Chapter 12
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 12
Ta daɗe tana tunane tunane kwance kusa da salmah da duk a tsammaninta barci take yi, bata san sanda barci ɓarowa ya kwashe ta ba, jin saukar nunfashinta yasa Salmah mikewa zaune, ta tankwashe ƙafa tayi a tsakiyar bed din tare da rafka uban tagumi da hannun bibbiyu.
Bata san iya adadin lokacin data kwashe a haka ba, ba komai take yi ba sai tufka da warwara a karshen dai ta tsaida matsaya É—aya wanda take ganin shine daidai ta tabbata za su yi babbar asara, amma ba komai wani hanin ga Allah baiwa ne, za ta yi komai domin ganin farin cikin A'ishatu a duniya ciki harda sadaukar da nata farin cikin.
Ƙarar shigowar message wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula da sauri ta buɗe saƙon, kamar ɗazu lamba ce babu suna, tana gama karantawa ta saki kayatatcen murmushi, juyawa ta yi ta kalli Aysha dake barci sai haɗa uban gumi take duk da gudun fankar da suka ƙure, kallo ɗaya ta mata ta san barcin bana dadi bane Kawai fin karfin ta yayi ya kwashe ta ba da son ranta ba, wayarta ta saita a daidai fuskarta ta dauke ta hoto kala biyu, juyawa ta yi kan wayarya ta yi ɗab danne danne na kamar minti uku kafin ta kife wayar ta mike ta shige toilet.
Ruwa ta sake watsa wa tare da yin alwala ta fito daure da tawel, sharp sharp ta shirya cikin dogon rigar materiya mara nauyi saboda yanayin da suke ciki na shigowar zafi gadan gadan, sallar la'asar ta gabatar, wanda tuni masallatai sun idar, har ta idar Aysha bata motsa ba, sai da ta gama addu'o'inta, ta shafa, sannan ta matsa kusa da ita a hankali ta shiga tashin ta ta hanyar kiran sunan ta ƙasa ƙasa tana ɗan bubbuga kafar ta.
Bata kasance mai nauyin barci ba hakan yasa kira biyu tayi firgigit ta bude idanu a firgice tana karanto *A'uzu bi kallimatil lahi, tammat min sharri ma kalaƙa* ganin Salmah a gabanta tana sakar mata kayataccen murmushi mai dauke da manufofi kala kala, ya matukar bata mamaki, a hankali tace "Salmah kin tashi ne ya jikin naki?"
"Da sauƙi sosai alhmdllh na ji dama, na farka tun ɗazu har na gabatar da sallar la'asar."
"Alhmdllh Allah ya ƙara sauki."Aysha ta faɗa ntana ƙoƙarin sakkowa daga kan bed ɗin, har ta miƙe tsaye ta fusakanci haryar toilet ta ji Salmah ta ri'ko hannunta jutowa tayi ta kalleta, murmushi Salmah ta sakar mata tare da cewa "Meke faruwa naga kamar baki cikin kwanciyar hankali."
"Mafarki nayi Salmah me firgitarwa, da ace abin da na gani a mafarkina na yau zai zama gaskiya da babu makawa sai na saka wuka na farke cikina, domin babu amfani rayuwa a gareni."
"A'uzubillah minash shaidanir rajim." Salmah ta fad'a cikin zaro ido.
Hannun tasa ta ɓamɓare hannunta daga riƙon da Salmah ta mata jiki a sanyaye ta shige toilet.
Hankalin Salmah ba ƙaramin tashi ya yi ba da jin kalaman A'ishatu, ta sha jin tana furta kalamai makamantan wannan a lokuta mabanbanta, amma basu taɓa tashin hankalinta kamar yadda wannan ya tashi hankalinta ba, a da bata san wacece A'ishatu ba kuma bata san wanene Babangida ba shiyasa bata damuwa da kalamanta masu shige da zaurence, amma a yanzu da ta riga tasan komai baza ta juri jin makanatan su na fitowa daga bakinta ba, duk da bata tambaye ta ba tasan ba zai wuce mafarkin Babangida ta yi ba.
Wuri ta ne ma ta zauna a toilet ɗin, ta yi shiru ta zurawa waje guda ido, mafarkin da ta yi yanzu na sake dawo mata filla filla a kwkwalwa, rintse ido tayi lokacin da take hango shi rungume da ƙugunta, idanuwansu cikin na juna, a hankali ya dinga matso da kyakkyawar fuskarsa gare ta har ya yi nasarar hade bakunansu waje guda ya fara sakar mata wani irin al'amari mai kama ƙwaƙwalwa, abin da yafi bata takaici da ba'kin ciki yadda take mayar masa da martani cike da shauƙin soyayya.
Fashewa tayi da kuka mai cin rai, cikin murya kasa kasa yadda tasan Salmah baza ta jiyo ta ba, ta ce "Ya Rabbi na roƙe ka kada ka sake muna min makamancin wannan mummunar al'amarin, wanda ganin ranar mutuwata ta fi shi sauki a gareni."
Tafi minti 30 a zaune a cikin toilet ɗin, kafin ta miƙe da kyar ta watsa ruwan sanyi tare da dauro alwala ta fito.
Koda ta fito Salmah bata É—akin hakan ya mata daidsi don dama tana shakkar tsareta da tambayoyi da salmah za ta yi, shiryawa ta yi ita ma cikin riga da wando marasa nauri sakakku ne sun mata kyau sosai, hoda da kwalli ta shafa duk a kokarinta na kar Salmah ta gane ta yi kuka, wanda tuni bata san aikin gama ya riga ya gama ba domin harta addu'ar da ta yi duk a kunnen Salmah.
Tana cikin sallah, Salmah ta turo kofar ta shigo ganin bata idar ba yasa ta zauna a bakin bed ta jira ta, tana sallamewa ta kalleta, already dama ita idanunta na kanta, ido cikin ido suka kalli juna kowacce zuciyarta da abin da take saƙa mata, Salmah ce tace "Allah ya karɓa.“ da amin ta amsa mata, ta sake cewa "Ammi ta dawo tana kiraki." Cikin ɗan mamaki tace "Ammi ta dawo fa kika ce?" Gyada mata kai Kawai ta yi, "Amma dai ba da moto ta dawo ba ko?" Salmah tace "kamar yaya?"
"Naga ko karan bude get ban ji ba ne balle dirar motar ta." Ta6e baki Salmah tayi tareda watsa mata wani kallo tace "Ta yaya zaki ji diran motarta bayan kin shige toilet kin rufe kina kuka." Shiru tayi ta rasa me za ta ce, sai kawai ta tasttsarreta da idanu, ganin haka yasa Salmah mikewa ta yi ficewarta.
Sai da ta yi yan addu'o'inta ta shafa, ta kwashe daddumar sannan ta dauki siririn gyalen kayan jikinta ta yafa, ta bi bayan salmah, basa falo hakan yasa ta nufi bed room din Ammi kai tsaye, sallama ta yi a tare duka amsa mata, tana shiga gaban Ammi ta zarce ta risina tare da cewa "barka da dawowa Ammi." Murmushi Ammi ta saki tare da amsa mata da "barka kadai A'ishatu." Ita ma murmushi tayi tare da cewa "ya aiki ya zafi."
"Lafiya kalau Aisha ya makaranta. " tace "Alhmdllh."
"Salmah ta gaya min kun dawo ba tare da an tashi, shiyasa nace ta kiramin ke, a kul! kar ku sake yin haka, idan d'aya baiji dad'i ba d'aya ya tsaya yayi karatun shi kunji ko." Har suna hada baki wurin cewa "to Ammi."
Ammi tace "Salman bai dawo ba ko." Ta fad'a tana kallon A'ishatu don already ta riga ta tambayi Salmah tace mata bata sani ba ita tana barci, Aisha tace "ya dawo sun zo tare da Suraj har na basu abinci,to na shiga daki barci ya kwashe ni ban san sanda suka fice ba." Kwafa Ammi tayi ta ce "zai dawo ya same ni daga shi har surajon ba motata ta zama ta tsarar wasan su ba, A'ishatu kuje a daura sanwa tuwon shinkafa za'a yi miyar ogun, kuje ku fara zan zo na same ku Salmah ki yanka Ogun ki nika kayan miya,ke kuma Aisha ki daura tukunyan tuwo ki wanke shinkafa ki zuba ki dibi naman rago ki tafasa, kafin nazo."
Bayan sun fice toilet Ammi ta shige ruwa ta watsa ta fito ta kimtsa cikin dogon rigar atamfa duk da bata shafa ko mai ba saboda zafi sai da ta balbale jikinta da tsadaddun turarakan ta Ammi akwai son kamshi kasancewarta haifafaiyar Maiduguri kanuri ce gaba da baya, hula ta saka mai kyau wanda ya shiga da atamfar jikin ta fito tana baza kamshi ta nufi kitchen.
Ta tarad duk sun maida hankali akan aiyukan data saka su, duba wa tayi taga sunyi komai yadda ta umarta, kujera ta ja ta zauna a kitchen tana basu umarni suna yi sai dai fa cikin taka tsantsan dan Ammi ko kadan ba son kazanta, kuskure kad'an wanda su suna ganin shi ba komai bane zata fara musu fad'a, tana cewa bata son kazanta haushi kuwa duk ya cika Salmah don anfi samun matsala da ita a haka har suka kammala lafiyayen tuwan farin shinkafa miyar Ogun da agushi da yaji naman rago da stock fish ga ganda, ba tare da ta saka musu hannu ba, sai da suka jera komai a dinning sannan ta umarce su da suje su su watsa ruwa suyi sallah, cikin dan kasa² da murya Salmah tace "Ammin nan wlh tsabtan ta ya wuce misali minti daya biyu tace ayi wanka sai kace wasu kifaye wlh ni ba wankan da zanyi." Ammi da bata jita sosai ba tace "me kika ce?" A'ishatu ne da taji komai rass ta bud'e baki zata yi magana, da sauri Salmah ta kai hannu ta rufe mata baki tare da cewa "cewa nayi Amminmu mutuniyar kirkice sosai ga tausayi." Da ji ma tasan karya take yi hararanta ta yi tace "kuje Allah ya shirye ki, ban iyawa da jidalinki Salmah." Dariya suka saka kafin su fice daga kitchen ɗin.
******************
Tafe yake a motar shi kaÉ—ai yana driving sai sharara gudu yake yi a hanya, Allah Allah yake ya isa gida domin bakin shi cike yake da labarai kala kala , sai gyada kai yake yi yana sakin murmushi kamar sabon gaula, can kuma kamar an tsikare shi ya ce "kaiii! Mutumin nan duniya ne wlh, Allah ya tara mai baiwa alkur'an ina ma nine Suraj wai da anga fankama da iyayi." Haka yai ta sambatu shi kadai kamar sabon kamu, yana isowa layin su ana tada sallar isha'i a masallacin bakin layin, fakin yayi ya fito don gudun rasa jam'i bayan an idar ya fito, ya 'karasa gida, yana isa bakin get motar Abie na 'karasowa, kusan a tare sukai parking, da sauri ya isa wajen Abie yana mishi sannu da dawowa, ya kar6i jakar shi da ledodin dake hannunshi, tambayar shi Abie yayi daga ina yake, kasancewar yasan ba'a ma Abie karya yasa direct ya gaya mishi daga gidan su Suraj, Abie yace "Waya aike ka." Yace "babu kowa." Ba zato yaji saukar rankwashi a kokon kanshi, "washhh!" Yace tare da dafe wajen
"ban hanaka kaiwa dare a waje ba."
"Kayi hakuri Abie wlh 'kwa'kwaran uzurine ya tsare ni bansan dare yayi ba sai jin kiran sallah magariba mukayi."
Abie yace "OK to da kyau, itama Ammin ku na hanata ta baka mota indai ba school zaku ba taki ji." Jin Abie ya ambaci Ammi da mota sai da hantar cikin shi ta kad'a, shi sai yanzu ma ya tuno da abin da ke gaban shi, bai ankara ba tuni Abie ya kusa shigewa ciki da gudu ya rufa mai baya.
Falon babu kowa duk suna ciki, Allah Allah yake Abie ya amshi kayan shi ya samu ya je dakin su Salmah ya fesa shafa musu labari.
Har d'aki ya raka Abie gaban shi na fad'uwa kar yayi kicibus da Ammi aiko dai bata ciki, da sauri ya ajiye kayan hannun shi tun kan Abie ya kai ga amsa, don yasan yana kara kwakwkwaran mintuna biyu Ammi zata shigo d'akin, aiko dai cikin rashin sa'a yana fitowa sukayi kicibus, rass gaban shi ya yanke fadi, idanun su na haduwa yayi kasa da kai, bai san karasowarta ba sai ji yayi ta kama kunnenshi d'aya ta murd'a "Auww wayyo Allahnahhhh Ammi!" Tace "kunnnen kashin nan yau sai na tsinke shi." "Dan Allah kiyi hakuri Ammi." Ya fada yana mi'ka mata key,sai da ta amsa da daya hannunta sannan ta sake mishi kunne tare da bashi kyakkyawan rankwashi dafe kai yayi yana sosa wajen, da sauri ya fice, shigewa dakin Abie tana surutu akan kunnen 'kashi irin na Salman.
Direct dakin su ya dosa, da sallamar shi a baki ya shiga dakin, Salmah na kwance tana karatun novel É—in nata na fama, Aysha na zaune kan rug a tsakar dakin ta barbaza takardu da alama wani abu take nema.
Yana shigowa duk suka tsaya da abin da suke yi suka d'ago suna kallon shi, fuskar shi cike da mad'aukakin fara'a yace "bebs albishirin ku." Har suna had'a baki gurin cewa goro tuni salmah ta mi'ke zaune, tana kallon shi, ya ce "yau nayi hand to hand da Mr Ahmad Idris Ahmad kangiwa." Gaba ki d'ayan su sai da gabansu ya yanke ya fadi, kusan a tare suka furta “ Are you serious.........