FARGAR JAJI

19

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

*19*

*BAYAN WATA BIYU*

Wattani biyu sun zo sun shafe kamar ƙiftawan ido, rayuwar dai ta cigaba da tafiya cikin godiyar Ubangiji, haka yake a bangaren Ummu Salma  sai godiyar Allah an samu canji sosai daga yanayinta yanzu Ummu za ta zauna ta yi hira har da dariya, ta saki jikinta tana ƙokarin yaƙi da kaddaranta.

 Duk da ba ta manta ba amma ta aro jarumta ta yafa ma rayuwarta saboda iyayenta da ƴan'uwanta, tana so ta ga farinciki a fuskokinsu kuma in dai tana son ganin haka sai ta aro ma rayuwarta farinciki, kuma da ta yi hakan ta ga canji Baffa da Ammah sun rage damuwa ganinta cikin farinciki ba abin da ke damunta ko ma yana damunta tana yaƙi da shi. Za ta fito ta yi ta nuna farinciki a fuskarta amma a zuciyarta Ubangiji ne kaɗai ya san irin ciwon da take ciki, sai dai in abin ya taso mata sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka ba ta yadda ta fito sai ta wanke fuskarta.

 Za ta manta amma ba da wuri haka ba domin taɓon da Habib ya yi silan saka mata a cikin zuciyarta ba mai warkewa ba ne da wuri tana tunanin nan da shekara goma wataƙila har abada ma.

A yanzu a ƙalla cikin ta ya kai kimanin wattani bakwai ne, kuma da ita da cikin jikinta duk suna cikin ƙoshin lafiya. Ba abin da za ta ce ma Iyayenta da yan'uwanta sai godiya, domin sun tsaya mata sun kula da lafiyanta da cikin da Habib ya ce ba ya so. Tana zuwa asibiti awo kuma Ummin ikki ke rakata duk lokacin da za ta je, sannan Hamma Abdullahi ke kai su sai dai in baya nan sai su hau kekenapep, su je su dawo kuma komai za a yi na laluranta kafin ma Baffa ya ba da yayyenta sun ba da ta yi komai da shi, cikin ya yi girma tsini gare shi ya yi wani ƙasa, Ummu Salma ta yi baƙi sosai ga kuraje duk sun lalata mata fuska kafafunta sun kumbura gabaɗaya dai hallitan ta ya sauya, jiki duk ya yi wani iri alamun rai na rayuwa tare da kai, Har kuma yau Habib ko wani ahalinsa ba su nemi Ummu ko iyayenta ba, su ma kuma kamar yadda Baffa ya ce ba wanda ya sake neman su, da farko Baffa Umaru ya so ya sake neman su Baffa ya ce har abada kuma shima baya fatan su neme shi nan gaba.

 Ammh ba ta barinta ta yi aiki sai dai ita ce ke matsawa sai ta yi aikin tunda a asibiti an ce ta riƙa yawan motsa jikinta girman cikin ya sa kowa ke tunanin namiji za ta haifa, kuma ko a scanning ɗin da ta yi namiji ya nuna amma ita ba ta damu ba ita dai a koda yaushe fatan ta ta sauka lafiya namiji ko mace duk wanda Allah ya bata tana so, domin bayan cikin ba ta da wani abu na rayuwarta da ya yi mata saura, sannan ba ta zuwa ko'ina daga asibiti sai gida ko kwanaki Umma Salamatu ta aurar da Autarta Ammah ta so sai ta je bikin nan wai in ta ga y'anuwa za ta sake sosai ita ko ba ta son zuwa ko'ina ba, ba ta so ta je ana kallonta ana nuna ta cikin tausayi ana cewa Allah Sarki shi ya sa ta ce ba za ta je ba Baffa kuma ya goya mata baya sai dai Ammah ce ta je aka yi biki ta dawo.
Ko a anguwa an gama yawo da maganar an hakura  tunda da dawowar Ummu yanzu wajen wata biyar kenan tuni zukata sun haƙura.

 Komai na bukatar haihuwa Mami ta siya mata kaya masu kyau da yarari, domin ta ce duk abin da Ummu za ta haifa ita ce uwarsa da ubansa. Wasu kayan ma duk yan waje ne Mami ta siya mata kwanaki ma da suka je London ta siyo mata wasu kayan yara masu kyau sannan itama ta zo mata da dogayen riguna masu kyau sama da kala biyar tunda yanzu su take sawa kayanta duk sun yi mata kaɗan, balle ma tunda ta dawo gida ta daina amfani da kayan lefen Habibu kayanta tun na gida take sawa kuma yanzu ba sa shiganta sai dogayen rigunan da Mami ta siya mata take bumjumawa a cikin gida sannan atamfan wajen Hamma Lamiɗo da Ammah ta ba ta ta raba shi uku duk ta yi zannuwa faya tana ɗaurawa a gida biyun kuma suna cikin ɗan kit ɗin kayan haihuwan da Mami ta yo mata.

Ba mai zuwa wajenta sai Baɗɗo Shamsiya ma ta ja baya da ita ba ta san dalili ba. Sun daina waya kamar yadda suke a baya sannan tun bayan dawowanta gida sau uku ta zo, na ukun ma cingham da minti ta kawo mata wai an saka ranar aurenta ta daɗe tana faman mamaki, ita dai kamar yadda Shamsiyan ta faɗa mata gidan su ba ka yin aure sai ka yi Degree ka yi bautar ƙasa kuma haka ne tunda duk yayyen Shamsiyan ba wacce ta yi aure tana cikin karatu sai da suka gama, amma za ki iya ɗora karatunki na gaba a gidan mijin ki,  amma sai ga shi ita tana aji uku ne ma a lokacin amma za ta yi aure sannan ƙarin mamakinta ba ta san Bestie na da wani saurayi ba, saboda dokar gidan su amma sai ga shi ta kawo mata mintin saka rana, sannan ita ko a labari ba ta taba faɗa mata ta samu miji ba, da Ummun Salma ta yi mata ƙorafin  ta samu miji amma tana ƙawarta na kusa da ita ba ta sani ba?

Sai ta ce ta yi hakuri ganin tana cikin damuwa shi ya sa ba ta faɗa mata ba, kuma ba su daɗe da haɗuwa da mutumin ba. 

Har tambayanta ta yi ya aka yi mahaifinta ya amince ta yi aure ba ta gama makaranta ba.? Sai da Shamsiyar ta yi wata bazawaarar dariya kafin ta ce dangin mahaifiyarta ne suka shige mata gaba, sannan shima mahaifin na su yana sonta saboda maraicinta shi ya sa ya yi mata abin da take so. Ummu ta yi mata fatan alheri  da cewa ta bi dai a hankali domin yanzu maza ba a gane musu sai ka shiga kuma zence ya sha bambam.

"Bestie ki kwantar da hankalinki. Sweety yana sona, ni ce kusan rayuwarsa nima kuma shi ne rayuwata. Kuma ki cire ma kanki tunanin wai don ke ba ki yi sa'ar aure ba ki yi tunanin koma ba zai yi sa'a ba. Ke dai kawai ba ki yi dace ba ki bar shi a haka amma ni na san abin da na zaɓa ina mai bakin tabbacin na yi kyakyawan zaɓi kuma na yi dace.".

Kalamanta su ɗan yi ma Ummu tsauri amma ba ta nuna mata ba, ta yi mata fatan alheri da ta tambayan ta yaushe ne lokacin bikin! Sai ta ce ba a saka date ba amma in an sanya za ta faɗa mata har Ummu ta yi fatan cewa Allah ya sa lokacin ta haihu yadda za ta samu zuwa, domin ko ta daina fita ba za ta ƙi zuwa bikin Shamsiya da Baɗɗo ba su ne suka yi mata komai a nata bikin da Habib.

Ko Baɗɗo da ta zo Ummu ta faɗa mata an sanya ma Shamsiya ranar aure sai da itama mamaki ya kamata har sai da ta maganta da cewa ita da ta ce a dokar gidansu sai ka gama Jami'a za ka yi aure, nan fa Ummu ta karanta mata abin da ta ce mata bayan itama ta yi mata wannan tambayar.

"Tab. Ni ko ta ba ni mamaki duk yadda kuke bai kamata a ce sai dai ta zo kawo miki minti ba."
A lokacin Ummu shuru ta yi ba ta yi magana ba, Baɗɗo ta yi ta faɗa tana cewa Shamsiyar ta sauya tunda Ummun ta dawo gida.

"Ko saboda yanzu kin yi aure kin fito shi ya sa ta ja baya dake?
"Kin san tana makaranta, ba ta samun lokaci."
Daƙyar Ummu ta samu Baɗɗo ta bar maganar saboda kar Ammah ta ji daman da ta ce mata an sanya ma Shamsiyar ranar aure ga ma mintin da ta kawo mata nan ta nuna mata taɓe baki ta yi ta ce shi ya kawo ta kenan? Domin ita Ammah ta ce tun maganganun da ta ji tana yi yarinyar ta fita zuciyarta.
 Ita kanta Ummun ta san alaqar su da Shamsiya ta ja baya kuma kamar Shamsiyan ne ke gudunta tunda ita tana kiranta amna ba ta ɗauka, sai a yi kwana huɗu sama da sati sannan za ta kirata da cewa karatu ya yi zafi shi ya sa ba ta samun lokaci itama daga baya da ta ga haka sai ta kama kanta amma ranar ta yi kuka, yau ace mutane sun fara gudunka saboda kaddara ta faɗa maka, tana tuna a baya yadda kowa ke haba haba da ita saboda tana gidan mijinta yanzu kuma duk abin da take tunanin ta samu sai da Habib ya dawo da ita baya ba ta da komai a rayuwarta in ta tuna yadda rayuwarta ta sauya lokaci ɗaya sai ta yi kuka sosai, har kuma yau yana nan a cikin zuciyarta duk da tana ta addu'an Allah ya cire mata tunanin shi da soyayyarsa a cikin zuciyanta. Tana ta samun sauƙi amma kuma bai fita duka ba, ta dai dangana ta kuma aminta da cewa wataƙila Habib ya yi nisan da ba zai taɓa dawo gare ta ba.

In ta kalli kanta a madubi da katon ciki, mara duk ta yi baƙi fuska ta lalace komai dai na ta ya sauya sai ta yi ta zubar ƙwalla. Tabbas ta rasa komai Duk wani abun sha'awa da namiji zai gani a jikin mace ya yaso ta, ta rasa shi. Da gaske Habib ya lalata mata gobenta wataƙila ma har da jibinta. Ya raba ta da martabamta na har abada. Ba za ta taɓa komawa Ummun Salman baya ba, ko shekaru tun tura ta na nan a yadda Habib ya sako ta. Sai dai za ta haihu kuma za ta shayar da abin da za ta haifa komai na jikinta zai saki to wani kuma taƙama gare ta? Ba ta da komai sai godiyar Allah da imani kawai.
In tana kuka sai ta yi hamdala ta ce Ya Allah Ummu Salma ta gode,  domin ya barta da rai da lafiya ya kuma ba ta iyaye masu jajircewa yau da babu su ba ta san wani hali za ta shiga ba wata kila da ta kashe kanta cikin ƙunci da baƙin ciki.

***

Hamma Saddam ya sake zuwa gida sun ɗan smu misSemister break, dawowar shi ne ya matsa ma Ummu sai da ta amince ya buɗe mata WhatsApp, ganin ya nace ne ya sa ta ce ya buɗe mata da sabuwar lambar nata.

Nan take ko ya buɗe mata ya kuma yi adding ɗinta a family group ɗin su, tunda ya buɗe mata ba ta ma shiga saboda yanzu ta saba da rayuwarta ba waya. Ba ta da lambobin kowa sai na yan'uwanta.

In ta ma duba chart ɗin sai dai ko Baɗɗo in ta yi mata magana sai Shamsiya da yanzu a chart ɗin suna ɗan gaisawa jefi jefi, sai Hamma Abdulrahim tun da shi yana can wata ƙasar suna yawan magana da su Hamma Jibo suna ɗan jan ta da mgana.
Hamma Kabiru da ta yi masa sallama sai da ya yi sati sannan ya buɗe.

Kuma bayan ya amsa sallaman ta gaishe shi ya ga saƙon amma bai sake yi mata magana ba itama ba ta sake bi ta kansa ba sanin halin shi 
Sun zo shi da matarshi da yaran shi suka yi sati suka koma, Hamma jibo ma da Hamma Mustpaha sun sake dawowa har Hamma Lamiɗo ya zo shi kaɗai kuma bai kwana ba a ranar ya wuce Daura da kuma zai wuce bai sake biyowa ta nan ba, Ammah ke ta faɗin yanzu ya sauya ma'aikata ba zai riƙa daɗewa ba a gan shi ba sanda ya zo ma Ummu na asibiti ta je awo ita da Ummin ikki sai da suka dawo suka ga Ammah da kuɗi sabbin yan dubu dubu ta ce ba daɗewa da fitan Lamiɗo ya wuce Daura duba kakarsa Fulani ba ta ji daɗi ba.

Akwai wata class mate ɗin su ita da Shamsiya da suka yi Ahmadu Ribaɗo tun primary har sakandiri duk da dai ba sa wani yi da Ummu amma suna ɗan gaisawa a chart sannan lokacin tana group ɗin su na makaranta da wancan layin suna ɗan magana, shi ne da ta ga ba ta ganin Ummu a online da wancan lambar kuma ta yi ta kiran wayar a kashe sai ta yi ma Shamsiya magana. Ita kuma sai ta ce mata Ummu ta sauya layi ne sannan kuma ta ba ta sabon layin na ta, sai dai kawai ta ga Madina Jafar ta yi mata magana suka gaisa ta kuma ce Shamsiya ce ta ba ta sabuwar lambarta.

Ba tare da izinin Ummu Salma ba Madina ta saka ta a cikin group ɗinsu na makaranta da sabuwar lambarta tunda su Madinan su ne ke jagoranta group ɗin, ba ta ma sani ba domin ta yi kwana biyu ba ta hau ba, ba kuma don ba data ba kawai dai wayar ce ta fita daga zuciyanta. Data sai tana yin expering a wayarta yayyenta da sun ga ba ta online za su saka mata kati ma ya fi na dubu biyar a wayarta ba wanda take kira da shi.

 Sai can da ta hau ne ta ga ta saka ta, tsoro take ji kar ya zo sun samu labarin abin da ya faru da ita, ba ta son ta zama abin dariya a wajen ƙawaye kamar za ta yi left sai kuma ta fasa lura da cewa kamar ba su sani ba, tunda Madina na yawan tambayanta ya Oga sai ta ce yana lafiya. Shi ya sa ta ɗan saki jikinta suke ɗan gaisawa kuma ba ta yi left a group ɗin ba.

Ranar da daddare ta kunna data suka yi video call da Hamma Abdulrahim har da Ammah da Baffa ma duk sun yi magana da shi ya zama kamar ɗan turawa saboda zaman turai yana ta murna shekara mai zuwa zai dawo gida ya gama karatunsa na likitan ci gabaɗaya.

Ta ga Baɗɗo ta yi mata saƙo da Madina amma ba ta duba ba sai da safe.
Baɗɗo lafiyanta ta tambaya ta ce tana lafiya saƙon Madina ne ya ɗan ba ta mamaki.

"Ya shirye shiryen biki?

Ta yi mamakin tambayan cikin mamaki itama ta mayar mata da tambayar shirye shiryen me?
Madinan ba ta online itama daga nan ta sauka ba ta sake hawa ba sai bayan kwana biyu.

"Bikin Bestie ki mana, ba farkon watan gobe ba ne ko an ɗaga ne?

Sakon da ta ga Madina ta tura mata kenan a gabanin tambayar da ta yi mata tun ranar.
Mamaki ya kamata,yanzu har bikin Shamsiya ya zo amma ba ta sani ba, wayance ma Madina ta yi da cewa ba ta gane tambayar ba. Ta so ta yi ma Shamsiyar magana sai kuma ta fasa a zuciyarta ta ce za ta tsaya ta ga ni shin Shamsiya za ta faɗa mata, in ba ta faɗa mata ba sai ta samu tabbacin zarginta na cewa ta ja baya da ita tunda ta zama bazawara sannan ba ta son yadda ta zama cukus ta je bikinta to in har hakane itama ba cewa ta yi za ta je ba Allah ya sa a yi lafiya a gama lafiya.

Abin ya dame ta amma ba ta faɗa ma kowa ba ta yi shuru da bakinta sai dai har watan ta gangara Shamsiya ba ta yi mata maganar ba ranar har ce mata ta yi har yanzu ba a saka date ba tace mata ba a saka ba, ai ta ce in har sun saka za ta yi mata mgana.
Tun daga ranar ta yi ma kanta alƙawarin ba za ta sake yi mata magana ba, in ma har an yi bikin ne ba ta fada mata ba, ba za ta zargeta ba sai dai ta yi kudirin za ta kirata a waya ta yi mata fatan alheri. Amma fa zuciyarta ta yi mata nauyi  yau wai Bestie ce ke gudunta to waye ya yi saura yanzu da ba zai guje ta ba.
Har Ammah ta ɗan fahimci tana cikin damuwa har sai da ta yi magana amma ta ce mata ba komai.

****
Thursday.

A farkon watan da cikinta ya shiga wata na takwas ta koma awo, ranar Ummin ikki ba ta nan ta je Mubi Baɗɗo ce za ta raka ta ita kuma an kira ta suna da test a makaranta sai ta tafi. Baffa ya ce Ammah ta rakata ta ce ba za ta je ba, da man shima ya san ba zuwan za ta yi ba saboda kawaici maganar cikin dake jikin Ummu ba ta yadda a yi maganar da ita in dai tana wajen saboda kawaici.

Ummu Salma Ita kaɗai ta je da aka yi mata awon sai da likitan ta sake yi mata faɗa kan yanayin kwanciyar da take yi, na ringigine da man wancan awon da suka zo da Ummin ikki sun ce kwanciyar jaririn jikinta ya jirkita kuma a wattanin cikinta ya kamata a ce kanshi ya dawo kasa, da yana kasan ne daga baya ne ya jikirta. Kuma ta ce saboda yanayin kwanciyar da take yi ne.

"Dr to yanzu ya zan yi?
Ta tambaya cikin damuwa, ba ta san wani abu ya samu cikin jikinta. Saboda shi ta rasa komai na ta 

"Kar ki damu in dai kika kiyaye irin kwanciyar da mai ciki bai kamata ta yi ba zai komai daidai in sha Allahu."

Ta faɗa mata ta daina kwanciyar ringigine gwara ma na gefe da gefe saboda lafiyan abin da ke cikinta.
Sannan sun ba ta yanzu bayan sati biyu za ta dinga zuwa awo tunda ta kusa haihuwa. saɓanin da sati uku ne.

Da za ta dawo Kekenapep ta hau ta dawo da gida, haka ma ta hau da za ta je Hamma Abdullahi ba mota a hannun shi sai mashin, ita kuma ba za ta iya hawa mashin a yanayin ta ba.

 Ta dawo gida wajen sha biyu na rana ta samu Ammah har ta gama abincin rana. Da man da yunwa ta dawo jikinta har rawa yake yi in ta na jin yunwa yanzu.
Sai da ta ci sannan ta ɗan kwanta saboda a gajiye take daga nan barci ya ɗauke ta.
Sai wajen biyu saura na rana ta iya tashi ta yi salla.
Haka kurum ta ke jin kasala jikinta ba daɗi zuciyanta tana ta tsinkewa sai ta ɗauko Qur'ani ta yi karatu, sannan ta ɗan samu salama Baffa ba ya nan sai Yamma ya dawo. Daga ita sai Ammah a gida kuma ba hira suke yi ba, kowa na ɗakin shi.

Misalin shidda na yammah tana cikin ɗaki ta ji maganar Hamma Abdullahi sai bayan ya bar gidan ne ta fito ta ga Ammah baki har kunne.

"Ammah Me ya faru ne?  Kamar muryan Hamma Abdullahi na ji yanzu?

Ta tambaya tana kallon Ammah.

"Baba ne ya zo yana faɗa  mini Yayanki Lamido ya kira shi, da cewa ya je filin jirgi ya ɗauke shi yanzu nan."
Ummu ta yi shuru ba ta yi magana ba.

"Zuwa ba sanarwa, ai da ya yi magana da ko gidan na shi an je an ɗan share"

Ammah ta faɗa tana miƙewa.
"Amma dai nace Baba ya yi ma matarsa mgana ya ɗan kaita ta je ta ɗan gyara gidan kafin ya iso "
Ummu ta ɗan yi yaƙe ba ta yi magana ba.
Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye tana tunanin abin da za ta dafa masa.

"Ummu ko na yi masa tuwo ne? Kin san yana so"
"Kai kuma yamma ta yi gaskiya."
Ita kaɗai take ta maganganunta
Ummu Salma na jin ta ba ta ce mata komai ba shigowar Baffa ne ya katseta sai ta juya tana faɗa masa halin da ake ciki.

"Ba laifi ga Ummu nan ta ɗan yi masa abinci nan da take yi mana na yan gayu."
Ya faɗa yana kallonta, mamakin Baffa ya hana ta magana wannan ne zai ci abincinta.
Ta ma san Ammah za ta ce aa ga mamakinta sai Ammah ta juya tana ce mata ta ɗan sama masa wani abun.

"Za ki iya ko?
Ba ta da magana in ta ce ma ba za ta iya ba Ammah ce za ta ɗaga hankalinta.

"Zan iya Ammah."
Ta faɗa a fili amma a zuciyanta sai ƙunƙuni take yi tana faɗin sai kawai mutum ya zo ba sanarwa da man halin shi ne ya yi ta abu gaban kansa.

Haka nan ta shiga kitchen chinese rice ta ce za ta yi, Allah ya sa akwai cefanen kayan lambu shekaran jiya Hamma Abdulrahaman ya kawo, amma sai da ta dafa ganyen zoɓo sauran nata ne ma da aka dawo da shi ta fito da shi tana yi musu zoɓo lokaci bayan lokaçi. Girkin kaɗan ta yi tunda suna da sauran taliya da miyan da Ammah ta dafa shi da rana, gogan ne ba zai ci ba tunda shi na musamman ne.

Bayan mangariba ta gama aikinta tunda gas ne Ammah na da gas na tsaye mai uku da electric da shi ake amfani, shi ya sa aikin ya yi mata sauri zobon ta zuba a wani jug na tangaran ta saka a firiza, abincin kuma ta zuba a ƙololin Ammah sabbi ne ma a kwalin su da ta je bikin Autan Umma Salamatu ne ta zo da su ko Baffa ba a taɓa sanya masa abinci a ciki ba amma yau Ammah ta ce ta ɗauko a zuba ma Lamiɗo a ciki.

Ta gama komai ta jera saman faranti sauran kuma ta zuba ma Baffa a ranta tana faɗin ai nima sai ubana ya ci tunda Ammah ba ta kanshi take yi ba.

 Har ta koma ɗaki ta yi alwala ta yi sallan Mangariba shuru ba Hamma Abdullahi ba ɗan Ammah, sai da Ammah ne da kanta ta leƙo tana ce mata ta kira mata Baba a waya ta ji ko lafiya ba su kariso ba ita wayarta kamar ba kati ta dai ki shiga.

Hakanan ta ɗau wayarta ta kira shi sai ga shi ta shiga ta ba ma Ammah suka yi magana.
Ashe Hamma Lamidon bayan an ɗauko shi daga filin jirgi gidan shi ya ce a wuce da shi zai yi wanka. Sannan ya ce ma Hamma Abdullshi ya koma gida in ya gama abin da yake yi zai tuƙo kansa zuwa gida.
Haka Ammah ta ke faɗa mata ita da Baffa da bai daɗe da dawowa daga masallaci ba.

Abincinsa Ummu ta kai masa ɗaki sai ya wuce can Ammah kuma ta bi bayan shi.
Ita kuma sai ta koma cikin ɗakinta da tsinin cikin ta a gaba wayarta na hannunta kamar an ce ta buɗe data sai ta ja sama ta kunna ba wasu saƙonni  ne masu yawa take samu ba tunda sabuwar lamba ce ba kowa ya santa da lambar ba.

 Sai dai saƙonnin da ta gani a group ɗin makarantar su ne ya ɗan ja hankalinta, kuma ta ga har tagging ɗinta an yi sai ta shiga.
Sai ta ga ana ta fatan alheri  da Allah ya ba da zaman lafiya.

"Ga wacce za ta dinga amsa addu'o'in ku nan."

Madina ta faɗa bayan ta yi tagging ɗinta akan an ce ana ta fatan alheri amarya ta yi shuru ba ta amsa ba.
abin ya sake ɗaure mata kai ganin Shamsiya ake tagging ana mata fatan alheri kasa wasu hotuna ne guda uku jikinta har rawa yake yi wajen dannawa ta buɗe hotunan domin ta ji suna ta cewa Allah ya sanya alheri ya kuma kai mu lokacin
Zuciyanta ya ba ta cewa auren Shamsiya ya zo ba ta faɗa mata ba.

Sai dai me katin biki ne ya fara buɗewa da farko.
Ba ta ko tsaya duba sunan angon ba ta fara duba date ɗin bikin jibi ne ɗaurin auren. Mamaki ya sake kamata da al'ajabi kenan da gaske ne Shamsiya ta ja baya da ita sannan da gaske ne zargin da take yi a kanta cewa tunda yanzu ta zama bazawara ba ta bukatar ta.

Tana ta hawaye ita kaɗai tana zaune da waya a hannunta.
Jikinta ya fara karkawa ne lokacin da hoton ƙasa suka buɗe. Sai ta ga kamar ko idanuwanta ke yi mata gizo ba gaskiya ba ne. Har sake murza idanuwanta ta yi ta sake ƙura ma wayar idanuwanta cikin fitan hayyaci.

Zuciyanta ne ya tsaya da bugu na lokaci ɗaya.
Me take gani haka?
Shamsiya ce da Habib cikin shigar alfarma a cikin hotunan nan guda biyu.
Ɗaya ya kwanto ta bayanta ya haɗe hannayensu a saman cikinta. Dayan kuma tana zaune a kan kujera shi kuma ya tsaya a bayanta suna masu kallon juna suna mirmishi cikin yanayin da amarya da ango kan yi a lokacin yin hotunan pre-weeding pic, tamtama take yi kamar ba Habib ta gani a jikin hoton ba sai dai kuma ina shi ne domin ba za ta taɓa mantawa da kamaninsa ba har abada.
Habib ne mijin da Shamsiya za ta aura?

"Kai gaskiya sun dace."
Ta ga saƙon wata Hamdiya"

Kar dai a ce Shamsiya Habib za ta aura tunanin da take yi kenan zuciyanta na sake tsinkewa.
Ko ba ta san Habib ba ne? Ko ba ta san Habib shi ne mijin da ta aura ba? To ai in mijinta ne a da a yanzu ba mijinta ba ne sun rabu. Ba kuma za ta ce Habib bai san Shamsiya ƙawarta ba ce, ba kuma za ta ce Shamsiya ba ta san Habib ba.

Dukkansu sun san juna, kuma shi ne za su yi aure! Da man shi ne mijin da ta samu lokaci kaɗan? Ko da man shi ne dalilin da ya sa ta ja baya da ita. Ta sani ta san Habib ne za ta aura ta sani kuwa.
Zuciyan Ummu ya daina aiki kwata-kwata kanta na sarawa ta ma rasa tunanin da za ta yi, wayar na hannunta addu'oin fatan alheri ke ta shigowa ga Shamsiya da mijinta Habib, tun tana tunanin mafarki take yi har ta gasgata a zahiri ne yake faruwa. Ta kashe wayarta yafi sau uku tana sake kunnawa amma still in ta sake shiga hotunan take gani hoton Habib da Shamsiya a cikin yanayin farinciki.

Ta kasa zama ta kai gauro ta kai mari a cikin ɗakinta. Tana jin har abin da ke cikinta yana juyawa tsabar halin datake ciki.

"A'a Bestie ba za ta auri Habib ba."

"Ba za ta aure shi ba."

Take faɗa tana kallon hotunan lokaci ɗaya tana faman girgiza kai. An ce kuka ma Rahama ne ta kasa kuka amma a kasan zuciyanta take jin wani irin zafi zafin da ba ta taɓa jin irin shi ba har ya ninka irin zafin da ta ji lokacin da Habib ya sake ta. Ta kasa gasgata gaskiyan abin da ta gani, in har auren ne da gaske to watakila Shamsiya ba ta san Habib ba ko shi ne bai gane Shamsiya kawarta ba ce, ga shi dai zuciyanta na cigaba da hasko mata hotunan su  a lokutan da Shamsiya da Habib suka sha haɗuwa tun kafin aurenta da shi har ma bayan auren amma wani shashi na zuciyanta faɗa mata yake kila dai kuskuren fahimta ne ba abin da idanuwanta ke ganin mata ba ne.

 Saboda ma ta samu tabbacin abin da ta gani sai  ta sake duba katin bikin ga sunan Habib Idris Mai imani nan raɗau a jikin katin tare da na Shamsiya.

"Aa No.."

"Ba gsskiya ba ne."

Ta faɗa kamar mahaukaciya. Ba ta yarda ba zuciyanta ba ta aminta da abin da ta gani ba tana bukatar wani ya yi mata karin bayani 
Jikinta da hannunta na rawa ta lalubo lambar Shamsiya ta kira ta amma kira sama da sau goma ba ta ɗaga kiran ta ba, in wayar na ringing tafiya yake yi da bugun numfashin Ummu Salma tsabar tashin hankalin data ke ciki.

Ganin da ta yi tana ɓata lokaci a daran nan a wannan lokacin take son karin bayani take kuma son sanin gaskiyan komai tun kafin zullumi da fargaba su saka zuciyanta bugawa. Wani dogon hijabin da take salla ta raruma ta saka a saman bakar doguwar rigar jikinta.
Har ta fito falo sai ta tuna ba ta ɗauki kudi ba sai ta koma da gudu ta yayo mu ƙaramar jakarta dake saman madubin dakin, tunda ta dawo daga asibiti ta ajiyeta a wajen wayarta na hannunta ta fito, takalmin Ammah dake kofar ɗaki wani na roba na zirga-zirgan tsakar gida ta zura ta fice daga gidan ba tare da tunanin komai ba, tana jiyo hiran Ammah da Baffa a turakansa amma ko waiwayowa ba ta yi ba, a lokacin hankalinta ya bar  gangan jikinta. So kawai take yi ta buɗe idanuwanta a cikin na Shamsiya ta nuna mata hotunan da ta gani ta ji shin abin da ta gani gaskiya ne ko ƙarya ne?

 Ba ta ko ganin gabanta kafin ta isa titi ba ta san adadin sau nawa ta ci tuntuɓe ba, amma ba ta damu ba Kekenapep ta tsayar ta shiga ta ce ya kai ta barraks road suna tafe amma ji take yi kamar ta yi tsuntsuwa ba ta taɓa ganin nisan gidan su Shamsiya ba sai a ranar suna isa tun daga kofar gidan ta san ana sha'ani domin get ɗin gidan ma yana buɗe ne ga motoci nan birjit a haraban gidan wasu har waje, ba ta damu da kowa ba, ita dai ta san ta fiddo kuɗi da ba ta san ko nawa ba ne ta mika mai nepep ɗin daga nan sai kawai ta tsinci kanta a falon gidan su Shamsiya akwai mata ga sunan da yawa amma idanuwanta ba su tsaya tantance fuskokinsu ba. Waige-waige kawai take yi ba wacce idanuwanta ke son gani irin Shamsiya.

"Wa nake gani kamar Ummu Salma."

Ta ji an faɗa daga bayanta tana juyowa sai ta ci karo da Anty marikiyar Shamsiya.
Mirmishin dole ta yi mata wanda ya tsaya iya saman fuskarta.

"Ni ce ina yini Anty"

Ummu ta faɗa tana sauke numfashi.

"Lafiya lau sannu Ummu Salma."

Ta faɗa tana kallonta daga sama har ƙasa.

"Ai na yi ta cewa Shamsiya za ta rako ni gidanku na yi ma Umman ki jajen abin da ya faru ban samu dama ba."
Ummu ta sunkyar da kai,  amma tana ta kalle kalle domin hango ta in da za ta ga Shamsiya.

"Allah ya kyauta na gaba. Allah ya zaɓa mafi alheri."
Ko amsata Ummu ba ta yi ba domin ba ta ita take yi ba.

"Kin samun kin rarafo kenan? Da man da na ga ban ganki ba Shamsiya ta ce ai kin yi nauyi."

Da gaske kenan Shamsiya za ta yi aure, amma dai da tabbacin Habib za ta aura ne ba ta sani ba kuma shi ta zo ta sani daga bakin ita Shamsiyar.

"Shiga ciki tana cikin ɗakinta ba ta ma daɗe da dawowa daga wajen gyaran kai ba"
Ko kafin Anty ta gama magana Ummu ta wuce ta zuwa cikin ɗakin Shamsiyar da dama ta san ɗakin.

 Kofar ma tana buɗe suna ta hayaniya ta san ta shiga cikin ɗakin kuma ta ga harda yayyen Shamsiyar a ciki amma wacce idanuwanta ke son gani ta nema sai ko suka haɗa ido tana zaune gefen gado ta buɗe kanta yan'uwanta na duba gyaran kan da aka yi mata.

"Kai Ummu kin rarrafo kin zo?

Badawiyya yayar Shamsiya ta faɗa bayan duk hankula ya dawo kanta.
Ita dai kawai tana yaƙe ne amma hankalinta da natsuwarta na kan Shamsiya.

Wato ta ce ba za ta samu zuwa ba ne saboda ta yi nauyi to ai ba ta yi ƙarya ba tabbas ta yi nauyi tunda ga nauyi nan a gabanta tana fama da shi.

"Bestie sannu da zuwa."

Shamsiya ta fada bayan ta taso zuwa gare ta har tana riƙo hannunta.
Ta kuma ja ta har gefen gado ta zaunar da ita, ita kuma kamar gaula ta zauna.
Suna ta yi mata sannu ta kasa amsawa kawai Shamsiya take kallo ko a jikinta sai jikinta ya bata  wata kila ba gaskiya ba ne Shamsiya za ta yi aure amma ba Habib ne mijin da za ta aura ba.

"To mu je ko mu bar Bestie ta gana da Bestien ta."

Badawiyyya ta faɗa tana tattara sauran yan matan dake ɗakin, wasu ta san su yan'uwan su Shamsiya ne wasu kuma ba ta ma tsaya iya gane su ba. Tunda in dai na kusa da Shamsiya ne ta san su kamar yadda itama ta san duk wani da ya shafe ta. Kamar yadda Shamsiya take zuwa gidansu itama haka take zuwa nan gidan wajen Shamsiya tun ma kafin ta yi aure.

Dukkansu suka fita sannan suka rufe ƙofar, suna fita Shamsiya ta kalle ta, tunda daman ita Ummu tunda ta shigo take kallon ta. 
Mirmishi ta yi mata irin mai ƙayatarwa nan kafin ta ce" Tunda na ganki na san cewa zuwa yanzu kin ji komai ko kin ga komai."

Ta faɗa tana mai yi ma Ummu wani kallo.
Cikin wani yanayi Ummu ta ce" Na ji mana, na ji za ki yi aure amma ba ki faɗa mini jibi ne bikin ki ba."
Ta faɗa kafin ta ɗan ja fasali.

"In ba ki so na zo bikin ki Bestie ba sai kin ɓoye mini ba nima a wannan halin ba zan zo ba ballatana har na na ɓata miki bikin ki."
Ta faɗa cikin rawan murya, tunani kawai take yi ba gaskiya ba ne , ko dai ita ce ba ta gani daidai ba ko kuma an samu wani kuskuren.

Shamsiya ta sake kallonta kafin ta kwashe da dariya.
Ummu ta yi jagale tana kallonta ganin tana yi mata dariya 

"Wai akan me kike magana?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana mikewa..
"Kin ce ma su Anty na yi nauyi shi ya sa ba zan samu zuwa bikin ki ba, alhalin ni ba ki faɗa mini ranar bikin ba."
Shamsiya ta sake kwashewa da dariya tana nuna Ummu kafin ta ce" Wai da man ba abin da nake tunani ya kawo ki ba?

"Me kike nufi?

Ummu Salma ta tambaya cikin shan jikin jikinta.

"Ba ki san abin da na ke magana akai ba?
Ko dai kin sani kin zo ki tabbatarwa ne kina yi mini alaye"
Ta faɗa tana mai kallonta cikin kurullah.
"Me me kenan?
Ummu Salma ta tambaya har bakinta na harɗewa.
Shamsiya ta dauko wayarta a gaban madubi ta yi danne danne ta miƙa ma Ummu wacce ta yi tsai tana kallonta.

"Karɓi ki duba."

Hannunta na rawa ta karɓa. Tana dubawa, sai gata ta sake ƙamewa a zaune.
Ba sabo ba ne a idanuwanta hotunan nan ne dai da ta gani ɗazu ta kasa gasgatawa.

"Ki yi ta yin gaba, hotuna ne ne ni da mijina in sha Allahu"
Hannun Ummu na rawa zuciyanta na bugawa, haka ta rika wucewa tana kallon hotuna kala kala sama da kala goma ba ta ko gama gani ba ta ɗago idanuwanta cikin wani yanayi tana kallon Shamsiya.

"Da ma. Da ma da gaske ne?

Ta faɗa cikin rawan baki da na zuciya.

"To da kin ɗauka karya ne?
Shamsiya ta faɗa tana ɗan dariya.

"Habib ne fa! Ko ba ki gane shi ba ne?

"Habib ne, na gane shi Sweety ba."

Shamsiya ta katseta cikin ba ta tabbaci.
Ummu ta kasa magana bakinta na rawa, tare da jikinta Shamsiya kuma ta ɗaure fuska tana kallon Ummu kallon kasƙanci.
"Ga shaida nan na nuna miki. Jibi uwar haka ina gidan Habib a matsayin matarsa in sha Allahu."
Ta sake faɗa tana sakin wani mirmishi.

"Habib fa! Habib miji."

"Kul ɗinki. Kar ki sake kiran shi da mijin ki domin Habib ba na ki ba ne nawa ne. Ummu Salma."
Ta faɗa tana taso mata a fusace
Kafafun Ummu har gara suka yi saboda jin abin da ba ta taɓa tsammani ba.

"Ban karya ta cewa ke kika fara sanin Habib kafin ni ba, amma zan baki tabbacin ni na baki aron shi har kika aure shi kika kuma yi zaman aure da shi."
Ta dawo gaban Ummu Salma ta tsaya sannan ta nuna  cikin jikinta da yatsunta guda ɗaya.

"Ni ce har na baki damar da kike da wannan cikin a jikin ki. In da na so da baki aure Habib ba, in da na so da yau ba ki rigani ɗaukan cikin shi ba"

Ummu ji take yi kamar mafarki amma da ta runtse ido sai ta sake ganin ta a gidan su Shamsiya kuma ga ta a gabanta tana faɗa mata wasu maganganu waɗanda ta kasa yarda da su.

"Ke Habib ya fara gani yana so, ranar da kika nuna mishi a matsayin saurayin ki na ji dama ace shi ɗin nawa ne, bani na fara kai kaina ga Habib ba shi ya kawo kansa gare ni da cewa sai da ya ganni ya san ba sonki yake yi ba sha'awarki ya ke ji, tun a lokacin muke tare muna soyayya a ɓoye, saboda ke ba zan hana zuciyata abin da take so ba Ummu Salma."

"Me ya sa to ya aure ni baI aure ki ba?

Ummu ta samu karfin gwiwan tambayan Shamsiya domin ko hawaye ma ba ta ji ya kawo mata ba zuciyarta ke suka tana hasaso mata wasu abubuwan, au da man Shamsiya ce masoyiyarsa da yake ta magana a kanta ita ko me ta yi ma su Habib da suka zaɓi su yi mata wannan yankar ƙaunar.

"Ina son Habib ina son abin da zai saka shi farimciki. Yana tsananin sha'awarki kuma yana so ya kauda wannan sha'awar ni kuma a gida ba za a bari na yi aure a lokacin ba. Shi ya sa na ba shi daman ya aure ki amma na shekara ɗaya ya yi amfani dake son ranshi ya sake ki zuwa lokacin ni kuma na shawo kan matsalata a gida.  Mun yi da shi ba zai bar ki ki samu ciki ba, amma sai da kika ɓata mana plan din mu."

 Nan ta shiga ba ta labarin duk yunkurin zubar da cikin da Habib ya yi mata da saninta domin tare suke shirya komai.

"Ki ma gode ma Allah na baki aron shi, ki kuma jinjina mini yadda na bari kika fara ajiye ƙwaan Habib a mahaifarki kafin ni, saboda haka godiya ya kamata ki yi mini Ummu domin na ba ki aron abin da na fi so a duniya."

Ta gama faɗa tana fuskanta ta. Ummu ta yunƙura ta miƙe tana jin ɗan cikinta na haɗewa waje ɗaya saboda halin da ta ke ciki, cikin ido ta kalli Shamsiya kafin ta ce" Ai ban neme da ki ba ni aron shi ba Shamsiya. Me ya sa kuka yi mini haka? Riban me za ku samu?
Ta faɗa cikin soyewar zuciya.

"Na samu riba, domin Masoyina ya biya bukatarsa, ni ma kuma na samu nawa biyan bukatar, ga shi za mu yi aure."

"Shamsiya mijin da na au"

"Haramun ne? Ai ya sake ki, kuma ko bai sake ki ba zan iya auransa in na ga dama. Amma ni ba zan iya zaman kishi dake ba shi ya sa nace ya sallame ki daga rayuwar mu."

"Da man ba don Allah kike tarraya da ni ba?

"A baya don Allah na ke zaune dake amma daga lokacin da kika auri Sweety na tsane ki Ummu Salma."
Ta dakata tana kallon Ummu da ta koma tana mirmishi kamar mahaukaciya

"Kuma na ja baya dake ne saboda bana son alaqar mu, bana son ki a rayuwata. Ki je ki cigaba da rayuwarki amma ki manta da kin taɓa sanina ballatana Habib. Mu zama kamar mun shuɗe daga tunanin ki."

Ummu ta girgiza kai ba za ta iya fassara a yanayin da ta ke ciki ba.
"Sannan kar ki damu kaf dangina ba su nan kin auri Habib ba, sun san shi ne kawai a matsayin sa na mijina."
Ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya cikin dariyan shaƙiyanci.

"Na gode, da man tabbacin nake son sani tunda kuma na same shi daga wajen ki ba komai."
Ummu ta faɗa cikin aro jarumta.
Kawai sai ta juya za ta bar ɗakin tana jin maranta na daurewa a waje daya, ga ɗakin na juyawa mata amma ta daure.

"Ba ki ji ba."

Ummu ta juyo tana kallon ta.

"Na so ki zubar da cikin nan,  watakila da kin iya samun wani wanda zai kwashe ki, amma kika yi taurin kai ki ji be ki fa yanzu? Wa zai kwashi bazawara mai ɗa, ɗan ma mai kama da ɗan shege tunda uban cikin ya ce ba ya so"

Ta gama faɗa tana kwashewa da dariya har tana tafa hannuwanta
Juyawa kawai Ummu ta yi ta fice daga ɗakin tana jan kafa, ita dai ta san ta bar gidan ta kuma yi tafiya mai nisa a hanya kafin ta samu abin hawa.

 Ta san kamar hankalinta ya gushe domin ba ta ma san har ta faɗi sunan anguwarsu ba, ita dai an sauke ta a bakin titin gidansu ta sauka ta ba shi kuɗinsa sannan ta yi tafiya zuwa gida da kafafunta.

Ba ta kuka ba ta komai amma tana ji kamar yau za ta bar duniya.
Masallatan anguwan har sun idar da sallar isha'i wasu ma sun daɗe da idarwa.
Ta shiga gida ba ta damu da Ammah ko Baffa su ganta ba.
Ba ta damu da su tuhumeta ba.

Kawai ta faɗa ne kai tsaye.
Hamma Lamiɗo na tsaye wajen ɗakin Baffa yana waya ya juya baya. Ba ta san shi ba ne sai da ya juyo shima ya ji ana ta jefa kafafuwa ne yaraf yaraf shi ya sa ya juyo.
Ido huɗu suka haɗa domin akwai hasken wuta a tsakar gidan.

 Mamakin ganinta yake yi ga ciki a gaba sannan yarkace-yarkace kamar ba ta cikin hayyacinta. Ta kalle shi cikin wani yanayi shi dai juyawa kawai ya yi ya cigaba da wayarsa ita kuma ba ma ta shi take yi ba da sauri ta faɗa falon Ammah.

Tana shigewa ya bi bayanta
Da kallo  cikin mamakin me ya fitar da ita a cikin wannan daran? Me ya same ta ya ga kamar ba ta da lafiya. Duk da fa ya daɗe bai ganta ba, ba haka take ba.
Sai kuma ya yi tunanin watakila ciki ne ya mayar da ita haka.

 Yana gama wayarsa ya  koma cikin ɗakin Baffa abinci yake ci aka kira shi a waya ya ta shi.
Ammah kuma ta shiga ciki ta je yin sallah. Komawa ya yi gaban abincin shi Baffa na gefen shi da man Ammah ce ke hiran bayan ta tashi sai ɗakin ya yi shuru.
Shi Lamido da man bai iya hira ba shi kuma Baffa sanin halin shi ya sa bai ma bata bakin shi ba 

Ammah na ɗakinta ta idar da salla ta ji kamar an shigo 
Ta fito haka dai daidai lokacin da Ummu ta shige ɗakinta ta rufe kofa.
Sai Ammah ta ɗauka ita ce ta fito falo ta koma, domin ba ta san Ummun ba ta a gidan ba, bayan fitan ta Lamiɗo ya zo suna ɗakin Baffa gabaɗaya.
Daga nan kawai ta fice ta koma ɗakin Baffa.

 Ummu ta sulale a kasan cafet tana jin zuciyarta na zafi kamar za ta mutu. Abubuwa suna gilma mata. Shamsiya da Habib.
Me ta yi musu da za su lalata mata rayuwarta haka?.
Shamsiya fa da suke ƙawance tun suna yara ita ce ta ci amanarta da namijin da ta ba ma Amanar rayuwarta.
So take yi ta daina jin zafin da ke ji a cikin zuciyanta.
So take yi duk wani damuwarta da take ji ta daina jin su, so take yi ta bar duniyan nan ko za ta samu yar salama.
Amsar kuwwan Kalaman Shamsiya sun kasa barinta ta huta, sun saka ta jin gwara kawai ta ji shuru gwara ta sama ma kanta natsuwan zuciya.

Miƙewa ta yi tana layi ta isa gaban madubi ta ɗauki reza sabuwa a cikin kwalinta ta buɗe. Rezan ba na ta ba ne na Ammah ne kwali ɗaya take siyab itama shekaranjiya cizgiya ne ya fito mata a gefen hannunta sai ta yi ma Ammah magana ta bata, bayan ta cire sai ba ta mayar mata ba sai ajiye a saman madubin ɗakin.

kallon kanta take yi a madubi tana tunanin yanzu rayuwarta ba ta da amfani hijabin jikinta ta cire ta na kallon cikin jikinta.
Ba amfanin ta haifa ma Habib yaro ko yarinyar dake cikinta domin bai cancanta ba, yadda zuciyanta ke zafi ne take son kawai ta hutar da kanta.

Ba tare da tunanin komai ba ta ciro rezan ta daidaita tsitsiyan hannunta na hagu za ta yanka lokaci ɗaya tana mai runtse idanuwanta hawaye na wanke mata fuska, sai ƙaran vibration ɗin wayarta ya dakatar da ita wayar na kan madubin ne, idanuwanta na ganin duhu amma sai da ta ga sunan mai kira, Sisna Baɗɗo ce take kiranta a lokacin da ba za ta saurare ta ba, a lokacin da ba za ta iya amsa wayarta ba.

Tana mai zubar ƙwallah wasu na fitowa wasu na ƙoran wasu ta sake daidaita hannunta 
ta yanka sai ga jini ya tsartsu, ta runtse ido tana jin wani irin zafin azaba na ratsa ta daga ƙafafunta har saman ƙwaƙwalwarta.
Sake yanka hannun nata ta yi a  karo na biyu  jini ya sake tartsuwa, ta sake runtse ido sabo da azaba mai raɗaɗin da ya dabaibaye jinta da ganinta tana gani jininta na zuba a kan madubi yana gangarawa a kasan cafet da gudu kamar an buɗe famfo.

Azaba take ji amma kuma tana jin daɗi yanzu za ta daina jin abin da take ji a cikin zuciyanta. Gwara ta mutu in ta mutu za ta huta.
Tana mai kallon kanta a madubi tana hawaye ta fara ganin kanta biyu biyu kafin ta ji jiri ya kwashe ta, ta yi baya  ta dafa gado amma ina ya rinjayeta, tuni idanuwanta suka hau lumshewa jikinta ya saki da ta kasa iya riƙe kanta
nan ta sulale ta faɗi kasa ta gefen hagu.

Hannunta kuma har a lokacin bai daina zubar da jini ba, ga rezan da ta yanka kanta nan a yashe a gefen ta 
Ta ji daɗi domin jinta da ganinta ya tsaya cak zuciyarta ta daina aiki ta daina jin komai ta samu salaman da ta ke fata.
Ta ji ɗif, ta samu natsuwa ta samu hutun zuciyan da take muradi.




*Janafty*