TALES OF THE WAZEERIS

Consipracy

by @surayyahms

*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms

#Royal hate-love

#Forbidden bloodline

#Obsession

#royal politics

#Sisters love hate

Bismillah rahmanir raheem.

5.

Da sanyin kamiya uwar jini ta tsura ma nana A data durkusa agabanta ido tana kuka batare da ko ta nuna alaman ta girgiza ba dan ita macece wanda da wuya kaga ta fito fili tanuna maka rauninta a bayyane, duk dama zuciyarta ya riga ya bala'in raunata tanaji ajikinta danta khaleefa ya mutu kusan acikin wata irin nitsuwa ta bayarda hnklinta a nitse wanda zallar kasaitar ta datake ji dashi ne yasaka komi nata yake cikin sanyi.

ajiyar zuciya ta sauke kmr batasan abunda zai fito abakin nana A ba kusan adake tace "Atiqa..ina jinki...

kai tsaye nana A ta tattaro nitsuwarta cikin muryan kuka dake kkrin yafi karfinta ahnkli ta furta....

...uwarjini ki gafarce ni. banyi zaton zanji matukar nauyi wajen furta miki wannan kalman ba

cikin kara fashewa da kuka tace..."Allah yay ma shugaba khaleefa waxeeri vale rasuwa!!!

gawarsa yana can a turakarsa tare da matarsa nana hafsa da dansa abdallah...

cak uwar jini ta dauke numfashinta wajen yay wani irin shiru nadan lokci sai can sautin numfshn uwarjini ya zamto kamar shi kadai ke fita ahnkli tana jin zuciyarta na tafasa kamr zai amon wuta dan wani irin tsananin baqin ciki da rauni me tsanani taji sun kwabe mata gwiwointa a lkci guda saidai harga Allah tasan yanxu ba lkcin jin wayannan feelings din bane.

lokaci ne da zata tsaya ta dauki tsauraran matakai na gaba dan takare zuriarta da jininta, snn ta jefa wann laananen zuria ta zamkora da sukayi sanadiyar da ruhi ya jawo karshen rayuwar babban danta khaleefa a wann dare.

cikin shanye alhinin mutuwa da zafin dake ci a ranta tace"..Atiqa ya isa haka kidena kukan nan...kitashi kawai kije ki kiramin jakade me rubutu. ki sanar da imran, da zafar, akan zancen mutuwar. snn a aika sako can lagos wa yar uwarsu ummu salma acemata umarni na ne marmaza ta tattara ta dawo gida kafin safiyar gobe dan ina bukatr ganin duka yarana taredani agidan nan kafin safiya.

jiki a sanyaye Nana A ta miqe tana share hawayenta batare da amsa ba cikin ladabi ta fice, bata jima ba sai ga tanan ta dawo da jakade me kula musu da duk wata aika da rubutun sirri., a babban falon sashen suka tarar da uwarjini tafito da complete baqin kaya ajikinta tana tsaye tana lissafe lissafe.

yana isowa ta bashi umarni agaggauce akan da ya rubuta sakonnin gayyatar meeting din gaggawa ma duk wani babban masarauta dake nan karkashin ikonsu gobe da safe take bukatar ganinsu a fadar mulki saidai wann karon bata cire zamkora aciki ba.

sosai kansa ya daure dan shikansa bazai iya tuna shekarar da aka yanke duk wata alaqa tsakanin tharim vale da masarautar zamkora ba.

amma dake suna matukar shakka da tsoron uwar jini bai iyayin tambaya ba har saida ta fice, nan da nan ya hau rubuta sakoninsa wa dukan masarautunsu guda bakwai da kuma hakimai da gomnonin dake karkashinsu.

bangaren nana A kuwa kai tsaye suka nufi sashen Shugaba khaleefa tare da uwar jini dan uwar jinin taje taga gawar danta

suna shiga ta samu jikanta abdallah datake bala'in ji dashi sabida tsabar uban kyansa da kwarjininsa, mutum ne nitsattse sosai tunda khaleefa ya haifesa take matukar kaunarsa sabida bakaramin kama da asalin mijinta marigayi shugaba wazeeri tharim vale yakeyi ba. dadin karawa abdallah shine jikanta na farko daya haifi É—a namiji a shekarar farko da yin aurensa da matarsa hajarat-sakeena wacce itama jinin zuriarsu ce.

kallo daya tamasa lkcin yana tsaye tare da dansa shamsan agefensa yana kan shirin yadda za ama mahaifinsa wanka a shiryashi domin gbtr da kwanan keso dan washe gari da sassafe suka yanke hukuncin za'a masa sallah sann a binneshi.

tunda ta shigo ta je gaban gawar ta bude fuskarshi ahnkli tafi minti goma atsaye tana kalla kafin nan ta rufeshi daga nan sai bata kara cewa komi ba araunace tanemi waje zauna akan royal kujeran iko nana A ne kawai take xaune kusa da ita..

daga gefe kuma nana hafsa ne, da surkuwan ta, matar abdallah hajarat-sakeena jinin sarauta ce daga yankin maruwa, ta dan rungume yar autarta mace rihanna wazeeri babbn danta shamsan kuma yana tare da babansa suna shirya gawan atsanake.

anakan shirya gawa harsai can wajajen 10pm na dare snan shugaba imran wazeeri shine 3rd born kuma namiji aciki uwarjini ya samu shigowa daga garin Abuja...

shikadansa ya taho agaggauce sabida saqon mutuwar dan uwansa khaleeefa ya girgixa sa baitsaya ma yaxo da matarsa da yarsa ba.

isowarsa tharim vale bada jimawa ba saiga nan autansu zafar wazeeri ya taho daga garin zamfara shima agaggauce shida matarsa bilqessu da take dauke da katon ciki dan shi bai jima sa yin aure ba.

anan sashen shugaba khaleefar duka aka taru anakan aiwatar da wasu al'adu da adduoi

..

har alokcin uwarjini batace uffan ma kowa ba, dan ko angaisheta saidai ta daga kai a nitse sbd tsananin baqin ciki yariga ya saka bata iya furta ko kala itadai tana xaune ne kmr mutum mutumi akan kujerar iko acikin tunanin zuci mezurfi da kaifi.

Wann daren kusan shine mafi muni acikin zukatansu tsawon lkci suna tare a waje guda da gawar khaleefa da aka kammala gyarawa aka masa komi,wani irin shirune mei nauyi ya mamaye daren.

kowa yana zaune da iyalinsa agefe sai kusan da asubah kfin anty ummu salma, 2nd born na uwarjini ta iso cikin gidan arikice cikin kuka da dumbun alhini tareda da jikarta leelah wadda tay kusan sa'a da shamsan a shekaru

ummu salma itace immidiete sister na shugaba khaleefa wacce ko kadan ba taso datazo duniya amatsayin Æ´a mace ba, dan tsabar son mulki yasaka tayi auri da wuri wuri da tunanin zata haifi É—a namiji da shima zai gaji kujerar iko acikin tharim vale wata rana, sai kuma cikin ikon Allah duk dama tariga shugaba khaleefa yin aure amma Allah bai bata namiji ba sai ya bata Æ´a mace me suna suhaila wazeeri, tanaji tana gani shugaba khaleefa kuma ya haifi dansa abdallah.

nan ma bata rusuna ba da kankantr shekaru tay maza tama suhaila aure da tunanin zata haifa musu namiji su samu magaji, but still itama suhailar bata jima a duniya ba awajen haihuwa ta rasu tabarwa ummu salman yarta mace mesuna falilah amma LEELA ake ce mata..

tarin baqin ciki yay yawa aranta musmn da abdallah ya haifi da namiji me suna shamsan, sai ta soma ganin kamar duk wani abu datake muradi aranta shine kawai Allah ya tattara ya bawa dan uwanta khaleefa ita kuma ya hanata.

tafi shekaru araba'in tana zama a lagos tana lira da business na familynsu amma wann dumbin baqin cikin data jefa kanta aciki yasaka da wuya kaga ta kira gida ko taxo zumunta tharim vale. tana rayuwrta ne a garin lagos da ita da mijinta shima jininsu ne ana cemai alhaj fuad wazeeri da yar jikarta leela data dauki sangarta da son duniya ta daura akanta

tunda ummu salma ta iso kukan baqin ciki kawai takeyi tana kururuwa tana harbe harben iska dan ita macece me tsananin rashin imani, baqin hali da gajen haquri, ya mata zafi sosai daya zamto she dint get the chance to see her brother for the last time duk dama ta jima tana kullatarsa aranta akan duk abunda ke faruwa da ita na rashin samun magaji, tsabar raqin ta kusan babu wanda ya runtsa ido har aka kira sallahn fajr, sann akazo aka fara shiri. kafin kace wani abu dukannin masarautu da sakon uwarjini maqboola hanim yaje musu jiya cikin dare har sun shirya hallarowa da duka hakimai da gwamnoninsu face yankin zamkora.

wanda tunda aka kai musu sakon uwarjini xallan mamaki da girman kai da tsananin kiyayya da tsana shi ya hana sarki murad zamkora bude takardan bare harma yasan me ake ciki bare harma ya bari a aika sakon asanar da masarautar dala.

masarautar Zamkora wani yanki ne babba akarkashin ikon garin dala (kano emirates) wanda uwarjini ke iko da yankin sun gabaki daya...

dolene saqo yabiyo ta hannun sarki murad kafin nan ya isa sama zuwa masarautar kano

sarki murad yasan idan har yabari sakon uwarjini ya isa dala sarkin kano zai iya turasashi suje tharim vale shikuma baiga dalili ba dan haka ya hana sakon isa ga dala

daga dayan bangaren kuwa gabaki daya yankin Maruwa, baushe, nabutu, daura,Talashir, maru,

biram, duk sun amshi sakon manyan hakimai da gwamanoni da ministocinsu iyakan wanda aka gayyata sunxo cikin tharim vale da sassafe.

atakaice dai zamkora ne kawai da dala basu ko karanta saqon ba bare su aiko wani maijin musu ba'asi....

ganin haka yasaka uwarjini bata damu ba dan saida har mutanen da ta gayyatan duka suka iso tharim vale snn tasaka danta na biyu imran waxeeri ya sanar dasu labarin mutuwar shugaba khaleefa sabida abune na sirri basu kaunar bayyana ciwo hakama basu tsananta labarta zancen mutuwa.

wajajen karfe bakwai da rabi na safiya aka taru duka with all the nobles and pure blood na wazeeri snn aka ma shugaba khaleefa sallar jana'iza aka kaisa killataccen wajen da ake binnesu acikin garin maruwa.

garin maruwa kmr maxaunar kakaninsu ne, acikin zazzau din shima garin yake, dan baida nisa da tharim vale, duk wata mace da aka aurota daga waje aka kawota cikin ahalin wazeeri toh daga garin maruwa kawai tafito sbd sune kadai ahali da suke da tsaftaccen jinin zuriar wazeeris ajinin su.

maruwa is like their ancestral town, suna da babban sarki,gari ne da babu gurbattacen jinin bayin wani zuria ko kadan sai zallan family blood line na wazeeris snn anan ne ake binne gawakin ahalin wazeeris gabaki daya tun kakan kakani.

bayan an binne shugaba khaleefa haka duka aka taru a fadar mulki dake can sashen uwarjini anata karban gaisuwa...

babu kowa dayazo daga masarautar dala hkma babu kowa daga zamkora amma sam uwarjini bata damu ba saima dadi dataji aranta da suka fada acikin tarkon data É—ana musu...

dan ta riga tasan ahalin zamkora suna tsananin gaba da ita ba zuwa amsa kirarta zasuyi ba, dala kuma sun fada tarkon da zai saka ta samu sauki wajen sauke sarkinsu sann tadaura jikanta abdallah.

duk wannann wasu lissafi ne data bugasu a kwakwalrta tun tuni

********

kwanaki uku bayan jana’izar shugaba Khaleefa lkcn hawaye sunriga sun fara bushe wa a idanuwa iya abin da ya rage shine wani shiri mai kaifi a zuciyar uwarjini Maqboola Hanim.

haryau bata sake tay kuka ba, bata sake yin wani magana a fili ba. amma sosai tagama lura da yadda sauran masarautu suma suka dau zafi tarefa kullatar masarautar xamkora da dala aransu musmn da basu xo amsa kirar tharim vale ba dan aganinsu ai mutuwar shugaba khaleefa ya wuce gaban komi.

saida ta lura da cewa kowa yana riqe da abun aransa, yau da akayi zaman kwana uku ana gama addua nan ta gayyace kowa cikin babban zauren fada aka rufe kofa tareda da royal coucils da hakimai da wakilai da manyan malamai fa alkalai da gwamnoni ba mai shiga ba mai fita.

shugabannin dukknin masarautu da yankuna dake karkashin su an zauna fuska da fuska da juna domin duka atattauna sauyin tsaruka saidai babu wanda ya yake iya kallon cikin kwayar idanuwan Maqboola dan itace kullum take da cikakken power tare da ikon dire sharuda na karshe akowani irin hukunci da za'a zantar.

a kujerar sama tahau zauna ita da yaranta maza imran da zafar da suka rage mata sai yarta ummu salma datake kama da ita sosai.

hannun uwarjini na riƙe da wata takarda ba ta yi musu jawabi mai tsawo ba snn ba ta yi barazana ba. kamar kullum muryarta na fitowa ne a hankali da sanyi mai saka nutsuwa…

tace "daular nan tana bukatar sabon tsari… domin kada mu sake rasa abin da ba za a iya mayarwa ba..

nan ta É—ora takardar a gaban su duk snn tace ba umarni bane wata yarjejeniya ce domin kare martaban kowa

ajikin takardan an rubuta SHARUÆŠÆŠAN YARJEJENIYA...

kasaitaccen danta zafar ne ya miƙe tsaye ya hau karantawa a fili kowa yanaji afayyace, doka na farko yana cewa duk wanda ya riga ya saka hannu daga yau duk wani haraji da kudaden da zasu shiga yankinsa zasu rika wucewa ne ta baitul-mali na tsakiya, rarrabawa za ta dawo kai tsaye daga fadar tharim vale..

wanda baisaka hannu ba kuma za a rika katsewa tareda jinkirta musu kuɗin harajinsu akai-akai..sann duk rundunar sojoji dake ƙarƙashin ikon duk wata gari da kuma masarauta za ta bayar da kaso na sojojinta da za atura su inda daula taga dama, anan ma in baka saka hannu ba mafi ƙarfi daga cikin sojojinka za'a rika fitar dasu da karfi kullum snn akwai canjin mukamai, da ikon sauya jami’ain tsaro tsakanin masarautu

wanda baisaka hannu ba za'a kwashe duk wani makaman tsaron sa musamman masu aminci snn asauya jami'an garinsa dana uwarjini,..

sann an kafa sabbin dokoki kan kasuwanni, gona da kiwo kowa ana bukatar yana daukar izini daga tsakiya

..babu shirya wani babban taro, ko horon soja ba tare da sahalewar tharim vale ba, za'a kafa sabon masarauta da jinin tharim vale wanda zata rika fallasa kura- kurai da masu aikata manyan laifuka a bayyane musmn wnda basu cikin wann tsari...

daga karshe ya sanar da cewa daga yau Imran wazeeri, shine sabon shugaban tharim vale, sann daga kowa ya saka hannu akan wann takarda doka zata fara aiki daga wann lkcin haka ma duk wani hkunci zai tabbata ga duk wanda baisaka hannunsa acikin wann takarda ba daga zuria zuwa zuria.

babu wani musu babu wani tambaya daya bayan daya suka miƙa hannu suka sanya hannu dan sunsan basuda wani mafita inbasu xamo masu biyayya ba..

awannan ranar aka kulla yarjejeniyar hadin kai ta duka masarautu saidai a ƙarƙashinta wani abu ne daban dake a ɓoye.

ƙakkarfar shiri ne da uwarjini tay wanda zai bada cikakken dama dan ta samu shigewa cikin generational economy pattern na cikin zuriyar zamkora dan ta karya musu arxikinsu da kimarsu acikin ruwan sanyi batare da nuna iko a bayyane ba, shiyasa wann meeting din bawai kawai na simple yarjejeniya bace tarko ne kuma wanda aka fi tanada musu tarkon har yanzu basu gane ba.

A wannan ranar ana kammala saka hannu aka daura shugaba imran wazeeri akan kujerar shugabancin tharim vale. anan take shikuma yay maza ya zaɓi jajayen wuya daga cikin DC commitee na sarakuna,hakimai da alkalai da masana wnda za'ay cikakken zama dasu game da lamarin masarautar dala da kuma zamkora da suka kasance basu cikin tsarin sabuwar yarjejeniyar duka yankuna da aka gabatar..

kai tsaye duka aka yanke hukuncin yin bincike tareda sauƙe duk wani ahali da zuriar da suke kan garagar mulkin masarautar kano (dala)za'a sauya tsarin mulkin kano bisa iko da izinin uwarjini. zamkora kuwa fadar tharim vale ce dakanta tace zataji dasu bayan an gama gbtr da bincike.

ana gama zantar da hakan aka sallame kowa dayazo tharim vale bisa gayyatar uwarjini, kowani yanki da masarauta sun tafi da takardan yarjejeniya. commitee na bincike kuma atake suma suka hau aikin su.

acikin kankanin lokaci garin tharim vale da kewaye suka san da labarin sabon shugabansu mei girma imran wazeeri, bayan kwana biyu ana karban gaisuwar da yamma Nana A ta fito ta samu wani amintaccen steward dinta kai tsaye tabashi wani sabuwar takarda tace

“ka sake aika wann sakon zuwa can masarautar zamkora

kansa akasa yace Ranki ya dade… shekaru da dama babu wata alaqa ko hulɗa tsakaninmu da su inaga shiyasa babu canjin tsari ta wajensu.

murmushi tay kai tsaye tace "Ba canjin tsari bane umarni ne daga uwar jini. nan ta fito da shedar da ruhi ya bayar na agogon zinari tace kaje da wann in sunqi ka tabbata an nuna masa wann agogon...

yace 'toh rankishi dade....bai wata wata ba ya wuce yankin zamkora da dumbin mamaki yaje ya samu an zazzauna a fadar sarki murad zamkora ana famr ƙarban gaisuwar rasuwar mahaifinsa sarki salim zamkora., wanda ya kasance ɗa ga marigayi imamu wazeeri, shima ya jima yana kwance cikin ciwon da uwarjini ce take saka musu, acikin raɗe raɗe steward din yaji ana lisafin cewa ranar da aka binne shugaba khaleefa ranar ne sarki salim zamkora shima ya rasu cikin dare....

dake yana da basira sai bai miƙa sakon ma sarki murad kai tsaye ba sabida yasan yadda yake cikin alhinin mutuwar babansa salim zai iya sakawa ma akashe shi, da layarsa kawai yay amfani ya danna yay yan subbace subbacensa ya billo cikin gidan sarkin snn ya aje sakon akan gadon babban ƴarsa ta gaban goshinsa wato ARISHA murad zamkora da kusan kowa yasan mahaifinta sarki murad yana matukar ji da ita sbd itace yarsa ta farko a duniya, ya balain sakaltata ta kusan sai abunda tace ma babansun kawai ake mata..

Arisha bata shigo dakinta ba kuwa harsai washe gari sabida wasa da hanklin iyayenta datay wajen yin kukan bankwana da tayi da yar uwanta USHNA murad da aka turata wani boarding school a kasar London da karancin shekaru sosai domin yin duka karatunta acan sabida Arisha ta jima da ɓoye bala'in tsanar datakeyiwa yar uwartan ushna acikin ranta...

kusan koyaushe itake take hure ma babansu kunne akan duk wani lamari daya shafi rayuwar yar uwarta ushna cikin ruwan sanyi sai ake ganin kmr soyayya ce.

badon komi ba saidan ta lura kamar bata da wnn natsuwa, ilimi, basira da tsananin kyaun halitta da Allah yariga ya bambamce su dashi, duk dama bata taɓa nunawa a fili ba amma babu wacce takeyiwa hassada a duniya daya wuce little sister inta ushna, saidai a idon duniya da iyayensu kullum takan waske ta nuna ita me tsananin sanyin hali da tausayi ce sann tanama yar uwarta so wanda zaka rantse da Allah babu wanda yakaita kaunar yar uwartata a zahiri...

washe gari da safe tabar royal chambern mahaifinta tashigo private dakinta kenan zata fara murnan cin nasarar korar yar uwarta ushna london datay cikin ruwan sanyi, tanajin dadi aranta kasancewarta ita daya agidan inda zata sake ta baza tsantsar mulki da kasaita kusa da babanta caraf kuwa idonta ya sauka akan saqo, hannu ta miƙa batare da bata lokci ba tana daukawa kuwa ta budesh ahnkli..

agogon zinari daya faɗo ne kasa ne yafara dauke mata ido ta tsuguna ta dauƙa ta dinga kallon agogon tanajin mamaki sai can kuma ta lura da jan hatimi(stamp) ajiki an rubuta tharim vale.

acikin tsananin razana ta sake takardan kasa jikinta na rawa rawa tayi juyi da agogon ahannunta nata tsaya koina ba sai gaban mahaifinta...

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025