TALES OF THE WAZEERIS

the message

by @surayyahms

*TALES OF THE WAZEERIS🦋* Arewabook@surayyahms

#Royal hate-love

#Forbidden bloodline

#Obsession

#royal politics

#Sisters love hate

Bismillah rahmanir raheem.

6.

The message..

cikin rawar jiki arisha ta turo kofar private chamber na mahaifinta ba tare da tay knocking ba tana budewa taga wajen yay shiru da alaman babu motsin kuwa aciki

da wani irin tsorataccen juyi ta nufi cikin fadarsa tanamai damƙe da wannan agogon zinarin acikin hannunta kafafuwanta harna harhadewa cikin sauri sauri ta fado cikin fadarsan kai tsaye da rawar murya me karfi tace

"Babaa...

atake kusan kowa da ke cikin fadar taron ya dago kai lokaci guda suka juyo suka xuba mata ruwan idanuwan su sunata kallonta da dumbin mamakin yanayin data shigo musu fadar dashi..

sarki murad zamkora yana zaune a kan royal seat dinsa jikinsa lullube da alkyabbar mulki nan shima ya dago kyakkwan farin fuskarshi dake a cunkushe da bakin ciki da wani irin gajiya jin qishin qishin na labarin cewa uwarjini tanakan aiwatar da shirin xabqe ahali da duk wata zuria na masarautar kano gabaki daya...

…manyan hakimai da masu fada aji na fadarsa kaf suna zaune a gefensa a cikin yanayin jimami da tsananin jin tsoron abunda zai biyo baya

shigowar yarsa Arisha arikice yadada sakawa duk wani motsi ya tsaya...dogare ya matso kusa tare da daga ido xai mata magana yaga tawani irin dauke mishi kai batare da ta tsaya jin shi bare amsashi ba ta karaso gaban sarki murad kai tsaye ta rusuna…

tunkan yay magana tay sauri tamika masa hannunta data dunkule agogon zinarin a ciki ruwan idanunta sun cika da firgici. ahnkli tace “baba…inaga kmr wannn abun daga tharim vale yazo.

da jin wannan kalma fuskar sarki murad ya sauya acikin sauri ya mike tsaye yanata kallonta cikin hadiye tsana da bacin rai cikin wuyarsa “me kika ce?

agogon kawai ta mika masa ya karba…

kallo daya yay ma agogon jikinsa ya dau wani irin xafi taciki domin tuni ya gane cewa alama ce ta umarnin ruhi.

nan take ya sunkuyar da kai jin maganganun mahaifinsa na karshe na dawo masa kansa yuuuu kamar saukar ruwa inda yake cewa

"Murad,...uwarjini ba mace bace kamar sauran mata duk abinda kake tunanin zaka yi,ita ta riga tayi irinsa, ta riga ta taɓa tunaninsa, tun shekaru aru aru da suka shude. kuskuren ka shi ne girman kai, kullum kana daukawa zaka iya tsayar mata ko ka karya mata iko. ahaka ahalin zamkora ya rasa zaratan maza irinka guda goma daga cikin yan uwanka sbd wannan kuskuren namu. ynxu kai kadai ka rage mana, kada ka bari kiyayya ta rufe maka ido domin kiyayya ba zata taba baka nasara akanta ba. ita bada yaki take cin nasara ba, da hakuri…da lissafi…da lokaci..idan ka tsaya kana kallonta a matsayin makiyyarka toh ka riga kashiga tarkonta. idan lokaci yayi… za ka gane.

cikin lumshe ido da budewa ahankali zuciyarsa na bugawa dakarfi hannunsa da ke rike da agogon zinari yadan matse yanajin zafi da nauyin kalaman mahaifinsa a kirjinsa

ahankali ya daga kai kwayar idanunsa sun riga sun canza kala sunyi jaaaa ya kalli yarsa Arisha yace" A ina kika samu wann agogon..

kanta kasa muryanta na rawa rawa tace a daki na nagani....acikin wani takarda.

da sauri ya daga ido ya kalle zaratan maza masu tsaronsa yace "Ku je tare ta dauka min takardan.

ya bisu da kallon karku sake wani abu ya taɓa lafyar ƴata

nan da nan ta miqe ta wuce gaba mazan nan suna biye da ita daf daf acikin kankanin lkci suka iso cikin dakinta ta tsuguna ta dauki takardan saqon suka dawo cikin fadar agaggauce.

zuwa sukayi suka samu har iyanxu sarki murad bai samu zama ba yana daga tsaye yana jeka ka dawo, tuni iskar dake yawo a cikin fadar ya sauyawa kala izuwa na tashin hankli kusan kowa tunanin abunda suke tsoron faruwa dasu din shine yagama mamayesu taciki.

tana mika masa saqon yamika hannunsa ya karba tareda bude takardar a hankali kwayar idanuwansa na karantawa fuskarshi na kara tsananta duhu.

wani irin shiru mai nauyi cikin fadar ya dauka kusan kowa na jiran me zai biyo baya can sarki murad ya dago kai a hankali yace umarni ce ba gayyata ba.. shiru wajen ya dauka dashi kowa yana kallonsa har ya rufe takardar snn shika ya juyo yakalli dukkan mutanensa dake zaune

“afara gudanar da shirin tafiya... tharim vale…

daya daga cikin manyan hakimansa daya kasa rike fargaba da sauri yace"rankashi ya dade… tharim vale fa kace???..bayan duk abinda yake faruwa tsakanin....

da ido sarki murad ya katse shi cikin tsimewa yace "this meeting is dismissed. zuwa nan da kwana biyu a zamto angama shiri.

shiru ne ya mamaye wajen bayan duka sun amsa, arisha ta tsaya cak tanata kallonshi zuciyarta na bugawa da sauri sauri domin a karona farko kenan dataga fargaba da ciwo mai radadi acikin idon mahaifinta.

bangaren tharim vale kuwa nana A na tsaye agefen uwarjini maqboola hanim a cikin babban zauren fadarta ruwan kwayr idanunta a kasa tana murmushi me sanyi tace an kai sakon…

uwarjini tay shiru bata dago ba saidan karamin mrmshi mai sanyi da ya dan bayyana a gefen lebenta. kasar wuyarta da nitsuwa tace“ hmmm sai ashirya mana zama, zamkora zasu iso nan da kwana biyu..

nana A ta dan dago kai cikin ladabi da mamaki tace..“kina da yakinin haka?ranki shi dade taurin kan murad fa yafara bani mamaki.

cikin katseta uwarjini ta jinjima kai idanunta cike da wani irin zurfi.

“Taurin kansa na banza, ya riga ya fada tarkona ayayinda da la'anannen mahaifinsa saleem ya rasu...

mamaki yasaka Nana A dagowa kai da sauro ta kafeta da ido sbd bbu wanda yasan da labarin cewa tsohon shugaban zamkora saleem yarasu

acikin jan numfashi me sanyi uwarjini ta kara rage murya me tattare da nitsuwar cikin rai tace ..."ni na kashe shi Atiqa!!!...jinin É—a na khaleefa bazai tafi abanza ba. i dont care if yana cikin wutar jahannama makomar ire irensa bayi saidai inada yaqini cewa ynxu shikansa murad baida wani zabi a duniyar nan dolensane yay gggwar amsa kirana ko yaqi ko yaso msmn idan yaga wnn agogon.

tana fadin hakan ta juya kadan takalli Nana A ahnkli tace "yanxu kije cikin fadar iko ki tabbata saqo na ya isa ga dukkan yayana da jikokina ace musu zuwa yau da dare ina son magana dasu...

da ladabi nana A ta gyada mata kai kafin nan saita fita...

kai tsaye sashen Mai girma Imran wazeeri ta nufa inda already ya mamaye kujerar iko na dan uwansa marigayi khaleefa...

tana shigowa fadar iko ta yi gaisuwa, fuskarta dauke da murmushin ganinsu duka tare da ummu salma da kaninsu zafar...

sai abdallah babban jika agidan da suka sakoshi a atsakiyarsu da alaman suna kan zantar da wasu matakai da bayanai ne game da wasiyyar da shugaba khaleefa ya riga ya bayar kafin rasuwarsa.

daga su sai wani babban malamin addinini me ilimi fwanda shi zai kasabta duk wani abu daya shafi rabon gado, da uwa uba batun wasiyar shugaba khaleefa daya bayar na gaggawa akan a tura jikansa shamsan .A. wazeeri cikin daularsu ta darul zahra domin araineshi bisa tsari da umarnin jini.

ganin tattaunawa ce me muhimmanci ya saka nana A bata wani jima agabansu ba tana isar musu da saqon nn ta fice kai tsaye ta koma nata chamber.

Chan da dare bayan isha kamar yadda uwarjini ta bukacesu hakanan duka yaya da jikokinta suka hallara acikin zaurenta....

shugaba imran, ummu salma da zafar. sai jikanta abdallah, da marida babban ya ga shugaba imran, dake zafar harynxu matarsa bata haihu ba tukuna

bayan kamar awa daya

suna tattaunawa aka samu masalaha akan abubuwa guda uku, na farko daura Abdallah akan kujerar mulkin kano, na biyu alkwarin hada auren jini da zuriar zamkora. na uku tura shamsan dahrul zahra dan azamto dashi cikakken dan sarki bisa umarnin khaleefa agaggauce.

cikin kankanin lokaci kowa ya qamsu da wann zantukan face ummu salma da wasu abubuwan basu zauna mata aranta ba...

msmn data san cewa yanxu haka shamsan, shine zai zamu 1st sultan, wato crown prince na farko acikin zuriarsu koda ace zafar da shugaba imran sun haifo yaya maza daga baya

sarauta da mulki zai zamo kenan a zallan zuriar jinin shugaba khaleefa su da baza suyi sarauta ba kenan bandasu, dadin karawa datasan shamsan din shine kadai jika kwalli daya ga marigayi shugaba khaleefa wazeeri wanda akwai wani darajawa da kima me girman gaske kuma na musammn atattare da jininsa, sosai taso ace jikarta leelah kawai shamsan zai girma ya aura dan itama zamo tana da wani sabon iko me karfi a harkokin fadar tharim vale tunda Allah bai bata namiji ba...

taqasa cewa komine sbd tanada yaqinin cewa saida uwarjini tay lissafi ne meikyau kafin nan ta zaɓe jinin shamsan da sanin cewa jini ne me dumbin daraja da ƙima wanda zata cimma tsaftace haɗin auren da zatayi da ahalin zamkora...zunubinta ya a idon ruhi ya kankare ya zamana har abada.

ummu salma tasan koda ynxu ta kawo musu shawarar hada alkwarin aure akan shamsan da jikrta leelah ba lallaine uwarjini ta karba ba.

awajen meeting bata nuna komi aranta ba dan batason ko kadan abasar da ita agaban wanda tasan ta riga ta girmesu da shekaru, ranta a dagule da baqin ciki amma murmushin yake ne a fuskarta kwakwalrta na famar buga lisaafin yadda zata shawo kan lamarin..

dan batajin zatay sake har tarihin jinin zuriarta ta ya tafi abanza, babu wani daraja, ga kaninta imran ya riga ya xamto shugabar tharim vale, bata kuma san me matar zafar datake da tsohon ciki zata haifo musu ba.

...dole ne kawai tasan yadda zatay ta cusa jikarta leelah acikin rayuwar shamsan koda ace zataje gidansa a matarsa na biyu ne bazata wani damu ba.

ita wannan kima da daraja ta jini kawai takeso ace itama ya fito daga tsatsonta.

bayan ankammala tattaunawa an watse har washe gari da safe bata samu nitsuwa ba sai can aikarta ya riske Nana A daga chamberta.

cikin shiri Nana A tasake fitowa, daga ita sai baiwarta sabuwa suka nufo cikin killataccen chamber ummu salma mai tashi da qamshin dark oud wood mei hade da frankincense tanutsa ciki ita daya baiwarta sabuwa na tsaye daga kofa tana kan jiran fitowarta cikin ladabi..

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025