FARGAR JAJI

20

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

*20*

*DAAMA SPECIALIST HOSPITAL*
NO:70 72 Abubakar Atiku Rd. Jimeta Adamawa.
VIP:Room 23.

Ta daɗe tana jin wucewar iska a cikin kunnuwanta. Sannan kanta ya yi mata nauyi sosai tana ji kamar an ɗora mata katon dutse, idanuwanta take so ta buɗe amma ta kasa ji take yi kamar an danne idanuwanta nata da wani abu mai nauyin gaske. Tana ta ƙokarin motsa gangar jikinta lokaci ɗaya da fitar da numfashi sosai amma ta kasa jikinta ya tamke, ko ɗan yatsanta ba ta iya ɗagawa sai ma take ji kamar wuyanta ya rabu da gangan jikinta ne. Sannan bakinta da wani abu  an yi mata takumkumi da ya hanata damar iya sakin numfashi sosai.

Tana jiyo ɗan maganganu daga can nesa da ita amma ba za ta tantance komai ba, tana cikin kamar tsakanin rayuwa da mutuwa ne. Komai daga nesa take jin sa kamar ba a kusa da ita ba ne, tunani take ko dai ta mutu ne tana cikin kabari, tabbas ta mutu ƙasa ne ya danne ta da ya sa ta kasa motsa gangan jikinta.

"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."

Ta furta a cikin zuciyanta, tana ta ƙokarin buɗe idanuwanta ta kasa sai da ta daddage sannan ta samu nasaran buɗe kumburarrun idanuwanta da suka yi mata nauyi kamar an ɗora mata jakan duwatsu a sama, dishi dishi ta fara gani kafin ganin ta ya ɗan fara washe.

Farin POP ta fara cin karo da shi lokaci ɗaya da karamar farar fanka a sama tana gudu sosai, shi ne iskar da take jin ƙaran wucewarsa a a cikin kunnuwanta.
So take yi ta tuna abin da ya faru da ita amma ta kasa tuna komai, tunanin ta ya fi karkata da cewa ta mutu ne, to amma in har ta mutu to nan ba a cikin Kabari take ba, domin a cikin kabari babu rufin ɗaki sannan babu fanka.

A hankali a hankali ganin ta ya fara washewa. Daƙyar ta iya ɗan waiga damanta da hagunta, daga lokacin ne ta fahimci kamar tana asibiti ne domin a yanayin ɗakin ita kaɗai ne a kan ƙaramin gado sannan ta ga tsitsiyan hannunta guda ɗaya da ƙarin ruwa.

Me ya same ta? Me ta sa take kwance  a asibiti?
Tana so ta yi tunanin yanayinta na ƙarshe amma ta kasa, kanta ya yi mata nauyi kamar ba na ta ba.
Tsil ta ji daga gefen cikin ta, sai ta ɗan daga idanuwanta, ciki ta gani ya yi tsini a jikinta gabanta ya faɗi ras! A lokaci ɗaya kuma tunanin abin da ya sameta ya fara dawowa cikin kanta daki daki.

"Hasbunallahi wani'mal wakeel."

Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata ta gefe da gefen idanuwanta masu raɗaɗi sai a yanzu ta samu damar kuka sai a yanzu ne nadama da dana sani suka rufeta sai a yanzu ta ke tunanin da a ce ta mutu fa? Shike nan ta mutu a kafira sai a yanzu ta tuna da Baffa da Ammah, sannan sai a yanzu ne ta tuna da sauran yan'uwanta amma a lokacin idanuwanta sun rufe zuciyanta ta ƙuntata fatan ta kawai ta yi nesa da jin zafin zuciya da raɗaɗi burinta ta samu salama da raɗaɗin dake taso mata a cikin kasan zuciyanta. Amma ina haƙanta bai cimma ruwa ba, ga in da ta kare nan, wataƙila Allah ne yake son ta shi ya sa ya ba ta wata damar.

Ƙokarin tashi take yi amma ta kasa tana cikin wannan yanayin ne aka buɗe kofar ɗakin lokaci ɗaya wata nurse da fararen kaya ta bayyana a cikin ɗakin.
Cikin ruwan hawaye Ummu Salma ta ɗago kanta tana kallon Nurse ɗin da ta shigo.

"Laa kin farka?

Nurse ɗin ta faɗa tana kallon Ummu kafin lokaci ɗaya ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Ummu ta bi ta da kallo a tunaninta in ta ƙariso za ta ce ta taimaka mata ta zauna sannan ta cire mata wannan igiya mai takumkumi da yake hanata numfashi da magana.

Tana cigaba da ƙoƙarin tashi zaunen aka sake buɗe kofar aka shigo. Wannan karon ba iya mutum ɗaya ba ne,  likita ne akan gaba sanye da rigansu na likitoci da zugan wasu Nurses guda uku daga bayansa ciki har da wacce ta fara shigowa da farko.

"Ma sha Allah"

Ta ji ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙarisowa gaban gadon da take kwance.
Kallon shi ta yi da idanuwanta da suka shige ciki mamaki ta yi da jin abin da ya faɗa ba ta yi tunanin ma musulmi ba ne sai da ya sake magana sai ta sake shan mamaki.

"Sannu ko?

Ya sake faɗa yana kallonta da ɗan mirmishi a saman fuskar shi.
Bayan musulmi ne, ashe ma yana jin hausa ba ta ɗauka ma yana ji ba ganinsa jajir kamar bature.
Idanuwanta ta ɗan motsa tana cigaba da ƙokarin tashi ta zauna.

"Kina so ki zauna ne?
Ya tambayeta. Ita kuma sai ta lumshe idanuwanta ta sake buɗe domin ba zata iya ɗaga kan ta ba, ji take yi kamar kanta zai rabe gida biyu.

"Okay.."

Ya faɗa lokaci ɗaya ya kalli Nurse ɗin dake gefensa da ido kawai ya yi mata magana nan da nan sai gata ta nufo ta,  ta saka hannu ta cire mata abin da ya tare bakinta daga magana da shakar numfashi da kyau.
Sannan kuma ta cire mata zaren karin ruwan dake tsitsiyan hannunta na hagu, amma ba ta cire canula ɗin ba sai a lokacin ma ta lura hannunta ya kumbura sosai watakila an yi ta fama kafin a samu jijiyar ne.
Hannunta na dama Nurse ɗin ta kama za ta ɗan dago ta, ita kuma sai ta yi amfani da hannunta na hagu ta ɗan dafa gefen gado lokaci ɗaya ta ji wani mugun zafi ya ziyarce ta har ƙwaƙwalwa.

"Wash..!

Ta faɗa cikin fitan hayyaci murya a dashe.

"Sorry, ki yi a hankali kin san left hand ɗinta akwai  rauni."
Sai da ya faɗa haka sannan ta iya duba hannun nata na hagu, dai dai ta ɗan ɗagota ta zauna tana jin bayanta na sagewa saboda kwanciya.

Rabin hannunta na hagu yana nannade da bandeji ne, ƙura ma hannu ido ta yi tana kallo hawaye na sake biyo kumatunta kamar an buɗe famfo.

"Sannu ko?

Ta ji an sake faɗa sai ta ɗan dago tana kallon likitan lokaci ɗaya ta na ɗan gyaɗa kanta dakyar.
Kujera suka matso masa da shi wata fara ya zauna a gabanta, ɗaya Nurse ɗin ta miƙa masa Fayel ɗin Ummu Salma a hannun shi ya buɗe yana dubawa.

"Ummu Salma Hadi Baba right?

Dr. Ahmad ya faɗa yana sake kallonta ta cikin farin gilashin dake fuskarta.
Nan ma kai ta gyaɗa masa cikin karfin hali, jin ta take yi kamar ba ita ba komai na jikinta ya yi mata kamar ba nata ba.

Doguwar rigar dake jikinta ne na ranar da abin ya faru amma an yanke duka hannuwanta watakila da aka kawota asibiti ne wajen sauƙaka ma likitoci aiki ne ya sa suka yanke sannan mamaki take yi anan ta kwana ne? Tunda dai dai ta san lokacin da ta yi ma kanta illa, dare ne amma yanzu tana facing window ɗin ɗakin tana kuma ganin haske alamun kamar yamma ne ko rana.

"Ba abin da ke damun ki ko?

Ta ji likitan ya sake faɗa yana kallonta kuma da harshen hausa yake yi mata mgana.

Idanuwanta ta lumshe ta sake buɗewa alamun babu abin da ke damunta, sai nauyin jikinta da ciwon kai.
Dakyar ta iya buɗe baki ta ce" Kai na "

"Sannu."

"Da jikina kamar ba nawa ba."

Ta faɗa lokaci ɗaya hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuɗowa.

"Sorry duk zai bari in sha Allahu."

Ya faɗa yana mai kallonta.

"Ya hannun ki? Ba wani pain?

Sai ta ɗan bi hannun da kallo kafin ta ɗan gyaɗa masa kai.

"Babu."

"Ya kike jin cikin jikin ki? Ba wata matsala dai ko?

Ya tambaya yana mai sake nazarinta.
Yana kallonta a matsayim mai sa'a a halin da aka kawo ta, bai ɗauka za ta tashi ba.

"Babu,"

"Amma ina jin motsi."

"Lafiyan jaririyan dake cikin ki ne, mun yi miki scanning mun gamsu da cewa jaririn dake cikin ki bai shiga hatsari ba."

Ya faɗa yana ɗauko biro daga gaban aljihunsa ya fara rubutu a cikin fayel ɗin dake hannunsa.

"Ummu Salma."

Ya kira sunanta yana cigaba da rubutunsa.

"Naa'm"

Ta amsa cikin dashewar murya.

Shuru ya yi bai sake magana ba, ita kuma tana hawaye tana tunanin ita kaɗai ne? Ina Ammah ina Baffa? Ina sauran danginta? Ba ta gansu ba.

"Ina iyayena?

Ta faɗa gashin idanuwanta jike da ruwan hawaye.
Sai da ya gama rubutun shi sannan ya ɗago yana kallonta lokaci ɗaya yana mika ma Nurse ɗin dake gefen shi fayel ta rankwafa ta amsa cikin ladabi.

"Duk suna waje."

Ya faɗa yana nuna mata kofa.
"Suna jiran mu gama aikin mu sai mu ba su damar su shigo su duba ki."

Ya sake faɗa yana ɗan wasa da biron hannunsa.
Kuka kawai Ummu take yi hawaye har sun jika mata gaban riganta, wannan ɗacin da zafin da ta so ta kashe kanta saboda shi, shi ne yanzu ya taso mata yana yi mata maƙakin a kasan zuciyarta ga shi yanzu ta sanya iyayenta da yan'uwanta a cikin damuwa.

"Ummu Salma."

Ya sake kiran sunanta.

"Za ki iya tuna dalilin da ya sa kika tsinci kanki a asibiti?

Ya tambaya kai tsaye yana mai kallon ta.
Hawaye suka sake kece mata zata tuna mana. Za ta tuna cin amanar da ƙawarta Shamsiya ta yi mata tare da Habib, wadanɗa suka ba yar da guddumuwa wajen gurguta yau ɗinta da gobenta. Har a yanzu kalaman Shamsiya na yi mata amsa kuwwa  a cikin kanta ba za ta taɓa mantawa da abinda ya same ta ba, domin wannan baƙin cikin watakila in bai yi ajalinta ba, to har ta koma ga Allah yana nan a cikin zuciyarta kuma yana saka ma gangar jikinta ciwo.

"Kiin tuna?

Ya sake tambayanta 

Kai ta gyaɗa masa cikin kuka da hawaye, shessheƙa take yi tana jin zuciyanta na bugawa da sauri da sauri.

"Kin san cewa tun shekaranjiya da daddarre aka kawo mana ke ba kya numfashi?
Ummu ta kalle shi cikin mamaki.
"Tun shekaranjiya?
Ta maimaita a saman laɓbanta.

"Daƙyar muka iya ceto rayuwanki, ga shi kina da juna biyu ga shi kin zubar da jini kin shiga hatsari sosai da yasa ko bayan mun ceto numfashin ki, mun sanya miki oxygen amma ba ki farfaɗo ba sai yanzun nan."
Majina ta ziraro ma Ummu amma ta kasa iya wani numfashi.

Kuka kawai take yi hawaye suna zubowa wasu na sake kwaranya.
Nadama take yi, dana sanin me ya sa ta aikata abin da ta aikata? Lalle Allah na son ta da ya sake ba ta wata damar a karo na biyu.

"Kin yanka hannun ki sau biyu kuma yanka mai zurfi. Kin zubar da jini sosai da ya sa sai da ɗan'uwanki ya ba ki jininsa leda biyu muka sanya miki. Ba domin shi ba, da wataƙila wajen neman jinin lokaci ya ƙure har ki mutu bamu samu damar ceto rayuwarki ba."

"Allah sarki ɗan'uwa. "
Ta san ma Hamma Kabiru ne ya bata jininsa kamar yadda a baya ya taɓa bata jininsa.


"Me ya sa kika yi yunkurin kashe kanki Ummu Salma?

Dr Ahmad ya tambayeta kamar yadda yake a rubuce a jikin ɗan aninin dake jikin rigan likitancin jikinsa.

Kuka Ummu Salma ta fashe da shi muryanta baya fita, bai hana ta ba gwara ta yi kukan ko zuciyanta za ta samu salama.
Yadda take rera kukan ne, abin tausayin duk wanda ke kusa da ita yake kuma sauraranta. Kuka ne mai taɓa zuciya kukan nadama da bakin ciki.
Nurses ɗin dake gefensa har akwai wacce ta yi ƙwalla jikinsu duk ya mutu.

"Ke fa musulma ce, kin ta so gidan tarbiya da gata, ko daga yadda yan'uwanki suka cika asibitin nan saboda ke na shaida ke yar gata ce, wani dalili ne zai sa ki yi yunkurin kashe kanki? Kin manta duk wanda ya kashe kansa kafiri ne? Ko kin manta cewa da kin mutu a lokacin wutar jahannnama za ki shiga?
Tsoro da wani irin imani suka sake kama zuciyar Ummu, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin dake ɗakin.

"Komai ya faru dake ki gaya ma Allah Shi zai yi miki mganin komai. Mu musulmai ne mun san yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau yana cikin imani ne. "
Ya sake faɗa yana mai kallonta.

"Ina so ne, ina so ne na daina jin zafi da radaɗin dake cikin zuciyata."

Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka majina da hawaye na kwanraya.

"Me ya sa ba ki karanta Qur'ani ba? Me ya sa ba ki kira sunan Allah ba! Yana sane da halin da kike ciki, da kin daga hannun kin roƙesa salama da amimci da ya sama miki ba sai kin yi tunanin kashe kan ki ba Ummu Salma."

Kuka kawai take yi tana jin kamar ta  mayar da hannun agogo baya.

"A lokacin da kika yanke shawaran kashe kanki ba ki yi tunanin wannan ran dake motsi a cikin ki ba ? Da kin mutu fa? Da kin kashe rai biyu? Sannan kin manta da iyayenki da dangin ki? Kin yi tunanin yadda za su dauwama cikin kuka in har kika bar rayuwwansu? 

Ummu ta fara girgiza kanta tana cigaba da kuka.

"Mahaifiyarki ana taho dake ta faɗi, kina ciki muna ceto rayuwarki ita kuma tana kwance ana daidaita numfashinta."

"Wayyo Ammah."

Ummu ta faɗa kamar za ta shiɗe."

"Mahaifinki duk da ya yi dauriya amma kuka yake yi yana fargaba rasa ki, yayyenki maza duk da suna da jarumta sun shiga damuwa saboda ke, yau da ace kin mutu kina tunanin za su manta irin mutuwar da kika yi? To har abada ba za su taɓa mantawa ba."

Ummu na kuka tana numfarfashi, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin nan suna ta goge ƙwallah

"Kin yi sa'a. Allah na son ki ya sake ba ki wata dama. Ina so ki sani ki yi ta neman gafaran Allah ki kuma tuna kowani tsanani akwai sauƙi a wajen Allah."

"Astagafurullah"
"Allah na tuba."
Ummu ta faɗa cikin matsanacin kuka kamar ranta zai fita.

"Daga yau in tunanin kashe kanki ya sake zuwa cikin tunaninnki. To ki tuna da abubuwa guda uku, na farko yadda za ki koma gaban Allah a matsayin asararriya na biyu kuma halin da iyayenki za su shiga saboda ke. Na uku kuma ki tuna ke musulma ce, kuma duk musulmin kwarai yana da imani sannan ya yarda kaddara mai kyau ko mara kyau."

"Na tuba Allah ka yafe mini."
Take faɗa tana jin wani irin tsoro na sake shiga cikin zuciyanta.

"A matsayina na likitan da ya karɓi case ɗinki har ya ceto rayuwanki, shi ya sa na baki shawara sannan a matsayina na musulmi na tunasar dake abin da kika manta, in kin shiga damuwa ko baƙin ciki ki yi kuka har sai kin gaji amma ki yi addu'a ki karanta Qur'ani ki samu salama, kar ki yadda ki bari tunanin sake aikata irin haka ya sake shigarki, ki sani in a wannan karon kin rayu watakila na gaba ba za ki rayu ba Ummu Salma."
Ya gama faɗa lokaci ɗaya yana mai mikewa tsaye.

"Na gode Dr."

"Sunana Ahmad Salisu."

Ya faɗa yana kallonta.

"Ya isa haka, ki sassaita kukan ki saboda yanayin jikin ki."
Kai ta gyaɗa masa hawaye na kece mata.

"Allah ya ba ki lafiya."
Ta amsa da Amin
Kafin ya wuce nurses ɗin suka bi bayan shi jiki a sanyaye.

"Ku ba ma Family ɗinta damar ganin ta."

Ya faɗa ma Nursea ɗin kafin ya fice daga ɗakin su bi bayan shi.
Bayan fitan shi kuka Ummu Salma ta cigaba da yi har da shessheƙa.
Sai dai kukanta ya tsaya ne lokacin da ta ji an buɗe kofa ta ɗago jiƙakkun idanuwanta tana kallon kofar shigowa.

Sai da ta ga yan'uwanta suna shigowa. Wani na ture wani, Mami ce akan gaba sai Baɗɗo bayan ta Adda Suwaiba ce, sai Adda Ummu Sulaim, Sai iklima sai Umma Balki sannan mazan suka biyo bayan su.

Hamma Abdullahi ne ya shigo bayan sa kuma Hamma Mustpaha, Hamma Abdulrrahman sai Hamma Kabiru ne ya zama karshen shigowa. Ba Ammah ba Baffa haka Ummu ta faɗa a cikin zuciyanta, a tunaninta ko suna baya ne ba su shigo ba amma sai ta ga Hamma Kabiru da ya zama karshen shigowa ya rufe ƙofar sannan ba ta ga Hamma Jibo ba, sannan ba ta ga Hamma Saddam ba, shi da man baya nan ya koma makaranta.

Baɗɗo da Mami suna rige-rigen ƙarisawa gare ta cikin wani yanayi a saman fuskokinsu.

"Ma sha Allah. Sannu Daughter."

Mami ta faɗa tana zama gefen gadon data ke kwance har tana rumgumota ta gefen hannunta na hagu.
Jin ta a jikin Mami kawai sai ta saki kukanta wiwi kamar karamar yarinya nadama ya sake kamata ta.
Ta saka kowa ya zo, zuwam kuma ba na lafiya ba, ba kuma zuwan shiri ba.

"Shii is ok. Mun gode ma Allah tunda kin farfaɗo, kukan ya isa haka."

Mami take faɗa tana bubbuga bayanta.
Baɗɗo ma kusa da Mami ta zauna tana mai kallon Ummu idanuwanta cike da hawaye ga shi sun kumbura.
Tun shekaranjiya take kuka ba ta daina ba.
Sai aka koma ita ake ba hakuri ana lallashi.

"Sisna"

Baɗɗo ta faɗa tana mai riƙe hannun Ummu wanda aka cire ma ƙarin ruwa.

"Sisna me ya sa?

Baɗɗo ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka.
Ummu ma hawaye suka sake kece mata kamar an ɓude famfo.

"Ku yi haƙuri."

Ta faɗa a hankali bakinta na rawa.

"Shii. Ya isa nan asibiti ne."

Mami ta faɗa tana mai share ma Ummu hawaye da mayafinta jikinta har da majina.

"Bar kuka kin ji ko? Mun gode ma Allah da kika rayu."
Mami ta sake faɗa tana share mata hawaye.
"Mami."
Ta kira sunanta cikin dashewar murya da kuka.
"Naam My First Daughter."
"Ku yafe mini Mami."
Ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka.
Sake rumgumota Mami ta yi, itama hawaye sun kawo mata saboda tausayin halin da Ummu ke ciki.

"Ya isa, is ok kin ji.?

Ta sake faɗa tana mai ɗan tapping ɗin bayanta alamun lallashi.
Sannan ta sake ɗagota tana mai share mata hawaye da gefen mayafinta.

"Sannu Ummu kin auna arziƙi."

Umma Balki ta faɗa cikin wani yanayi.
"Amma dai abin da kika yi sakarci ne, gabaɗaya kin ɗaga mana hankali? Haka ake yi? Kan ki farau mutuwar aure?
Ta faɗa cikin faɗa, da man ita da Ammah ne a ɗakinsu suke da faɗa

"In da kin mutu fa? Wani hali iyayenki za su shiga! Jamila tana ganin halin da aka kawo ki rai ƙwai kwai ta yanke jiki ta faɗi yanzu in da ya zo da karan kwana fa? Me za ki faɗa ma Allah, ke kin kashe kanki bakincikin ki ya kashe uwar da ta haifeki duk saboda namiji? Namijin banza, namijin ƙanin ajali to ni a matsayina ta uwarki na ce in kika sake ma tuna wannan maci amanan ba mu yafe miki ba shashasha kawai."

Ta gama faɗa har tana nuna ma Ummu Salma ɗan yatsa wacce ta lafe a jikin Mami tana ta kuka.

"Umma ku yi haƙuri."

"Kaniyarki da haƙurin, sakarya, ba ki da tunani ne! Ina ilimin ki da hankalin ki yake Ummu Salma? Kawai ki yanka kanki kamar a wasan ƙwaiƙwayo"
Ummu kuka take yi har yana ba da sauti ga hawaye ga majina.
"Na yi nadama."
Ta ke faɗa muryanta na shaƙewa.

Mami ke lallashinta amma faɗan Ummu Balki ne ya sa kukanta yaƙi tsayawa.

"Umma Balki don Allah ki yi haƙuri a bar maganar nan tunda dai ya faru kuma an ci sa'a abin ya zo da sauƙi ba sai a yi hakuri ba."
Mami ta faɗa tana kallon Umma Balki.

"Ke ma Fatima kaniyarki? Ke ce ke ɗaure mata kugun ta yi sakarci sannana za a yi mata faɗa ba? Kenan ma abun da ta yi mai kyau ne."
Mami ta yi shuru jin an zage ta.
Su Hamma Mustapha da suke ɗakin sun yi shuru kamar ruwa ya ci su.

"Ki yi haƙuri Umma tunda muna asibiti ne."

Adda Suwaiba ta faɗa, itama tsaraban hararan ta samu da ya sanya ta kama bakinta ta yi shuru.

"Ai Umma abin da kika yi ya yi daidai. Ni ba domin na lallashi kaina ba, na so ne ina shigowa na falla mata maruka goma sannan na taka wuyanta sai ta kusa mutuwan da gaske sannan zan ƙyaleta."
Hamma Kabiru ya faɗa cikin kaushin sa.

"Yauwa, faɗa mata ina daɗin shi ai ko ba a mare ta ba, a yi mata faɗa shi dukan in ta warke a yi mata tunda ba ta da tunani haka kurum, kin tayar mana da hankali mun kasa sukuni da fargaba."
Umma Balki ta sake faɗa cikin yanayin faɗan ta.

"To a dai yi haƙuri tunda muna asibiti ne."

In ji Hamma Mustapha da ya faɗa yana kallon Ummu dake kuka kamar ranta zai fita duk tausayin ta ya gama kashe masa jiki.

"Ni ban taɓa tunanin Ummu za ta iya yin wannan sakarcin ba wallahi."
Hamma Abdullahi ya faɗa yana ɗan cije leɓensa na ƙasa.

"Ni wallahi wani takaici na ke ji in ma tuna akan wani sakarai wanda rayuwarta ba ta da amfani a wajen shi ta so kashe kanta. Wallahi ji nake yi kamar na kamata da duka."
Hamma Abdulrahaman ya faɗa yana mai jin takaici na taso masa.

"Don Allah ku bar wannan maganar har mu koma gida."
Mami ta sake faɗa tana kallon su Hamma Abdullahi.

"Gaskiya ko don natsuwar ita Auta."
Ummu Sulaim ta faɗa tana kallon Ummu cikin tausayawa.

"Sai fa mun faɗa mata Mami, mu dai kar ta yi sanadiyar mutuwar Ammah, in hakan ya faru wallahi ba za mu yafe mata ba."
Hamma Kabiru ya faɗa yana balla ma Ummu Harara kukan banza take yi, shi da za a bar shi da ya lallasa ta, in aka tsaya ana jin tausayinta gaba ma za ta sake aikata irin haka. Dukkansu suna wajen aikinsu ta ɗaga musu hankali ta sanya sun baro komai sun taho saboda ita.

"Hamma."

Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka.

"Ina Ammah?
Ta faɗa tana ware idanuwanta akan dukkansu.

"Tana gida tare da Ummi."

Iklima ta faɗa cikin sanyin jiki.
Halin da ta ga Ummu ya sake tsoratar da ita ga lamarin maza.

"Kar ki damu ba abin da ya same ta, suma ne ta yi tana farfaɗowa suka koma gida."

"Baffa fa?

Ta sake tambaya cikin muryan kuka.

"Yana gida amma Baba ya kira shi a waya ya sanar da shi farkawanki na san yana tafe."
Mami ta fada tana mai sake share ma Ummu hawaye.
"Ki daina wannan kukan, likita ya ce kar mu saka ki kuka, su na son ki samu hutu saboda jinin ki ya ɗan yi sama.".
Kanta ta ɗan gyaɗa, a tunanin ba su san abin da ya saka ta yanka kanta ba, ta ɗauka kawai suna tunanin saboda sakin da Habib ya yi mata ne.

Gabaɗaya suka yi ta masa sannu tana amsawa. Ba su wani daɗe ba mazan suka fita tunda ta farfaɗo zaman asibiti kuma ya kare, Baɗdo kawai aka bari da Mami, su Adda Suwaiba ma sun bi mazajensu zuwa gida tunda tun safe suna asibitin.
Ummu ta tambayi Baɗɗo karfe nawa ta ce mata biyar da rabi na yamma.
Sai ta ɗan runtse idanuwanta sannan ta sake buɗewa tana kallon Baɗɗo, an samu sa'a Umma Balki ta bi su Hamma Abdullahi zuwa gida.

Mami kuma mijinta ya kirata a waya sai ta fita daga ɗakin bayan fitan su ne Ummu ta kalli Baɗɗo lokaci ɗaya tana fadin" Yanzu kwana biyu na yi a asibiti ban san in da kaina yake ba?
Ta faɗa cikin sanyin muryan da ta disashe da kuka.

"E, tunda aka kawo ki kina emargency sai yau ne ma da safe suka kawo ki wannan ɗakin."
Ummu ta dukar da kanta saboda hawayenta da suka kawo 

"Allah na tuba."

Ta faɗa tana kecewa da kuka wannan karon Baɗdo aka bari da lallashi.

"Why Ummu Salma?
Akan Habib ko akan Shamsiya?
Da sauri Ummu ta kalleta cikin mamaki.
"Da man kin sani?
Ta tambayeta cikin raunin murya.

"Na sani, ai dalilin kiran da na yi ta miki a daran shekaranjiya kenan ba ki ɗaga kirana ba. Nima a status ɗin wata course mate dina na gani, ban taba tunanin Shamsiya za ta iya cin amanarki ba. Amma ban yi mamakinta ba, daga baya ta sauya dake sai da haka ta faru na fahimci dalilinta na kare ma Habibu ashe maciya amana ne."
Ta gama faɗa cikin bakinciki da takaici.
Kuka kawai Ummu ke yi kamar ranta zai fita.

"Na tsani Habib, na tsani Shamsiya. Ba zan taɓa yafe musu ba.'

Ummu ta faɗa majina na zilalo mata.

"Ki tsane su, amma ki fara cire su daga tunanin ki da rayuwarki gabaɗaya. Ba su da amfani kuma in dai amanace da suka ci taki su je ga su ga duniyanan nan da ikon Allah sai Allah ya saka miki."
Baɗdo ta sake faɗa itama tana hawaye

"Shamsiya fa? Ashe duk abin da Habib yake yi mini da sanin ta.".
Nan Ummu ta fara ba ta labarin yadda suka yi da Shamsiya a gidan su.
"Ni dai na san na dawo gida cikin baƙinciki, ina so na ji zuciyata ta daina kuka, baɗdo ban san me ya sa na yi tunanin kashe kaina ba ni dai kawai ina so na samu salama ne a cikin zuciya ta."
Ta faɗa tana mai gunjin kuka.
Baɗɗo ta rumgumeta ta gefe tana ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi.

"Ni ce na fara iskoki kwance jini na tsiyaya a hannun ki. Daman da na yi ta kiran ki baki ɗaga a daran na ce ma Ummi zan zo wajen ki, ina zuwa na samu Ammah da Baffa tare da Hamma Lamiɗo a dakin Baffa bayan mun gaisa sai na shigo ɗakin ki na iske ki kwance ba numfashi a tare dake nan fa na fasa ihu su Baffa suka rugo zuwa ɗakin ki."
Ummu na cigaba da tsiyayan hawaye tana sauraran Baɗɗo 

Baffa da Ammah sun shiga tashin hankalin da suka kasa iya baki wani taimako. Ba domin Hamma Lamiɗo na nan ba da watakila jininki ya tsiyaye mu ba mu samu mafita ba."
Cak kukan Ummu ta tsaya ta da kukanta ta yi kasaƙe tana kallon Baɗɗo cikin mamakin jin sunan wanda ta ambata.
Tabbas a ranar ya zo, amma ita tama manta da shi kwatakwata.

"Shi ya yanki zanin ki ya ɗaure hannun ki zubar jinin ya tsaya. Sannan shi ya ya ɗauke ki cak zuwa mota da ni da shi da Ammah da Baffa muka kawo ki wannan asibitin cikin tashin hankali."
Ummu ta sake ƙura mata ido cikin mamakin wai Hamma Lamiɗo ne ya yi mata haka? Da man yana da tausayi.? Ita kallon mara tausayi take yi masa wanda bai damu da kowa ba.

"Dakyar suka karɓe ki, sun ce case ne na hatsari suna bukatar yan sanda Hamma Lamido ne ya yi cuku cukun da suka karbe ki. An yi nasaran ceto numfashin ki amma suka ce sai an sanya miki oxygen kuma kina bukatar jini, ga shi Hamma Kabiru ba ya kusa ana maganar a je a duba a lab a ko za a samu wanda zai dace dake, kawai Hamma Lamiɗo ya ce jininsa O ne, nan take kuma aka je aka gwada shi ba wata matsala aka ɗibi leda biyu aka sanya miki a daran nan."
Ummu sai da ta yi yar shaƙuwa.

"Daman ba Hamma Kabiru ba ne ya ba ni jininsa ba?

"A daran ta ina Hamma Kabiru zai taho? Yau ne ma ya samu zuwa ba daɗewa. Hamma Lamiɗo ne ya ba ki jininsa Sisna, ni kaina lamarin ya ba ni mamaki ban taba tunanin yana da tausayi haka ba"

Ummu Salma ta haɗiye wani miyau a maƙwagaronta.
Jikinta take kallo tana jinjina kai wai akwai jinin Hamma Lamiɗo a jikinta yanzu haka.

"Kin ga farar shaddar jikinsa duk ta ɓaci da jinin ki, Baffa ya yi ta cewa ya je gida ya sauya bai tafi ba saboda faɗuwar da Ammah ta yi shi ya zauna da ita har asuba aka sallameta sai ya ɗauketa zuwa gida ni da Baffa kuma muka kwana dake sai da safe ne Ummi ta zo sannan ya koma gida."
Ummu ta share hawayenta da gefen hannunta na hagu, hannunta na dama take kallo dake dauke da bandage ya kumbura 

"Ɗinki aka yi miki. Likitan ya ce Allah yasa yankar bai yi zurfi ba."
Ummu dai sai sharan kwalla ba magana.

"Kin faɗa musu abin da ya faru ne?
Ta tambaya tana kallon Baɗɗo 

"Na faɗa musu, kawarki Shamsiya ce ta za ta auri Habib shi ne kika yi yinkurin kashe kanki."
Ummu ta runtse idanuwanta tana jin kalmar kashe kanta ita ta aikata amma nadamar take yi, tsanar kalmar take yi.

"Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrahaman sun yi ta faɗa, Baffa na fama da kansa bai ma yi musu magana ba zuwan Mami ne ma da ta yi musu mgana suka ɗan yi sauki da faɗan na su, amma kaf din su sun shiga damuwa ana kiransu a safiyar jiya suka cika asibitin nan tare da matan su, Mami ma ajiyan ta iso da rana. Hamma Jibo ne kaɗai bai zo ba saboda aiki Hamma Sadam na makaranta bana ma tunanin ya san abin da ya faru."

Ummu ta yi shuru kafin ta ce" Baɗdo na yi nadamar sanin Habib na yi nadamar sanin Shamsiya a rayuwata."
"Ki bar su da Allah, yau ne daurin auran an ma ɗaura tun dazu ta je ga ta ga Habib ɗin shima ga shi ga Shamsiyan in dai don sun tozarta ki ne suka samu damar auran juna. To da ikon Allah suma sai Allah ya tozarta su."

"Allah ya isa, ba zan taɓa yafe musu ba, sun lalata mini rayuwata. Me na yi musu?
Ummu ta sake fada tana kuka.
"Ba ki yi musu komai ba, ki dauka a haka a matsayin kaddaran ki. Ki bar masa faɗan shi zai saka miki "
Ummu ta cije lebenta na kasa tana jin wani irin turiri a zuciyanta. Ta tsani Habib ta tsani maza ma gabaɗaya dalilin shi yau take kwance akan gadon asibiti ta gode ma Allah da ya sake ba ta wata damar da yanzu ta mutu shikenan ta mutu a kafira ta yi asaran rayuwanta saboda Habib da Shamsiya da man burinsu kenan. In dai haka ne ba za ta sake ba su wannan damar ba, za ta cire su daga duniyarta har abada amma ba lalle ne abin da suka yi mata ya bace daga zuciyarta ba, har abada sun riga sun dasa masa ciwo mai wuyar warkewa a zuciyanta.

"Ki yi hakuri, ki yi hakuri amma don Allsh kar ki sake tunanin kashe kanki Ummu Salma."
Baɗdo ta faɗa cikin karaya.
"Ba zan kara ba, in sha Allahu ba zan kara ba."
Ta faɗa cikin kuka da hawaye shaɓe-shaɓe.
Suka rumgume juna Ummu na kuka da shessheƙa Baɗɗo na hawayen tausayin Ummu.
A haka Mami ta dawo ta same su, sai ta fara faɗan ya haka kuma? Ita Baɗɗo da za ta yi lallashi sai ta bige da kuka nan take tace su bari ba ta so.

Dole suka share hawayen su, sai dai ajiyar zuciya.
Sai mangariba likita ya dawo suka sake ɗaura ma Ummu karin ruwa sannan suka yi mata allura.
Mami ta koma gida da Hamma Abdullahi ya kawo Baffa ya duba Ummu ya sameta idanuwanta biyu tana kuka ta rirriƙe hannayen Baffa tana cewa ya yi hakuri.
"Bakomai Auta, na yi ma Allah godiya da kika kuɓuta ina sake masa godiya."
Da yakee an yi mata allura ashe akwai na barci ba daɗewa sai barci ya kwashe ta.

Baɗɗo ne da Mami suka kwana da ita, can dare Mami ta dawo da abinci da kayan da aka samu aka sauyawa Ummu.
Sai a daran Ummu Salma ta sha tea cikin ta ya warware sannan ta ɗan ci abincin kaɗan.

Washegari ma yan'uwa suna ta zuwa duba ta, don ma nurses ɗin suna hanawa, sai a ranar aka ɗan rike Ummu zuwa tiolet ɗin Mami ta ɗan yi mata wanka amma ba a bari ya taba hannun ba.
Bayan sun fito Baɗɗo ta kama mata suka sanya mata wata doguwar riga mai bubu, ta samu ta rarrafa ta yi rama sallolin da suka suɓuce mata daga zaune.
Wasa wasa sai da Ummu ta yi sati a asibiti sai da ta yi ras suka tabbatar da ba wata matsala sannan suka ba su sallama bayan an cire bandejin hannun ɗinkin ya fara shigewa ciki ya ɗan yi baƙi wajen  sun ce ta samu hutu saboda jininta ya hau da kuma lafiyan jaririn jikinta.

Har aka sallameta Mami ne da Baɗdo ke jinyarta
Ammah ta zo ta duba ta sau daya itama haka ta riƙeta tana kuka tana cewa ta yafe mata Ammah ta ce ba komai amma ta sani in ta kashe kanta saboda Habib ko Shamsiya ta sani ba za ta taɓa yafe mata ba.
Yan'uwan Ammah duk sun zo har su Umma Salamatu.
Bangaren su Baffa Umaru dai Baffa bai faɗa musu ba yace kar a tayar musu da hankali.
Hamma Kabiru da Hamma Mustapha sun koma wajen aikinsu tun kafin a sallami Ummu ganin ta samu sauki sosai.

 Ummu tana so ta tambayi Hamma Lamiɗo domin ba ta ganin shi ba tun bayan da ta farka amma ba ta samu hali ba, sai a daran da suka koma gida ta ji Ammah na faɗa ma Hamma Jibo a waya da cewa komai na asibitin nan shi ya biya. Ashe baya nan tun washegarin ranar da abin ya faru ya koma Lagos, amma yana kiran Ammah da Baffa yana jin yanayin da ake ciki.

Ummu Salma kunya take ji in aka ba ta waya za a gaisheta sai ta yi ta tunanin shike nan yanzu kowa ya ji labarin ta kusa kashe kanta. Har matar Hamma Lamiɗo ta kira a wayar Ammah an ba ta sun gaisa, haka ma Hamma Jibo da Adda Nauwara amma ba a fasa zahirin abin da ya faru ga kowa ba.
 
Hamma Saddam da Hamma Abdulrahim ba a gaya musu ba. Saboda suna nesa ba amfanin yayata maganar tunda lamarin ba mai daɗi ba ne.
Ummu ta yi nadama ko da yaushe kuka take yi tana neman gafaran Allah tun ballanta da Baffa ya kirata ya zaunar da ita ya sake tunasar da ita abin da ta manta.
Ya horar da ita hakuri da imani, Ammah kuma faɗa ta yi ta yi, domin daman ta ce tun lokacin da ta ji Shamsiya na wannan maganar ta ɗora mata ayar tambaya.
Ta kuma ce in Ummu Salma ta haifu to ta manta da Habib ballanta Shamiya har a gaban Ka'aba ta yi ma Allah kirari da kukan cewa Allah ya saka musu, yadda Habib ya wulakanta su shima Allah ya mayar masa da abin da ya yi musu.

Ita dai Ummu sai kuka ta yi nadama sanadin Habib ta goga ma kanta taɓo, yankan hannunta ko da ya fara warkewa har abada za ta koma ga Allah da wannan tabon a hannunta in ta kalli hannunta sai ta tuna da wannan bakar ranar.

Baɗɗo ta cika ƙawa kuma yar'uwa domin bayan ta yi jinyarta a asibiti da suka dawo gida kullum sai ta zo, makaranta ma daina zuwa ta yi a cewarta karatu kawai suke yi wacce suke tare ke saka mata attendence in za a yi test kuma tana yi mata, Ummu ta riƙe alherin Baɗɗo a cikin zuciyanta, tana fatan nan gaba kafin ta mutu Allah ya ba ta ikon da za ta iya saka ma Baɗɗo da tarin alherukan da ta yi mata.

Ba Baɗɗo ba hatta Ummin ikki ba ta zauna ba ita ke zaune da Ammah a gida lokacin Ummu tana asibiti. Ita da zuru'anta ba aminta ba sun zame ma Ammah ahali ita da ya'yanta da ƴan'uwanta gabaɗaya.

Mami dai wannan karon ta ce kafarta kafar Ummu Salma. Za ta ɗauke ta gabadaya daga Jimeta ta koma Kaduna a can kuma za ta haihu. Baffa ma wannan karon bai yi gaddama ba, shima zai so Auta ta ɗan yi nesa da wannan garin na wani dogon lokaci duka yayyenta ma sun amince da haka domin sauya muhalli da jama'a da yanayin iskar gari na kawo kwanciyar hankali. Ummun ma ta aminta daman ko Mamin ba ta ce kafarta kafarta ba ita za ta ce za ta bita domin ta gaji da Jimeta ji take yi gabadaya tana kuntace ne da zaman garin, da Umma Balki ce ta ce za ta tafi  da Ummun Mubi Mami ta ce Kaduna za ta tafi da ita har sai da ta ji haushi wai a cewarta ita kanta Mamin yarinya ce ba za ta iya kula da Ummun ba sannan biye mata za ta yi ba za ta yi mata faɗa in ta yi ba daidai ba. Baffa ya yi ta dariya ya na ce ma Umma Balki mai ɗa kamar Lamiɗo ne yarinya? Ta ce E mana ai auran wuri ta yi ta haife shi Lamiɗo ai ɗan yarinya ne. Baffa kamar cikinsa zai kulle Mami dai tana jin ta ba ta saka baki da man tun tana gida kafin ta yi aure a Kaduna in dai Umma Balki ta zo gidan sai sun yi tsiya ba ta gani ta ƙyale.

Baffa ya raba gaddama ya ce Auta ta zabi in da za ta je ita kuma ta ce Kaduna. Umma Balki ta ce Allah ya kiyaye hanya amma ba haka taso ba. Hamma Abdulrahaman ya ce itama dai Umma Balki da rigima nauyi kawai Ummu za ta kara mata, gwara dai Mamin ta tafi da ita can Kaduna zai fi. Haka ko aka yi tuni suka fara shirin tafiya Kaduna kayan Ummu masu dan kyau kaɗan Mami ta ce za ta tafi da shi sauran har na wajen Habib ta ce duk Ammah ta aika da su Mubi a kyautar da su in suka je can Kaduna za ta yi mata sabbin ɗinkuna. Alhaji Isa ne zai zo da yara ranar asabar in suka kwana lahadi sai su koma gabaɗaya tare da Ummun da Mami.

Shi ya sa ranar jumma'a da safe Mami ta ɗauketa suka je can asibitin da take awo Hamma Abdullahi ya kai su ta yi musu bayanin za ta tafi da Ummu tana son report na bayananta saboda in sun koma can in za ta fara zuwa sabon asibiti sai ta nuna musu. Abu na kuɗi ba daɗewa suka rubuta duka bayanan suka ba ta, wajen sha ɗaya suka dawo gidan nan Ammah ke faɗa musu Hamma Lamiɗo ya zo bayan fitan su ba daɗewa sun fita tare da Hamma Abdulrrahman.

Gaban Ummu sai da ya faɗi saboda jin sunan Lamiɗo, in ta tuna da shi sai ta tuna da cewa jininsa na yawo a cikin jinin jikinta sai ta ji wani iri a acikin zuciyanta.

Ita dai ciki ta shige ta ɗan cigaba da kimtsa kayanta, ta ɗauko tsohuwar wayarta bayan ta cire layin ta karya ta ba ma Ammah tace ta kyautar. Ta sake komawa ciki tana cikin har aka yi azahar Mami na falo suna ta hira da Ammah.
Ta idar da salla kenan ta ji shigowar su gidan ba ta ji dai muryansa ba amma ta san da shi tunda ta ji Ammah na kiran sunan shi 
Ba ta aikin komai yanzu tunda dai ba ta fara amfani da hannunta na hagu ba, duk da dai ɗinkin ya shige kuma wajen yana warkewa.

Saboda Hamma Lamiɗo ta ki fitowa ga shi tana jin yunwa ta so ta je ko kitchen ne ta samu abincin tunda Ammah ta gama shinkafa da miya tun ɗazu, amma ba ta son kallon Hamma Lamiɗo kunya take ki shi ya sa ta kasa fita, ta aikata abu yanzu kuma daga baya tana jin matsanacin kunya idan aka danganta ta da abin da ta aikata. Allah ya sa ma ba a yayata lamarin ba iya na gida ne da na jiki jiki na kusa suka san meke faruwa ko can su Baffa Umaru da suka ce sun ji cewa Auta ba lafiya sai Baffa ya ce kawai rashin lafiya ne ta yi, to babu amfanin faɗin komai tunda dai ba abin daɗi ba ne.

Haka ta naɗe yunwarta a cikin ɗaki ba wanda ya  tuna da ita tana jin hiransu a falo da alama ma abinci suke ci domin tana jin Hamma Abdullahi na cika baki da abinci yana magana yau daga Ammah har Mami sun manta da ita, to ai gwara Mami yau watakila ta sha'afa ne Ammah kuma yau tunda Lamiɗo ya zo ko Baffa sai ta manta da shi ba ma ita ba.

Tana cikin halin yunwar nan Mami ta shigo yin salla ita ce ta taimake ta, bayan ta idar ta ce mata yunwa take ji sai ta fita da sauri ta je ta zubo mata abinci ta kawo mata sannan ta fita falo ta ɗauko mata ruwan gora da ake ajiyewa saman frizan saboda Ummu ba ta shan ruwa mai sanyi ba duka ake sanyawa a firizan ba.

Tana jin Hamma Abdulrrahman na ce ma Mami wai tana shagwaɓa ta, ta kai mata abinci har ɗaki ruwan ma da shi za ta bita.

"Kafafunta ne ke ciwo? Haba Mami."

Amsar da Mami ta bashi ne yasa tana cin abinci sai da ta yi dariya sai da ta kusa ƙwarewa.

"Ina ruwan ka? Nan kuma Ammah ke rawan jiki da ku ban yi magana ba, ta manta da mai juna biyu, nima shine na miƙe na ke kula da ya'ta."

"Ah Mami ki ce dai kawai kishi kike yi da mu kawai."
Hamma Abdullahi ya faɗa yana dariya.
"Ku dai kuke kishi da Auta, ku ana kula da ku, tun shigowarku Ammah ta ba ku abinci ita mai yaron ciki ta manta da ita."
Ammah na dariya ta ce" To ba kin fanshe ni ba, ina nan ina ji da mazan ke kiji da macen ba shike nan ba."
Mami ta yi wucewarta ta bar suna mata dariya.

Lamido na zaune a gefe ko tak bai ce ba, dukkansu shigar fararen kaya suka yi. A saman cafet din Ammah suka baje suna cin abincin Lamiɗo salat kawai ya ke ci da miyan shinkafan kaɗan yake ɗibaa, duk hiran da ake yi ba kasafai yake saka musu baki ba.
Ko Mami sun gaisa irin gaisuwan da suka saba, ya tambayi su Islam tace ai za su haɗu gobe za su taho tare da babansu, ya kasa ce mata shi yau zai koma Lagos, sai kawai ya yi mata shuru.

Baffa kuma ba ya nan ma ba a masallaci ɗaya suka yi sallar Jumma'a da shi ba, da wuri ya tafi yace akwai wanda zai gani ne.
 Ita dai Ummu sai da ta gama cin abincin ta sha ruwa sannan ta ji ta ta dawo daidai, sai cikinta ya sake yin ƙasa saboda ta ci Abinci kwanciya ta yi ta gefe tana ɗan sauke numfashi ta kasa zama saboda tana jin cikinta ya cika.
Mami ne ta sake shigowa ta shiga tiolet tana yi ma Ummu sannu ta amsa dakyar.

Shigan ta ba daɗewa Ammah ta leƙo ganin Ummun kwance ya sa ta ce" ke kuma daga ci sai kwanciya."
Ummu ta yunkura ta tashi zaune kafafunta a kasan cafet duk sun kumbura.

"Ammah na kasa zama ne."

"Da dai kin daure."

Ta faɗa tana ɗan kallonta ganin tana ɗan cije baki.

"Sannu."

Ammah ta ce cikin tausayawa tana kallonta.

"Ga Lamiɗo nan zai wuce ya ce zai shigo ya sake duba ki.'
Sai Ummu ta fara kifta idanuwana saboda mamaki.
Hamma Lamiɗo ne zai ce zai shigo ya duba ta, abin da ba ta taba zato ba. Ta tuna wani lokaci a baya can tun ba ta yi aure ba, ta taɓa wani irin ciwo kamar za ta mutu na typiod , kowa ya yi mata sannu ya duba ta amma ban da shi, ita tana jin ma sannu na ciwo bai taɓa shiga tsakanin su ba.

Kafin ma ta yi wani yunkuri Ammah ta fita, ta miƙe dakyar domin ta nemi hijabi ta saka sai ga Ammah ta dawo bayanta kuma Hamma Lamiɗo ne ya sawo kai cikin ƙwarjininsa.

"Gata nan ai hannu ya ɗauko warkewa."

Ammah ta faɗa tana nuna masa Ummu Salma da ta sandare a tsaye ga ciki a gaba kanta ba ɗan kwalli wani tujajjan kitso ne da ba ta san ma daɗewar shi ba, tun dawowarta gida tana jin sau ɗaya ta taba yin kitso shima Baɗɗo ce ta ga kan ya tsufa ta tsefe ta ɗan yi mata duka baya guda goma kitson bai wani kamu ba, shi ya sa duk ya zare da wuri.

Ummu kunyar duniya duk ya kamata sai kawai ta dukar da kanta ta koma tana wasa da zaren adon rigan jikinta doguwa mai kalan purple.

"Auta ba ki gaishe da yayan na ki ba, jininsa ya cece ki daga mutuwa don kaniyarki"

Ammah ta faɗa cikin ɗan zolaya.

"Ina yini Ha. Hamma."

Ta faɗa cikin ɗan rawan murya.

"Lafiya."

Ya amsa a saman leɓensa.
Hamma Abdullahi ne ya kira Ammah daga falo sai ta fita ta bar Ummu da Lamiɗo a ɗakin. Tuni ta ji jikinta ya fara rawa, haɗa inuwa ɗaya da Hamma Lamiɗo ma tashin hankali ne zuciyanta taji tana tsinkewa kamar kasa ta tsage ta shige.
Shuru na mintina biyar ta ma ɗauka ya bar ɗakin ne tana ɗagowa suka haɗa ido, ya kafeta da kaifaffun idanuwansa hannayensa duka zube a cikin aljihun wandon farar shaddar jikinsa. Kafarsa akwai safa amma bai ɓoye zarazarab yatsun kafafunsa ba.

Da sauri ta sake sadda kanta ƙasa jikinta na sake ɗaukan bari, har ɗan cikinta sai da ya motsa.

"Ashe ba ki da wayau."

Ya faɗa cikin muryansa cike da ƙasaita 

"Ban sani ba "

Ya dire maganarsa yana mai kafe ta da idanuwansa.
Ummu ta kifta ido ta buɗe sai hawaye sharr suka kece mata ba ta son ana tuna mata shirmen da ta yi, ba ta so.

"Kin san abin da kika yi."
Numfashi ya ja kafin ya dire.
"Ya saka Ammah Suma."
Ya dire maganarsa abin na sukan zuciyansa. Yana tuna lokacin da Ammah ta zube a kasa a bakin emergency, ya ji tsoro ya kuma ji fargaban in wani abu ya same ta ya zai yi??

"Kina so ki kashe mini uwa ne.?
Ya faɗa ya ɗan ɗaga murya.
Wai uwa, itama ai mahaifiyarta ce.
Tuni har ta fara kuka har yana sauti

"In kin shirya mutuwa saboda wani rubbish, "
Ya dakata yana ɗan sauke numfashi domin ya fara harzuƙa in ma ya tuna dalilin da yarinyar nan ta nemi kashe kanta 

"To ki mutu, amma kar ki bari sanadin haka ya taɓa Ammah ko Baffa."

Ummu ta fashe da kuka sai ga ta duke ganin ta ƙasa durƙusawan zai yi mata wahala sai kawai ta baje a zaune tana kuka har da gunji. Mami na makewayi sai faman Uhm uhm take yi amma Lamiɗo bai saurare ta ba, bai ma nuna yaji ba.

"Hamma ka yi.."

"Will you keep your mouth shut."

Lamiɗo ya faɗa cikin murya mai amo da ta yi sanadiyar shigowar su Ammah ɗakin cikin mamaki, kafin ka ji muryan Lamiɗo a sama ahaka ana daɗewa sai in ranshi ya ɓaci ganin Ummu durkushe tana kuka ya ba su amsar tambayar su.

"Ai gwara kai ma ka yi mata faɗa yarinya kamar wacce ba ta yi makaranta ba? Har gobe in na tuna da abin da ta yi sai na ji kamar na mutu saboda bakin ciki. Baffa da Mami sun yi tsaye sun hana a yi mata faɗa."
Hamma Abdulrrahaman ya faɗa cikin jin haushi, shi ya ji daɗi domin har gobe bai huce ba tunda ba a bari ya yi mata duka ba.

"Me ya sa kike kuka?

Ya cigaba da mgana cikin kaushin muryasa.

"Me ya sa lokacin da za ki aikata ba ki tuna da komai ba.?
Ummu dai ta daina kuka ta haɗiye shi, tun tsawar da ya yi mata da farko.
"Tunda ya ce ba ya sonki ya sake ki."
"Dole ne."
"Za ki yi pushing kanki in to a relatioship ɗin da ba ki da amfani ne a wajen ne?
Are you Stupid? Ko ke ba ki da wata daraja  matsayinki ta ƴ'a mace ne?
Ya gama faɗa a jere yana haki cikin ɓacin rai.

"Faɗa ma ta dai Lamiɗo "

Ammah ta faɗa cikin bacin rai, ba ta ma son tuna abin saboda ɓacin ran da ta ke shiga 

"Ki sani kina da komai ba ki kuma rasa komai va saboda haka ki sani wannan abin da kika yi is a stupidity, kuma kar ki sake."
Ya faɗa har yana ɗaga murya.

"Domin in kika sake ba mgana zan tsaya ina yi dake ba. I will deal with you. "

Ya faɗa yana ɗan jinjina kansa.
Ummu kuka har da majina.

"Ku yi haƙuri."

Take faɗa, tana kuka Hamma Abdulrrahman ya cigaba da faɗa yana masifa.
Daidai lokacin Mami ta fito daga tiolet, cikinta ne ya karta tun ɗazu take Allah Allah ta fito, saboda ta ga an yi ma Auta taron dangi.

"A'a Lauya bari, shi ya yi na shi ya gama kai kuma sai ka ɗora naka! Wallahi ku fita daga idanuwana na rufe."

Mami ta fada tana isa gaban Ummu ta duka tana fadin" is ok ya isa yi shurun ki"
Hawaye take share mata da hannayenta.

"Fatima ki bari a yi mata faɗa don Allah."

Ammah ta faɗa da ya sa Mami ta tashi a fusace tana fadin" To duk ba an yi mata ba, kuma ta yi nadama don Allah ku ko kukan da take yi bai ba ku tausayi ba?
"Wani tausayi? Mu ma ai haka ta ɗaga mana hankali."

"To ta ji, ku fita kawai."

Mami ta katse Hamma Abdulrraahman tana nuna musu hanyar fita, Lamiɗo ya juya zai fita Mami ta jawo hannunshi tana fadin" Kai ne ka fara ko?  Kai ba ka san na saka dokar kar wanda ya yi ma Auta mgana ba? Kalli yadda ka sanya ta kuka juna biyu gare ta ba fa"
Mamaki ya kama shi sai kawai ya tsaya yana kallon Mami bai yi magana ba.

"Ammah ja zugan yayanki ku je falo. Ganin su ma firgita mini yarinya yake yi "
Ta faɗa tana sakin hannun Lamido ta juya ga Ummu.
Ya daɗe yana kallon hannun shi da ta rike, kafin ya juya ya bar ɗakin.

Ammah ta ce su fita kawai.
"Ke ma dai Fatima ki zama mai gaskiya "
"Gaskiyan kenan Ammah."
Ta faɗa bayan sun fice.
Nan suka bar Mami da zaman lallashi, Ummu ta yi ta kuka tana ce ma Mami ta yi nadama ba za ta kara ba..
Haka Mami ta yi ta masifa, da  hamma Abdulrahaman shi dai Lamiɗo ya gudu Hamma Abdullahi ya tafi kai shi filin jirgi.
"Wai ina ganin Basamuden ɗan Ammah da ba ya magana, shi ne zai zo ya tasa ya'ta yana yi mata faɗa, wallahi da ina kusa bai isa ba."

"Kar ku manta dai ya ba ta jininsa, ba domin shi ba da yanzu kina zaman makoki.,"
Ammah ta faɗa tana dariya.
"To sai me! Ai don Allah ya yi kuma ba a saka shi ba, da sai ya bari a saka mata na siya "
Ammah na ta dariyan Mamin ganin ta da karfin hali.
"Shima ɗana taimako ya yi, kuma fadan da ya yi mata na ta so kanta ne."

"To ina ruwan shi? Sai da ta warke ne zai  zo da wani tsawonsa kamar falla waya yana yi ma mutane faɗa "
Mami ta sake faɗa cikin kufululewa.

Ammah ta yi wucewarta ɗakin Baffa domin ta gyara tana ce ma Mami.
"Ku kuka sani dai Fatima."
Mami ita kaɗai ma faɗanta ta dinga yi.
Hamma Abdulrrahaman ya sulale ya gudu shima Abdullahi daga filin jirgi bai dawo gidan ba.
Faɗan da Mami ta yi ranar har dare, sai da Ummun ta koma ba ta hakuri.

"Gwara na tattaraki mu tafi can su daina ganinki, tunda Ammah ta daure musu kugu, Baffa kuma ba zaman gidan yake yi ba, balle ya tsaya miki "

Haka da Baffa ya dawo ta tare shi da cewa Ammah ta yi gayyar yayanta sun saka Auta kuka.
"Baffa har da wannan ɗan nata kamar basamude, shi ya fara zuwa ya yi mata kerere a gaba yana ta masifa, ashe karyan miskilanci yake yi tunda yana faɗa, Ammah na gefe da sauran yayanta suna cewa ya yi daidai."

"Ba su kyauta ba "

Baffa ya faɗa yana danne dariyansa.

"Ammah ce fa ba ta tsawarta musu ba."

"Ammah ma ba ta kyauta ba."
Ya sake faɗa yana dariya.
Ammah ta shigo ɗakin kawo ma Baffa abinci ta ce" An zo an kawo ƙarana kenan?
"E wai har da basamuden danki kika kira ya zo ya yi ma Auta faɗa."
Ammah ta kwashe da dariya Baffa na ta yata.
"Allah ya shirye ki Fatima."
Ammah ta faɗa tana ficewa daga dakin.
"Gwara ki dauki yarki ku koma Kaduna sai kun shekara ba su ganta ba, ina ce va shike nan ba, sai na ga wanda ya'yan Ammah za su yi ma faɗan"

"Ai Baffa ka bar su da ni, boko ce suke gwada mana, nima yar bokon ce sai dai mu buga ta."
Baffa na dariya sosai ya ce" A gaida Fatima Baba, Fatin Gwaggo. Yau da ma suna raye su ga yadda Ubangiji ya mayar da Fatin su."
Sai kuma suka koma tuna rayuwarsu ta baya tare da yi ma iyayensu addu'a daga karshe ma tare suke cin abincin Ammah ta sake dawowa ganin suna cin abinci ya sa ta rike baki tana fadin" Fatima kin zo kin ƙwace mini Baffa, miye nufin ki?

"Jibi za mu bar muku gidan."

"Umma ta gaida Aisha."
Baffa dariya kawai ya yi yana girgiza kansa.
Ammah itama zama ta yi suna cin abincin su uku daga faranti ɗaya, in ya kalle su sai ya tuna a shekarun baya shikenan raba faɗa a tsakanin Mami da Ammah, amma shaƙuwa ce mai tsanani a tsakaninsu, wacce ma alƙalami ba zai iya rubutawa ba.



*Janafty*