ALWASHI 2

20

by @rufaidaumar

ALWASHI

   45

YOBE

Gaba daya ya tattara akalar rayuwarsa wurin addu'a da kuma tunanin yanda zai fara aiki. Adam ya bar zancen Kubra da yaransa zuwa nan gaba kaɗan gudun jefa su cikin hatsari. Zai ba da lokaci, duk da yana ji zuciyarsa tamkar za ta yi bindiga, amma yana kyautatawa Allahnsa zato, ya san ya fi shi son su. 
   Ta hanyar wani tsohon amininsa kuma abokin aikinsa, Lawan Nagoda ya samu damar neman gurbin aiki a ma'aikatar BBC dake Abuja. Ya kuma ba shi tabbaci da cewa in sha Allahu za'a dace. 
   Yan uwansa duka an zuba masa idanu, tun ana saka ran zai ɗau wani mataki har dai aka yi watsi da tunanin hakan. Babbar damuwar mahaifiyarsa bai wuce ya yi wani auren ba, sai dai ta san ko giyar wake ta sha ba za ta tunkare shi da zancen ba. Bai fasa zama cikinsu a taɓa hira kaɗan ba. Ya ɗan saki jiki, ya saka a rai cewa duk lalacewar naka to fa naka ne. Can ƙasan zuciyarsa, shi kaɗai ya san me yake ji. 

***
  LONDON

Ta bararraje a saman gadonta daga ita sai vest da wandon da bai ƙarasa rufe cinyoyinta ba, hannunta ɗaya riƙe da kwalbar giya sai ko ɗaya hannun da ta ke faman zuƙar sigari da fesarwa. Ba ka jin tashin komai a ɗakin sai kiɗa da ta kunna, waƙar Soso na Omah Lay.
  Cikin yanayin maye ga kuma hawaye shaɓe-shaɓe a saman fuska, Nihla ke bin waƙar tana rangaji, wani bin ta fashe da dariya wacce da ka gani ka san cewa na zallar baƙin ciki da tafarfasar zuci ne. 
  Daga falon kuwa, mahaifiyarta Momi Inayah ce ta ji sautin kiɗan  ga kuma muryar ɗiyarta da ta ke ɗan tsinkaya da ƙarfi yana fita tamkar na wacce ke a buge. Ba shiri ta miƙe ta nufi ƙofar ta murɗa sai dai a ƙulle, nan ta hau bugu amma babu ko alamun Nihla ta ji ballantana ta buɗe. 

 "What's wrong?"

Ta ji muryar Daddy Affan a bayanta wanda ke takowa yana rage shaƙar da ya yiwa wuyansa da necktie, ya ajiye coat din dake hannunsa a saman kujerar dining sannan ya ƙaraso ganin Momi Inayah na mishi nuni da ƙofar, daƙyar ta iya magana murya na rawa ta ce,

  "I think she's drunk." 

"What?!"

Sai kawai ya shiga bugu da ƙarfi,

"Baby! Baby! Open the door!"

"No!"

Ta amsa murya a sama. 

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"

Faɗin Momi Inayah da ta fahimci dagaske fa ɗiyarta a buge take. Shi kuwa Daddy Affan cigaba da bugu ya yi amma Nihla sai ihu ma da take akan ya dameta, ya rabu da ita. 

 "Nihla! Don't destroy your life because of this mere issue! Please!"

Ji suka yi an buga wani abu ya faɗi, kiɗan ya tsaya cak! Ga kuma ƙarar fashewar kwalba da ya ratsa kunnuwansu, suka yi saranda suna duban juna hankali a tashe. Kusan lokaci guda suka kai hannu zasu ƙara bugun ƙofar sai kawai suka ga ta buɗe a fusace. Kallo ɗaya suka yi mata suka tabbatar dagaske ta yi mankas, ga warin giya ga na sigari cakuɗe wuri guda. Gashin kanta a hargitse, idanun sun yi jawur ga kuma kumburi. Ta tafi luu za ta faɗi, da sauri Daddy Affan ya riƙo ta. Ta ture shi ta yi taga-taga gami da nuna sa da yatsa. 

 "Ka ce me?! Ka ce me?!! I lost the love of my life and you call it a mere issue Daddy?!! I hate you! Kai ne silar da hakan ta faru! I will never ever forgive you! I am your only daughter! Amma ka kasa samar min abinda nake so! I hate you!!"

Tana maganar tana kokarin ƙwatar kanta daga riƙon da ya yi mata amma kuma sam ta kasa saboda gaba ɗaya jikin ba ƙwari. Ita kuma Momi Inayah da ta bi ta da kallo ta ga ƙafarta na fidda jini ta yi saurin duban ɗakin. Can ta hango ƙaton duvet din dake kan gadon ba hayaƙi. Da sauri ta ƙarasa har sai da ta taka kwalbar ta kuwa ambaci sunan Allah gami da riƙe ƙafar, shi kuwa Daddy Affan tuni ya cicciɓi Nihla yana faɗan ta tsaya ta ji ciwo a ƙafa zuwa falonsa. Momi Inayah ta ɗauki ruwan jug dake a saman bedside drawer na Nihla ta watsa a gadon. Ba shiri inda sigarin ya soma ci ya mutu murus. Haka sigarin. Kawai sai ta durƙushe ta fashe da kuka, kuka mai ƙarfi. Giya? Nihla ke shan giya? Wannan wace irin rayuwa suke haka wai? Ta gaji! Lallai dole ne Daddy Affan ya gyara rayuwarsu idan kuwa ba haka ba za ta gudu da ɗiyarta su fice a rayuwarsa. Rayuwarsu kamar wasu kafirai? Anya tana da hujjar kare kanta a gobe ƙiyama? Ba ta ƙara gano kuskurensu ba sai bayan da ta rayu na ɗan lokaci a gidan Alh Sada
Bilyaminu, yanda yaransa ba sa wasa da lokutan sallah, da kuma irin nutsuwar yanmata  gidan, nan ne ta ƙara gano dukkan kura-kuranta sai dai babu damar tunkarar mijinta. Yau ga ɗiyarta kuma da kwalbar giya bayan sigari da take ɗan sha lokaci-lokaci. 

 'Idan kuma watarana ta kawo maki wani namijin a gidan nan fa? Ko ta faɗa harkar neman jinsi?'

Tunanin nan ya yi mugun razanar da Momi Inayah, Allah ne ya kare ta kawai a karo na biyu ba ta ƙara taka kwalbar ba sakamakon fitar da ta yi zuwa wurinsu da saurinta. A can falon Daddy Affan din ta iske Nihla ta ɓingire tana bacci ga wani amai a gefe mai aikinsu na mopping. Shi kuwa ya duƙufa wajen yi mata dressing ƙafarta da ta ji ciwo. 

Sai bayan fitar mai aikin kafin ta dube shi da nata jajayen idanunta. Bai ko dube ta ba don ba ya son jin wani ƙorafin wofi. 

 "Affan!"

Cak ya tsaya, ya ɗago da ɗumbin mamaki a saman fuskarsa ya dube ta. Da leɓɓansa ya fahimci kalmar 'what?' ya furta, ba don sautin ya fito sosai ba. Duk da ƙirjinta da ke bugu cike da tsoro, hakan bai sa yau ta kasa karya bille wurin yin magana ba. 

 "Lokaci ya yi da zamu bar ƙasar nan!"

Ta furta zuciyarta na zafi, hawayenta suka zubo. Jikinta kaɗawa yake yi kamar mazari, shakka babu tana tsoronsa, sai dai kuma tsoron a yau idan ta duba me ya haifar mata? Sau ɗaya tak! Ya taɓa yi mata hukuncin rufe ta a ɗaki tsawon sati babu abinci sai ruwa kaɗan, ya kuma mare ta sau da dama, duk saboda ya ganta tare da wani tsohon saurayinta suna gaisawa tun ma kafin ta samu cikin Nihla. Tun daga wannan azabatuwar da ta yi, da kuma rantsuwa da ya yi cewar zai iya kashe ta  idan har ta ce za ta rabu da shi wataran. Wannan ne ya sa tun lokacin Inayah ke tsoronsa. 
  Ga mamakinta kawai ta ga ya yi dariya.

 "Kina tunanin ba ni da wannan shirin ne? Toh nan da sati biyu zamu tattara mu koma Abuja. Dukkan wasu ayyukana zan yi mayar can, zan kuma ɗora waɗanda zasu kula da nan din."

Ta yi mamaki, matuƙar mamaki. Amma kuma jikinta ya ba ta akwai wata a ƙasa, ba banza ba, ba haka kawai Affan ya yarda zai bar London ba. Madadin ta sake magana kawai sai ta juya a sanyaye ta fice tana ɗan ɗaga ƙafar da kwalba ta ɗan huda mata kaɗan. 

 Ya bi bayanta da kallo kafin ya furzar da huci. A hankali ya sauke ƙafar Nihla ya ɗora saman kujerar gani da shafar kanta. 

 "Wanda duk ya yi silar jefa rayuwarki cikin ƙunci Nihla, lallai ya shirya guzurin tarbar jahannamarsa a duniya domin wallahi sai na yi duk yanda zan yi wurin tarwatsa farin cikin Sada's family."

***
  KANO




A YI MANAGE DA WANNAN PLS ZUWA GOBE IN SHA ALLAH. BA DON MA NA YI ALƘAWARI YAU BA, DA SAI GOBEN ZAN BAKU DOGON SHAFI.

Rufaida Umar