19
by @rufaidaumar
ALWASHI
44
Sallamar Hajja ce ta katse hirar Mami da Mardiyya wacce tun Azahar ta shigo gidan. Mami sai da ta ji faɗuwar gaba ganin Hajja Zayha na murmushin nan nata, sai dai ta ba wani labarin murmushin nan na Hajja Zayha, idan har ta yi shi gareta, to fa ta shirya wata ƙetar.
"Ina wuni Hajja." Faɗin Mardiyya fuskarta ba yabo ba fallasa, Hajja ta amsa har lokacin da murmushi saman fuskarta. Ba ta ko zauna ba, ba kuma za ta iya tuna ƙarshen ranar da ta sa mazaunanta a saman kujerun Salma ba da sunan zama.
"Kuma sai Allah ya gwada mana ikonsa a kan Areef ko? Ko labarin bai risƙe ku ba?"
Mami da Mardiyya suka ɗan dubi juna kafin Mardiyya ta yi magana don ita Mami ji ta yi ma harshenta ya yi nauyi.
"Meyafaru Hajja?"
Idanunta a kan Mami ta yi ƴar dariya.
"Alhamdulillah, dayake ya haɗu da dangin da suka san mutunci da darajar DAN ADAM, kun ga dai ana zuwa madadin sha'anin ya tsaya a saka rana, an damƙa masa Laila halak malak. Abin nufi, Laila ta zama uwargida ran gida a gidan Areef. Aure ya ɗauru."
Mami ranta ya yi mugun ɓaci, har wani zafi take ji ƙirjinta na mata.
"Wai Hajja kina nufin an ɗaura aure daga zuwa tambaya?"
Mardiyya ce dai ta ƙara magana domin Mami ba baki sai kunni.
"An ɗaura Anti Diyya. Areef ya zama Angon Laila, yanzu saura Kausar. Itama zamu ga nasu karamcin. Ko a yi yanzu, ko kuma sai an ɗau lokaci. Allah dai ya sanya alheri, ya zaunar lafiya. Bari na je don zama ni bai gan ni ba."
Daga haka ta juya bayan ta sakarwa Mami murmushi karo na biyu kuma mai ma'ana ta musamman.
Mami ta dafe kanta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mardiyya kodai matar nan sharrinta ne? Ina wayata? Yanzu haka Dakta zai min? Haka muka yi da Sada?"
Mardiyya ta miƙawa Mami wayar jiki a sanyaye.
"Yanzu toh me za ki cewa su Dada? An riga an ce musu ai Kausar zai fara aura."
Mami ta ja tsaki ranta a ɓace. Abba ta dannawa kira, koda ya ɗaga daƙyar ta amsa sallamar da ya yi ta gangara kan abinda take son tabbatarwa kanta.
"Dagaske an ɗaura aure?"
Shi ne kawai abin da ta ce, ya yi murmushi da sautin ya ratsa kunnuwanta.
"An ɗaura Salma, haka Allah ya ƙaddara. Sai ki sanar da can gida domin a sani ko? In sha Allahu gobe dai za'a ƙarasa Adamawar."
Ta furzar da huci gami da runtse idanu.
"Amma haka muka yi fisabilillahi?"
"Salma, ba maganar yanda muka yi ba ne, magana ce ta yanda Allah ya yi tsarinsa. Don haka please ba na son jin wani ƙorafi. Ni ban ga mene ne bambancin Uwargidan da Amarya ba. Duka dai matansa ne ko?"
Mami ta yi shiru, jin dariyar Hajja ta cikin wayar ya sa ta kawai ta katse kiran. Hawaye suka zubo mata don baƙin cikin hakan, don cin fuska wai Sada zai dinga amsa wayarta gaban matar da ba ta ƙaunarta har a kai ga ta tsinci abin dariya cikin zantukansu?
"Mami please, kar ki bari wannan abu ya ɓata maki mood. Akan abin da ba hannunmu yake ba ki ke hawaye? Mami bikin fa ɗanki ne za'a yi, your only son fa."
Tsaki Mami ta ja, a fusace ta ce.
"My only son a gidan uban wa? Ai ba shi kaɗai na haifa ba. Ko ɗa namiji ne kaɗai ɗa?"
"Allah ya huci zuciyarki Maminmu." Mardiyya ta furta tana murmushi. Duk don ta ɗan sanyaya ran Mamin. Nan dai ta dinga kwantar mata da hankali. Sai bayan sallar Magrib ta bar gidan kasancewar tana da night shift a asibiti.
Koda ta fito parking space tana shirin ƙoƙarin buɗe motarta ta hango Areef ya shigo gidan, ga dukkan alamu tunda ya fita masallaci sai lokacin ya shigo. Ya yi wanka ya sauya kayan zuwa jallabiya marar nauyi ruwan ƙasa.
Ganinta ya ƙaraso yana murmushi itama ta maida mishi martani.
"Our Groom."
Yana murmushin jingina bayansa a jikin motarta.
"Our Nurse. Barka da dare. Har za ki wuce?"
Ta gyaɗa kai.
"Na jima ai tun azahar ina gidan nan. Na ɗauka ka fita ma ko da Fareed, saboda na ga motarka a ajiye."
Ya shafi sumar kansa.
"No, ban je ko'ina ba."
Ya dubi ɓangaren Mami sannan ya maido idanunsa ga Diyya fuskarsa a ɗan marairaice. Ta yi dariya.
"Ta huce. Ta kuma san ba wai laifinka ba ne. Kawai ba haka ranta ya so ba. Idan ka je kar ka ɗauko mata zancen muddin ba ita ta maka ba. Ka dai san halin abinmu."
Suka yi dariyar a tare.
"Allah ya sanya alheri, ya ba ka ikon riƙe amanarsu duka. Bari na wuce ina latti."
Ya buɗe mata ƙofar ta shiga ya rufe.
"A gaida min su Zayyad." m
Ta amsa gami da tayar da motar. Shi kuma ya nufi ɓangaren Mamin don ya sani tabbas ƙin yin hakan ma kan iya zama laifi.
***
KANO
Laila ba ta samu kanta ba sai Magriba domin can ɗakin Gwaggo Samha aka tare. Ƴan Maiduguri sai videocall ake ana taya juna murna. Mama ce kawai Laila ba su yi magana da ita ba, ita ce kuma wayar da ta fi fargaba don ta sani, zuwan bikinta daidai yake da dawowar Mama Nigeria. Ta sha faɗi cewa in sha Allah koda ba a sallame ta ba, za ta nemi sallama matuƙar bikin Lailan ya zo wanda shi ne kaɗai burinta a yanzu.
Ta zauna nan saman darduma bayan ta kammala addu'o'inta. Haseenah na can babban falo tana duba hotunan laces da ma atamfa, ta dage lallai ita za ta fidda ankon ƙawaye don a cewarta ai yanzu ne daidai lokacin fitarwa.
Kamar kuwa jira ake ta keɓe din, sai ga shigowar waya, gabanta ya faɗi ganin tabbas Mama ce. Shikenan, sai kuma da ta yi tunanin ba lallai Mama ta san wasu abubuwa masu yawa ba har zuwa yanzu balle ta zargi ko ta riga ta ji ma cikakken sunan Areef din ɗan Sada Bilyaminu. Ta ji ta ɗan samu nutsuwa ta ɗaga gami da gyaran murya.
"Assalamu alaikum."
Mama ta amsa mata cike da annashuwa da kuma kulawa.
"Waalaikumussalam My Little Baby, koda dai you are no longer a baby tunda kin zama matar aure. How i wish ina nan aka ɗaura."
"Mama mana." Ta furta a shagwaɓe kawai sai ta soma kuka, Mama ta yi shiru ba ta ce uffan ba, ita kuwa kuka take sosai har da sheshsheƙa.
'Auren nan dai da Mama ke so ta ga mun yi, in sha Allahu tare za'a yi mana. Yanda take kokarin saka mu farin ciki, in sha Allah haka zamu sanya ta itama. Wayaga mun samo mata surukai twins mu ma?'
Ba ta mance kallon hararar da ta aikawa Sameerah ba, har sai da Sameerah ta dara.
'Oh, mu shikenan kuma gadon ƴan biyu zamu yi ta yi ko? To ki saka a ranki ma mijin da zan aura koda ace zan yi auren ne ma, sai ya ninka naki kyau yarinya.'
Kamar yanzu ne suke tafe a hanyarsu ta dawowa gida daga boko, kamar yanzun ne suka yi wannan tattaunawar. Fuskar Sameerah ta dawo mata a idanu kamar a lokacin take mata dariyar tana ƙara rungume jakar litattafanta. Yau sai ga shi ba ta auri kowa ba sai wanda ya gurɓata rayuwar ƴar uwar baki ɗaya.
"Ya isa, ya isa hakanan."
Muryar Mama ta maido ta hayyacinta, ita ma bisa dukkan alamu dakiya ce kawai irin ta Uwa.
"Mene ne na kukan? Rashin godiyar Allah ko me? Kina zaton duk sadda tunanin ƴar uwarki ya faɗomaki a rai kuka shi ne abin da ta fi buƙata a wurinki madadin addu'a? To kar na ƙara jin kina wannan kukan. Abin alfahari ne gareta da ace yau tana tare da mu, ta ga wannan ranar da kika shiga sahun masu aure. Allah ya yi maki albarka Laila, ya albarkaci aurenki. Allah ya sa gidan mijinki ya zame maki wani dausayi na aljannar duniya da zai sadar da ke da na lahira."
Laila ta kasa cewa amin, ta dai maye gurbin addu'ar Mama da nata son zuciyar na Allah ya ba ta ikon cimma mafarkinta.
Basu jima suna waya ba suka yi sallama. Nan ta yi wa Zakiyya gajeran rubutun saƙon an ɗaura aure ta tura mata, haka Na'eem shima. Ta kashe wayar baki ɗaya don ba ta buƙatar doguwar hira a ranar. Kanta ciwo yake sosai.
***
KATSINA
Kallo ɗaya ta yi masa ta kauda kai tana amsawa Anti Amarya gaisuwar da take mata. Benazir da Afrah suka gaida shi, ya amsa. Ganin Haj Nafisa ya gaishe ta. Ta faɗaɗa fara'arta.
"Lafiya lau Angon biyu. Daga zuwa kuma an yi wuff da kai? To Allah ya sanya alkhairi, ya sa alherin aka ƙulla. Saura Kausar itama Allah yasa hakan za'a bamu kayarmu. Ka ga sai batun shan biki kawai."
Ta yi dariya su Benazir na taya ta kafin su yi ɗif ganin kallon da Mami ta watso musu a sace. Shi ko murmushi ya yi kawai. Daga haka ta fice zuwa sashinta suka bi ta da sai da safe.
"Barka da dare Mami."
"Barka dai." Ta amsa ba tare da ta kalle shi ba. Duban Benazir ta yi.
"Kin ɗumamin miyar nan?"
Da sauri ta miƙe.
"Wallahi na manta, bari na yi."
"Ai dole ki manta tunda auren uwarki aka ƙara ɗaurawa ko? Kema tashi ki bar nan tun ban ɓallaki ba."
Benazir dai jiki na rawa ta yi hanyar kicin. Afrah ma ta ɗauki wayarta ta yi ɗakinsu. Areef na kallon Maminsa kawai, ya sani ranta har yanzun a ɓace yake. Don haka ya yi shiru, sanin da ya yi mata idan ma ya yi magana to ƙara hawa za ta yi.
"Kai ka tsarawa Dakta hakan? Saboda ka nuna min zaɓinka shi ne zaɓi, nawa zaɓin da banza duk ɗaya ko?"
Ya ji zancen a tsakiyar kansa, girgiza kai ya yi yana kallonta kafin ya sadda kan.
"Allah shaida Mami ban san ya aka yi hakan ya faru ba. Ni dai iya abinda na sani, tambaya aka je, ban zaci har aure za'a ɗauro ba. Amma don Allah ki yi haƙuri, da ace na san hakan za ta faru, tun wuri da na yiwa Baba Dakta maganar a fara zuwa Adamawa kafin Kanon. Ina girmama zaɓinki Mami, ba zan taɓa wulaƙanta Kausar ba. Ƴar uwata ce fa ko babu aure tsakani, ki taya ni addu'a kan Allah ya ba ni ikon adalci da sauke nauyin da ya ɗora min a kai. Ni ban ga wani bambancin uwargida ko amarya ba, duka fa igiyoyin aure ne."
Ta ɗan harareshi. Ya shafi ƙeya yana murmushi.
"Sorry."
Ta nisa kafin ta hau kiran Benazir. Sai ga ta ta fito.
"Ki zubowa Hammanku abinci."
Bai yi musu ba don yunwar yake ji, bai kuma yi mamakin da ta fahimci hakan ba. Duk wacce za ta karance ɗa ai dama a bayan Uwa take.
***
Washegari koda aka je Adamawa, sun karɓi kudi sun kuma ce a jira har sai lokacin bikin nan da wata biyun sai a yi ɗaurin aure. Sun faɗi ne da jin zafin an riga an ɗaura da Laila a farko. Abin sam bai musu daɗi ba. Haka su Baba Dakta suka juyo zuwa Katsina.
Koda suka dawo ma, Baba Dakta a washegari ya tattara tare da matarsa Hidaya don tuni yaransa kaf sun koma Abuja ana kammala bikin babbar sallah saboda ayyukansu.
Shi ma Areef aikinsa kawai ya sanya a gaba, a gefe kuma sa ido kan aikin gidansa wanda a farko zaman mace ɗaya aka yi shi, yanzun ko Abba ya sa ana sauya tsarinsa na mata biyu. Sati guda kenan amma ya kasa kiran Laila, ban da gajeran saƙon da ya aikamata na addu'ar nema musu albarkar aure bai ƙara uffan ba. Ba ta maido amsa ba. Fareed ne yace lallai ya kamata ya kai ziyara Kano don jin irin tsarinta, kuma ko ba komai tunda har aka ba shi mata, ya kyautu ace yanzun nauyinta na wuyansa. Idan a baya ba ta karɓar kyautar kuɗaɗe, yanzun don ya kashe mata ba laifi ba ne.
"Ok." Ita ce amsar da ya ba Fareed wanda ya sa shi ɗuramasa ashar. Abin ma sai ya ba shi dariya. Can ƙasan ransa faɗi yake da ace Fareed din ya san wace Laila Sameerah toh tabbas ba zai yi mata wani karambani ba. Shi fa bayan da yake ja ba ya son ketare iyakarta ne. Ya ga alamun ganinsa ma ɓacin rai yake ƙaramata. Balle yanzu da igiyar aurensa ya sarƙe ta ta ko'ina. Sai dai ya saka a ransa ranar Lahadi zai shiga Kanon in sha Allahu.
***
KANO
Ranta idan ya yi dubu to fa ya ɓaci, ta kasa cewa Momi Fannah komai kawai ta sadda kai tana jin zafin lamarin. Ba ta taɓa hana ta fita wani wuri ba sai yau fa take son zuwa siyayyar kayan shafarta wai ta kira ta nemi iznin mijinta?
"Au ba za ki kira ba? To nemi wuri ki zauna. Ai daman fitar ya ci an rufe maki ita don sati mai zuwa za'a soma maki gyaran jiki."
Ta juya kawai tana tura baki ta fice zuwa dakinsu, tana ji Haseenah na fadin
"Aikuwa dai Momi." gami da dariyar mugunta.
Ba don tsoron zunubin ba ai da ta koma bayan mintina ta cewa Momin ya yarje mata. Sai kawai ta gwammace ta haƙura da fitar baki ɗaya don haka ta sauke mayafin ta ajiye gami da fidda gown din ta dauko riga da siket marasa nauyi ta saka. Dama tuni Momi ta tsaida lalle, duk wanda ya zo ce masa ake an daina lalle a gidan. Wannan ba ta damu ba saboda ita kanta ta sani ba ta da nutsuwar ma da za ta ƙirƙiri wani style ta yi maka ya yi kyau yanzun.
Wayarta ce ta yi ƙarar shigowar saƙo. Areef ne, bayan kwanaki biyar da daurin aurensu, bayan saƙon da ya aikomata ta share shi.
"Assalamu alaikum, zan shigo Sunday in sha Allah."
Abin da ya rubuta kenan kawai. Ta karanta ta ajiye wayar, tsakin ma ya daina fita sai na zuci kawai. Ba son zuwan take ba, amma ya dace ya zo ɗin saboda mutan gidan.
***
©Rufaida Umar