RAYUWAR DA NA ZAƁA

Part 06

by @hussainyusuf

RAYUWAR DA NA ZABA

Part 06...

​Gaba ɗaya jikina ya dauki rawa kamar mazari, na kasa ko kwakkwaran motsi yayin da Baba yake tsaye a kaina kamar wani zaki da yake shirin daka wa ganima wawa. Ya dade yana kallon lambar Khalid a kan fuskar wayar, sannan ya wurga wayar a kan gado cikin bacin rai.

​“Maryamu, kema kin fara girma ko? Kin fara ganin cewa kin isa ki binciki rayuwata ko?” Muryarsa ta fito can kasa-kasa, wadda ta fi rurin tsawa ban tsoro.

​“Baba... ba haka ba ne...” na fara magana cikin kuka. “Ina son sani ne kawai. Me ya sa za a sayar da ni kamar yadda ake sayar da dabba a kasuwa? Shin ni ba diyarka ba ce? Shin rayuwata ba ta da daraja a wajenka da har ka bayar da ni a inda ba a san darajar mace ba, a matsayin biyan bashin da ka ci?”

​Baba ya daka min wata tsawa da ta sa na kusa faɗowa daga kan gadon. “E, na sayar da ke ɗin! In ma sayar da ke din na yi, ai ni na haife ki! Inda ban ci bashin nan ba, da yanzu ba ki da gidan da za ki zauna ki samu nutsuwa, ba ki da mutuncin da za a kalle ki, balle har ki samu sukunin yin karatu mai zurfi ki samu aiki. Alhaji Sani ne ya tashi mutuncin gidan nan, kuma ke ce kaɗai hanyar da zan iya biyansa da shi.”

​Ya nuna ni da yatsa, “Kuma ina so ki sani, daga yau na hana ki fita ko ina. Ko ofis ba za ki ƙara komawa ba. Duk abin da kike bukata, Innarki za ta kawo miki. Idan kuma kika kuskura kika sake tattaunawa da wannan yaron Khalid, to ki tabbata cewa ba Alhaji Sani ba, ni kaina zan iya zama sanadin ajalinki!”

​Yana fita, ya sa sakata ya rufe kofar dakin ta waje. Na ruga zuwa jikin kofar ina jan ta da ƙarfi, ina kuka, amma kowa a gidan ya yi kunnen uwar shegu da ni. Haka na ji muryar Inna tana cewa Baba, “Malam Wallahi ka yi min dai-dai, har yanzu Maryamu yarinya ce sai ta ji jiki sannan za ta gane cewa wannan auren nata da Alhaji Sani shi ne rufin asirinmu."

​Na koma tsakiyar daki na zauna, na rasa abin da zan yi. Wayata tana nan a kunne, ashe Khalid bai kashe ba! Na dauka da sauri na kara a kunne.

​“Khalid! Kana ji na? Baba ya kulle ni a ɗaki ya ce ba zan sake fita ko ina ba!” Na faɗa masa muryata tana rawa.

​“Ina jin ki Maryam. Kada ki damu, wannan ma yana cikin shirinmu. Dama na san Baba zai iya yin hakan. Yanzu abin da nake so ki yi shi ne; ki nuna musu kin yi sanyi, kin amince da auren. Ki daina kuka, ki daina damuwa da yin musu. Amma a asirce, ina son ki nemo takardun filin nan da nake gaya miki a dakin mahaifinki.”

​“Amma Khalid, ta yaya zan fita daga dakin nan?”

​“Akwai wata yarinya, kanwarki ce ko? Fatima. Na gama magana da ita, za ta bude miki kofa idan dare ya yi. Dole ne a daren yau ki hadu da Hajiya Zainab matar Alhaji Sani ta farko. Ita kaɗai ce take da sirrin da zai ruguza Alhaji Sani har abada.”

​Cikin tsoro da fargaba, na fara aiwatar da shirin Khalid. Lokacin da Inna ta kawo min abinci da daren ranar, ko kaɗan ban yi kuka ba. Na karɓa tare da murmushin yaƙe na ce, “Inna, na yi tunani mai zurfi a kan auren nan. Ashe kun fi ni gaskiya, babu amfanin bijire muku. Na amince zan auri Alhaji Sani kuma zan yi masa biyayya.”

​Inna ta washe baki, “Yauwa diyar albarka ko ke fa! Yanzu kika yi magana mai kyau. Ai dama na sani, fushi ne na yarinta yake ɗibanki.”

​Bayan kowa ya yi barci, na ji ana taɓa sakatar kofata. Fatima ce, kanwata mai bi min, idanunta cike da hawaye. “Yaya Maryam, fito da sauri. Na ji duk abin da ya faru. Ba zan taba barin su cutar da ke ba, zan taimaka miki iyakar ƙoƙarina.”

​Na fito sanye da hijabina, na gifta ta ƙofar dakin Baba cikin sanɗa har na isa kofar gida. A can waje, na ga wata baƙar mota ta faka a cikin duhu. Khalid ne.

​Mun tafi har zuwa wani gida dake wani kauye can nesa da gari. A nan na hadu da wata mace, wadda duk da tsufan da ta yi da kuma wahalar rayuwa da take ciki, tana da alamun kyau da haiba. Tana ganina, ta fashe da kuka.

​“Ke ce Maryam ko? Dubi yadda kike da kyau da ƙuruciya. Kada ki kuskura ki shiga gidan Sani. Sani ba mutum ba ne, aljani ne a siffar bil'adama! Ki gyara zama ki saurare ni da kyau, zan faɗa miki babban sirrin da mahaifinki yake boye miki...”

​Ku biyo ni a Kashi na 7 don jin yadda zata kaya...

Hussain Yusuf✍️