Chapter 13
🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀
By
AyshaNalado
Page 13
Kamar saukar aradu haka kalaman salman suka daki zuciyarta,cikin matsanancin bugawar zuciya ta zare manyan idanunta tare da watsa su a kan shi, bai kula da yanayin da ta shiga ba sai ma ƙarasowa cikin ɗakin da yayi ya nemi bakin gado ya kai zaune, cike da zumuɗi ya gyada kai tare da ce wa " Hmmm! yau naga abin mamaki da al'ajabi, gaskiya ba banza ba mutane ke haukacewa da son ganin bawan Allah nan, Innalillahi! wlh ya haɗu ta ko ina ne guy ɗin nan kaiii! miskiline na ƙarshen ƙarshe, ban ta6a ganin mutumin da murmushi ke bala'in yi mishi kyau kamar shi ba, kamshin turarensa kawai ya isa ya shaida maku shi na musamman ne, kyawun shi mai firgitarwa ne, takun shi abin kallo ne wallahi kamar wani basaraken bijimin zaki a dokar daji ,dole ka mata su haukace a kan shi, don ba su kadai ba hatta maza shagala suke da kallon sa."
Tun da Salman ya fara zubo bayanai, bakinsa ta tsurawa idanu tana kallo, babu abin da zuciyarta ke yi sai luguden daka, so take ta buɗe baki ta tambaye shi a ina ya ganshi amma ta kasa.
Salmah da take jin zancen Salman kamar wani almara ko tasuniyar gizo ne ta ce "You are not serious, mu zaka rainawa hankali, a ina ka ganshi da har ka mishi irin wannan sanin a gani na farko, ka kuwa san wa ka ke cewa ka gani, Mr AA kangiwa fa, haba haba dai in mafaɗin magana wawa ne ai mu majiyan ta ba wawaye bane kai dai barshi Kawai a kaji ana bada labari ka kwaso ka gaya mana, Mr AA kangiwa ya wuce duk yadda kake tunani."
Harara ya ɓalla mata tare da jan guntun tsaki "Tsiyata dake shegen kankanba aure bashi, ke da ko fuskar shi baki taba gani da kyau ba kike wani maganar banza, abin da baki sani ba sai ki ringa wani zaƙewa a kai, to bari na miki mai kankat, Mr AA kangiwa yayan Suraj ne, da mahaifin shi Gen. Idris kangiwa da Mother uwarsu ɗaya ubansu ɗaya." Ba Salmah da Aysha ba hatta Ammi dake rike da handle din kofar sai da abin ya dakar mata zuciya, kusan suman zaune Aysha ta yi wanda dama tunda Salman ya fara bayani ta nemi inda kanta yake ta rasa, a ranta sai maimaita sunan Suraj ta ke yi.
Ci gaba Salman yayi da cewa "ko ni kaina na shiga shock din da yafi wanda ku ka shiga, da farko na dauka karya ce sai da idanu na suka gane min shi ra'ayil aini a cikin gidan suna zaune a kujera daya shida mother, tana bashi damammiyar fura a baki, ba ku ga yadda Suraj ya ɗane jikin shi ba da sunan yana mai oyoyo ba, wlh kai na kwancewa yayi, mother da kanta ta gabatar dani a gurin shi da ya dago ya zuba min idanun shi kadan ya rage na saki futsari kwarjini gareshi kamar zaki, kallon 20 seconds ya min sai kuma na ga ya saki wani irin kayataccen murmushi na gefen baki wanda ya kusa tafiya da imani na, ya miƙo min hannu, alamar na zo, kamar mara laka haka karasa na bashi hannu, baku jo taushin tafukan hannunshi ba kamar auduga ban san sanda na lumshe ido ba, uwa uba kuma ga dadɗan kamshin shi daya cika falon, kusan suman tsaye na yi ba zato na tsinci maganarsa a kunne da husky voice ɗin shi ya ce “Salman Right? ai ba shiri na ware idanuna Suraj kuwa sai dariya yake min baku ga yadda ya ringa mai shagwaba ba wallahi lamarin ya tashi kaina."
A mamakance salmah tace "Dakata, Salman, wai wani Suraj din ma tukunna?”
"Suraj dai da kika sani." "kai I swear ban yarda ba." "Wlh tallahi da gaske ne in kin musa bari ma kiga hoton su a tare." Ya fada yana lalubar wayar sa a aljihu.
Hotunansa daya turo a wayar Suraj din ya shiga nuna mata, wani shi kadai wani shida Suraj da wasu da ba ta sani ba wani shida Mother ga dai hotunan barkatai sun fi ashirin, shi da familin shi makusanta, Wawan ajiyar zuciya ta sauke, a ranta ta ce “Tabbas shine.“ A zahiri kuwa cewa ta yi "To ya akai duk shakuwar ka da Suraj baka taba sani ba." Yace "bar dan rainin hankali wai shi bai gaya min bane saboda kar nace ba zan yi abota da shi ba." Wani hoto ta tsurawa ido da yafi daukar hankalinta, shi ne da wata mata da wani dottijon mutumi mai tsananin kama dashi sai kuma wata yarinya wacce take kama da matar sosai kamar an tsaga kara, kallon sani take ma fuskar yarinyar amma ta rasa a in da ta ta6a ganinta, kafin ta kai ga tambayar salman, Ammi ta shigo ɗakin bakin ta dauke da sallama, fisge wayar shi yayi a hannun Salmah yana gyara zama, bai ji daɗin shigowar Ammi ba don bai kai ga gaya musu abin da yake zumuɗin gaya musu ba.
Shigowar Ammi ne ya dawo da Aysha daga suman wucin gadin da tayi don ko batun hotuna da Salmah ke kallo bata san suna yi ba gaba daya tunanin ta ya tafi wani waje can dabam.
Kallon su daya bayan daya Ammi tayi har ta bude baki da niyyar yin magana akan abin da taji yanzu sai kuma ta fasa, bai kamata tayi magana a gaban su Salmah ba, zata bari sai sun ke6e da Salman din, canza akalar zancen ta tayi da ba su umarnin fitowa su yi dinner, Daga haka ta juya abinta zuciyarta cike da al'ajabin wannan lamari, bata karyata shi kuma bata yarda sosai ba, amma ta yanke shawaran zata tambayi Abie tasan idan ma hakan ne shi bazai rasa sani ba.
A dining suka tarad da Ammi da Abie , kujera suka ja suka zazzauna Ammi da kanta tayi serving din kowa, cike da nishaɗi Salman ke cin tuwan shi sai murmushi yake yi, albishir yake so yama Ammi da Abie akan gagarumar kyautar da Mr AA kangiwa ya basu shida Suraj amma tsoro ya hana shi, bai san yaya zasu karbi lamarin ba.
Salmah kam al'ajabi ne ya hanata sakin jiki ta ci abinci da kyau, kanta ya ƙulle tamau, yayin da Aysha rashin kwanciyar hankali da faduwar gaba ya hanata cin abinci, tsab Abie ke kallonsu yana lura da takun kowa, akan Salman ya tsaida idanunshi, yana kare mai kallo can yace "Salman lafiya dai wannan irin fara'a kamar wanda aka ba kyautar mota." Rass gaban shi ya yanke ya fadi, a tsorace ya dago ya kalli Abie can kuma ko me ya tuna sai ya saki murmushi yana ɗan sosa kewa, murmushi Abie yayi yace "to naga fara'ar ce taki karewa, nasan dai kyuatar mota kawai za'a maka ka ringa irin wannan farin cikin haka."
Rasa abin cewa yasa ya kyalkyale da dariya, duk dagowa sukayi suna kallon shi, Abie ya ce "tofahh!" Yana rike haɓa.
"Abie yau ji nake kamar an min albishir da Aljannah, Abie kasan wani abu wai Ashe Suraj kanin Mr AA kangiwa ne." Zaro ido Abie yayi cike da mamaki yace "wane Suraj din."
"Suraj abokina, yau da na je gidan su na ganshi har..." Sai kuma yayi shiru, Abie yace "ikon Allah, amma kuma ni ban san yana da ƙane namiji ba."
"Ba Maman su daya ba, Maman Suraj ita ce kanwar Gen Idris kangiwa." Abie yece "ikon Allah Ashe surajo dan gida ne, rashin sani yafi dare duhu."
A haka suka ci gaba da cin abincin Salman na ta basu labarin, makudan kudaɗen da ya bayar a rabawa mutanen dake tsatsaiye suna jiran fitowar shi abin sai da ya basu mamaki baki daya kudi ne bana wasa ba, murmushi Abie yayi ganin yadda duk suka rude ya ce "to ai hakan ba komai bane a gurin shi, don ya dauki irin wadannan makudan kudin ya ba mutum daya kyautar su karamin abu ne a gare shi daga shi har mahaifin shi haka suke shi yasa ko cikin yan siyasaa suka fita dabam." Ammi tace "hmmmm lallai kuwa Allah ya basu."
Kallon salmah , Salman yayi yace "yawwa sister ina tambayar da kika ma Abie shekaran jiya."
Duk i zuba mai ido duk su ka yi, ya ci gaba da cewa, “ Da gaske fa kamar yarinyar nan ta fiki gaskiya, domin da kunne na na ji Suraj ya kira sa da Yaya B, kuma ya amsa, ni sai yanzu ma abin ke dawo min, ina da tabbacin Yaya Babangida ya ke nufi.” Ya karshe maganar cike da confidence.
Zaro idanu Salmah ta yi gabanta na wani irin faduwa, ta ce "ka rantse da Allah."
"Bangane na rantse da Allah ba." Yana aika mata harara, sai lokacin ta gane ɓaram ɓaramar da ta ku sa yi, cikin pretending ta kalli Aysha ta ce " Lol! Kin ji ko Sister shikenan Sahla Balarabe ta yi winning ɗina dama bet muka kulla." Ta karshe maganar tana yar dariya.
Kallonta Abie yayi ya saki guntun murmushi tare da dauke kai.
A'ishatu kam tunda ta ji abin da Salman ya fada, ta daina fahimtar komai, tuni kanta ya fara juyawa ta rasa a sama take ko kasa, har suka kammala cin abincin bata san me suke cewa ba.
Abie ne ya fara barin dining din, Ammi tabi bayan shi. Ajiyar zuciya salmah ta sauke kamar kazar da aka ɗagawa wuka a maƙogaro, Dama Allah Allah ta dinga yi su tashi don tun dazu ta lura da yadda gaba daya Aysha ta fice daga hayyacinta, tsoro ta ringa ji kar tai wani abin da zai jawo musu zargi, ganin sun shige yasa ya tashi da sauri ta kimtsa dining din, ba tare da ta kula salman dake ta yi mata surutu ba ta kama hannun Aysha ta mikar da ita, ba musu ta bi ta, kamar wata sakarai, dakin su ta nufa da ita suna shiga ta maida kofar ta rufe tare da murza key.
Kallon juna suka yi, cikin rawar murya ta ce "Salmah kin ji ko a she shine Babangida,dama ni zuciyata ta bani, cewa shine, Salmah ki dubi yadda yake rayuwa cikin kwanciyar hankali cike da ɗumbin nasarori bayan ya tarwatsa nawa farin cikin." Tana gama faɗin haka na ta fashe da wani irin kuma mai ban tausayi, da saurin Salmah tafaɗa jikinta ta rungume ta tana bubbuga mata baya alamar rarrashi.
Kuka ta yi sosai, ba tare da ta kula da rarrshin da Salmah ke mata ba, ji take a lokacin zuciyar a lokacin kamar zata faso kirji ta fito, babu abin da take yi sai iza mata wutar ɗaukar fansa, a hankali ta tsagaita da kukan da take, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta dau tsawon lokaci a haka kafin ta dago ta watsa Salman runanun idanunta, ta daure fuska tamau babu alamar fara'a ko dariya a kausashe ta ce " ki zama shaida yar uwata Salmah, wannan hawayen dana zubar, shine na karshe da zan zubar akan Babangida, ada na dauki alwashin a duk sanda na hadu da shi, baza mu rabu ba saina dauki ranshi da hannuna, but a yanzu na canja shawara, bazan kashe shi ba saina bari ya ɗanɗani bakin cikin duniya, sai na fallasawa duniya cewa shi ɗin mugun ne mara imani mara tausayi mai tarwatsa farin cikin wasu domin gina nasa butulu ne shi wanda yake saka alkhairi da sharri, a karshe kuma sai ya girbi abinda ya shuka da hannunwansa."
Da sauri salmah da tunda Aysha ta fara magana jikinta ke rawa zufa na karyo mata, ta kai hannu ta dafe bakin ta,cikin tsananin tashin hankali tace "baki da hankali wai A'ishatu, wannan wace irin magana ce haka, wani irin zuciya ne a kirjin ki haba sai kace ba musulma ba, Shin kina da cikakken tabbacin B din Babangida yake nufi kamar yadda Salman ya faɗa, ki bari mu bi komai a sannu fa Aysha kar mu yi gaggawa."
Buge hannunta Aysha ta yi kafin a fusace ta ce "Shin dama kin nemi dana baki labarina domin ki karya min gwuiwa ne Salmah?"
Da sauri Salmah ta girgiza kai, ta sake cewa "Shin bake ki ka ce zaki taya ni na dauki fansa akan Babangida?" Sake girgiza kai Salmah ta yi, Alamar E , "To me ya canza mini ra'ayi?" Ta fada cikin tsattsare ta za rinannun idanunta. Shiru Salmah ta yi ta kasa amsa yayinda Zuciyata ke wani irin bugu na wuce misali, girgiza kai Aysha ta yi bayan ta dauke kai daga kallon Salmah, ta ci gaba da cewa, “ A tunani na sai kin fini daukar zafi idan gaskiya ta yi halinta, Amma abin mamaki sai gashi kina neman tankwarar da ni.“
"Ba canza ra'ayi na yi ba A'ishatu ina nan akan bakata zan taya ki zan taimaka miki har sai kin dauki fansa akan shi, amma dan Allah da manzonsa ki daina cewa zaki kashe shi da hannunki, bana son ji yana tada min hankali,insha Allah baza ki taba zama silar rasa rayuwar wani ba."
Murmushi takaici da bakin ciki ta sake tare da dafa kafadar har ta bude baki za ta yi magana sai kuma tayi shiru, da sauri ta juya ta fada kan bed tare da kife kanta tana sakin wani irin nurfarfshi.
Juyawa salmah tayi da sauri ta bar dakin hankalinta a tashe kitchen ta nufa ta bude kofar kitchen ɗin wanda idan mutum ya biyo zai fitar dashi backyard din gida. bata kula da rashin takalmin dake kafar ta ta ringa zuba sauri, sai da ta tabbatar tayi nisa da asalin part din su, sannan ta ciro wayar ta, Yaya Anas shine lambar data laluba hannunta na rawa, babu bata lokaci ta danna mishi kira, ringing biyu ya ɗaga.......
Kuna fahimta ko dai har yanzu kan ku ƙara murfi yake😅