13
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*13*
Ammah ta bi bayan Abdulrrahman da sauri zuwa cikin ɗakin, dukkansu sun dukufa kan Ummu Salma har Baffa shi ne mai yi mata addu'a yana tofa mata, Saddam da Baɗɗo da Ummin ikki sun rirriƙeta tana ta fizge-fizge tana wani gunjin kuka har a lokacin ba ta daina maganganu ba kamar wacce ta fita daga hayyacin ta.
"Baffa zuciyata zafi take yi. Baffa ba zan iya rayuwa a haka ba. Ku bar ni na kashe kaina na huta."
Haka take faɗa tana rera wani irin kuka wanda ke kassara zuciyar mai sauraranta.
Ummin ikki haka take hawaye Baɗɗo har da majina Hamma Saddam ma idanuwansa sun kala saboda tashin hankali Baffa kam har da ƙwalla kwance a idanuwansa.
"Ummu ki daina faɗin haka. Ki yi ta maimaita Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.."
Baffa ya faɗa lokaci ɗaya yana dafe kanta yana karanto mata addu'o'i Fatima kawai yake tunawa da irin wahalan da ta sha kafin ta iya karɓan kaddaranta amma Fatima ba ta taɓa cewa za ta kashe kanta ba. In har aka bar Ummu ita kaɗai wata rana za ta iya yin abin da hankalinta zai gushe ba a sani ba.
"Ku sake ta "
Suka ji an faɗa daga bayan su.
Gabaɗayansu suka juya cikin mamaki sai suka ga Hamma Abdulrrahman tsaye shi da Ammah a bakin ƙofar ɗakin.
"Na ce ku sake ta don Allah.".
Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana shigowa cikin ɗakin sanye yake da suit masu ruwan toka ya matse wuyan sa da tie. Gefen kafaɗansa kuma jakarsa ce ta aiki.
"Cewa take yi za ta kashe kanta fa Hamma."
Saddam ya faɗa yana kallon yayan na shi cikin mamaki.
"To ku saketa ta kashe kan nata mana"
Ya faɗa cikin halin ko in kula ba su Baffa ba har Ummun dake fizgewa sai da ta natsu idanuwanta na lumshe sai da ta buɗe su ciike da hawaye tana kallon Hamma Abdulrrahman tsaye a gaban su fuskar nan ta sa babu fara'a ko kaɗan hannayensa duka suna cikin aljihun wandon suit ɗin sa.
"Haba Abdulrrhaman me ya sa za ka ce haka! A wannan yanayin da take ciki za ta iya yi ma kanta illa ba tare da ta sani ba."
"To ku kyaleta Baffa ta yi ma kanta illa saboda wani wanda ya cire ta daga rayuwarsa cikin tozarci da wulaƙanci. Ku barta in ba ta kashe kanta ba, ba ta haifu ba."
Baffa ya yi shuru kawai yana kallon ɗan nashi.
"Kai sake ta."
Hamma Abdulrrahman ya ba ma Saddam umarni.
Da sauri ya saki Ummu ya miƙe tsaye, tun kafin ma ya sake magana Ummi da Baɗɗo suka saki hannayen Ummun Salma suka matsa gefe suka bar Baffa kaɗai a durƙushe a gaban ta.
"Baffa kai ma don Allah ka tashi daga durƙushen nan."
"Abdulrrahman."
"Baffa don Allah."
Hamma Abdulrrhaman ya faɗa lokaci ɗaya yana kallon Baffa cikin ɓacin rai, ba lallashi take bukata ba fata fata za a yi mata sannan za ta dawo cikin hayyacin ta.
Baffa ya ƙi tashi sai da Ammah ta shigo ta kira sunan shi.
"Baffa."
Kallonta ya yi kawai sai ta gyaɗa masa kai, dole ya tashi jiki a sanyaye amma sai da ya kalli Abdulrrahman yana faɗin" Ka yi mata a hankali."
Ya faɗa yana dafa kafaɗan shi ya ɗan bubbuga.
Fita ya yi daga ɗakin ya koma falo Ammah ta bi bayan shi ganin shi cikin damuwa.
Hamma Abdulrrahman ya yi tsaye a gaban Ummu Salma da ta natsu kamar ba ita ce ya shigo ya ga ana rirriƙeta ba, amma yanzu ta yi shuru sai dai kawai hawaye take yi wasu na zuba wasu na karanyowa.
"Kin fasa kashe kan na ki ne?
Ya faɗa yana kallon ta, kawai sai ta fashe masa da kuka.
"Ban hana ki ba, go ahead ki kashe kanki Ummu Salma.".
Ya faɗa yana sassauta fushinsa.
"Hamma.."
Ummu Salma ta kira sunan shi cikin kuka da fitan hayyaci.
"Na ce ki kashe kan naki don Uban ki."
Ran maza ya ɓaci a gabanta ya duƙa lokaci ɗaya yana kallonta.
"Ai sai kin kashe kanki za ki nuna mana kaf ɗin mu ba mu da amfani ko matsayi a wajenki Ummu Salma."
Ya faɗa cikin ɗaga murya. Ta ɗago jajayen idanuwansa tana kallon shi, bai dagata ba ya cigaba da faɗin.
"Ammah da ta yi cikinki na tsawon wata tara ta kawo ki duniya ta rene ki, da Baffa da ya yi ɗawainiyar rayuwarki tun daga ranar farkon ki a duniya har zuwa girman ki. Da mu y'an'uwanki da muka yi rayuwa dake sama da shekara ashirin duk yau bamu da muhimmanci, wannan dai banza a banza da ba ki da amfani a wajen shi, wanda kika haɗu da shi a baya baya shi ne kike ikirarin kashe kanki saboda shi Ummu Salma?
Hawaye kawai ke shatata ta kasa magana, tana so ta yi ma Hamma bayanin yadda take ji amma ta kasa wataƙila ba zai saurareta ba, saboda bai taɓa riskan kansa a cikin halin rayuwar da take ciki a yanzu ba.
"Are you stupit? Ko kuwa kin rasa tunanin ki ne saboda wanda ko shekara biyu ba ki yi da sanin shi ba? Da kin san shi? Ba ki san shi ba kuma kin yi rayuwa Ummu Salma ba ki mutu ba to yanzu ma haka za ki cigaba da rayuwa ba za ki mutu saboda wani wanda bai dace ya fita daga rayuwarki ba."
Ya karishe faɗa yana kallon ta, duk da tausayinta na kama shi amma ba zai nuna mata ba gwara ya yi mata jan ido domin ya ga ba ta da hankali.
"Za ki cigaba da rayuwarki kamar yadda kika fara tun farko. Bai hallata ki cigaba da kuka ko damuwa akan wanda bai damu dake ba, wanda ya yi miki sakin wulakanci har uku sannan ya sake ki da cikin shi a jikin ki ba tare da ya damu ba. To ki sani in kika sake cewa za ki kashe kanki saboda shi, to kin nuna ma duniya cewa ke ba y'ar halas ba ce."
Shuru ya yi yana kallonta tana ta kuka har da gunji.
"Wanda ke son ki ba zai ƙi haɗa jini dake ba Ummu Salma."
"Ai ya ma ce ba sonta yake yi ba mara mutumcin."
Ummin ikki ta katse shi ya ɗago yana kallonta.
"A takardan sakin abin da ya rubuta kenan maganganu masu muni ai tsakanin mu da wannan yaron sai Allah ya isa."
Ummin ikki ta sake faɗa tana matsar ƙwalla.
Hamma Abdulrrahman ya miƙe cikin mamaki yana faɗin" Ina takardan sakin?
"Ko yana hannun Baffa?
Ya sake faɗa.
Sai Ummin ikki ta amsa mishi da cewa yana hannun Baffa. Da sauri ya bar ɗakin yana zuwa falo ya ga Ammah da Baffa, yana ganin shi ya miƙe yana kallon shi.
"Baffa ina takardan sakin?
Ya tambaya yana miƙa masa hannu, bai yi musu ba ya laluba aljihun rigan shi ya ɗauko ya mika masa. Ya karɓa daga tsayen ya fara karantawa bai ko kai ƙarshe ba ya yi wurgi da jakar hannunsa da takardan yana faɗin.
"Wannan yaron so yake mu nuna masa matsayin mu Baffa."
Ya faɗa a fusace lokaci ɗaya yana ɗauko wayarsa daga aljihun wandon shi, da sauri Baffa ya riƙe shi yana tambayan shi abin da zai yi sanin halin shi rudaɗde ne in ran shi ya ɓaci.
"Abokin aikina zan kira. Baffa dole fa mu yi ƙaran wannan yaron mara tarbiya."
Ya faɗa har jijiyon kansa na miƙewa raɗau saboda ɓacin rai.
"Aa"
"Baffa za mu shigar da ƙara sai mun yi shari'a da shi sai kotu ta karɓo ma Ummu Salma haƙkin ta."
Ya faɗa cikin ɗaga murya.
"Na ce maka A'a."
Shima Baffa ya katse shi a tsawa ce lokaci ɗaya yana ƙwace wayar hannun shi, Abdulrrahman ya fusata kawai sai ya fara zagayen falon yana ciccijewa saboda ɓacin rai, Baffa ya bishi ya riƙo shi yana faɗin ya je ya zauna ya samu natsuwa.
"Baffa wai ba ka karanta maganganun dake cikin takardan nan ba ne? Raina mu ya yi da zai rubuto mana haka?
Ya faɗa yana kallon Baffa cikin fusata.
Ammah na gefe zaune ba ta yi magana ba daman ta san sai an yi haka don ma ɗayan fusattacen bai zo ba Kabiru ai da Baffa ba zai iya da su shi kaɗai ba.
"Zo ka zauna ka natsu mu yi magana."
Da lallashi da ban baki ya amince ya zauna Baffa ya zauna a gefen shi.
"Kwantar da hankalin ka Abdulrrahaman."
Baffa ya faɗa yana kallon sa ganin yadda yake huci ba abin da ke yi masa yawo wai sai don jikinta ya aure ta kuma tunda ya gama mora shi ya sa ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da kuda.
Tuna hakan da ya yi ya sa ya sake miƙewa a zuciye yana faɗin" Kai ina! Bai isa ya ci bulus ba, dole ne mu nuna masa kuskurensa yadda ko nan gaba ya ji an ambaci sunan gidan nan sai ya fara mazari don uban sa."
Da sauri Baffa ya sake riko shi yana ba shi haƙuri.
"Baffa ka bari mu koya masa hankali. Ko nawa zan kashe daga nan har kotun ƙoli so kawai na ke yi na ga ya wulakanta."
Abdulrrahman ya sake faɗa yana ta da jijiyoyin kansa saboda ɓacin rai.
Mirmishi Baffa ya yi kafin ya ce" Abdulrrahman"
Ya kira sunan shi yana mai kallon shi.
"Ba za mu je kotu ba, ba za mu je mu buɗe ma duniya cikin mu ba. Shi fa namiji ne ita kuma Ummu mace ce, ita ce za ta zama abin nunawa ba shi ba. Gwara mu kai shi kotun da ba wanda ya isa ya kwace daga zaluncin da ya yi ba wannan mahaluƙin in dai ka yi zalunci sai ka karɓi sakamakon ka, daidai da abin da ka ka aikata."
Hamma Abdulrrahman ya kalle shi cikin mamakin kalaman shi shi kuma Baffa ya jinjina masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Kotun Allah Abdulrrahman. Mu bar shi da Ubangijinsa shi zai yi ma Ummu faɗa shi zai saka mata in sha Allahu."
Sai ya yi shuru yana sauraran Baffa ta wani fannin gaskiya ya faɗa.
"Za mu iya kai shi kotu mu yi nasara amma zafi da baƙin cikin dake zukatan mu ba za su gushe ba Abdulrrahman. Kuma ba za mu iya sauya cewarsa na baya son yar mu ba, duk abin da za mu yi sai dai mu yi ba mu isa mu ƙanƙarema Ummu bakin cikin zuciyarta ba amaimakon mu saukaka mata sai mu sake dagula mata lissafi."
"Haka ne Baffa."
"To ka yi hakuri da maganar shigar da ƙara. Ba wai don ba za mu iya sharia da shi ba ne. Aa sai domin mu taimaka ma Ummu wajen mantawa da shi, shi kuma Allah ne ya hana zalunci kuma ya yi, to ko Ummu ba ta furta Allah ya saka mata ba wallahi sai Ubangijin adalci ya yi mata sakayya ko a nan duniya ko a ranar gobe ƙiyama.".
"In sha Allahu."
Ammah ta faɗa cikin sanyin murya Hamma Abdulrrahman ya yi ajiyar zuciya kafin ya yi magana Baffa ya dafa kafaɗan shi yana faɗin." Ina fatan ka fahimce ni yanzu ko?
"Na fahimta Baffa. Allah ya kyauta na gaba."
Ya faɗa yana jin fushin sa na sauka.
"Allah ya yi maka albarka "
"Amin Amin Baffa "
Ya amsa a sanyaye shuru na wani lokacin kafin Baffa ya tambaya Ummu.
"Na yi mata faɗa, Baffa ba a lallashi a irin haka, ba ta da hankali sai zuciya ta zuga ta."
"To yanzu dai ka koma ka matsa mata taci wani abu. Amman ku ta ce tunda suka zo ba ta ci komai ba, kuma ka ga ba ita kaɗai ba ce "
"To Baffa."
Ya amsa yana kallon shi.
"Baffa cikin fa? Mu za mu riƙe shi ko bayan ta haihu za a mayar da shi wajen uban shi?
Baffa ya girgiza kai kafin ya ce" A'a ba ka ji abin da ya ce a takardan ba ne?. Ba ya bukatar cikin shima "
Nan Baffa ya sanar da shi yadda suka yi da waliyin Habib da hukuncin da ya yanke.
"Baffa saboda dai ka ƙi yarda ne amma ai Ummu kaɗai muka aura masa ba da ciki ba. Bai isa ya ƙi karɓan abin da yake nashi ba ne ƙaryan shi tasha ƙarya"
"Ba komai. Ai Ummu ce za ta haifi koma mene ne, saboda haka ba za mu ƙi jinin ta ba."
Hamma Abdulrrahman ya jinjina kai amma da ace Baffa zai bari wallahi ba za su karɓi cikin nan ba sai an je kotu alƙali ya yanka mai kuɗin ɗaukan ciki da reno tana haihuwa bayan ta yaye ya zo ya karɓi abin ya ɗiga shi. Rayuwar Ummu ba za ta kare wajen wahala ba tunda ba shi da mutumci.
Umarnin Baffa ya bi ya koma ciki ya iske gabaɗayan su har da Saddam sun tasa Ummu kowa yana bata baki amma ba ta ji ba kuka kawai take yi tana gunji ko tsayawa ma jin kukanta bai yi ba ya ce a haɗo mata tea mai zafi a kawo masa ba musu Baɗɗo ta mike ta je ta haɗo mata daman akwai ruwan zafi a fulas ta ciko wani jug ta kawo ma Hamma Abdulrrahman ba wasa a fuskar shi yana miƙa ma Ummu jug ɗin ta karɓa hannunta na rawa.
"Shanye shi duka ki ba ni Jug ɗin ina jiran ki "
Ya faɗa ba wasa a maganarsa jiki da hannu na rawa ta karɓa ba ko gaddama ta kafa kai ta kwankwaɗe shi ta dire kofi su Baɗɗo na ta murna.
"Yauwa ko ke fa Ummu Salma yanzu ai kya ji dama-dama"
Ba ta gama rufe baki ba Ummu ta yunkura da sauri kafin ta iya miƙewa amai ya biyo baya duk kuma ruwan shayin da ta sha sai da ta amayar da shi a wajen nan Hamma Abdulrrahman ya matsa baya yana rufe hancin sa, saboda ba ya son ganin amai ko ya shaƙa yanzu nan shima zai fara fita ya yi ya ce in sun gyara wajen su sake haɗo mata wani shayin. Hamma Saddam ma ya bi bayan shi aka bar Ummin ikki ta kama Ummu zuwa tiolet ita kuma Baɗɗo tana gyara in da Ummu Salma ta yi aman.
Sai da aka gyara wajen aka kunna turaren tsinke ɗakin ya ɗau ƙamshi ita kuma Ummu Salma wanka Ummi ikkin ta yi mata domin jikin na ta ba karfi sannan duk ta ɓata kayan jikinta kawai sai ta taimaka mata ta yi wanka bayan ta fito Baɗɗo ta ɗauko mata wata doguwar riga cikin kayanta da suka zo da shi. Hamma bai tafi ba ya sake dawowa da wani kofin cike da ruwan tea ya ce Ummu ta sake shanyewa sai ta fara hawaye tana faɗin.
"Hamma zan yi amai."
"Ko sau ɗari za ki yi amai sai kin sha, in dai zai zauna a cikin ki."
Ta san halin shi in yana magana da lalama a yi abin da yake so in ya birkice bashi da kyau dole ta karɓa ta shanye.
Ya karɓi jug ɗin yana faɗin" Good. Ki riƙa cin abinci sosai kar ki bari na ji labarin kina zama da yunwa kin ji ko ba ki ji ba?
Sai ta gyaɗa kanta tana mai zubar ƙwalla
"Ba ki da baki ne?
"Na ji."
Ta faɗa tana danne kukanta.
Sai ya miƙe lokaci ɗaya yana faɗin" In ma kina so ki mutu ne ki yi mutuwar da Allah ya tanadar miki, amma in har saboda wancan ne to ki sani har abada rayuwarki ba ta da wata amfani a wajen shi. Ki riƙa tuna hakan a cikin zuciyarki."
Daga haka ya fice ya koma falo ya yi ma su Ammah sallama da cewa zai tafi.
"Ka tsaya ka ci abinci mana."
"A'a Amma bana jin cin wani abu."
Jakarsa ya ɗauka ya rataya ya ce zai shigo gobe da safe kafin ya wuce wajen aiki in dai ba ta ci abinci da yamma ba Ammah ta yi masa waya zai sake dawowa da haka suka yi sallama ya fice Baffa ya koma ɗakin sa can ya bi shi suka yi sallama sannan ya fice daga gidan cikin tausayin Ummu har da su Baffa gabaɗaya gwara Baffa na bayyana damuwarsa Amma ce ke ɓoye abu kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci ta rame a tsaye cikin yini ɗaya.
Ranar sai dare Abdullahi ya kai Ummin ikki gida. Daman da ya dawo da yamma tare da matarsa Adda Suwaiba da Madibbo ya zo. Ita ce tare da Baɗɗo suka zauna da Ummu suna ta ɗan ba ta baki ta daina kuka sai dai suyan zuciya kawai. Baɗɗo nan ta kwana tare da Ummu matar Abdullahi sai wajen sha ɗaya na dare suka koma gida.
Washegari ma wajen ƙaryawa sai da Baffa ya zauna ma Ummu ta ɗan sha tea kaɗan shi ma ba daɗewa sai da ta yi aman shi, da rana faten wake Amma ta yi mata amma ba ta iya ci ba sai da Hamma Abdulrahman ya zo ya tsaya mata sannan ta tsakura haka da daddare ma sai da ya tsaya mata tunda suna gidan har dare tare da Adda Suwaiba kowa Ummu yake tausayawa. Habib kam ya sha tsinuwa da mugun baki Ummin ikki ma tana gidan har dare ita da Kaltume washegari kan Ammah ta fara karɓan baƙi masu zuwa mata jaje, yayyen Baɗɗo dukkansu sun zo Iklima har dare sannan ta tafi. A waya ma Ammah tana ta samun wayoyin sauran yaranta da matan su.
Hamma Jibo ya ce sai karshen sati Hamma Mustapha dai ya ce sai karshen wata za su shigo har Baffa duk sun kira suna mai jajanta musu da wannan lamarin da ya faru su da yake suna da sauƙin kai sun ce hukuncin Baffa ya yi daidai. Kuma duk sun yi magana da Ummu Salma ta wayar Ammah suna ta bata baki amma har yanzu Ummu ba ta daina kuka da damuwa ba.
Hamma Kabiru ne ya yi ta masifa a waya yana faɗin ba za su karɓi wannan cikin ba, ba wanda ya saurare shi daga AmmaH har Baffa sanin halin shi shi ma dai ya ce yana tafe a karshen satin nan.
Saboda hankula ba'a kwance yake ba shi ya sa Amma da Baffa suka manta da maganar kwaso kayan auren Ummu Salma. Sai da su Umma Balki suka zo daga Mubi suke maganar kwaso kayan tunda duk Ammah ta sanar da su, abin da ke faruwa.
Da Ammah ta yi masa mganar kwaso kayan Ummu sai Baffa ya ce za a je a kwashe in zukata sun samu natsuwa. Kwanan su ɗaya suka juya cike da alhini.
Baffa ma ya sanar da su Baffa Umaru kowa ya ji labari sai jikinsa ya yi sanyi barin ma in suka zo suka ga yadda Ummu ta koma cikin kwana biyar ta faɗe ta rame ta lalace abinci in ba Baffa ko Hamma Abdulrrahaman suka tsaya mata ba, ba ta ci in kuma ta ci ba ya zama a cikin ta za ta amayar da shi. Sannan Baɗɗo ta ce Ummu ba ta samun barci da daddare.
Abdullahi shi kan shi ya ga ɗashewar Ummu Salma ya ce ya kamata a kaita asibiti a duba lafiyanta. Shima Baffa ya ga haka saboda komai ta ci baya zama a cikin ta.
Ranar Jumma'a da Safe Baɗɗo da Ummin ikki da Hamma Abdullahi suka kai Ummu Salma asibiti Boshin clinic in da take da fayel, suna zuwa likitoci suka riƙe ta acan suka ba ta gado likita na ta faɗa jininta ya hau ga maleria ga rashin cin abinci. Yana ta faɗan cewa yanayin zai iya zama barazana ga cikin jikinta.
Baɗɗo suka bari da ita, Ummin ikki da Abdullahi suka koma gida suka sanar da su da halin da ake ciki sannan suka zo da mata da wasu kayan sawa sai fulas ɗin ruwan zafi da kayan tea. Kwanta ɗaya a asibitin sai ga Hamma Kabiru ya zo shi kaɗai ya shigo garin daman Baɗɗo ne ta kwana tare da ita da safe Ummin ikki ta je tana taya ta zama sai Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim da suka zo da rana su ɗan taya su zama.
Hamma Kabiru ya zo har asibitin ya duba Ummu Salma shi da Abdulrrahman da Saddam nan suka bar ma Saddam ɗin suka tafi, tana ta barci saboda an yi mata alluran barci tana ta samun barcin da ta yi kwanaki ba ta samu ba.
Hamma Kabiru da Hamma Abdulrrahman suka koma gida suka samu Baffa shi Hamma Kabiru faɗa yake yi don mai Baffa zai ce a karɓi ciki ai tun da dai ya amince shi ya ɗiga shi to bai isa ba.
"Baffa Ummu ta koma kamar wata horror tsabar rama da fari."
Ya faɗa cikin damuwa.
"Nima na ce Baffa ya bari a yi ƙararsa amma ya ce ba za mu yi ba."
"Baffa ka bari mu yi amfani da kuɗinmu mu jijiga duniyarsa kamar yadda ya jijjiga rayuwar ƙanwar mu."
Baffa dai ya yi shuru yana jinsu suka gama bambamin faɗan su suka sauka sannan ya yi magana da su kalaman dai da ya faɗa ma Abdulrrahman shi ya faɗa ma Kabiru ya dai bar maganar ne amma ba wai don ya fahimci Baffa ba, ai tunda ya nuna shi ba shi da mutumci gwara suma su nuna masa yan zamani ne, bai karanta takardan sakin ba amma duk kalaman dake ciki Abdulrrhaman ya karanta masa tun yana Jalingo.
Ba kwana zai yi ba a ranar yake so ya koma amma ya ce zai dawo tare da Adda Safinatu da yara su duba Ummu su ɗan kwana biyu. Hamma Abdulrrahman ya tafi saboda akwai in da zai je shi kuma sai ya shiga falon Ammah su sake gaisawa tun da lokacin da ya shigo gidan tana da baƙi, labari kamar ana ta aike maƙota duk sun ji labari ana ta shigowa yi ma Amma jaje har Baffa in ya fita haka za a tsayar da shi ana masa jaje, to ai tunda lamarin ya faru ba wanda ya isa ya hana a yaɗa labarin
Ko Ammah abin da Hamma Kabiru ya ke faɗa mata kenan ta lallashi Baffa ya bari su yi ƙaran yaron nan.
"Baffa ba zai amince ba Kabiru ku bar maganar nan kawai."
"Ammah to sai ya kashe mana ƙanwa! Kin ga yadda Ummun ta koma ne?
Amma ta yi shuru tunda ita dai ba ta je asibitin ba Baffa ma ya kasa zuwa amma dai sun yi waya da Ummin ikki ta ce mata ta samu sauƙi tana ta barci dai. Gwara ta samu barcin ko za ta samu yar natsuwa.
"Kawai Baffa ya koma gefe ya bar mana faɗan nan. Wallahi ko ba mu tura yaron nan gidan yari ba sai ya gane ba shi da wayau sai ya san ba a taɓamu a zauna lafiya. Ɗan iska kawai ni da man bai yi mini ba yana wani sunkunyar da kai kamar nagari Ammah ki tsoraci mutum mai kirki da surutun tsiya daga baya sai ya aikata mugun abu. Nonsense kawai"
Amma ta ɗan murmusa ba ta yi magana ba, in dai Kabiru ne da man karatun sa kenan ta kiyayi mutumin da ya cika kirki ba shi da gaskiya. Sake gyara zama ya yi yana kawo maganar da ta wuce wai bai so da man a yi ma Ummu aure ba kamar ya san abin da zai faru daga karshe kenan.
"Yanzu Ammah ina daɗin abin da ya faru? Ummu ƙaramar yarinya ta zama bazawara ga ƙaramin ciki. Haba don Allah in da a ce yarinyar nan ta ji maganar mu da yanzu ta kusa gama Degree ɗin ta da yau ba ta can akwance rai a hannun Allah saboda wani stupid irin yaron da ta aura"
Amma dai ta yi shuru tana sauraran shi yana ta faɗa yana nuna mata harda kuskuren Baffa da itama ma kanta tunda Baffa na jin maganarta ba ta hana a yi ma Ummu aure a wancan lokacin ba.
"Kabiru ka ishe ni fa. Baffan ne ke da laifi? In ya tara sani zai aura ma ta shi? Kaddara ne kuma mu duka musulmai ne musan karɓan kaddara gare mu wajibi ne."
"Amma ki gane magana ta mana. Me ya sa aka goya mata baya! Da a lokacin ke da Baffa kun dage mata wallahi da ta koma makaranta ta bar ra'ayin aure. But kalli abin da ya faru at the end Ammah Rayuwarta ta da dawo baya fa."
"Haka Allah ya hukunta Kabiru ni ko Baffan ka ba mu isa mu sauya faruwan haka ba"
Shi dai sai wani kawo na shi tsarin yake yi Ammah ta gaji ta yi masa tsawa tana faɗin" Kabiru zan ci maka mutumci ba za ka bar ni na ji da damuwata ba, ka zo kana damuna da turancin ka na banza da wofi."
Domin daga karshe sai ya koma yana yi mata mgana da turanci sai da ya ji Ammah ta buɗe masa wuta sannan ya ɗaga hannuwa sama yana dariya.
"Afuwan Ammah na yi shuru."
Ya faɗa cikin harshen fillanci wata uwar harara ta maka masa da ya sa ya ɗinke bakin shi, shuru na wani lokaci sai da ta sauka don kanta ta tambayi Safinatu da yara, duk da ta kira ta waya ta yi mata jaje, ya ce duk suna lafiya yana tunanin za su zo karshen wata su yi musu ko kwana biyu ne Ammah ta ce Allah ya kaimu ya amsa da Amin.
"Ammah gaskiya ya kamata in Ummu ta haihu ta koma makaranta."
"To Baffa."
Ta faɗa cikin gatse tana hararan shi sai ya yi shuru yana dariya.
"Amma shawara ce fa."
"Ba'a son shawaran naka"
"Allah ya ba ki haƙuri Amman mu."
Ya faɗa yana ɗan mirmishi, sake maka masa harara ta yi shi kuma sai ya kwashe da dariya.
"Allah ya huci zuciyar Amman Lamiɗo"
Kamar ya sani sai ko ga shi ta yi mirmishi dariyan ya sake yi kafin ya ce" Da man na sani sunan Amini ne kaɗai zai saka ki dariya."
Amma ta yi mirmishi kafin ta ce" Kwana biyu ma ba mu yi waya ba. ya ko san abin da ya faru na Auta?
"An ya! Kamar bai sani ba don ko shekaranjiya mun daɗe muna waya kuma ban ji ya yi mini magana ba ina tunanin bai sani ba."
Amma ta jinjina kai kafin tace" Ko jiya na gwada lambarsa ba ta shiga. Haka ma Fatima itama ba na samun ta a waya."
"Mami fa kamar ba ta ƙasar, kwanaki mun yi chart da ita tace mini suna Paris."
Amma ta ce" An yi haka na manta Baffa ya faɗa mini sun yi tafiya. Lamiɗon ne na damu amma tunda har ka yi magana da shi yana lafiya Alhamdulillah."
Hamma Kabiru ya ce" Lafiyan shi lau Amma ga ma wani labari mai daɗi."
"Me ya faru?
"Kin kusa fara ganin ɗanki yanzu akai,-akai."
Amma ta washe baki tana fafin" Kai don Allah?
Hamma Kabiru ya gyara zama yana faɗin." Wallahi a shekaranjiyan da muka yi waya yake faɗa mini kamfanin Chevron da ya nemi aiki da su daman can kwanaki ya faɗa mini sun yi online interview. To sun ba shi aiki nan da wattani biyu zai fara aiki da su in sha Allahu."
Amma ta washe baki kafin ta ce" Ma sha Allah. To shi wannan kamfanin anan ne ko? Ba sai ya yi ta yawo a cikin jirgin ruwan ba ko?
Hamma Kabiru ya yi dariya kafin ya ce" Ammah duka kamfanonin na gida Nigeria ne, sai dai shi wanda Lamiɗo ke aiki da su yanzu kamfanin Nigerian Port Authority su jirgin da yake tuƙawa suna jigilan mutane ne da kayan masarufi suna zuwa ƙassashe da yawa kuma suna ɗaukan lokaci shi ya sa yake daɗewa bai zo ya ga mutane ba. Ammah ko a can Lagos ko Balkisu ba ta cika ganinsa ba sai su zo Tashar jirgin ruwa dake Apapa Lagos sau nawa bai je gida ba saboda aikin yana da ɗan tsauri shi ya sa na bashi shawaran gwara ya sauya kamfani wanda zai dinga zuwa gida bayan sati biyu ko uku in ya daɗe ne wata ɗaya."
Ammah ta gyaɗa kai tana faɗin" Haka ne, ya fara tara iyalai bai kamata yana yin nisa da gida lokaci mai tsawo ba gaskiya ka ba shi shawara mai kyau Kabiru."
Hamma Kabiru ya karɓa da cewa" Shi ne fa har sun ɗauke shi aiki yanzu ya rubuta takardan ajiye aiki da kamfanin da yake yi ma aiki yanzu sun ƙi saka hannu. Kin san Lamiɗon naki gifted ne suna son shi duk cikin matuƙan jiragensu ba kamar shi, yana musu aiki tukuru sannan yana da jajircewa akan aikin shi aiki yake yi musu tukuru bai damu da jikinshi ko gajiya ba shi ya sa ba sa son rabuwa da shi."
"To ai sai dai su yi haƙuri mu ma muna son ganin shi sannan muna son ya riƙa hutawa"
Ammah ta faɗa tana dariya.
Tun bayan faruwan al'amarin Ummu sai yau Amma ta saki ranta hiran Lamiɗon da suka yi da Hamma Kabiru.
"Ai zai samu hutu da lokaci ishasshe sosai Ammah. A yadda na yi binciken sabon kamfanin da zai fara aiki da su, suna sauyin matukan jiragen in wannan yaje ya yi kamar wata ɗaya to za a bashi kamar break na sati ɗaya yaje gida ya gana da iyalai da yan'uwa sannan ya dawo kuma kin ga su babu daɗewa sosai kamar na wannan aikin."
"Gaskiya wannan ɗin yafi Kabiru to shima duk tuƙin jirgin ne?
Hamma Kabiru ya sake gyara zama yana faɗin" E mana shi ma kamfani ne kamar wanda yake aiki da shi a yanzu amma suna da ɗan bambamci.
Shi wannan kamfanin na Chevron Nigerian Limited.
Kamfanin dake da alhakin fitar da Mai kasashen waje domin a cire su kalanzir, fetur, dessel, LLG. Suna da jirage da matuƙa jiragen dake da alhakin fita da man zuwa waje da dawowa dashi bayan an tantance shi. Su kawai aikin su fita da man zuwa ƙasar waje domin a tantance a cire abubuwan da na lissafa miki, kamfanin na haƙo Mai ne kuma suna da jirage da matuƙan da ke jigilan Mai zuwa in da za a tace shi a fidda abubuwa masu amfani a jikinsa yadda za a dawo mana da shi mu samu damar amfani da shi kin gane Ammah.?
"Na fahimta Kabiru. Ubangiji ya tsare mana ku. Shi kuma Lamiɗo Allah ya sa ya fara a sa'a Allah ya taimake shi ya tsare shi."
Ammah take faɗa Hamma Kabiru na amsawa da Amin Amin.
" Ya ce ƙarshen watan nan ko ba su saka masa hannu ba zai dawo gida ya yi hutu sosai kafin ya fara aiki da sabon Kamfanin."
"Allah ya amince. Allah ya ba shi nasara."
Sun ɗan jima suna ta hira rabin hiran ta su duk akan Lamiɗo ne sai wajen biyar saura Hamma Kabiru ya yi sallama da Ammah da Baffa ya kama hanyar Jalingo tunda motarsa ce tafiyar awa uku ce zuwa da rabi.
Ummu kuma sai da ta yi kwana huɗu a asibiti sannan aka sallame ta tare da dokokin likita, ta riƙa samun hutu da barci sannan sun ba ta bedrest ga maganguna har da na barci tunda an faɗa musu ba ta samun barci cikin ta kuma ya na gabda shiga wattani huɗu likita ya ce tana buƙatar kulawa da an ga wata matsala a dawo da ita asibiti sannan ta riƙa cin abinci mai gina jiki saboda inganta lafiyan abin da ke cikin ta.
Bayan sun dawo gida Hamma Abdulrrahman ya sake zaunar da ita daga shi sai ita a ɗaki ya sake yi mata faɗa daga karshe ya koma lallashi ya faɗa mata ga dokokin likita sai ta kiyaye ma kanta da shiga damuwa in tana son ta tsira da abin da ke cikin ta, bai barta ba sai da ta yi masa alƙawarin za ta daina damuwa sannan za ta kula da kanta ko domin abin dake cikinta da take jin wani son shi na ƙaruwa a tsakiyar kirjinta ba kukan sakin da Habib ya yi mata take yi ba har yanzu kukan bakin ciki da faɗa da zuciyarta da har lokacin ba ta daina son Habib da tunaninsa ba. Tana yi iya yin ta domin ta manta da shi amma ta kasa da ta keɓe shikenan za ta yi ta tunanin shi da irin good momories ɗin su tare da juna ba ta ma sanin lokacin da ta ke fara kuka.
Ba za ta taɓa mantawa da Baɗɗo ba sai da ta kwana goma da ita tana kula da ita sannan ta koma gida tunda sun koma makaranta. Sannan Ummin ikki ma kullum sai ta leƙo kowa dai burinsa ta samu ta sake ta fara walwala. Ga Baffa da duk ya sakar ma Hamma Abdullahi harkokinsa yana zaune a gida saboda ita. Shi dai nasihan shi ta daina damuwa ta yadda da kaddaranta. Ammah ma tana nuna nata kulawan amma in ta yi lallashin ta gaji za ta fara masifa ne da faɗa, ga Hamma Saddam ma yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen zama da ita yana yin duk wani abu da zai sanya ta farinciki, haka ma Hamma Abdulllahi, da matan su in ba su zo ba yau ba za su zo gobe su Hamma Jibo duk da ba sa kusa duk ranar duniya sai ta yi magana da su ta wayar Amma tunda ita wayarta tana cikin kaya ta kashe kanta ma ba chaji, ganin yadda kowa ya damu da ita ya sa ta rage damuwa amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta ke ciki tare da Ammah suke kwana Baffa ne ya ce ta riƙa kwana da ita amma in ba magungunanta ta sha ba tana daɗewa tana juye-juye ba ta samu barci ba gani take yi kamar a mafarki wai yau ita ce a gida a matsayin bazawara. Ba ta sare ba tunani take da yaƙinin cewa Habib zai dawo ya neme ta, tana ma mantawa da cewa har abada yanzu ta haramta ga Habibu ita soyayyar shi ta gama rufe mata ido da duk abin da ya yi mata ta kasa jin tsanar shi ta kasa daina son shi, duk da tana son ta tsane shi ɗin amma ta kasa tunda ba ita ke da alhakin sarrafa zuciyar ta ba.
Hamma Abdulrah. yana can kasar turai ya ji labarin abin da ke faruwa shi auren ma baya nan aka yi sai ga shi yana can komai ya ƙare. Ya shiga damuwa sosai barin ma da Saddam ke ba shi labarin yanayin da Ummun ke ciki Vedeo call ya kira aka bata ya yi magana da ita kuka kawai take yi tana ma kasa mgana shima daga ƙarshe kashewa ya yi ya fashe da kuka, yana da saurin kuka da tausayi shi ya sa bai sake kira ba sai dai duk lokacin da ya yi magana da wani na gida zai ce a gaishe masa da Ummu, ba ya son su sake magana ta saka shi kuka ga shi yana shekaran ƙarshe ne karatu yake yi kamar injin ya yi ya gama shima ya dawo gida cikin ahalinsa.
Mami ma suna Paris Hamma Saddam ya faɗa mata halin da ake ciki ai a daran ta matsa ma Abban islam cikin kwana biyu suka dawo gida Nigeria. Washe gari kuma suka sake biyo jirgi zuwa Jimeta. Tun da Mami ta zo ta ke kuka kowa ya san kukan da take yi kuka ne na fami daga tsohon gyambon dake zuciyanta. In ta kalli Ummu sai ta ji kukanta ya kasa tsayawa ta yi kuka kamar ranta zai fita sai da Baffa ya zauna yana ta ba ta baki Abban islam na gefe domin ko ya ba ta baki ba ta yin shuru sai ta ce wai ba zai gane yanayin ba ne.
Ummu Salma kukanta ya dawo sabo da zuwan Mami da kukan da take yi, tausayin Ummu Salma take ji duk da ta ɗan fi ta shekaru ita lokacin ko ashirin ba ta cika ba ta faɗa wannan kaddaran amma duk yadda za a fassara lamarin ba wanda zai gane yanayin sai wanda abin ya faru da shi.
"Baffa yaron nan ya cutar da Ummu Salma. Muma ya cutar damu kuma wallahi sai Allah ya saka mata."
Mami take faɗa tana kuka kamar ranta zai fita.
"Ummu ki yi kuka ki yi ta kuka ko za ki sami salama. Amma kar ki yi dogon damuwa cuta za ta kama ki, in kuma hakan ta faru za ki samu cikin damuwa."
Haka take ta faɗa ma Ummu lokacin da ta rungumeta a jikin ta dole Alhaji Isa Ɗanmarke ya nemi hotel ya kwana washegari ya juya Kaduna tunda yara na gida tare da su Baraka, ya bar Mami a Jimeta ita ta ce ya tafi kawai za ta zo daga baya.
Zuwan Mami ya tado ma Ummu taɓon ta amma kuma ta samu sauƙi saboda Mami ta zaunar da ita, ta ba ta labarin rayuwarta da yadda ta yi gwagwarmaya da kaddaranta daga ƙarshe ta yi nasara da yadda Ammah da Baffa suka yi ta ƙoƙari a kanta.
"Ummu Salma akwai zafi na sani amma sai kin daure. Yanzu ki sani ke uwa ce a gobe. Ki kula da kanki saboda abin da ke cikin ki, ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki cire damuwa a ran ki, in kin ji kuka ki yi kuka domin shi kaɗai ne zai samar miki da salama."
Haka take ta faɗa mata cikin ƙarfafa mata gwiwa.
"Za ki ci wannan jarabawar Ummu. Za ki yi nasara kamar yadda na yi. Muna nan dake Allah zai kawo miki wanda zai share miki hawaye. Shi kuma Habib sai ya yi Fargar jaji da ikon Allah."
Ummu Salma tana kuka ta nuna ma Mami jikinta tana kuka take faɗin" Mamina wa zai aure ni a haka? Me na ke da shi? Ba ni da budurci ba ni da jiki mai kyau, nonuwana sun kwanta, ciki gare ni Mami nan da wata biyar zan haihu na buɗe na zama uwa na shayar da jariri, Mami ki faɗa mini wa zai kwashe ni a haka? Me ya sa shi da ya fara bai ƙarisa ba Mami na?
Haka Ummu ke faɗa tana ta gunjin kuka.
"Allah zai kawo shi, wanda ba jikin shi yake so ba ke yake so Ummu in kina tunanin ba zai yuyu ba ki riƙa duba rayuwata. In kika kalle ni za ki samun ƙwarin gwiwan cewa ke ma komai zai wuce zai zama sai labari, sai dai ki tuna ki yi mirmishi ko kin yi kuka sai dai ki yi kukan farinciki da tuna rayuwar baya."
Ita dai Ummu Salma jin Mami kawai take yi ba ta san irin yadda zuciyanta ta so Habib ba ne. Ba ta san yadda jikinta da rayuwarta ya saba da shi ba ne, shi da ya fara me ya sa bai ƙarisa ba? Me ya sa ya rabu da ita? Ta amince za ta zauna da shi ya yi ta moran jikinta har illa masha Allah, amma yanzu da ya sake ta ina za ta je? Ji take yi kamar ta rasa komai na rayuwanta ne in ta ce komai tana nufin komai, mafarkin ta burukanta da dukkan wani tanadinta na rayuwa Habib ya yi sanadiyar da yau ita Ummu Salma ta dawo ba komai ba, ya kuma ma yar da rayuwarta kwanko babu wani abin mamora a rayuwarta a yanzu.
Kwanan Mami biyu da zuwa Jimeta sai ga Hamma Mustapha da iyalan shi a rana ɗaya suka zo da Hamma Jibo amma shi kaɗai ya zo bai zo da su Nauwara ba, jirgi ya biyo ma. Suma dai duk haƙuri da nasihan suka yi ta Ummu Salma ganin yadda duk ta faɗe ta rame ba ta mgana. Daman a wannan lokacin kowa haƙuri yake ba ta, domin babu wani abu da za a yi mata.
Zuwan su Hamma Jibo aka yi maganar kwaso kaya. Mami da Ummin ikki ne suka je gidan tun da key ɗin gidan da man su Baɗɗo sun taho da shi kaf aka haɗa kayan ta waje ɗaya babban mota mai budaɗɗen baya ta zo ta kwashe zuwa gida a ɗakin kusa da na Ammah mai ciki da falo aka saka kayan aka rufe, kayan abincin da Hamma Jibo ya siya mata jibgi haka aka kwaso su sai dai aka kai su store ɗin Baffa.
key ɗin kuma suka ba ma maigadi sallahu in megidan ya zo ya bashi ko masu duba gidan tun da suna zuwa duk sati kayan Habibu ko ɗaya ba su samu a gidan ba tun washegarin ranar da ya yi sakin kafin ya tafi sai da ya kwashe duk abu da yasan na shi ne daman iya kayan sawa ne da takalma sai takardunsa duk ya kwashe su.
Ranar da aka kwaso kayan kwana Ummu ta yi tana kuka. Ba kuma wanda ya hana ta Mami ta ce a ƙyaleta ta yi kukanta ko za ta samu suƙuni kar baƙincikin ya ƙume mata a zuciya ta samu matsala. Tunani take yi shike nan komai ya ƙare tunda gashi an kwaso kayan ta, shike nan ta rasa komai ba ta da wani abu kuma da ya yi mata saura. Cikin dake jikinta ne kawai ya rage mata shi kaɗai ne abin da ya rage ta ƙarisa a halin yanzu.
Habib ya cuce ta, Habib ya gama da rayuwanta.
Habib ya yi ma duniyarta kaca-kaca, Habib ya yi sanadiyar da labarinta ya shiga bakin mutane ya mayar da ita bazawara ya sanya kanta a cikin mata masu taɓo a zukatan su, ya jijjiga duniyanta sannan ya bar ta da abin tunawa har na tsawon rayuwarta na har abada.
*Janafty*