RAYUWAR DA NA ZAƁA

Part 02

by @hussainyusuf

RAYUWAR DA NA ZABA 

Part 02...

​Na jefar da wayar a kan gado, numfashina ya rinƙa fita sama-sama. Kalaman Alhaji Sani suka tsaya min a rai kamar ƙashi a maƙoshi. Wannan wacce irin takurawa ce? Mutumin da duniya ta yi masa shaidar rashin mutunci, da neman mata, amma don kawai yana da abin hannu kuma ni shekaruna sun ja a gida shi ya sa iyayena suke ganin auren nasa shi ne kwanciyar hankalinsu.
​Washegari da safe, tun kafin na fito daga daki, na jiyo muryar Babana a tsakar gida yana kiran sunana cikin fushi.
​“Ina Maryamu take? Ki fito nan yanzu ki same ni!”
​Na fito jikina yana rawa, na samu Baban zaune kan kujerarsa da yake zama a tsakar gida, Inna kuma tana gefe tana tsintar shinkafa, amma idonta yana kaina..
​“Gani Baba,” na fada muryata can kasa-kasa.
​“Yau Alhaji Sani ya kira ni. Ya ce ya gaji da jan ajin da kike masa. Maryamu, ki saurare ni da kyau ki ji, maganar gaskiya zuwa yanzu hakurinmu ya gama ƙarewa. Ki duba gaba daya kawayenki babu wacce ba ta yi aure ba, har kannenki ma aure za a fara shirin yi musu. Ke kaɗai a cikin gidan nan kin zame  mana alakakai, mun rasa yadda za mu yi da ke. To bari ki ji, idan har kika kuskura kika bijirewa wannan auren naki da Alhaji Sani, to ba ni ba ke har abada, kuma ki nemi wani uban amma ba ni ba!”
​Wani daci ya ziyarci makogwarona. "Baba, Alhaji Sani fa ba mutumin kirki ba ne. Kowa ya san halinsa, yadda yake wulakanta mata..."
​“Rufewa mutane baki shashashar banza!” Inna ta daka min tsawa. “Wulakancin me zai miki wanda ba za ki iya jurewa ba? Yana da kuɗi, sutura da abinci ba za su taba yanke miki ba. Ko kina so ki zauna ne har sai kin tsofe a gida? Kina ganin dai yadda mutane suke ta faman maganarki a unguwar nan? Har tsegumi ake wai ko ’yar madigo ce ke, ko kuma kin taba yin barin ciki shi ya sa kika rasa miji!”
​Kalaman Inna suka soke ni har can cikin zuciyata kamar an caka min mashi mai kaifi. Na fashe da kukan bakin ciki. "Inna har da ku ake zargin mutuncina don kawai Allah bai kawo min miji da wuri ba?"
​“Mu dai mun gama magana.” Baba ya faɗa, yayin da ya mike tsaye yana saka takalmansa. “Gobe magabatansa za su zo su kawo kayan baiko. Kuma ba na son jin wata magana.”
​Na koma daki na fada kan gado, saboda tsabar kuka har idanuna sai da suka kumbura. Na ji na tsani kaina, na tsani rayuwar gaba ɗaya, har ma na fara nadamar karatun da na yi da aikin da nake yi. Shin da gaske ne aure shi ne kadai ma'aunin mutuncin 'ya mace a duniyar nan?
​Ina cikin wannan halin, wata abokiyar aikina, Hafsat, ta kira ni. Na fada mata komai cikin muryar kuka mai tsuma zuciya.
“Maryamu,” ta kira sunana cikin sanyin murya. “Kada ki taɓa yarda ki auri mutumin da kika san zai ruguza miki rayuwa don kawai tsoron maganar mutane. Amma kuma, ya za ki yi da maganar Baba?" Nan take ​zuciyata ta rarrabu gida biyu. Can kuma, wani tunani ya fado min. Akwai wani tsohon abokin karatuna, mai suna Umar, wanda ya dade yana sona amma saboda talaucinsa, ban taba kawo shi gida ba don kar Inna ta wulakanta shi.
​Na dauki wayata na duba lambarsa. Shin zan kira shi mu kulla wata yarjejeniya ne? Ko kuwa zan mika wuya ga kaddarar Alhaji Sani?
​Ban kai ga yanke shawara ba, sako ya shigo wayata daga wata lamba da ban sani ba, “Kada ki damu da damuwar da kike ciki a yanzu, domin wanda kike gudu shi ne zai zama sanadin alherinki, amma ba yadda kike tunani ba.”
​Na zaro ido. Wanene wannan? Kuma ta yaya ya san halin da nake ciki?


​Ku biyo ni a Kashi na 3 don jin yadda zata kaya...

Hussain Yusuf✍️