TALES OF THE WAZEERIS

the visits

by @surayyahms

7.

Tana kaiwa cikin chamber da tsananin sauri aka bude mata kofa tashiga can ciki kai tsaye hanyar fankacecen bedroom din ummu salman tayi bayan ta wuce babban falonta na musamman inda babu mai shigowa duk fadin tharim vale daga ita sai mijinta sai sangaryacciyar jikarta Leela wazeeri, datake mata kamr yar gwall

Duk wani mutum nadaban iyakacinsa falonta na farko cikin uwar dakinta kuwa ko amintaccyar jakadiyarta bataba shigaba bare wani na daban banda servants masu gyara mata waje kawai ke iya shiga suma ba kasafai ba.

da dumbin mamakin ganin ta bayarda izinin gayyata har daki Nana A ta shigo fankacecen bedroom din taganta a zaune akan lafiyayyan gadon dakin tana jera dalolin kudi acikin wani akwati cikin nitsuwa tasaka wani irin sophiscated golden colour silk me duhu dayasha dinkin celeopatra boubou me wani irin tsada da sheqi.

wani irin tsaftaccen kwalliya ne a fuskarta da adon sarqar gwal dayaji wuya da hannunta bazaka taɓa cewa she is in her early 50s ba.

tsayuwar cak nana A tay ta kare mata kallo dan tasan koma miye zaisaka ummu salma ta gayyato har cikin uwar dakinta to abu ne me girma kuma na sirri ne

Daidaita nutsuwarta da fuskarta tayi tareda sakin gyaran murya batareda takalletaba don sosai yanayinta ya fara bata cewa da akwai wani boyayyen matsala...

Juyowa ummu salma tay ta dan kalle nana A ayayin datasaki wani irin numfashi mai nauyi daya bayyanarda halin bakin cikin data tsinci kanta aciki wanda tsabar jinin kasaita yasaka duk da sun hade ido batace mata uffan ba

cikin tsananin taushin murya da tsantsar rarrashi Nana A tace,.."ranki shi dade....ina fatan komi lafiya.

miƙewa tsaye ummu salman tay bayan mintina data dauka tana jan aji cikin sanyin nuna iko kai tsaye tace

...nasan kina da masaniya akan duk abunda ke faruwa agidan nan danke ma a matsayin uwa kike agare mu babu wani hukunci da uwarjini zata yanke agidan nan batare da saninki ba

. ..is'nt dat correct???

kafin nana A ta amsa cikin katseta da wani irin kasaita tace inason na isar da saqone, amma banason nakai shi dakaina gaban uwarjini snn taje ta yanke min hukuncin da bazan so araina ba..

A nitse nana A tace

....inajinki ƴata. menene saqon naki.

juya mata baya tay muryanta da karsashi ahnkli tafara cewa Acikin gidan nan koda ace akuya nake ba mutum me daraja ba baikamata ace uwarjini ta tsallake ra'ayina wajen yanke hukuncin bada umarnin zaben matan aure wa yarima shamsan batare da amincewata ba, bayan duk kunsan da cewa akwai ƴar jikata leelah datafi kowa kwarjini kyau da haske agidan nan wacce a qa'ida itace yakamata ta zamto tabbattacyr matar aure ga yarima shamsan ba wata ba.

tana gama furta hakan ta juyo ta kalle nana A cikin ido da karsashi a muryanta snn tace..."sanin kanki ne bani da ɗa namiji magaji, yata suhaila da na haifa kuma ta rasu da jimawa bazan sake iya haihuwa ba..jikata Leela ce kawai ta rage min. sama da shekaru 100 da suka shude a wann ahali ansaba haɗa auren jini da jini a zuriar nan saida yazo kaina ne za'a dena???

ke kanki kinsan cewa jikata leela itace tafi cancanta data auri babban jika agidan nan, dan sarki, kuma jikan dan uwana shugaba khaleefa..nagaji da wann rashin adalcin da ake kkrin min in ba akaunar jini na ne sbd dan ban haifi ɗa namiji ba a fito fili kawai agayamin.

cikin sauri Nana A tace "ya isa haka salma, ki iye bakinki dan kowani bango agidan nan yana da kunne, bai dace ya zamo kece babba kuma kina jayayya da umarnin uwar jini ba

..yakamata ki nitsu. snn kisani bayan shugaba khaleefa kece kawai babba agidan nan, saidai naga kmr kikan manta ke wacece...to bari in tunashe ki wallh jini yafi ruwa kauri kedin jininmu ce, bazai taba yuwa haka kawai a dora darajar wani zuria sama danaki ba saida babban dalili kema kuma kinsan da haka.

Daga mata kai ummu salman tayi batareda sakin fuskaba kamar yanda suka sababa muryarta a tamke tace Abun ne da ciwo nana, idan har shamsan bai auri leelah ba meye datajata da kima na agidan nan?? idan imran ko zafar suka samu ɗa namiji nan gaba..bansan ya zan kare acikin gidan nan ba dan kowa yasan bani da wani magaji kuma har tsufana haka zan zamo tamkar wata batacciya acikin rayuwarku Shiyasa dolene hankalina ya tashi,..ke kanki kinsan yadda nakeson hada jini na dana dan uwana khaleefa daya rasu bana son harna mutu banida wani daraja a gidan nan...baxaiyu ace yarima me daraja kmr shamsan abarshi har yakare raywrsa da mata daya tal kuma daga ahalin zamkora ba.. nana A....me xai hana itama jikana leelah ta zamo cikin jerin xabi na matayen da shamsan zai aura daga jininsa tunda ruhi me tsarki baice lallai sai ya kare rayuwarsa da mata daya ba.

Ajiyar zuciya mai nauyi nana A ta sauke ganin yadda ummu salman take mgn da tsananin damuwa da rauni

dan kwafa tay snn ta kalle cikin kwayar idanuwanta daya gama canzawa zuwa kalar tausayin kanta.

Daidaita nitsuwarta tay snn tace Ki yarda dani salma. akwai hanyoyi dayawa da xamu warware wannan matsalar Dan haka Nayi miki alkwari zan kai maganan wajen uwarjini yau amma duk abunda ta zantar xakiji daga baya.. Yanzu ki tashi ki shirya kanki idan mijinki zai karaso tharim vale kice masa ya taho da kaninsa da ke hannunsa, likitar ki zaizo nan bada jimawa ba domin dubaki. Ni zan wuce na barki lpya yata.

Daga mata kai ummu salaman tay batare da tadena sauke ajiyan xuciya ba dan tasan duk duniya babu wacce take da kaifin basira da kuma kusanci na amana da uwarjini kamar Nana A....

daga nan wajen wanka ta fada domin ta shirya jiran likitarta da zai karaso bada jimawa ba.

wani irin shiru gidan ya dauka na dan lokaci sai wajajen 10:30am kafin nan dirin motoci sun kai kusan qoma baqaqe kirin na alfarma kirar luxury cardillac xx800mgh suka cike tsakar gidan da armed securities zagaye dasu

matar shugaba imran ne ta iso da servants dinta guda hudu, kasaitacciyar mace hajiya zulaiha ana ce mata ummu xulaiha fara ce solll kyayywan gaske. dan dama ita bata tattaro gabaki daya ta dawo tharim vale ba tana can Abuja ne tana kula musu da wasu abubuwan tattalin arxikinsu iyaka yarsu marida waxeeri kawai turo ta rigata isowa. daga dayan extra convoy din kuma Ummu bilqees ce wato matar zafar wazeeri tana tura tsohon ciki da ayarinta itama.

tarba na musmn aka musu a fadar uwarjini, bada jimawa ba can sai mijin ummu salma alhaj fuad shima ya iso tare da matashin kanin sa dayake zama a wajensa wato farees salman.

wanda nana A ce ta bada umarnin cewa ataho dashi batare da sanar da kowa dalilin hakan ba

kafin kace wani abu waje ya cikka infact mansion din waxeeris bai taɓa cika kamar nayau da kowa da kowa da kowa ya iso cikin tharim vale ba dan duk wani mutum dakagani anan jinin xuriarsu ne..tsatsonsu na tharim vale da na garin maruwa.

bayan angama taaziya da gaishe gaishe da ayyana wasu zantuka masu amfani musmn game da bikin naɗin sarautar sarki abdallah da zasu gabatar gobe da safe, atake uwarjini tabada umarni cewa duka matayen gidan da surkunayenta da yayansu duka suka wuce private chamber su akabarta da zallan mazan..

dan dolene su zamto cikin shiri dan gobe ne zamkora zasu taho ayi mgn hadin jini da aure,

snn yaune xa'a tura shamsan wazeeri cikin gidansu na dahrul zahra a matsayin sa na yarima, ancestral royal training home dinsu dayake chan qasar morocco inda xa'a trainesa sosai.

Darul-Zahra sanannen waje ne across all emirate where future rulers are confirmed. babu wani dan sarki da zai zamo cikakken dan sarki face har sai royal council nacikin fadar dahrul zarah sunbada blessing dinsu akansa.

Young princes kamar shamsan din are sent to live quietly among warriors nd scholars dan akoya musu ilimin addini ,Adalci, Tawali’u, Hakuri, juriya, Hikima da daraja ahali da kuma uwa uba sirrin tattalin arziki da iko akan siyasa cikin ruwan sanyi.

Dagata dayan bangaren kuwa gabaki daya fadar zamkora bata sake gane kan sarki murad ba, dan tun da yaga wann agogon sarauta yasan cewa babbn masifa da bala'i ce take kkrin tunkarosa daga tharim vale, saidai dayake Allah ya zuba masa uban taurin kai da jiji dakai yasaka ya killace kansa ya shiga neman mafita wajen malamai da masu ilimin taurari tunjiya da yabar fada ya shiga zauren ilimi har yau bai fito ba.

matarsa gimbiya Amani noorain ta shiga tsananin fargaba sbd yadda kowa yake zancen batun gayyatar da zasu amsa gobe na uwarjini a tharim vale dan bazata iya tuna rana na karshe da suka taka kafarsu garin ba.

cikin wannan tashin hankali ne ta kasa zama waje guda, daga hadadden chamberta tafito tana yawo a cikin dogayen hallways na killataccen sashensu kasaitaccen takunta na gimbiyar zamkora na amsa amo bisa gogaggen marble tiles din datake takawa.

tun jiya rabonta da saka yarsu ta farko wato sarauniya Arisha acikin idanunta, ahnkli take rarraba hanklinta cikin kowane lungu da sako na sashen kamar wacce take neman wani abu acikin nitsuwa tafara kwalla mata kira tana cewa

“Arisha…” Areesha.

shiru wajen ya dauka babu amsa. ta kara takawa gaba, zuciyarta na bugawa da wani irin sauri sauri dan tun da aka tura kanwarta Ushna london karatu ko kadan bata kara fahimtar yanayin Areesha ba.

duk dama yara ne da basu wani girma ba amma cikin ranta she feel like kmr Areesha tana da hannu acikin batun tura yar uwata wani kasa me nisa karatu dan ita kadai tay mulki tare da babanta, saidai abun nada wuyar cankowa kai tsaye dan Arisha always seems very innocent, calm nd sensible agaban mutane kowa da kowa yana balaeen daukarta yarinya me sanyin xuciya da nitsuwa sosai.

hannun gimbiya Amani noorain na dan rawa yayin da take tura kofar kowani bangare nacikin killataccen sashen nasu tana ambatar sunan Areesha

har kaman zata wuce daga can gefen wani karamin indoor pool ta hangeta daga can nesa tana zaune a kurkusa da wani irin karamin black stoned aquarium dake cike da ruwa.

cikin sauke ajiyar xuciya tafara zagowa ta wajen tana takawa ahnkli idonta nakan hadadden wayarta datake latsawa ahankli

lokcin Arisha na zaune cikin nutsuwa inkaga kayan dake jikinta ma soo simple babu wani hayaniya, fuskarta is calm tamkar da babu komai dake gudana acikin ruhinta tana dan murza fararen yatsun ta cikin ruwan pool tanata kallon wasu pages na takardunta da ta baza a gabanta masu cike da zane zanen dreams inta na son kasancewa acikin wani babban gidan mulki ko sarauta..

ajikin takardan ta zana manyan fadodi da rawanin iko…

duniyar da take tsananin so da mafarkin mallaka anata rayuwar...

snn tabi zana kanta acikin fadar amma da kyakkywan fuskar yar uwarta ushna bada nata fuskr ba...

dan tunda aka haife kanwarta ushna tajima tana balain tsananin kishi da jin haushin irin kyaun fuska da Allah ya zuba mata sedei bata taɓa fitowa fili ta fallasa hakan ba saidai tayi ta mata mugunta a boye

tay nisa cikin tunanin dreams inta wanda ko kwala kirar da gimbiya amani noorain tay ta mata afarko bata jiba bare taji sautin takunta dake karatowa.

adede gefenta akwai wata karamar mage dake yawo caraf sai magen ta dan firgita mistakely ta zame acikin ruwan aquarium din tanata kokarin neman tsira.

ko kula wann magen dake kokowa da ranta Arisha batayi ba sai can da dison ruwa ya fetso ajikin papern ta snn dago kai kadan ta kalle magen ido cikin ido.

magen duk ya zama abun tausayi cos she was clearly abt to be drowned ruwan yafi karfinta..

zakayi tsammanin Arisha zataji tausayi ta taimaka amma inaa babu wani alamar tausayi, ahankali ta kalle ruwan da magen ta fetto mata akan zanen snn tamike tsaye takarasa kurkusa da magen ta sunkuyar da kai tanata kallonta da wani irin icy cold wicked low tone tace "nobody messes with my dream. da karfi ta danne kan magen a ruwan snn tarufe bakin ruwan inda iska bazai shige ciki ba wanda kafin kace wani abu sai shiruuuuu da alaman magen nan tayi drowning cikin ruwan har tadena numfashi.

tunda ta tabbata magen ta mutu calmly tadawo ta zauna wajen zamanta a nitse kamar bata aikata komai ba ta fara tattara zanen da sauri sauri adede

lokacin da Amani Noorain ta iso kusa da ita kenan sede kafin ta samu damar magana cikin sauri Arishan ta bude ruwan tafito da matacciyar magen ta ajeta akan table cikin katse gimbiya armani da innocent face tace

mummy…kiga..wnn magen ta fadi a ruwa harta mutu.

gimbiya Amani noorain tatsaya cak ta zura mata ido jin wani abu strange ya dan soki zuciyarta sbd ta hango faruwar komi snn magen nasu na tarihi ne they believe suna kawo musu hadin kai da kariya acikin gidan once magen gidan suka fara mutuwa alama ce na cewa wani jarabawa me wuyar dauka zata shigo musu abazata.

cikin basarwa dai ta nemi waje tazauna agefen areeshan a hankali tanata kokarin boye tashin hankalin dayake kkrin cika mata kirji msm game da strange dabiun areesha.

anitse tace meyafaru da magen har ta fadi nd i tot ure allegic to cats..ya akayi kika ciro gawarta???

cuccusa zanenta tay a jaka kafin nan ta dago fuskarta da mrmushi cikin nitsuwa tace" mummy bansan ya akayi ta fadi ba. a tunani na a life is far better than my fear na boye tsoro nane dan nay kkrin ceto ranta

gimbiya amani noorain ta gyada kai batace komi ba tanata kallon fuskarta da babu alaman wani abu akai sai nitsuwa.

“toh wannan sakon da kika kai wa mahaifinki jiya daga ina kika samo shi ne..

Arisha tadaga kai akaro na biyu tace na same shi ne a dakina nima bansan wa ya aje min ba.

shirune yadan sake ratsa tsakaninsu sai kuma gimbiya Amani ta dan sauke ajiyar zuciya. tace ‘yar uwarki fa amma kin san abin da kika jawo mata jiya ko?...

nan Arisha ta dan dakata da cusa paprs din ta dago kai sama zatay magana

gimbiya amani tace dakata min Areesha, hankalina bai kwanta game da batun tura ushna london ba amma da nay magana da babanki sai na lura from his words na dan fahimce kmr kece kika fara bashi wann idea din cewa akaita can da nisa

..meyasa???

calmy Arisha take kallon maman nata sai can ta dan murmusa kadan tace “mummy, kinsan babu wanda yakaini kaunar yar uwata ko..inhar kin yarda magana ta baba ya dauka har ya yanke mata hukuncin maida rayuwarta london ai itace take jawo wa kanta. she doesnt listen to anyone, she doesnt follow the palace rules. baki ganin abubuwan kunya datake jawowa ma gidan nan ne? i am just trying to protect her, since grand pa salim is dead banason baba ya gaji da ita yazo ya tsaneta har rayuwarta ya lalace.

duk wayannan kalaman cikin tsananin sanyi da nitsuwa ta fito dasu ta inda har gimbiya Amani ta kasa cewa komai na dan lokaci.

wani abu a cikin zuciyarta yana kokarin fada mata gaskiyar lamarin arisha amma tana kin amincewa.

dan tunda aka sakasu a makaranta kusan koyaushe sai an kawo karar ushna cewa tay wani abu marar kyau ko ta karya wani dokan fada me tsanani, nd tanaji ajikinta kmr Areesha has sumting to do with it sbd ta lura kamar kusan koyaushe in wani abu me muni ya faru tsakanin yayanta arisha bata bari amata kallon me laifi saime gaskiya she is always the hero nd d good girl in every story kanwatta kuma itace ake dora mata laifin kullum

kafin gimbiya amani ta sake cewa komai wata baiwa ta bayyana a bakin kofar wajen da ladabi ta sunkuya cikin girmamawa snn tace

“ranki ya dade… an umurce mu da a fara shirye-shirye. gobe da azahar za a tashi zuwa Tharim Vale.

cikin runtse ido da budewa na dan lokaci ta sauke kwayar idonta a hankali akan yarta Arisha wacce tuni ta koma cikin duniyarta na tunanin me xai faru idan sukaje yankin tharim vale.

dan dukiya da karfin ikon tharim vale is her biggest obsession musnmn da ake cewa sun hada jini dasu ta wani waje saidai wnn tsanar dake tsakanin ahalinsu yasaka bata taɓa zuwa garin ba ta dai san garin zazzau ne amma kuma yankin tharim vale kusan mai shigarsa sai wane da wane sbd suna da power bana kadan ba

har cikin zuciyarta ta san tafiyar nan ba tafiya bace kawai hala da akwai wani abu me muhimmnci dake zuwa aciki wanda zai iya sauya mata rayuwarta anan gaba..

dan inhar Allah yasaka ta shiga zuriar uwarjini toh duk duniya babu wanda zai kaita jin farinciki dan irin rayuwarsu na tsananin iko da power take mutuwarso.

sanar dasu saqon tafiya da baiwar tay yasaka gimbiya amani bata sake samun dama tay ma Areesha wasu tambayoyi ba.

sabida wnn calm nd innocent nature na Areeshah ita kanta tana shan wahala wajen gama fahimtar ita wacece dan ako yaushe kallon yarinya me nitsuwa da sanyin hali suke mata face saida shekaran jiya da aka tafi da kanwarta ushna london kafin nan tafara fahimtar wasu irin strange abubuwa daga yanayin arisha da har yanxu bata gamsu dashi ba..

kai tsaye suka bar wajen suka fara shirin tafiya, Arisha ta boye zanenta da nisa inda tasan babu wanda zai iya ganinsa,.

gata da kwakkwla tuni tafara fahimtar kamar gimbiya tafara zarginta akan tafyar kanwarta ushna sai kawai tafara wani irin dabiu kamar na wanda batajin dadin jikinta dan kar gimbiya ta sake dago mata mganar yar uwartan kwata kwta

dagata bangaren uwarjini kuwa wajajen karfe 12pm na rana suka gama tattaunawa nan shugaba imran wazeeri yaa nada strong delegations da royal councils da chambers na hakimai da kaninsa zafar wazeeri. aka je masarautar kano da sabbin shaidoji da dokoki domin a sauke duk wani jini da zuria na sarauta snn a dora sabo tall daga jininsu na tharim vale wanda uwarjini ta riga ta zaɓa.

ana daf za'a yi sallahn azahar suka isa fadar kano, saidai zantar da dokokin uwarjin da shaidu bai wani xo musu da wahala ba sbd tsantsar daraja da iko da ahalin wazeeris suke dashi,.

jama'ar kano sunyi murna sosai tare da tsammanin cewa wnn kmr sabuwar daraja suka samu daga tharim vale da aka basu kimar hada jini da tsatson da suke iko da sarauta, tsaro da kuma mulki..

kai tsaye jamaar garin sukayi maraba da sabbin shugabanci da dokokin da uwarjini da shugaba imran suka bayyyana.

sukuma ahaluka da xuriar sarukanar da aka sauke gani suke kamar sakaci da taurin kan sarki murad na masarautar zamkora ne kawai yajawo musu wannan ruwan bala'i na rasa matsayinsu da jawo musu kaskanci da zubewar daraja a idon uwarjini.

acikin kankanin lokci wannan hukunci da tharim vale ta shimfida a yankin dala gameda sarautar kano yabi yadawo abun alfahari ga dumbin jamaar garin, saidai awani bangare kuma juyin mulkin ne daya jawo wa masarautar zamkora wani irin baqin jini da tarin maqiya daga wasu ahali da zuri'oin sarauta masu karfi.

TO FA YARIMAR THARIM VALE GUDA DAYA NE AMMA...

GA COUSIN DINSA LEELAH

GA YAN MATA BIYU YAN UWAN JIJI DAGA ZURIAR MAQIYANSU

ARISHA DA USHNA

SHIN WACECE KUKE GANIN ZATA SAMU NASARA A WANN TAFIYAR??

ZAN JIRA COMENTS DINKU SAI MONDAY ZAMU CIGABA

THE JOURNEY OF 1000 MILES BEGIN WITH A STEP !!!

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWABOOKS

@SURAYYAHMS

WATTAPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025