Part 04
RAYUWAR DA NA ZABA
Part 04..
Hannuna yana ɗan rawa na matse takardar a tafin hannuna. Ƙamshin turaren saurayin nan ya tsaya a hancina, amma fargabar abin da na karanta ta fi komai ruɗani. Wanne irin sirri ne zai haɗa mahaifina, mutumin da nake gani a matsayin madubin gaskiya, da mutum irin Alhaji Sani?
Na koma daki na fada kan gado, zuciyata tana bugawa kamar za ta fito. Inna ta shigo tana washe baki, ta ɗauki damin kudin da Alhaji Sani ya ba ni, ta fara ƙirgawa.
"Lallai Maryamu kin yi katari! Dubi dukiya, dubi naira. Ai ko kishiyoyinki sai sun san ke ta daban ce a wajen Alhaji, saboda ba ki ga yadda yake ta zumuɗi a kanki ba. Hakurin da kika yi shi ya kawo miki wannan babban rabon.
Na kalli Inna, idanuna suka cika da hawaye, "Inna, kudi ne kawai ma'aunin farin ciki a wajenku? Ba ku damu da irin zaman da zan yi da shi ba? Alhaji Sani ya ce sai na bar aiki, kuma zai hana ni hulɗa da kowa."
Inna ta tabe baki, "Aikin me kike yi da ba za ki bari ba? Dubi kudin nan, albashinki na shekara biyu ne fa a hannuna yanzu. Zaman daɗi zaki yi Maryamu, ki huta, ki ci kaji, ki sha madara son ranki. Mu dai fatanmu daya a yanzu; shi ne a yi auren nan mu huta da surutun mutane."
Ta fice tana rera wakar murna, ni kuma na bude takardar saurayin nan na sake karantawa. Wajen da ya ce in hadu da shi wani babban restaurant ne da yake gefen garinmu. Na san idan na fita a halin yanzu, Inna za ta zarge ni. Amma dole ne na san zan yi.
Washegari, na yi amfani da damar cewa zan je ofis don mika takardar ajiye aiki (resignation) kamar yadda Alhaji Sani ya buƙata, ko da yake karya nake yi, kawai ina son samun hanyar fita ne.
Ina isa gurin, na iske saurayin nan zaune a daya daga cikin kujerun restaurant ɗin, ya saka baƙin gilashi. Da na ƙarasa, ya cire gilashin, idanunsa cike da alamun tausayi.
"Maryam sannu da zuwa. Na san a halin kina cikin rudani sosai," in ji shi.
"Wanene kai? Kuma me kake nufi da maganar mahaifina?" Na tambaya cikin sauri, ban ma zauna ba.
Ya yi gyaran murya ya ce na zauna, ban yi masa gardama ba na zauna, ya sa aka kawo mana lemo mai sanyi.. Tsiyayawa ya yi a wani ɗan ƙaramin kofi ya kurɓa sau ɗaya sannan ya kalle ni ya ce, "Suna na Khalid. Ni dan uwan tsohon abokin kasuwancin mahaifinki ne. Shekaru biyar da suka wuce, mahaifinki ya shiga wani babban basussuka na harkar kasuwanci. Alhaji Sani ne ya biya masa wannan bashin, amma da sharadi daya..."
Ya yi shiru, ya kalle ni sosai. "Sharadin shi ne; idan lokacin da Alhaji Sani yake so ya ƙara aure ya yi, mahaifinki zai ba shi ke a matsayin biyan wannan bashin. Mahaifinki ya sayar da ke ne ga Alhaji Sani, don ya biya bashin da yake kansa."
Nan take na ga duniyar tana juya min. Jiri ya kwashe ni na dafe teburin da yake gabana "Ƙarya kake yi! Babana ba zai taba yi min haka ba. Yana sona, ba zai sayar da ni ba kamar wata haja!"
Khalid ya zaro wasu takardu daga jakarsa ya ajiye a gabana. "Wadannan takardun yarjejeniyar ne da sa hannun mahaifinki. Alhaji Sani yana amfani da wannan damar ne don ya ƙuntata miki, domin ya san ba kya son sa ko kaɗan. Kuma babban abin takaicin shi ne, Alhaji Sani yana da niyyar amfani da ke ne kawai don ya samu wani babban fili da yake ɗauke da sunanki wanda kakanki ya bari, wanda kudin sa ya ninka bashin da yake bin mahaifinki."
Na ji wani sanyi ya ratsa jikina. Ashe duk takuran nan, duk kukan nan da nake yi, makirci ne aka hada min? Ashe mahaifina ne ya jefa ni a wannan gararin?
"Me ya sa kake gaya min wannan?" Na tambaya ina kuka.
Khalid ya gyara zama, "Saboda ni ma ina da nawa lissafin da Alhaji Sani. Kuma ina so na taimake ki ki kubuta. Amma fa, akwai hadari. Idan kika ki auren nan, Alhaji Sani zai kai mahaifinki gidan yari."
Zuciyar Maryam ta buga da ƙarfi...
Ku biyo ni a Kashi na 5 don jin yadda zata kaya...
Hussain Yusuf✍️