FARGAR JAJI

16

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

*16*

*Zone ,3. Jimeta*

BAYAN SATI ƊAYA.

Ummu Salma na zaune a tsakar gida a saman kujera yar tsugunno da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safiyar ranar talata.
Farin wake ne a cikin wani farantin silba tana gyarawa Ammah kuma na daga cikin kitchen tana ɗora sanwa amma jefi-jefi tana yi ma Ummu hira wacce ta yi shuru kamar ruwa ya cinye ta. Ammah ce ke ta maganarta ita kaɗai. Baffa baya nan tun jiya suka tafi ibadan shi da Hamma Abdullahi.
Gidan sai ya rage daga Ammah sai Ummu Salma, Saddam ma ya koma makaranta shekaranjiya.

 Gajiya da kwanciya ya sa take ɗan fitowa tsakar gida ko za ta samu abin da za ta iya taimaka ma Ammah da shi amma ba ta barinta ta yi komai sai ta ce ai Likita ya bata hutu, ita kuma ta bata tabbacin ta warke, jiya ne ma Hamma Abdurrahaman  ya zo ya ji suna wannan takaddaman, shi ya yi ma Ammah magana ya ce aikin da za ta yi daga zaune ta riƙa bata saboda ta riƙa ɗan motsa jikinta hakan ma lafiya ce ga abin da ke cikinta shi ya sa yau ɗin Ammah har ta amince ta bata wake ta ce ta gyara mata.

"Saura fa kwana biyu zuwan su Lamiɗo Auta, daga yau sai gobe jibi ne ya ce mini za su taho."
Ummu ta yi shuru hankalinta na kan waken da take gyarawa amma kuma hankalinta da tunanin ba ya wajen ta tafi duniyar tunanin rayuwarta.

Yau wajen kwana uku kenan Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye murnanta ya kasa ɓoyuwa tunda Hamma Lamiɗo ya kira ta ya ce za su zo shi da matarsa da yara ranar al'amis kuma za su ɗan kwana biyu ta kasa sukuni tun jiya ta tura matan su Hamma Abdullahi su Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim suka je gidan shi dake anguwan Jambutu Haske suka gyara suka yi share-share. Sannan yau da safen nan ta ji Ammah na waya da Hamma Abdullahi tana tunasar da shi Hamma Lamiɗo ya ce ya ɗauki motarsa ya kai ta wanki sannan a ɗan duba ta tunda ta yi wattani a ajiye ba a hauta ba, tana can gidan lullube a cikin tamfol.

Alhalin ba Ammah ya bama saƙo ba da kan shi ya kira Hamma Abdullahin ya faɗa masa, shi ma jiya ne kafin su wuce da Baffa yake mata maganar shi ne yau ta kira shi tana sake tunasar da shi har da cewa in ba za su dawo ba ne ya kira Abdularrahaman shi ya je ya ɗau motar ita dai maganarta kar shalelenta ya iso garin nan ba a yi masa abin da yake so ba.

"Da man Kabiru ya faɗa mini zuwan nan da ya yi kwanaki Lamiɗo ya samu sauyin wajen aiki yanzu zai dinga samun hutun sosai tunda ya sauya wajen aiki."
Ammah ta sake faɗa tana daga cikin kitchen.

Ummu Salma dai na jin ta amma har a lokacin ba ta yi magana ba, tunani take yi in da ace tana da in da za ta je ta ɓoye ma ganin Hamma Lamiɗo da matarsa za ta je, har sai sun tafi sannan ta dawo, tana jin kunya da nauyin su zo su ganta a haka,  su ga yadda rayuwarta ta dawo baya, yanzu kunyar mutane take ji da Ammah tayi baƙi ko tana falo za ta shige ciki tana jin nauyin haɗa idanuwana da Jama'a ko yayyenta kunyar haɗa idanuwana take yi da su, tana ganin kamar ita ba ta da sa'ar rayuwa ta tafi gidan aure amma ga shi ta dawo musu ba ma ita kaɗai ba tare da nauyin cikin jikinta. Duk da Ammah ta ce ba ta faɗa masa ba amma in ya zo ya gan ta ko bai ta tambaya ba Ammah za ta iya faɗa masa dalilin zamanta a gida tunda shi tambaya ba ɗabi'ansa ba ne ko zai shekara yana ganinta ba zai damu da ya tambayi dalilin zamanta ba.

Ta yi nisa cikin tunanin ta ba ta ma san Ammah ta fito tana yi mata magana ba, sai da ta ji ta taɓa ta sannan ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

"Ammah kina magana ne?

Ta faɗa tana kallonta lokaci daya tana koƙarin shanye hawayen da suka cika mata kwarmin idanuwanta.

"Auta"

Ammah ta kira ta, sai ta sunkunyar da kanta tana jin kamar ta kace da kuka.

"Ba an hana ki shiga zurfin tunani ba, sai yaushe ne za ki saduda ki fahimci duk abin da Ubangiji ya yi daidai ne? Sai yaushe za ki dogara da Allah ki san cewa Habibu ya shuɗe daga rayuwarki Ummu Salma.?
Ammah ta gama faɗa tana tsaye tana kallon Ummu wacce har ta fara tsiyayan hawaye a saman ƙuncinta 

"Wallahi in na ga kina kuka da damuwa kan wannan yaron haushinki na ke ji, bai ma kamata kina yi masa kuka ba, an san da damuwa amma haƙuri ake yi tunda damuwa da kukan ba zai sauya komai ba. To gwara a yi hakurin yafi alheri in kika yi hakuri wata rana za ki ci riban haƙurin ki Auta."

Ummu Salma ta rushe da kukan da take ta riƙewa. Ammah ta duka a gabanta lokaci ɗaya tana dafa kanta.
"Ki yi hakuri Auta kin ji ko?
Sai Ummu ta gyaɗa mata kai amma kukanta ya kasa tsayawa.
"Mu kan mu muna cikin damuwar abin da ya faru, amma yanzu mu damuwarmu taki ce Auta. In ba ki kwantar da hankalin ki ba, muma hankalin mu ba zai kwanta ba. Samun kwanciyar hankalinki shine farincikin mu da mu da yan'uwanki  gabaɗaya, tunda dai ba mu isa mu sauya abin da ya faru ba, to gwara mu taru mu yi haƙuri gabaɗaya mu fauwalla ma Allah duka lamuranmu da sannun komai zai wuce sannan kuma zai yi miki sakayya in sha Allahu "

Duk wannan dogon nasihan da Ammah ke yi mata ba ta ji ba kuka kawai take yi har da gunji.

"Yanzu shike nan Habib ya rabu da ni har abada Ammah?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ammah idanuwanta suna masu zubar da ƙwalla.
"Shike nan Habib ya rabu da ni. Shike nan ya gama da ni Ammah?
Amma ta yi kasaƙe tana kallonta cikin takaicinta. Ba ta son ta yi ta ma yaro magana yana yi mata taurin kai.

"Ammah ina son Habib. Ina son na sake rayuwar aure da shi. Wallahi ina son shi, na kasa mantawa da shi sai na ke ganin kamar tunda ya rabu da ni har abada ba zan sake farinciki ba Ammah."

Ta ƙarishe faɗa tana mai sakin wani marayan kuka mai fitowa da shessheƙa 
Ammah da takaici ya ƙume ta, ture ta ta yi kafin da sauri ta miƙe tana faɗin" Ke kam dai an yi sakara Ummu, wallahi in da kin san yadda na tsani sunan yaron nan da baki yi gangancin ambaton shi a gabana ba. Haba don Allah yaron da ya yi miki wulakanci ya tozarta ki kike ikirarin har yanzu kina so saboda ba ki da zuciya Auta?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana balla mata harara.
Ummu ta danne kukanta sanin halin Ammah yadda ta fusata sai ta iya kai mata duka ma in ba ta yi wasa ba.

"Yaron da tunda ya sake ki bai sake waiwayoki ba, ba ruwan shi da ke ballatana yadda kike rayuwa, cikin dake jikin ki ma bai damu da shi ba ballatana ke, amma saboda wawanci ke kina nan kina kuka kina cewa wai kina son shi, to Allah ya tsine ma wannan son Ummu ba shi da albarka tunda bai tsinana miki komai ba sai tozarci da wulakanci"

Yadda Ammah ta harzuƙa tana ta faɗa ne yasa Ummu tana hawaye ta ce" Ki yi haƙuri Ammah."
"Ke kika sani wannan kuma ruwanki ne, ki yi hakuri ki rumgumi kaddaranki, ki sani yanzu rayuwarki ta sauya ki rika tuna Habibu a matsayin wani darasi ne wanda ya shuɗe daga rayuwarki, sannan ki riƙa tuna ba ke kaɗai ba ce nan da wani lokaci za ki zama uwa. Abu na ƙarshe kuma ki zauna ki yi ta kuka da damuwa kar ki yi farinciki a kan wanda har abada bai san kina yi ba sannan bai damu da rayuwarki ta cigaba ko ta tsaya ba. "

Ammah ta gama faɗa tana barin wajen zuwa kitchen ta bar Ummu na kuka wurjajan lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi haƙuri Ammah."
Ammah na jinta ta yi mata banza takaici duk ya kumeta, tana jin baƙin ciki in ta ga Ummu Salma na kuka saboda wannan yaron mara mutumci, wanda bai san kana yi ba har da cewa wai tana son shi, Allah ya tsine ma wannan soyayyar domin su kansu iyayenta bata amfanesu da komai ba.

Nan Ummu ta bar ma Ammah gyaran wakenta ta shige ɗaki ta kwanta a saman gado ta cigaba da rusan kuka kamar ranta zai fita kowa yaƙi ya fahimceta, kowa ya kasa gane yanayinta.
Ko za ta manta da komai ba yanzu ba,  wataƙila sai an ɗauki wani lokaci su yi mata uziri su gane yanayinta har gobe mafarkin Habib take yi sannan tana begensa ba laifinta ba ne laifin zuciyarta ne da ta kasa tsanar shi har yanzu.

Ranar yini ta yi kuka fuskar duk ta yi ja, idanuwana sun tasa Ammah ba ta sake bi ta kanta ba ko abincin da ta shigo mata da shi cewa ta yi in ta gama dama ta tashi ta ci in ba ta ga dama ba ta cigaba da kuka saboda wanda bai san tana yi ba, ba ta sake bi ta kanta ba ballanta ta lallasheta. Ita ce don kanta ta haƙura da kukan ta sauko ta ci abinci jin cikinta na ta murɗawa, su Baffa ba su dawo a ranar ba sai washegari da rana, Ammah kuma ba ta sake mata magana ba, tun bayan gaisuwan safe, itama sai ta kama kanta ta daina kuka amma a ƙasan zuciyanta dankare take da damuwa.
Da ta je gaishe da Baffa idanuwanta ya kalla kawai ya fahimci ta yi kuka.
"Auta har yanzu dai ba ki daina koke-koken nan ba?
Sai ta kasa yi masa musu, tunda gaskiya ya faɗa shuru ta yi kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabin jikinta 

"Har yaushe ne za ki kai kina wannan kukan Auta? Kuka fa ba zai yi miki magani ba sannan ba zai taɓa dawo miki da abin da kika rasa ba. Hakuri da tawakwalli shi ne mafita ki samar ma da kanki lafiya ki bar zuciyarki ta huta sai gangar jiki ta amshi canjin ki Auta. Juna biyu kike da shi halin da kike ciki zai iya shafar abin da ke cikin ki, in hakan ta faru kuma kema kina cikin matsala, faruwan haka kuma daidai yake da muma kin saka mu cikin damuwa Auta"

Tunda Baffa ya fara magana ta fara hawaye.
"Ki yi hakuri Auta ki yi tawakalli. Ubangiji yana sane dake, shi ya haɗa ki da Habibu a karon farko, kuma da saninsa ya raba ku, in kina yin haka sai ki yi masa bultulci, ki sani in kika yi hakuri Ubangiji mai rahama ne mai jinƙai, watakila ya yi ma rayuwarki wani kyakyawan canji anan gaba. Canjin da zai goge miki dukkan wani bakin cikin da kika taɓa shiga a rayuwarki."

"Ka yi hakuri Baffa."

Ta faɗa cikin kuka tana toshe bakinta da hijabin hannunta.

"Ka yi hakuri Baffa, in sha Allahu na daina."

Ta sake faɗa cikin kuka.
Baffa ya ji daɗi ya jinjina kai kafin ya ce" Allah ya sa Auta. Ina fatan Ubangiji ya sake sauƙaƙa miki."
Ta amsa da Amin a hankali tana mai sharan ƙwalla ta jima a ɗakinsa yana ta yi mata nasihan kafin ta koma ɗakin Ammah.

 Ammah ko sai da Ummu  ta bar ɗakin Baffan sannan ta shiga tana faɗan cewa Ummu Salma ba ta bukatar lallashi, in ba ta bayan gida aka fito mata ba haka za ta zauna tana neman kashe kanta saboda wanda bai san tana yi ba.

"Jamila."

Baffa ya kira sunanta, ta kalle shi amma ba ta yi magana ba.

"Ki yi haƙuri da Auta, don Allah ki yi haƙuri da ita domin a halin da take ciki tana bukatar lallashi da ban baki ba faɗa ba."
Ammah ta yi shuru ba ta yi magana ba.

"Na san kina ƙoƙari amma don Allah ki ƙara kin ji ko?
Ya sake faɗa yana riƙo hannunta guda ɗaya.
"Ba ki ce komai ba.'
Ammah ta yi jim kafin ta ce" Baffa cewa fa take yi wai har yanzu tana son yaron nan wai kuma tunda ya rabu da ita ba za ta sake yin farinciki ba,"
Ammah ta faɗa cikin takaici in ta tuna maganar sai ta ji zuciyanta na zafi.

"To ai wannan sai a hankali Ammah, a sannu sannu duk za ta manta da komai. Ke dai kawai ki ɗan bata lokaci."
Ammah ta ɗan ɓata rai kafin ta ce" To Baffa wani irin so kuma! Kalli fa wulaƙanci da tozarcin da ya yi mata amma ita har yanzu  son shi take yi?

Baffa ya yi mirmishi kafin ya jinjina hannunta a cikin na shi yana fadin" Ina ruwan zuciya Ammah, ba laifin Auta ba ne bata da alhakin sarrafa zuciyarta. Amma lokaci ne wallahi tallahi za ta manta da komai, watakila sai dai in ta kalli abin da ke cikinta bayan ya fito duniya ta iya tuna da shi"
Ammah ta yi shuru tana kallon shi sai ya gyaɗa mata kai kafin ya cigaba da faɗin" Na baki tabbacin haka, ki dai kawai ki ɗan kara mata lokaci."

Sai Ammah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Shike nan Baffa Allah ya ba ta dangana."
Ya amsa da Amin yana faɗin" Ko ke fa matar Baffa"
Ammah ta yi mirmishi ba tare da ta yi magana ba.
Fita ta yi zuwa kitchen ta shako wani ƙaramin faranti da kulolin abinci sai ruwa da kofi ta kai ma Baffa yana ci suna ɗan taba hira kaɗan kaɗan ita kuma tana gefen shi tana yi masa fitita da mafici tunda ba wuta sun ɗauke.

"Baffa gobe fa su Lamiɗo na hanya."

Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce" Na ji Abdullahi na maganar shi zai je fillin jirgi ma ya taho da su."
Ammah ta washe baki tana faɗin" Haka ya ce mini, Baffa Lamiɗo fa ya fi wata biyar rabon shi da garin nan"
"Zai yi gaskiya."
Ya faɗa yana kai cokali bakin shi cike da shinkafa da wake jallop.
Ammah ta cigaba da faɗa masa ta kira Ummin ikki ta faɗa mata gobe za ta zo ta taya ta girkin da za ta yi musu na tarba.

"To ke ki bari surukan ki su zo su yi girkin mana."
Da sauri Ammah ta ce" A'a Lamiɗo ya ce na yi masa tuwon shinkafa miyar zogale. Kuma kasan in bani na yi girki ba yana ganewa."
Baffa ya kalleta kawai ya yi ɗan mirmishi.

"To uwar Lamiɗo."

Ammah ta kwashe da dariya Baffa na kallonta yana jin sanyi a ran shi, gabaɗaya ta faɗa damuwar halin da Ummu ke ciki na ta sukanta a ciki, shi ya sa ta yi ta rama a tsaye amma yau saboda zuwan Lamiɗo ta saki har yana ganin dariyanta kuma farincikinta ya kasa ɓoyuwa shi kan shi ya tabbata Ammah renon ɗa na cikinta ta yi ma Lamiɗo shi ya sa take jin sa fiye da ƴaƴan cikinta.

Shi dai har ya gama cin abincin Ammah na yi masa hira kan zuwan Lamiɗo yana jinta kawai yana mirmishi.
Suna cikin ɗakin ne ma Baɗɗo ta zo gidan, har ɗakin Baffa ta shiga suka gaisa ta ce daga makaranta take ta biyo.

"Sannu Baɗdo, Ammah  ba ta abinci ta ci.".
Baffa ya faɗa yana kallon Ammah.
"Ta je Kitchen ta ɗiba mana"
Baɗɗo ta amsa da bari ta yi salla tunda tana makaranta aka yi la'asar kuma tana sauri ba ta tsaya ta yi acan ba.
Ɗakin Ammah ta shiga Ummu na kurya cikin ɗakinta kwance tana tunani ba ta ma ji shigowar Baɗɗo ba sai da ta ji ta faɗo saman gadon sannan hankalinta ya dawo kanta.

"Kina kwance kullum kullum dai Sisna?
Ta faɗa tana mai kallon Ummu Salma da ta ɗan tashi zaune tana kallon ta.

"Daga makaranta kike?
Ta tambaya, daidai Baɗɗo na sauke jakar hannunta lokaci daya da yaye mayafin jikinta.

"E na ce bari na ɗan leko ki kwana biyu? Ya jikin! Ina fatan dai ba wata matsala,?

"Babu."

Ta faɗa a sanyaye.

"Kin tabbata?

"Allah bana jin komai, sai yar kasala ne da ɗan ciwon kai."

"To magungunanki sun ƙare ne?
Sai ta ɗan jinjina kai kafin ta ce" Bai wuce in na sha yau da gobe ba."
"Yakamata mu koma asibiti "
Baɗɗo ta faɗa tana kallon cikin jikin Ummu.

"Cikin fa har ya ɗan turo"
Ummu ta bi cikinta da kallo saboda riga da sikat ta saka shi ya sa sai cikin ya ɗan turo 
Shuru kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba 
"Kila fa in muka koma su ce ki fara zuwa awo".
Ummu ta kalli Baɗɗo na wani lokaci nan ma ba ta yi magana ba.

"Me ya faru?

"Sai na haihu har abin da na haifa ya girma bai san uban shi ko ba ta san uban ta ba?

Ta tambaya idanuwanta na cikowa da ƙwallah.
Baɗɗo ta ce" To wa ya ce ba zai san uban shi ba? Za a faɗa masa komai har labarin tun yana ciki uban ya ce ba ya bukatarsa."

Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa.
"Bari na yo alwala'
Tana gama faɗin haka ta shige tiolet domin ba ta san ma ta tsaya Ummu Salma na damunta da mganganu kan Habib wallahi ta tsane shi ta tsani ma jin sunan shi
Fatan ta yadda ta tsane shi itama Ummu ta tsank Habib amma ina, ita har gobe tana begensa tana ganin zai iya neman ta, ta manta da cewa ya ce ya riga ya gama amfana da ita.

 Alwala ta ɗauro ta zo ta yi salla bayan ta idar ta fita ta je ta ɗibo abinci ta zo  ta hau gadon tana ci suna ɗan taɓa hira da Ummu, ko da ta kawo mata maganar Habib Baɗdo za ta ɓata rai ta kauce da hirar.

"Har yanzu Habib bai kira ki ba?
Ummu ta tambayeta tana kallon ta.
"Ni bai kirani ba, tunda ya sake ki na goge lambar shi a cikin wayata."
Ta ba ta amsa tana mai cigaba da cin abincinta.

"Me ya sa kika yi saurin gogewa? Da kin kira shi, kin tambaye shi me ya sa ya yi mini haka?
Baɗɗo ta kasa haɗiye abincin da ta saka a bakinta tana kallon Ummu da mamaki.
Ganin har ta fara hawaye.

"Baɗɗo na kasa mantawa da Habib. Wallahi a mafarkina da farke na duk tunaninsa ne."

Ta karishe faɗa cikin kuka.

"Kowa laifina yake gani, ba laifina ba ne, zuciyata ne har yau tana son Habib na kasa jin na tsane shi. Nima ina so na tsane shi, amma na kasa ya zan yi? Na rasa yadda zan yi da rayuwata."
Ta ƙarishe faɗa tana mai fashewa da kuka 
Baɗɗo ta yi shuru ta ma kasa mgana, maganganunta sun ƙare duk wani kalami na lallashi ta gama zayyana ma Ummu amma har yau ba ta gane annabi ya faƙu ba.

"Ni ba ni da abin da zan kira Habib na faɗa masa. Domin duk wani abun da za mu sani ya sanar damu. Ummu ki saka a ranki ko da ganganci Habib ya kira ni sai ya yi nadama wallahi, domin ba zan raga mishi ba. Tunda shi batulu ne kuma mayaudari, sannan maganar kina son shi, ko kin kasa tsanar shi duk bai ta so ba, ki yi ma kanki faɗa Ummu cewa fa ya yi bai taɓa son ki ba, don jikin ki ya aure ki. Kuma ya gama amfana da ke shi ya sa ya sake ki, da cikin shi amma bai damu ba, to ke ki yi tunani da hankalinki wanna mutumin da ya gama yi miki haka ne zai dawo gare ki? To ko ma ya dawo da sunan mene? Bayan abin da ya haɗa ku ya riga ya kawo karshensa duka. Ko kin manta saki uku Habib ya yi miki ne Ummu Salma?

Ta gama faɗa tana kallonta.
Ummu tana hawaye ta ce" Ban manta ba"
"To gwara ki tuna cewa har abada aure ya haramta tsakaninki da Habib a yanzu. Kuma koma bai haramta ba shi baya sonki ba kuma zai dawo gare ki ba, in ma za ki yi daina tunanin ki cire sa a cikin zuciyarki ki cire shi, in kuma ba za ki iya ba har yanzu kina son shi to ki ba da himma. Amma ina so ki sani ko mutuwa kika yi wallahi tallahi Habib ba zai damu ba domin ba shi da asara."

Baɗɗo ta faɗa tana zare ma Ummu Salma idanuwanta domin yau itama ta kai ta bango.

Ummu ba magana sai kuka, tana faɗin kowa haka yake ce mata ko jiya ma Ammah ta yi mata faɗa yau ma Baffa ya yi mata nasiha.

"To ai duk muna son ki ne, gaskiya ce mai ɗaci muke faɗa miki. Bayan mu masoyan ki, ba wanda ya san zafin ki Ummu Salma."
Ta faɗa tana ɗan sassauta fushinta.
Ummu na kuka take faɗin" Ina so na manta nima ina so manta. Amma na kasa."
Sai gunjin kuka, tausayinta ya kama Baɗɗo dole ta sauke filet ɗin abincin hannunta a saman dirowan gado ta karisa wajen Ummu ta rumgumeta tana lallashinta.
"Ki yi hakuri, ke ce za ki yi ma kanki wannan yaƙin. Ki koma ga Allah ki roƙesa ya cire miki, in sha Allahu zai cire miki."

Ummu ta amsa da cewa wallahi tana yi tana addu'a amma kamar sai kara gaba tunaninta akan Habib yake, ita kuma Baɗɗo na sake ba ta tabbacin kar ta gaji ta cigaba da kai kukanta wajen Allah zai kawo mata ɗauki.
Da lallashi da ban baki Ummu ta yi shuru.
Sannan Baɗɗo ta karishe cin abincin ta ta fita da filet ɗin zuwa kitchen ta haɗa wanke-wanken ta wanke sannan ta share tsarkar gidan Ammah na ta saka mata albarka.

Sai da ta yi mangariba sannan ta yi shirin tafiya.
"Ke wai na ji Ummi na faɗin gobe Hamma Lamiɗo zai zo tare da iyalansa."
Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana gyara zaman jakarta a saman kafadanta.
Suna tsaye a tsakar ɗakin Ummu ta zumbuɗa hijabin da ta yi salla da shi za ta ɗan rakata haraban gida..

"Uhm haka na ji Ammah na faɗa."

Ummu ta faɗa cikin basarwa.
Bata son ya zo, haka kurum ba ta son su samu baki anan kusa, ita dai da Baffa ya sani ya barta ta bi Mami Kaduna da ta fi samun kwanciyar hankali.
Dazu ma da Baɗɗo ta yi mata maganar waya ta ce sun yi waya da Mami ta ce za ta aiko mata da sabuwar waya da layi, wayarta ba za ta iya amfani da ita a yanzu ba.

"Ai Ummi ta ce tun safe tana nan gidan Ammah ta ce ta zo ta taya ta abincin tarban shalelen Ammah.."
Ta faɗa tana yar dariya
Ummu ta kalleta kafin ta ce" Uhm kin san halin Ammah, in ban da ma ɗaukan ma kai, girki ko su Adda Suwaiba ba za su yi musu ba? In su Hamma Jibo ne za su zo ban taɓa ganin ta yi musu girki na musamman ba amma Hamma Lamiɗo duk abin da yake so ita ce za ta yi masa."
Ummu ta karishe faɗa da jin haushin Ammah haka kurum mutum kato da iyalansa amma har yau ba ta daina wahala a kan shi ba 

"Ke ko ɗan gaban goshin Ammah ne, naji ma Ummi na faɗin za su kwana biyu."
Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba tunani take yi in da hali ta guje ma gidanan har sai sun tafi, duk da ba dariya za su yi ma kaddaranta ba, ita kawai tana kunyar ya zo ya ganta a gida kawai a ce mijinta ne ya sake ta sai abin ya yi mata wani iri.

Bayan Baɗɗo ta yi ma su Baffa sallama Ummu ta tafi rakata har haraban gidan, suna tafe Baɗɗo na tambayan ko Shamsiya ta zo? Ummu ta ce ta zo kwanaki ta ma ce za ta dawo amma ba ta dawo ba.

"To watakila ta koma makaranta ne"
Baɗɗo ta faɗa Ummu ta yi shuru kafin ta ce" An ya! Ko dai ta ji haushin mganganun da Ammah ta faɗa mata ne"
"Me kuma ya faru?
Baɗɗo ta faɗa tana zare idanuwaanta.
Nan Ummu ta kwashe komai ta faɗa mata.
"Kin san halin Amman taki, ba ta da haƙuri ta yi ta masifa."
Ta karishe faɗa tana kallonta.

"To ai ban ga laifin Ammah ba, itama dai Bestie ba ta yi nagana mai kyau ba duk wannan abin da Habib ya yi miki sai ta ce laifin ki ne?  Haba ko Habib ta sani ba ke ba ai ta faɗi gaskiya ballanta ta sanadinki ta san Habib ɗin, ai wallahi Ammah ta yi mini daidai ko ni ce a wajen haka zan yi mata."

Ummu ta kalleta kafin ta ce" Ku yi ma Bestie uziri kin san yanayinta da gidan su."
Baɗɗo ta taɓe baki kafin ta ce" Haba koma dai mene ai ke tata ce, in ba ta tausaya miki ta ba ki baki kan abin da ya same ki ba, bai kamata ta zauna a fuskarki tana cewa ke ce da laifi ba, kuma har tana fadin cewa ba za ki samu kamar Habib ba ni wallahi kalamanta ma sun saka ta l zube mini a idanuwana Habib ɗin banza? Wallahi sai kin samu wanda ya fi shi kuma ta jira ta sha kallo."

Ummu dai ba ta kara magana ba ganin Baɗɗo ta ɗau zafi ta samu suka yi sallama ta tafi, ita kuma ta dawo cikin gida. Itama fa kalaman Shamsiyar sun ba ta mamaki ita ce ta farko da ta fara cewa Habib ba shi da laifi. Sannan ta yi mamakin rashin dawowarta sannan ko a waya ba ta kirata ba, ai tana da lambar Ammah.
amma ba ta kawo komai a ranta ba, Ammah na ɗakin Baffa ta ɗau wayarta ta kira ta har sau biyu ba ta ɗauka ba, sai daga baya ta kirata tana ce mata ba ta gida ne da yake ta koma makaranta.
Sun ɗan jima suna hira Shamsiya ta bata hakuri kan cewa komawarta makaranta ne ya zo a gaggauce shi ya sa ba ta dawo ba. Amma kafin su yi sallama sai da ta yi ma Ummu tambaya.

"Yanzu Bestie haka za ki yi renon cikin nan ki haife shi a ƙasƙantan ce! Alhalin uban cikin ya ce ba ya so?

"In shi ba ya so ai ni ina so. Kuma da ikon Allah zan haifi abin da ke cikina da goyon bayan iyayena da dangina"
Ummu ta bata amsa muryanta a raunane domin kuka na shirin ƙwace mata..

"Tabɗijam. To Allah ya kyauta."

Ta faɗa cikin ganin karfin halin su tunda wanda ya yi cikin nan ya ce ba ya so to me kuma za a jira da shi? Kafin su yi sallama ma wayar ta katse kamar katin ta ne ya kare. Ranar kamar an yi ma Ummu Salma fami kan damuwarta ta kusa raba dare tana koke-koke ballanta da Ammah ba a wajenta ta kwana ba, ganin ta yi kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta je ta ɗauro alwala ta fara salla daga zaune domin jiri take gani  addu'a take yi Allah ya cire mata soyayyar Habib a cikin zuciyanta ko za ta samu salama.

Ba ta samu barci ba sai da ta yi sallar asuba shima ba daɗewa ta tashi da ciwon kai da jiri, tana kuma karyawa sai amai kamar za ta yi amayar da hanjin cikinta, sannan da ta shiga tiolet sai ta ga jini a ruɗe ta fito ta faɗa ma Ummin ikki da ta zo gidan tarban su Hamma Lamiɗo. Baffa baya nan ya shiga cikin gari tare da Abdullahi can harkokinsu.
Sai kawai Ammah ta ce Ummin ikki ta raka Ummu zuwa asibiti, tare suka tafi har da Adda Suwaiba da tun safe suna gidan.

****

Ƙarfe biyu saura na rana Hamma Abdullahi ya je filin sauka da tashin jirage na YOLA INTERNATIONAL AIRPORT JIMETA. da kuma motar Hamma Lamiɗo wata hilux ƙiran Toyota da alamu dai Hamma Lamiɗo na son mu'amala da motocin kamfanin Toyota.

Lokacin da suka iso gidan su Ummu ba su  daɗe da dawowa daga asibiti ba, cikinta ya shiga wattani huɗu amma likita ya ce ya yi rauni ta riƙa samin hutu sannan jininta ya yi sama again, ba kuma ta samun isasshen barci. Amma dai ya rubuta magunguna sannan ya ce nan da sati uku za ta fara zuwa awo, suna son ta samu hutu sosai sannan ta riƙa cin abubuwan da za su gina mata jiki, amai kuma da kasala laulayi ne za ta bari in cikin ta ya yi girma watakila ma sai ta haihu ya danganta da yanayin ta.

Ummu Salma na kwance a cikin ɗakinta lamo akan gado tana sauke ajiyar zuciya tana ji daga falon Ammah ana ta yi ma baƙi maraba. Har da Adda Ummu Sulaim, duk tare suka taimaka aka gyara gidan girki dai Ammah ta yi a cewarta Lamiɗo na ganewa in ba ita ta yi mishi abinci ba.

Ga muroyoyin su nan har na Ammah amma ko tarin Hamma Lamiɗo ba ta juyo ba, kuma yana falon tunda ga Ammah can na ta masa maraba kamar ta goyasa.
Da ga cikin ɗakin dai ta ji na matarsa cikin yauki da yanga kamar yadda ta saba tana gaishe da Ammah da su Ummin ikki.

Barci ne ya kwashe ta daga nan ba ta farka ba sai wajen biyar saura shima ɗin ta tashi ne don kanta, Adda Suwaiba ta gani a ɗakin tana zaune tana ba ma ƙaramar yarinyar ta Mimi mama.

"Adda an yi salla ne?
"Tun ɗazu. Biyar ma ta kusa."
Ta bata amsa.
Sai ta miƙe da sauri tana faɗin.
"Shi ne ba wanda ya tashe ni?

"Ummi ta ce a kyale ki likita ya ce ki huta sosai."
Ba ta sake magana ba ta shiga tiolet ta yo alwala ta zo ta yi salla. An riga an shigo mata da abincinta ta ja ta zuba tuwo ɗaya a filet ta fara ci, miyar ma daɗinta na musamman ne saboda zuwan Hamma Lamiɗo.
Tana jiyo muryan Hamma Abdullahi da na Hamma Abdulrrahman, har da na Ammah da Baffa amma ba ta jiyo na Hamma Lamiɗo ba.
Sai ta yi tunanin ko har sun karisa gidan na su ne?

"Adda su Hamma Lamiɗo sun tafi gidan su ne?

"Aa ba su tafi ba, ga shi can shi a falo suna hira da su Baban Mimi a falo, har da Baffa ma."

Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba.

"Balkisun kuma tana ɗakin Ammah tare da hadiman ta da suka zo tare."
Ummu ta ɗan gyaɗa kai, da man in dai za ta zo, tana tare da hadimanta.

Nan Adda Suwaiba ta fita ta barta bayan ta gama cin abinci tana son shan ruwa amma ba za ta iya fita falo ba tana jin kunya.
Sai kawai ta yi zaman ta.
Har fa mangariba duka suna gidan ba su tafi ba. Ummin ikki ce kawai ta tafi gida.
Bayan mazan duk sun fita sallan magariba itama ta idar kenan Ammah ta leƙo ta ganta saman darduma tana lazimi.

"Ke kam ba ki ji zuwan yayanki tun ɗazu ba ne? Ko da yake kina ta barci."

Kafin Ummu ta yi magana Ammah ta riga ta da cewa.
"To taso ki gaishe da matar yayan naki, kafin su dawo daga masallaci."
Ba ta isa ta zille ba domin Ammah ba a yi mata wasa.
Dole ta miƙe ta bi bayanta zuwa ɗakin Ammah in da ta iske Balkisu da ya'yanta tare da Sabuwa da Anitha
Da ta gaisheta ta amsa tana kallonta.

"Ba ki da lafiya ne?
Ta faɗa cikin yanayin maganarta.
Ta kasa mgana, domin ba ta san me za ta ce ba.
"Uhm ba ta da lafiya ai tana ma gida ne sun rabu da mijin"
Balkisu ta yi salati cikin yanayinta ta ce. "Subhanallahi."
Nan fa Ammah ta gyara zama ta shiga ba ta labarin abin da ya faru.

Ummu ta kasa zama ganin har Sabuwa na yi mata wani kallo, Anitha ma ta kafe ta da kallo kamar ta san me ake faɗa. Sai kawai ta tashi za ta fita Beena ta biyo ta a baya  tana magana ba ma ta jin me take faɗa, ba shaƙuwa da yaran ta yi ba ko a baya suka zo gidan ba ta ta kan su.

Tana fitowa daidai su Hamma Abdulrahaman suna shigowa falon Ammah.
Sun riga sun ganta ba ta da yadda za ta yi, ga Beena ta rike mata gefen hijabi tana fadin egg za ta ci.
Kanta na ƙasa ta ma kasa ɗagowa tsabar kunya da nauyi.

"Ummu kin ta shi? Na leƙo ɗazu aka ce kina barci. Sannu ya jikin?
Hamma Abdullahi ya faɗa
"Ba ta da lafiya ne?
Hamma Abdulrrahaman ya faɗa yana kallon ta.

"E sai da suka je asibiti da Ummin ikki."

"Allah ya sauwake. Sannu "
Shima ya faɗa yana kallonta.
"Papa."
Beena ta faɗa ganin babanta sai kuma ta saki Ummu ta nufe sa ta faɗa jikinsa.
Kamar tsautsayi Ummu ta ɗago kanta karaf sai a idanuwan Hamma Lamiɗo da yake zaune saman kujeran zaman mutum biyu da ke falon Ammah.




*Janafty*