TALES OF THE WAZEERIS

the new king

by @surayyahms

9. The crown.

har ta isa chamberta babu wata mata daga cikin surkunayen gidan ko yayansu da suka shirya tahowa cikin sasshenta domin mata jaje ko tayata jimamin bankwana da danta shamsan datayi

dan dama irin xaman jiji dakai da gasar ikon nan kawai akeyi agidan duba da kusan duka ƴaya da surkunaye sun jima suna jin haushi da qishin hajarat sakeena sabida bayan uwar jini babu wata mace a ahalin wazeeris data haifo musu ɗa namiji a haihuwar farko kuma a tsatson marigayi shugaba khaleefa da kusan kowani ahali da zuria dake karkashin tharim vale suke balain darajawa..

Duba da yadda kowacce mace take mugun jiji dakanta tare da xuba kasaita a ko yaushe kowaccensu tana killace ne acan cikin sashenta da full time servants dinta 24/7 akewaye da ita

Banda baqar maqirci da son ganin wata ta fi wata daraja da kima a zuriar wazeeris babu wani abunda suke ayayyanawa ga juna

duk dama bakasafai suke da damar fitowa tsakar gidan, ko samun iko ko wata daman tsoma baki akan duk wani hukunci da uwarjini take yankewa ba musmn ma akan abunda yashafi rayuwar yayanta da jikokinta ba, but lowkey kowacce mata tanaji aranta inama ace da itace ta haifi ɗa namiji me masifr kyau da kwarjini kamr shamsan wa ahalin gidan.

daga kan matar shugaba imran wato ummu zulaiha har izuwa kan karamarsu ummu bilqees datake mata ga zafar hamshakai ne na wuce misali dan kusan kowacce tana jin cewa ita watace a duniyar nan, musmn da ynx da akasan cewa shugaba khaleefa ya riga ya rasu sn dansa abdallah ya zama sarkin dala

babu shakka shugabancin tharim vale da dokoki xai karkata ne ya dawo hannun mazajensu da yayansu da zasu haifa anan gaba.

da can ummu zulaiha da ummu bilqees sun so su haɗe kansu sbd basa kaunar hajarat sakeena sam sam tun akan batun haihuwar namiji datayi ita daya acikinsu, saidai yanxu da batun shugabancin tharim vale ya shigo ciki atake kowacce tafara kkrin yin nakanta suka fara aje batun common enermy dinsu agefe dan suma adama dasu a kujerar iko na tharim vale.

hakan yasaka ummu xulaiha ta dawo gidan da shiri da kuma wani irin boyayyen fargaba tare da tashin hankli acikin ranta wanda duk dama tasan ynx ta riga wuce matsayin raini kasancewarta matar shugaban tharim vale amma kuma tana balain tsoron karda matsayinta yazo ya gushe da wuri ya koma ga ummu bilqees, sbd ƴa mace kawai ta haifa wanda haryau da yarta maridan ta doshi cika shekara 16yr aduniya bata kara samun wani haihuwa ba.

agefe kuma ganan ummu bilqees din dats heavily pregnant kusn haihuwa ko yau ko gobe kuma anjima ana ce musu ɗa namiji zata haifa, tasan idan har ummu bilqees ta haifi ɗa namiji toh babu wani tantama ko shakku daga zarar shugaba imran yazo ya rasu ko ya sauka daga kan kujera toh shgbcin tharim vale zai koma hannun qaninsa zafar da unborn dansa ne....

tun hakan bai faru ba amma jitake kamar tafi karfin ma ace macen dataxo ta sameta agidan waxeeris wacce tariga ta bata ratan shekaru, tarin dukiya da ilmi kamar bilqeesu tazo ta haifi ɗa namiji agabanta har kuma zamani ya zago kansu da zafar da unborn son insa su zamto shuwagaban tharim vale anan gaba.

tunda ta iso gidan ta kasa samun nitsuwa dan ji take dolene kawai tay duk wani tsiyar da zatay dan itama ta samowa mijinta shugaba imran magaji tun lkci bai kure mata ba

tunda ta shigo tharim vale bata wani kula yarta marida ba kawai tunanin yadda zatay ta sake daukar ciki dan tasamu ɗa namiji wa mijin ta shugaba imran shine ya bala'in cike mata cikin kwkwalwar ta ba damuwar kowa ba.

ita kuma ummu bilqees is like a silent snake, itace karamar surkuwa agidan amma sosai take lissafe da komi aranta saidai ita bata daga hankli sbd duk tsiya tasan daga zarar ta haifi da namijin da akace na cikinta daga mijinta zafar din har ita da dansu da zasu haifa sune zasu zamo new future favourites din uwarjini snn suma za'a rikesu da sabon mhmcin kmr yadda hajarat sakeena da danta shamsan suka samu matsayi da kulawa....

awa daya bayan tafiyar shamsan hakan nan gidan ya dauka da wani irin shiru kowa yanacan sashensa yana aiyyana abunda ke gabansa face har saida su zafar suka dawo daga yankin dala

aka fara shirin official public ñadin sarauta agaban mutane da zaa yishi washe gari da safe.

daren gabaki daya kafafun maaikata da securities bai dauke agidan ba sbd shirye shiryen komawa dala da sarki Abdallah da matarsa zasuyi gobe

washe gari tun kafin asuba yayi wani gabjejen servant ya fito da karfe yahau buga wani katon royal alarm clock dake daure da chains a tsakiyar mansion din domin kowani servants da maids su farka sufara aiyukan dake gabansu kmr yadda aka saba kullum.

after few moments bayan an idar da sallan fajr da mintina kadan cikin sanyi safiya da iskan da ke kadawa a hankali Nana A ta fito daga sashenta ita daya cikin cikakken shiri na muhimmin event din dake karatosu ayau

bangaren uwarjini ta nufa kai tsaye tawani irin kawata jikinta da golden brocade mai nauyi da aka masa ado da royal silk da veil mai dan sheki, takalmanta na hermes mai launin nude take takawa ahkli dashi cikin nutsuwa.

Wajajen karfe 6:30am na safiya ne amma dake tun jiya uwarjini ta bada umarnin cewa kowa ya fito da ssafe dan suje dala su dawo yasaka kowani sashe yazama soo buzy dan babu wanda yake iya saɓawa umarninta.

tsabar iko datake dashi yakan dauki tsawon lokaci kafin kaga tabar cikin tharim vale saidai tsabar muhimncin da jikanta abdallh yake dashi a zuciyarta da rayuwarta yasaka kusan dolene taje har dala dakanta dan tasaka ma mulkinsa albarka snn tay casting magic spells na kariya, iko, da muhibba akan kujeran da jikatta zai zauna akai na tsawon lkci.

…Nana A tana isowa sashen uwarjini tuni masu tsaron kofofin suka bude mata udaya bayan daya cikin ladabi har ta isa babban inner chamber din uwarjini daya gama gumewa da wani irin tsadadden qamshin turaren wuta me azaban dadi da bugarwa.

jin shirun da wajen ya dauka dashi yasa ta rage sautin kasaitaccn takun datakeyi sai can kafin nan ta karasa shiga ciki ta tsaya cak a gefen wani killatccen sashe da ba kowa ke zuwa ba tana lekawa kuwa ta hango uwarjini tana zaune a kan wani low carved stool na zinariya, fresh fresh virgin servants guda hudu mata na duke a gabanta sun rike wani babban silver bowl mai dauke da nonon jaki mai kauri da kamshi ayayinda uwarjini take shafawa a jikinta a hankali batare da sauri ba dan tariga da ta saba da wann al’adar da haryau babu wnda ya isa ya tambayeta dalilinsa.

xama a killatcen dakin wankan yazame mata tamkar sensual ritual dan ko wani rana intay wanka sai an dauki lokaci ana goge mata fatarta da nonon jaki yadda ake fadi acikin sirrin ageless skincare na Cleopatra…

shiyasa duk dama ta jima sosai a duniya amma babu alamar tsufa ko yamutsewar fata sosai ajikinta ftrta kullum da laushi yake kamar ana saka mata wani sabo duk dama mutane dayawa sunfi amincewa da cewa tsafi ne kawai yake hanata tsufa.

Nana A dake tsaye daga kofa ta sauke ruwan idanuwanta a kasa cikin girmamawa

saidai kafin ta ynke hukuncin karasowa ciki wata servant ta dago kai da sauri sauri tanamai dakatar da ita cikin ladabi.

“ranki ya dade uwarjini zata fito ta sameki nan bada jimawa ba bayan ta gama wankan.

Nana A bata ce komai ba ta gyada kai kawai ta juya cikin nutsuwa ta fita tafara zagawa domin ta tabbata cewa acikin matan gidan kowa yagama shiri akan lkci sbd yaune ahalin zamkora zasu karasu kusan yau din wani babban ranace agare su.

bayan kamar rabin awa harabar gidan ta canza qamshi ya cika iskar dake yawo gaba daya kowane bangare suka fara fitowa saiya zama kamar wani babban fashion parade ground

kowani namiji da iyalan sa suna fitowa cikin cikakken shiri kowanne da irin kalar kasaitarsa snn kowanne da ikon da yake wakilta.

shugaba imran ne farkon fitowa ya fito cikin imperial noir all black brocade babban riga da aka kawatashi da aikin hannu na saƙa da golden zare amma bamai yawa ba, da wani dan uban black rawani mai paired with royal babouches dake nuna zallar authorityn dinsa a fili. daga nan gefensa kasaicciyr matarsa ummu zulaiha ce sanye da wani irin emerald green couture gown na Elie Saab, ta lullube kanta da sheer silk veil mai dauke da duwatsun diamonds masu laushi sai ‘yarsu mareeda wazeeri wnda tsayinta da nutsuwarta bazai bari ma kamata kallon yarinya ba sanye take da wani custom made dress mai launin wine red very simple amma mai tsadar gaske.

kallon daya zaka samu kadai ya sanar dakai cewa sune ynxu masu shugaban cin tharim vale,.

ilimi, dukiya da hutu yabi jikinsu, tun lkcin da suke zama a abuja sune kadai suke da cikakken ikon kulawa da duk wani harkan kudi, wato fannin globl finance nd investment na wazeeris gabaki daya, sune kadai suke da cikakken haqqin kulawa da harkokin juya kudade kamar irinsu private banking, stock,global monetary investments da fin tech empires na gaba daya zuriarsu na wazeeris da ke zagaye da duniya kasashe daban daban.

kusan matattarar kudin ahalin a hannunsu ake juyawa

daga gefe kuma zafar wazeeri ne shima ya

fito cikin wani midnight blue velvet babban riga me sapphier detailings da rawaninsa sai wata crocodile slip-ons daya rataya,matansa ummu bilqees da cikinta ya fito fili amma hakan bai rage mata kyau ba, itama sanye take da wani calm champagne gold flair gown dogo har kasa na valentino couture ta kawata jikin ta da wani silk cape mai tsayi shima sai wani dan ubansun gwalagwalai data bazasu.

yadda suke jin kansu daga ganin su zaka san su ne masu rike da duk wani harka daya shafi wazeeris mineral resources, wato xallan maadanai na, ckamr oil, natural gas, coal, gold, rare diamonds, precious stones da kuma oda valuable solid minerals. luxury nd lifestyle assets duk karkashin ikon su yake

amma a garin zamfara suke da zama suna dan saka ido akan wasu abubuwan dake ba su jima da yin aure ba…

sai can ummu salma ta fito cikin wani soft beige dress na Dior haute couture shigarta mai sauki amma mai matukar daraja dake nuna asalin girmanta da yawan shekarunta dan dama itace take bin shugaba khaleefa a shekaru, a tare da ita mijinta engr alhaji fuad ne yana sanye da wani classic babban riga na Canali da kuma jikarsu leelah karamar yarinya sangartacciya sanye da simple silk dress sai kanin alhj fuad din wato farees salman dake da wani irin yaudarren kyaun fuska amma kuma shi yadan girma kadan.

ahalin ummu salma kusan sune masu rike da agricultural nd land investment empire na ahalin wazeeris, duk wani gonaki da filaye a kasashe daban daban na duniya da kuma

food supply chains da

global agro business da su phamerceuticals nd health care duk a hannunsu yake shiyasa ma take mutuwarson jikarta leelah ta gama jarabawa atura kasar waje taje can itama tafara karantunta a fannin biomedicals dan ta zama expert a harkokin da sukeyi.

kusan sai da kowa ya fito snn wanda ake jira wato sarki mai jiran gado king abdallah wazeeri ya fito cikin wata pure white royal embroidery na babban riga, hdadn rawaninsa fari kal ne da dan white slight gold thread ajiko her nd der da classy royal slips on dinsa shima, wanda duk dama fuskarsa babu wani murmushi amma

idanuwansa cike suke da iko, daga gefensa

hajarat sakeena ce

sanye take da wani charcoal grey brocade gown da aka mata limited edition na loro piana, doguwar classy alkyabbar dinta na raw silk yana bin takunta yana sauka akasa ahankali kyakkwan fuskar tan nan cike da natsuwa duk dama kwana tay da tunanin danta shamsan acikin zuciyarta.

daga gefenta yarsu ce rihanna wazeeri wacce duk gidan babu wanda yakaita sanyin hali da hankali, krmr yarinya ce data fara girma kadan kadan, sanye da soft blush pink dress na Chanel. duk dama ita kanwar shamsan ne amma ko kadan basu yi kama da junamsu ba she looks more like her uncles amma tana da kyaun fuska da sura dede gwargado.

ahalin sarki abdallah dama sune masu rike da harkan real estate empires da dukkkan wani strategic equity holdings na ahalinsu na wazeeris gabaki daya.

duk wani gini duk wani land development duk wani luxury property na ahli da zuriar wazeeri kaf a hannunsu yake, snn dake abdallah yana da ɗa namiji yasaka uwar jini ta kara masa da major wazeeris groups nd share holdings shiyasa babbn dansa shamsan tun yana jariri sunansa yake zaune akan wasu muhimman takardun wazeeris industrial shares, da su energy, telecoms, da irinsu logistic da A.I tech ciki da wajen qasa.

kaf yaran gidan ma babu wani wanda yayi kusa da kama kafar shamsan wazeeri a dukiya tun ayanxu da bai gama girma ya mallaki hanklin kansa ba, shiyasa komi nashi daban yake dan ynxu haka he is the yungest multi billionaire in the family.

saida kowa ya hallara a harabar gidan kafin nan uwarjini maqboola hanim itama ta fito daga bangarenta kusn atsanke tay shirinta ta fito tsaf sanye da wani pure black expensive regal attire mai dauke da golden gold threads masu sheki tafiyarta ba kamr na kowa bane dolekaji sautin wnn kawakkiyar sarkan kafa na zinari dake makale akafarta idan tana tahowa

tana fitowa babu bata lokaci Nana A ta wani tunkaro ta tanamai rufa mata baya kmr inuwarta, tun daga nan ba a bata lokaci ba duka aka doshi jerin motocin alfarma dake jere kowani bangre ya kama convoy dinsa acikin jerin mayun mercedes-Maybach, Rolls Royce Phantom da kuma armored SUVs masu aji da zasu wuce dasu.

daidai karfe 7:40am na safe duk suka shiga mota convoy din ya wuce dasu acikin nutsuwa akai dasu zuwa babban filin jirgin garin inda private plane dinsu yake yana jiransu zuwa kano…

after few hours da isarsu kano aka fara hidima bikin ya zama kamar wani abu na tarihi dan duk wasu sarakuna daga sassa daban daban,secret societies,gwamnoni,ministoci da manyan attajirai duk sun hallara domin girmama sabon sarki

nadin sarautar sarki abdallah wazeeri ya gudana cikin cikakken tsari dan rawanin da aka daura masa me daraja ce saida kowa ya rusuna snn aka tabbatar da cikar taron saidai kamar yadda aka tsara uwarjini tana gama tsafe tsafenta da kafe kafenta agidan sarautar basu jima ba duk suka koma cikin jirgin su dake jiransu ba tare da bata lokaci ba suka dawo cikin tharim vale dan a tarbe ahalin zamkora.

Doka mai karfi Uwarjini tasaka cewa kowace mace tazauna acikin sashinta da yayanta dan batason kowa ya fito fadar iko face har sai ahalin zamkora sunzo sun tafi.

hankalin ummu salma yakara tashi sbd lkci ne datasan da za'a yanke hukunci na karshe akan matar aure da shamsan zai aura.

gabaki daya ta kasa zama ta kuma hana nana A sakat dan tun da taje dala taga irin tsabar daular mulki da iko da sarki abdallah zai zauna aciki taji kawai obsession dinta na son jawo daraja ajininta ya karu fiyede dana kowani lokaci

kai dolene ma kawai jikarta leelah ta zamo daya daga cikin zaɓin aure da za'ayi ma yrma shamsan amma kuma sai taga kamar nana A ba wann shirin bane a zuciyarta wani abu ne daban takeso ta shigo musu dashi wanda bata gane ba

dan daga dawowarsu daga dala ta lura kmar nana A tafara cusa kanin mijin ta farees salman acikin rayuwar rihanna wazeeri kmr tanasone su kulla wata boyayyar abota.

duk tarasa dalilin meyasa ta bijiro da wann shirin yau gashi babu lokcin yin wani bayani me yawa tsakaninsu dan ahalin zamkora sunriga sun kamo hanyar zuwa nan bada jimawa ba zasu iso cikin tharim vale.

#Surayyahms

#Tales of the wazeeris.

#2026

idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata

AREWAPEN

@SURAYYAHMS

WATTPAD @SURAYYAHMS

WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER *** TO BE ADDED

#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025