FARGAR JAJI

21

by @jamilaumarjanafty

*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

*21*

Washegari asabar Alhaji isa ya iso Jimeta tare da Islam da Faruk. Mami da kanta tare da Hamma Abdullahi suka je filin jirgi suka ɗauko su zuwa gida.

A shashen mazan gidan daman ya kan sauka in ya zo duk da in kwana ya kama shi hotel yake tafiya yau ɗin ma a bangaren su Hamma Saddam Mami ta sauke shi sai bayan ya ci abinci ya natsa sannan ya shigo cikin gida suka gaisa shi da Amma, Baffa ba ya nan ya je cikin garin Jalingo sai can yamma ya dawo tare suka yi sallar mangariba da Alhaji isa har isha'in ma daman abokan kasuwanci ne tun a baya sannan megida ne da yaronsa. Yanzu kuma har da surukanta da ya haɗa su dalilin auran Mami, duk da hakan zumumcin da ya haɗa su bai yanke ba yau ɗin ma bayan sun dawo daga masallaci a tsakar gida Ammah ta yi musu shimfiɗa ta kuma haɗe musu abinci waje ɗaya suka zauna suna ci suna hira, irin ta su ta masu kasuwancin ƙarafa da siya da siyarwan motoci daga jin yadda suke magana a tsakaninsu za ka fahimci akwai kyakyawam alaqa a tsakanin su.

Mami kuma da Ammah suna falo suna kallo tare da Faruk jefi-jefi suna taɓa hira a tsakanin su, Ummu kuma tana cikin ɗakin ta tare da Islam sarkin surutu tunda suka iso tana makale da ita tana yi mata zence, ta sha labarai kala-kala har sai da ta gaji, tamboyoyi har ta gaji da amsa mata su. Tun a can Kaduna Babansu ya sanar da su Ya Ummu za ta koma gidan su da zama to fa suna sauka ɗakinta ta fara zuwa tambayanta na farko shi ne.

"Ya Ummu wai da gaske gidanmu za ki koma da zama?
Ummu Salma na mirmishi ta ce.
"In sha Allahu Islam."

Nan fa ta fara murna da tsalle, Islam yarinya ce mai shiga rai, tana da son mutane da mgana kamar Mami yar kimanin shekara sha biyu 12, Faruk kuma ɗan shekaru bakwai ne 8, shi bai da surutu sai dai rigima ce da shi sosai kamar yaron goye.
To duk bayan mintina sai ta zagayo ta ce"Ya Ummu da gaske za ki bi mu gidanmu?
In ta amsa mata da E bai hana anjuma ta sake dawowa da irin wannan tambayan har sai da ta gaji da amsa mata. Mami ma cewa ta yi ta kore ta daga ɗakin ta ce a ƙyaleta, ganin ta da surutunta na sanyata nishaɗi, kuma ta tabbata ko can ta je islam da Faruk ba za su barta ta yi kewa ba, domin samun yara a gida yana haskaka gida tare da samar da walwala ga mazauna gidan gabaɗaya.

A can tsakar gida kuwa bayan su Baffa sun gama cin abinci sun wanke hannuwansu a roban wanke hannun da Ammah ta ajiye musu, suka ɗan shiga hiran yadda kasuwancin siyar da tsoffin karafan motoci ya yi kasa yanzu ba kamar a baya ba, Baffa na mganar kasuwancin motocin da sabbin ƙarafan ma sun fi tafiya a yanzu shi kuma Alhaji Isa na sake kora masa jawaban, tun da shi dila ne kamfani guda gare shi na siyar da motoci wani lokacim ma su Baffa kan siya motoci a wajen su in hakan ta kama.

A cikin hiran ne Baffa ya kalli Alhaji isa cikin nisawa kafin ya ce" Alhaji ina son mgana da kai, duk da na san kun gama mgana da Fatima amma amatsayina na wakilin Fatima, uban Ummu Salma ya kamata na yi magana da kai."

"Ina jin ka ina fatan ba kan maganar zaman Ummu a wajen mu ba ne ko Baffa?
Tunda shima Baffa yake kiran shi tun ma kafin aure su da Fatima, abokan kasuwancin Baffa duk da wannan sunan suke kiran shi.

"Akan maganar ne."
Baffa ya amsa masa cikin ɗan sanyin magana.

"Haba Baffa, ai ina ce mun wuce haka a tsakaninmu. Ko ban auri Fatima ba ni mai riƙe Ummu Salma ne, ballantana ina auren Fatima. Ba ka da sauran haufi ko tsoro. Ummu Salma za ta samu sauyin rayuwa tare damu na ba ka tabbacin yadda zan yi ma Islam da Faruku haka zan yi ma Ummu Salma. Sannan haka itama Fatima saboda haka ka kwantar da hankalinka ba abinda zai sake faruwa da yardan Allah."
Yana mgana Baffa na ta gyaɗa kansa cikin gamsuwa.
Yana direwa ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce.

"Na gode sosai, Ubangiji ya yi ma arziƙin ka albarka. Da man tsoro na ke ji, kar Auta ta sake tunanin kashe kanta a karo na biyu"
"Hakan ba zai sake faruwa ba in sha Allahu."
Alhaji Isa ya sake ba shi tabbacin sa.
"Allah ya sa haka. Ubangiji ya sa tafiyarta ya zama mabuɗin alherin rayuwarta."
Suka amsa da Amin a tare, tare da su Ammah daga cikin ɗaki domin sun rage ƙaran talabijin ɗin Faruk ne ma ya matsa sai da aka mayar masa da tashar carttoon, shi ya sa hankulansu ya ɗan karkata kan mganganun Baffa da Alhaji Isa.

Wajen goman na dare Alhaji Isa ya tafi makwanci ya kwanta daman jirginsu karfe sha ɗaya na safe zai ta shi zuwa Kaduna.
Shi ya sa sai wajen goma ya zo gidan abin karyawa ma tun a waya ya ce ma Mami kar ta wahalar da kanta, ya riga da ya yi breakfast a hotel ɗin da ya kwana.

Ko da ya zo gida cike da yan sallama.
Ummin ikki da Baɗɗo, tare da matan su Hamma Abdullahi da yayan su, Hamma Abdullahin ma yana nan tunda shi zai kai su filin jirgi, Hamma Abdulrrahaman ne matarsa ta ce ya yi sammakon fita yana da wata sharia da yake jagoranta.

Ko da garin Allah ya waye daman Ummu Salma ta ji kamar ta buɗe idanuwanta ta ga ta yi nesa da garin Jimeta gabaɗaaya garin ya fita da ga zuciyanta a baya ba ta taɓa tunanin wata kaddara za ta iya raba ta da mahaifarta ba sai ga shi kaddaran Habibu ta sa za ta yi nesa da iyayenta da duka yan'uwanta domin tsira da salamar zuciyarta, ta tsani garin Jimeta da duk wani farincikin da ta samu a cikin ta dalilin Habib..
Sai ga shi suna sallama da Baɗɗo tana hawaye itama tana hawaye.

"Zan yi kewar ki Sisna. In sha Allahu in muka samu hutu zan dinga zuwa ina ganin ki."
Baɗɗo ta faɗa tana sharan ƙwallah.
"Na gode Aisha. Ba zan taɓa mantawa da alherinki ga zumuncin mu ba, nima Allah ya ba ni iko da tsawon rayuwa domin na samu damar saka miki."
Ummu Salma ta faɗa cikin kuka sannan suka sake rumgume juna.

Dakyar suka saki juna, Ummin ikki ma ta rike hannuwanta tana fadin" Ki je can ki sake sabuwar rayuwa. Kar ki dawo mini sai da sabon suruki kin ji ko Ummu?
Ta faɗa cikin mirmishi a zuciyan Ummu Salma faɗi take yi wa zai sake sona a haka Ummin ikki? Amma a fili mirmishi ta yi lokaci ɗaya tana gyaɗa kanta cikin fitan hawaye.
Ammah ce kawai ba ta yi kuka ba, ita da ba a ganin raunin ta.

"Ammah zan tafi, ki yafe mini."
Ummu ta faɗa bayan ta duka a gaban Ammah tana zubar ƙwalla."

"Ba ki yi mini komai ba, ki je na yafe miki duka laifukan ki da wanda na sani da wanda ban sani ba.  Ina so ki tuna da cewa rabuwa da Habibu ba shi ne ƙarewar rayuwarki ba Auta, ki sani Allah na tare dake in kika mika masa lamuran ki, shi zai kawo miki agaji, don Allah ki cire komai a zuciyarki ki yi rayuwarki cikin farimciki."

"Zan yi haka Ammah."
Ta sake faɗa tana ta kuka kamar ranta zai fita.
Baffa ne ya ɗagota yana share mata hawaye.
"Bar kuka Auta, can ma Kaduna ai duk gida ne, kuma duk lokacin da kika ji kina son dawowa ai za ki dawo gida kin ji ko?
Sai ta gyaɗa masa kanta tana mai sake zubar da ƙwallah.
"Baffa ka yafe mini."
"Ban taɓa rike ki ba Auta. Ki tuna da Ubangiji a dukkan sakannin numfashinki, shi kuma ba zai barki ba, in sha Allahu."
Kanta ta gyaɗa tana sake sakin kuka har da jan majina.

"Allah ya tsare ku, ki yi ma Fatima Biyayya, ki riƙe Alhaji a matsayin Uba a gareki, domin yanzu alhakin komai na rayuwarki yana hannunsa ne."
"To Baffa.'
Ta faɗa tana sharan ƙwallah

"Fatima kama hannun ɗiyarki ku je. Allah ya sada mu da alherinsa."
Baffa ya faɗa idanuwansa na kawo ƙwalla sai ya bar ɗakin bayan ya danƙama Mami Hannun Ummun Salma, Ammah kuma ba ta ga tafiyar su ba ɗaki ta shige tana sharan ƙwalla a zuciyanta tana yi ma Ummu Salma fatan samun kwanciyar hankali da salama a in da zama zai sake cilla ta.

Masu rako har ƙofar gida akwatina biyu na kaya Ummu ta tafi da su sai kayan haihuwa sauran Mami ta ce ta bar su in suka isa can za a siya mata wasu.
Har da Baɗɗo aka tafi filin jirgi rako. Karfe sha ɗaya daidai jirginsu ya ɗaga zuwa garin Kaduna.
A first class suka zauna hatta da Faruƙu da Islam da kujerunsu, Mami da Alhaji suna waje ɗaya tare da Faruƙu ita kuma 
Ummu Salma a bangaren window, Islam na gefenta yaran nan ko a jikinsu daga gani sun saba shiga jirgi, ita ko da ba ta saba ba sai da cikinta ya karta sau ɗaya ta taɓa shiga jirgi lokacin da suka je Daura naɗin Sarautan Hamma Lamiɗo shi ya turo musu kuɗin jirgi ita da Ammah suka tafi shi ne na farko sai wannan na biyu

Lokacin da ta fara ganin gajimare, jirgin ya daidaita a sama ya fara tafiya. Hawaye suka sake kece mata, tana jin shuuuu alamun jirgi na tafiya sai take jin komai na rayuwarta kamar yana gogewa, tabbas haɗuwarta da Habibu a baya tana kallon shi a wani nasara ne amma a yanzu tana cikin fargan jajin shigowarsaa rayuwanta. Saboda shi ya sa ta tsani duk wani ɗa namiji, tana ganin duk halinsu ɗaya saboda Shamsiya ya sa ta ƙara tsorata da lamuran mutane da ƙawaye, sun yi dalilin da ta gudu ta bar in da aka haifeta sun yi sanadiyar haifar mata da ciwon da har abada ba zai taɓa warkewa daga zuciyanta ba.

Amma ta yi ma kanta alƙawarin manta da duka rayuwanta a garin Jimeta. Za ta koma Kaduna a wata sabuwar Hallita. Za ta manta da Habibu da duk abin da ya dangance shi cikin jikinta kuma za ta haife shi, tana son shi amma baƙin cikinta ɗaya in ta tuna akwai jinin Habibu a jikin abin da ke cikinta. Ba ta fatan wata danganta ta sake shiga tsakaninta da Habibu, ba ta ƙaunar sake ganinsa a rayuwanta shi ya sa ta kudirta a ranta cewa za ta yi nesa da rayuwar Habibu da duniyarsa yadda ba zai taɓa cin mata ba har abada. Cikin daman ya ce ya bar mata to babu sauran wani abu da ya rage a tsakaninsu

Tana hawaye wasu na korar wasu, amma tana ji kamar komai na ta na sauyawa. Tabbas dole ne ta manta komai in dai har tana so ta sake cigaba da rayuwa a matsayin Ummu Salma Hadi Baba
Tana kallon gajimare da gizai-gizai tana kuka tana jin ta bar Jimeta har abada sai da ta zo da ziyara amma garin ya bar mata wani wawaken taɓon da ba zai taɓa cikewa ba har gaban abada.

Wataƙila tafiyar Ummu na ɗan lokaci ne, amma Jimeta za ta sake maraba da ita a lokacin da ta yanke dukkan tsammani da samun rayuwa mai inganci.

***
*ANGUWAN DOUGIREI*
JIMETA.
9:50pm

A kayattacen sabon gidan Habib shi ne zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya kan jikin shi kuma Shamsiya ce a lafe marabanta da tsirara kaɗan ne saboda yanayin ƙaramar rigar dake jikinta da ba ta iya ɓoye sirrukan jikinta ba. shima ɗin ba shi da riga daga shi sai ƙaramin wando amma falon akwai duhu da yake dare ya ɗan fara shiga. Ba kuma don ba wuta ba ne ya sa falon ya yi duhu ba, masu gidan ne suka rage hasken falon suka bar na talabijin ɗin da suke kallo wanda ke ɗan haskaka falon kaɗan-kaɗan.

Hira suke ƙasa-ƙasa ba tare da sun yi wani motsi ba ballatana aji abin da suke furta ma juna, talabijin ɗin ma shi yake ta ɓaɓatu shi kaɗai akan tashar MBC2, su hankulansu na kan junan su lokaci bayan lokaci kuma suna sumbatar bakunan junansu cike da soyayya tare da muradi mai girma.

"Sweety ina son ka, kai ne rayuwata."
Shamsiya ta faɗa cikin irin amo a muryanta.
Kanta na saman kirjinsa yana shafa suman kanta dake tsefe har zuwa ƙasan wuyanta zuwa ƙirjinta tunda rigan mai budaɗɗen wuya ne.

"Nima ina son ki Sweety,da ban same ki ba da na zama mai asara."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta itama sai ta ba shi dama suka rike kan juna suna masu sumbatar juna kamar za su cinye bakin juna lokaci ɗaya hannayensu na kara kaina a kan jikunna junansu cikin soyayya da muradi mai girma.

Sun daɗe cikin wannan yanayin kafin su saki bakin juna su koma su sake curewa waje ɗaya suna masu sauke ajiyar zuciya a jejjere, Habib ya sake matse Shamsiya dake kan jikinsa kamar ya mayar da ita cikinsa haka yake ji, bai san haka yake son ta ba sai da ya mallaketa bai san bai taɓa son Ummu Salma ba sai da ya auri Shamsiya daga lokacin ya fara ganin tarin bambamcin dake tsakanin su.

Shamsiya sonta yake yi da dukkan zuciyarsa zai iya zama da ita na har abada in dai tana tare da shi ba tare da ya takura mata ba. A farkon auren shi da Ummu Salma shi kan shi ya ɗauka yana daga cikin harijan maza ma su yawan buƙata domin yadda yake hakarta kamar Allah ya aikosa sai da ya auri Shamsiya ya ƙaryata haka, yau kimanin sati uku da auran su amma komai na rayuwarsa ya sauya. In dai zai ganta ga ta gashi ko ba za su yi wani abu ba farinciki ya ishe shi, sonta ne ke masa nauyi a zuciyarsa ba sha'awanta ba shi ya sa ko bayan faman da ya yi kafin ya mayar da ita cikakkiyar mace bai wuce sau uku zuwa huɗu suka marabanci juna ba tsausayinta yake ji ba ya so ya ba ta wahala, ita kaɗai ne ya ke jin daɗin yin wasanni da ita aamm a lokacin Ummu Salma wannan ba ya yi masa shi dai kawai sha'awanta ne ke azalzalansa so kawai ya ke yi ya marabance ta domin kauda wannan kaifin sha'awan a zuciyarsa wani abu kamar asiri in yanzu zai gama to yana sake kallonta zai ji yana son ƙari, har yanzu in ya kwanta barci ko in ya kaɗaice tana yawan faɗowa tunaninsa ko da ya saketa ba wai wannan ƙishiruwan sha'awan nata da yake ji ya gushe daga zuciyarsa da gangan jikinsa ba ne, kawai ya rabu da ita ne saboda lokaci ya yi amma karya yake yi har gobe akwai sauran abin mamora a jikin Ummu Salma.

"Sweety'
Kamar daga sama ya ji Shamsiya na kira sunan shi ya faɗa dogon tunani sannan ne fa ya yi saurin dawowa cikin hayyacinsa.

"Naam Sweety me ya faru?
Ya faɗa yana mai kallon fuskarta ta cikin duhun ɗakin.
Baki ta tura masa kafin ta ce" Gani a tare dakai tunanin me za ka yi kuma?
Sumbatar bakinta ya yi yana yi mata mirmishi kafin ya ce" Ai ke ce tunanina kuma ga ki a tare da ni Sweety na"
Itama sai ta sake sumbatar bakin shi tana yi masa wani irin kallo.

"I love you mai tsada na."
"Love you too madara ta."
Ya mayar mata da martaninta yana mai shafa bayanta zuwa ƙugunta.

"Ko tunanin tsohuwar matarka kake yi ne?
Ta faɗa tana masa dariya.
Fuska ya haɗa kafin ya ce" Kin fara ko?
Ɗan gemunsa ta ja kafin ta ce" Ai kun yi zaman aure ba laifi ba ne in ka tuna good memories ɗin ku tare da juna."
Hannunta ya ture daga fuskarsa.
Sannan ya kalleta yana faɗin" In ina tare dake ina mantawa da kaina ne Sweety,  ki sani ko da tana nan ke ce tunanina bayan ba ta ma ke ce tunanina, ni na ma manta da ita ko tana ma wani hali oho."
Ya faɗa cikin alhini da amon tausayi.
Shamsiya ta kwashe da dariya har tana sarƙewa sai da ya riƙa bubbuga bayanta yana yi mata sannu.

"Kin gani ko? Ki yi a hankali kin ji ko?
Yake faɗa yana ɗan shafa bayanta har da ma kirjinta.
Amma duk da haka ba ta daina dariyan da ta fara ba.

"Me ya saka ki dariya!
Ya tambaya shima yana ɗan taya ta dariyan kaɗan.

"Ummu Salma na tuna, baiwar Allah har gobe tana tsananin son ka."
Sai ta sake kecewa da dariya.
Shima dariyan ya ɗan saki kafin ya ce" To ai yanzu dolenta za ta cire ni a zuciyanta domin ta fahimci ba a hallice ni don ita ba, an hallice ni don ke ce kawai. Ke kaɗai ba ki da abokiyar tarayya."
Ya gama faɗa yana sumbatar saman sumar kanta.

"Abin da ke bani dariya in na tuna, ta zo gidammu ana jibi bikin mu ta ga hotunan auran mu amma wai ta kasa gasgata gaskiya ne, ta yarda da ni ta aminta da soyayyar da take yi maka a wautar ta tana tunanin wata rana za ka dawo gare ta? Ka daɗe kana ce mini yarinyar nan ba ta da tunani ban taɓa yarda ba sai ranar."

Ta gama faɗa tana sake kwashewa da wata dariyan daga gani tana cikin nishaɗi da labarin da take bayarwa.
Nan fa ta cigaba da faɗin maganganu marasa daɗi a kan Ummu Salma labarin zuwanta gidansu da duk abin da ya kwana kullum sai ta tuna ta yi dariya kamar ya zama abun tunawarta ta yi nishaɗi.

"Wawancin iyayenta na gani, suka barta da cikin jikinta alhalin wanda ya yi cikin ya ce ba ya so, to mene ne amfanin haihuwar da za ta yi?
Ta faɗa tana kallon shi, sai ya ɗan juya mata ido alamun bai sani ba.

"Ni dai har abada ba za ka kawo mini jinin da ba nawa a gidana ba, ba mu yi wannan alƙawarin ba."

"Ba ma zan kawo ba? Me zan yi da abin da ta haifa! Ke da za ki yi ta haifa mana yara?
Ya gama faɗa yana ɗan jan hancinta mirmishi ta sakar masa har tana sumbatar gefen kumatunsa.

"Da gaske na ke yi na bar ma Ummu Salma da iyayenta wannan cikin har abada ba ni da alaqa da shi"
Ta jinjina kai cikin farinciki.

"Wayyo ta ba ni tausayi, "
Ta sake faɗa tana sake saka dariya.
"Lokacin har wani ɗaga kafaɗa take yi. Bestie Allah kuma ya ba ku miji wanda ya fi Noori na ma komai da komai."
Ta gama faɗa tana kwaikwayon muryan Ummu Salma daga shi har ita sai da suka sake tsintsirewa da dariya.

"Ko haihu ta yanzu? Domin ganina da ita na karshe na ga cikin ya yi kasa. Ko da yake ina ruwanmu ko Sweety?
Ta tambaya tana kallon shi.

"To ai ke ce ke ɗauko maganarta. Ni tuni na gama da babinta."
"Labarinta na sanya ni nishaɗi ne."
Ta sake faɗa tana dariya.
"Na san zuwa yanzu kowa ya san na aure ka, na san na sha tsinuwa wajen yan'uwanta barin ma uwarta din nan bafullatanar banza, da wannan yayanta na ta lauya masifaffe da shegiyar ƙawar nan nata Baɗdo ba ta da mutumci, ka ga saƙon cin mutumcin da ta turamini ranar biki! Wai duk abin da ya samu Yar uwanta ni da kai Ubangiji ba zai ƙyale mu ba to ina ruwan mu? Daman ai aro na ba ta kai kuma na zo na karɓi kaya na sai aka ga laifina Sweety?

"Bai kamata a ga laifnki ba, ai su ba su nan abin da ya faru ba ne."
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Ko da Ummu Salma ta riga ni haɗuwa da kai. Amma ai ni ka zaɓa sama da ita ko?
Ta sake tambayan shi tana ɗan kallom shi.

"Tabbas."

Ya faɗa abin da ya faru a lokacin yana dawowa masa.
"Wallahi tun a ganin farkon da na fara yi maka kishi da hassada suka kume ni, a raina ina faɗin me ya sa sai Ummu ce za ta fara haɗuwa dakai? Ranar na koma gida da baƙinciki ina ganin kai ne irin namijin da nake burin aure ban taɓa tunanin za ka kawo kanka gare ni ba wallahi tallahi da ka makara ba ka zo ba, ni da kaina zan neme ka na yi maka tallar kaina sannan na sanar dakai na fi Ummu Salma bukatar ka a rayuwata."

Ta gama faɗa cikin wani yanayi kamar ta yi kuka.
"Sweety wallahi ina sonka."
Sake rumgumeta ya yi a jikinsa yana faɗin" Na sani, nima ai kinsan ina son ki! In kika yi duba da tsawon lokacin soyayyarmu da yadda na cika alƙawarin kema za ki san bayan ke ba na son kowa a duniyar nan a matsayin matar auran da zan zauna da ita. Na fuskancin komai saboda na mallake ki "
Ta sake ƙamƙame shi tana faɗin" Na sani Sweety na sani wallahi."
Sumbatar sumar kanta ya yi kafin ya ce" Ki bar tuna duk abin da ya wuce, rayuwarmu ce yanzu kawai a gabanmu Sweety, mu zauna mu gina sabuwar rayuwa wacce za ta yaɗu zuwa nan da wani lokaci kaɗan. Can wait na ga ranar da za ki haifa mini ɗa ko ƴa daga mahaifarki."
Ya faɗa yana kai hannunsa ƙasan maranta ita kuma sai ta noƙe wai tana jin kunya.

"Ke ce na zaɓa ki zama uwa ga ƴa'ƴana. Kuma ba zan sauya miki ba."
Gabaɗaya ya gama kashe mata zuciya da kalamansa. Sai ta sake narke masa cikin shagwaɓa shi kuma yana biye mata sun daɗe a haka domin da ya ce su je ɗaki su kwanta sai taƙi karshenta a saman jikinsa ta yi barci ta bar shi da sake shuga tunani mai zurfi.

Tabbas a ganin farko da ya yi ma Ummu Salma ya ji yana son ta amma lokacin da ya haɗa idanuwansa da na Shamsiya sai ya fahimci ashe ba so ya ke yi ma Ummu ba sha'awanta yake yi, in yana tare da ita burinsa kawai  jikinta ne a gabansa amma in yana tare da Shamsiya burinsa kawai ya dauwama tare da ita ko da ba za ta amfanesa da komai ba, tun bai fahimci karatun ba har dai ya fahimta ba shi da mafita illa ba ma zuciyansa abinda take so sai kuma aka yi saa itama shi take so, kawai sai suka jone suka kuma tsara komai. A lokacin a gida ba za a aurar da Shamsiya ba sannan shi kuma yana son auran Ummu Salma saboda ya cire wannan kwaɗayim nata a zuciyarsa shi ya sa ya yi ma Shamsiya alƙawarin zai yi auren shekara ɗaya ya sake ta sannan ya zo su yi aure daga baya ta aminta amma babu sharaɗin haihuwa, kaddara ce ta gifta har wannan cikin ya zama rai a cikin Ummu Salma amma ba shirin su ba ne, bai samu matsala a bangaren iyayen Shamsiya ba saboda dangin mahaifiyarta sun tankwasa mahaifinta, kuma gidan yan boko ne ba wani damuwa aka yi da dogon bincike ba tunda aka fahimci shima yana da iliminsa da aikinsa sannan ko da aka ce ya saki matarsa ta farko ba wanda ya yi bincike mai tsanani akan haka, kuma a cikin ahalin Shamsiya ba wanda ya san shi a matsayin mijin kawarta, shi kawai a san shi ne a matsayin mijinta na yanzu. Ya so ya samu matsala da Alhaji Sheriff shi ne ya ce ba zai sake zuwa ya nema masa aure ba, amma Baba Usman da su Gwaggo duk ya siye su da kyauttuka tuni suka manta da komai, shi ma dai Alhaji Sheriff ɗin da magiyan Habib ɗin da Baba Usman da Gwaggo ya amince ya je ya nema masa auran Shamsiya har aka ba shi amma da sharaɗin in wani abu ya biyo baya kar ya saka shi a ciki.

Shi kuma ya amince a tunaninsa me zai biyo baya? Masoyiyarsa fa ya aura, yana tunanin dukkan wani buri na shi zai cika, ya gama samun farinciki bayan ya watsa farimcikin wata,bai san cewa watakila farincikin na shi na lokaci kaɗan ba ne, ƙila nan gaba kaɗan Fargar jaji zai kama shi ya fara nadaman abin da ya aikata nadama mara amfani alhalin kuma lokaci ya sare masa.

****
*NDC QUATERS KADUNA NAGERIA.*

*BAYAN SHEKARU BIYU.*

"A Yau na koya mana yadda za mu sarrafa shinkafar mu zuwa chinese rice, za ki yin ta da kowani shinkafa amma ta kasance mai kyau ce saboda gudun caɓewa. Uwargida da Amarya har da ma ƴan'mata tare da zawarawa duk a yi pratical ma'ana gwaji domin da gwaji ne ake ƙwarewa ni ce dai taku ɗin nan HANAN DELICIOUS sai mun sake haɗuwa daku a wani sabon video na gode kar ku manta ku yi like in yau kika fara kallon videos ɗina to kar ki manta ki bibiya duka shafukana a Facebook Hanan B Jimeta a Youtube channel ɗina za ku kama ni a Hanan Delicious, in kuma a instergram ne za ku iya kama ni a Hanan B Jimeta, in kuma a Tiktok ne za ku iya kama ni a Hanan Delicious domin samun kayattacen videos ɗina akan girke girke masu  kayatarwa tare da snacks na zamani domin jin daɗin ku. "

"Mahmah..."

"Mahmah.."

Ta ji ana kiranta daga falo, ta kuma san yanzu za ta shigo kitchen ɗin in kuma ta shigo za ta ɓata mata Video ya sa da sauri ta ce.

"Bissallam. Sai mun sake haɗuwa. Bye."
sannan da sauri ta matsa wajen ringligt ɗin da ta ɗaura a wayarta ƙiran iphone 15 ta  yi saving ɗin Video ɗin dai dai lokacin da ƙaramar yarinyar ta ƙariso cikin kitchen ɗin.

"Mahmah."

Aka sake faɗa cikin murya irin ta yara masu shagwaɓa.
Da sauri ta baro in da take tsaye sanye da abaya baƙa ta yi rolling ɗin mayafin J.c mai ruwan madara kyakyawan farar fuskarta da dogon hancinta ta yi kyau sosai.

Sama ta ɗaga yarinya tana faɗin
"Waye ya taɓa mini Hanan ɗina?
Ta faɗa tana share mata idanuwanta ganin hawaye.
Dakyar ta lallaɓata ta yi barci sannan ta zo ta fara Video ɗin nan, da ta kwana biyu ba ta ɗora komai a shafukanta ba  Hannan da man akwai rigima balle kuma ba ta da lafiya tana ɗan zazzabi ga zawon haƙori na can gefe da suke fitowa shi ya sa rigimanta ya ƙaru kuma rigiman saboda ta san sun kwanta tare kuma ta farka ba ta ganta a gefenta ba shine ta taso tana kuka.

Sanye take da bulawus ta yara mai kyau, kanta kuma kitson kalaba ne an kama da band ga ta dai yarinya yar kimanin shekaru biyu amma tana da suma kai da gashi ga ta fara jajir da ita amma ko kusa ba ta kama da Ummu Salma, kamaninta da komai kamanin mahaifinta ta ɗauko, wanda kullum in Ummu ta kalleta sai ta ji baƙin ciki, ba ta so ta sake cin karo da mai irin fuskar wannan mutimin ba, amma sai ga shi tilon yar da ta haifa ta ɗauko kamaninsa

"Mahma"

Ta sake faɗa tana sake lafewa a jikin uwar ta ta,.
"Gani nan kukan na mene ne? Ko yunwa kike ji ne?
Sai ta gyaɗa kanta.
"Tea Mahma."
Ta ce tea za ta sha, nan da nan Ummu ta saɓa ta a baya tana faɗin" Hau bombu yanzu na haɗa miki tea ɗin ki sha."

Nan da nan ko ta lafe a bayanta ita kuma da haka ta yi amfani ta saka ruwan zafi a wata butar a kitchen ɗin tunda suna da wuta su da sai su yi sati ba a ɗauke musu wuta ba koma an ɗauke akwai solar ba ka gane ma akwai wutar ko babu.
Tana cikin tattara kayan video ɗin ta Basira ta shigo Kitchen ɗin.

"Ya Ummu da kan ki kika goya wannan yar rigimar!"

Ta faɗa tana dariya Ummu ta juya tana kallon Basira yar matashiya ce ko za ta girmeta bai wuce da shekaru biyu ba, itama kaddaran aure ne ya faɗa mata suka rabu da mijin watanni kaɗan da auran su, ita ce wacce Mami ta sake ɗaukowa daga can garin su Daddy ɗanmarke bayan sun mayar da Baraka an yi mata aure.

"Ba ruwan ku a ciki Basira."

Ummu ta faɗa tana sake zumkuɗa Hannan a bayanta.

"Yi kwanciyarki Hanan kar ki biye ta Basira."
Saboda suna yin ta Hanan kiyuwa da rigima Basira kuma faɗa ta yi ta janta tana saka ta kuka amma bai hana anjuma Hanan ɗin taje wajenta da zanin goyo tana faɗin bombu.

Hanan na son goyo sosai ko domin da aka haifeta ta sha goyo ne? Lokacin Baraka nan nan ko da yaushe tana bayanta Mami ma in tana gida za ta goya ta haka ma Islam har Faruku rigima yake yi a lokacin sai an goya masa shima.

"Ke sauko ki kyale Ya Ummu ta huta, ta ho nan ki hau nawa bayan da kika saba hawa.."
Basira ta faɗa tana leka Hanan sai ko ta makale bayan uwarta tana kallon Basira.

"Ba ki tahowa ko?

Ta faɗa tana miƙa mata hannu kawai sai ta saka kuka tana kiran Mahmah, Ummu na dariya ta ce"Hanan ke da Basirun na ki."
Haka Hanan ke kiranta su yi ta dariya ita da su Mami Basira tun tana masifan cewa ni da na reneki ki san sunan kowa daidai amma ni basiru kika mayar da ni har ta zo ta haƙura domin ya kama bakinta.
"Ba ruwana in ta ce ba za ta sake goya ki ba."
Ummu Salma ta faɗa tana dariya.

Kamar kuma tana ji sai ta daina kuka ta kura ma Basiran ido tana kallonta sai ga shi da kanta ta miƙa mata hannu ita kuma ta kama tana faɗin" Yauwa Hannatuna."
Tana dariya dariya yarinyar ta bar bayan uwar tata ta haye na bayan Basira tana zillo.

"Basiruu."

"Ke ni sunana Basira ba Basiru ba."

"Basiru.."

"Kai wannan yarinyar, to ke ma Habu ba hannatu ba."

Ummu na gefe tana cin dariyanta.
"Ku je falo Basira bari na haɗo mata tea ɗin."
"To, na ji jikinta da ɗumi ya kamata ta sha maganinta na rana."
"To ta sha tea ɗin sai na ɗauko mganin ki ba ta yar rigimar nan ai sai ke Basira."
Ta fice tana dariya.
Basirace ta taimake ta har ta samu ta haɗa mata tea ɗin bayan ta kawo mata ta bata ta sha, sannan wajen shan mgani sai da aka yi mata ɗure ba ta son magani tana ta kuka da rigima bayan nan Basira ta yi mata wanka ta sauya mata kaya sai barci bayan ta goyata ram a bayanta da zani.

Mami ba ta nan ta shiga cikin makaranta gidan daga Ummu ne sai Basira Faruku na makaranta sai biyar da rabi zai dawo tunda nan Al'areeb yake yi a Kaduna yana primary 6, Islam dai ana bording  zaria can FGGC BASAWA tana jss2 yanzu sai an yi hutu take zuwa gida amma suna zuwa yi mata visiting zuwa ma biyu duk Ummu ke zuwa ita da Basira da Faruk Hamisu ke tuƙasu.
Daddy kuma ba ya nan ya yi tafiya kasar Turkey ya fi sati acan.

Sai a lokacin itama Ummu ta samu ta ɗan sake yin wanka ta sauya kaya wayarta ta ɗauka ta shiga shafukanta tana ganin video ɗin da ta yi ɗazu ta fara ɗora shi a kan Youtube sai kuma nan da nan ta yi sharing ɗin shi zuwa Handles ɗinta na sauran shafukan sada zumumta an yi mata comments amma duk akan godiya da yabawa ne sannan da masu cewa suna gane koyarwaanta don Allah ta buɗe musu online class mana, itama tana so ta buɗe amma ba yanzu ba sai ta sake tara yawan mabiya.
Bayan ta gama duba shafukanta sai ta shiga kan whatsApp ɗin ta, tana duba saƙonni, ko wata biyu ba su yi da dawowa daga Jimeta ba tun bayan barin ta gida sai a lokacin ta sake komawa Jimeta shima ya kama dole ne Baɗɗo ce ta gama makaranta shi ne ta je mata graduation Mami ba ta samu zuwa ba daga ita sai Hanan suka tafi kwananta goma ta dawo Kaduna duk da ta yi kewar garin amma ba ta jin za ta sake zaman garin ya wuce na sati biyu ba, yanzu Ummu Salma yar kaduna ce ba yar Jimeta ba.

Hamma Saddam ne ya yi mata sako tana dubawa ta ga ya ce" Ke nifa ina Lagos."
Mamaki take yi sai yanzu ta san dalilin da ya sa Hamma Saddam ya zaɓi shiga Camp  a garin Lagos.

Ashe saboda ya je ya huta a gidan Hamma Lamiɗo ne.
Hotuna ne ya turo mata sama da goma, har da wasu ma yana driving a wata mota mai kyau da tsada.

"Ni fa har motar Hamma Lamiɗo nake hawa yanzu"

Ta tuna mganarsu ta kwanaki da ta tambaye shi motar waye yake aro yana ta wayon gari ya ce tashi ce ashe wasa yake yi mata.
Yanzu ma hotunan shi ne a bakin ruwa kala kala.

"Ya mutanen gidan?

Haka kawai ta rubuta masa saƙon ya maka biyu domin ta san yana online, Hamma Saddam da waya kamar 5 and 6 ne.
Tun bayan barin ta Jimeta ba ta sake ganin Hamma Lamiɗo ba wataƙila Mami na haɗuwa da shi tunda ta je Jimeta sosai a wannan shekaran amma ita ba ta sake ganinsa ba kuma ba ta sake bibiyan labarin shi ba, ta dai san ya biya ma Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman tare da matansu sun je Umra tare da Ummin ikki da babansu Baɗɗo, a shekaran da ta dawo Kaduna itama Daddy ya biya musu sun je gabaɗaya acan suka haɗe a masauƙi ɗaya ma suka sauka ta kan ji ana hiran ya yi kaza ya yi kyauta kaza amma ita dai tunda bai taɓa yi mata ba, ba ta taɓa damuwa da shi ba.

Hamma Abdulrahim ne ta ga ya saka hoton shi cikin likitoci turawa kamar yana can ƙasar waje alhalin yana Abuja yana Housemanship ɗin shi a asibitin NIZAMIYE HOSPITAL ABUJA.
Bayan ya dawo ya yi jarabawa ta Medical and Dentel council of Nigeria.
(MDCN) Sau ɗaya ya yi kuma ya samu nasara.

Abdulrahim kamar wani bature daman ga shi jajir da shi ɗabi'unsa ma da komai na shi ya koma na turawa, hausa ma tana neman ɓace masa magana kaɗan turanci fillanci ko har ya fara mantawa shi da ya shafe sama da shekara bakwai a kasar Singpore.

Da ya dawo Ammah ta yi ta masifa, in suna hira ya dinga yi mata turanci.
"Buraubaka, tir da wannan kasar turawan tunda ya sa ka manta da al'adanka ka kwaso mana daɓi'an turawa."

Lokacin da ya zo Kaduna ne ya ke ta ba ma Ummu labari tana cin dariya.
Har waliman dawowarsa an yi amma Ummu ba ta je ba Har Mami taje shi ne bayan ya natsa ya huta ya zo ya ganta kwana biyu ya yi suka sha hira suka fita yawo cikin gari kafin tafiyarsa.
Tun da yanzu Ummu har driving ta koya kuma ta iya, tana tuƙa motar Mami wani lokacin.

Ummu Salma ba ta taɓa tunanin da gaske rayuwarta za ta sauya ba sai ga shi Ubangiji ya sauya mata rayuwa, rayuwar da ba ta yi hasashe ba, lokacin da suka zo Kaduna ga shi dai gidane amma ta yi ta baƙunta da rashin Sabo ba abin da za ce da Mami da Daddy sai godiya domin sune tsanin da rayuwarta take kai a yanzu. Sun kula da ita da lafiyanta da ita da abinda ke cikinta, da karfi da yaji suka yakice damuwa da tunani a zuciyanta. 

Kwanan ta arba'in a Kaduna ta haihu a asibitin kuɗi na Garkuwa, aiki aka yi mata domin ta yi doguwar naguda, an samu nasaran ciro mata ya mace wacce ta saka ma suna Hannatu suna kiranta Hanna, Daddy da Mami su suka yi mata komai, raguna biyu Daddy ya yanka mata kuma ya shirya taron suna.

Baɗɗo da su Ummin ikki da matan su Hamma Abdullahi duk sun zo Kaduna taron suna Umma Balki da Umma A'i ma sun zo Umma Balki sai da aka yi arba'in ta koma Mubi ita ta yi ma Ummun wankan jego mai tsada, Baffa ma ya tako har Kaduna ya ga Hanna amma ban da Ammah sai dai ta gan ta a hoto. Kaf yayyenta ba wanda bai kira ta ba, sannan sun tako tare da iyalansa ita da Hanan sun ga gata sosai, kuma ga shi yarinyar ta taso da ƙiriniya kowa na son ta Daddy ko kamar shi ne mahaifinta yadda in dai yana gida tana tare da shi haka ma Mami shi ya sa su ta fara kiran sunayensu bayan ta fara iya magana sai Faruƙu da Ilam wato Islam ko Mahma sai daga baya ta fara iya faɗa, gata na duniya Hanan ta na gani kuma tana kan gani komai na rayuwa ba abinda suka nema suka rasa Daddy ne da Mami ke tsaye kanta ita da yarta.

Har kuma gobe Habib bai nemeta ba, itama ta manta da wanzuwarsa a rayuwanta ba za ta ce ta manta gabaɗaya ba, domin ba zai mantu ba, amma ta kan daɗe ba ta tuna ba  in ta tuna ita kaɗai ta yi ta kuka, Rayuwarta ta ya sauya a Kaduna Mami macece mai kirki da yaƙana kaunar da take yi mata ko rabin shi ba ta nuna ma Lamiɗo, ba ta zuwa ko'ina tana gida daga baya ne ma ta fara bin Mami zamfara in za ta je ganin Dangin Daddy, bikin Baraka ne farko, amma ba ta bin ta Jimeta itama ba ta matsa mata  tunda ga waya tana mgana da kowa daga gida.

Tun kafin ta yaye Hannan Hamma Kabiru ya matsa wai sai ta koma makaranta ita kuma har abada ba ta son karatu shi ya sa a wannan karon ma ta turje, Daddy da Mami suka goya mata baya dole suka ƙyaleta, da ta watsar da girke-girkenta sai dai kawai tana yi a gida, tunda ta hana Mami ɗaukan mai girki tace ita za ta dinga yi, Mami ce ta matsa mata ta dawo dashi, ta kuma ce za ta neme mata catering school ko wani program haka ta shiga domin ta sake ƙwarewa haka ko aka yi Mami ta nema mata ta shiga yanzu haka a Kaduna tana da certifacate sama da huɗu na catering da program kan abin da ya shafi girke-girke kuma da shawaran Mami da na Baɗɗo tare da na Hamma Saddam tare da Hamma Abdulrahim ta ƙirkiri sabon account da sabon suna lokaci ɗaya kawai tunanin yin amfani da sunan Hanan ya zo mata. Hanan Baba Jimeta sai ta ke amfani da Hanan B Jimeta.

 Ta fara video tana ɗorawa a youtube na girke-girke duka-duka wattani shidda ne da fara abin amma har ta ɗan fara tara mabiya da farko har ta sare da karfin gwiwansu ta cigaba a hankali ta buɗe sabbin accounts a Tiktok da instagram.

 Daddy kuma ya gwangwajeta da sabuwar waya Mami kuma ta siya mata ringlight kayan girki da komai akwai su a kayattacen kitchen ɗin Mami, wanda wasu ma saboda kyan kitchen ɗin ya sa suke kallon Videos ɗin Hanna Delicouis ba a ganin fuskarta in ta ɗora videos ɗon sai dai a hangi rigarta daga ƙasa haka sai maganarta, ga shi yanzu wasa wasa videos ɗinta suna ta tafiya a kafafem sada zumumta mata da dama suna ƙaruwa da ita saboda ta iya koyar da komai a saukaƙe.

A dalilin Mami da Daddy ta je Umra sau ɗaya ta je Niger sun je Ghana, a Nigeria kuma sun je Abuja da Kano. Daddy  na da gidaje a Kano da Abuja haka kawai in yara sun samu hutun makaranta zai kwashe su suje su huta na kwanaki, idanuwanta sun buɗe tunda suna yawan fita yawon buɗe ido, babu in da ba ta sani a garin Kaduna ba.

Wani lokacin ma har cikin makaranta ta sha raka Mami, zuwanta Jimeta wannan karon sai da ta zama abar kallo, Baɗɗo ita kanta ta zo Kaduna sau biyu sai da ta yi mamakin ganinta.
Ta yi kiɓa ta sake fari ta zama wata babbar mace lalle kwanciyar hankali ma ni'ima ne.

"Auta ke ce kika zama giwa haka? Ai ke da uwar taki ma sai a rasa uwar da yar."
Ammah ta faɗa domin in suka jera da Mami kamar yaya da ƙanwa a jami'ar da Mami ke koyarwa da suka fara ganin Ummu sun ɗauka kanwarta ce, sai da ta ce ɗiyar yayanta ne suka saki baki, Baffa kam bakinsa yaƙi rufuwa.

"Auta Auta an zama uwa manyan mata."
Haka yake faɗa, Hanan ko kiyuwa ta fara yi musu farkon zuwan su, sai da Ammah ta yi mata jan ido sannan ta shiga taitayinta ta yi ta kuka tana rigima Baffa me mai lallashi ya ce shi kan ai ya ga mata, dole ya yi biyayya Ammah ko ya ce kishi take yi ta ga wacce ta fi ta jan fata.

Ammah cikin gatsale ta ce bai ko yi dace ba ana ta dariya.
Hanan kuma ba ta iya kiran sunan Baffa ba sai dai ta ce Bacca.
Ammah ta yi ta masifa tana faɗin ke ba sunan mijina Bacca ba sunan shi Baffa in ba ki iya faɗa ba ki yi shuru ki bar ɓata masa suna, sai suka koma suna ba ma mutane dariya.

Kowa ya zo ya ga Ummu sai ya yi magana haka da ta je gidan su Baɗɗo su kaltume suna ta mamakin sauyawarta ta zama wata mai tsada da ita.
Ummin ikki sai da ta ce ina surukin da take jira, Ummu ta yi dariya ba ta ce komai ba, domin ita a zuciyanta ma ba ta son duk wani namiji in dai da aure ne, aure ya fita kanta gabaɗaya. Yadda ta tsani Habib haka ta tsani kalmar aure, ta je Mubi saboda an yi rashi ɗiyar Umma Salmatu ce ta rasu wajen haihuwa, nan ma suka yo ma ta caa kan maganar aure har da su Baffa Umaru shi ya sa ta baro musu garin ma gabaɗaya.

Ita yanzu me za ta sake tsinta a aure da za ta sake yi? Ai tana jin babu sauran wani abun da ba ta gani ba, yanzu abin da ke gabanta kawai ba ma Hanan tarbiya amma a zuciyanta ta yi kudiri ita da aure har gaban abada. Tana ganin ta rasa komai, ba ta da wani sauran wani abu da rage mata da za ta sake takama da shi, Habib ya gama da komai kafin ya cire ta daga rayuwarsa.

***

Sai bayan la'asar ta fito daga cikin ɗakin ta a baya a ɗaki ɗaya suke kwana da tare da Islam amma tun bayan da ta haihu Mami ta gyara mata ɗakinta ita kaɗai, balle ma yanzu da Islam an fara zama yan mata shekarunta sha huɗu, Faruƙu ne goma. Kicthen ta shiga ta duba abin da za ta sarrafa na dare yau ko abincin rana ba su yi ba ita da Basira tea suka sha  Hamisu kuma da kuɗinshi ba zai  jira su ba, Sunusi kuma ya yi aure matarsa na aiko masa da abinci, Mami ma tana maganar za a gyara musu bangaren waje kawai ta dawo kusa da shi.

Alele kawai ya faɗo mata a rai sai ta ce bari ta yi musu mai nama a ciki sai ta yi musu miyar source ɗin ƙwai store ta shiga ta ɗobe waken suna da ƙaramin turmi ta ɗan saɓa shi ta wanke ta niƙa shi a blander wani katon friza ne a kitchen din cike da kayan amfani, nau'ikan nama ba wanda babu sai dai kawai a ɗauka in za a yi amfani da shi.
Tana kitchen ɗin tana aiki Mami ta shigo gidan ba ta sani ba sai da ta leƙo kitchen ɗin ta yi mgana.

"Ya Ummu sannu da aiki."
Haka Mami da Daddy ke kiranta hatta Hanan ta kama wani lokacin haka take kiranta.

"Laa Mami yaushe kika dawo?
Ta faɗa tana kashe blander ɗin tunda ta gama niƙa waken.
"Yanzu na shigo me aka yi mana ne na fara jin ƙamshi?
Mami ta faɗa tana ɗan shigowa kitchen ɗin kaɗan.

"Mami alele mai nama zan yi mana ko kina son wani abu ne?

"Aa ki yi mana yaushe rabo na da alala, amma ki yi mana na manja."

"To Mami."

"Ina Hanan yar rigima? Ya zazzaɓin ya sauka?
Ta tambaya tana buɗe fridge ta ɗauko rowan gora Ummu kuma ta ɗauko mata kofin tangaran a wani dirowan kitchen ɗin ta mika mata ta tsiyaya ruwa.

"Ta ji sauƙi ta na can bayan Basira."

"Ban gan su a falo ba."

Mami ta faɗa bayan ta gama shan ruwan.
"Ƙila suna bangaren Basira."
"To bari na je na watsa ruwa. Kafafuwana sun gaji Ya Ummu."
"Mami za a yi tausa anjuma."
"Yauwa yar albarka."
Mami ta faɗa tana dariya sannan ta fita, Ummu ta amsa da Amin tana ɗan mirmishi har ta fita sai kuma ta dawo tana faɗin" Baffa ya kira ki kuwa?
Ta tambaya tana tsaye a ƙofar kitchen.
"A'a Mami."
Sai ta kalleta ganin ta yi shuru.
"Me ya faru Mami?
Ta tambaya a ɗan tsume.

"Aa ba komai, kawai na tambaya ne."
Tana gama faɗin haka ta wuce tana faɗib" Na shiga ciki."
Mamaki ya kamata, me ya faru ne? Mami ba ta saba mata irin waɗanan tambayoyin ba, suna waya da Baffa kusan ko da yaushe yana kiranta amma itama tana yawan kiran shi saboda yadda suke daɗewa suna hira, saɓanin Ammah da suna gaisawa da tambayan yara hiransu take katsewa. Sai ba ta saka tunanin komai ba, sai ta ɗauka ko Baffa ne ya kira ta yau shi ya sa take tambaya kanta tsaye ta cigaba da aikinta tana sanye da riga da wando kalan ruwan ƙasa yan pakistan Mami ce ta siya mata su a Saudiya ta ce ma zaman gida ne.

Mami kuma na shiga bedroom ɗinta dake saman bene ta watsa jakanta saman gado lokaci ɗaya ta ciro wayarta ta kira wata lamba, sai da ta katse ba a ɗaga ba ta sake kira nan ma shuru.

"Kai."

Ta faɗa tana cije baki, tiolet ta faɗa ta yi wanka ta fito kenan ɗaure da babban towel a ka kira wayarta ganin mai kiran yasa ta ɗauka da sauri.

"Na ji shuru har yanzu."

Magana aka yi mata daga can bangaren sannan ta gyaɗa kai tana faɗin.
"To ka tabbata dai cikin satin nan, ba fa da wasa  na ke yi ba da gaske nake yi."
Daga haka ta katse wayarta tana ɗan wani nazari kafin lokaci ɗaya ta saki mirmishi ita kaɗai.
Daga ita sai Allah sai zuciyanta sai wanda suka yi waya suka san abin da take ƙullawa.

****
*Sunday*

Daddy bai dawo ba, Mami ta ce akwai wasu sabbin shigowan motoci ne da zai yo oder shi ya sa ya ɗan jima, sun saba duk karshen sati su kan ɗan fita yawo cikin gari tare da Mami da Barira da Faruƙu, yau ma ko da Daddy baya nan sun fita bayan la'asar suka je Shoprite su ɗan biya store suka yi tsince tsince, suna mota a hanyar dawowa gida Hamisu ne ke tuka su a wata mota ƙiran toyota RAV4, Baffa ya kira wayar Mami sun daɗe suna mgana abin da ma yasa Ummu ta gane Baffa ne ta ji Mami na ambaton sunan shi duk da ba ta fahimci kan me suke magana ba, tunda ita Mami faɗi kawai take yi" Kuma ka yarda da maganansa Baffa? Ni dai Allah ban yarda da shi ba."
Abin da kawai taji tana faɗi kenan.

Sai kuma in da ta ce" Baffa ni fa ba wai na ƙi mganar ba ne, sam shi da ƴata ba su dace ba. Ba za ta iya da halin bamuden ɗan Ammah ba."
Kamar ta so ta ɗau saunar mganar, Hamma Lamiɗo ne Mami ke kira da wannan sunan amma kuma yarta ta fa? Wacce take nufi.

"To Baffa muna hanya ne, zan kira ka in mun koma gida"
Bayan ta katse wayar kuma ba ta ba da wata kafa da za a fahimci wani abu ba, sai ta bige da jan Ummun da wata hiran da ya sa ma ta manta da wayar Mamin, bayan sun koma gida kowa ya shiga ɗakinsa, daga nan ba ta sake jin wata mgana ba.

Bayan isha'i sai ga Baffa ya kira Ummu Salma a waya bayan sun gaisa kamar kullum ya ce ina amaryansa Ummu ta ce ta kwanta.

"Ummu Salma."
Tunda ta ji Baffa ya kira sunanta  ta san akwai magana a bakinta.
"Naam Baffa."
"Wane ni a wajen ki?
"Kai mahaifina ne"
"Alhamdulillah kin san duk abin da zan yi ga rayuwarki ba nufin na cutar dake ba ne ko Auta?

"Na sani Baffa."

Har idanuwanta sun fara tara ƙwalla saboda ba ta son me ya faru ba.

"A lokacin auran ki na farko ban yarda an yi miki dole ba. Duk abinda kika nuna baki so ni ma zan ce bana son shi. Har kuma yanzu da kike bazawara kina da haƙƙin sake yi ma kanki zaɓi a karo na biyu."
Baffa ya yi shuru yana jan nunfashi.
Ummu har ta fara kuka, tsoro take ji kar Baffa ya ce ta yi aure, ba za ta iya masa gaddama ba amma tabbas hakan cutuwa ne a gare ta.

"Ummu Salma."

"Naam Baffa."

"Jiya an zo neman auran ki a wajena."
Gabanta ya amsa ras!
Jikinta har ya fara rawa.

"Kuma wamda ya zo ɗin ba zan iya hana shi ba, na hango miki kyakyawan rayuwa tare da shi."
"To Baffa."
Ta iya faɗa tana kuka.
"Ba dole zan yi miki ba, amincewarki  nake nema Auta, in har kin amince gobe da safe ni da yayyenki dake kusa zamu jagoranci ɗaurin auran ki."

Wannan ba amincewa ba ne, Umarni ne Baffa ke ba ta amma a fakaice duk yadda ta tsani aure ba ta isa ta yi ma Baffa gaddama ba su suka tsaya ma rayuwarta kuma ba ta isa ta bijire ma mganarsa ba.

"Kar ki damu in ba ki amince ba, ba komai sai na bashi haƙuri."

Ya faɗa cikin wani yanayi a muryansa akwai zumuɗi daga a farko, daga karshe shurunta sai ya sanyaya ma muryansa ƙarsashinta.

"Baffa."

Ta kira shi cikin muryan kuka.
"Naam Auta, kuka kike yi ne?
"Aa Baffa."
Ta faɗa tana share hawayenta da hannunta.

"Kar ki damu na ce in ba ki amince ba sai na ba shi haƙuri."

"Aa Baffa."

"Kin amince?

"E Baffa."

"Kin tabbata?

"Na amince Baffa, in dai ka amimce nima ba ni da ja."

"Na amince da shi Auta, wallahi ina mai yi miki rantsuwan da cewa yadda zai kula da kansa haka haka zai kula da ke Auta."

"To Baffa."

Ta faɗa tana danne kukanta 

"Allah ya yi miki albarka Ummu Salma, yadda kika karɓi tayina Allah ya wanzar da farimciki a rayuwarki ta har abada. Na gode miki Allah ya gode miki Auta."

"Amin Baffa."

Ta faɗa tana jin sanyi a zuciyanta.
Baffa kuma jin ba ta tambayi ko waye ba shi ya sa bai faɗa mata ba suka yi sallama suna gama waya ta tashi da gudu ta fita ta haura sama zuwa ɗakin Mami tana kuka, Mami na zaune gefen gado waya take yi sanda Ummu ta faɗo tana gunjin kuka ai sai ta saki wayar saman gado ta nufeta cikin rawan jiki.

"Subhanallah Ummu me ya ke faruwa ne?

"Mami."

Ta faɗa cikin gunjin kuka lolaci ɗaya tana faɗawa jikinta.

"Shi, bar kuka yi mini bayanin abin da ya faru."
Ta faɗa tana janta gefen gado suka zauna.

"Mami aure Baffa zai yi mini"

Mami ta zaro ido kafin ta ce" Aure kuma? Da wa?
"Ban sani ba Mami"
Ta faɗa tana tsiyayan hawaye.
"Yanzu Baffa bai bar mganar nan ba? Na ce nima ban amimce ba. Yanzu ma da Abban Islam muke mgana shima ya kira shi ya faɗa masa, kuma da alamu ya goya ma Baffa baya."
Kukan Ummu ya ɗauke kenan kowa daman ya sani? Har Daddy ma ya amince kenan

"Bar kuka, in dai ba ki so ba wanda zai yi miki dole."
Wayarta ta jawo za ta kira Baffa.
"Baffan zan kira."
Da sauri Ummu ta riƙe mata hannu lokaci ɗaya tana mai girgiza mata kai.

"Ki bari na kira shi na ce ba ki so."

"A'a Mami, ki bar shi kawai."

"Me ya sa? Kin amince kenan?

Ummu na hawaye ta ce" Na amince Mami, ba tilas ba ne sai da Baffa ya nemi zaɓina."
"Tilasa ne mana ai ba ki ga wanda za a aura miki ba, ballatana ki ji kina son shi har ki amince da shi."
"Mami ba komai in dai Baffa ya amimta da shi a wajena Amintattace ne."
Mami ta yi shuru tana kallonta.
"Kin tabbata? In dai ba ki so zan ta da auran nan"
Da sauri ta sake girgiza kanta.
"Aa ina so Mami kar ki yi mgana."
Sai Mami ta sake yi mirmishi.
"To share hawayenki, ɗiyar albarka"
Sai ma ta taya ta ta share hawayenta.

Sannan ta riƙe hannuwanta tana faɗin" Ki natsu kin ji ko? Ki yi ta addu'a in sha Allahu kin samu sauyin rayuwa. Ina tare dake har numfashina na ƙarshe."
Sai Ummu ta fashe da kuka ta faɗa jikin Mami.
"Mami Allah ya bar min ke."
"Amin ɗiya ta."
Ta daɗe a ɗakin Mami suna ta hira, sai daga baya ta koma ɗakinta, ranar ta sha kuka amma ta kwana salla da addu'an neman zaɓin Allah.

Kuma da garin Allah ya waye ta samu natsuwa amma tana cikin fargaba, tun safe Mami ta fita Faruku ma na makaranta daga ita sai Baraka.
Ba wanda ya kira ta ballatana ta ji ko an ɗaura auren ko ba a ɗaura ba

Can wajen huɗu da wani abu na yamma tana ma zaune ne ta idar da sallar la'asar ne  Daddy ya kira ta da lambarsa tana ta mamakin yaushe ya dawo? 
Amma abin da ya tambayeta ne ya sa ta fara rarraba ido.

"Ummu Salma gamu a masallaci za a ɗaura auran ki, nawa kika yanke Sadakin ki?

"Naam"

Ta faɗa cikin rashin sanin madafa.
"E nawa kika yanke masa?
"Daddy duk abin da ka ce."
"Aa haƙƙin ki ne."
"Dubu dari."
Ta ji bakinta na faɗa.
"Tana jin Daddy na maimaita ta ce Dubu ɗari daga nan ta ji mganganun mutane ta cikin wayar sannan Daddy ya kashe wayar, abin mamaki yaushe Daddy ya dawo? Ba daɗewa Mami ta dawo da ta ba ta labarin Daddy ya kirata kamar fa yana Jimeta.

"Yana can, Baffa ya ce sai ya dawo shi zai ba da auran ki."

Mami ta faɗa cikin fara'a. Daga gani abun ya yi mata daɗi.

"Shi ne ya ta so a yau, saboda shi ne ma ya sa daurin auran ya kai bayan la'asar."

Ta sake faɗa tana kallonta.
Ummu dai ta kasa magana saboda yadda jikinta ya yi wani sanyi ƙalau Mami ta shiga kiran Basira wacce ta fito tare da Hanan biye da ita tana ganin Mami ta nufeta tana kiran sunanta.

"Mami oyoyo."

"Oyoyo Hanan."

Mami ta faɗa tana cafe ta, tare suka zauna saman kujeran falon tana shafa kanta.
"Barka da dawowa Mami."
'Yauwa basira."
Sai ta kalleta yadda ta ɗan rankwafa cikin ladabi
Ummu ta juya za ta bar falon kenan Mami ta kalli Basira tana faɗin" rangwaɗa ma Ya Ummu guɗa yau an ɗaura mata aure Basira."
Ai Basira na jin haka ta miƙe ta rangwaɗa guda har sai da Uummu ta toshe kunnuwanta ta bar falon da gudu Mami ta bi ta dariya Hanan ma na ta yata.

"Ma sha Allah, Allah ya sanya alheri Mami."
"Amin Basira.  Yau ki shiga kitchen Amarya ba yanayi gobe ayi abinci da yawa Hamisu zai kawo takeway, za a fita a yi sadaka."
"Allah ya biya ki Mami."
Ta amsa da Amin nan ta bar falon tana ta ya Ummun Murna domin ta ɗan san wani labarinta, tana tausayin kanta amma tana tausayin Ummu Salma duk da tana cikin gata.

Ummu Salma ɗaki ta shige tana ta kuka, ba ta taɓa hasaso ma kanta a aure awannan tsakanin ba, sai ga shi kaddara ta sake juya rayuwarta a karo na biyu, wayarta ma kasheta ta yi domin ba ta son ma a dame ta. Mami ma ba ta sake nemanta ba, sai dare da Daddy ya dawo ya kirata.

"Ga Sadakin ki, na ba da auranki akan dubu ɗarin da kika lamince."

Daddy ya faɗa bayan ta karɓi kuɗin a farin takarda. Mamaki take yi, kenan da gaske ne?

"Allah ya ba ku zaman lafiya. Kin yi dacen samun nagartattacen miji Ummu Salma."

Kowa na faɗin ta yi dace amma ba a faɗa mata waye mijin ba, itama ba ta son sani shi ya sa ba ta tambaya ba.
Har da goro da dabino da minti duk Daddy ya taho da su, ita dai kuɗin kawai ta karɓa ta koma ɗaki ta tasa su gaba tana sharɓan kuka komai ya dawo mata sabo, yanzu kuma ina za ta je? Wata rayuwa za ta sake faɗawa? Menene makomar Hanan?

Washegari tun safe Mami da Basira suka shiga kitchen jalop din shinkafa da nama suka dafa aka saka a takeway ɗari har da matar Sunusi ta zo ta taya su aiki Ummu na ciki ba ta fito ba, ta dai fito sun gaisa da Mami, ba ta kawo dalilin auran ta ne ya sa Mamin yin Sadaka ba, da yake ta san suna yi duk karshen wata amma yau ɗin na daban ne har da drink da ruwa.
Hamisu ya fita da shi a mota zai je makarantan almajirai a hayin banki zai raba musu.

Ummu abincin ma ba ta ci ba sai da Mami ta leƙo ta yi mata mgana sannan ta fito ta sha tea, ga shi dai ita ta amimce amma kuma abin duk ya dame ta. Ta yi na farko ba ta dace ba yanzu kuma ba ta san wata irin kaddara za ta sake faɗawa a karo na biyu ba.

Sannan da ta kunna wayarta kowa fatan alheri yake yi mata cikin yayyenta,  Hamma Jibo har da cewa Amarya, shi ko Hamma Mustapha wani suna ya kira ta da shi our princess
amma ba wanda ya kira sunan mijin da  aka aura mata, itama ba ta tambaya ba har Baɗɗo da suka yi waya murna take yi mata.

"Sisna, tabɗijam kin samo mai zafi wannan karon. Cancaɗi."

Amma ba ta faɗa mata waye ba, itama ba ta ce tana son sani ba.

"Sisna, ni fa bana son auren nan. Ban zan iya ma Baffa Gaddama ba ne."

"Sisna, ai wannan auren na musamman ne, ya doke wannan auren naki na farko, tab ai tazaran kamar tazaran kasa da sama ne, Habibun banza shi ko a hanya bai isa ya haɗa kafaɗa da mijin ki na yanzu ba wallahi."

Ummu dai ba ta biye ma Baɗɗo ba, ba ta son ma tana jin sunan Habibu saboda tsanar da ta yi masa.
Har Ammah da suka yi waya ba ta nuna mata wani abu ba sun dai gaisa kamar Yadda suka saba, kuma ta ji ta duk a cunkushe ba cikin walwala ba. Baffa ne ma da suka yi waya ya dinga saka mata albarka cikin farincikin da ta jima ba ta ji shi a cikin sa ba.

Sati ɗaya da ɗaurin auran ta, har a lokacin ba ta saki jikinta ba. Sukuku take, da gaske ne ta tsani aure domin ta tabbata ba komai cikinsa sai baƙin ciki da da dana sani, ta fa gwada kuma ba ta dace ba.

Amma ba ta da yadda za ta iya tunda ta amsa ma Baffa an riga kuma an ɗaura baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.
Mami kamar murna ma take yi domin ba ta ga alamun ta damu da ganin yanayin ta ba, tunda aka ɗaura auren nan duk dare sai ta yi kuka, so kawai take yi ta samu wani dalilin da za ta sauwaƙe ma kanta wannan auren, in ta tuna auren sai ta tuna makomar rayuwanta anan gaba, ba ta san mijin ba amma ta fi karkata tunaninta da wataƙila daga can Mubi ne tunda ta ga kowa ya san shi.

Ranar Ummu ta yini  cikin nazari, duk hanyar da za ta ɓulle da ita sai kuma ta je karshe ta iske a toshe take, yini ta yi a ɗaki ba ta fito ba kamar wata mara lafiya
Hanan na wajen Basira, kamar ta san yanayinta na yau ba ta zo ta yi mata rigima ba. Tana kwance Basira ta zo tana faɗa mata Mami ta yi baƙo, mamaki ya kamata wani irin baƙo kuma? Kuma Basira ta ce yana Falo, kafin ta fita ta yi ta kiran wayar Mami ta ji ko ta san da zuwan baƙon amma wayarta ba ta shiga shi ya sa ta saka mayafin abayan dake jikinta ta fita zuwa falon Mami.
Duk a tunaninta tunda aka ce ya shigo har falo to ko daga Jimeta ko daga cikin dangin Daddy shi ya sa ta fita kanta tsaye ba fargaba.

Mamaki ya sandarar da ita lokacin da ta yi arba da ganin Hamma Lamiɗo zaune a falon Mami yana ɗauke da Hanan a jikinsa tana ta wasa da sajen fuskar shi.

Sanye yake da farar shadda, har tana ƙyalli kansa da hula amma saboda suma a saman gashin hulan tasa baƙa ta tsaya.
Ya ji shigowarta amma bai iya ɗagowa ya kalleta ba.
Ummu ta ce a ranta lalle Mami na da Babban baƙo
Domin tunda ta zo gidan ba ta taɓa ganin ya zo ba sai yau.
Me ya kawo shi? Ta tambaya a cikin zuciyarsa.

"Ko kin manta Mami mahaifiyarsa ne?

Wata zuciyar ta tunasar da ita abin da ta manta. Har ga Allah mantawa take yi da Mami ce ta haifi Hamma Lamiɗo.

"Barka da zuwa Hamma Lamiɗo."

Ta faɗa bayan ta ɗan ƙariso falon. Da farko ta so ta yi wucewarta ne saboda Mami ta tsaya da kuma tuna ya fa taimake ta, da jininsa take rayuwa a yanzu.

"Lafiya."

Ya amsa mata, sau ɗaya ya kalleta bai sake ba, wasa yake yi ma Hanan. Ta so ta yi komawarta ɗaki ne domin ita yanzu neman ma kanta mafita take yi amma ganin yadda ya ɗauki Hanma ya sa ta ji sanyi a zuciyarta, ko ita bai yi mata kallon Daraja ba ta ji daɗi da ya yi ma Hannan kallon mutumci shi ya sa
ta je kitchen ta haɗo masa ruwa da lemu, Daddy ba ya nan ya je Abuja tun jiya amma a yau Mami ta ce zai dawom

Har ta kawo ruwan ta ajiye ta fita falon bai ɗago ba, itama ba ta damu ba ɗaki ta koma ta yi kwanciyarta tana cigaba da sabon lissafin da ya kamata tun bayan auran da aka ɗaura mata, tunani take yi me ya sa Allah bai amsa addu'arta ba? Ita da har a masallacin Madina ta roƙesa da Allah ya sa ta mutu ba ta sake aure ba. Me ya sa kuma Kaddara ta sake buɗe mata wani sabon shafin rayuwa? Ba ma batun ba ta son mijin da aka aura mata ba, auren ne gabaɗaya ba ta so. Ta ma manta da baƙon Mami ta na ciki tana tufka tana famam warwara
Har Mami ta dawo  ba ta sani ba sai da ta shigo ɗakinta sannan a lokacin ta san ta dawo 

"Kika zo nan kika kwanta Ummu?

Mamin ta faɗa tana kallon ta.

"Mami sannu da zuwa Yaushe kika dawo?
Ummu ta faɗa tana ɗan miƙewa zaune a saman gadon data ke kwance.

"Ban daɗe da dawowa ba. Sai kika bar baƙo shi kaɗai a falo Ummu?

"Mami to na ga Hamma ne ya zo, kin san shi ba ya son hayaniya shi ya sa na baro falon na dawo ɗaki ."
Ta faɗa tana ɗan mikewa zaume.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna ba ai ba za ku fahimci juna ba."

"Na'am"

Ummu Salma ta faɗa tana kallon Mami domin sai ta ji kamar ba ta ji daidai ba.

"Ko ba ki san baƙon ki ba ne?

Mami ta sake faɗa tana kallonta.
Ummu ba ta son ta dire ƙasa ba sai da ta ganta a tsaye kan kafafunta.

"Baƙo na kuma?

Ta faɗa cikin mamaki.

"Baffa bai kira ki ba?

Mami ta sake tambaya, domin sun yi mgana da Baffa shi ya faɗa mata Lamiɗon zai zo su yi magana da Ummun a tunanin ta Baffan ya kira Ummun ya sanar mata.

"Mami."

Tana ta yi magana amma ta kasa jikinta ya yi wani irin sanyi.

"Ki gyara jikin ki, ki je ki same shi."

Mami ta faɗi haka da sauri lokaci ɗaya kuma tana barin ɗakin.
Ai sai Ummu Salma ta ji kamar ta daina jin mgana ta kurmance, kamar shiga da fita haka ta ji kalaman Mami.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna da shi ba ta ya za ku fahimci juna?

Idanuwanta sun fito waje saboda firgici da razana, in dai har ta ji daidai to Mami na nufin Hamma Lamiɗo ne mijin da aka aura mata.

Innalillahi wa'inna ilaihirraju"um."

Ta faɗa a zucci da sarari lokaci ɗaya ta ɗora hannu akai ta fashe da kuka.

"Ina ni ina Hamma Lamiɗo, wallahi bana son shi."

Take faɗa tana kuka lokaci ɗaya ta koma ta zube kan gado, ji take yi kamar ta yi hauka, ina, ina za ta iya zaman aure da Hamma Lamiɗo, ai an gudu ne ba a tsira ba, sai ta ke jin kamar ta fita ta yi ta gudu kar ta tsaya, ita da ko inuwa ta minti goma ba ta taɓa haɗawa da shi ba, ta ya ya za ta iya haɗa inuwar aure da shi? Mafitan ta na ƙarshe shi ne ta samu mijin ta roƙe shi ya sauwake mata domin ba za ta iya masa biyayya ba, amma jin wai Hamma Lamiɗon ne mijin tuni lissafinta ya ƙwace. Ko burkutu ta sha ba za ta iya doguwar magana da shi ba, in tunanin ta ma ya kawo mata sunan shi ji take yi kamar ta haukace. Innalillahi ta shiga ta uku ta lalace. Ita Ummu Salama ina ita ina Hamma Lamiɗo?



Ƙarshen littafi na ɗaya.



*Janafty*