17
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*17*
Sanye yake da wani baƙin yadi mara kauri domin in ka ƙura ido sosai za ka iya hango farar vest ɗin dake jikin shi ta ciki.
Ɗinkin zamani ne amma rigar ta kai har wajen gwiwan ƙafafunsa, kansa da hula amma saboda ya tara suma sai hulan ta samu matsugguni a saman gashin kan nashi, sannan gefe da gefen fuskar shi sumar ta ɗan bayyana.
Ummu ta yi saurin kauda kanta, shi da man bai nuna ma ya ganta ba, Beena ce ke yi masa raɗa a kunne yana sauraranta.
Ummu ta so ta yi sauri ta koma ɗakinta ne amma ina ta juya za ta shige kenan kawai ta ji Hamma Abdullahi ya kira ta.
"Ummu"
Ta juyo tana kallon shi.
"Ba ki ga Lamiɗo ba ne? Na ji ba ki gaishe shi ba ne"
Ummu ta runtse ido tana cije baki Hamma Abdullahi ya kwafsa mata, ita fa ba ta so ma ya ganta ba, ballatana ma har gaisuwa ya haɗa su ita a fatan ta ma har su gama zaman garin su koma ma ba za su haɗu ba sai ga shi tun a ranar farko Allah bai cika mata wannan manufar ba
"Sannu da zuwa Hamma, in yini?
Ta faɗa daga in da take tsaye.
Amma Hamma Lamiɗo ya yi kamar bai ji ta ba.
Da man halinsa ne ko a baya sai ka yi ta gaishe shi yana ji ya yi kamar bai ji ba in kuma ya amsa to a gajarce ne.
"Anan kuma! Ƙariso ciki wataƙila bai ma ji ki ba."
Hamma Abdullahi ya sake faɗa. Kamar Ummu ta fashe da kuka har hawaye sun kawo mata cikin kwarmin idanuwanta.
Haka nan jikinta a sanyaye ta ƙariso tsakiyar falon ta ɗan rankwafa daga gefe jikin kujera
"Ina yini Hamma".
Ta faɗa cikin rawan murya.
"Fatan an zo lafiya?
Ta sake faɗa kanta na ƙasa.
Nan ma shuru ya yi kamar bai ji ba sai da Hamma Abdullahi ya ce ana gaishe shi sannan ya ɗago yana kallon shi, Ummu ya nuna masa yana faɗin" Autar Ammah ke gaishe ka."
Kanta na ƙasa ba ta ɗago ba, saboda haka ba ta san ko ya kalleta ba ta ji dai ya amsa da lafiya da muryansa nan na shi a ginshiƙe kamar ba zai yi magana ba.
Zumbur ta miƙe ta bar falon har tana harɗewa da hijabin jikinta sai da ta ɗan laɓe daga can korido tana so ta ji ko zai tambaya me ya sa ya ganta a gida? Duk da ta san ba zai taɓa tambaya ba. Bai yi magana ba suma su Hamma Abdullahi ba su yi masa maganar ba sai ma suka shiga wata hirar ta dabam hakimin yana zaune yana sauraransu yana amsa musu ɗaya bayan ɗaya a ginshike cike da kasaita. Ita dai tunda ta shige ɗakinta ba ta sake fitowa ba, ana yin sallar isha'i ta tashi ta yi Adda Suwaiba ta ɗauko mata ruwa ta sha magungunnan ta, ƙila akwai na barci ne a ciki nan da nan barci ya ɗauketa. Cikin barci sama-sama ta ji Baffa ya shigo duba ta, ba ma za ta iya tuna me ta ce masa ba, shi dai ta tuna yana ce mata Auta ya jikin naki? Daga nan sai asuba ta iya farkawa shima wasu masallatan sun sallame salla.
Gidan shuru ashe tun jiya da daddare da baƙin da suka zo da yan gidan duk sun tafi gidajen su.
Da safen ma Ammah ta yi abin ƙari Hamma Abdullahi ya zo ya ɗauka bayan shi ma Adda Ummu Sulaim ta yo, sannan haka ma Adda Suwaiba ta kawo duka ya haɗa ya tafi da shi gidan Hamma Lamiɗo dake Jambutu haske.
**
*Jambtutu Haske*
Gidan Hamma Lamiɗo babban gida ne, mai ɗauke bangare biyu manya manya. Ɗayan bangaren an gyara shi amma babu kayan amfanin yau da kullum yana ma rufe ne ɗayan bangaren ne suke sauka in har sun zo garin. Kayattacen gida ne mai kyau wanda ya dace da zamani
Ko da Hamma Abdullahi ya kai musu abin ƙari ya daɗe yana knooking ɗin gidan ba a zo an ɓude ba. Kuma ya yi ta kiran wayar Lamiɗo tana shiga amma ba a ɗagawa.
Har ya yi niyyar juyawa sai ga Sabuwa ta zo ta buɗe gidan ganin shi ne yasa ta rankwafa tana gaishe shi ya amsa lokaci ɗaya yana miƙa mata kwandunan dake hannunsa masu ɗauke da abincin ta karɓa tana yi masa godiya.
"Uwardakina da Ranka shi daɗe ba su tashi ba."
Ta faɗa tana kallon Hamma Abdullahi
Agogon fatan dake tsitsiyan hannun shi na hagu ya kalla ƙarfe 9:50am da man ya yi tunanin haka su ai yan Lagos ne ba sa buƙatar tashi da wuri ba irin su da sukan fita ƙwadago da sassafe ba.
"Ba matsala in sun tashi ga saƙo nan daga Ammah."
"Allah ya saka da alheri. Madalla mun gode."
Sabuwa ta faɗa sannan suka yi sallama ya wuce zuwa motarsa ita kuma ta rufe gidan ta koma cikin gidan
Duk wanda ya san matar Lamiɗo ya san ta da amintattaciyar hadimanta Sabuwa tunda duk in da ta saka kafa nan itama take sakawa shi ya sa kowa ya san ta a bangaren Ammah itama tas tasan kowa, haka ma Anitha mai kula da su Sultan duk in tafiya ta kama Balkisu ko na kwana ɗaya ne in dai tare da yara za ta yi tafiyar Anitha na tare da ita saboda kula da yaran shi ya sa itama ta san kowa kamar yadda kowa ma in ya ganta ya san amfaninta ba sai ya yi magana ko tambaya ba
Hidiya da Debora kaɗai da su James ake bari a gida.
Hidiya ana tafiya da ita amma sai in Bilkisu za ta je kano haka ganin gida ko kuma in za su je Daura amma yawan cin tafiye-tafiyenta ta fi yin su tare da Sabuwa da Anitha.
Kitchen Sabuwa ta kai kwandunan abincin tunda masu gidan ba su tashi ba sai sha biyu na rana su da ƴaƴan su. Sai da suka yi wanka suka shirya sannan Sabuwa ta jera musu abin karin a saman dinning
Akwai ruwan zafi da kayan tea sannan akwai kunin ɠyaɗa da soyayyen fanke wannan na Ammah ne, sai soyayyan ƙwai da daffaffe, sai soyayyar indomie, na gidan Hamma Abdullahi kenan na gidan Hamma Abdulrrahaman kuma soyyayar doya ce da ƙwai da plantain sai ruwan zafi, Bilkisu ta ba da umarnin Sabuwa ta ɗibar musu ita da Anitha tunda abincin ya yi musu yawa.
Ita dai tea ta sha da soyayyan doya yaran kuma sun ci ƙwai da plantain Lamiɗo kuma kunun ɠyadan shi ya sha da fanke, har wani jin daɗi yake yi domin ya yi kewar abincinka Ammah na'u'i masu daɗi, ta san yana so shi ya sa ta yi masa, shi fa har gobe yana faɗa babu wacce ta san shi dari bisa ɗari irin Ammah, ko bai yi magana ba ta san abin da ya fi so da wanda ba ya so.
Sai da suka gama karyawa sannan suka koma cikin ɗakin barcin su, yaran kuma Anitha ta ja su falo ta kunna musu tibi suna kallon cartoon aka bar Sabuwa da gyara in da suka ci abincin.
Tunda suka koma cikin ɗakin barcin su, magana ko ta fatar baki ba ta sake shiga tsakanin miji da matan ba, shi yana zaune a wata kujera kwara ɗaya dake cikin bedroom ɗin ita kuma tana kishiɠide a gefen gado tana duba wayarta shi ma ɗin ya duba wayar tasa har ya ga Abdullahi ya yi ta kiran shi amma bai bi bayan kiran ba.
Kansa kawai ya ɗan jinginar a jikin kujeran ya ɗan yi balance kafafunsa na lumshe a cikin tattausan cafet ɗin da ke cikin dakin barcin.
Idanuwansa na lumshe kamar mai barci sai dai ba barcin yake yi ba, a halin shi ko awa uku zai iya yi a haka ba tare da ya gaji ba shi dai kawai yana son shuru fiye da komai a rayuwarsa.
Sanye yake da riga da wando bakake, rigar mai gajerun hannu ne tana da ɗan taushi sai wandon iyakarsa gwiwan kafarsa, gargasan da ke kafafun nashi duk sun bayyana a waje.
Kansa ba hula sumar kan ta kwanta haka gemunsa da sajensa, Balkisu ta ajiye wayarta kawai tana kallon mijinta tana mai jin wani alfahari.
Da farko ta ɗauka tara gemu da saje ba na manyan mutane ba ne ta ɗauka na talakawa ne irin uztazan nan sai da ta haɗu da Lamiɗo ta san tara gemu ma baiwa ne da ƙasaita saboda shi ya sa take son gemu da saje. Kuma itama ta fahimci yana so, wai a haka ma yana ragewa in yana wajen aiki in suka yi video call gashi duk ya cika masa fuska sai ta ce ranka ya daɗe ya kamata a yi aski kai kawai yake ɗaga mata baya magana, tana so ta riƙa rage masa amma baya barin ta, sau ɗaya ya taɓa bari ta rage masa shima ita ce ta matsa daga ranar kuma ko ta ce za ta ce za ta yi masa sai ya ce a'a. Ita da ta so har private part ɗin sa ta dinga masa sheving amma ina ta san ba zai taɓa aminta ba.
Ko fa kaya ta saka in dai jikinta ya bayyana ba ya son kallonta sai ya dinga wani kauda kai in ta matsa kuma sai ya runtse ido yana faɗin
Ki je ki sauya kayan jikin ki mana"
Yau ma wata riga ce a jikinta mai santsi tana da yar ciki da jaket. Da za su fita beakfast sai ta saka jaket din suna dawowa ɗaki ta cire ta zauna daga ita sai ta cikin mara hannu ta ɗan kamata amma tana da ɗan tsawo tunda ta kai wajen gwiwan kafafunta, kanta kuma da man mayafi ne ta saka ta yi rolling shima tuni ta cire, ta bar suman kan nata da ya sha gyara sai ƙamshi yake yi yana ƙyalli.
Mirmishi take yi ita kaɗai tana tuna daran jiya. Ba ta ɗauka zai kula ta ba, ganin sun yini gidan Ammah kuma ga gajiyan tafiya amma suna yin shirin barci ta shige jikinsa ta lafe masa tana sauke numfashi ya birkice mata, in ta tuna irin yadda ya yi mata rawan jiki sai ta ji wani irin daɗi ya kamata. A baya kafin ta fahimce shi sai ta yi ta kuka tana tunanin ko ita mijinta baya jin daɗin ta ne ? Mata da yawa ƙawayenta ƴaƴan sarakuna da abokan karatunta masu aure suna irin hiran yadda ko gyara suka yi irin yadda mazajensu ke ruɗewa har da waɗanda ake yi ma kuka da ihu, amma ita mijinta bai taɓa mata ko sambatu ba, kuma in zai dawo haka za ta yi ta shiri ta gyara ciki da waje, daga can Kano Umma me aiko mata da kayan gyara da yawa ta yi ta sha ammah in ya dawo suka kaɗaice ba ta ganin wani canji. Sai da ta ga wani rubutun wani likitan kan maza yana bayani kan kashe kashe da rukunin maza da ta bi rubutun sa anan ne ta gano mijinta a cikin rukunin maza.
Namijin da ba ya iya bayyana ƙololuwar jin daɗinsa ko da daɗin zai kashe shi ne, amma zai yi rawan jiki sannan zuciyarsa za ta tsananta bugu sannan zai ta yin zufa amma ba wai ya yi kuka ko sambatu ko wata alama ba, daga lokacin ta samu salama tunda ta fahimci duk yana yin haka kawai dai sambatu ne da ihu ba ya yi, jiya ma da ta tafiyar da ragamar ya yi ta mata nishi kamar numfashinsa zai kwace daga ƙirjinsa. Shi dai in har wajen zai yi duhu to zai iya sakin jiki a yi komai sai bayan sun natsa ne in haske ya gauraye ɗakin ya yi kamar ba shi ba, kai tana son Lamiɗo domin ta san ta yi ma sauran mata zarra samun namiji mai kama da maza ɗari a waje ɗaya.
Tana so su dinga zama suna hira duk da itama ba ta da surutu amma tana so ta ga tana yi masa hira ko ba zai yi magana ba ya yi ta kallonta da yanayin kallon shi mai narkan mata da zuciya.
Amma matsalan itama ba ta iya hiran ba, da ta fara sai ta rasa me za ta ce, in dai ba hiran can Daura ba shima sama sama, har gwara ma in tana yi masa hiran Ammah har mirmishi za ta ga yana yi mata sannan in ta yi tambaya yana bata amsa jefi-jefi. Ta daɗe da shaida cewa Lamiɗo na kaunar Ammah ninki da yadda yake son mahaifiyarsa Mami ita kuma kowa ya shaida yadda take ƙaunarsa, shi ya sa itama kamar ta lasheta saboda ita ɗin Matar Lamiɗo ce, tana gani in ta je matan su Hamma Abdulrrahaman Ammah ba ta yi ta kan su, amma ita da yaranta da jikinta da komai take yi musu wahala. Da farkon auren su ba ta san dawan garin ba duk da ta san a hannun Uncle ɗin sa ya taso yayan mahaifiyarsa. Ta ɗauka mahaifiyarsa na da tasiri a rayuwarsa sai daga baya ta fahimci komai domin lamarin ma a bayyane yake. Mami da Lamiɗo in suka haɗu ban da gaisuwa ba abinda ke sake haɗa su, a waya ko sai su yi sama da wata ba su yi magana ba in ba wani abu ba ne ya taso ya kirata ba. Musamman ma dai ya fi kiranta ya gaisheta in su Islam na gida ya ce a ba su wayar shi dai yana da son yara duk da baya son hayaniya. Wayar ma da yake yi mata Ammah ce ta ce ya riƙa kiranta yana gaisheta mahaifiyarsa ce, amma mijinta Alhaji Isa akwai girmamawa mai girma a tsakanin shi da Lamiɗo shi har ya fi Mami ma jawo shi a jiki amma ita kamar ba ɗan ta ba, ko da yake da man ta ce ba ɗanta ba ne ɗan Ammah ne.
Da fari har ita tana kira ta gaisheta lokaci bayan lokaci ranar dai Mami ta faɗa mata gaskiya da cewa in za ta yi kamun kafa ne ta je ta kama kafar Ammah ita uwar Lamido ce kawai a haihuwa amma nan duniya ba shi da iyayen da suka wuce masa Ammah da Baffa kuma ta ga haka, domin a wajensa shima ba shi da iyayen da suka fisu, akwai wani zuwan da suka yi Daura ta tambayi Fulani Daura ita ta zaunar da ita ta bata labarin mafarin komai ta kuma shaida mata Mami ta yanke alaqa da duk wanda ya danganci Lamiɗo da su Ammah kawai suke zumunci, kuma ta ga hakan in za su haɗu sau nawa bayan gaisuwa ba ta taɓa ganin sun yi wata magana ko da mintina goma ba ne, Mamin ma kwata kwata ba ta yi ta kansu, ko su Sultan a matsayin jikokinta ba ta taɓa ganin ta ja su jikinta ba. Tun lamarin na ba ta mamaki har yanzu daga baya ya zame mata jiki. Ta riƙe Ammah a matsayin uwar mijinta da Baffa a matsayin uban mijinta, sannan ta riƙe Maimartaba a matsayin uba sannan ta riƙe Gimbiya Shahida a matsayin uwa Fulani Daura kuma a matsayin kaka.
Mami kuma sai ta saka ta a cikin sahun wasu makusanta Lamiɗonta.
Tashi ta yi tana yanga kamar yadda ta saba ta karisa kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi, kanta ta ɗora saman kafaɗan shi tana sauke numfashi jikinta da gashin kanta suna fitar da wani sihirtattacen ƙamshi mai daɗi.
Ya ɗan motsa amma bai buɗe idanuwansa ba tun da ya san ita ce, hannunta ta tusa cikin yatsun hannunsa guda ɗaya ta jimƙe shima sai ya taya ta suka jimƙe yatsun hannunsu a tare, mirmishi ta yi har yana fidda sauti kafin ta sake lafewa daga gefen kirjinsa.
Sun fi minti goma a haka sai ita ce ma ake jin sauka da hawan numfashinta amma shi ba ko a jin motsin na shi numfashin, in za su kai gobe a haka ba zai ce mata komai ba.
Ta san shi ta san waye Lamiɗo, ko mai za ta yi ba zai taba cewa aa ba, mutum ne mai girmama zamannsu mai daraja aure da sauke haƙƙoƙi.
Ta tuna bayan haihuwan Beena ta faɗa masa ta yi planning tunda ta samu haihuwan a jere da juna, ko faɗa bai yi mata ba ko irin ya ce me ya sa ba ta faɗa masa ba. Shi ba wanda ya isa ya gane ya ji daɗi abu ko bai ji daɗi ba fuskarsa ta iya shanye komai ba ta kuma bayyana abin da ke fuskarsa. Hausawa na cewa wai labarin zuciya a tambayi fuska to shi Lamiɗo labarin zuciyarsa sai dai a tambayi bakinsa, domin komai bin kwafkwafin ka ba ka isa ka fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba.
"Ranka ya daɗe."
Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi.
Bai amsa ba kuma bai buɗe idanuwansa ba, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta san ba zai yi magana ba amma tana da tabbacin yana jin ta.
"Ashe kuma abin da ya faru da Autan Ammah kenan?
Ta faɗa lokaçi ɗaya tana ɗan wasa da gargasa hannun shi, da hannunta guda ɗaya.
Shuru na wani lokaci sannan ya buɗe idanuwansa da suka ɗan ƙanƙance sun ɗan kuma sauya launi.
Kallon shi ta yi, shima sai ya kalleta yadda ya kalletan ne ya sa ta san bai san komai ba.
"Ba ka sani ba?
Ta faɗa cikin sanyin murya lokaci ɗaya tana goga masa gashin kanta samana kirjinsa cikin wani salo.
Bai yi magana ba amma ta ga ya ɗan jinjina mata kai alamun bai sani ba.
Sa sauri ta tashi daga kan kirjinsa tana fuskanshi.
"Jiya da na ganta wani iri na tambayeta ko ba ta da lafiya ne? shi ne fa Ammah ke ba ni labari."
Ya yi mata kuri da ido yana son jin ƙarshen maganar..ita kuma sai ta yi shuru tana nazarin shi, yana so ya ce mata me Ammah ta ce? Amma kuma bakin shi ya gaza furtawa.
"Uhm labarin fa ba daɗi ga tausayi yaron nan ya zalunci Autar Ammah"
Ta faɗa tana matse hannunta cikin na shii.
Idanuwansa ya ke buɗewa a kanta, zuciyarsa har wani tsalle ta yi amma bai nuna ba, yana nan a yanayin shi tun farko.
Ita kuma Bilkisu ba ta fahimci ya matsu ya ji labarin ba sai ta cigaba da faɗin" Ta rame fa duk ta yi wani iri. Ai ka ganta ko?
Ta gama faɗa da sigan tambaya.
Ya yi shuru kawai yana kallon ta.
"Ko ba ka gan ta ba?
Ta sake tambaya tana kallon shi, sai da ta ja yatsunsa sannan ya ɗan lumshe ido ya buɗe lokaci ɗaya yana mai jinjina mata kai alamun e ya gan ta.
"To ba ka ga ta rame ba? Duk ta yi fari ashe ma da ciki ya sake ta."
Hannunta dake cikin na shi ya matse har sai da ta ɗan kalle shi lokaci ɗaya kuma ya zare hannun shi ya yi shuru ba tare da ya yi magana ba.
Bilkisu kuma ta shiga ba shi labarin da Ammah ta ba ta ganin kamar Lamiɗon ya tattara hankalin shi a kanta.
Har ta gama bai ce komai ba amma hankalinshi da natauwarshi yana kanta ya yi mata kuri yana kallonta kuma yana sauraranta.
"Ammah ta ce hankula sun tashi sun shiga damuwa amma dai yanzu da sauƙi tunda an kwarari wata biyu cikin na uku. Ummu Salman ce sai a hankali har yanzu ba ta daina yan koke koke ba.".
Ta gama ba shi labarin kuma ya saurare ta amma bai ce mata komai ba.
"Wai ko Ammah ba ta faɗa maka ba?
Ta sake tambayan shi.
Sai wannan karon ya yi magana
"Ba ta faɗa ba."
Kawai ya iya cewa sannan lokaci ɗaya ya miƙe yana kallonta kafin ya ce" zan yi wanka"
Da ga haka ya wuce ta ya fara tafiya a hankali cikin takunsa har ya shige tiolet ta bishi da kallo, ko maganar ta dame shi ne ko ba ta dame shi ba, ba za ta iya sani ba. Amnma ta yi mamakin yadda bai sani ba ko Ammah ba ta faɗa masa ba ta yi tunanin amininshi KB zai faɗa masa, ta wani fannin kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin mijin nata, ba ko da yaushe kake samunsa ba. Za ka iya tura masa saƙo sama da wattani bai gani ba, kuma sanda aka yi abun yana can wajen aiki ba lalle ya sani ba, ita dai ta tausaya ma Ummu Salma, ƙaramar yarinya ta haɗu da jarabawa, ita fa ta ga ƙokarin su Ammah yadda suka yi ma Ummu auren wuri haka a lokacin ta yi ta ce ma Lamido ta yi ƙarama da aure bai ce mata komai ba, ga shi nan ya sake ta ya wulakanta ta da ƙananun shekarunta.
Ta shi ta yi ta ɗau wayarta ta bar ɗakin domin ta san in gogan ya fito ya iske ta ba zai ji daɗin shiryawa ba, shi ya sa ta bar masa ɗakin ta koma ɗayan bedroom ɗin ta ɗan kwanta.
Shi ko bai wani daɗe ba ya fito daga wankan, sai da ya tabbatar da Balkisu ba ta ɗakin sannan ya saki jikinsa da ga shi sai towel ɗaure a kugunsa ya fito ba ya ɓata lokaci wajen shiryawa yanzu ma cikin lokaci ya shirya ya saka farar shadda gezner ɗinkin zamani riga da wando, rigar yau har ta fi sauka masa saboda yau jumma'a za su je masallaci tare da su Baffa, wani nishaɗi yake ji tun safe na tunowa da rayuwar baya amma labarin da Balkisu ta bashi ya ɗan hanashi sukuni.
Taje kansa ya yi da gemunsa da yake tunanin yau zai je gyaran fuska a rage masa gashin fuska. Turare ya fesa kaɗan saboda shi ba ya son kamshin turare ya yi masa karfi da yawa yanzu kan shi zai fara ciwo, ko Balkisu ta cika turare har kansa yake hawa in kuma ya shaƙa da yawa haka zai yini da ciwon kai, bai taɓa ce mata ta daina sawa ba, saboda shi a tunanin shi saboda abin da ba ya so shi kaɗai ba zai tauye mata haƙkinta tunda ita tana so ba.
Shi ya sa ko ba ya son abu ba ya faɗa, gani yake yi kamar son kai ne. In kuma yana son abu shima ba ya faɗa gani yake yi don shi kaɗai yana son abu kaza kamar ya shiga haƙƙi ne ya ce kowa sai ya so abinda yake so ko ya zama irin sa ba.
Sai ita Bilkisun ce da kanta ta gano ba ya son mu'amala da turaruka tunda in ya yi birthday tana siya masa a matsayin gift zai karɓa amma sai shekara ta sake zagayowa bai taɓa amfani da shi ba, uban turarukan dake ɗakin shi kamar za a buɗe shago amma baya amfani da su tun daga lokacin ta fahimci bai cika son ƙamshi ba, ita kuma gata tana son ƙamshi tana mu'amala da turare sosai in ka yi mata kyautar turare ba ta mantawa.
Ba ta daina amfani da shi ba amma in suna tare sai ta yi amfani da mai sauƙin ƙamshi, ita fa koda yaushe jikinta a cikin ƙamshi yake duk bayan wata ɗaya tana zuwa a yi mata gyaran jiki na skin care. Shi ya sa fatar ta kamar ta turawa wajen taushi da santsi sannan ba aikin da take yi, daga zuwa asibiti ta duba patients shike nan ta dawo gida ta kwanta.
Sannan gaba da baya tana cikin jin daɗin rayuwa.
Kan kujeran da ya tashi ya koma ya zauna da wayarsa a hannu ƙiran samsumg ita ce wayar da yake amfani da ita na Family, shi in ba zai yi kira ko an kira shi ba sai ta yi kwanaki bai yi amfani da ita ba, a wajen aiki kuma suna da wayoyin aiki shi ya sa.
Yana so ya tambayi wani labarin abin abin da ya faru amma ba zai iya ba.
WhatsApp ya buɗe ya shiga, 24/7 datar shi tana buɗe ne tun a can ma wajen aiki suna da wifi a Lagos ma haka. Ta kwana a kunne saƙonni su yi ta shigowa amma sai a fi wata bai duba ba. Tun ballatana in yana wajen aiki bai cika duba wayar ba.
Wasu saƙonnin ma sun fi wata biyu bai duba ba.
Ya ga saƙon Mahma tana tambayan lafiyan shi?
Giransa guda ɗaya ya sosa da hannu ɗaya yana jin nauyi , bai kyauta ba ya kamata ya kira Mahma.
Har da saƙon Maimartaba yana faɗin sun ji shuru kwana biyu ba a samun wayarsa Fulani ta damu.
Bai amsa ma wannan ba tunda lokacin da ya koma Lagos ya yi magana da su gabaɗaya.
Ƙasa ƙasa ya yi ta yi, can ne ya gano group ɗin Ammah da Baffa ya dai san an buɗe amma bai taɓa bibiya ba sai yau ya shiga ya ɗan duba saƙonni.
Ya ga Date ɗin da Hamma Jibo ya sanar da labarin da Balkisu take faɗa masa an kwarari wata biyu cikin na uku ma.
Sake sosa giran shi ya yi, haka ne ƙololuwar nuna damuwarsa, tunani yake yi ko shi ya sa daga Baffa har Ammah duk suka rame masa a ido, bai yi magana ba ne amma a zuciyarsa sai da ya ce duk sun rame amma sai ya danganta haka da ɗan daɗewar da ya yi bai gan su ba.
Fita ya yi daga group ɗin, ya je ya nemo KB da sunan shi ke a matsayin Friend a wayar Lamiɗon.
Sai ya ga ma ya yi masa mgana.
"Amini mutanen Jimeta."
Haka ya rubuta masa dubawa ya yi sai ya ga yana online.
Rubutu ya fara yi na wani lokaci kamar zai rubuta wani abu ashe kalma ɗaya ne ya rubuta.
"Amini."
Ya ɗan ja fasali kamar yana ganin sa.
"Me ya faru..?
Ya sake rubutawa ya tura masa sai kuma ya dakata kawai yana kallon wayar.
"Naam Amini ya gajiya! Ya baƙun ta?
"Me ne ya faru kuma!?
A ina?
Duk wayar na hannunsa saƙonnin suna ture juna suka shigo
Sai ya fara rubutu sai ya goge ya yi ya kai sau uku sannan ya samu ya rubuta.
"Ummu Salama."
"Me ya samu Ummun?
Hamma Kabiru ya turo masa cikin mamaki.
Haushin chart ɗin Lamiɗo yake ji magana ba magana ba ya rabata ya ɓata maka lokaci.
Kawai sai ya kira shi Video call kamar ba zai ɗauka ba sai dai ya ɗaga kiran.
Hamma Kabiru ya bayyana a cikin lap na asibitinsu yana sanye da suit da farar rigar lapcot ɗin sa. A jikin lapcop din an rubuta sunan shi..
Kabiru Hadi Baba.
"Amini wai me ya faru da Ummun ne?
Ya faɗa yana kallonsa, shuru ya yi masa yana kallonsa sanin halin shi ya sa ya ce" Wai ko maganar abin da ya faru da sakinta da ɗan iskan yaron nan ya yi?
Sai da ya ɗan lumshe idanuwansa sannan ya ɗan gyaɗa masa.
"Kai ai an kwana biyu Amini, lokacin kana can wajen aiki shi ya sa ban faɗa maka."
Nan shima ya shiga sanar da shi duk abin da ya faru
"Amini na so Baffa ya cire hannunsa mu kai yaron nan kotu amma kasan dai halin Baffa, Ammah ma ta goya masa baya. Ya sako yarinya ga shi ya barta da wahalan ciki tunda ya sake ta an ce ba ta kara lafiya ba, kullum kuka da rashin cin abinci, ita a damuwa su Baffa ma cikin damuwa. Amini da a ce su Baffa sun matsa ma Ummu Salma ta cigaba da karatunta da yanzu duk wannan abubuwan da suka faru wallahi ba su faru ba."
Ya karishe faɗa yana jin haushi in ya tuna cin mutumcin da Habib ya yi musu.
Shuru kawai Lamiɗo ya yi yana jinsa ba tare da ya yi magana ba.
"Wai yaron nan ne zai ce shi ba son Ummu yake yi ba auren sha'awa ya yi da ita yanzu kuma tunda ya gama moranta bari ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda"
Lamiɗo ya sake sosa giran shi na dama wannan karon kansa ya duƙar ƙasa bai kuma yi magana ba
"Ya ce ba ya son cikin jikinta tunda ya ce ta zubar ba ta zubar ba. Baffa kuma ya ce ta haifa su suna so kuma za su riƙe, ka ji halin da ake ciki ni tun zuwan da na yi ma ban koma ba, ga tausayi in ka ganta amma haushinta zai sa in kana kusa da ita ka yi mata dukan tsiya"
Lamiɗo ya ɗago yana kallon shi.
"Me ya sa?
Ya tambaya a hankali kamar ba ya son magana.
"To Abdulrrahaman na faɗa mini har yanzu tana son wannan shegen bayan ya gama tozarta ta, saki uku fa ya yi mata Amini bayan ya haɗo ta maganganun cin mutumci, shi ne har yanzu take so? Wallahi da ina garin nan sai na taka wuyanta tunda ita shashasha ce."
Sai da Lamiɗo ya motsa bakinsa ya ɗan murmusa.
Amma dai bai yi magana ba shi kuma Hamma Kabiru ya shiga faɗa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, shi dai kawai su Baffa yake ba ma laifi da ba su yi ma Ummu aure ba da duk haka bai faru ba ya manta da zanen kaddaran bawa ba ka iya guje masa.
Gajiya Lamiɗo ya yi ya motsa bakinsa ya katse Hamma Kabiru sanin halin shi in ya fara kawo hujjojinsa sai fa kowa ya fahimce sa.
"Ammah ta damu ko?
Shi ya sa ta rame ita da Baffa."
Ya tambaya ɗaya bayan ɗaya.
"Ai damuwa ta zama dole Amini, gwara ma Baffa ana iya gane damuwarsa Ammah ce sai dai ta kunshe ita kaɗai."
Shuru ya yi, Ammah tana cikin damuwa duk ta rame baiwar Allah. Ko saboda Ammah da yana nan aka yi haka sai ya saka an yi ma yaron nan ladabi tun da ya saka Ammah damuwa ita da Baffa.
Lamido gajiya ya yi da tsarin Kabiru ya kashe wayarsa ya ce zai je gida za su je masallacin jumma'a da su Baffa, amma ya ce in ya dawo gida za su yi magana.
Hula ya baƙa saka da wani rufaffen takalmi mai rufewa.
Har ɗaki ya bi Balkisu sai ya isketa ta yi barci har bargon ya ɗan gyara mata sannan ya fita. A falo ya iske su Sultan suka naɗe shi suna kiran sunan shi, kaya ya ce Anitha ta sauya musu tare da su zai fita ba daɗewa aka shirya su Sultan ma kamar ubansa farar shadda ya saka har da hula Beena kuma wata riga ce yar kanti a jikinta pick colour ga takalminta na mata cover mai kalan pick, gashin kanta an kama mata da kananun ribbors masu kala-kala.
Ganin ba a saka mata hula ko hijabi ba ya sa ya ce Anitha ta nema mata hula saboda Ammah za ta yi magana ko Baffa in su ka ganta ba ɗankwali ko hijabi.
Shi ya tuka su zuwa gidan Baffa, Ammah na ganinsa da yara ta tarbesu. Sultan da Beena sun saba da kakarsu suka make suna kiranta da Ammah. Ita kuma ta rumgume su tana murna.
Da su kaɗai Ammah ke wasan jika da kaka domin tana ta ce ma Sultan ya yo wanka yana so ya kwace ma Baffa gwammati a wajenta ko? Baffa ma da ya fito cikin manyan kaya ya ce ina ai ba wanda ya isa ya ture gwamnatinsa.
Ummu na cikin ɗaki tana jin su amma ba ta fito ba.
Tana jin zuwan su Hamma Abdulrrahaman da tafiya su masallaci su huɗu har da Hamma Abdullahi.
Sultan ma sun tafi da shi Beena kawai aka bar ma Ammah tana ta fama da ita, yarinya akwai shagwaɓa ta ce wannan za ta ci sai an bata ta ce wannan Ammah kuma ba ta gajiya.
Kafin su dawo Ummu ta fito ta shigar da ruwa ɗakinta karma ta nema daga baya, ba ta kaunar ma su sake haɗuwa har sai sun tafi.
Nan gida suka dawo a falon Ammah suka ci abincin suna ta hira duk da shi ɗan kasaitar ba a jin muryansa sai dai ta su Hamma Abdulrrahman.
Sai can yamma suka watse, Allah ya taimaketa har suka bar gidan ba ta fito ba kuma ba wanda ya neme ta sai Baffa shima sai bayan ya dawo sallan mangariba ya zo ya duba ta.
Kusan satin su Lamido ɗaya a jimeta suna hutawa. Kullum sai ya zo gidan Ammah shi da yara Balkisu kuma bai wuce sau uku ta zo ba, tana gida tana hutawa amma dai ta leka gidajensu Hamma Abdullahi Lamiɗon ma Ammah ta tura su tare da matarsa ta shi gidan Ummin ikki sun gaishe ta.
Ranar da suka yi sati suka tafi Jalingo gidan Hamma Kabiru kwanan su biyu suka dawo daga nan Ammah ta ce ya kamata su je Mubi ana ta tambayan shi tunda ya daɗe bai je ba, suka shirya tafiyan da Hamma Abdullahi da matarsa sai shi Hamma Lamiɗo da iyalan na shi a helux ɗin Lamiɗo suka tafi suka yini suka dawo. An ce Hamma Lamiɗo ya yi ta rabon kuɗi ga su Baffa Umaru da iyalansu har gidajen su Umma Balki duk ya je haka Hamma Abdullahi ya zo yana faɗa, shi daman mai wuyar Ammah ta yi magana ko bai yi ra'ayi ba zai je.
Ummu dai ba ta sake bari sun haɗu ba amma dai sun sake haɗewa da Balkisu da yaran tunda ko da yaushe suna gidan.
Lamiɗo bai yi ma Ammah maganar Ummu kai tsaye ba ya dai ce ta daina saka damuwa a ranta kar cuta ta kamata ta ce za ta daina in sha Allahu.
Bai kara ganin Ummu Salma ba, sannan bai sake tambayan wani game da ita ba, suma mutanen gidan ba wanda ya yi masa hiran abin da ya dangan ce ta. Suna da kwana goma da zuwa suka tafi Daura.
Daga can Balkisu za ta koma Lagos da yara saboda aikinta da makarantan yara amma shi Lamiɗo zai dawo ta Jimeta kafin ya koma Lagos.
****
*KATSINA STATE, DAURA.*
*MASARAUTAR DAURA.*
Garin Daura karamar hukuma ce da ke cikin Jihar Katsina. Garin yana cikin jihar katsina ne a arewa maso yammacin Nigeria, kuma ya yi iyaka da jamahuriyar Nijar ta wajen Damagaram daga arewa.
Masarautar Daura Jiha ce ta addini, da ta gargajiya a Arewacin Nigeria.
Sannan an kira Masarautar Daura a matsayin ɗaya daga cikin kasashen hausa bakwai, domin itace tare da Biram, Kano,Katsina, Zazzau, Gobir da Rano. Wanda zuriyar ƴa'ƴan Bayajidda suka yi mulki, tare da Daurama da magira,(matarsa ta farko)Jami'ar calfornia's Afircan. American studies na nufin Daura, da kuma Katsina a matsayin tsofaffin kujeru na al'adun musulunci da ilimantarwa.
Akwai al'adan da suke gudanawar a garin Daura bikin hawan sallar gani na ɗaya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da dawaki ke kece reni a cikinsa, wanda kuma za a iya cewa ya samo asali ne daga Daura sannan garin ya fice wajen gudanar da wannan al'adan.
**
Tun zamanin sarkin Jafaru ɗan Umaru zuru'an su Lamiɗo ke mulkin Daura sama da shekaru sittin da suka gaba ta.
Mai martaba Sarki Alhaji Dr. Nasiru Daura ya yi hau karagan mulkin Daura shekaru talatin baya sannan shi ne sarki na 42 a lissafin masarautar.
Kuma ya samu nasaran hawa karagan ne bayan rasuwar mahaifinsa tsohon sarki Mai martaba Muhammad Shitu.
Masarautar Daura kayattaciyar masarauta ce mai ɗimbin tarihi.
Lokacin da suka iso filin jirgi na Umaru Musa yar'aduwa da yake an san da zuwan su tuni wasu aminttatun Mai maitarba irin su Waziri da wambai tare da rakiyan dogarai sai ƙanin Lamido Saleem(Sardaunan Daura Hakimin Daura) suka zo tarban su. Shi kaɗai ne ke karatu a Nigeria shi ne kuma ke gida Daura tare da Maimartaba kuma yawancin yana wakilta shi zuwa wajen taro ko wani abu da ya shafi sarauta, mutanen garin Daura suna tunanin Saleem(Hakimin Daura) ne zai gaji Sarki duk da yana da karancin shekaru domin bai wuce 26 ba amma yana da hikima da hangen nesa sannan mai fara'a da son mutane saɓanin Lamido da ba shi da fara'a sosai, sannan ba mazaunin masarauta ba, amma shima an yi shaidarsa da kyakyawan zuciya da son takalawa da matasa, duk da kuma shi ke da Sarautan Yarima Daura mai jiran gado hakan bai hana wasu tunanin Hakimin Daura a matsayin wanda ya cancanta ba, duba da shi jinin Sarauta ne gaba da baya saɓanin Lamiɗo da iya bangaren uba ne sarautarsa take da ƙarfi.
*Janafty*