Namiji Ƙanin Ajali (Book 01)

Chapter --- 07

by @amdeeytejjdunique587

Bismillahir Rahmanir Rahim

        ***Namiji Ƙarin Ajali***

                            By

                   Amdy Tejj

Page 07.

Sauke ajiyar zuciya nayi sannan nace"wlh bakomai nake tunani ba sai lamarin ciwon Hajja,abin yana damuna gashi mu ba kuɗi ba,ba dan kada nayi saɓo ba da nace shima ciwon bai san inda ya kamata yaje ba,amma nasan komai jarabawa ce daga Allah sai dai fatan Allah ya bamu ikon ci"

"Hmmm yaya Haula kenan, kamar yadda kika faɗa ne wannan jarabawa ce kuma Allah ya bamu ikon ci,ta bakin mai waƙa ne yace inda yafi siriri nan yake tsinkewa, amma ya batun wanda yace zai taimaka ɗin?"ta tambaya bayan takai ƙarshen maganar tata.

"Ki bari kawai kinsan wasu masu kuɗin nan idan zasu taimake ka sun dinga maka walaƙanci kenan,bai daɗe da dawowa ba wai bai samu ganinshi ba,wai ance yana meeting,Ni ' na fara zargin ja mana rai kawai yakeyi"nayi mata ƙarya a zuciyata kuwa cewa nayi “da kinsan ƙudirin wannan bawa da bakiyi maganarsa ba”kuma nayi mata ƙarya kawai saboda bakomai ne za'a dinga bayyanawa kowa ba akwai abin da yake buƙatar sirri, musamman tsakanin mata da miji.

Na cigaba da faɗin"amma mun yanke wani shawara ni da shi"nan na gaya mata yadda mukayi.

Murmushi tayi sannan tace"gaskiya yaya Haula muna godiya da kulawar ki ga mahaifiyarmu, duk da abinda take miki amma hakan bai sa kinƙi nuna kulawarki a gareta ba".

"Dan Allah ki daina wannan maganar Hajja ai mahaifiyata ce kuma dama su iyaye haƙuri akeyi dasu akoda yaushe dan a rabu lafiya,dan Allah kada ki sake wannan zance"na faɗa dan duk da ƙiyayyar da Hajja take nuna min ban damu ba ni kawai ɗanta nakeso kuma tunda shima yana sona shikenan.

"Ai kin cancanci hakanne dan wlh ni bazan iya irin nakin nan ba,yauwa batun neman sabil ɗin nan kuma sai nake ganin me zai hana a haɗa da masallatai a raba takardun neman taimako''

''Eh kuma haka ne fa kema kin kawo shawara,dan wlh tunanina sam ba kai haka ba"na amsata

"To ya batun yara?'' ta tambaya

"Yara zasu zauna a gidan Garba kafin mu dawo"na bata amsa

Ta kalleni kafin tace"amma dai kinsan matar yaya Garba bata sonki ko, kuma akan idonki ma bata barsu ba balle bakya nan, kuma ace ita zata yi musu hidima,kema kinsan dai wuya zasu sha"ta ƙarashe maganar rai a ɓace da alama dai halin matar yayan nata baya mata daɗi, koda duk wanda ya santa yasan ba mace ce mai daɗin zama bace,ga makirci da kisisina shiyasa take da fada a wajen Hajja, kuma nima nasan ba ƙaunata take ba amma ba yadda zanyi tunda bazan ɗauki yara muje yawon bara ba, kuma anan nidai bani da ƴan uwa balle inkaisu,amma nasan shi bazai rasa ba, Kallon Rabi'ah nayi sannan nace.

"Ba yadda zanyi ne Rabi, kuma Allah na tare dasu idan taci amanar su ita da Allah,nidai ga amanar ƴaƴana na bata''kafin ina ƙarasa ta katse ni da faɗin.

''Ni ki barmin su zan kula dasu har ki dawo''

Na kalleta nasan ƙarfin hali kawai yasa tace haka amma itama fama takeyi da kanta tunda mijinta shima ba  ƙarfi yake dashi ba sai godiyar Allah,zan so ace yaran su zauna a gunta amma dai, maganarta ta katse min tunani kafin na kai ƙarshe.

"Ko baki ji ba?, wallahi na miki alqawarin riƙe miki su amana har ki dawo"

"Bawai naƙi bane Rabi'ah kema fama kikeyi da kanki kuma shima mijin naki buga-buga kawai yake yi ba ƙarfi yake dashi ba,gaku ga yaranku,ga mahaifiyarshi ga ƙannen sa mata su biyu duk shi kaɗai,yanzu kuma mu tattara yara har uku mu ƙara masa haba,muyi tunani da hankali mana Rabi"

"Wlh yaya Haula kada ki damu da wannan Rabi'u bashi da damuwa,dan kai su Jidda gida kafin ku dawo, kuma na miki alqawarin ko garin ƙasa na kwaɓa naci haka suma zan basu suma su ci"

Murmushi na ɗan yi sannan nace"Nagode sosai Rabi Allah ya bar ƙauna"na faɗa cike da farin ciki dan naji daɗi sosai ko ba komai bani da fargaban halin da yara na ke ciki,dan idan akwai mai sona tsakani da Allah a dangin Habibu to bayan Rabi'ah ne.

"Meye na wani godiya, ba ƴaƴana bane, kuma ko bani da alaƙa dake ai ko dan abin kikayiwa mahaifiyarmu kin can-canci fiye da haka".

Ɗan murmushi kurum nayi,daga haka muka cigaba da tattauna yadda tafiyar zata kasance na haɗa kayana waɗanda zan tafi dasu dana yara wanda Rabi zata tafi dasu dan sammako zamuyi gobe, inayi ina tuna Habibu dan nasan ba a son ranshi za ayi tafiyar nan ba,ni na rasa Habibu ya daina kishi nane koyaya,amma inayi mishi uzuri dan akan mahaifiyarshi ake magana, uwa kuma tafi gaban wasa...


Halima....

Rayuwa ta miƙa abubuwa sai faruwa suke,halin Bature kam sai abin da yake ƙaruwa kullum da samfurin da zai fito dashi zuwa yanzu dama na daɗe daina mamakinshi,Lubna ta dawo kamar yadda tace har so biyu kuma nima naje, itama ta koma kuma har ta koma maman jummai bata san yaji tayi ba kusan zance ma bayan ni ba wanda yasan dalilin zuwan nata,umma taji sauƙi duk da baza ace ta warke gaba ɗaya ba amma da sauƙi sai hamdala,ina zuwa in dubata akai-akai,a wannan hali na cuccuɗa nasa Layla a makaranta, makarantar da na cewa Bature ko da biyar da goma ne mu dinga sawa a asusu ko adashen Lantana wata matar gidanmu amma saidai kullum yace babu, wanda nidai zuwa yanzu nayi amanna da cewa babu ya riga ya auri Bature,dan kullum shi a bashi dashi yake,haka na ƙuƙuta na haɗa na sata a makarantar da har daidai da biscuit bai taɓa siya ya bata dan tayi break ba.

Zaune nake a bakin ƙofa ta na jiyo karaɗin Ladiyo,Hmmmm ban baku labarin Ladiyo ba ko,koda yake idan nace sai na baku labarin kowa na gidan nan namu ne wallahi labarin zai ƙare a iya gidan ba muje ko ina ba,dan wallahi wani irin bahagon gidane mai ɗauke da mutane daban-daban iri da kala iya kallonka, sai dai abin ya samu in tsakura muku, Ladiyo dai  wata mata ce a gidan wacce duk anguwan aka santa da makirci,tuggu,kilibibi da kisisina da munafurci ba wanda ba a bata  certificate akai ba.

Ji nayi tana faɗin "Ai wallahi ni dashen Allah ce,badai mutum ba wallahi sai dai mai sama"

Da yake ata gun ɗakin Lantana take wuf ta fito, Hassana uwar tsurku kan kace kobo har ta isa wajen,inaji har suna haɗa baki wajen tambayar "me ya faru?".

"Har ni za a gwadamin ƴan uwantaka,ai ni wanda yaci tuwo dani miya yasha,har ni za a kawowa wani feleƙe da iskanci"

"Wai me ya faru ne kike ta maganar da bamu gane kanshi ba,mu inza ki gaya mana magana ki gaya mana ni bana son magana da kwana-kwana?''na jiyo muryar Hassana ta faɗa da alama ta ƙagu da son jin labarin.

"Ke ki shiga hankalinki uwar munafikai,na kira ki ne?"Ladiyon ta faɗa a hassale da alama zata iya sauke bala'inta akan Hassanar,to da yake ko shege ma da ubansa sai  Hassanar tayi shiru, kuma dayake tana son jin zance ko dan ta ɗorara a gaba,da yadda akayi da yanda ba ayi ba duk tayi mai ado tace anyi, sai tayi shiru,dan na tabbata wallahi da wani yau ya yiwa Hassana wannan zagin da akwai bala'in da Allah kaɗai yasan sanda zai ƙare, muryar Lantana na jiyo tana faɗin

"Daɗi na dake Hassana wutar ciki bakya cin ribar  zance sam,muna jinki Ladiyo"

Ga mamakina sai naji Hassana tace"auuuw hakane nayi shiru,gaba Allah yace".

Taso ban dariya amma sai nayi murmushi

"Yauwa ko kefa muna jinki Ladi"Lantana ta faɗan.

Ita kuwa Ladiyo kamar dama  pause aka danna mata,ko mai karatun da yasa alama ta cigaba daga inda ta tsaya bayan tayi ƙwafa......

To ku daka ce ni anan....

Mu haɗu a next page sai kun jini..

Nagode 🙏🙏🙏

See you next time👀