Chapter --- 06
Assalamualaikum masu karatu ya aiki da fatan kowa yana lafiya...
Kwana biyu zakuce kun jini shiru to bada gangan bane,mutuwa aka min har guda biyu lkc daya,kakata da cousin brother dina shiyasa,da fatan zaku min uzuri nagode 🙏🙏🙏 Allah ya barni daku......
Bismillahir Rahmanir Rahim.
**Namiji Kanin Ajali**
By
Amdeey Tejj
Page 06.
Ina komawa ciki nayi sallah nayi shirin kwanciya tunda mun riga munci abinci ni da lubna.
Bacci har ya fara ɗaukana naji muryarshi akaina yana tashi na,
Hmmm wai kunsan me yace?to wai abincinsa yake tambaya na,nayi shiru wai dan naji ko ba dani yakeyi ba,amma tsabar rashin ta ido irin nashi,sai ya sake maimaitawa har yana buga ƙafata ganin kamar bacci ne ya fara ɗauka ta,wani malolon takaici da ya tokare min maƙoshi ya hanani magana sai kallo da nake binsa dashi kamar wata wawiya,a raina kuwa ina jinjina rashin kunya irin na wasu mazan.
“Dake fa nakeyi”ya sake nanatawa
Da kamar in ƙyaleshi, amma sai na kasa dan dama ba haƙuri nake dashi ba,kawai ƙoƙarin koyan haƙurin nakeyi kamar yadda umma take gaya min kullum mai haƙuri shi ke da riba a ko da yaushe, to amma wannan bazan iya kau da kai ba,dan haka na miƙe zaune sosai ina kallonshi.
"Amma kai Bature yanzu har kai kana da bakin tambayata abinci, ko dai kamanta a inda kake ne ko yaya,idan ban manta yau kusan kwana shida kenan rabonka da bamu ko daidai rairayin ƙasa da sunan abinda zamu ci,shine kake tambayata abinci, to ma ba wannan ba, yanzu kai ba abin kunya bane agareka ba, baka bayarda abinci ba a gidanka ka dawo ka samu an dafa an sa maka ka ɗauka kaci, batare da kasan daga inda ya fito ba,amma kai tsabar rashin ta ido irin naka har kaine kake tambaya da kanka,kaico da halinka Bature"na miƙe na fice a fusace,ji nayi kamar inja tsaki amma sam ba halina bane tsaki dan na tsani ayi tsaki a kusa dani,waje na fito na tura ƙofar ɗayan ɗakin da ƙarfi na shiga na saka dakata dan kar ya biyoni, na kwanta na barshi a can shida yara,duk yadda naso bacci ya ɗauke ni yaƙi saboda tunani,duk kuma yanda naso na ya kice shi yaƙi barina haka na dinga yi na kwance wannan, na saƙa wancan, wannan yace shi zanyi har bansan sanda ɓarawon ya sace ni ba.....
Jahar Nasarawa Najeriya,Ƙaramar Hukumar Shabo.
"Innalillahi Wa'inna Ilahir Raji'un,Habibu anya kanka ɗaya kuwa?,kasan me kake faɗa kuwa? to gaskiya ni bazan iyaba, talauci ai ba hauka bane, ko talauci ya isa dalilin da zaisa bawa ya saɓawa Ubangijinsa?,kaga, wannan jarabawa ce ta Ubangiji kuma idan aka daure za'a ci riba gaba"
A fusace cikin katseni yace"Sai yaushe za'a ci ribar iyehh?,bayan mahaifiyata ta mutu kenan?,a ina zan samu kuɗin da ake da buƙata nan da kwana bakwai wanda a kwana ishirin da uku da suka wuce ban sameshi ba?"sai kuma ya sassauta Murya yace, "kinga, alfarma zaki min ki taimakeni ki taimaki rayuwar mahaifiyata ki amince dan Allah, wannan ce kaɗai mafitar mu ki taimakeni dan Allah" ya faɗi yana haɗa hannayensa biyun a lokaci guda yana kai gwiwarsa ƙasa alamar roƙo.
Ya ban tausayi tabbas da kuma Abinda yake nema a gareni ba saɓon Allah bane da nayi mai amma kash yazo da abu mai girman da bazan iya ba, sannan ina yimai uzuri idan na tuna da nice a halin da yake da ya zanyi kenan,ban ban iya bawa kaina amsa ba, amma dai nasan zaiyi iya bakin ƙoƙarin sa,ina tausayawa halin da hajiya take ciki, duk da tausayin da nake mata nasan ban kai shi ba,amma wannan jarabta ce.
"Na kawo mana shawara wacca nake ganin zata ɓille mana amma ka ƙi yarda,Habibu dole ne mu karɓi ƙaddara a yadda ta zo mana,ka amince idan Allah ya dube mu sai kaga ya yaji ƙanmu ya kawo mai taimakon mu, dan rahamar Allah tana da yawa, wannan ma ai ba muyi tsammanin zamu samu ba,sai kuma Allah ya kawo shi,tunda manufarsa ba mai kyau bane yaje da halinsa"na faɗa bayan na gama wancan tunanin.
"Kina nufin sai munyi Bara kenan?"ya faɗa da alamar tambaya, kamar ma dai neman tabbaci yake.
"Eh mana tunda bamu da wata hanya sai wannan,mukayi sa'a sai mu samu masu taimakon mu tsakani da Allah batare da sun nemi wani abu daga garemu ba"na bashi amsa.
Kau da kai yayi sannan yace"gaskiya a'a,ni ba zan iya bara ba, sannan ke kina tunanin a bara daza a baka ishirin goma shine za mu haɗa kuɗin da ake bukata a nan da kwana bakwai, wannan ma ai ba mafita bane".
Banyi mamaki ba dan nasan za'a rina,kuma nima ina wannan tunanin to amma ai lalube ake a duhu,kuma bamu san inda ni'imar Allah zata faso ba, haka muka dinga jayayya dashi har da ƙyar daga baya ya yarda zamuje Lafia gobe idan Allah ya kaimu,daga nan ya fice ya barni a ɗakin ni kuma na faɗa tunani, Ni dalilin da yasa nace muyi bara a Lafia shine akwai wata maƙwabciyar mu da ƴarta take fama da ciwon zuciya yarinya ƙarama dan bazata wuce shekara shida ba, to suma ɗin dangina ne ba ko sisi gashi yarinyar kenan ƙwalli ɗaya da ƙyar aka samu ita ɗin ta tsaya dan mutuwa suke yi,to dasu suka rasa yanda zasuyi ga ciwo na tayin gaba dole tasa suka tafi Lafia da yarinyar suka soma yin bara cikin ikon Allah ya haɗa su da wani bawan Allah ya taimake su ya ɗauki nauyin jinyarta gaba ɗaya,haka wata tsohuwa ma itama maƙwabciyar muce ita kuma bata taɓa haihuwa ba sannan ga ciwon sugar gashi itama ba mai hali bace, rashin cin abinci da aka gindaya mata a asibiti da kuma rashin kuɗin sayan magani yasa ciwon shirin kashe ta tunda sauran kwananta,a taƙaice dai itama birnin taje Allah kuma ya dafa mata ta samu wanda ya ɗauki nauyin abincinta da magani duka, shine nima nake sa ran Allah zai dube muma idan munje
Tafin da naji a saitin fuskata ya ankarar dani wani shigo kenan ban sani ba na faɗa duniyar tunani,kamar kuwa yadda na zata dan koda na ɗago sai naga Rabi'ah ce ƙanwar Habibu itace ta shigo.
"Yaya Haula tunanin me kikeyi haka ina ta sallama amma da alama hankalinki baya tare dake"ta faɗa bayan ta nemi wuri ta zauna akan kwaraɓaɓɓiyar kujerar dake cikin ɗakin ƙwalli ɗaya data rage cikin ɗakin.
"Hmmmm" na sauke nannauyar ajiyar zuciya kamar wacca nayi gasar tseren gudu saboda dogon tunanin da na tafi sannan nace "Rabi kece yaushe kika shigo,ya jikin Hajiyar ya kika barota?"nayi mata a lokaci ɗaya bayan na dubeta na dawo da hankali na gareta.
"Ban daɗe da shigowa ba ina ta sallama amma hankalinki baya nan, Hajiya kuma jiki kam sai dai muce Alhamdulillah, amma tunanin me kikeyi haka daya ɗauke miki hankali baki ɗaya?" ta bani amsa haɗi da tambaya a lokaci guda......
To masu karatu sai kun kuma jina ga wannan kuyi haƙuri dashi duk da naso nayi yafi haka amma sakamakon yanayin aiki yasa banyi kamar yadda na tsara ba...
So goodbye 👋👋👋
See you next time👀👀👀👁️👁️👁️
Ina ƙaunarku sosai❤️💕❣️💝
Amdy ne.....