FARGAR JAJI

14

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"


*14*

Sai da Mami ta shafe sati ɗaya a garin Jimeta kafin ta koma Kaduna. Kuma zaman ta ya yi amfani tunda Ummu na jin maganarta sannan tana sauraranta, zamanta a gidan kafin ta tafi ya taimaka ƙwarai wajen sake dangana a zuciyar Ummu Salma, tana cin abinci tana kuma samun hutu sannan koke-koken da take yi ya ɗan ragu sai dai abin da ba'a rasa ba.

Mami ta so Baffa ya amince ta tafi da Ummu Salma Kaduna wajenta ta zauna na wani lokaci saboda yanzu garin Adamawa gabaɗaya ya yi mata ƙunci in ta yi nesa za ta fi samun sukuni da jin daɗi lokacin Hamma Jibo na nan shi bai koma ba ya yi na'am da shawaran Mami har Ammah ma ta ce gwara ta ɗauketa su tafi na ɗan lokaci har zuwa komai ya lafa, shi kan shi Baffa ya fahimce su amma sai ya yi tunani a matsayin shi na Babba, bai ba ta Ummu ta tafi da ita da farko ba amma ba wai ya hana ta ba ne.

"Fatima Auta fa ƴ'arki ce, ni ko Amman ku ba mu isa mu hana ki tafiya da ita ba. Sai dai ya kamata mu yi abin hankali, ke fa matar aure ce kina da miji da kike zaune a ƙarkashin ikon sa, bai kamata ba tare  da sanin shi ko izinin shi ba kawai ya ga kin zo da yarinya ba. Ya kamata ki yi shawara da shi in ya amince ki zo ga Auta nan halak malak Fatima ba wanda ya isa ya yi miki iko da ita."

Abin da Baffa ya faɗa mata kenan ana gobe za ta koma da ta same shi da maganar son tafiya da Ummu Salma gidanta dake Kaduna.

"Baffa ka  fa san Abban Islam ba shi da wata damuwa. Mun yi ma magana da shi a waya shi ya ma kawo wannan shawaran na cewa ko zan taho da ita ne ta ɗan samu natsuwa? Shi fa ko har abada za ta zauna damu ba shi da wata damuwa."
Mami ta amsa ma Baffa cikin magiyan ya amince ta tafi da Ummu amma ya hana ta, ba da niyyar ba ta da hurumi ba sai da niyyar ta bi komai a hankali da cewa ta koma su tattauna da mijinta in ya amince daga baya sai ta zo ta tafi da Ummu sun ba ta ita har abada.

Dole Mami ta amince amma ba haka taso ba, ita ma ta ce ba domin wajen aiki ba, da sai ta yi wata a garin Jimeta amma saboda aiki ya sa ta yi shirin komawa. Kafin tafiyarta haka ta zaunar da Ummu  ta sanar da ita za ta koma Kaduna amma ba daɗewa za ta dawo ta tafi da ita can ta zauna tare da ita.

"Mami me ya sa ba yanzu ba?

Ummu ta faɗa cikin raunin murya har ta fara hawaye. Za ta fi son Mami ta tafi da ita, domin garin nan da mutanen cikin ta sun gama fita da zuciyarta, wani ƙunci take ji da duhu daga cikin zuciyarta watakila da za ta yi nesa da gida da garin gabaɗaya za ta fara mantawa da kaddaranta har ta manta da Habib daga zuciyarta gabaɗaya.

"Ni ma haka na so, to amma kin san halin Baffa ya matsa sai na koma gida na yi magana da Abban Islam."

Ummu tana ta kuka har da shessheƙa, Mami ta yi ta lallashinta da ban baki, ba ta so Mami ta tafi tana son zama da ita domin ita ce kawai ta fahimci halin data ke ciki, ita ce kaɗai ta san irin raɗaɗi da zafin da kaddaran take da shi, ita ce kuma ta san irin yanayin da ake shiga in ka rasa dukkan wata dama ko mafitar daka ke tunanin ka kama ko ka dafe tuntuni amma sai daga baya ba ka shirya ba, ba zato ba tsammani komai ya kubce daga hannun ka.

"Ki yi haƙuri Daughter in sha Allahu zan dawo na tafi dake. I promise you in sha Allahu."
Da haka ta samu ta lallasheta ta daina kuka. Sannan ta bi ta da kalamai masu sanyaya zuciya da alkawarin ko bayan ta tafi ba za ta cigaba da damuwa ko kuka ba, sannan ta riƙa cin abinci saboda lafiyanta da inganta abin da ke cikinta kuma ta yi mata alƙawarin duk za ta ji maganarta. Sannan ta umarce ta da duk abin da take so kar ta yi ma Baffa ko Ammah magana ta kirata ta sanar da ita, ita kuma ta yi mata alƙawarin komai take so in dai bai fi karfinta ba za ta yi mata.

Ranar Jumma'a da misalin ƙarfe goma na safe jirgin da Mami ta shiga ya ɗaga zuwa Kaduna. Abdullahi ne ma ya tuƙa ta zuwa filin jirgin, bayan tafiyarta Ummu ta yi ta kuka ba wanda ya hana ta kowa ya san akwai shaƙuwa mai tsanani tsakaninta da Mami, balle itama Mamin lokacin da za su yi sallama har tana sharan ƙwalla kamar kar ta tafi haka take ji.

Bayan tafiyar Mami kamar Ummu ta saduda sai kuma ta koma gidan jiya, ita kenan sai kwanciya tana kuka ba ta cin abinci sai Ammah ta shigo ta yi magana ta tsakura kaɗan, ko Baffa in ya tsaya mata ko kuma ta ji zuwan Hamma Abdulrrahman, ga ta da juna biyu amma ba ta taɓa cewa yau ga abin da take sha'awa ba ko Ammah ta tambayeta ba ta magana sai ta ce komai aka ba ta za ta ci, ita a ganinta ba ta da wani sauran zaɓi kuma a rayuwarta tunda Habib ya sake ta kamar tara sa dukkan wata damarta ne.

Koda Baɗɗo ta koma gida saboda makaranta tana yawan leƙewa duba Ummu Salma, wata rana ma in ta yi dare nan take kwana da safe ta wuce makarantan daga nan haka ma Ummin ikki koda yaushe tana kan hanyar zuwa domin duba Ummu, kuma in dai ta zo sai ta zaunar da ita tana yi mata nasihan haƙuri da ɗaukan kaddara zuwa lokacin tuni Ummu Salma ta yarda da kaddaran Habib ya sake ta amma ta kasa gasgasta kaddaran cewa ya rabu da ita har abada, gani take yi zai zo gare ta ko da take gida zai dawo gare ta, ta kasa ba ma zuciyarta hakuri da fahimtar cewa Habib ya yi mata nisa har lokacin ba ta sare ba, saboda tana son shi duk abubuwan nan da suka faru ba ta jin haushin shi sai ma soyayarsa dake sake kassara tunaninta kuma ko yanzu ya dawo gare ta, za ta iya yin komai domin itama ta koma gare shi. Habib kaɗai ta sani shi ne fa Duniyarta ya za a yi ta fara yin wata sabuwar rayuwar da ba shi a cikin ta. Gaskiyan da Ummu Salma ta kasa karɓa kenan gani take yi ba ta da wani sauran jin daɗi kuma tunda dai ba tare da Habib, ta lamkaya jin daɗin ta da samun komai na duniya a lokacin da take Matar Habib ba a yanzu da ta ƙare ba ta da komai ba.

Tafiyar Mami da kwana goma sai ga Shamsiya afufujan tana kuka wiwi tana faɗin ita ba ta san abin da ke faruwa ba kenan ta yi tafiya zuwa Taraba gidan Sister ɗin ta, tun a can take faman kiran wayar Ummu a kashe kuma ba ta ganin ta a chart hankalinta ya tashi shi ne fa ta kira Baɗɗo ita ke faɗa mata wannan mugun labarin mara daɗi.

"Bestie Habib ya sake ni."

Ummu ta faɗa hawaye suna kece mata.
"Ya sake ni Bestie."
Ta sake faɗa tana mai kwantar da kanta saman cinyar Shamsiya dake zaune a saman gadon ɗakin da Ummu Salma take.

"Na yi komai domin na tsira da aurena amma na kasa Bestie. Na kasa na faɗi.."

Take faɗa tana wani irin gunjin kuka Shamsiya na ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi take faɗin" Sai da na ce ki bi umarninsa Bestie amma kika yi taurin kai, da a ce kin zubar da cikin da yanzu kina gidan mijin ki, da yanzu ba ki zauna kina kukan nadama da dana sani ba."
Take faɗa tana sharan kwalla itama, amma ba ta fasa faɗa ma Ummu ita ce ke da laifi ba, ita ba ta ganin laifin Habib a wannan maganar.

"Bestie su fa iyayenmu tunanin su da namu ba ɗaya ba ne. Ban so ki kawo maganar gida ba, da kawai kin bi umarninsa kin zubar da cikin da yau duk ba a yi haka ba. Da kina can gidan mijin ki ba wanda ya san abin da ya faru."

"Besite ko na zubar da cikin nan ko ban zubar ba Habib ya gama samun duk abin da yake so a wajena. Ba zai ɗaga mini kafa ba sai ya sake ni, da man kawai cikin ya zo a gabar da ya fake da dalilin shi ne, amma ba ya so na ya ma faɗa mini da bakin shi."
Ummu ta faɗa tana cigaba da kukanta.

"Ni fa ban yarda Habib ba ya son ki ba Bestie kawai kin ɓata masa rai ne da kuma shigowar su Baffa cikin maganar, amma ke kanki kin san cewa Habib na son ki Bestie."
Shuru kawai Ummu ta yi mata, ba za ta gane ba ne, amma tunda har ita ta furta mata cewa Habib ba ya sonta to ai ya kamata ta yarda da ita. Itama da fari ba ta gasgasta ba amma daga baya da abubuwa suka yi ta faruwa dole ta aminta ta kuma gasgasta cewa Habib ba ya sonta , sannan saboda jikinta ya aureta kuma tun da ya gama biyan bukatar shi ai ba ta da wani amfani a wajen shi kamar yadda ta faɗa.

"Shima ya yi kuskure me ya sa ya yi saki uku? Ai da ya yi ɗaya ne in iyaye suka shiga ciki sai a gyara lamarin. Ni fa har kiran shi na yi ta yi bai amsa kirana ba daga karshe ma kamar ya rufe ni ne kwata-kwata bana samun shi."

Ta faɗa tana kallon Ummu Salma wacce ta miƙe daga kwancen da take, tana kallon Shamsiya da mamakin maganganun ta.
Ta buɗe baki za ta yi magana kenan Shamsiya ta katse ta.

"Ban ji dadin faruwan wannan lamarin ba Bestie. Na yi miki kaico domin da wahala ki samu kamar Habib. Ba ma tamtama ba za ki taɓa samun kamar sa ba har Abada Ummu Salma."

"Za ta samu, za ta samu wanda ya fi shi komai da komai in sha Allahu."
Suka ji magana a bayansu, suna juyawa gabaɗayansu suka ga Ammah ta shigo da kulan abinci ba da niyyar laɓe ba ne, amma ta daɗe tsaye a kofar ɗakin tana jin irin maganganun da Shamsiyan ke faɗi.

"Ammah."

Shamsiyan ta faɗa lokaci ɗaya tana saukowa daga saman gadon. Kulan abincin hannun Ammah ta amsa tana faɗin" Sannu da aiki Ammah."
Ta sakar mata lokaci ɗaya tana cewa" Yauwa."
Sai kuma ta kalli Shamsiya da take sauke kulan a saman side drower ɗin gadon tana mai ɗagowa, Ummu Salma ta kalla ita kuma tana ta kuka har da sauti.

"Shamsiya."

Ammah ta kira sunanta sai ta ɗago tana amswa cikin ladabi.

"Don Allah ki daina tuna ma Auta da wani Habibu. Ba shi da wata amfani yanzu a sabuwar rayuwarta. A matsayin ki na ƙawarta ki lallasheta ne ba wai ki zaunar da ita kina nuna mata kamar ta ci baya ba. Habibu da man bai cancanta da zamowa abokin rayuwar Auta ba, kaddara ce ta aura mata shi kuma yanzu ta raba su. Ina mai baki tabbacin shi ne ya yi asara shi ne kuma har abada ba zai taɓa samun madadin ta ba, amma a gare ta za ta samu ire-iren su masu tarin yawan da sai ta zaɓa ma, kuma ni na faɗa miki Ummu Salma za ta sake yin farinciki fiye da irin farincikin da ta yi a farkon rayuwarta da Habibu."

Ammah ta gama faɗa tana mai kallon Shamsiya, ta ma ɗan kausasa maganganunta, amma har cewar da ta yi da Ummu Salma ta bi umarninsa ta zubar da ciki duk ta ji, kamar a mganganunta ita ba laifin Habibu take gani ba, laifin Ummu ne ita da su iyayenta. Ai ko ba ta san Ummu  bai kamata ta faɗi haka ba, ballanta Ummun ce silan da ya sa ta ma san Habibun gabaɗaya.

"Haka ne, in sha Alkahu Ammah ba zan sake tayar mata da maganarsa ba."
Shamsiya ta faɗa kanta na ƙasa cikin jin nauyin Ammah.

"Yauwa na gode da kika fahimce ni, ga abinci nan bari na kawo muku farantai da ruwa."

Tana gama faɗin haka ta juya har za ta fita sai kuma ta sake juyowa tana kallon Shamsiya. Duk da suke ƙawance da Autar ta ba ta taɓa jin ba ta natsu da ita ba sai yau, haka kurum yau sai ta ji maganganunta sun bambamta da yanayinta.

"Maganar zubar da ciki kuma."

Sai ta dakata tana kallon Shamsiya da ta yi tsuru tsuru.
Ummu ma ta daina kuka tana kallon Ammah ta san halin ta ba ta ɗaukan wani reni ko sakarci ko waye kuwa sai ta faɗa masa gaskiya ita kanta ta ji maganganun Bestie yau sun ɗan yi tsauri amma ba ta ga laifinta ba yanayi ne da tsarin gidan da ta taso kowa abin da ya ga dama yake yi babu takura.

"Na jinjina ma Auta da ta yi wannan jarumtar. Har yau mu iyayenta ba ma cikin nadaman dawo mana gida da ta yi da ciki a jikinta. Tunda dai cikin  kowa ya san uban shi to ai an gama magana. Da Ummu Salma ta tashi a ranar lahira cikin waɗanda Allah zai tuhuma da kashe rai gwara ta mutu wajen haihuwa a tashe ta a matsayin shahidiya."
Ammah na gama faɗin haka ta fice daga ɗakin ta bar Shamsiya da ajiyar zuciya.

"Kamar Ammah ba ta fahimce ni ba Bestie"
Ta faɗa lokaci ɗaya tana zama a gefen gadon tana kuma kallon Ummu Salma.
"Ki yi hakuri. Watakila ba ta fahimci maganarki ba ne"
Ummu ta faɗa cikin wani irin amon mai sauti mai cike da rauni.

Sai Shamsiya ta yi mirmishi kafin ta ce" Ba damuwa. Na san anan gaba za ta fahimci in da maganganuna suka dosa."
Ta faɗa  tana sake kallon Ummu cikin mirmishin da ya kasa ɓacewa a saman fuskarta
Sai ga Ammah ta dawo ɗakin ɗauke da filet da cokula guda biyu sai ruwan gora guda biyu ta kawo ta ajiye tana faɗin Shamsiya ta sauko ta zuba musu.

"Sannan ki matsa ma ƙawar ta ki ta ci abinci."

"To Ammah."

Ta faɗa cikin ladabi, kuma ta yi abin da ta saka ta,ta matsa ma Ummu ta ci abinci taliya da miyar jajjage ne. Ummu ta ji daɗin taliyan nan saboda miyan na ta ƙamshin kayan kamshi ta kuma soyu sosai, ga cikin ta ya cika amma bakin ta bai daina son ci ba sai ta koma tana lasan miyan saboda ta yi mata daɗi a bakin ta.

"Bestie ki bar lasan miyan nan kar ki yi amai ko cikin ki ya lalace fa."
Shamsiya ta faɗa tana kallon Ummu Salma na ta lasan miya 
"Bar ni na sha, na ji daɗinta ne sosai "
Jin haka yasa sai ta ƙyale ta, sai da ta shanye duka miyan da ta rage kuma Allah ya taimake ta, ba ta yi amai ba.

Shamsiya na gidan har yamma sai gabda kiran mangariba ta tafi lokacin Baffa ya dawo tun safe daman suka fita da Abdullahi har ɗaki Ummu ta kai Shamsiya ta duƙa ta gaishe shi.

"Lafiya lau Shamsiya, ya kwana biyu ya makaranta?
Ta amsa da lafiya lau mahaifinta ya tambaya Dr. Nura babban ma'aikaci ne a minitary of Education na Jahar Adamawa. 
"Ashe kuma abin da ya faru da ƙawata kenan?
"Wallahi Kuwa Shamsiya "
Baffa ya ba ta amsa.

"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya saka mata."
Baffa ya amsa da Amin yana faɗin" Ya za a yi da lamarin da Ubangiji ya hukunta kenan. Zai wuce in sha Allahu."
Da za ta tafi ya yi ta mata addu'an Allah ya kawo mata miji na gari mai albarka nagartattace. Domin duk wanda ya san Ummu Salma a dangi ya san ta da ƙawarta Shamsiya tun suna yara. Kamar yadda aka san Shamsiya a gidan su Ummu haka aka san Ummu Salma a gidan su Shamsiya duk da mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama matar mahaifinta da suke kira Anty ke riƙonta.
Da za ta tafi bayan ta yi ma Ammah sallama ta ce ta gaida mutanen gidan.

"Ammah don Allah ki yi haƙuri da maganganun da na yi ɗazu ba ki fahimce ni ba ne ba da wata manufa na yi maganar ba na damu da abin da ya faru da Ummu Salma sosai Ammah."
Shamsiya ta faɗa bayan ta duƙa har kasa a gaban Ammah.

Ammah ta yi mirmishin su manya kafin ta ce" Kar ki damu na fahimce ki. Ki gaida gida mun gode."
Har haraba Ummu Salma ta raka ta. Direban gidan su da ya saba kawo ta shi ne ya zo ɗaukan ta.
Sai da suka tafi sannan Ummu dawo cikin gida ta iske Ammah na zaune a falonta kamar yadda suka bar ta.

"Har ta tafi?

Ammah ta tambaya tana kallon Autar na ta 

"E ta tafi Ammah."
Ta faɗa a sanyaye cikin dashewar murya kamar ba ta son magana. Sai Ammah ta ɗan gyaɗa kanta amma ba ta yi magana ba.

Shuru na wani lokaci Ummu na tsaye ita ba ta koma ɗaki ba sannan ita ba ta zauna ba Ammah na lura da ita amma ba ta nuna alamun ta fahimci tsayuwarta a wajen ba sai ma ta yi kamar hankalinta na wajen tibin da yake ta ɓaɓatu. Nan ko tana lura da duk motsin Ummun, tana kare mata kallo daga tsaye har cikinta ga shi nan ya fara turowa ta cikin doguwar rigar dake jikinta amma fa Ummu ta zube ta rame duk ta lalace kullum sai jan fuska da kumburarrun idanuwana saboda kuka, tausayinta take ji in ta kalleta sai ta tsine ma Habibu tsinuwar da ba ta so ya koma ga Allah bai ga sakayya tun a duniya ba.

"Ammah."

Ummu Salma ta kira sunan Ammah, ba ta amsa ba amma ta ɗago tana kallon ta.
Sai kuma ta yi shuru ta kasa magana.
"Me ya faru?
Ammah ta tambaya tana mai tsare ta da idanuwanta lura da cewa kamar akwai magana a bakin ta.

"Da ma Ammah.."

Sai ta yi shuru ta kasa mgana.

"Dama mene ne? Wani abu kike so?
Ammah ta tambayeta cikin kulawa.

"Aa dama mganar da kika ji Shamsiya na yi ne."

"Uhm sai aka yi ya ya?

Ammah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon ta ba.
Sai Ummu ta daburce kafin ta fara mgana tana in da in da.
"Da ma, zan ce ne kar ki ji haushin ta, ba da wata manufa ta faɗi haka ba."
"Madallah."
Ammah ta yi saurin katse Ummu Salma saboda ba ta son ma tana tuna mganganun yarinyar suna kona mata rai, suna sakawa tana jin kamar yarinyar za ta fita daga zuciyarta. Ta so ma ta ce mata in saboda su ko Ummu take kiran Habibu to kar ta sake sai kuma ta ga kamar ta yi tsauri da yawa shi ya sa ba ta yi maganar ba, amma sam maganganun yarinyar ba tausayawa ga halin Ummu ke ciki sam.

Ummu Salma ta gaji da tsayuwa, ganin Ammah ta yi mata banza daga ƙarshe ma cikin ɗakinta ta shiga ta ce za ta yi salla dole itama ta koma ciki ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Bayan ta idar sai ga Baffa da Hamma Saddam sun shigo falon Ammah, sai ta fita falon ta duƙa ta gaishe da Baffan tun da tun safe sai yanzu suka sake samun zama

"Auta ya karfin jikin?

Kanta na ƙasa tana sanye da hijabinta dogo da ta yi salla da shi ta amsa cikin sanyin murya.
"Na ji sauƙi Baffa."
"Kin tabbata ba in da ke yi miki ciwo?
Sai ta gyaɗa kanta sannan ta amsa da cewa ba in da ke yi mata ciwo.
"To Baffa ka tambayeta tana cin abinci?
Hamma Saddam ya faɗa yana yar dariya, da a baya ne harara zai sha a wajen Ummun amma yau kallon shi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba.

"Tana ci mana ko Auta?
Ya tambaya yana kallon ta.
"Ina ci Baffa, yau ma ba ka ga taliyan da na ci ba."
Ta faɗa da ɗan mirmishi. Sai ta ga Baffa na dariyan jin daɗi da man abin da take son gani kenan.

"Madalla da Auta. Sannun kin ji? Allah ya raba ki da cikin jikin ki lafiya."
Kanta na ƙasa ta amsa da Amin a cikin zuciyarta, sai dai idanuwanta sun cika da kwallar tausayin kanta da na iyayenta.
"To gwara dai ki riƙa ci Ummu ko za ki yi kumari, kin gan ki kuwa? Kin ga ƙasusuwan da ke wuyan ki kuwa?
Ya faɗa yana yar dariya cikin zolaya sai a lokacin ta ɗan murmusa kanta na ƙasa.

"Kyale shi Auta. Za ki yi kiba har sai ya ce ki bar ta yi yawa."
Ita dai kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta. Baffa da Hamma Saddam suna ta hiran su, lokaci bayan lokaci suna ɗan sako ta a ciki koda ba za ta yi magana ba har Ammah ta idar da salla ta fito suka cigaba da hiran tare.

"Yaushe hutun na ku zai ƙare ne Saddam?
Baffa ya tambaye shi, kai tsaye ya ce sati na sama za su koma zai bari sai upper week sannan zai koma makaranta. Baffa da Ammah suka yi masa fatan alherin da suka saba a koda yaushe suna nan zaune suna hira har aka kira sallar isha'i Baffa da Saddam suka tafi masallaci itama Ammah ta shiga ciki domin ta gabatar da na ta, sai ita ma Ummu Salma ta tashi ta koma ciki tana da alwalanta ta tayar da salla.

Bayan ta idar ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta zubo taliya ta ciko miya saboda cikinta kamar an yi yasa yanzu tana yawan jin yunwa sosai ba kamar baya ba.
Tas kuma ta cinye tana suɗan kwano, har Hamma Saddam na yi mata dariya Baffa ya ce in bai isheta ba ta je ta ƙaro ta ce ta koshi da yake a falon Ammah ta zauna tana cin taliya su kuma suna dawowa masallaci nan suka sake yada zango.

  Har wajen goma na dare tana falon tare da su Baffa suna ta hira, ita dai ba ta magana amma kuma zama cikin su yana rage mata damuwa da shiga tunani da ɗaki take shigewa zuwan Mami ne yasa dolenta ta fara fitowa falo. Sai da ta fara hamma wajen sha ɗaya saura na dare sannan Baffa ya ce ta je ta kwanta Hamma Saddam ma ya yi musu sai da safe ya wuce ɗakin sa. Ummu kuma bakin ta kawai ta wanke ta sha magungunanta ta kwanta ba daɗewa sai barci.

Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi. A bangaren Ummu Salma rayuwa ba daɗi amma tunda ita musulma ce ta yarda da kaddara kuma tunda tana da rai da lafiya dole za ta cigaba da rayuwa a hakan nan, ta ɗan rage kuka yanzu amma duk lokacin da ta tuna sai ta koka ita kaɗai a ɗaki ta yi kukanta har sai ta ƙoshi sannan ta share hawayenta ta dangana tunda ba ita isa ta mayar da hannun agogo baya ba. Mai afkuwa ta afku ba ta kuma da yadda za ta yi ta gyara abubuwan da suka riga suka lalace tun daga farko.

Har yau kuma Ummu ba ta bi ta kan wayarta ba, tana nan a kashe a cikin kayanta. Duk wanda zai yi magana da ita sai dai ta wayar Ammah. Baɗɗo ce ta ce ta ɗauko wayar ta dawo amfani da ita wataƙila za ta deɓe mata kewa, amma ina ba za ta iya sake amfani da wannan wayar ba matuƙar akwai abubuwa da dama da za su iya tuna mata da Habib da irin rayuwar da suka yi mai daɗi a baya shi ya sa ba ta jin za ta iya amfani da wayar a yanzu in ma za ta yi amfani da waya sai dai sabuwar waya da sabon layin da ba zai tuna mata da komai ba.

In ta zauna tana tunanin farkon rayuwarta da Habib har zuwa ranar ƙarshe da komai ya ƙare. Sai ta ji da man ace ba ta san shi ba, domin sanin shi bai ƙare rayuwarta da komai ba sai ci baya. Ya shigo rayuwarta domin ya lalata mata gobenta kuma ya yi nasara. me take yi haka? me ya sa ta kasa tsanar Habib? me ya sa ta kasa mantawa da shi? me ya rage mata, ba ta da komai domin bai bar ta ba sai da ya ƙwace duka martabanta ya lalata mata rayuwarta ya juya baya ga gudan jinin su? me ya sa ba za ta yanke tsammani ba, ba ta da wani abu da zai sake jan hankalin wani namiji a kanta HABIB ya riga da ya lalata duk wani ƙwanjinta akan ko wani namiji a duniyar nan.

****

* SATURDAY:MURIVILL HOTEL YOLA, ADAMAWA OFF GIREI ROAD.
ROOM:226.
*8:21Pm*

Habib ne tsaye a gaban madubin dake ɗakin Hotel ɗin da ya zama gidan shi a halin yanzu tun bayan rabuwar su da Ummu Salma.
Turare yake fesawa bayan ya gama ya ɗauko wata hula baƙar dara ya ɗora saman sumar kansa da ta sha gyara tunda ya ɗan tara suma. Jikinsa kuma wata farar shadda ce tana maiƙo da yarari daga ganin ta ma sabuwa ce yau ya taɓa sakata saboda yadda take maiƙon sabunta.

Kallon kansa kawai yake yi a madubi yana mirmishi shi kaɗai saboda yau ranar ta musamman ce a gare shi da abar ƙaunarsa. Yau ne rana ta farko da za ta gabatar da shi a wajen mahaifinta a matsayin wanda take so kuma take mafarkin aura. Gabaɗaya jin sa yake kamar yana yawo a saman gajimare saboda tsabar farinciki. Ya saka kaya sama da kala goma ba su dace da ranar yau ba, ga su nan duk ya zube su a saman gadon dakyar ya samu waɗanan na jikinsa suka dace da yanayin yau ɗin.

  Agogon fata baki ya saka a tsitsiyan hannunshi na hagu yana sake kallon kanshi a madubi yana sake yin sakin ɗan mirmishi. Ya ɗauko wani bakin booth ɗin takalmi yana sakawa kenan aka kira wayarsa tun kafin ya duba ya san ita ce domin sun yi magana da ita bayan ya fito wanka ya tabbatar mata da mintina goma zai gama shiryawa ya fito.
Sai da ya gama saka takalmin sannan ya ɗauki wayar dake gaban madubin farinciki ya sake dabaibaye shi ganin ita ce ta kira shi.

"Gani nan zuwa Sweety."

Ya faɗa cikin wani amo bayan ya ɗaga kiran.

"Kar ka bar ni na saƙe wajen jiran ka Habib."

Daga can bangaren ta faɗa cikin muryan shagwaɓa.

"Gani nan zuwa In sha Allahu."

Daga haka suka yi sallama, suna katse wayar ya turata cikin aljihun wandonsa tare da wallet ɗinsa bai tsaya kwashe kayan da ya watsar a tsakiyar ɗakin ba ya suri key ɗin motar shi da na ɗakin ya fice bayan ya rufe ƙofar ya tura komai cikin aljihun wandon sa ya sauka ƙasa zuwa haraban hotel ɗin suna ta gaisawa da ma'aikatan wajen a wattani biyun da ya kwashe a hotel ɗin ya saba da duka ma'aikatan wajen ba laifi, Tun ballanta ƴan ƙananun kyatttukan da yake yi musu, yau ma saboda yau ɗin rana ce ta musamman a wajen shi. motarsa ya shiga da yau ya kaita wanki ta yi fess yadda motar take  fess shima haka yake fes, ya fiddo kuɗin sabbi yan ɗari biyar biyar ya kira wani ma'aikacin hotel ɗin yana daga cikin masu kula da tsaftan ɗakunan Hotel ɗin sunan su ɗaya shima Habibu sunan shi, kuma in dai ya ga Habib ya yi ta masa kirari kenan shi ya sa tasu ta zo ɗaya.

Kuɗin sun kai 20k ya ba ma Habibu ya ce ya raba shi da sauran ma'aikatan gabaɗaya.
Har ƙasa ya duka yana godiya lokaci ɗaya yana masa kirarin da ya saba.

"Allah ya taimake ka ranka ya daɗe Allah ya ƙara arziƙi da wadata."

Habib ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce" Amin Habibu na gode da addu'arka kamar ka san yau rana ce ta musamman a waje na."
"Allah ya kara maka farinciki da wadata Megida."
Ya riƙa amsawa da Amin kafin ya rufo motar ya daidaita zaman shi sannan ya tayar da motar ya yi riverse ya yi hon megadi ya buɗe masa get ya fita, yana tafe yana jin nishaɗi har redion motar ya kunna da wakar Auta waziri yana tafe yana kaɗa kai kamar wani kadangare.

Tun a daran ranar da ya saki Ummu Salma bai yi barci ba sai da ya gama haɗa dukkan abin da yasan mallakan shi ne gari na wayewa karfe shidda na safe ya kwashe komai zuwa mota ya bar gidan. Yadda suka rabu haka yake so alaƙarsu ta ƙare na har abada.

Hotel ya je ya kama ya saka kayan shi a ciki, tunda gidansu yanzu ba shi da mazauni kuma ba shi da in da zai je ya zauna, gidanshi da yake ginawa ba a gama ba, gidan da Ummu Salma ta yi ta mafarkin shi a matsayin ita ce za ta shige shi abin da ba ta sani ba bai kafa ginin gidan nan da sunan ta ba sannan zanen gidan ma ba zaɓin ta ba ne na masoyiyarsa ne da suka shirya sabuwar rayuwa tare, an kusa gama ginin gidan tunda yanzu tayels ake sakawa na ɗakuna da tiolets da an gama za a yi filista da fenti shike nan shi kuma a yadda yake so bikin shi kar ya wuce wata biyu saboda ya ƙosa ya mallaki masoyiyarsa sannan yana son ya samu natsuwa. Tunda har yau za ta gabatar da shi ga mahaifinta an gama mgana, da man a cikin wata ɗaya ta bayyana shi a wajen iyayenta da y'anuwanta mata a matsayin wanda take so yana zuwa gidan su zan ce yau ne za su haɗu da mahaifinta. Jin sa yake yi kamar sabon haihuwa saboda farinciki kamar bai taɓa aure ba. To kamar bai taɓa ba ne domin Ummu Salma amfani ta yi masa kuma tunda ta gama amfaninta ya fitar da ita daga rayuwarsa, sai yanzu yake jin kansa sakayau kamar bai da wata damuwa. Duk da ya ɗan fuskanci ɓacin rai daga wajen Gwaggo da Abba Alhaji Sheriff amma duk ya jure.

Gwaggo haka ta yi ta masa faɗa bayan an ɗan lafa da faruwan lamarin ya je gidan, ba shi da masaniya amma ya san labarin rabuwansa da Ummu Salma zai je musu kuma zargin shi ya tabbata. Mahaifinsa dake kwance haka ya riƙa son ya yi magana da shi amma ya kasa sai kuka hawaye na ziraro masa ta gefe da gefen idanuwansa.

Ransa ya ɓaci ya yi baƙin ciki sannan ya sake jin tsanar Ummu Salma a cikin zuciyarsa. Sanadiyarta iyayensa sun yi fushi da shi. Gwaggo ma sai da ta yi kwanaki ba ta amsa gaisuwarsa har ƴan'uwansa mata wasu sun nuna ba su ji daɗin abin da ya aikata ba shi kuma sai ya ce ai ita ce ta ci ƙwalan shi ta ce in ya cika haihuwan uwarsa da ubansa ya saketa shi ne ya sake ta. Wasu dai sun yarda wasu kuma ba su aminta da maganganunsa ba, kamar Gwaggo da jinsa kawai take yi ta san ya faɗa ne domin ya kare kansa. Haka ya yi ta zuwa Gidan Alhaji Sheriff kusan sau uku amma ba ya ganin shi ya ƙi bari ma su haɗu kwata-kwata, amma duk da haka bai haƙura ba sai ya bi ta hannun Baba Usman da lallashi da daɗin baki ya samu shi ya saurare shi, duk ya ɓata ma Ummu Salma suna a idanuwansa da cewa ba ta da tarbiya rashin kunya take yi masa shi ya sa ya sake ta kuma ma ita ce ta neme sakin, Baba Usman ne ya shiga tsakiya ya sulhutansu da Alhaji Sheriff ya kuma haɗa su waje ɗaya suka yi magana. Habib ya duka yana ta bashi haƙuri Baba Usman na kora wajibin cewa yarinyar ce ashe ta ce sai ya sake ta shi dai Alhaji Sheriff jin su kawai yake yi yasan ƙarya Habibu yake yi ya dai faɗa ne domin kawai ya samu hanyar kare kan shi.

"Koma mene ne wannan ya zama tarihi tunda ya sake ta ta koma gidansu magana ta kare. Habibu kai ba yaro ba ne daidai gwargwado kana da ilimin ka, ka san abu mai kyau da aka sin shi. To ka sani in har kai ne ka yi zalunci Allah ba zai barka ba, in ma ita ce ta zalunce ka duk Ubangiji na gani kuma zai yi ma duk wanda aka zalunta sakayya"

Abin da ya faɗa masa kenan a lokacin da ya sake rankwafa yana sake bashi haƙuri sai ya ɗaga masa hannu yana sake faɗin.
"Ni fa ba ka yi mini komai ba Habibu. Ka je kawai Allah ya kyauta na gaba."
Duk da haka bai haƙura ba yana zuwa gidan shi sannan yana kiran shi a waya har dai ya samu ya ɗan sauko daga fushin da yake yi da shi, shi da man burin shi kenan saboda nan da lokaci kaɗan amfanin su zai ta shi kuma in babu su ba zai samu cikar burin shi ba shi ya sa bai gaji ba sannan bai sare ba, Baba Usman ma duk ya siye shi da kuɗi sannan haka ya yi siyayyan kayan abinci ya kai masa, gidansu ma duk ya kashe bakin su da kuɗi suma ɗin kayan abinci ya siya musu duk da daman ya saba yi, yan'uwansa mata kuma duk ya kashe bakin su da kyauttuka har Gwaggo ma bakin ta ya yi shuru shike nan babin Ummu Salma ya kare a gidansu da zuru'an su gabaɗaya yanzu ne zai sake buɗe ma rayuwarsa wani sabon shafi.

Kai tsaye anguwar Barraks road ya nufa, ya yi parking ɗin motarsa a wani babban gidan bene mai makeken bakin get. Bai yi hon ba sai da ta ya kira ta ya ce ga shi nan a ƙofar gida sai ta ce kawai ya shigo gata nan fitowa. Sai a lokacin ya yi hon megadi ya leƙo shi kuma sai ya zuge gilsshin bangaren  da yake zaune  ya gane shi baƙon gidan ne tunda yana zuwa kuma ya san shi, har ma wani lokacin yana yi masa kyauta 

"Alhaji barka da zuwa."
Bafullatanin maigadin ya faɗa da hausar sa irin ta fulani.

"Yauwa."

Habib ya faɗa yana mirmishi, get ɗin ya ruga ya buɗe masa shi kuma ya sulala motar tasa zuwa cikin haraban gidan da ga motoci nan guda uku a haraban gidan, alamun megidan yana ciki tunda yaran gidan ba sa tuka kansu a mota sai in kin yi aure baban zai ba ki mota amma in dai kina gida direba ne zai kai ki duk in da za ki je, kuma ya koma ya dawo da ke.

Habib ya daɗe yana tunanin kamar gidan da ya zo sun fi ƙarfin shi amma in ya tuna yadda soyayyar su ta fara sai ya ji ya samu ƙarfin gwiwa da yadda abar kaunarsa ta ba shi tabbacin duk abin da suke so shi mahaifinsu ke so, kuma shi ya yarda da kan shi duk da shi ɗan talakawa ne amma yana da ilimi da dukkan nagartan da duk in da ya je za a ba shi aure.

Bayan ya daidaita motarsa a haraban gidan ya ɗau wayarsa ya yi kira.

"Gani na iso haraba."

Ya faɗa yana mirmishi.
Daga can bangaren aka ce.
"Na ga zuwan ka, ina sama ina hangen ka a cikin mota."
Jin abin da ta ce ne ya sa ya ɗaga kai yana kallon saman, dai dai lokacin da aka saki labule aka juya. Mirmishi ya yi zuciyarsa har wani rawa rawa take yi saboda yadda yake daraja wannan ranar.





*Janafty*