FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
They say everyone has a story, but I’ve made it my passion to tell them. I write because I believe stories are the bridges that connect us all. Whether it's a whisper of romance or the weight of a life-changing choice, I pour everything into the tales I tell here on ArewaPen. I'm...
Sample · Her Uniqueness
*** FATOUMSPASSIONS*#UniqueOneOfAKind#NotYourTypicalLoveStory#HalalLoveStory#FamilyDrama #PowerAndPolitics#ControlVsFreedom#DarkMeetsLight#TestOfFaith#GoodGirlBadBoySAVE MY NUMBER ***LET'S HAVE EACH OTHERS CONTACTS.OR DM ME DIRECTLY THROUGH THE ABOVE NUMBER.***@fatoumspassionINSTAGRAM@fatoumspassionTIKTOK@fatoumspassion*IMSAAL* *(Unique, one of a kind)*It's fatoumspassions IMSAAL another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM, INTENSE LOVE AND EHSAAS.Free pages بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِChapter1(Her uniqueness)Ahankali nake jiyo tashin muryar zazzaƙar ƙira'ar Al ƙur'ani mai girma da take tashi daga wani ɗaki wanda ke can ƙarshen corridor din jerin ɗakunan gidan,"Masha Allah"Na furta acikin zuciya ni fatima domin kuwa karatune wanda ke ratsa zuciyar duk wani mai sauraronsa, inda take karanta suratul ƙasas tabbas duk inda wannan murya take nasan za'ai haziƙa ma'abociyar karanta wannan littafi mai girma a koda yaushe.Sosai abin ya shigeni na leƙa don ganin me karatun tana zaune aƙasan purple colour carpet dake shimfiɗe adaƙin, ga mamakina ba ƙur'ani a hannunta, amma ko ɓatan wasali batayi ga tajwidi daya zauna abakin ta kamar wata balarabiyar masar.kaya ne azube aƙasa inda wasu ta ninkesu ta ajje saman gado wasu kuma tana kan ninkewar, nayi mamaki kwarai da gaske ganin aikin tama take tana karatunta.Ahankali take ninkin tana ƙara sautin muryar karatun cikin nutsuwa wacca da gani tagama zama a jinin jikinta, bude ƙofar dakinta na jiyo anayi,Na juya ina jiran ganin wanda ze shigo, wata dattijuwar tsohuwa ce tashigo fara tas kana ganinta kaga ba fullatana, fuskarta dauke da murmushi kamar wacca aka mata kyauta da kujerar Hajj, tashiga kallon yarinyar wacca har yanzun bayan ta ajuye yake amman jin tura ƙofar da tsohuwar tai yasa ta juyo fuskarta dauke da ƙayataccen murmushi tana kallonta,"tabarakallah Masha Allah"Na furta lokacin da nakalli kyakkyawar Farar fuskarta tana dauke da wani irin gigitaccen kyawu mai ƙaya tarda me kallo, zan iya cewa ko a irin fina finan india da larabawa da nake kalla bantaba cin karo da fitinannen kyau da hasken fata irin na wannan yarinya ba.har yanzun murmushi take tana kallon matar da dara daran Bluish green eyes dinta tana jiran jin me hajiyan tasu zata ce mata don tasan tunda tashigo dakinta ashirye haka ta ta cakara dauri haka ƙila fita zatai akwai abinda take son faɗa mata"GWANA IMSAL afwan na katse miki muraji'arki ko?"Hjy ta faɗa tana gyara zaman babban gelenta wanda fallen atamfar da yake jikinta ne guda.girgixa kai tai tana ajje kayan data ninke saman bed tace "hjy ainama kai ƙarshe yanzun zan kammala,"murmushi ta sake yi tace "gwana imsal toh asamu addu'a,"rufe fuska Im...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.