Part 08
RAYUWAR DA NA ZABA
Part 08..
Hasken fitilun ofishin ya mamaye idanuna, amma duhun da yake cikin zuciyar Alhaji Sani ya fi komai ba ni tsoro. Ya tsaya a bakin ƙofa, hannunsa daya rike da makullin mota, daya kuma yana kokarin daidaita hularsa. Idanunsa sun yi kankance suna kallo na cikin tuhuma da wani irin mugun nufi..
“Me kike yi a nan, Maryam?” Muryarsa ta fito a dake, ba tare da alamar wasa ba.
Na ji yawuna ya ƙafe, numfashina ya tsaya cak. Cikin sanyin jiki na tashi tsaye, hannuna yana rawa ina kokarin boye takardar da na riga na dauko a bayana. “Alhaji... dama... dama neman banɗaki nake yi, sai na manta hanya na shigo nan.”
A hankali ya tako daya, biyu, har ya iso gabana. Kamshin turarensa mai karfi ya cika min hanci, amma wari yake min na jini da yaudara. Ya zuba min ido na tsawon sakanni, wadanda a gare ni suka yi kama da shekaru.
“Bandaki kuma a ofis ɗina? Maryam, kada ki manta da wanda kike magana. Na san dabarunku na mata tun kafin a haife ki. Kin zo neman wani abu ne, ko kuma wani ne ya aiko ki?”
“A’a Alhaji, kuskure ne kawai,” na fada ina kokarin fita ta gefensa.
Ba zato ba tsammani, ya damƙo damatsena da karfi. Na saki wata 'yar kara saboda zafi. “S
Ki saurare ni da kyau ki ji! Idan har kina tunanin za ki iya yi min zagon ƙasa kafin wannan auren, to ki sani kin yi babban kuskure. Mahaifinki a tafin hannuna yake, kuma kema kanki a tafin hannuna kike. Idan na ga dama, zan iya sa a kulle ki ke ma a matsayin wadda ta san da kisan da aka yi amma kika ɓoye!”
Gabana ya fadi. Ashe ya san cewa na san komai?
“Ni ka sake ni! Kana cutar da ni!” na fusata sosai ina kokarin kwatar kaina.
Ya watsar da hannuna a wulakance “Ki fice min daga nan! Kuma ki sani, daga yau har zuwa ranar ɗaurin aure, ba za ki kara fita daga gidan nan ba. Zan kira mahaifinki yanzu, na shaida masa cewa kin fara sakin layi, don haka a matsayinki na amaryata, a nan zan ajiye ki a karkashin kulawata na saka miki ido, saboda kin fara wuce gona da iri.”
Na zaro ido cike da mamaki. “Me kake nufi? Sati biyu fa suka rage a ɗaura auren!”
“Sati biyun a nan za ki yi su. Zan sa direbana ya dauko miki kayanki daga gida.”
Ya fice da sauri ya sa makulli ya rufe ofishin ta waje. Na ruga jikin kofa ina bugawa da ƙarfi, amma saboda gidan babba ne, babu wanda ya jiyo ni. Na faɗa kan kujera ina kuka mai tsuma zuciya. Na ji na tsani kaina da na zo gidan nan ba tare da wani tsari mai karfi ba.
Ina cikin wannan halin, na tuna ashe ina da wayata a jikina! Na ciro ta da sauri na duba, na ga har ta kusa ɗauke wa saboda rashin caji. Na kira Khalid.
“Khalid! Ya kama ni! Yana shirin tsare ni a nan har sai an ɗaura mana aure!”
“Kwantar da hankalinki Maryam,” muryar Khalid ta fito cikin nutsuwa. “Wannan ma wata babbar dama ce muka samu. Idan kina cikin gidan, hakan zai sauƙaƙa mana nemo wannan faifan muryar (recording). Akwai wani boyayyen daki a cikin babban dakin kwanansa. Ki nemi hanyar shiga can. Ni kuma ina waje, ina tattara sauran hujjoji daga wajen tsohon direban da ya san komai.”
“Khalid, ina jin tsoro. Idan ya gano ni kuma fa?”
“Kada ki damu. Ina tare da ke. Kuma ki sani, wannan takura da matsin lamba da kike sha, shi ne zai zama silar yancin mata da dama a kasar nan. Kada ki karaya.”
Ina gama wayar, na ji ana bude kofa. Wata mace ce mai matsakaicin shekaru, fuskarta babu annuri, ta shigo da abinci. Ta kalle ni ta girgiza kai.
“Ina tsananin tausaya miki yarinya. Kin fada tarkon da babu mai fitar da ke sai Allah.”
Na kalle ta da sauri. “Wace ce ke?”
Ta ɗan yi murmushi mai ɗaci. “Ni ce wadda na daɗe ina bauta wa Sani a cikin gidan nan. Kuma ni ce wacce zan taimake ki yanzu... idan har kina da jarumta.”
Ku biyo ni a Kashi na 9 don jin yadda zata kaya...
Hussain Yusuf✍️