Part 03
RAYUWAR DA NA ZABA
Part 03...
A daren ranar ban rintsa ba ko kaɗan. Sakon nan da na gani ya rikita min lissafi gaba daya. Wane ne yake bibiyar rayuwata har yake sanin halin da nake ciki? Na juye nan, na juye can, amma zuciyata ta gaza ba ni amsa. Ga kuma tsoron abin da zai faru washegari ya mamaye min zuciyata.
Tun kafin ƙarfe goma na safe Inna ta sa aka share tsakar gidan tas, aka shimfida tabarmi a babban dakin baƙ. Kamshin turaren wuta ya gauraye ko'ina, amma a gare ni, wannan kamshin kamar na turaren gawa ne.
“Maryamu! Taso ki zo ki gyara fuskarki mana!” Inna ta shigo dakin tana harara ta. “Don Allah dubi yadda kika wani saki jiki, kamar wadda aka zare wa laka. Maryamu yakamata ki hsani fa, Alhaji Sani ba karamin mutum ba ne. Idan ya ganki a hakan zai iya fasa auren, kuma wallahi idan ya fasa, ni da ke ne a cikin gidan nan!”
Na tashi ba dan raina ya so ba. Na mulke fuskata da hoda, na saka leshina mai tsada, amma da na duba madubi, wata baquwar mace nake gani. Macen da aka sace mata farin ciki, aka mayar da ita tamkar wata haja..
Ina cikin kintsa kaina, na ji muryoyin maza a waje. Sun iso. Gabana ya fadi, ya rinƙa dukan uku-uku, na ji jikina ya shiga rawa kamar mazari.
Bayan kusan awa daya da shigowar mazan, Inna ta shigo dakin tana washe baki, hannunta rike da wasu damin kudi da ledoji na gani ta fada.
“Alhamdulillah! Maryamu ke kam kin yi arziƙi, ashe wani jinkirin alkhairi ne, har an riga an gama magana. An karbi kayan baiko, an saka bikin wata daya kacal! Saboda Alhaji ya ce ba ya son ɓata lokaci. Dubi wadannan kudaden, naki ne iya na gyaran jiki.”
Na kalli kudin, maimakon in ji dadi, sai na ji kaina yana neman sara mini da ciwo. “Inna, don Allah...”
“Kar ki kuskura ki ce komai!” Ta katse ni. “Yanzu haka ma Alhaji Sani yana waje, ya ce yana son ganinki kafin su wuce. Fito maza ki je ki same shi!”
Na fito jikina a sanyaye. Alhaji Sani yana tsaye kusa da motarsa ta alfarma, yana kallona da wasu jajayen idanunsa yayin da nake kusanto inda yake. Da na ƙarasa, bai ko amsa gaisuwar da nake yi masa ba, ya kalle ni sama da kasa sannan ya ce,
“Kin gani ko? Na gaya miki karshen kurege gidan maza. Yanzu dai tunda an riga an yi baiko har an saka rana ina so ki san sharaɗina guda ɗaya tun kafin a kai ki gidana. Daga ranar da aka kaiki cikin gidana, maganar aikin ofis ta ƙare. Ba zan auri mace tana yawo ana kalle min ita ba. Kuma wayar nan taki, zan canja miki ita, zan ba ki ƙarama wadda za ki rinka kiran iya yan gidanku."
Wani irin ɗaci ya mamaye zuciyata. Aikina? Abin da na sha wahala na yi karatu akai? Shi ne zai rushe a rana daya?
“Amma Alhaji...”
“Ba wani amma! In har kina son zaman lafiya, to ki bi umarnina kawai.” Ya fada yana wani murmushin mugunta, sannan ya shiga motarsa ya tayar da ita, ya yi tafiyarsa.
Ina tsaye ina hango ƙurar motarsa, sai ga wata baƙar mota ta faka a kofar gidanmu. Wani matashin saurayi ne ya fito kyakkyawa da shi, sanye yake da kananan kaya waɗanda suka yi masa kyau sosai. Ya kalle ni, ya dade yana kallona kafin ya tako ya ƙaraso kusa da ni.
“Sannunki dai ƴan mata, nan ne gidan Malam Usman?” Ya tambaya cikin muryar da na tabbata na taba ji, amma na rasa a inda na taɓa ji..
Na gyada masa kai, ina mamakin wane ne shi. Ya yi murmushi, ya miko min wata takarda a ninke. “Wannan taki ce Maryam. Kuma game da saƙon daren jiya... har yanzu ina nan a kan bakana.”
Na zaro ido. Shi ne? Amma ta yaya? Ban taba ganinsa ba! Kafin in yi magana, ya juya ya shiga motarsa ya bar gurin da sauri.
Na bude takardar da sauri, rubutun ciki ya sa zuciyata bugawa da karfi, “Alhaji Sani ba shi ne mijinki ba. Akwai sirrin da kika daɗe ba ki sani ba game da mahaifinki da Alhaji Sani. Idan kina son sanin gaskiya, ki same ni a...”
Wane sirri ne yake tsakanin mahaifina da Alhaji Sani? Kuma wanene wannan saurayin da yake kokarin ruguza shirin auren da aka riga aka sa rana?
Ku biyo ni a Kashi na 4 don jin yadda zata kaya...
Hussain Yusuf✍️