INUWAR BAYA (Tale of Haseena)

HAƊARIN DUHU

by @ayshnur

INUWAR BAYA (TALE OF HASEENA)

Daga Alkalamin Ayshnurpyar (Hameesha)✍🏻

BABI NA DAYA: HADARIN DUHU

Wasu hadurra ba sa faruwa kwatsam.
Ana shirya su ne tun kafin mu san suna tafe.



🩺 DR. HUSSAIN - THE HEALER

Akwai mutanen da aka halicce su domin ceton wasu.

Akwai kuma waɗanda aka ƙaddara za su fuskanci duhu domin wasu su rayu.

Dr. Hussain ya daɗe da sauraren duhun da ke rayuwa a zukatan mutane;
ya saba da ihu.
Ya saba da hauka.
Amma akwai wani irin duhu...
wanda ba ya cikin kwakwalwa.

Yana cikin ƙaddara.

A wannan daren,
ba shi zai haska rayuwar wasu ba... zai shiga duhu.


4th Jan 2025 - 12:45 a.m

Daren ranar Juma'a ne. Sararin samaniyar garin Kaduna ya cika da gajimare baƙi ƙirin, iska mai ƙarfi tana kaɗo ƙurar da ke nuna alamar saukar babban hadari.

Titin da ya ratsa ta gefen dajin dake hanyar zuwa Asibitin (Psychiatric Hospital) ya yi tsit. Hanyar ta yi fanko kamar an manta da ita, sai ƙarar kukan tsuntsayen dare da ke tashi jefi-jefi, kamar suna gargaɗi game da wani abu dake shirin faruwa.

Dr. Hussain yana zaune a cikin motarsa kirar Range Rover, hannunsa ɗaya yana kan sitiyarin motar, ɗayan kuma yana gefen kansa yana murzawa saboda matsananciyar gajiya. Idanunsa sun yi nauyi luf-luf.

Awanni ashirin da huɗu kenan yana fama da tunanin marasa lafiyar kwakwalwa... kuka, ihu, hauka da labaran da ba su da mafita.

"Ina buƙatar hutu..." ya furta a hankali cikin muryarsa mai sanyi tana cike da kasala.

Kwatsam, wani haske mai tsananin ƙarfi ya gauraye madubin motarsa ta baya. Zuciyarsa ta buga da ƙarfi!

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"

A saninsa shi kaɗai ne a titin. Tun karkatowarsa kan hanyar bai san daga ina motar bayansa ta bullo ba....

Kafin ya ankara, wata mota baƙa ta daki bayan motarsa da ƙarfin gaske. Motarsa ta karkace, sitiyarin sa ya kubuce masa....

"Kiiiiii....!"

Dr. Hussain ya yi ƙoƙarin sarrafa sitiyarin sa, amma motar ta fara juyawa kamar tana rawa a kan titi. Da kyar ya samu ya tsaya, sai dai kafin ya daidaita kansa, wata mota ta biyu ta fito ta gaba, inda ta daki hancin motarsa.

GWARAM!!!

Wani ƙarar ƙarfe ne ya tashi. Motar Dr. Hussain ta yi birgima ta kauce hanya tare da bin gefen titi har sai da ta gangara ta bugi wata ƙatuwar bishiya da ƙarfi.

Tassss...!! Ƙarar zubewar gilashi.

Tare da wani ƙarar fashewa "paff", nan take wata farar jaka mai cike da iska (airbag) ta fito daga sitiyarin motar, ta tare gaban Dr. Hussain don gudun kar kirjinsa ya bugi sitiyarin.

Komai ya tsaya cak.

A cikin duhun dajin, motocin biyun ba su tsaya ba. Ba su yi ƙoƙarin taimako ba.
Sun juya cikin sauri suka ɓace cikin duhu - kamar aikin da aka riga aka kammala.

Dr. Hussain ya ji kansa ya nutse cikin wani abu mai laushi kamar katifa, sakamakon wannan farar jakar iskar da ta tare shi. Nan take Wani farin garin foda ( talcum powder ) ya cika cikin motar, yana tashi a iska. Garin ya gauraye da hayakin radiator ya mayar da cikin motar kamar hazo. Wani wari na daban wanda Dr.Hussain bai san shi ba ya ziyarci hancinsa.

Kirjinsa ya matse, numfashinsa ya ɗan dauke na wasu dakiku sakamakon bugun da jakar iskar tayi masa.

Can ya soma tari kaɗan saboda gari-garin da ya cika motar.

Duk da halin da yake ciki hancinsa na jiyo masa warin sinadarin dake cikin jakar, hayaki mai kauri ya fara tashi daga gaban motar, yayin da shirun dajin ya sake dawowa.

**

A Cikin motar Dr. Hussain kwance, kansa a kan jakar iskar da ke karkashin sitiyari. Ya yi ƙoƙarin buɗe idanunsa amma ya ji wani abu mai dumi yana gangarowa daga goshinsa zuwa cikin idanunsa da gefen fuskarsa; jini ne.

Ba rauni guda ba ne.
Gilashi ya soke gefen wuyansa, yana zubar da jini sosai.

Wuyansa ya yi masa nauyi, wani radadi yake ji kamar wuta sakamakon gogewar da bel din motar yayi masa lokacin da take juyi.

Numfashinsa na fita sama-sama, duniyarsa na neman zama duhu...kamar wanda ke bankwana da duniya. A hankali duniyarsa ta fara dusashewa...gani ya koma kore, sannan duhu ya mamayi idanunsa, hayyacinsa ya bar jikinsa.


RAYUWA A CIKIN INUWA

Riiiiiiiiiin... Riiiiiiiiiin...
Ƙarar da ya rinka ji a kunnuwansa kenan lokacin farfaɗowarsa, iska da hayakin motar ne suka soma dawo masa da tunanin abu da ya faru taryan-taryan.

Cikin yanayin da yake tsakanin rayuwa da mutuwa, Dr. Hussain ya soma bude idonsa da kyar.

Jikinsa gaba daya yaki amsa masa, jini na ci gaba da gangarowa daga goshinsa zuwa fuskarsa.

Bai san tsawon lokacin da ya shafe a haka ba.

Lokacin iskar hadarin ya lafa, hasken wata ya fara fitowa dalilin gajimaren dake rabuwa a hankali a hankali.

Cikin jiri da gani dishi-dishi, daga cikin duhun bishiyoyin ya hango wata baƙar inuwa tana nufo shi.

Hasken wata ya kama gefen jikinta, yana bada siffa tsakanin inuwa da mutum.

Mace ce.

Sanye take da ƙaramin hijabi, gaba ɗaya fuskarta a rufe, sai idanunta kaɗai dake walwali tamkar taurari cikin duhun daren.


Ta karaso da sauri, sai dai ganin jinin da ya lullube shi, da wanda ke jikin airbag din da ya taresa yasa ta tsaya cak. Numfashinta ya ɗan dauke na wasu sakanni.

"Jini...ne!" ta furta cikin rawar murya, jikinta na kakkarwa tsoron jinin da take fama dashi (hemophobia) ya fara kokarin tashi, don har ta soma ganin jiri.

Amma ganin yadda Hussain yake fafutukar numfashi, sai wani irin ƙarfin gwiwa ya ziyarce ta. Ta kauda tsoron jinin ta, tayi wuf ta fara kokarin bude kofar motar da ta lankwashe.

Da kyar ta samu ta zaga ta dayan bangaren. Tasa hannu ta cire masa bel din da ya takure wuyansa, sannan ta duba yanayin numfashinsa da kwarewarta.

Cikin sauri, ta kwance mayafin dake daure a kugunta, ta yaga gefen mayafin, ta matse inda jini ke zuba a goshinsa sannan ta daure.

B'alle boturan rigarsa ta shiga yi don bude hanyar numashinsa. Dai-dai nan idanuwansu suka hade cikin na juna.
Dr. Hussain ya lumshe idanunwansa, hannunsa na dafe da gefen wuyansa wanda duk ya baci da jini.

A hankali ta d'ora hannuwanta akan nasa, kyawawan idanunta na nuna alamar neman izininsa, tana kokarin cire hannunsa daga raunin da ya dafe, sake lumshe idanunwansa yayi jin dumin hannayenta a jikinsa.

Anan ta ga wani sabon rauni; yankan gilashi ne a wuyansa, yana zubar da jini sosai.

"Ka da ka mutu...
Don Allah ka da ka mutu kai ma..." Ta fad'a cikin kuka muryarta na rawa.
Amma hannuwanta suna aiki da kwarewar da ba a saba gani ba.

Ta sake yaga sauran mayafinta gida biyu, ta danne inda jinin ke fitowa a wuyansa. Cikin wani irin kuzari, ta jawo shi daga cikin motar da karfi fiyeda yanda jikinta ke iya dauka, kafin hayaki ya koma wuta.

"Ba za ka mutu ba...da ikon Allah ba za ka mutu ba..." ta rinka maimaitawa cikin sanyin muryarta.

D'an yayyafin ruwan dake sauka ya taimaka wajen sanyaya turirin dake fita a motar.

Da kyar Dr. Hussain ya d'aga hannunsa yana nuna mata wani waje da yatsarsa. Cikin hanzari ta maida hankalinta wajen, tabi inda yatsarsa yayi da sauri, akwatin taimakon gaggawa (First Aid Box) ta hango. 

A gefe guda ta kwantar dashi tana sauke numfashi.

Komawa tayi cikin kwarewa ta wanda ya saba bada taimakon gaggawa ta dauko first aid box din. Ta bude tana duba kayan dake ciki "Alhamdulillah."
Abinda take nema akwai su a ciki.

Had'a kayan tayi gu daya, sannan ta soma wanke raunin dake goshinsa da gefen wuyansa, da sinadarin kashe kwayoyin cuta (Antiseptic).

Anan ne ta kula raunin dake wuyansa ya fi tsanani. Gilashi ya soke shi, jini na fita da yawa.

"Ba za a bar shi haka ba." Ta furta cikin sanyinta.

Sai da ta sake daure masa rauninkan, sannan ta koma cikin motar duddubawa take cikin sa'a ta hango wayarsa yashe ta d'auko ta.

Allah ya taimaka babu lambar sirri, 'security.' a tare da wayar, kamar yanda wasu ke rufe wayarsu ko yaushe ba tare da tunanin zuwan tsautsayi irin wannan ba.

Ta shiga duba kiran ƙarshe (Recent Calls). Tana yi jikinta na rawa har a wannan lokacin
Second Bro...
Lovely Bro...
Sune lambar karshe da akayi waya dasu, kawai sai ta danna kira kan guda daya.

Bugu daya akayi picking

"Ya Hussain...."

"Mai wayan yayi had'ari..." Ta katse mai maganar cikin muryar dake shake da kuka, da tsoron kar a d'auki muryarta.

Daga nan ta ci gaba da bayyana mishi inda suke da cewa...Azo da wuri, ba tare da ba shi damar amsawa ba, ta danna jan button ta katse kiran, tana maida numfashi kamar wacce tayi tseren gudu.

Ta tsaya ta kalli fuskarsa. Wani irin tausayi wanda ta jima rabon da taji irinsa tun akan Ya Muhsin dinta, shine taji ya ziyarci zuciyarta, ta sa hannunta mai sanyi, wanda ke rawa saboda fargaba da tausayi, ta goge masa ragowar jinin da ya rage a kuncinsa.
Dr. Hussain ya lumshe idanunwansa ya ji wani irin dumi na daban, ba na jini ba, face dumin tausayi da ya kwarara har cikin bargonsa.

Ganin jinin dake wuyansa bai tsaya ba yasa ta rintse idanunwanta, kafin ta kuma bude akwatin taimakon gaggawan.

Ta dauki zaren dinkin da take bukata.

Da sauri ta kunna fitilar wayarsa domin samun haske.

Hasken wayar ya haskaka fuskar sa... sannan ya haskaka idanuwanta.

A cikin wannan haske mai sanyi, Dr. Hussain ya iya ganin idanuwanta a sarari...cike da tsoro, amma kuma tana aiki cike da ƙuduri.

Tayi masa kamun dinki biyu agun da zai tsaida zuban jinin da yake, cikin gaggawa da kwarewa.

Cikin ikon Allah ta samu ta tsayar da jinin.

Ganin idanunwansa na neman rufewa ta fara bashi kwarin gwiwa "Ka rike numfashinka... don Allah ka da ka bari duhu ya dauke ka..."

Tana durkushe gabansa bata barshi ya sake dogon barci ba, duk da yayyafin ruwa na tab'a ta, gashi ta sake cire wani dogon mayafi dake zagaye da jikinta, ta lulluba masa, sam bata damu da sanyin dake shigarta ba, hankalinta gaba daya na garesa.

Zuwa wannan lokacin Iska ta lafa, hadari ya washe ya bar yayyafi na dukan ganyayen dake wajen, in banda karar kukan tsuntsayen daren babu sautin komai sai nishin Dr. Hussain dake jin jiki da alama.

Can Dr. Hussain ya buɗe idonsa a hankali lokacin da ya fara jiyo ƙarar jiniyar 'yan sanda da hasken motocin danginsa, wanda hakan yasa ta mike tare da fara ja da baya.

Ya so ya mika hannu ya riko gefen mayafin ta, yaso ya dakatar da ita...Yaso ya furta koda harafi daya ne....Amma harshensa ya yi masa nauyi kamar dutse, muryarsa yaki fita. Sai sanyayan idanunsa da yake binta dasu, labb'ansa na son motsawa.

Ganin hasken motoci da siren d'in 'yan sanda na kusantowa, ta kara firgita ta ja baya da sauri, ta sake kallon fuskarsa a karo na ƙarshe, idanunsu suka tsarki juna na wani dan lokaci, kafin ta juya da gudu cikin duhun dajin. 

Ba tare da sanin ta bar takalminta guda daya agun ba...

Ta ɓace kamar ba ta taɓa wanzuwa ba.

Nan ta barshi da sanyin kamshin jikinta yana shawagi a hancinsa.

Dr. Hussain ya sake lumshe idanuwansa, sautin muryarta na sake amsa kuwwa a kwakwalwa da kunnuwansa.

"Kada ka mutu...."

'Shin wacece ita?' 

Me take yi a cikin wannan dajin cikin wannan Daren?

Vote.
Comment and 
Share.

Pyar 💗 ✍🏻