RAYUWAR DA NA ZAƁA

Part 05

by @hussainyusuf

RAYUWAR DA NA ZABA 

Part 05...

​Na fito daga restaurant ɗin ina tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Ƙafafuna ba sa iya dauka na, tunanina ya cushe gaba ɗaya. Kalaman Khalid suna ta kai kawo a ƙwaƙwalwata. "Mahaifinki ya sayar da ke ne ga Alhaji Sani don ya biya bashin da yake kansa." Wannan jumlar ta fi harbar min zuciya kamar an harba min kibiya. Na daɗe ina jin haushin kaina a kan rashin aure, ashe asalin matsalar ba daga gare ni take ba, makirci ne na wasu mutane da nake kallon su a matsayin garkuwata.
​Ina isa gida, na iske tsakar gidanmu cike da mata, ƴan'uwa da ƙawayen Inna ne suka zo taya ta murnar ganin kayan lefen da Alhaji Sani ya aiko. Akwatuna ne guda goma sha biyu, kowanne yana dauke da dukiya ta gani ta fada.
​“Masha Allah! Maryamu kin ga kayan arziki?” Daya daga cikin matan ta fada tana washe baki tana kallona. “Wannan ai sai wadda Allah Ya zaba wa miji mai hannu da shuni. Dubi leshi, dubi gwalagwalai. Gaskiya ke dai Allah Ya hutar da ke daga wahalar rayuwar nan.." 
​Na kalli akwatunan, na kalli fuskokin matan da suke ta zumudi suna farin ciki, sai na ji wani irin haushi da takaici sun ziyarce ni. Suna murna ne domin suna ganin kudi, amma ba su san cewa wadannan akwatunan tamkar sarka ce ta zinare da za a daure ni da ita ba.
​Na wuce daki ba tare da na ce musu uffan ba. Inna ta biyo ni da sauri, fuskarta a murtuke. “Ke Maryamu! Wane irin kalar wulakanci ne wannan? Mutane sun zo taya mu murna amma kina wani yamutsa fuska, kina yi musu wani irin kallo? Ko dai har yanzu wannan banzan kukan kike yi?”
​“Inna,” na kira sunanta cikin rawar murya. “Shin Baba ya gaya muku dalilin da ya sa yake son in auri Alhaji Sani lallai-lallai?”
​Inna ta danyi shiru, kwayar idonta ta juya ta yi ja, sannan ta ce, “Don ya ga yana da kudi mana, kuma ya ga lokacinki yana ta kurewa. Me kike nufi?”
​“Inna, bashi ne. Baba ya sayar da ni tun shekaru biyar da suka wuce!” Na fada ina kuka mai radadi.
​Wani mugun mari Inna ta sakar min wanda ya sa na ga taurari a cikin idanuna. “Rufewa mutane baki! sha-sha-sha kawai. Don ubanki yana ta ƙoƙarin yi miki gata zai aurar da ke ga mai kudi shi ne zaki fito da wani sharri? Wallahi idan kika na sake jin irin maganar nan a bakinki, sai na sa ya fasa miki baki a gidan nan!”
​Ta fice daga ɗakin da sauri tana huci. Na dafe kuncina, zafi yana ratsa ni amma zafin zuciyata ya fi na kuncina raɗaɗi. A lokacin ne na fahimci cewa ba ni da wani mai taimako a cikin gidan nan. Kowa idonsa ya rufe da kudin Alhaji Sani.
​Na dauki wayata na kira Khalid. “Na amince. Zan yi duk abin da kake so mu yi don in bankado gaskiya. Amma ta yaya zan dakatar da wannan auren? Sati uku ne kacal suka rage.”
​Muryar Khalid ta fito a sanyaye, “Akwai hanyar da zamu bi, amma sai kin yi amfani da dabararku irin ta mata. Alhaji Sani yana da wani babban taro da zai yi a karshen makon nan, inda dukkan manyan abokansa da gwamnati za su hallara. Za mu yi amfani da wannan damar domin nemo wasu abubuwa masu muhimmanci. Amma kafin nan, ina son ki hadu da wata mata... matarsa ce ta farko wadda ya kora bayan ya karbe mata gaba ɗaya dukiyarta.”
​Gabana ya fadi. Ashe Alhaji Sani haka yake? Ya riga ya lalata rayuwar wata macen, yanzu kuma kaina ya dawo?
​Ina shirin ajiye wayar, sai na ji muryar Baba a bakin kofa. “Da wa kike magana, Maryamu?”
​Na tsorata matuka, wayar ta fadi daga hannuna. Baba ya karaso cikin dakin, idanunsa sun yi jawur kamar garwashin wuta. Ya dauki wayar ya kalle ta, sannan ya kalle ni.
​“Ashe bincike kike yi a kaina? Ashe kin fara sauraron muryoyin makiyana?”
​Ku biyo ni a Kashi na 6 don jin yadda zata kaya...

Hussain Yusuf✍️