ita ma ta rufa masa baya. Nuratun kuma ta koma kan aikin da take yi kamar daga sama ta jiyo maganarsa yana nufo falon yana waƙa "Ke kika san kisisinar da za ki yi wa saurayi ko angon ki in ya biɗo komai ya ba ki warrrr. (Baitin waƙar ado gwanja ta warrr)"
"To fa Allah ya masa dawowa yanzu zai zo ya takura mini" Ta faɗa a fili, daidai lokacin ya ƙarasa shigowa falon yana tafiya yana kwarkwasa "Me kike cewa ne?" Ya faɗa yana riƙe ƙugu. Matashi ne da a ƙalla zai kai shekaru ashirin da bakwai. Dogo ne mara jiki, fuskar nan tashi ya ci mai har da ƙananun ƙuraje, kamarsu ɗaya da Nuratun. Jikinsa Jallabiyya ce fara, ya ɗaura kallabi a kan sa.
"Ni babu abin da na ce" Ta faɗa tana tura baki "Ƙarya kike yi kin yi magana kuma daga ji gulmata kika yi ai kin saba, kuma wallahi ki kiyaye ni kafin na yi ƙuli-ƙulin kubra da ke." Ya ƙarasa da tura ɗankwalin kansa gaban goshi, sai kuma ya yi gaba bayan ya sa ƙafa ya wargaza takaddun ya kuma bi ta kai ya shige ciki abinsa.
Cike da jim haushi ta bi shi da kallo ganin ya zauna a kujera "Ko za a saka mini duka ne?" Ya ƙarasa yana girgiza ƙafa, ba ta kuma bi ta kan sa ba ta fara tattara takaddun, tsaki ya ja kafin ya ƙara da "Aikin kenan ke kullum abu ɗaya ko gajiya ba kya yi daga wannan ki koma wannan, maza ki je ƙwaƙwalwarki ta tarwatse a aikin banza, kuma wallahi tsufa za ki yi da wuri kina tarawa kan ki aiki ato ni dai babu abin da ya shalle ni."
Duk cikin maganarsa ta ƴan daudu yake yi da ya dage ta ƙarfi sai ta koma maganar mata, yana yi yana tauna cingam gami da yin ƙwai da shi. Tana gama tattare takaddun ta nufi ɗakinta sai da ta shiga sannan ta ziro kai ta ce "Ai wallahi gara ni sau dubu a kan ka, Allah ya yo mutum a halittar maza sannan ya ce sai ya mayar da kan shi mace ta ƙarfi da yaji kaico, kuma ai ba a taɓa canjawa tuwo suna" Zabura ya yi ya nufo ta, ba shiri ta datse ƙofar.
"Ai da kin bari na iso wurin, wallahi ban ƙi na tuɓe mu dambatu ni da ke ba kuma ko a kwalar rigata."
"To Allah ya maka dawowa ko? Tun ɗazu nake jiyo maganarka sama-sama ai." In ji Hajiya Nuratu tana saukowa ƙasan, Alhajin na biye da ita a baya. Sosa kai ya hau yi, sai kuma ya yi farrr da ido "Ni da Nuratu ne rashon kunya take yi mini kuma wallahi ta ji gaba ni da ita ɗan halak ka fasa." Ya ƙarasa yana hararar ƙofar ɗakin nata bayan ya zungura baki gaba
"Ai kai ne ba ka jan girmanka wani lokaci, kai ke takalo ta." Cewar Daddyn yana nufar danning table ɗin. "Kirawo ta ta fito mu ci abinci" Ya kuma faɗa. "A'a daddy ni sai na yi wanka tukunna, ka gan ni yanzun nan na shigo gidan duk warin rana nake yi" yana maganar da yatsunsa guda biyu a haɗe yana girgiza su. Sai ya juya ya doshi ɗakinsa yana rangwaɗa. "Allah ka shirya mana." Cewar Mamyn. "Amin dai, kira ta a waya ta fito mu fara ci, don ba za mu jira shi ba" Daddy ya faɗa. "Aikam dai, don kuwa kafinya gama ƙalƙale-ƙalƙalen ya fito ma aiki ne, a kai awa guda." Mamyn ta faɗa tana ciro waya domin kiran Nuratun....!
Comment and share pls