15
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*15*
*DUALA ROAD. APAPA LAGOS NIGERIA*
*NO:447.*
Teusday, 2:30pm.
Wata baƙar mota ƙiran TOYOTA(PRIUS) ta fito daga General Hospital dake Apapa Lagos (C9R9+QG7 Abaraham adesanya road) da misalin ƙarfe biyu da rabi na ranar talata gabaɗaya gilasan motan tintec ne shi ya sa ba lalle na waje ya iya ganin na ciki ba. Gudu motar ta yi ta shararawa a kan shararen titunan da ke Apapa na garin Lagos ba daɗewa sai ga shi motar ta iso anguwan Duala road a bakin wani katafaren gida mai blue ɗin get lambar gidan 447.
Hon motar ta yi ba ɓata lokaci kawai get ɗin gidan ya wangale motar ta sulala cikin haraban gidan, kusa da wata mota itama kirar toyota amma camry dake fake a haraban gidan motar ta tsaya.
Daga can cikin parking space kuma akwai wata ɓakar RAVA ita ma ƙirar Toyota.
Yanayin parking ɗin da ta yi ba ta daidaita tsayuwar motar ba
Da gudu bayarben megadin tare da wani matashi suka rugo a guje har suna bangazan juna wajen buɗe murfin motan sannan bayan sun buɗe suka rankwafar da kawunansu a ƙasa a tare suka haɗa baki wajen faɗin.
"Welcome Mah."
Haka suke faɗa, kuma ba su daina faɗa ba, sannan wacce suke kira da Mah ɗin har a lokacin ba ta sauko daga motar ba, sai da tafi mintina goma sannan kafaarta ɗaya ta fara saukowa farar kafa da wani takalmi mai igiya baki hill mai tsini sannan ta sake sauko da ɗayan kafar nan ma sai da ta ɓata lokaci kafin jikinta da ita kanta su bayyana a waje.
Farar mace ce doguwa mai kaurin jiki jikinta sanye da riga da wando suit na mata masu ruwan toka, wondon yana da buɗewa ta ƙasa, saman rigar jikinta rigan likitoci ne, a jikin ɗan wani anini da ke jikin rigan an rubuta DR. BILKISU BAYERO.
Sannan kanta ta yane shi da wani baƙin mayafi mai santsi idanuwanta ɓoye cikin wani baƙin glass. Kyakyawa ce domin fuskarta doguwa ce ga dogon hancin ta har baƙa yanayin fuskarta ba wani fara'a, hannunta riƙe da jakarta na hannu ƙarama baka yatsunta sanye da zabban gold guda biyu masu kyau da tsari.
Taku ta fara yi cikin taƙama da isa kamar yadda ya zame mata jiki da daɓi'a, ko kallon ma'aikatan da suke rankwafe suna yi mata sannu da zuwa ba ta yi ba ta yi wucewarta ta nufi wata ƙofa babba mai kyau da tsari sai da ta saka password sannan kofar ta buɗe ta shige kuma ta rufe kanta, sai da ta ɓace ma ganin su sannan Maigadi Baban Adila ya koma wajen aikin shi da sauri ya yin da James mai kula da tsaftan haraban gidan sannan kuma shi driver ne shi ke kai yara makaranta ko ya kaisu wajen wassani ko kuma in fita ya kama ma'aikatan gidan, Uwar ɗakin na su ba kodayaushe take yadda a tukata ba ita ke tuka kanta wani lokacin Megidan kuma ba mazauni ba ne, in ma ya dawo ba ya fita ko'ina in kuma fita ta kama shi ba na kusa ba sai dai na nesan da filin jirgi kawai ake kai shi.
Shi ya tsaya ya shiga cikin motar ya gyara parking ɗin sannan ya ciro makullin ɗin lokaci ɗaya yana fitowa ya kuma rufe motar.
Ita kuma tana shiga makeken falon gidan mai ɗauke da kayattatun kujeru saiti biyu, sallaman ma da ta yi a ciki- ciki ta yi amma ƙaran tsinin takalminta ya bayyana shigowarta falon yan aikin ta suka rugo zuwa gare ta.
Sabuwa wata yar dattajiuwa ta karɓi jakar hannunta sannan ta duƙa tana faɗin" Barka da dawowa Uwar ɗakina."
Hadiya kuma yar yarinya ce matashiya itama duƙawa ta yi tana faɗin" Barka da dawowa ranki ya daɗe."
Ma'aikatan cikin gida huɗu ne Sabuwa da Hadiya daga masaautarsu ta taho da su tun auranta da Lamiɗo aka ba ta su, sai Anitha da Debora anan garin ta ɗauke su, Anitha ce mai kula da Sultan da Beena duk abin da ya danganci abincin da za su ci, kwanciyar su ta shin su, aikin makaranta da shirya su komai da komai dai yana sarƙe a wuyan ta ne,
Karatu na musamman ta yi
akan sanin kula da yara.
Ita kuma Debora mai kula da girkin gidan gabaɗaya cikakkiyar Chef ce da ta karanci nau'in girki a jami'a ita ce ke da alhakin kula da duka wani abinci a gidan.
Sabuwa kuma amintattaciyar hidiman Dr. Balkisu ce, duk wani abu da ya shafe ta yana wuyan Sabuwa ne, gyaran ɗakin ta gyaran kayan ta, cin abincin ta da duk wani abu da za ta bukata Sabuwa ke kula da shi, ita kuma Hidaya ita ce mai kula da share share duka gidan da tsabtace ko'ina har ɗakin mai gidan ita ke da alhakin tsabtar gidan ko'ina ya yi kal yana tashin kamshi wannan nauyin yana wuyan ta ne.
Har ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun falon ba ta amsa musu gaisuwar su ba. Debora ce ta ɗibo ruwa mai sanyi daga despenser a wani kofin tangaran mai kyau da tsada ta kuma ɗora shi saman wani kyakyawan faranti mai kyau ɗan caras da shi. Shi ta kawo mata bayan ta rankwafa ta miƙa mata tana faɗin" Welcome Mah."
Sai da ta yi kamar ba za ta miƙo hannu ba sannan ta mika ta karɓa ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙa mata da sauri ta tashi cikin girmamawa ta bar falon.
Da kai kawai ta amsa ma Hidaya da Anitha da ke faman gaishe ta sannan ta ɗaga musu hannu alamun su watse, ba sai ta yi magana ba zaman su da ita na tsawon shekaru uku ko sama da haka ba sai ta yi magana ba sun san abin da take nufi.
Sabuwa ce kawai ta rage a wajen itama tana jiran uwar ɗakin nata ne, sai da ta gama zamanta shuru kawai idanuwanta a lumshe tana ɗan hutaawa sannan ta miƙe da sauri Sabuwa ta rigata mikewa ta yi gaba da sauri wani korido suka shiga, Sabuwa ta buɗe wata ƙofa tana biye da ita a baya suka bayyana a wani ƙaramin falo kayattace. Nan ɗin ma ba su tsaya ba wata ƙofa Sabuwa ta sake buɗewa sai ga su a wani babban bedroom mai ɗauke da gado wanda ya ji shimfiɗun alfarma da wawaken wardrope daƙin very neat, sannan yana tashin wani ƙamshi mai daɗi ga wani sanyi sanyi mai shiga ƙashi yana saka natsuwa da jin daɗi.
komai dai na cikin muhallinsa tana shigowa a gefen gado ta zauna lokaci ɗaya tana warware mayafin da ta yane kanta da shi, ita kuma Sabuwa sai ta isa ma'ajiyar jakunkunanta ga su nan a jikin wani ɗan katako dogo sama da guda ashirin ta ajiyeta a muhallinta sannan ta koma da sauri ta duka a gabanta ta cire mata takalmin kafar nata shima ta koma ta ajiye shi a wani ɗan dirowa mai faɗi in da takalmin suke a jere resas ba adadi ga su nan kala kala iya kallon ka har ka ɓace ƙirgawa.
Sai da Sabuwa ta kwashe komai da Balkisu ta watsar a saman gadon mayafinta da jaket ɗinta tare da glass ɗin ido ta shiga clotheset ta mayar mata a jikin hanger sannan ta rankwafa tana faɗin" A fito lafiya Uwarɗakin"
Ta faɗa cikin ladabi da kai ta ɗan amsa mata lokaci ɗaya tana ɗan mikar da kafafunta a saman tattausan cafet ɗin da ke malale a kasan Bedroom ɗin. Alamun gajiya a tare da ita har Sabuwa ta buɗe kofa za ta fice Balkisu ta kira sunanta a hankali.
"Sabuwa."
Da sauri ta juyo ta dawo da gudu ta duka a gabanta tana faɗin" Uwar ɗakina"
Ta faɗa cikin ladabi da ƙaskantar da kai kallonta ta yi na wani lokaci idanuwanta manya suna mai lumshewa suna buɗewa cikin sanyin murya ta ce" Bai fito ba?
Ta faɗa tana ɗan sauke kallon ta akan Sabuwa.
"Bai fito ba, tunda kika fita bai fito ba Uwarɗakina."
Sabuwa ta faɗa cikin ladabi, Balkisu ba ta bukatar ta yi magana ko hannu ta nuna sun san abin da take nufi
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ce" Na sallame ki Sabuwa zan huta"
Ta faɗa cikin sanyin murya kasa ƙasa kamar ba ta son yin magana
"To to a huta lafiya Uwar ɗakina."
Tana gama faɗin haka ta miƙe da sauri ta fice lokaci ɗaya tana rufo ƙofar saboda Uwar ɗakin nata ba ta son sauti ko ƙara ko hayaniya hatta ƴa'ƴanta sun san yanayin gidan duk da suke yara suna da natsuwa sai gidan ya yini tsit ba ka cin motsin kowa, kowa na bangaren shi yana gudanar da rayuwarsa suma ɗin ma'aikatan gidan suna shashen su luf, sanin masu gidan duka ba sa son hayaniya sun fi son su ji ko'ina shuru.
Bayan fitan Sabuwa ta daɗe zaune tana ɗan daidaita jikinta kafin ta miƙe tiolet ta shige bayan mintina goma sai ga ta ta fito sanye da rigan wanka fara sama sama ta ɗan shafa lotion a saman fatarta wacce ke wani irin shining ds glowing na jin daɗi da hutu clotheset ɗin ta buɗe ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta sake fitowa sanye da wani riga da wando pick, wando dogo ne ya na da ɗan faɗi ta kasa rigar ma haka ba ta kama ta ba amma kayan suna da laushi da ɗan shara shara tunda har ana iya ganin farin pant ɗin jikinta da brazeya ɗin da ta sanya. Gashin kanta a tsife yake yi ba ta da wani suma amma saboda yana shan gyara yana nan mai kyau da shi, ta ɗaure shi da band sannan ta saka wata hula pick tsakiya a buɗe daga saman ne an yi tuntu na kwalliya mai zanen heart. Ta manta da wayarta a jikin jakar da ta shigo da shi sai ta isa wajen kafafunta na lumshewa a cikin lausasan cafet ɗin da ke Bedroom ɗin mai buzu buzu, ta isa wajen jakar ta ɗauko a hankali ta ciro wayarta ƙiran Iphone 16, sannan ta sauke jakar a in da ta ɗauke ta.
Kan makeken gadon da ke bedroom ɗin ta kwanta sannan ja jawo farin bargo mai laushi ta rufe kafafunta, ta ɗan duba wayar na wani lokaci kafin ta sauke ta a gefenta ta juya ta sake juyawa sannan idanuwanta suka fara lumshewa a hankali a hankali kafin barci mai nauyi ya ɗauke ta na gajiya domin tun safe yau take asibiti tana ganin patients.
***
Ƙarfe 3:45pm Balkisu ta tashi daga barci, har an fara kiran salla a wasu masallatan dake kusa da su har da ma waɗanda ke nesa. Duk nauyin barcinta lokacin salla na yi kamar tana ji a jikinta za ta tashi. Shi ya sa in za a tambaye ta a zamanta da Lamiɗo na shekaru shidda wani hali mai kyau ta koya daga gare shi za ta ce tsaida salla a kan lokacin ta. Tunda take da Lamiɗo ba ta taɓa ganin lokacin salla ya wuce sa da gangan ba. Mutum ne mai kiyayewan lukatan salla duk abin da yake yi koma mene ne salla na gaba da komai, ta taɓa tambayan shi ya ya yake yi in lokacin salla ya shiga kuma sai aka yi rashin sa'a yana tuki a lokacin? sai ya ba ta amsa da cewa in ya zo bakin gaba zai tsaya ba zai cigaba da tafiya ba sai ya yi salla, ko ya san wannan ka'idar shi ne in dai a lokacin tukinsa ne.
Tun ba ta saba ba har itama yanzu daɓi'an ya zame mata jiki, tana kokarin kiyayewa lukatan salla. Yanzu ma mika ta yi sannan ta sauko da fararen kafafunta daga saman gado lokaci ɗaya tana mikewa. Tiolet ta shiga ta dauro alwala sannan ta fito ta daidaici gabas ta shimfiɗa darduma babba a ɗan koridon cikin bedroom ɗin nata, ta ɗauki dogon hijabin da take salla da shi a goge a saman side drower ɗin gadon. bayan ta idar da sallar ta ɗan ɓata lokaci tana kirga yatsun hannunta kafin ta shafa adduar'ta a fuskarta lokaci ɗaya tana mikewa ta ninke darduman da hijabin jikinta ta mayar da su ma'ajiyar su. Wayarta ta ɗauka ta sake duba lokaci.
Huɗu har da mintina goma,
wani takalmi ta saka mai taushi na zaman cikin gida sannan ta buɗe kofar bedroom ta fita ba ta zauna a falon bangarenta ba sai ta fita can main falo in da ta iske Debora na faman kwashe lunch ɗin da ta dafa tun ɗazu amma daga matar gidan har Maigidan da ya dawo jiya ba su sauko ba, kuma a ƙa'ida ba za su ci ba sai dai a kwashe a sake jera Dinner wanda aka sake dafawa.
Cikin ladabi Debora ta rankwafa tana yi ma Balkisu barka da fitowa cikin harshen turanci.
Ba ta amsa ba sai da ta zauna saman kujera mai zaman mutum biyu.
Sannan ta ɗaga mata hannu.
Wayarta ta ɗauko tana ɗan dubawa ita kuma Debora ta gama kwashe komai zuwa katon kitchen din da ke can yamma da falon sannan ta dawo ta duka gaban Balkisu tana tambayanta ko akwai abin da take so cikin harshen turanci, domin gidan ba a cika yin hausa ba, matar gidan turanci take yi haka ma yaranta. In har ta yi hausa sai dai in za ta yi magana da Sabuwa ko Hidaya su da suke yan kauye ba arabi babu boko.
Amma kaf ma'aikatan gidan masu ilimi ne, kamar yadda ma mallaka gidan suke da tarin ilimi da nasaba.
"Coffea."
Haka ta faɗa kamar bakinta na ciwo, in da sabo sun saba da yanayin ta. Gidan nan kamar wata masarauta ce ta yan boko domin sarauta da ji da kai tare da takama da ƙasaita masu gidan sun iya shi, to yar Sarki ce fa jinin sarauta a jininta yake yi, maigidan ma jinin sarauta ne, kamar ma ya fi matar gidan ji da sarauta komai na shi na dabam ne.
Da sauri Debora ta koma kitchen ta haɗo mata coffea a cikin wani karamin jug mai kyau sannan ta ɗauko wani karamin faranti fari ta ɗora akai sannan ta kawo mata ta kuma jawo mata ƙaramin table din tangaran ɗin da ke falon ta ɗora komai a kai sannan ta duka ta zuba mata ta zuba kaɗan ta ji Balkisu ta ce
" Is ok."
A hankali.
'Yes Mah."
Debora ta faɗa lokaci ɗaya tana mika mata, sai da ta yi sama da sakwan goma sannan ta miƙa dogon hannunta ta karɓa ta rike a hannunta amma hankalinta na wajen wayarta sannan duka kafafunta suna miƙe a saman kujeran da take zaune ne.
Har Debora ta kwashe komai ta koma kitchen mug ɗin na hannun Balkisu ba ta fara sha ba sai can sama da minti uku sannan ta iya kai shi bakinta ta ɗan kurba sau ɗaya ta mayar da shi saman ɗan teburin gabanta ta ajiye ta cigaba da duba wayarta.
Gidan ya yi wani irin shuru sai wucewar iskar A.C ko tibi ba a kunnawa a gidan yara ne kuma suna da shi a ɗakin su, suma ba sosai suke kallon ba in ma za su yi volume kaɗan ne ko na falo ba mai jiyowa, Balkisu ba ta son hayaniya shi ya sa duk abin da zai saka ta ta ji ta takura ba ta yin shi, to ita data ke ma kwana a gidan koda yaushe kenan ba maigidan da sai ya yi wattani biyu uku ba shi a gidan ba.
Ta yi zaman sama da awa ɗaya a falon nan bayan Debora ba wanda ya sake giftaawa. Sau uku ta kurɓi coffea ɗin da aka kawo mata daga nan ba ta ƙara ba.
Agogon wayarta ta duba biyar da mintina an kusa tashin su Sultan daga makaranta.
Dan ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko da ƙafafunta ta sauke su a saman wani cafet mai taushi da kyau a ido. James ba ya bukatar sai an tunasar da shi lokacin tashin su Sultan ya fi kowa sani tunda alhalin kai su da ɗauko su yana wuyansa ne, tana zaune ta ji an buɗe get an fita daga gidan ka'ida ne da wuri yake zuwa yana bakin makaranta yana jiran su za a tashe su sannan ya ɗaukosu su dawo gida.
Karfe ,5:30pm na yamma ake tashin su kuma tun 7am suke tafiya makaranta tana haɗe da boko da islama ne mai suna AL.TASLEEM ISLAMIC SCHOOL.
Suna karatu tun daga saturday har Wednesday. Thurday ne da Friday ba sa karatu.
Miƙewa tsaye ta yi ɗauke da wayarta a hannunta sannan ta fara takawa cikin wani irin taku na ɗaya bayan ɗaya kamar ba za ta taka ƙasa ba, lokaci ɗaya ƙafafunta dake sanye cikin tattausan takalmi suna nitsewa cikin lallausan cafet ɗin daya malale falon gabaɗaya wata kofa ta nufa daga kudu, sai ka ma lura sosai sannan za ka fahimci akwai ƙofa a wajen tana zuwa ta buɗe a hankali ta shiga, sai ga ta a wani dogon korido tana zuwa karshen koridon sai ga wata ƙofa itama tana buɗewa ta shiga sai ga ta cikin wani falo mai girma da ya ji kayan alfarma sai dai falon ya yi duhu tunda gabaɗaya labulanyan falo da windows ɗin suna rufe ne, ba ka jin motsin komai a falon sai dai na sanyi-sanyi da ƙamshin turaren wuta mai shiga hanci sannan kuma mai sanyaya zuciya.
Daga gabas da falon akwai wata ƙofa ita ta nufa ta ɗan tsaya sannan ta ɗan ƙwanƙwasa shuru ba wani motsi na wani lokaci sannan ta murɗa handel ɗin ta shiga cikin ɗakin.
Bedroom ne shima kamar falon ya yi duhu dum, tunda shima duka windows ɗin a rufe suke sannan labulayan a sake suke.
Tana tafiya takalminta na taka cafet din da ya malale bedroom ɗin idanuwanta na hango masa shi sambal cikin bargo, ba a ganin fuskarsa tunda ya yi kwanciyar gefen dama ne ya danne fuskarsa da filon da ya rumgume a hannun shi da shi.
Har ta iso gaban shi bai sani ba domin barcin sa kawai yake yi, amma fa ko hucin numfashin sa ba ka ji hakan zai alamta maka ko barcinsa cikin natsuwa yake yi
Ta ɗan jima tsaye tana kallon shi, kafin ta ɗan matsa baya ta isa jikin window ɗin ɗakin ta zage labule gefe da gefe sannan ta buɗe glass ɗin haske ya shigo.
Kan drowers ɗin gefen gadon ta ɗau remot ta rage karfin A.C ɗin. Ta rasa yadda aka yi Lamiɗo ke son sanyi haka da yawa daga ɗan shigowarta ɗakin barcinsa sai da ta ji sanyin har kasusuwan jikinta.
Shi fa ko hatta handel ɗin kofar ɗakin shi in ka taɓa sanyi ne ƙalau saboda ko yana nan ko baya nan ba a kashe A.C ɗakin 24/7 cikin sanyi yake yi, ita ta yi ta cewa sanyin ya yi yawa amma shi haka yake so duk da bai taɓa faɗa mata yana son sanyi ba a zamansu na shidda biyar ta fahimci haka, in ta zo ta ga ya ƙure sanyin za ta ɗauka ta rage ba zai yi mata magana ba amma tana barin wajen zai ƙara karfin gudun sanyi, tun ba ta fahimta ba har ta gane, daga baya sai ta fahimci haka Allah ya yi sa yana son rayuwa cikin sanyi, in ta ma tuna shi da yake rayuwa a saman ruwa ya saba da sanyi ba lalle ya yi masa illa ko cutarwa ba.
Har ta dawo ta zauna a gefen gadon saitin da kafafunsa ke shimfiɗe bai sani ba. Bargon ya ɗan yaye kafarsa doguwa fara sambal mai cike da gargasa mai yawa ta bayyana a waje, ɗan mirmishi ta yi har bakinta na matsowa wayarta ta ajiye a gefenta sannan ta saka taussaun hannayenta ta ɗago kafar tasa ta ɗora a saman cinyarta, lokaci ɗaya tana jan yatsun kafafunsa da suke wasu irin dogaye tafin kafarsa wani irin taushi kamar bai taɓa taka k
Ƙasa ba saboda yadda suke wani ja ja da fari fari kal, haka kumbunansaa kamar kumba bai taɓa fitowa ba tsabar yadda suke tas da su. Har ta gama jan yatsun na shi kuma duka sun yi ƙara, ita haka kurum tana son kafafun Lamiɗo balle ma in ta yi ta jan 'yan yatsunsa suka yi ta ƙaran nan yana saka ta a cikin nishaɗi.
Ɗayan ta jawo daga cikin bargo itama ta ɗaura a saman cinyarta itama kamar ɗayan haka ta yi mata amma ko motsi ma mallakin kafar bai yi ba duk da ta san zuwa yanzu ya san da wanzuwarta a ɗakin tunda ba shi da irin nauyin barcin nan.
Gargasan kafarsa guda ɗaya ta ja da ƙarfi har sai da ta tsinke, hakan da ta yi ne ya sa ya ɗan motsa kafarsa guda ɗaya sai ta kalle shi da mirmishi a fuskarta kafin a hankali ta ce.
"Ranka ya daɗe ka tashi haka nan yamma ta yi "
Ta faɗa wani wani irin omo mai cike da aji da sanin ciwon kai
Shuru kamar ma baya jin ta, domin bai kara motsawa ba
"Tun jiya da daddare da ka shigo gidan nan kake barci har wayewar garin yau. Ba ka ci komai ba fa Ranka ya daɗe?
Ta sake faɗa tana ɗan jan gargasan kafarsa guda ɗaya.
Sakwan goma sannan ya iya motsawa daga kwanciyar lokaci ɗaya yana cire filon da ya rufe fuskar shi ya mayar da shi bayan shi, sannan ya miƙe a hankali kamar bayansa ya samu matssala bakinsa na ɗan motsi yana karanta adduar tashi daga barci, lokaci ɗaya kuma yana sauke kafafunsa daga saman cinyarta ya samar musu mazauni a saman lallausan cafet ɗin ɗakin.
Kafin kuma da sauri ya saka hannu yana kare fuskarshi saboda hasken waje ya ɗan shigar masa ido.
"Ni na buɗe windows saboda haske ya shigo kaɗan."
Ta faɗa cikin sautin ta, akwai wuta amma ba ta kunna gulop ba sanin ba ya son haske sosai.
Miƙewa ta yi ta ɗuka a gaban shi hannu kawai ta ɗan zira kasan gadon sai ga shi ta jawo masa wani ttatausan takalmi na maza zuwa wajen kafafunsa.
Ba musu ya zura dogayen kafafunsa a ciki sannan ya yunkura ya miƙe lokaci ɗaya itama tana miƙewa sai ga ta a gaban shi yar firit. Kallon shi take yi tana mirmishi a fuskarta shima ya kalleta da idanuwansa masu ɗan girma kaɗan kafin ya ɗan rusuna su, mirmishi ya yi mata amma daga gefe da gefen bakin shi ne kawai ya ɗan motsa.
Muhammad Nasiru Muhammad (Lamiɗo) Sannan kuma Yariman Daura, magajin mai Maimartaba Yarima mai jiran gado.
Wani irin dogon namiji ne faffaɗa, ga tsaho ga jikin murjewa ta cikakkun maza. Lamiɗo na da tsawo sosai domin ko size ɗin takalminsa 45 ne, kuma wannan tsahon na zuru'ar sarkin Jafaru ne, sarki na 11 a tarihin masarautar Daura, shi ne asalin tsatson su har kawo yanzu. Su ke da wannan tsawon kamar ƙiran samudawan farko, sannan suna da girman jiki matansu da mazan su. To Lamiɗo haka yake har ma yafi mahaifinsa Maimartaba Alhaji Dr Nasiru Muhammad Daura cika ido da ƙwarjini. Ahalinsa na Daura ba su da hasken fata sosai amma shi Lamido fari ne jajir, saboda Mami farar bafullatana ce kyakyawa, a wajenta ya ɗauko dogon hanci amma fuskarsa tana da ɗan faɗi ita kuma ta mahaifinsa ce, amma sumar kansa mai santsi da cika ta Mami ce, da yake shi ma'abocin tara suma ne gashi nan sumar ta yi yawa ta kwanta luf tana shan gyara. Sannan bakin sa yana da ɗan faɗi kaɗan zagaye da sajensa da ya zagayo har gemunsa da ya yi ɗan tsawo. Lamiɗo tun yana saurayinsa yana son tara sumar kai da barin gemu har kuma yanzu bai sauka daga kan wannan daɓi'an nasa ba.
Ko a yanzu ma gashi duk ya cika fuskarsa amma duk da haka kyawunsa da cikar zatinsa sun bayyana. Balle ma da ya fara tafiya ya bar gaban Balkisu cikin tafiyarsa ta gif gif ta cikkakun mazan duniya kallo ɗaya za ka yi masa ka shaida Muhammadu ɗan Nasiru da Fatima Sadauki ne, kuma jarumi ne yanayin sa irin na fusattatun maza ne giant masu mazantaka da ke dukan zuciyan duk wanda ya kalle su, jarumatar su ba ya ɓoyuwa, sannan suna iya rike numfashin wanda ya kalle su gaba da gaba na wani lokaci saboda ƙwarjini da haibar da baiwa ce Allah ya ba su, sannan yanayin su komai karatun mutum akan sanin hallayan ɗan adam baka isa ka fahimci yana yin su ba, ko ka ce ga abin da suke so ko ba sa so ba, irin su Lamiɗo sai zama ya haɗaku na shekaru masu yawa shi ne har za ka iya fahimtar lamuran rayuwarsu, amma ba wai don su furta da bakin su ba.
"Wanka za ka yi ranka ya daɗe?
Balkisu ta faɗa tana mai kallon bayan shi.
"E.."
Ya amsa mata cikin dakakkiyar muryansa amma cikin sanyin amo a karon farko sannan ya tura ƙofar tiolet ɗin ya shige ya rufo.
Numfashi ta fesar tana mai sake bin bayan shi da kallo bayan ya shige. Sanye yake da bakin wando wanda iyakarsa gwiwan kafafunsa sannan jikinsa wata farar riga ce mai dogon hannu tana da botira a gaba amma bai saka boturan ba, ƙirjinsa mai cike da gargasa ya bayyana a waje kuma tasan ma dalilin da yasa ya yi saurin barin in da take tsaye saboda haka ne.
Tunda take ba ta taɓa ganin namiji mai kunya irin mijinta Lamiɗo ba
Yau shekaran su shidda da auren su tare da albarkan ya'ya biyu amma bai taɓa yarda ta gan shi daga sama har ƙasa naked ba, itama za ta yi rantsuwa bai taɓa kallonta haka ba. Da farko ta ɗauka ko ba ya son ta ne yasa yake yin haka sai da zaman su ya mika ta fahimci haka Allah ya yi shi, yana jin kunyar tsaraici shi ya sa ko kayan barci baya sakawa masu sharara, in zai kwanta sai ya saka dogon wando, da riga mai dogon hannu ya rufe jikinsa ba ya so ya fidda wani tsaraici na jikinsa duk ko da ita ɗin matarsa ce, yana jin nauyi da kunyar ta gan shi a haka, shima bai iya mata dogon kallon matukar ta fidda masa tsiraici, domin akwai wani lokacin tana da cikin Sultan suna gudanar da Sunna ta kudiri niyyar sai ta ga abin da Allah ya hallata mata. Ita da mijinta amma ace ba ta san girman shi ba, sai da ta bari sun natsa cikin harkan sannan ta kunna hasken ɗakin, ranar ta ga abin mamaki da saurin gaske ya faɗa gefenta cikin zafin nama ya jawo bargon dake gefe ya rufe jikinsa, sannan ya juya mata baya cikin wani sauti amon murya ya ce itama ta rufe jikinta. Ta daɗe lamarin yana ba ta mamaki kuma ta ji haushi har sai da ta yi masa magana da cewa ita fa matarsa ce halaliyarsa amma yana jin kunyar ta ga jikinsa, ko shima ya ga jikinta. Har ta gama maganganunta bai ce mata komai ba, bai ma sake tayar da maganar ba sai da ya tafi ne ya tura mata da saƙon cewa ta yi haƙuri daga haka bai ce komai ba kuma bai sauya ba, dole ita ta bi shi a yadda yake tunda haka Allah ya hallice shi, hallayan shi ne a haka kuma ba zai iya canza kan shi ba.
Gadon ta ɗan kakkabe tana ninke farin bargon. Gabaɗaya ɗakin kalan baki da fari ne Lamiɗo na son abu fari kuma yana son baki ko kayan shi rabi farare ne rabin su kuma baƙaƙe ne, bayan ta gyara gadon ta ninke bargon ta ɗan saka shi a gefen gadon ya ɗan ba da styel, itama sai ta koma ta zauna tana ɗan mirmishi.
Tana son mjinta tana son Lamiɗo, lokacin da mahaifinta ya kirata akan Lamiɗo ta ji wani iri, da jin labarin Baban shi ne ya yi gadon Sarauta, mahaifiyar shi ba yar kowa ba ce. Bata taɓa tunanin haka za ta ga Lamiɗo ba, sai da ya zo haɗuwar su ta farko anan ta fahimci ko a cikin maza shi na dabam ne, ko ita da take jinin sarauta gaba da baya tunda kakanta na bangaren uwa ya yi sarautan Kano, to ba za ta nuna ma Lamido iko da sarauta ba, tafiyar shi, maganar shi, yanayin tsarin rayuwarsa kaf kamar wanda aka haifa a gidan sarauta ya kuma girma acan, sai ga shi ta ji labarin shi bai ma zauna a Daura ba sai da ya girma ya zo. Kenan duk wani abu na hallayar shi ko yanayinsa halitar shi ce haka Allah ya yi shi.
Ba auren soyayya suka yi ba kakar sa Fulanin Daura ce ta zo ta nema masa auran ta, saboda kyayawan alaqan da ke tsakanin masarautun ba jayayya aka amince, kuma daman a zamanin da muke ciki ƴa'ƴan sarakuna sai ƴaƴan sarakuna ƴan'uwansu ko kuma ƴaƴan masu riƙe da madakan ikon a kasar gabaɗaya. Shi ya sa sai haɗin ya yi daidai duk da ana ta cewa mahaifiyar Lamiɗo ba ƴar sarauta ba ce wataƙika ba zai yi gadon Sarauta ba amma kwarjinsa da tasirinsa bai gushe ba. Balkisu ma tun a ganin farko da ta yi masa ta ce ya yi mata tana son shi. Duk a tunanin ta wannan shuru shurun na shi, da wannan ji da kan duk zai sauke su bayan aure. Itama jinin sarauta ne tana ji da takama da girman kai amna haɗuwarta da Lamiɗo sai ta sara ta kuma jinjina masa ta san ita ba ta yi komai ba. Bayan auren su babu abin da ya sauya Balkisu ta yi tunanin za su yi soyayya ta kwatance a yanayin yadda take, yar gayu wayayyiya mai ilimi. Amma sai ta ga sabanin haka, shi fa ba ka iya gane yanayin da yake ciki yana son abu ko ba ya so duk ba ka isa ka gane ba. Ta sha wahala sosai kafin ta fahimci Mijin data aura, komai in za ta yi masa ko ya yi masa ko bai yi masa ba, ba zai taɓa magana ba in ya yi masa ba zai nuna alamu ba, in ma bai yi masa ba, ba zai nuna ba.
SSai da ta yi ta karatun nazarin hallayan Lamiɗo sannan ta fahimce shi, shekaran su shidda da aure ba ta taɓa jin ya ce yana son ta ba, sunan ta ma bai wuce sau goma ya taɓa kira ba, in ma magana ta kama sa dole sai dai ya yi maganarsa kawai kai tsaye, da yawan lukata baya gida in ya kirata a waya suna gaisawa ya tambayi yara bai kara cewa komai sai dai in ita ce ta dauko masa hira. In ya dawo za su zauna a gida ɗaya amma bayan gaisuwan safe in dai ba itace ta yi masa magana ba za su iya yini su kwana ba su sake yi ma juna magana ba. Zai iya yini a bangarensa bai fito ba, wani lokacin sai dare in ya fito cin abinci tare da yara. Tunda duk da yanayin shi yana son yara yana wasa da su Sultan, suma ɗin akwai lokacin haka in yana son kaɗaici ma ba zai fito daga bangarensa ba yana son shuru fiye da komai a rayuwansa.
Bangaren abinci kuma sai da Ammah ta taimaka mata ta ɗan ba ta satar amsa, duk da ba ita ke yin abincin ba sai dai ta ba da umarnin a dafa masa. Lamiɗo na cin tuwo amma ba ya shan duk wata miya mai yauƙi, ba ya son yaji ba ya son mai ya yi yawa. Ba ya cin naman jan akuya sai kaza ko kifi, kuma ba ya cin shinkafa tsura ko wani abu sai da miya, miyar ko wata iri amma ban da miyar yauƙi, yana son ganye sosai. Da Balkisu ba ta sani ba ta yi ba shi miyar yauƙi sannan ita tana son cin yaji. Gashi dai ba ya so amma ba zai taɓa magana ba, sai dai ta ga baya ci da yawa sai dai ma wani lokacin ya yi ta cin abun gaya ba miya, in ta yi masa mgana sai dai kawai ya yi mata shuru, Ammah ce ta taimaketa anan ne ta san ba ya shan miyan yauki. Shi fa in dai shi zai fada maka abin da yake so da bakinsa to ba za ka taɓa sani ba. Tuni Balkisu ta sauke jin kai da sarauta ta fara karantan mijinta domin ta san cewa ba irin mijin kowa ba ne, Lamiɗo mijin Balkisu na dabam ne a cikin maza.
Da haka ta samu ta karance shi tsab har suke zaune lafiya cikin mutumtawa. Ko bai furta da bakin shi yana son ta ba, tana ganin haka a aikace. Ba ta damu ba ta amince da na shi salon nuna son ne a haka bai taɓa danne mata hakkinta na aure ba, tana daga cikin sahun gaba a matan da suka yi sa'an aure, ta samu miji na nunawa sa'a ga shi gwarZo kuma jarumin namiji mai iyawa da duka bukatunta, farkon auren su sai ta zauna jiran sai ya zo gareta ta yi ta cutuwa shi kuma ko yana son abu ba ya nema. Ba ma ka gane yana so ko ba ya so. Shi ya sa da ta fahimce shi ta riƙa ba da kai bori ya hau abin mamaki kuma sai ya fi ta ma rawan jiki da son nuna jin daɗinsa, tun daga lokacin ba ruwanta in tana bukatarsa za ta je gare sa shi kuma a kowani hali yake ciki bai taɓa tankwafar da bukatarta ba sai ya tabbatar da ta samu gamsuwa ɗari bisa ɗari.
Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta ji karan buɗe kofar toilet ba sai dai kawai ta gan shi ya fito sanye da rigan wanka baka, gaban rigan ta ɗan buɗe, ganin ta a zaune kuma sun haɗa ido. Da sauri ya juya baya lokaci ɗaya yana jan rigar wankan ya rufe ƙirjinsa.
"Me za ka ci na sa Debora ta dafa maka."
Ta faɗa cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana mikewa tsaye.
"Anything is ok. Buh zan fara da Coffea mai zafi."
Shima ya mayar mata da martanin maganarta cikin harshen turancu muryansa mai kama da ta jaruman maza.
"Okay"
Ta faɗa, bai ma jira ta fice ba shi ya fara shigewa cikin clothset ɗin sa, domin ya sauya kaya. Ita kuma sai ta fice tana zuwa main falo su Sultan na shigowa falon James na bin bayansu ɗauke da jakunkunansu da basket ɗin su na makaranta
Suna ganinta Beena yarinya yar shekara uku
Yar ajin Baby class dabar dabar da lukutun jikinta na yara ƴan hutu ta nufe ta da gudu da karamar muryanta tana kiran sunanta
"Momi."
Da sauri ta tarbeta ta ɗaga ta sama tana nishi, tunda Beena akwai jiki kamar kazar turawa.
"My Beena."
Ta faɗa tana jan kumatun ta, ita kuma ta tsinke da magana tana fada mata ta ci egg a makaranta da plantain, da muryansu ta yara da turanci tana jinta tana dariya, Sultan kam a natse shi ya kariso falon yana faɗin.
" Good Afternoon Momi."
"Afternoon My Sultan. How was school?.
Ta faɗaa tana ɗan shafa kan shi. Shi nursery 1, yake shi ne sak Lamiɗo Beena ce ke kama da ita.
Ya amsa mata da lafiya lau da turanci yaro ne ɗan shekara biyar amma yana da tsawo da ɗan kiba shi ya sa sai ka yi zaton shekaransa takwas in ba ka san shekarunsa ba.
Anitha ta fito daga wani korido daga yamma da sauri domin ta na sane da lokacin dawowar yaran tunda alhakin kula da su yana wuyanta ne suna ko ganinta Beena ta ƙwace a hannun uwar ta nufeta ita kuma ta tarbeta tana mata oyoyo.
James cikin ladabi ya gaisar da Balkisu sannan ya sauke kayan hannunsa ya fice daga falon.
Har Anitha ta ja Beena zuwa cikin ɗakin su Sultan yana bin bayan ta Balkisu ta kira shi yana juyowa ta ce
"Ku sauya kaya ku ci abinci Papa is at home."
Jin ta ce Papa ya sa ya fara tsalle yana murnan Papa ya dawo ya bi bayan Anitha har suka ɓace ma ganin ta, tana tsaye tana kallonsu tana mirmishi,. Ba su san ya dawo ba tunda a jiyan ma cikin dare ya iso gidan kuma ya kwanta yau yana ta barcin gajiya ba su haɗu ba.
Kitchen ta shiga ta iske Debora na ta aikin Dinner tana ganin ta ta rankwafa tana gaisheta ba ta amsa ba ta ce ta haɗa ma Baban su Sultan coffea mai zafi nan da nan ta amsa falo ta fita ta zauna ba daɗewa sai ga shi ta haɗo ta kawo mata a cikin wani karamin fulas fari da karamin mug fari da faranti, Balkisu ta karɓa ta wuce da shi ɗakin Lamiɗo ta iske shi ya sauya kaya zuwa wani wando blue da farar riga mara hannu yana gefen gado yana kunna wayarsa da tafi sati a kashe.
Karamin teburin tangaran ɗin da ke cikin bedroom ɗin ta jawo ta sauke farantin hannunsa.
"Thanks"
Ta ji ya ambata a saman leben shi, halin shi ne duk abin da za ta ba shi ko za ta yi masa zai yi mata godiya wannan daɓi'an shi ne..
Zuba masa ta yi ɗan daidai a mug ɗin sannan ta miƙa masa ya karɓa yana sake yi mata godiya wannan karon da harshen fillanci, duk da ba ta ji amma tana tsinta a bakin shi da bakin yaran tunda yana yi musu magana da fillancin.
Gefen shi ta koma ta zauna shi kuma sai da ya kunna wayar sannan ya kai mug ɗin baki ya kurɓi coffea ɗin. Tun safe bai saka ma cikinsa komai ba rabon sa da wani abu tun jiya da daddaren da ya dawo ya sha tea. Barci ya yini yi na gajiya yanzu haka ma yana jin kamar kasusuwan shi suna naɗe tsabar gajiya.
Sama da wata ɗaya shi ke tuƙi saboda zai bar aiki da kamfanin don kar su bar shi ya tafi haka shi ne sai da suka wahalar da shi, yanzu dai ya samu sun karɓi takardan barin shi aiki sun saka hannu shi ne dalilin dawowar shi gida, nan da wattani biyu zai fara aiki da abon kamfani amma yana da sauran hutu kafin ya kama aiki.
Yana kurban tea din yana ɗan duba saƙonnin dake reto a saman wayarsa.
"In ka samu natsuwa ka kira Maimartaba da Fulani sun kirani suna tambayana kai, da cewa ba su same ka a waya ba"
Balkisu ta faɗa tana kallon shi. Kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce a hankali
"Har su Ammah ban yi magana da su ba."
Sai kuma ya yi shuru ya ɗan ka fasali kafin ya cigaba da faɗin." Zan kira su, "
Sai kuma ya kalleta kafin ya ɗan kurɓi tea ɗin hannun shi
"Ina so ma na je,"
Ta san bai gama maganarsa ba shi ya sa ba ta katse shi ba.
"Na samu sauyin kamfani. "
Numfashi ya fesar a hankali sannan ya a jiye mug ɗin hannunsa a saman teburin gabansa.
"Zan yi hutun 2 month."
Jin ya yi shuru ya sa ta san ya gama magana.
"Ranka ya daɗe dogon hutu haka? Har Daura za mu je?
Ta tambaya cikin fara'a.
Kai ya ɗan daga mata kafin ya ce" In sha Allahu."
"Har da ni za a yi tafiyar?
Ta tambaya
"In za ki je.".
Shima ya ba ta amsa a yanayin maganarsa.
"In ba za mu daɗe ba, zan iya ɗaukan excuse a wajen aiki "
Sai ya jinjina mata kai, ta san halin shi zai ce in da takura ta yi zamanta
"Har da su Sultan?
Bai kalleta ba, amma dai ya ɗan motsa kan shi alamun e, sai ta fara yi masa bayanin sun koma makaranta, amma dai ba matsala in dai ba za su dade ba
"Sai ki dawo tare da su."
Ya furta daga haka kuma ya tsuke bakin shi.
Ma'ana shi yana can ita za ta iya dawowa da yara.
Tana da murna da jin daɗi za su samu tafiya ita da shi da yaran su abin da ba sa samu sai a shekara bai wuce sau ɗaya ba.
Duk da ba hira suke yi ba amma tana tare da shi har aka kira mangariba sannan ta kwaso fulas da mug din zuwa kitchen shi kuma ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi isha'i bayan ya shigo ya ɗan bata lokaci a haraba suna gaisawa da su Baban Adila da Jamess, Lamiɗo kowa ya san shi mutum ne mara ƙyamar mutane duk da yanayin shi, da ya shigo falon ma haka su Sabuwa suka yi layi suna gaishe shi kansu a kasa duk ya amsa musu cikin yanayinsa.
Kafin ya dawo Debora ta shirya tebur da abinci sama da kala uku, Balkisu kuma ta sake wanka ta sauya kaya zuwa material doguwar riga.
Tana fitowa ta iske shi a falo tare da su Sultan suna masa hira Beena na hawa jikinsa tana sauka.
Sultan ko faɗi yake yi Papa zan sha icream, papa zan ci shawarma Papa sai hira yake yi masa shi dai sai ya yi ta uhm kawai yana ɗan mirmishi, Beena kam tana ta wasa da gashin kansa kuma bai hana ta ba.
Balkisu ta kalle su cikin alfahari.
Tare suka yi Dinner jalop rice mai kaza sai kuma mandirice, shi Lamido Jalop din ya ci sai ya sha lemun abarba. Su kuma ita da yaran suka tsakura sauran abincin Beena ma madaran Naan na yara ta sha, Sultan kuma pepe chicken ya ci Bilkisu kum ta ci Mendi rice din da lemu.
Bayan sun gama cin abincin ba daɗewa Anitha ta zo ta tafi da su domin su yi shirin barci gobe makaranta, suma ba daɗewa suka shige ciki. Debora kuma ta zo ta kwashe komai na saman dining ɗin zuwa kitchen, abincin gabaɗaya ake dafawa su ɗiba na su da na su James ba shamaki, sannan Balkisu ba ta son a gama cin abinci a bar shi a wajen shi ya sa da sun gama take yin saurin kwashe komai zuwa kitchen.
*Janafty*