HADIN KADDARA

Chapter 11

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                    By 

        AyshaNalado



Page  11



Take jikinta ya dauki rawa zuciyarta ta shiga bugawa da karfi, ba tare  da wani zaɓi ba ta shige motar, shi ma mutumin ya shiga ya mayar  da murfin motar ya rufe, da mugun gudu driver ya ja suka bar cikin school ɗin.

A karo na uku ta ja guntun tsaki tare sake duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, kimanin awa daya  kenan ta kwashe tana jiran Salmah amma shiru, tun goma da rabi  take nan gashi  har sha ɗaya ya gota, mayar  da kai ta yi ta jingina da kujeran da take zaune tare da dafe goshin ta da ke matsanancin sara mata. A haka ta  sake kwashe wasu mintuna ashirin ɗin, amma shiru kake ji tamkar  malam ya ci shirwa, miƙewa tayi ta ɗauki jakarta ta rataya jiki a sanyaye ta fito daga wajen, kai tsaye  department ɗin su salmah ta nufa don ganin ko lafiya,  tun kafin ta ƙarasa ta haɗu da Zahra ɗaya daga cikin ƙawayen Salmah, kasancewar sun santa sosai yasa ta tsaya suna gaisawa bayan sun gaisa take tambayar ta Salmah,  Zahra ta ce "wlh nima ita nake nema kinga handout ɗinta nan da ta ce na riƙe mata tana zuwa shiru kusan awa ɗaya  gashi har ana shirin shiga second lecture." "OK nagode bari na dubata wajen Salman ko can ta je." Ta  juya ta tafi tana saƙe saƙe a ranta, shin ina Salmah ta shiga ne?

Ta tamu Salman da Suraj da wasu friends ɗins,  fitowarsu kenan daga lecture an zazzauna ana hutawa, Salman na hangota ya miƙe ya nufota da sauri, dakatawa ta yi ganin ya taho har ya isko ta, Suraj ne daya biyo shi ya fara gaisheta, amsawa ta yi, tare da ce wa "Salmah na zo nema ko tazo nan."  "Bata zo nan ba gaskiya don yanzu Suraj ke damuna ma wai mu je wajen ku, ina ce ma kuna tare ai." Cewar Salman,  "A'a bamu tare wlh." Ta faɗa cikin damuwa tare da ɗan fara waige waige, a zuciyarta tana cewa Salmah ina kika shige ne?

Ganin yanayin data shiga yasa   har suna haɗa baki wurin tambayarta ko lafiya me ke faruwa, girgiza kai tayi ta ce "ba komai abu zan ƙarba a wajenta, tunda bata nan, sai anjimanku." Daga faɗin haka ta juya da sauri ta wuce.

Duk  inda tasan zata samu Salmah ta je, ba ta nan itace har hostel don tasan ta da yawan ƙawaye wata ƙila wata cikin su ta ja ta, wasa wasa ana neman kwashe awa biyu babu Salmah gashi har ƴan class ɗinsu sun kuma shiga lecture,  ita ma ga nata lokacin shiga  second lecture ɗin saura 20 minutes jiki a sanyaye ta juya ta kama hanyar department ɗinta zuciyarta babu daɗi sai saƙe saƙe ta ke yi kala kala ga tunanin Ahmad daya addabi zuciyarta motsi kaɗan ya faɗo mata a rai ga kuma tashin hankalin  rashin ganin Salmah da yake neman dagula mata lissafi.

Daga bayanta ta ji an ce "A'ishatu Muhammad Lawal." Jin muryar Salmah yasa ta saurin juyowa, zaro ido ta yi ganin yadda idanunta suka yi jajur alamar ta yi kuka ta gaji, da sauri Aysha ta ƙarasa gareta a ruɗe take ce wa "ina kika shiga daga ina kike me ya same ki kike kuka?" Girgiza kai ta yi ta ce "babu komai Aysha." Ta kama hannunta ta fara janta ba tare da ta bata gamsasshen amsa akan tambayar da ta mata ba, a dan harzuƙe tace "ina tambayar ki baki bani amsa ba, nace me ya same ki daga ina kike na zageya faɗin school ɗin nan ban ganki ba yanzu kuma ga ki na ganki ki na kuka."


 Bata saurareta ba sai da ta kaita bakin wani matakala suka zauna, kallon fuskarta ta yi, sai kuma ta yi saurin kawar da kai, tare da sauke ajiyar zuciya zuciyarta na mata wasi wasi akan abinda take shirin aikatawa, sai kuma ta tuna girman alkawari, a sanyaye ta ce "Na gaya miki babu abin da ke damuna kin san dai bazan boye miki komai ba ko, kaina ke dan mini ciwo shine naje clinic aka haɗa mini magunguna, to ciki harda allura kin san ni kuma bana son allura ko? To shine ya saka ni kuka." Sauke ajiyar zuciya Eshart tayi ta san Salmah ba ta mata ƙarya kuma ba ta boye mata komai na ta, bugu da ƙari tafi kowa sanin ƴar tsaman dake tsakanin salmah da allura,  bata ƙaunar allura ko misƙala zarrati, don haka  ba tare da wani dogon nazari ba ta yi amanna da batun ta, take ta shiga jero mata sannu, lumshe ido Kawai Salmah tayi tana sauraren ta ba tare da ta amsa sannun da take jero mata ba, jikinta gaba ɗaya yayi sanyi tausayin Aysha ta ke ji a zuciyarta kamar kamar me, gaba ɗaya yanzu lissafinta a dagule yake, tana bukatar ke6ewa domin ta yi nazari da tunani, karar da wayarta ya yi alamar shigowar message yasa  ta ware idanunta, bude saƙon ta yi, ta duba lambar ce babu suna, tana gama karanta ta yi delete ɗin shi, juyowa ta yi ta kalli Aysha  da duk ta shiga damuwar jin cewa bata da lafiya, ta ce "Da sauki sosai na ji dama, ki tashi ki je class ba 1: 30 zaku shiga ba." 

"baza ni ba Salmah ko na shiga babu abinda zan fahimta a ciki kawai mu wuce gida." 

Shiru Salmah ta yi tana nazari ita karan kanta yanzu babu abin da take bukata kamar ta ganta a gida, da gaske kanta ciwo yake yi kamar ya rabe biyu, ganin halin da Aysha  ta shiga yasa ta amince  mata.
 
Text ta turawa Salman ta sanar masa wucewarsu,  ba tare da bata lokaci ba suka fice daga school ɗin.


Koda suka dawo gida babu kowa, Ammi bata dawo daga asibiti ba, dkai tsaye ɗaki Salmah ta wuce ta watsa ruwa ta yi Sallah ko abinci bata nema ba, ta haye bed ta kwanta tare da lumshe idanunta kamar tana  bacci duk da kuwa ba ta jin zata iya yin wani bacci a halin da take ciki.

 Aysha  kam kitchen ta nufa kai tsaye  don Samar wa salmah abin da za ta ci, sharp sharp ta daura farin couscous ganin akwai miyan sauce na hanta a fridge  dauka ta yi ta kunna  gas  ta daura shi ta dumama tana gamawa  ta zuba mata a plate ta dauka tare da ruwan sanyi,  koda ta shiga ɗaki sai ta tarar da ita a kwance tana bacci, a raunane ta ce "Ayya  ta samu bacci ga shi ba ta ci komai ba." Ajiye abincin ta yi ta rufe tare da shigewa toilet.

 Duk abin da take yi Salmah na jinta shiru kawai ta yi bata tanka ta ba, don a halin da take ciki bata tunanin zata iya buɗe baki tayi dogon magana.

Wanka ta yi sharp sharp ta shirya cikin bakin jallabiya plain bashi da adon komai sai dan zip ƙaramin dake kwance a gaban rigar hijjab ta zura  ta gabatar da sallah tana idarwa ta dauki abincin da ta zuba wa salmah ta hau tsakura,  duk da ba wani daɗin shi take ji ba haka ta shiga turawa kamar wacce aka ce ma ci ko ki mutu.

 Ko rabi bata yi ba ta jiyo sallaman Salman a bakin ƙofar ɗakinsu kafin ta kai ga amsawa ya sawo kai ,  ganintw yasa ya ce "Sister lafiya kuka samfo, me ya faru?."

Ta ce "Wlh salmah ce bata ji daɗi ba, Ashe neman da nake mata ɗazu tana clinic lokacin." Kallon salmah yayi dake kwance kan bed ya ta6e baki tare da cewa "Yau abin ya faɗa kan manya to Allah ya sauwaƙe, naga Ammi bata dawo ba har yanzu kuma naga kamar babu abinci a dining, wallahi mun kwaso yunwa don yau komai banci ba a school, dama mun sa ni wurin mother muka nufa."  Ya karashe maganar yana yamutsa fuska tare da shafa ciki, Aysha tace "A Kwai abinci ai, na dafa  couscous da muka dawo."  Dauke kai  yayi tare da jan dan ƙaramin tsaki, kallon shi tayi ta ce "Baza ka ci ba ne?"  Ya ce "To ya na iya muje ki zuba ma na mu kore yawa, amma wlh ba wani son abin nan nake yi ba, yzuɓi yake min da ƙuraje" Dakatawa tayi da tauna wanda ta zuba a baki ta dago ta kalle shi "menene haka Salman dan Allah, zaka haramta mana abinci." 

" To ai gaskiya na faɗa, na lura ku ƴan gidan nan kuna son wannan abin sosai har da Abie." 

Hararar shi Aysha ta yi tare da ajiye plate din da ke hannunta ta yi gaba tana fadin,  “ Kai dai ka sani, da iyayinka, wallahi Salman matarkw ta bonu” ya rufo mata baya yana dariya. A falo suka tarad da Suraj yayi balance a kan 3 sitter yana shan iska, jin motsi  yasa ya ɗago ya kalli hanyar stairs, ƙur ya ƙura mata ido baya ko ƙeftawa, har suka ƙaraso gaban shi bai sani ba, sai da Salman ya ce "kaiii surajo!." 


 Firgigit ya juyo ya kalle  shi,  "Irin wannan kallon shi mai ahlari ya kira nazaratuttuzihi.” 


Murmushi  Suraj yayi   yace "Afwan wlh kamar ce ta 6aci." Har suna haɗa baki wurin cewa "kamar me." Ya ce "kamar Sister Eshart da friend  ɗita Maamah da na ke yawan baka labarinta makwafciyarmu ɗin nan, kullum naga Sister Eshart wlh ita nake gani, komai nasu ɗaya bambamcin  Kawai jiki  siririya ce sosai ita, Sister Eshart ta ɗan fita gwa6i kaɗan, amma wlh kamar an tsaga kara zaka rantse twins ne, kai ko kai da Sweetie da kuke twins baza ku nuna musu kama ba." Salman yace "to Mallam zubairu na ji kullum sai ka dame ni da zancen wata ƙawar ka  Maamah amma har yau ka kasan haɗa ni da ita."  "Ka ji tsoron  Allah friend ranan ba ka ganta ba."  

"To ni ina na tsaya kallon fuskarta da daddare ne fa ga duhu." Suraj yace "OK to bari zan haɗa ka da ita anjima idan munje gidan na za ka sha mamaki kuwa."  

Aysha dake sauraren  su tace "Wai wa ku ke magana a kan ta ne." Salman ne ya amsa mata da "Wai wata makociyarsu ce take mugun kama dake, kamar an tsaga kara." Rass gabanta ya yanke ya faɗi haka Kawai ba tare da tasan dalili ba, zaro manyan idanunta tayi tace  " da gaske? aiko dai zan so na ganta yaya sunan ta?" Ta ƙarashe maganar idanunta a kan Suraj alamar shi take tambaya, ya ce "Sunan ta Maamah, Bafulatana  ce kyakkyawan kamar ke, ni karan kaina zan so ku haɗu, wlh Sister Eshart idan kika ganta zaki dauka kece, sai kin rasa gane wacce ce ke daga cikin ku." Dariya suka kwashe dashi ita da Salman jin  shirmen Suraj wani bin yin abu yake kamar ɗan 5 years ,cikin dariya salman yace "waiii! aiko dai wannan kama ta baci, to ke kinji tsabar kama har zaki rasa tantance wacce ce ke daga cikin ku." kallon su yayi ya ɗan bata rai ya ce " Oh dariya ma na baku ko, to shikenan zan yi kokari na haɗa ku wata rana wlh zaku gane ba wasa nake yi ba, ita ta daɗe ma da sanin labarin ki, don kusan kullum nazo nan na koma sai na mata zancen ki, wlh  Eshart har muryar ku iri ɗaya ne, badadan nasan cewa ke Buzuwa ba ce kuma  ƙanwar  Ammi ce ta  haife ki ba da sai nace ku ƴan biyu ne" Murmushi tayi tace "Wlh har naji ta shiga raina, dan Allah idan ka koma kace mata Ina gaisheta." Yace "Aikuwa ina koma wa Estate  ta gidan su zan fara biyawa na gaya mata." 

Salman ya ce "to munji Mallam Surajo, sis a bamu abinci." harara suraj ya maka masahi jin yana 6ata mai suna a cewar shi, kam ce wa tayi  "to acici mala'ikun kauna muje dining." 


Bayan tayi serving ɗinsu ɗakin ta koma ta duba salmah  tana nan yadda take a kwance  kamar yadda ta barta,  ji tayi tausayin ta ya kamata ƙarasawa tayi ta miƙa hannunta  ta taba goshin ta, babu zafi sosai ajiyar zuciya ta sauke a fili tace "Allah ya baki lafiya ƴar uwa." 

Sarai salmah na jinta don kuwa ba barci take yi ba.

Kwanciya tayi a gefen ta , ta lula duniyar tunanin abin da ke gabanta, shiru tayi ta tsurawa ƙaramin fankan Saman dake juyawa da mugun gudu idanu, ta fi minti ashirin a haka kafin ta sauke wani irin nannauyan ajiyar zuciya mai haɗe  da huci na zallar bacin rai , a fili  cikin kaushin murya ta furta  "Babangida! Babangida!! Babangida!!! hmmmmm  kaci gaba da 6oyewa kada ka kuskura nayi ido biyu da kai, domin daga ranar da ka ganni na ganka kayi ban kwana da farin ciki a duniya indai har na haifu cikin Inna da Baffa." Ta na maganar nan cike da kawarin gwuiwa da tsantar alwashi.


Da sauri salmah dake sauraren ta ta juyar kai gefe hawaye na ziraro mata, cikin azama ta kai hannu ta goge ɗon bata fatan Aysha ta ganshi a fuskarta, motsin juyawar salmah yasa ta juyo da sauri a kalleta, don a zatonta ta farka ne ganin ba farkawa tayi ba gyara kwanciya tayi yasa ta saki ajiyar zuciya, tare da gyara nata  kwanciyar ita ma.

Koda suka kammala cin abincin nan suka bar plate ɗin suka kakka6e duwawunsu suka fice , motar Ammi suka shiga da yake key na hannun Salman, shi ke kai su school da ya dawo take kar6an key sai kuma gobe, ganin bata nan bare ta amshe key ɗin yasa suke  Allah Allah  su bar gidan kafin ta dawo, sai da suka hau kan titi Suraj dake driving ya kalli Salman ya ce, “ Ina jin kamar na yi mantuwa a gidan Ammi fa.” “ Ya Salam! Me ka bari, Allah yasa ba mai muhimmanci ba ne, don ba zan koma ba kar mu yi kicibis da Ammi.”  Salman ya fadi cikin ɗan damuwa. Dauke kai Suraj ya yi ya mayar kan hanya kafin ya ce, “ Zuciyata, na baro friend, Salmah Zuciyata ce yau throughout ban ganta ba, i have missed her terribly ji nake kamar na shekara ban ganta ba“ Wani dogon tsaki ne ya kufcewa Salman, takaicin Suraj ya hanasa magana sai kawai ya shiga watsa masa wani kallo, irin na rasa abin fadan nan. Dariya Suraj ya tuntsire dashi, sai kuma ya yi gyaran murya, da deef voice dinsa mai daɗin sauraro ya fara rera waka cikin wani salo irin ta makawakar zamani  mai daukar hankali

{Salmah ke ce hasken idona,
Ko a duhu ina ganinki a raina,
Tun kafin na fahimci kaina,
Na tsinci zuciyata a hannunki ba tare da izini ba,
Ban san lokacin da na kamu ba,
Sai na tsinci raina yana kiranki a kowane lokaci,
Ko duniya ta juya mini baya,
Zan tsaya a gefenki ba gudu ba ja da baya,
Ko an ce min soyayya kuskure ce,
Ni kam zan zaɓe ki fiye da sau ɗari a rayuwata,
Idan soyayya laifi ne,
To ni na yarda a hukunta ni saboda ke, Salmahtah…..}

Duk da yanayin da Salman yake ciki sai da wakar ta dake shi, sosai ta yi dadi da ma'ana, ga kari irinta kwarewa da baiwa tsantsa da aka yi mata, da murya da ta samu mai daɗin amo, amma don dai kawai ya nuna Suraj baya tare shi, sai ya taɓe baki  kawai ya kawar da kai, dariya Suraj ya sake yi, ya ce “ Sai da kai surukina abokina, Allah ya nuna min ranar da za ka fita daga cikin yan adawata, ranar da  za ka damka min Salmahtah da hannuwanka. Yanzu dai ina muka nufa?"  Maganarsa ta karshe yasa Salman kallonsa  kadan kafin ya ce "Mu je wajen Mother mu ci abinci, dan wlh ban ƙoshi ba tsatstsakura kawai na yi don ba wani iya cin couscous na yi ba." "Ok sai dai mu faka motar Ammi a gidan su Maamah don kasan mother sarai ƙaniyar mu zata ci idan ta  ganmu da motar nan." Salman ya ce "su iyayen Maamah ba za su faɗa mata ba?" "Baza su fada ba, ai sun saba da rigimata." 

Tun kafin su ƙarasa  bakin get ɗin shiga kangiwa Estate su ka fara cin karo da mutane tsaitsaye,  yan kabu kabu, da ƴan napep, wasu a ƙafa wasu ma a mota, da alama an hana su shiga ciki ne don ga get ɗin wajen nan a garƙame Salman  ne ya fara lura da da sauri ya juyo ya kalli Suraj yace "friend what is going on here." Sai lokacin Suraj ya kula, wani irin zaro ido yayi cikin zaƙuwa ya ce "big bruh!" Salman yace "kai I don't understand meye big bruh."  Dai dai lokacin suka isa bakin get horn suka yi, sai da sojojin dake gadin bakin get ɗin wajen suka leƙa ganin Suraj yasa aka buɗe musu get ba tare da bata lokaci ba, tun da suka shigo cikin wajen zargin Suraj ya ƙara tabbata,  cikin maɗaukakin farin ciki ya ce "Salmah Ya Ahmad." Salman cikin rasahin fahimta yace "waye Ya Ahmad?" Suraj da duk ya ruɗe  Ya ce "Ya B"  Tsaki Salman yaja ya ce  "kaiii dallah nutsu kamin bayani ka na ta ƙara saka ni a kwana wanene   Ahmad wanene kuma  Ya B?" Sai lokacin Suraj ya tuna Salman fa bai san shi da haka ba, da  sauri ya ce "oh sorry friend , Mr Ahmad Idris Ahmad kangiwa nak e nufi." Zaro ido Salman yayi ya ce "A ina?".......


PLS AYI COMMENT KO BABU YAWA😅


Oum Ummeetarh ce😍

***