77
by @zahrabmrs02
gari ya waye a birnin Boston cikin sanyi. Farhana ta tashi da wuri ta shirya su Lamido, harda Kevin tunda tun jiya bataji duriyar su Hailey ba ,fuskarta tana nuna alamun tunani. Bayan tayiwa yara breakfast Sun koma gefe suna wasa dan Ak ya mata text Yau sai da yamma zai zo daukar su.Tana zaune a falo tana shan shayi, sai ga su Isabella da Hailey sun shigo , kowacce tana dafe kai saboda ciwon kan da buguwar jiya ta bari (hangover).
"Maryam, oh my God!Muna ba ki haƙuri," Hailey ta fara magana muryarta a dashe. "Jiya mun bugu sosae, ban ma san sanda kika bar Club ɗin ba. Liam ne ya kaini gida, ashe ke ma kin tafi."
Farhana ta yi murmushi kaɗan. "Ba komai Hailey. Abdulkadir ne ya ganni, shi ne ya dawo da ni gida."
Isabella ta zaro ido, ta manta da ciwon kan da take ji. "Abdulkadir? Ya zo Club ɗin? Me ya faru tsakaninku?"
"Ba abinda ya faru. Ya dai ga wani mutum yana neman takura min ne ya ja hannuna muka fita. Ya ajiyye ni a ƙofar gida, mun yi magana kaɗan, sannan ya tafi," Farhana ta ba su amsa a takaice.
Isabella ta zauna kusa da Farhana, tana juya wani katin kasuwanci (business card) a hannunta. Fuskarta tana nuna damuwa, ba irin Isabella mai nishaɗi da aka sani ba.
"Maryam, jiya na yi babban kuskure," Isabella ta faɗa a hankali. "Wancan sabon yaron da kika gani na bi jiya, sunansa Julian. Mun tafi gidansa, kuma... we had a one-night stand."
Farhana ta kalli Isabella cikin mamaki. Ta san al'adar su daban take, amma ta san Isabella tana da saurayi.
"Amma Isabella, kina da Ethan a New York fa ? Kin ce yana sonki sosae," Farhana ta tunatar da ita.
Isabella ta yi ajiyar zuciya. "Haka ne. Ethan mutumin kirki ne, kuma he's very loyal. Amma kwanan nan nake jin kamar zamantakewarmu tana wasa, ba ma ganin juna sosae. Amma yanzu ina jin ba daɗi, ina jin kamar na ci amanarsa. Amma Julian... yabani katin sa, kuma akwai wani irin connection da na ji da shi jiya ,girls Julian ya bani da best sex of my life ,oh my god yanzu haka tunawan danayi ya fara sani wanting more more and more of him ,wanda ban taɓa ji da Ethan ba. Ina tunanin ba Julian dama, amma Ethan yana Raina
Hailey ta kalli Isabella. "Isabella, Ethan yana da kyau kuma yana da kuɗi, amma idan babu wutar soyayya, rayuwar za ta yi tsami. Shi kuma Julian, kinsan fa one-night stand ne kawai kuka yi, baki san halinsa ba."
Farhana dai tana saurarensu ne kawai. A ranta tana tunanin yadda rayuwar Turai take da sarƙaƙiya. Isabella tana tsakanin Ethan (amintaccen saurayinta) da Julian (sabon mutumin da ya girgiza zuciyarta a dare ɗaya).
"Kowa da irin tashi jarrabawar," Farhana ta faɗa a ranta. "Isabella tana kuka kan maza biyu, ni kuma ina kuka kan yadda zan samar da $12,500 na karatun jirgi na."
Duk da captain miller be fada mata amma tayi research tasan tana bukatar $12,500 ta gama solo flight dinta
Bayan su Isabella sun wuce ɗakunansu, Farhana ta koma kan lissafin kuɗinta. Maganar Abdulkadir ta jiya tana sake dawo mata: "Do you really want this life?"
Ta girgiza kai. "Eh Abdulkadir, na fi son wannan ruɗanin na su Isabella da wahalar neman kuɗin Solo Flight ɗina, da in koma gidan da babu gaskiya, babu natsuwa
Farhana ta tsinci kanta a cikin wani irin yanayi da ba ta taba tsammani ba. Don ganin ta kammala sa'o'in tashi (flight hours) a cikin wannan kankanin lokaci, dole ta biya karin kudi. Saboda haka, bayan aikin NGO, Farhana ta samu wani aiki na wucin gadi a matsayin Waitress a wani babban gidan cin abinci (Italian Restaurant) duk dare take zuwa Bayan ta tashi daga Aikin Wajan 5pm ,zata tafi restaurant Wajan 8pm
Rayuwar waitress ba ta da dadi. Farhana takan shafe sa'o'i biyar tana tsaye, tana daukar tire mai nauyi, tana kai abinci ga mutanen da wasu lokutan ba su da tarbiyya.Kafafunta sukan yi kumburi, bayanta kuma yana mata zafi tamkar za shi rabu biyu.Akwai ranar da wani bako ya watsa mata ruwa a jiki saboda kuskuren oda, Farhana ta so ta fashe da kuka, amma sai ta tuna da kiran Abbi da kuma burinta na zama Pilot, ta hadiye kukan ta share ruwan.
Daga gidan cin abinci da karfe 11 na dare, Farhana takan nufi gida ta yi bitar karatun jirgi har karfe 2 na dare. Da asuba karfe 5, tana filin jirgin Hanscom Field don fara early morning flight Idanunta sun fada saboda rashin barci.Captain Miller takan daka mata tsawa: "Maryam! Focus! Rayuwarki tana hannun wadannan levers din!Hailey da Liam Sun zama sanyin idaniyar Farhana. Sune ke kai su Lamido makaranta su dauko su• Briana ma yawan zuwa , tana kula da su Sultana wadda har yanzu take yawan kukan neman AK.
Duk da wannan wahalar ta zahiri, akwai wata wahala ta zuciya dake cin Farhana daga ciki. Duk sanda Fateeha ta kira ta don ba ta labarin shirye-shiryen auren ta, Farhana takan ji kamar maciji yana sara mata zuciya.Ta kalli hoton Umma (Mahaifiyar Fateeha) a wayarta, tana jin wani irin guiltiness Fateeha kawata ce, ta tsaya min a lokacin kuncina, amma ni kuma ina rufa wa wanda ya nakasa mahaifiyarta asiri ban fada mata ba." * Tsoronta daya ne: Idan ta fada, za ta ruguza farin cikin auren Fateeha. Idan kuma ba ta fada ba, ta ci amanar kawarta.
Bayan kwanaki goma na azaba, gumi, da kukan zuciya, Farhana ta tsaya a gaban Captain Miller a dakin tattaunawa.
"Congratulations, Maryam," Miller ya fada yana sanya hannu a kan takardun ta. "Kin kammala dukkan sa'o'in da ake bukata. Nan da sati biyu zaki fara Solo Flight (tashi ke kadai ba tare da mai taya ki ba). Ke ce dalibar da ta fi kowa saurin kammala wannan matakin a wannan shekarar."
Farhana ta durkusa a kasan ofishin ta fashe da kuka. Kukan farin ciki ne, kukan sauke nauyin da ya jima a kanta. Ta tuna ta ga cewa yanzu ta riga ta wuce wurin.
"Na gode Allah,"
Ranar Lahadi ce, ranar hutu ga Farhana daga aikin NGO, amma zuciyarta ba ta huta ba. Tana zaune a karkashin wata katuwar bishiya a Boston Public Garden. Iskar bazara tana kadawa a hankali, tana gauraya da kukan tsuntsaye da muryoyin yara dake wasa.
A can nesa, ta hango su Lamido, Hailey, da Kevin suna gudu a kan ciyawa, Briana tana biye da su tana dariya. Farhana ta jingina kanta da jikin bishiyar, idanunta cike da damuwa.
Lissafin Karshe (The Final Hurdle)
Kalaman Captain Miller na daren jiya da sukayi waya suke ta yawo a kanta:
"Maryam, kin nuna kokari. Amma don fara Solo Flight dinki da kuma kammala dukkan takardun lasisi (License fees, fuel, and insurance), kina bukatar karin $12,500 nan da sati biyu. Idan baki biya ba, dole mu dakatar da karatun dake."
"$12,500..." ta fada a hankali. Ta yi lissafin albashinta na waitress da na NGO, ko ta hada su wuri daya ba zasu kai ko rabi ba. "Ina zan sami wannan kudin ba tare da na koma ga Abdulkadir ba?"
Tana cikin wannan zurfafa tunanin, sai ta ji takun tafiya a kan busassun ganye. Wani mutum ne ya karaso wurin, sanye da riga mai sanyi (hoodie) , sanye da gilashin ido na masu karatu. Ya zauna a daya gefen bishiyar, ba tare da ya lura da cewa akwai wata a wurin ba.familer kamshin turarensa ya mamaye wajan
Farhana ta kalle shi ta gefen ido. Gabanta ya fadi. FAROOQ KUMA?
my people una no dey comment again 🤭🥺