The Niƙab Girl
***
It's fatoumspassion IMSAL another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE, EHSAAS and SCARRED.
Free pages
Chapter 5
The niƙab girl
Tini ƙamshin turaren sa ya gama gauraye ajin baki ɗaya,
ajin yaɗau wani shiru kamar mutuwa ta ratsa, da yawa-yawa daga cikin yan matan sun ma kasa ɗaga ido su kalleshi tsabar kwarjini da haiba da Allah yayi masa ya ɗan yi few seconds gaban ajin atsaye kafin ya kalli wristwatch ɗinsa, ya ƙarasa inda aka tanadar ma malamai don zama yazauna yana faɗin
"bamuda isasshen lokaci,
wanda suka san sun bawa Principal karatu su ware can side ɗin wanda ba su bayarba su tsaya anan"
ya ƙarasa yana nuni da sashen da sit ɗin su Imsal suke, latifa ji take kamar tai hauka saboda takaici don kuwa waccan karon daya jisu hadda tana cikin wanda ya bawa punishment bata iyaba don ya cita gyararraki.
Kuma ta yima kanta alƙawarin duk sanda ya dawo zata mai karatu me kyau don tai proving mishi cewar ita ɗin bawai daƙiƙiya bace da karatun ta.
Se kuma gashi tayi ragon azanci ko tace Malam sani ya cuce ta daya karɓar mata karatu afarko, gefe suka ware ciki harda Natasha domin Malam sani already ya karbi izurinta, ajin ko me tarin kirki ba'a samu ba saboda yadda suke shakkarta.
Yan sit ɗin gaban row ɗinsu Imsal ne suka fara biyawa yana zaune saman kujerar waya ma ya ciro yana dannawa amman attention ɗin shi naga karatun ɓatan wasali ɗaya kikai yana jinki se ya dawo dake,
Ga ƙaƙale don ta biyu tana fara karatun yace ta dakata taja gefe,
alamar bata iyaba,
ta farkon dai da kyar tasha,
ta uku ma haka ana zuwa kan ta hudu, da ta biyar, da ta shida aya ɗaya biyu seya musu gyara hakanne yasa duk ya ware su gefe.
Mubeena ta duƙufa kan Kur'ani tanata bibiyan haddarta don tasan bata yi wani sosai ba, sanin malam dani ke jinsu zata iya mai gara-gara ta wuce, amman tasan Abdullah bawai kara ze mata ba indai fannin karatune besan wannan ba haɗasu zeyi ya hukunta baki ɗaya.
Imsal kuwa kanta na a ƙasa duk da tana cikin niƙab bata yarda ta ɗago ta kalleshi ba, tana ta ƙoƙarin calming kanta down, don batason ƙirjinta ya cigaba da bugawa haka zata iyayin bara gada akaratun,
ganin layin yazo kan mubeena da take farko kafin ita a bench ɗin yasa ta ƙara tsorata.
Shikam se ayanzun ne ya ɗaga ido ya kai duba gun inda ƙanwarshi take,
kallon wacca take kusa da ita yayi ta ƙunshe fuska da niƙab kuma bame tsagar ido bama,
balle ya iya gane wacece ta idanuwan ta,
be bada much attention gare ta ba, ya maida hankalinsa kan karatun da mubeena take yi,
tafara tiryan tiryan da tajweedi da komai cikin karatun ta da yake rainon shice akaratu, tana zuwa tsakiya tilawarta tai ƙasa alamun bata biya haddar da kyau ba, karatun sharp sharp tai,
yana cinta gyara na ɗaya, na biyu yace
"taja gefe,"
ransa ahaɗe kamar be taɓa sanin taba arayuwarsa bata ce komai ba ta ɗau ƙur'anin ta taja gefe tana ƙunci don daman tasan za'a rina, Imsal ce ta taso ahankali ta ƙaraso ta zauna.
latifa har ta fara dariyar mugunta aranta don tasan ba lallai Ya Sheikh ya karbi uzurin su na sababbin zuwa bane shiyasa basuyi hadda ba, ba kamar malam sani yake ba.
Be ɗago ba balle ya kalli inda me bada karatun take hankalin sa na akan wayarshi.
Ahankali tayi a'uziyyar data fara jan hankalin sa kafin tai basmalar daya tabbatar mishi da zarginsa ba tareda yayi niyya ba ya ɗago yana dasa idonshi akanta don ganin wacece yayin da ta fara karatu cikin zazzaƙar ƙira'a irin tasa sak-sak, domin duk wani tajweedi da Foundation na karatun ƙur'ani agurinsa ta samu har tafi mubeena ƙanwarshi iya mimicking salon sa ga zaƙin murya da zaunanniyar tilawa da ba iya shishi kaɗai ba dukkannin students ɗin ta ɗau hankalin su.
Dayawa basu taɓa jin muryar ta bama se yau, Abdullah lumshe ido yayi kawai because this is the exact voice dake hunting ɗinsa da karatu cikin mafarkansa,
tsabar yadda karatun yayi masa daɗi be san sanda imsal ta kammala ba.
ita kaɗaice be ciwa gyara ba dalili kuwa shine ita ba sabuwar hadda take ba maimaici ce sannan ta horu tun kuruciya da karatu da tajweedi a hannunsa.
Natasha ji take kamar ta tashi ta nuna Imsal cikin alfahari tace
"yar uwartace tsabar farinciki"
yayin da zuciyoyin wasu da yawa kamar nasu latifa ke cike da baƙin cikin baiwar da Allah yayi mata, bataji ta ƙara tsanar tsanar Imsal ba seda ta ji Abdullah yace
"mabrook"
acan ciki ba lallai wani yaji don ita kanta lips dinsa tai reading ta gane me yace saboda yadda ta kafa mishi ido.
Imsal miƙewa tai zata koma gurin ta bayan data kammala anitse taji yace
"na sallame kine,"
rintse ido tai tana rokon Allah yasa bai gane taba afili dawowa tai ta zauna calmly, ɗan nisawa yayi kafin yace
"suna?"
Cikin tsantsar sanyi murya da jan aji wannan ne karo na farko atarihin rayuwarsa a ajin daya taɓa tambayar sunan wata ɗaliba don ba wanda ya sani.
Latifa jitai ƙirjinta na dukan tara-tara ganin yarinyar nan me niƙab ta samu attention gurin sa, irin wanda ta daɗe tana ƙokarin samu tun shigowar ta makarantar, muradin yayi recognising ɗin ta, koda sau ɗaya ya tambayi sunanta amman be taɓa ba duk kuwa da yadda take shishshige masa, da kuma ƙoƙarin datake yi, duk shekara itace take yin na ɗaya a ajin.
Asanyeye cikin wannan muryar ta me zaƙi ta amsa mishi da
"Imsal,"
"full"
taji yace yana ɗauke idonshi akanta ya mayar kan wayarsa kamar ma bece komai ba,
Sosai Imsal tazama anxious saboda babu wanda yatsayar yake mai tambayoyi tunda aka fara karatunnan se ita,
"why her?"
"Meta mishi?"
Tashiga rayawa aranta, jin tai shiru batae komaiba na tsawan minti guda yasan yaɗan ɗago yana kallon ta itama dagowar tai ganin idonshi akanta yasa tai saurin rintse ido saboda kwarjinin da yayi mata dukda shi baya ganin ta,
"Imsal Umar"
tafada da ɗan ƙarfi,
daidai sanda wayar ta ya fara ringing acikin jakar ta data bari acan baya.
kwata-kwata ta manta yau bata sashi a silent ba ɗif ajin yayi don duk asirrince suke zuwa da wayoyin su dokar makarantar bata yarda da zuwa da wayaba.
Daina ringing tai, kafin in seconds ta cigaba asanyaye Abdullah yayi wa duka ajin kallo ɗaya kafin yace
"bring the phone out,"
Cikin sigar bada umarni
shiru kowa yayi don kowa yasan ringing din tashi wayar aka tsaya ana kallon kallo.
Ahankali Imsal ta mike ta ƙarasa gurin zamanta, tafito da wayar data tsinke ta dakko tana ƙarasawa gaban shi, cikeda ladabi ta durƙusa tana faɗin
"gashi"
hannayenta da suka ajje wayar saman desk ɗinsa yabi da kallo da suke cikin handglove kalar hijab ɗinta.
sassanyan kamshin jikin ta na ziyartar hancinsa, har cikin ƙirjinsa ya jishi, ji yayi yafara jin haushin kansa da kansa kan yadda gaba ɗaya yabawa yarinyar attention.
Komawa tai ta zauna agaba don bai bata iznin tafiya ba har lokacin, kira aka ƙarayi be san sanda idanuwansa sukai shifting zuwa ga karanta sunan da yake ciki,
Letter B ce da heart emoji ya gani kan screen ɗin ɗauke kanshi yayi daga kallonta yanaji baze iya cigaba da zama a ajinba Allah yasa itace ta karshe daman.
miƙewa yayi yasa hannun sa yaɗau wayar Imsal da, ada beyi niyyar ɗauka ba amman ganin anata kiran ta nonstop yasa yaji yanason yaji waye mai kiran.
"Ina labour prefect?"
ya tambaya hankalinsa na kan ɗaliban daya tsayar, da sauri latifa ta mike tana faɗin
"gani Ya Sheikh,"
ko kallonta beba yace
"ina wacca tazo da waya aji,"
Cikin sigar da kai bazaka ce yasan wacece ba balle direction ɗin inda take zaune, ahankali Imsal ta miƙe, yace
"join them,"
yana nufin wanda ya tayar basu iya karatu ba.
batace komai ba don daman tasan se anhukuntata, ta karanta a form cikin dokokin makaranta.
yace
"daga gobe in sunzo acema cleaners su hutu, they will be on duty for the whole week,"
Jinjina kai latifa tai tana mugun jindadin yadda Imsal tafaɗo hannun ta don seta tabbatar tayi mata abinda bazata taɓa mantawa da ita arayuwarta ba.
"Call the next teacher"
ya faɗa yana nufar ƙofa, suka bishi da godiya seda ya fita ajin ya kaure da hira wanda ya wanci ta ya sayyadin ce, harda masu zuzuta hular dayasa, da masu zuzuta kyan da ya ƙara, da masu fadar albarkacin bakinsu kan abinda ya faru na kwace wayar Imsal da akai.
Lila ce ta kalli Natasha dake rubuta sunanta ajikin sababbin littattafan take tambayar,
"gaskiya nidai duk yadda za'ayi inaso naga fuskarta,"
Natasha sak tai tana kasa cigaba da rubutun, latifa tace
"kinji yadda yar iskar take karya murya don taga namiji,
toh Dr yafi karfinta ƙwalelanta dama daga gani ɓoye ɓoyen fuskarnan da take muna fukace,"
Lila tace
"ai bama se kin faɗa ba beauty,
ni ai taban mamaki jifa tama samu arziƙin ya tambayi sunanta tai mai banza naso ya lallasa shegiya,"
Natasha batasan sanda tace
"ayyah ku kuwa meye tai muku, bafa ta shiga harkar ku, na gafa shine ma yake shishshige mata,"
beauty wani ɗan iskan kallo tama Natasha tana faɗin
"Wllh Dr yafi ƙarfin ya shigewa mace, kinsan mata masu ajin da suke bin gayennan kuwa,
Ita har wacece?
ubanta waye?
da ze shige mata wallahi Natasha kika sake maimata irin wannan kalaman da kikai se kin bar clique ɗinmu,
kaf naga take take-taken ki ba kyaso aringa faɗar aibun yar makotannan naku,"
lila tace
"ashe kema kin lura beauty,
amman dai yanzu ya za'ayi mu ga face ɗin nata,"
beauty ta saki wani shu'umin murmushi tace
ki barni da ita gobe badai tana ƙarƙashi naba, zanga ta yadda zatai escaping, wallahi senaga fuskar ta kotana tsafi da baƙar jaka, kuma sena wulakanta mummunar fuskar da take ɓoyewa saboda nasan ba'ayi macen da zata fini kyau a bin suhail ba,"
Natasha ji tai maƙoshinta na bushewa don tasan wata maƙarƙashiyar suke haɗawa Imsal.
Gashi ba damar tai wani abu, ta daiyi shiru tana ji suna ta zagin Imsal suna aibata har iyayensu.
Daga gurin su Imsal kuwa watace agabansu ta juyo tana kallon Imsal tace mata
"Imsal ko,"
mubeena ce tai caraf da har yanzun haushin haɗasu da labour prefect da Abdullah yayi yake cimata rai
tace
"meye?
dacan bakisan sunanta ba, don anji karatu shine za'a zo afara nace ma yarinya"
tace
"kefa mubeena matsala ta dake kenan,
ni shawara zan bata akan wayarta daya tafi da ita, indai kika bari yafita amakarantar nan baki karbi wayar nan ba tohm zaki iya kaiwa wani term biki ganshi ya dawo ba,
Ya taɓa kwacen waya kafin sauka seda aka cinye term dakyar yasa aka ban"
Imsal ɗan kallon mubeena tai alamar tambaya, tace
"karki damu inya kwace waya gurin malam sani yake kaiwa ni kuma Malam sani nawane,
kibari idan antashi se muje mu lallaɓashi baruwansa ze baki wayarki aike baƙuwa ce haka zamuce baki san dokar ba,"
Imsal tace
"nafa sani nagani cikin form"
mubeena sakin baki tai tana kallonta tace "tohm kije kice mai kinsani zaki gama term ɗinnan ba waya wallahi."
Shiru Imsal tai tana tinani har wani malamin yashigo, be daɗe ba aka tashi.
Duk ɗalibai se haramar fita suke tana kallon yadda Natasha ke satar kallon ta kamar da magana abakinta se kuma taga latifa tamata magana ta rataya jakarta sun fice tare.
office ɗin Malam sani suka nufa ita da mubeena, ta karbi wayar mubeena taiwa Natasha text kan ta jirata a napep ɗin tatafi amso wayarta kada ta sake tace zata bi wasu yauma.
Mubeena tace
"kome ma ya kawo shi makarantar nan yau?
Jin Imsal bata ce mata komai ba ta bawa kanta ansa da
"oho,
yanzun ya jamana wulakanci muna zaman zamanmu don nasan Allah ne kaɗai yasan aikin wahalar da latifa zata bamu gobe, do kiris take jira dama, mayya kawai"
Imsal tace
"koma meye ne ai mune mukaja da kinyi karatu dakyau, nikuma da banzo da wayaba aida ba'a ce za'a hukunta muba,"
Mubeena kallonta tai tana tsuke fuska tace "ataƙaice dai bin bayansa kike waike kinmanta da kalar halin yaya mu'allim ne muna yara kinmanta zane mun da yake kodan ke baya dukan ki dama can kece favourite ɗinsa,"
Imsal tace
"bawani favourite kinsan shidai bawai ɗagawa kowa ƙafa ya keyi gun karatu ba,"
Dariya mubeena ta farayi tana faɗin
"harna tina sanda kikai wata biyu a izaawaƙa,"
ita kanta Imsal sanda ta tina dariya ta farayi don lokacin har batason ace karfe biyu tayi, don kamar jira yake data fara biyawa zece ba daidai take ba seta sakeyi,
kuma tana nuna ƙosawarta zece ta miƙe tsaye kuma bazata zauna ba harse antashi.
Kwankwasa office ɗin Malam sani sukai, amman kamar baya nan shiru, mubeena ta leƙa ta taga ganin bakowa a office ɗin yasanya
tace
"Imsal bafa yanan ƙila be dawo ba,
yana cikin makaranta ko can za muje mu nemo shi?"
Imsal tace
"toh muje can mu duba"
don batason tafiya ba wayarta, ta nanne kaɗai take samun communication da iyayenta suna fara tafiya sukaci karo da Malam sani, mubeena cikin raha take cemai
"ai malam gurinka mukazo, se muka ga office ɗin skills"
yace
" tohm gani malama mubeena fatan dai komai lafiya?"
tace
"lafiya lau alhmdlh kaga Imsal na rako mu baka haƙuri batasan cewa ba'a zuwa da waya ba kaga baƙuwa ce?"
yajinjina kai yanaa sauraronta, tace
"shine ɗazun da yaya mu'allim, ina nufi ahmmm.... Ya Sheikh yazo yaji ringing yace afito da wayar,
shine tabashi kaga ko gardama batai bama Allah sarki baiwar Allah,"
takarasa cikeda siyaya da lallabi duk don yaji tausayin su yabasu
Malam sani yace
"ashsha-ashsha Malama me niƙab garin yaya?"
dasauri mubeena ta bashi amsa tana faɗin "malam bata sani bane,"
Yace
"shiyasa amman nan gaba seki kiyaye ba'a zuwa da ita kinji,"
jinjina kai Imsal tai, mubeena tace
"Malam tohm mu biyoka mu karbi wayar nasan kai yaya yake bawa idan ya karba yace rabona dashi tun a ajinku inaji yama fita amakarantar be kawo minba, ƙila yanada uzurine,"
ɗan juyowa Imsal tai tana kallon mubeena, wacca tace wa Malam sani
"tohm shikenan mungode Malam bari muje"
ta kama hannun Imsal suka bar wurin, seda suka kusa gate Mubeena tace
"Imsal tunda kikaga ya tafi da wayar nan Allah kuwa ya gane ki, muje gida kawai kanki bisa wiyanki ki roƙeshi yayi hakuri ya baki wayar ki,"
Girgiza kai Imsal tashiga yi tana faɗin
"Ni babu inda zanje mubeena
Malam garba fa jirana yake
Bazan iya barinsa yayi ta jiraba,"
Tace
"Imsal bason amsar wayar kikeba da alama" tace
"inason amsa mana amman ni gaskiya bazan iya binsa gidanku ba, haka kawai ya ƙakalo wani punishment ɗin yasani,"
Mubeena dariya tafara yi tace
"ke Allah ya rage wannan halin fa koni yanzun baya ko hararata sedai idan nice na shiga harkarsa Allah ya shiryu,"
Daidai suna karasawa bakin gate Imsal tace
"ban yadda ba akan dai waya bazan je inda yaya mu'allim yake ba Allah kuwan," ta ƙarasa tana shigewa napep dake duk yan makarantar sun tafi saura tsirari da uwar facemask taga Natasha kamar yadda tasa sanda zasu fito bye-bye taiwa mubeena tana kallon Natasha tace
"wai wannan facemask ɗin na menene," Natasha tace
"ƙura nima banaso,"
Imsal girgiza kai kawai tai tana faɗin
"Allah yashiryeki kyama faɗi gaskiyar dalilin sawar"
Natasha bata tanka taba se tambayar ta data farayi
"shin ta karɓo wayar,"
Girgiza kai Imsal tayi tana faɗin
"befa bawa Principal ɗinba,"
Natasha tace
"tohm base kisa ya Rayyan ya karɓar miki ba tunda abokaine"
Murmushi Imsal tayi tana faɗin
"kin kawo idea"
Natasha tai murmushi tana kallon gefen titi da suka fara tafiya, Imsal ta ɗan kalleta kafin tace
"Nats akwai wata matsalar ne?"
ɗan juyowa tai da sauri tana kallon ta kafin tace
"me kika gani?"
girgiza kai tai tace
"nothing,
kafin ta ɗaura da
"naga dai kinyi wani irine da aka tashi it seems kamar you wanted to talk to me, se wannan meye ma sunan tan ta miki magana kuka fita,"
Natasha murmushin yaƙe tai tana faɗin "beauty, eh fah dama bakomai tambayarki kawai zanyi ko zaki tsaya karɓar wayar,"
Jinjina kai Imsal tai kafin ta ɗaura hannunta saman kan Natasha dake kan jakarta tace "if there's anything you can always talk to me you know that right,"
ɗan jinjina kai tai tana fadin
"bafa komai Ya Imsal kawai jina nake banajin daɗi nasan kuma stress din zirga zirgane,"
Imsal tace
"sannu bari muje gida kici abinci seki huta zaki ji dadi,"
jinjina kai kawai tai ahaka har suka ƙarasa gida, kowacce ɗakinta ta wuce as usual.
*Abdullah*
Gaba ɗaya yama manta da Rayyan da yake gidan nasu,
yana fitowa daga ajin direct ya bar makarantar yayo hanyar gida, amsa gaisuwar da masu gadi ke masa yayi ya wuce zuwa flat ɗin sa direct.
falon bakowa se tashin ƙamshi yake ga TV tana ta ci ganin channel ɗin dake kai yasa ya tina Rayyan na nan don shi sam baya kallon film ko wani show kwata-kwata in ka ganshi agaban TV to ce ne labarai ne ze saurara ko kuma peace TV ze saurari shirye shiryen malamai.
Remote ya ɗauka ya kashe TV, yana kallon yadda Rayyan ya gama hargitsa mishi falon da kwalayen junk food ɗin da yayi order yaci naci ya bar na bari awurin, ga can ɗin drinks ɗin da yasha ya jefar da bottle water everyway is scattered.
dogon numfashi yaja don idan akwai abinda yafi tsana acikin rayuwar sa be wuce untidy spaces ba,
rigar jikinsa ya cire ya ajje saman couch ya cire agogon shi, ya ajje wayarsa data Imsal daya zira a aljihun sa ɗazun,
kitchen yanufa ya ɗakko kayan shara, ababban ledar shara ya juye duk wasu kwalayen junks da Rayyan yabari da cans da bottles, saura abincin ya haɗe shi guri guda da niyar inya fita ze bawa mai gadi ya samu almajiri ya bashi.
ya shiga tattare gurin, ya gama ya shiga goge-goge, nan da nan ko ina yayi fes-fes kamar ki lashe hatta da takalman da Rayyan ya zube tsakiyar falon seda ya dauke ya mayar dasu muhallinsu.
Ya kammala ya saka incense me daɗin ƙamshi, kafinnan ya ɗauki rigar sa da wayoyin ya nufi ɗakin, saman gado ya hango Rayyan ya baje kamar ɗakinsa ya nata sharar barcin sa, kallon ɗakin yayi ya kalli inda Rayyan ya jefar da kayan da yazo dasu da alama wanka yayi nasa kayan ne ƙananu ajikinsa.
girgiza kai kawai yayi ya shiga tattare su ya saka a inda ya dace kafinnan ya shiga toilet, seda ya fara wanke shi tas duk da a safiyar yau ɗin kafin ya fita seda ya wanke, amman yake ƙara wankewar, seda yagama wankewa yayi wanka da ruwa me ɗumi ya fito da bathrobe ajikinsa.
ƙamshin sabulan wankansa ne ya tayar da Rayyan daga barcin da yake yi, ya juya ya ganshi gaban mirror ya nata shafe-shafe yana lailaye skin ɗinshi kamar wata mace tsabar yadda yake kula da fatarsa yake ji da ita, Rayyan hamma yayi yana faɗin
"au ashe kadawo,"
Be kula shi ba ya shiga goga turarrukan sa na jiki, Rayyan yace
"kaci abinci?"
se alokacin ya juyo yace
"kai tunda dai kaci ba shikenan ba," murmushi Rayyan yayi don yasan fushin me yake sarai, yace
"zanfa gyara gurin kawai barcine ya kwashe ni,
kasan na kwaso gajiya,"
yace
"naga alama but as a responsible man haka ya kamata ka ringa cin abinci kana barin ko ina kaca kaca with due respect I hate how disorganized you are,"
dariya Rayyan ya kwashe da ita yana faɗin "kanka akeji yanzun dai ka gyara ko kuwa infita inyi?"
Cike da fushi Abdullah yace
"aiba kowane irinka ba,"
komawa Rayyan yayi ya kashingiɗa yana faɗin
"ka hutashsheni"
yaja wayarsa, straight number Imsal ya ƙara dialing don yasan by this time definitely zasu tashi a islamiyya.
jin waya ta fara ringing aɗakin yasa ya juya yana kallon Abdullah, shima shi yake kalla don duk su biyun sunsan ba ringing ɗin wayoyin su bane,
Rayyan katsewa yayi, aikuwa ta dena ringing nana take, da mamaki yakara dialing number Imsal, aiko ga cigaba da ringing a ɗakin.
Abdullah ne ya miƙe ganin Rayyan na mai wani iri-irin kallo na tuhuma ya nufi inda ya ajje wayoyi ya ɗakko wayar Imsal dake ringing, ganin da gaske wayar Imsal ɗince hannun Abdullah yasa Rayyan ya buɗe baki zaiyi magana se ya rasa me ma zece, ganin B again da heart emoji ke kira yasa yaja wayar yana sata a Flight mood.
Be cewa Rayyan ƙala ba ya ajje wayar ya koma wurin press ɗinsa yana cire kananun kayan da zesa Rayyan miƙewa yayi ya ƙarasa yaɗau wayar yana jujjuya wa, kafin yace
"kai!
Me wayar unique take ahannunka, "
Yi yayi kamar ba dashi yakeba,
"Ko mantawa da ita tai amakarantar?"
Ya tambaya yana ƙara jujjuyata, be san sanda Abdullah ya ƙaraso ba ya karɓe wayar a hannunsa yana faɗin
"I seize it,"
Yana nufar saman gadon shi da wayar yayi sliding yana buɗe wa hoton ka'aba ne screen wallpaper ɗinta, Rayyan ya rike ƙugu ya biyo shi saman gadon yana faɗin
"dama ajinsu ka tafi fitar da kai shiyasa fa yarannan suke tsoron ka yanzun fisabillah awannan era ɗin dama ana seizing wayane, ni da wayar Natasha nagani ahannunka nasan bataji bazance komaiba ƙila wani laifin tama but unique haba now Maza metai aka karɓar mata waya eh?"
se alokacin ya ɗago daga scrolling wayar da yake,don shi kansa besan meyasa ya karɓi wayar ba balle tahowa da ita balle buɗe mata ya shiga mata bincike he don't even know what his looking for.
Yace
"ai anhana su zuwa da waya,
She came with phone and it rang while I was in class, so I have to take action kada wani ya maimaita gaba,"
Ɗan kallon shi Rayyan yayi yana faɗin
"I don't trust you, bro in abinda kace gaskiya ne then give me the phone,"
Yana koƙarin karɓar wayar da sauri ya maidata bayan shi se lokacin yayi murmushi yana faɗin
"I won't give you ai hannu da hannu na karb8a kuma hannu da hannu zan mayar mata and plus I need to check something, tun ɗazun wani number B with heart emoji take kiran ta," Rayyan yace
"sunan datai saving number nane, B means blood, ans that heart symbolises the love she has for me,"
Abdullah ya kalle shi irin da gaskennan yace
"check in baka yarda ba, unique will never do something wrong I trust her with my life ba tada rawar kai irin na sauran yaran,"
buɗe wayar yayi ya shiga, ganin da gaske number Rayyan ɗinne yasa yaji wani sanyi na dira akirjinsa kafin ya damƙa mishi wayar,
Rayyan cikin ɗaurewar kai yake faɗin
yace
"but this kids are growing fast,
I'm surprised yadda ta girma, she's this tall fa sanda na bar ƙasar nan ya shiga kwatantawa da hannunsa, pretty like supernatural, with those eyes, is she still a crying baby?
yafada yana murmushi shi kaɗai batare da yasan yanayi na because memory ɗin little Imsal ne yashiga flooding a mind ɗin sa.
Wata yar iskar dariya Rayyan ya farayi da shishi kaɗai yasan ma'anar ya yana faɗin "ehen ehen, pretty eyes and, and...."
yana kwaikwayon yadda Abdullah din yake yi da hannunsa, kafin yace
"and now she's tall like this, and more prettier" yana daga hannunsa sama, Abdullah ganin Rayyan is making fun of him yasa ya haɗe rai yana miƙewa,
yace
"banson wulaƙanci kasan dai they will forever be little kids in my eyes,"
Rayyan cikeda shaƙiyan ci yace
"I see, and is better that way karka ja mana raini gurin yara,"
dan juyowa yayi yana kallonshi yace
"da nai me?"
yace
"eh wai tina maka nake last time da nace mubeena ta girma ko za'ai yad gidane nima haka ai kacemin ban manta ba,"
Abdullah yace
"ni fa ba irinka bane, why will I date yaran da nakusa haifa abeg I'm not like you, they are too small for me I want someone my age, kaidai kaje kaita fama da ƙananun yara suna samaka ciwan kai"
Rayyan dariya yasa yana faɗin
"su agemate manya kardai ka auro wacca zata ringama duka Allah, your 31 and you want someone 31"
Kiran sallar da aka farane yasa Rayyan ya kyale shi, sukai alwala suka nufi mosque atare, basu fito ba se bayan isha don Abdullah yana zama yi ma dattawa unguwar karatun bayan magrib indai yana gari.
Suna ƙarasawa gida Rayyan ya wuce shi kuma yashiga can cikin gida inda ya tarar da mubeena tareda auntyn su salma kanwar mahaifinsu ce da take zama tare da mubeena acikin gidan.
mijinta ya rasu babba ce sosai ƴaƴanta mata biyu kuma duk ta aurar dasu, da badan ita ɗinba besan yadda ze ringa yi da mubeena ba akoda yaushe,
da fara'a aunty salma ta tareshi tana sanar dashi yau bata bar mubeena ta musu kwaɓa ba da kanta ta mishi abincin dare.
Tare suka zauna sukaci duk su ukun lokaci zuwa lokaci mubeena na satar kallonsa so take ta mishi maganar wayar Imsal kuma tana jin tsoro, da kyar ganin har ya kammala cin abincin sa ze wuce sashen sa ta mike tana bin bayansa tace
"yaya bakaji ba,"
juyowa yayi yana kallonta, tai ƙasa da kanta tana fadin
"dama....dama.."
tunkan ta ƙarasa maganar yace
"bafa zan sassauta any punishment ba,"
da sauri ta girgiza mishi kai tana faɗin
"ba wannan ba,"
yace
"tohm yadai?
akwai damuwane?"
jinjina kai tayi kafin tace
"daman wayar Imsal, dan Allah kayi hakuri kabata kaga baƙuwa ce ita batasan ba'a zuwa da waya ba yaya nama alƙawari bazata sake ba,"
yace
"amman ke aikinsan ba'a zuwa dashi"
jinjina kai tayi alamar eh yace
"hakan yana nufin bakya zuwa da ita?"
ɗan zaro ido tai tana tinanin inda yasan itama tana zuwa da tata, ta fara kame kame ya girgiza kai kawai yana faɗin
"bin umar ya amsar mata"
kawai yana yin gaba jin me yace yasa tai tsalle tana bin bayansa cikin farin ciki tana faɗin
"Thank you yaya,"
jin har lokacin tana binshi ya juyo yana tambayar ta
"what again?"
tace
"punishment ɗin Please yaya ka sauya mana wani hukuncin, kaga latifa ɗinnan dama kiris take jira kuma...."
Banzan kallon da yayi mata yasa taja bakinta ta tsuke yace
"nafara miki wasa ko, aren't you even ashame ki zauna baki da aiki kullum se danna waya kin zubar da tilawarki baki ɗaya ki gode Allah bani da kaina zan hukunta kiba, and daga yau zamu dawo da karatun Asuba"
"Yaya wllh,"
kwalla ta ciko a idonta zata fara rantse rantse yace
"barmin gabana kafin raina ya baci"
da sauri ta koma aunty salma memakon tabi bayanta tana daga falo tana faɗin "aigara dai kai mata faɗa sam ta dena maida hankali akan karatu ba kamar daba, batada aiki se waya,"
fuuuu tai ɗaki aguje tana banka ƙofa se kuka ita takaicinta ba wai faɗan daya mataba a'ah latifa ɗin da itace zata basu aikin da zasuyi gobe abin ya tsaye mata aranta takeji kamar duk duniya angama da ita.
Ababban parlour Rayyan ya tarar da Imsal tanama Hajiya tsifa ya zauna yana musu sannu da gida suka amsa, Imsal da fara'arta take faɗin
"Blood na maka smoothie is surprise se kasha zaka guessing abubuwan dana zuba aciki"
yace
"really kice yau Blood ze sha daɗi,"
ta jinjina mishi kai Hajiya tace
"nayi-nayi a ɗan sammin ance wai bana tsofaffi bane nidai Rayyan tunda ka dawo Imsal ta dena min abubuwan arziƙi komai zatai kawai nakane donta burgeka," murmushi yayi yana faɗin
"Hjy kishi kikeyi dani kawai kuma ba tantama Unique tafi sona akanki na daɗe da gane hakan,"
Hajiya juyowa tai tana karɓe kanta ahannun Imsal tace
"ke waye kika fiso acikinmu?"
tana biyema Rayyan kamar wata sa'ar shi, dariya Imsal ta fara tana faɗin
"dukanku!"
tana ƙoƙarin cigaba mata da tsifar, yace "ba dai zata faɗa miki bane hajjaju amman na dede da mallake ko ina a zuciyarta ko unique na"
murmushi ta cigaba dayi tana sa hannunta ɗaya tana rufe fuska yace
"bari nahau sama kafin na sakko na sha kayan daɗin da aka min by the way ina yar Mummy take ne,"
Hajiya tace
"tana sama ni tunda suka dawo daga islamiyya banji ɗuriyar taba,"
Imsal ce tace
"ta gaji ne tace bata ɗan jin daɗi shiyasa ta kwanta,"
aɗan dame Rayyan yace
"let me check up on her,"
har ya fara hawa saman ya tsaya yasa hannu a aljihunsa ya ciro wayar Imsal yana faɗin
"take it,"
sakin kan Hajiya tai taje ta amsa da sauri don dama jira take yaci abinci ta mai maganar.
yace
"kidena zuwa dashi don in yagani yasake kwace wa baruwana, ke zaki je ki karɓi abarmu"
jinjina mishi kai tai tana faɗin
"yaya thank you"
yace
"your welcome sister,"
ya wuce sama direct zuwa ɗakin Natasha seda ya kwankwasa ta bashi izni ya shiga yana tambayar ta
"meke damunta?
duk tayi wani sakwa kwa cemai tai kawai "barci takeji tagaji ne"
seda ya dudduba ta ya tabbatar she's fine sannan yace ta fito taci abinci se tai barcin karta kwanta da yunwa da tohm ta ansa mishi yana komawa ɗakinsa ta sakko.
Lokacin imsal na bawa Hajiya labarin yadda aka kwace mata wayar, Natasha ganin wayar take tambayar Imsal
"har ya amso kenan,"
Imsal ta jinjina mata kai tace
"kuma banma yi mishi maganar ba ƙila suna tare tun ɗazun shiyasa,"
wucewa kitchen Natasha tayi ta ɗibo abincinta ta zauna a falon tana cakalkala kamar ba Natasha dake mugun son cin abinci ba.
Daga Imsal har hajiya sun lura da ita amman dai basu ce komai ba sun zata ko duk cikin rashin jin daɗinne tana gamawa tai musu seda safe tawuce sama.
sanda Rayyan ya dawo sun kammala tsifar, Imsal ta shiga kitchen ta wanko hannayenta tai joining ɗinsa saman dining table kaɗan yaci abincin don aƙoshe yake yayi ciye ciye da yamma, smoothie ɗin dai da aka haɗa mishi yasha sosai kuma yaji daɗin sa sosai saidai ya rasa ingredients ɗin da Imsal tai using dashi yafara guessing tana mai dariya, tana girgiza kai,
"Theres milk definitely aciki"
ya faɗa yana nuna smoothie ɗin tace
"yes but akwai wani abu bayan milk"
yace
"theres fruit"
tace
"wana kalad fruit?"
tana kallonsa, yace
"uhmmm fruit dai namanta sunansa, but I can feel the taste"
dariya ta cigaba da yi mishi da kyar tafaɗa mishi
"she mixed it with banana, berries, yoghurt and milk" murmushin yafara yana faɗin ehen nadai faɗa
"banana is fruit abi,"
tace
"amman baka canka ba,"
baka faɗi sunan shiba yace
"duk ɗayane"
Girgiza kai take tana faɗin
"is not the same."
Bayan sun kammala zaman hira sukai afalo, se ga mummy ta kirata video call haka suka haɗu duka harda Rayyan suka sha firansu tana tambayar autarta akace tayi barci, se ten suka gama kowa yayi nasa ɗakin.
Washegari da safe Imsal da Natasha da wuri suka tashi as usual suka tafi makaranta tare ahanya tayi ƙoƙarin sanar da Imsal yau kar taje islamiyya amman ta kasa daga karshe suna sauka daga napep ta kalleta tana faɗin
"Ya Imsal yau dan Allah kar muje islamiyya," da mamaki take kallonta tace
"daga samu shine zamu fara fashi Natasha, baze yiwu ba karma kifara wannan maganar,"
Turo baki tai tana faɗin
"toh ni banida lafiya fa, nafaɗa miki tun jiya,"
tace
"Allah yabaki lafiya zanje ni sena faɗawa Malam sani,"
tace
"a'ah nidai kema bazaki je ba,"
tafaɗa cike da bore, Imsal bata tsaya sauraranta ba tai wucewar ta aji kawai.
itama nasu ajin tai tana tinanin plan ɗin da zatai kawai ta hana Imsal zuwa makarantar nan batason sumata wani abin da zasu cutar da ita, wata idea ce ta faɗo mata aikuwa ana tashi ta aiko wata ƙawarta ajinsu Imsal wai ace mata batada lafiya ko takawa bazata iyayi Imsal cikin tashin hankali ta goyo jakarta zuwa ajinsu Natashan.
tanata yi mata sannu tace ko zasuje clinic ne ta girgiza mata kai pretending take sosai tanaa matse ciki wai cikinta ke ciwo suje gida kawai.
da zuciya ɗaya imsal ta yarda ta kamota suka fito har zuwa napep Malam garba ganin haka shima duk ya rikice yana tambayar
"ko ya kaisu asibiti?"
suka cemai
"a'ah ya kaisu gida,"
ahaka suka ƙarasa gida Natasha se sake langwabewa take imsal tana rikota tana sakar mata jiki gata ita ba kaɗan ba duk tabi ta sakar mata nauyi kuma tafita girma nesa ba kusa ba, amman haka ta daure ta riƙe ta.
har ɗakin ta takaita tana tambayar ta ko ta kira yaya ne ganin ba motarsa agidan girgiza kai tayi tana faɗin
"a'ah ya Imsal nidai kawai ki zauna tare dani I'll feel better,"
da kanta ta temakawa natasha ta cire kayanta tashiga wanka kamar gaske batada lafiyar ta fito tana dafa bango, Imsal tashiga tambayar ta mezata ci tadafa mata bayan taciro mata riga mara nauyi tabata ta zira, Natasha ba kunya take cemata "tanason taci pepper soup din Catfish da fateera,"
Imsal kitchen tayi ko uniform bata cireba tashiga kwaɓa fateera,
ganin basu da catfish a fridge tafito tana zira hijab ɗinta tai gate ganin Malam haruna da Malam garba yasa cikeda girmamawa tace ma garba koze amso mata Catfish abakin titi Natasha ce tace shi take son ci, karɓar katin ta yayi yana faɗin aibama seta rokesa ba,
Pin din ta fada mishi
ya shige napep ɗinsa ya buga, ita kuma takoma ciki, karo suka kusan yi da Hajiya da batama san sun dawo ba suna can sama sunata kara kainarsu bata jisu ba.
tace
"ke daga ina haka kamar anjefo ki ina jakar?"
dakyar ta iya smiling tana faɗin
"tana sama Hajiya,"
tai gaba ganin tayi hanyar kitchen Hajiya ta bita tana faɗin
"ba'ayi abinci baneba naga kina wani ƙoƙarin yin wani girkin"
Imsal tana kneading fateera tana faɗin
"anyi Hajiya
Natasha ce batajin daɗi shiyasa zanmata wannan"
Hajiya cikeda damuwa take faɗin
"wai jikin ne,"
Imsal jinjina kai Imsal tai tana faɗin
"wai cikinta ne ke ciwo she's in pain sosai Hajiya,"
Hajiya tace
"bari kiga"
tafice tana komawa ɗakinta wayarta ta ɗakko tana saka kiran Rayyan bugu biyu ya ɗauka yana sallama bata amsa ba take faɗin
"Rayyanu kana ina?"
Da mugun ƙarfi do it haka take waya kamar wanda ke ɗayan ɓangaren kurmane bayajinta,
yace
"muna site Hajiya"
tace
"inane kuma site?
toh ma duk inda kake ka dawo ga ƙanwarka ba lafiya ciwan ciki kamar ze kasheta,"
taƙarasa cikin exaggeration na tsofaffi, cikin damuwa don sanin Imsal ce take da wannan ciwan cikin yake faɗin
"subhanallah ganinan zuwa yanzunnan Hajiya"
yana katse wayar, Abdullah ya kalleshi yana faɗin
"lafiya?"
girgiza mai kai yayi yana faɗin
"wai Imsal ce ba lafiya,"
Abdullah yace
"subhanallah meya sameta ba dai asthma ba"
girgiza kai yayi yana fadin
"wai ciwan ciki bari naje,
we'll talk later,"
jinjina kai yayi yana faɗin
"Allah ya bata lafiya ko nazo muje?"
girgiza kai Rayyan yayi yana faɗin
"no stay here ku ƙarasa ai aikin ya kusa zuwa karshe kasan in kabar nan zasu iya maka bara gada"
jinjina kai yayi alamar hakane, yace
"tohm Allah ya sauwake,"
wucewa Rayyan yayi ya hau motarsa se gida.
Imsal na kitchen harta fara gasawa taji sallamar malam Garba yana kwankwasa main door na falo fitowa tai ta zira hijab ɗinta ta bude kofar karɓa tai tana mai godiya yayi mata
"ya mai jiki?"
ta amsa da
"da sauki"
yace
"Allah ya bata lafiya"
wucewa tai cikin lokaci ƙanƙani ta haɗa komai ta aza kifinta awuta, komawa saman tai, Natasha danna waya takeyi jin motsin shigowar Imsal yasa tai saurin sake tattarewa agado tana shagwaɓewa ita ala dole mara lafiya, Imsal ta ƙarasa tana faɗin "sannu Natasha yanzun kifin zeyi kinsan bashida wiya,"
tace
"Thank you ya Imsal,"
zama tai gefenta tana faɗin
"Don't mention sister Allah yabaki lafiya Nats,"
jin karan zuge gate da rufeshi yasa Natasha wara ido tar ta buɗe shi, don tasan Rayyan ne kaɗai ke shiga da fita da mota that means ya dawo Imsal tashi tai ta leka ta juyo tana murmushi tace
"laaaaa ga yaya nanma ya dawo kinga ze dubaki ya baki magani kawai,"
Natasha ji take kamar tafasa kuka.
Rayyan na shigowa arikice yake tambaya Hajiya da
"ina take?"
tace masa
" aitana sama yasan langwai ce,
intana ciwo bata da dauriya kwata kwata," da mamaki yake faɗin
"Imsal ɗin?"
jin sakkowar mutum yasa ya ɗaga kai suka haɗa ido da ita, ta karaso tana faɗin yaya "sannu da zuwa"
ɗan kallon Hajiya yayi, tace
"nice nace maka Imsal ce ba lafiya ko ita kaɗaice yar uwarka, toh Natasha ce,"
dogon numfashi ya sauke yana faɗin
"where is she?"
Imsal tace
"yaya tana ɗaki,"
tai hanyar kitchen don duba kifin data ɗaura, yana shiga ɗakin ya hangeta saman gadon ta wani nannaɗe kai bazaka taɓa cewa ƙarya take yiba, yace
"nats sannu ko,
can you here me?"
jinjina mishi kai kawai tayi ta juya mishi baya tana matse ido don tasan ze iya gane karya take inta bari suka haɗa ido yace
"wai cikin ki ke ciwo or is it cramps?"
da sauri ta shiga jinjina masa kai zama yayi saman gadon yana shafa kanta yace "you don't usually have thia painful cramp ko kinsha zaƙi dayawa ne,"
jinjina mishi kai ta sake yi, yace
"aibakijin magana ne shiyasa let me bring pain killer,
kinason kici wani abinne,"
asanyaye tace mishi
"uhmmm.... uhmmm" yace
"anything just tell me all your cravings"
ji take ga dama ta samu ba damar ta dama inda gari banzane list zata mai amman kasancewar tanason ayi believing da gaske batada lafiyan ta shiga girgiza masa kai fita zuwa daƙinsa ya dakko first aid box ɗinsa ya samo mata ibuprofen, tare suka ƙaraso kofar ɗakin da Imsal dake rike da tray din data jera mata plate ɗin data jera fateera akai ta rufe da wani da wani bowl data zuba peppersoup ɗin aciki karɓa yayi daga hannunta don harda tea ɗinta mai zafi ta mata.
Ya ajje maganin saman tray ɗin suka shiga tare, Imsal ce tace ta tashi gashi ta kawo mata,
ahankali ta te maka mata ta zauna tana sake shagwaɓewa da kuma yunwar dake addabar ta shiyasa ma taɗan faɗa kamar mara lafiyar gaske.
Rayyan da kansa ya shiga ɗibar peppersoup ɗin da spoon yana kai mata baki da kyar ta amsa irin bataso ɗinnan amman azahiri kamshinsa ya gama sata kara jin yunwa, ya gama hargitsa ta so take kawai su fita ta far mishi amman ba dama.
Imsal tace
"yaya ka ringa haɗa mata da fateera ɗin, zefi riƙe mata ciki"
haka kuwa akai hannunsa ya wanko yazauna ya ringa bata,
Tana yin rabi ba don ta ƙoshi ba tace
"ta koshi"
don kartaci da yawa su zargi wani abu, Imsal kamar zatai kuka don tasan tanada cin abinci tayi-tayi da ita ta ƙara tace
"itafa takoshi"
Rayyan yace
"ki kyale ta kawai anma samu taci"
yaballi maganin ya bata takora da ruwa kwata-kwata batasha tea ɗinba zata koma ta kwanta yace ta jingina tukunna karta kwanta daga cin abincin ta, kallon Imsal yayi ganin karfe uku tayi yace
"islamiyyar fa?"
Natasha wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, Imsal tace
"batada lafiya ai yaya,
kabari muje gobe"
yace
"kece bakida lafiyar,"
girgiza kai tayi, yace
"karna kuskura inji anfara wannan ɗabi'ar wai in ɗaya ba shida lafiya ɗayan ma baze jeba, ba gani ba, ba ga hajiya ba zamu zauna mukula da ita,"
ɗan kallon Natasha Imsal tai wacca takai hannu ta riƙe nata irin karta tafi ta barta ɗinnan kwalla taf idonta, sosai tausayinta ya cika zuciyar Imsal ta juyo a marairaice take faɗin
"ayyah blood kaga tanaso ta zauna dani Please kabari se gobe se muje mubiyu, kafinnan ta warke"
ta faɗa tana kallon Natasha datai saurin girgiza kai wani strict look ya bata da batasan sanda ta raba hannunta da na Natasha ba tana faɗin
"bari naje na shirya,"
tai gaba tanajin yadda Natasha ta fashe mishi da kuka tana kiran sunan
"yah Imsal"
itama tana fita kukan ta saka saboda tana mugun ƙaunar yar uwarta batason taga kowace irin damuwa atare da ita.
shikam strictly yace ma Natasha tamai shiru ko ya tashi ya lallasa ta, na dama ce fal acikinta na ƙaryar data sakeyi akaro na ba adadi yanzun da batai karyar rashin lafiya ba intaje atleast duk abinda za'a ma Imsal zata iya shigar mata gata ga mubeena insuka zama team they can defeat lila and latifa amman me ƙaryar ta ta ƙara jefa Imsal cikin wani haɗarin.
Imsal sharp sharp tayi wanka ta fito se alokacin tai sallar azahar, tanajin kamar ta aikata wani zunubi mai girma don bata saba yin sallah ba akan lokaci ba yau ciwan Natasha ya sha kanta, tana idarwa batai zaman yin dogon karatu ba tai addu'a ya wanci wa Natasha Allah ya bata lafiya ta shirya ta zura hijab ɗinta ta dakko jakarta har zata ɗau wayarta se kuma ta fasa ta mayar ta ajje tafito zuwa ɗakin Natasha riƙe da nikab ɗinta ahannu Natasha har barci ya ɗauketa da taci kukan zucinta ta ƙoshi.
Rayyan na ɗakin har lokacin don haka yake da muguwar kula akansu duk wanda yake ciwo cikinsu baya iya motsawa daga kusa dashi duk da faɗa da rashin shiri dake tsakaninsa da Natashan amman shima yana mugun ƙaunar yar uwarsa,
"yaya natafi"
tafaɗa ahankali sanda ta leƙa dakin ganin Natasha na barci ɗaga mata hannu yayi ta juya ta nufi hanyar stairs Hajiya na falon har lokacin ta kalli lokaci tana fadin
"kinfa makara,
aina ɗauka yau jinya zakiyi bazaki jeba," turo baki tai cikeda ƙunci take faɗin
"ba yaya bane yacemin se naje,"
tace
"yamin daidai ai saboda yadda kike rudewa in yarinyar nan bata da lafiya ko A'isha uwar data haifeta batayi,"
Imsal bata kula taba jin magana take nema tace mata
"sena dawo,"
Ta amsa da
"Allah ya kiyaye hanya,"
Garba yana nan bakin gate yana jiran tsammani shima kansa ya ɗauka baza taje ɗinba amman jin ba'a sallameshi ba tukunna yasa ya jira zuwa huɗu inbata fito ba ya ƙwanƙwasa ya tambaya ganin tafito yataho yana shiga napep ɗin yana tambayar ta
"ya me jiki?"
tace mishi
" da sauki"
yace
"Allah yaƙara sauki,"
Ta amsa da
"Ameen"
ya buga adaidaitar, Malam haruna ya bude gate yana musu adawo lafiya suka fice se bin suhail, gaba ɗaya yau ba walwala a tareda Imsal har ya sauketa akofar makarantar.
tun daga waje ta gane anfito sallah lokacin haka tai shige warta.
A bakin ƙaramar ƙofar shiga ɓangaren ajujuwa ta tarar da prefects na tarar makara, rabinsu duk yan ajinsu ne ta gane fuskokinsu se wasu da bata sansu ba, latifa na zaune saman wata plastic chair tana hura hanci yadda kikasan itace mai makarantar haka take ji dakanta duk ɗalibin da yazo wucewa seya gaidata kasancewarta yar babban aji kuma prefect.
lila na hango Imsal da tafiyar ta da jakarta ta gane ta tai saurin ƙarasawa bakin ƙofar tana faɗin
"Malama kin makara,"
Imsal taja gefe ta tsaya don ita bata taɓa makara ba hakanne yasa batasan ma ana tarar makara ba, yarinyar da tai mata magana tare da mubeena jiya ce ta ƙaraso itama tana cikinsu take faɗin
"a'ah mai niƙab ya akai yau kika makara,"
jin tai mata magana asanyaye yasa tace mata
"wani uzurine ya tare ta yar uwartace bata da lafiya shiyasa,"
yarinyar ta kalli lila tana faɗin
"kinga bata makara kuma sabuwa ce mu barta tawuce koh?"
wani irin kallon banza lila tai mata tana faɗin
"bar ganin kece head girl wallahi baki isa aiwa wannan alfarma tawuce ba,
watafi da kowa zezo yayi aiki ita taƙiyi," yarinyar tace
"lila naji batafi kowa ba amman ai wannan ne karonta na farko,
Please let her go,"
Lila ta riƙe kugu tana faɗin
"in an isa in mutu,"
Imsal na jinsu ko ci kanku batace musu ba latifa dake zaune jira take taji imsal ta fara pleading ita kuma ta taso ta yarfata amman jin lila da nana yarinyar dake kare Imsal se cece kuce suke gudun kada attention ɗin malamai ya dawo kansu latifa ta miƙe tana faɗin
"enough"
takalli Imsal kafin tace
"ke ai laifinki biyu ne,
jiya ya Sheikh yace zakuyi aiki shine wato kikace bari ki makara don kizo sanda angama komai ko,
toh wallahi bazaki ci bulus ba don haka yanzun bari a idar da Sallah kece zaki share gaba ɗaya compound ɗin da aka ɓata,"
se alokacin Imsal ta ɗago tama kalleta ta cikin niƙab ɗinta,
"aikin ki na makara kuma ki biyoni muje," takalli sauran da aka tare makarar tace "kuma ku biyo ni"
Imsal bata musa ba don ba tasan tashin hankali kwata-kwata tabi bayansu, banɗakin yara ta jasu da yaran suka riga sukai kaca-kaca dashi tace
"kowacce ta wanke ɗaya acikinsu"
ba tareda kyankyamin komai ba Imsal takarbi detergent da disinfectant ɗin da aka bayar ta shiga toilet na biyu tafara wanke wa kuma har lokacin da niƙab dinta afuskarta ta dai tattare hijabinta sauran ma suka farayi.
Latifa ce ta kalli lila itama ta kalle ta, se ta fice abanɗakin imsal ta kusa kammala wankin banɗakin kawai taji an buɗe juyawa tai dan ganin waye ze shigo kawai taji saukar ruwan sanyi ajikinta shaaaa ankwaro mata a bucket tun daga samanta har zuwa ƙasanta,
dariya gurin ya kaure da, ta rintse ido tanajin danshin yadda ruwan ya jiƙa mata niƙab da kayanta duka, muryar lila taji tana faɗin
"this serves you right"
ashe bucket biyu tazo dasu kafin imsal tayi yunkurin yin wani abu ta ƙara ɗaga na biyu ta shara mata wannan karon har cikin gashinta take jin ruwan yana shigewa, tsabar ta kaici batasan lokacin data durƙushe agurin ta fashe da kuka ba, sanyin yana ratsa har cikin ƙashinta.
Its fatoumspassion IMSAL
Don't forget to
Share
Like
Comment
Vote
SPECIAL ANNOUNCEMENT
Ina farin cikin sanar muku cewa zan fara posting sabon novel dina IMSAAL a ArewaPen da Wattpad 🤍
But don’t worry… WhatsApp readers are still my priority 🫶🏽
Nothing is changing here, this is still home ❤️
To celebrate this, I have something special for my real supporters
🎁 The FIRST 20 PEOPLE to:
✔ Follow me on ArewaPen
✔ Follow me on Wattpad
Will get FREE entry into my paid WhatsApp group 💫
🎁 HOW TO QUALIFY 🎁
After following me,
📌 Take a screenshot showing you’re following me on BOTH platforms
Then send it to me on WhatsApp 👇
📩 ***
⚠️ Include your username
⚠️ Only the first 20 valid people will be accepted
⚠️ No screenshot = no entry 👀
ArewaPen @fatoumspassion
Wattpad @fatoumspassion
Hurry… once the 20 slots are gone, that’s all 🔥