unveiling the prince
by @surayyahms
*8.* unveiling the crown prince.
wajajen yamma labari ya fara isowa kunnen uwarjini game da sauya zuria da kuma juyin mulki da akayi wa masarautar dala (kano emirate) duk dama ta san yin hakan ba wata aba mewuya ba ne awajen ahalin wazeris amma duk sadda ta tuna cewa hakn zaiyi ma mei martaba sarki murad zamkora ciwo fiye da zafin mutuwar ubans marigayi salim data dandana masa kwanan nan sai taji wani irin sanyi aranta data jima batajishi ba
babu shakka daga gobe tasan jikarta Abdallah wazeeri shine zai zauna akan kujerar sarki kuma shugaban yankin dala gabaki daya,snn sarki murad zamkora da duk wani karamin yankuna da suke wajen zasu kasance ne akarkashin ikon jikarta Abdallah dole ne ire iren su masarautar zamkora suy ma sarki abdallah biyayya, and..once again she have total control akan manyan maqiyanta sai yadda tagadamar yi wajen kaskantar dasu.
tun kafin wanda sukeje dalan sudawo gida ta umarci nana A akan ta sanar wa nana hafsa datake matar shugaba khaleefa da already take cikin maqoqi da idda cewa lokaci yay da zasu miƙa shamsan
zuwa dahrul zahra
tafiya ne me tsawo kuma acan xai karashi duk wani hidimar rayuwarsa da karatunsa harsai yazamo irin yarimar da suke bukata.
dan wann yarjejniyar auren da zata shirya masa anan gaba da zuriar maqiyansu kmr gadar zare ne datake ta shirya ma maqiya ya zamto itace take da cikakken iko akan zaman aure, duk wacce zaa auro ta zauna agidan yarima kamr baiwa, dan ba zaiyu wani jininta ya haifa musu jika daga jinin zamkora ba har abada.
shiyasa gabaki daya har cikin ran uwarjini bataso acewai ba anan agabanta shamsan xai girma har yazama cikakken ɗa namiji ayi aurensan agabanta dan ta samu damar sauya masa ra'ayi akan ahalin zamkora yadda take so.
tasan idan yaje dahrul zahra ya zauna da malamai zai koyi riqe addinin musulunci snn ya bar al'adarsu ta tsafi kmr yadda kakansa mrgyi khaleefa da baban sa abdallah suka bari ba.
to amma son datake ma jikarta Abdallah din ya riga ya zama mata rauni ya rufe mata ido sai batay wani jayayya akan tafiyar shamsan din ba kawai sai ta basu izini ita kuma ta shashantar da rashin jin dadinta a azuciyarta
bada jimawa ba Nana A taje har cikin killatacen chamber nana hafsa ta sanar da ita komi tana dawowa fadar mulki tasaka aka aiki wata baiwa domin taje ta kirawo hajarat sakeena
a hankali kofar sashen ya budu baiwar da aka aiko ta tsaya a bakin kofar cikin nutsuwa kanta asunkuye, hannuwanta a hade gabadaya jikinta na nuna tsantsar ladabi kafin ma ta karasa ciki.
the new king Abdallah shine jikar uwarjini namiji kwaya daya tall ahalin yanxu, kuma shima yazo ya haifi ɗa namiji ahaihuwar fari, shiyasa ake bala'in ji dashi sashensa agidan ma ba irin na kowa bane gini ne mai tsawo neoclassical cikin sa an gina manyan halls da aka lailayesu da cathedral length silk curtains masu faukar ido da tsayin gaske sun sauka daga sama har kasa suna kadawa a hankali
komai na cikin sashen na dauke da natsuwa dan banda sanyin Ac da qamshin wani irin turaren wuta masu tsananin dadi da saka nitsuwa daya mamaye bakajin komi...
saida mai tsaron kofar ya karbi izini snn aka bawa baiwar damar shigowa can ciki a tsakiyar wani mayen master queen sized bedroom daya amshi sunansa daki ta tafara cinkaro da kasaitaccen qamshin turaren matar abdallah wato hajarat sakeena, itama jinin sarauta ne daga dayan tsaftaccen zuriarsu na maruwa.
kyakkyawace tawuce misali gata da tsayi fuskar nan tata mai laushi da tsari, tana da tsiririn hanci da lebba masu tsananin laushi masu daidaito, kai duk wanda ya ganta zai rantse babu banbanci tsakaninta da deepika padukone dn kamar an dauko ta ne aka zubata a nan cikin tharim vale
tun bayan rasuwar surkuwanta shugaba khaleefa idanuwanta suke lullube da shakku da wani irin damuwa, fargabar zantukansa ya riga ya kama mata zuciya tunda taji mijin ta na ayyana batun cewa za'a dorashi akan kujerar mulkin kano, kenan zasu iya barin garin tharim vale har na tsawon lokaci kuma dolene ta koyi zamowa a dala kuma cikakkiyar gimbiya ga masarautar dala.
agabanta ɗanta ne shamsan, yaron da tsarinsa already yake nuni da irin mutumin da zai zama anan gaba fuskarsa nada wani irin kyakkwan tsari mai maseefar dauke ido ruwan idanuwansa is striking dim grey saidai a rikice kwayar idon nasa yake da wani irin hazo hazo aciki kamar hadari ne yake shirin tashi gashi da zurfi da maiko da kuma girma.
…wani irin kamilallen kyau da sanyin nutsuwa da zai tuna maka da fasalin dan sarkin dubai wato crown prince hamdan amma shamsan kuma yana da dogon baqin suma da ake daure masa ta baya kmar na jason mamoa, wanda duk dama kamanninsa baigama bayyana a fili basaidai daga kallo daya kariga ka san cewa yaro ne da zai zama cikakken dan sarkin da ba ataba ganin irinsa ba.
mahaifyarsa hajarat sakeena na tsaye akansa tana yawo da yatsun hannunta me tsananin laushi acikin sulbabben gashin kansa a hankali tana tsefewa cikin nutsuwa
lokaci zuwa lokaci hannunta na tsayawa tana lura da yanayinsa
sannan sai ta cigaba dan shamsan miskile na fitar hankali inbawai su dasuke iyayensa ba zaka dauka kurma ne dan da wuya kaga yay magana ko murmushi.
tunda ta fara tsefe masa gashinsa da yatsun hannunta yabi ya lumshe luuu in ruwan idanunsa baiya sauke ko numfashinsa a fili tsabar kamewa.
adede wannan lokacin ne baiwar ta karaso kadan daga bakin kofar ta durkusa ahnkli tace “rankishi dade…
batare da juyowa hajarat sakeena ta mata alamar tana jin ta snn ta dan dakata da motsin lallausar hannunta dake cikin dogon sumanshi batace uffan ba.
da ladabi baiwar tace
ranki shi dade uwarjini tana buqatar ganin ki a fadar iko..
cikin lumshe ido da budewa a hankali ta gyada mata kai wani sabon ajiyar zuciya ta saki hannunta ya sake motsawa cikin gashin shamsan…
sannan a hankali…ta cire hannunta cikin natsuwa, zagowa tay ta mika hannu ta kama na shamsan din tanata kallonsa ahnkli tace “sham..karkaje wajen baban ka kajira ni anan Ina zuwa…
kallonta kawai yay baice komi ba ta juya ba tare da ta sake magana ba ta nufi kofar dakin domin tasan daga wannan lokaci hala rayuwarta dana ahalinta zai iya canzawa na har abada.
bayan ficewar baiwar baifi da minti goma ba tashirya kanta cikin wani irin kasaitaccen golden lafaya bayinta na biye da ita ta iso sashen uwarjini
tana isowa sashen kai tsaye akay da ita fadar mulki inda ta samu
kusan kowa daya rage agidan yana nan dan dama zafar ne kawai dayabi delegates dinsu masarautar dala baya nan.
shugaba imran ne akan kujerar iko sai uwarjini agefe kusa da jikanta abdallah, sai nana A da nana hafsa, tareda ummu salma duk suna zaune cikin kasaitaccen shiga. tana isowa ta zube kasa da girmamawa da ladabi tay gaisuwa
Kamar yadda tay harsashe kusan lokaci ne yayi da za'a rabata da babban danta shamsan na tsawon lokaci nn ma aka fara bayyana mata dokoki, sharuda, da tsaruka na kasancwrta gimbiya na farko sa zata fito daga cikin xuriar tharim vale.
babban nauyi ne aka hau daura mata akanta bana wasa ba saidai duk nauyinsan nan baikai matsanancin ciwo da rauni datakeji aranta na karsashin rabuwa da danta shamsan da zatayi ayau ba.
bayan an gama kayyada mata dokoki, sharuda da iyaka na zamowa gimbiyar yankin dala, nan uwarjini ta saka dokarta na cewa muddin shamsan ya tafi dahrul zahrah. babu wanda zaije ya dubashi har sai nan da shekara daya, babu kira, babu zuwa ziyara. babu saqo, in ya cika shekara guda ne acan za'a bawa iyayensa izini suna zuwa garin dubashi sau biyu kacal a shekara. amfanin hakan shine akaucar dashi daga dukkan abunda xaina saka masa rauni da dauke masa hankali, snn agina masa intense focus, discipline da emotional maturity dinsa.., a tabbata ya xamo jajirtaccen namiji kuma yarima da ake bukatar gani nan gaba.
zantarwa ne mafi rauni da zuqi a zcyar hajarat sakeena amma babu yadda ta iya haka nan ta amince sbd babu wanda ya isa ya saɓa wa dokokin uwarjini
gobe da safe ana kammala nadin sarautar itama zasu tattara su koma kano da zama ta har abada,
Nana hafsa aka zaɓa akan idan tagama idda zata koma cikin garin kanon da zama atare da su a matsayinta na queen mother kuma uwa ga sarki dazata zame musu babba atacan.
…bayan an gama da wannan fannin…
fadar ta sake nutsewa cikin wani irin shiru mai nauyi, irin shiru nan da yake dauke da raunin hukunci, babu gardama babu ja da baya uwarjini bata sake cewa komai ba.
Ummu salma kuma duk ta kaqu akawo batun aurensa dan ta samu daman saka baki dan tana so taji shin menene nana A taje ta gayawa uwarjini jiya da dare game da batun sako jikarta leelah acikin alkwkarin hadin aurensu da shamsan.
a hankali hajarat sakeena ta sake sunkuyar da kanta bayan angama bata umarni babu alaman hawaye ko rauni sai wani irin numfashi da ya tsaya mata a kirji kamar an daure shi.
ta mike tsaye cikin nutsuwa, ta juya ba tare da ta sake kallon kowa ba, tafiyarta a hankali cikin nitsuwa amma cike da wani irin dauriya na dole wanda ba daga zuciyarta yake fitowa ba.
cikin kankanin lokacin ta koma sashenta dan tayi bankwana da ɗan ta shamsan
idanunta kusan arufe take tafiya tanajin tsananin rauni kofofin sashen nata ake bude mata daya bayan daya amma batama lura da komai ba dan zuciyarta gaba daya yana wajen tunanin inda ta barsa ne.
tanakaiwa bedroom dinta kuwa ta samesa a zaune, kamar yadda yake, bai motsa ba snn babu alamar ya gaji ko ya kosa, ruwan idanuwansa masu maiko da kaifi suna kallon wani bangare na dakin kmr yana ganin wani abu da ba kowa ke iya gani ba.
da shigowarta dakin yaji sallamarta amma bai tashi tsaye ba bare ya furta komai ruwan idanuwansa kawai ya danmotsa zuwa gareta ya kalleta da kallo daya mai zurfi mai cike da kasaita da nutsuwa me sanyi.
cikin tattaro makanta natsuwa ta tsaya cak daga inda take tanata kallon fuskarsa tanajin kafafuwanta suna yi mata sanyi da nauyi jin takasa matsowa kusa dashi harna wasu yan dakikun lkci…
ajiyar zuciya ne ya kwace mata tare da yin karfin hali ta tako a hankali harta iso gabansa tazauna a gabansa akan wani oak royal chair ba tare da ta damu da wani tsari ko martaba ba..
lallausar hannunta ta mikaar direct yatafi smoothly a kan fuskar sa tanamai rike masa kumatunsa biyu cikin tausasawa jin yadda rauni yake kkrin riqeta.
suna kallon juna ahnkli sosai ta kirashi da full name insa da bata saba kira a fili ba tace
..“shamsan…..
cikin idonta ya kara kallewa ahnkli batare da ya amsata ba..
ruwan idanuwansan ne kawai suka kara zurfi acikin nata da suka sarkafu cikin na juna.
yanaji tagama masa bayanin inda zaije wnda harta gama bayanin baice uhmm bare uhmm uhm ba face da yadan lumshe idanunsa ahankali tare da mata alamar cewa ya fahimci komai…
wanda koda ma bata gaya masa ba itakanta tasan zai iya sanin inda zaije din tunda kusan kowani lkci yana tare da mahaifinsa ne.
duk tatuna cewa daga yau da bazata sake sa kashi a idonta ko jin muryansa har na wani shekara guda ba hakan yana balain karya mata zuciya fiye da komai.
numfashinta yama fita da karfi amma haka ta danne komai tace "..is time to get dressed kai kawai ake jira.!
kallonsa takarayi ganin har yanzu bai ce komai ba face dan yatsunsa da suka motsa kadan sai kafin nan yadago lallausar hannunsa a hankali ya rike nata da yake kan fuskarsan ya hade da lallausar nashi ya hau shafawa da alamar rarasshi ganin
duk takasa daurewa hawayenta datake kan dannewa atake suka ciko suka fara zuba cikin rauni da sanyin jiki.
wani irin shiru ne ya sake ratsa tsakaninsu bai dena shafa mata saman hannunba har saida ta gama zubda hawayen tasamu sauki aranta, aransa ya tattaba cewa taji sauki saurki nd she is calm kafin nan ya kwace hannunsa a cikin natan ahnkli yamike kai tsaye ya fita yabar mata dakin cikin nitsuwa ya wuce nashi sashen dake kurkusa dana babansa ya fara shiri dakansa dan ko kadan baison servants akusa dashi.
he prefer to be alone, or with his father all the time.
*******after one hour kusan komai cikin tsari da nutsuwa akayishi duk dama zuciyoyin wasu na karyewa taciki
ana daf kafin kafewar rana harabar gidan wazeeri tharim vale ta cika da jerin tsadaddun motoci na alfarma masu tsaro da daukar ido qirar mercedez GMG bakake kirin.
private jirgin da zai dauki shamsan zuwa dahrul zahra dake can qasar moroco ya riga yashirya a Abuja intnl airpot snn kowa ya san wannan ba rabuwa ta yau da gobe bace zai dauki lokaci kafin su sake ganinsa.
hajarat sakeena na tafe ahnkli fuskar ta cike da wata kalar natsuwan da take tilasta makanta taciki
sarki abdallah yana tsaye kadan daga gefenta tunaninsa duka naga kan dansa ne duk dama fuskarsa babu murmushi babu alamr wani rauni a fili amma kuma kwayar idanuwansa suna nuni da kulawa mai zurfi.
nana hafsa ce a tsaye gefensu hannunta rike da tasbaha bakinta na motsi a hankali da addu’a da karamar kanwar shamsan din wato rihanna wazeeri agefenta wacce bata gama fahimtar abunda ke faruwa agidan bama tukuna
harsaida uwarjini tagama zantawa da wayanda zasu wuce dashi dahrul zarah snn ta juyo kamar kullum her calm steps always carries heavy grace da irin ego din nan na jinin royaltis
Allah ne kadai yasan inda ta tsani wannan tafiyar da shamsan zaiyi saidai ko kadan ba ta nuna a fuska ba,
ruwan idanuwanta kawai tabi ta tazuba akan shamsan din da yake fitowa daga cikin sashensa sanye da wata all black french design na Ermenegildo Zegna anmasa long chester overcoat daya daura akan wata turtle neck casual na brioni yana tafiya a nitse.
jikinsa da tsayinsa bai kai na manya ba amma kasaitaccen tafiyarsa me tafe da wani irin aji ta isa takasaka ɓarin jiki da mamakin irin intense royal aura da yaron yake ji dashi.
fuskar sa babu wani emotions shi bai daure ta ba, kuma bazadai ka kalleshi kai tsaye kace fushi yake yi ba saidai kuma bakazata taɓa iya tun karosa batare da kaji wani irin sanyin tsoro ko shakkar masa magana kai tsaye ba..
idanuwansa masu kaifi da tsananin kyau suna kallon gaba a haka har ya iso gaban mhfiyrsa ya tsaya yadan yi shiru
hajarat sakeena takalle shi kmr wacce takeson haddace komai na fuskarsa duk ta kasa cewa komi sbd bataso tanuna wani rauni akan danta musmn ma agaban su nana A da uwarjini
a hankali babansa ya sunkuya kadan kmar zai gyara masa wuyan rigar overcoat dinsan yanamai share masa wani abu da babu shi a jikinsa acikin haka ya dan dafa kafadunsa batare da ya rungume shi ba dan basu da wannan damar nuna raunin a fili..
muryasan kasa kasa suna kallon juna yace "shamsan. ka kula da ibaada ka riqe addua snn ka dawo min da ranka bayan ka zama irin yariman da suke so saidai kar ka manta da cewa kanada mahaifi da zai kareka akowani hali. ahnkli almost in a whisper yace i knw u can do this!
shamsan ya dago kai yakalle baban nasa na dan lokaci can sannan ya gyada masa kai nn sukama junansu kallo daya mai nauyi basu ce komi ba.
sai ya juya batare da ya kara kallon baya ba ya fara tafiya izuwa gaban motocin.
kusan kowa ya tsaya yana kallon yadda ya ke tafiya har isa gaban motar da already an riga anwangale masa shi cikin dakewa da nitsuwa ya shiga ya zauna abunsa.
masu gadinsa, bayi, da hakimai da aka shirya zasu zauna dashi acan duk sukayi sallama da kowa kafin kace wani abu motocin duka sun fara tafiya...
wani irin shiru wajen ya dauka babu wanda ya motsa face har saida motocin suka bacewa ganinsu.
nan me kusan kowa ya koma cikin sashensa amma banda hajarat sakeena dake tsaye a inda take har sai da ta samu nitsuwa sannan ahankali cikin sauke numfashi daya mai nauyi ta kama hanya izuwa cikin gida har a lokacin bata sake ta kara zubda hawaye ba.
itama kusan dolene ya kama yau yau din nan tafara shirin barin musu gidan domin yanzu ita gimbiya ce na yankin dala gabaki daya tasan rayuwarta da komi nata ya sauya kenan har abada.
#SURAYYAHMS
TALES OF THE WAZEERIS2026
ayi coment dan asamu kari anjima
idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata
*AREWABOOKS*
*@SURAYYAHMS*
*WATTAPAD @SURAYYAHMS*
*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED*
#SURAYYAHMS
#COMEBACK SERIES
2024/2025