HADIN KADDARA

Chapter 14

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         AyshaNalado


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page 14



Kusan 20 minute Salmah ta kwashe tana waya, kakkarfar ajiyar zuciya ta sauke, tana jin zuciyarta sam babu daɗi,  jiki a sanyaye ta juya ta kama tafiya a hankali  kamar mai tausayin ƙasa, ta koma ciki ta hanyar data fito. Tana isowa  tsakiyar main falo, ba zato ta tsinkayi muryar Abie “Daga ina ki ke?" A tsorace ta juyo ta kalle shi , bata taɓa zato ko tsammanin da mutum a falon fa, cikin inda inda tace "Ab, Abie na amsa call ne." Cike da mamaki yace "Call! Call ɗin wa?" Ya jeho mata tambaya, da sauri tace "call ɗin yaya Anas." Tsare ta da idanu yayi yana kallonta duk  alamar rashin gaskiya ya bayyana ƙarara a fuskar ta. Miƙa mata hannu ya yi tare da cewa "Mu ga wayar." miƙa misa ta yi zuciyar ta na bugawa, danne danne  ya yi na ƴan sakanni sannan ya miƙa mata, hannu biyu tasa ta kar6a ya ce "you can go." 

Da sauri tabar falon har tana haɗawa da gudu gudu,  da kallo Abie ya bi ta har ta ƙule ma ganinsa, kafin ya  girgiza kai yayi cike da nazari, a fili yace tabbas yaran nan akwai abin da suke ɓoyewa kamar yadda aka sanar masa, kuma  ya zama dole ya na ƙara sanya  idonu a kansu.


Jingina ta yi da ƙofar ɗakin na su bayan ta shiga ta  maida ƙofar ta rufe, ajiyar zuciya ta shiga saukewa, a gefe guda kuma abinda suka tattauna da yayan nata na sake dawo mata filla filla a kwakwalwarta, sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan idanunta ya sauka akan Aishatu, a yadda ta bar ta haka ta same ta a kwance sai dai yanzu  ta yi  lamo kamar tana bacci, sa6anin ɗazu da take ta sauke nunfashi, duk da haka a kallo ɗaya ta gane baccin ƙarya ne.

Bata ce mata komai ba sai ma toilet data shige ta watsa ruwa ta fito shiryawa tayi cikin kayan baccin ta, ta  kashe musu light tta haye kan bed ta kwanta a gefen ta.

Gaba ɗaya ranar basu samu  bacci kirki ba,   duk shiru suka yi kowacce na tukwa da warwara, kowacce da abinda take saƙawa da kwancewa, ba tare da ɗaya tasan ɗaya na farke ba, Salmah ce ta fara yin barci bayan ta gama tsaida matsaya ɗaya, yayin da A'isha sai da  ta raba dare sannan bacci 6arawo ya kwashe ta.

Koda suka tashi ba su yi wannan maganar ba, normally suka gudanar da ayyukan su na yau da kullum, bayan sun yi breakfast, ɗaki suka dawo domin yin shirin makaranta, Aysha  bata da lecture sai dai akwai  assignment mai mahinmanci  da za ta yi submitting Karfe takwas da rabi yayinda salmah ke da lecture ƙarfe tara.


Koda suka shigo ɗaki kwanciya A'isha tayi kanta na ɗan Sara mata saboda barcin da bata samu sosai jiya ba, kallon ta salmah tayi,ba dai ta tanka ba ta shige toilet.

Koda ta fito still tana nan a yadda ta barta bama ta da niyyar tashi, har ta gama shirin ta cikin riga da skirt na atamfa ta kuma 6ata lokaci tana   shafe shafen ta kasancewar gwanar kwallaya, A'isha bata motsa ba, sunan ta ta  kira "Aysha ki tashi ki yi wanka mana tym na going fa." 

Ba tare da ta ɗago ba tace "bana jin zan iya shiga school yau, amma dan Allah zan baki Assignment ɗina kiyi mini submitting." Salmah tace "saboda me ye baza kije ki kai da kanki ba, bakya tsoron a samu matsala kin san dai Sir Bala bahagon mutum ne." 

" Babu wata matsala Class Captain yace mu ba, shi za ki nema ki ba amma dan Allah ki kai da wuri dan Sir Bala yana da matsala yace 8:30 dot yake bukatar Assignment ɗin a office ɗinsa kuma Assignment  ne mai mahimmanci sosai, 30% na exam score ɗin mu ne, ki kula don Allah Salmah kar a samu matsala mutumin bauɗaɗɗe ne kuma bashi da imani."


Zama salmah ta yi a bakin bed ba tare da ta kalleta tace "Menene shirin ki akan shi domin baza mu bari lokaci ya ƙure mana ba." Jin Salmah ta taba mata inda ke mata ƙyaikyayi yasa ta miƙe zaune tare da dafa kafaɗar salmah tace , "Ina da kyakkyawan shiri a kan shi wanda na tabbatar zai yi aiki fiye da zato na."

"Da kyau,  menene  shirin  domin na san ta dame zan taimaka miki." 

"Ba wani abu mai tsauri ba ne, na yanke shawaran zan fallasa asirin shi a idon duniya zan tozar ta shi a idon masoyansa ta hanyar shiga gidajen redio da talabijin  media na faɗi wanene shi."

Da wani irin mugun dariya Salmah ta fashe, wanda ya saka Aysha ƙanƙance idanun tana kallonta .

Hakan baisa ta tsagaita da dariyar ta ba sai da tayi mai isarta tukunna, kallon  Aysha ta yi da nufin yin magana, da sauri ta daga mata hannu. A kausashe cike da tsananin fusafa tace, "I know dama karya kike min yaudara ta Kawai kike yi da kika ce kina feeling pain ɗina, nima nayi wauta domin na riga nasan babu macen da zata iya feeling pain ɗina sai wacce ta haɗu da irin ƙaddarata a rayuwarta, kin tasa ni gaba kina dariya wato ga mahaukacciya ko, ba komai laifi na ne dana gaya miki sirrina nagode." Tana gama faɗin haka ta miƙe tana share hawaye ta nufi hanyar toilet.

Har  ta kama handle ɗin kofar toilet zata shige salmah tace "baki fahimce ni A'isha ta yaya kike tunanin bazan yi dariya  akan shirmen  da kike faɗi ba , kin san kuwa me kike shirin yi, abin da kike shirin yi shi a ke kira da wayon rashin wayo hausawa kance idan baka iya kama 6arawo ba,to kuwa 6arawo zai kama ka, mutum kamar  Mr AA kangiwa kike tunanin zaki shiga kafafen  sadarwa domin aibatawa,ki sake tunani idan hankali ya gushe hankali ke nemo shi, ta yaya kike tunanin mutane zasu yarda da maganar ki, shin ina hujjar ki, menene shaidar ki? Wai tukunnama, kina da tabbacin shine wanda ki ke nema da gaske, kina da tabbacin shine Babangidan ko akasin haka?“ 

Da baya da baya ta ringa ja har ta iso bakin bed da6ass ta zaune tare da dafe goshin ta kwata kwata ta manta da batun wani  hujja ko shaida, idanunta ya rufe burinta Kawai fansa, tabbas da kuwa ta rafka babban kuskure, lallai Salmah alkhairi ce a gareta, ba da don ita ba da ta daka tsalle ɗaya ta faɗa rijiya wanda sai tayi dubu bata fito ba.

Maganar salmah ne ya katse mata tunani. "banji daɗi ba A'isha da kina ce bana feeling pain ɗin ki, idan da wanda ke jin ciwon abin da ya same ki a yanzu baya na yake, ki sani ko babu aminta tsakanin mu ciwon ya mace na ya macece."

Da sauri Aysha ta kai hannu ta rufe mata baki, cikin rawar murya ta shiga cewa "Kiyi hakuri ƴar uwa ta ki yafe min ban kyauta miki ba, kaidin zuciya ce wacce bata da kashi." 
Hannu salmah ta kai ta cire hannun Aysha  dake bakin ta ta kalle ta ta ce "Babu komai ƴar uwa na fahimce ki." 


Ɗagowa tayi ta kalleta ta itama murmushi suka sakarwa juna wanda bai kai zuci ba, Aisha ta ce  "yanzu meye abinyi." Shiru salmah tayi tana nazari  kafin tace "Abinyi shine, mu fara da samun tabbacin a kan Babangida ta hanyar bibiyar Mr AA, ina da tabbacin idan ma ba shi bane Babangida to tabbas ma kusancinsa ne, daga na sai mu ne mi shaida da hujja kafin mu kutsa kai gadan-gadan cikin aikin, na yi miki alkawarin in dai ina numfashi sai an bi miki  hakkinki Aysha."  

"Ta yaya zamu samu shaida da hujja nidai a yanzu kinsan bani da wani shaida  sai  Allah, sai iyayena waɗan da bansan a duniyar da suke ba a halin yanzu, bani da wani hujja kwakwara da zan kama."

Murmushi salmah tayi tace "kar ki damu ƴar uwa zamu samu shaida cikin sauki  ta hanyar bibiyar sahunsa, duk da bamu da isasshen lokaci don yanzu saura wata biyu cif za6e amma ki bar komai a hannuna."

Kafin A'ishatu ta bata amsa suka jiyo muryar Ammi tana kwala musu kira, da alama tana nufowa ɗakin nasu ne da sauri salmah ta miƙe tare da daukar Assignment ɗin A'ishatu da zata mata submitting ta saka a jaka ta fice.

Ammi da kanta ta sauke Salman da Salmah a school, sannan ta wuce Asibitin da take aiki.


Kwanciya ta gyara lokacin da ta ji get man ya maida koƙa ya kulle, rintse idanunta tayi ta shiga tunanin yadda  zasu samo shaida da hujja, ta dade a haka bata hango wata mafita ba, zumbur ta miƙe lokacin da ta tuno wani abu, durowa ta yi akan bed ta dauki wayarta da sauri ta fice daga ɗakin, bata zarce ko ina ba sai ɗakin Ammi in da take adana takardu masu mahimmanci, filla filla ta shiga dubawa cikin sauri sauri, bata ga abin da take nema ba, tattara takardun tayi ta mayar, a fili ta ce " ya ilahi!  ina takardun nan suke ne?" Dakin Abie zuciyar ta bata amsa, kamar wacce aka tsikara ta fito daga ɗakin Ammi  ta nufi na Abie har ta kama handle ɗin ƙofar zata buɗe,kira ya shigo wayar ta,lamba ce babu suna kamar ta share sai kuma ta ɗaga, daga ɗaya bangaren ta ji muryar namiji yana cewa "A'ishatu m Lawal kizo school yanzu yanzu, sister ki ta zo ta yi submitting Assignment dinki, na harhada na dauka na kai masa Office yace na mayar ya fasa kar6a a haka, zai biyo class ya kar6a a hannun kowa, means kowa zai yi submitting nashi by his self, kizo da wuri don 20 minutes ya bani akan na mayarwa kowa script din shi." Daga haka aka katse  call din ba tare da an bata damar cewa komai ba.

Sai lokacin ta gane mai magana class captain ɗinsu ne Al-mustapha.


Dafe kai tayi tare da furta "innalillahi wainnailaihi rajiun." a bayyane,tsaki taja ta ce "amma wannan mutumin anyi jarababbe." Tunani ta shiga yi ta yadda 20 zai kaita school, gata a gida ko wanka bata yi ba.

Dakin su ta koma a gaggauce  ta canza kaya , ta dauki kudin transport ta fito tana sauri kamar zata tashi sama, tafiya take tana duba agogon dake ɗaure a tsinstiyar hannunta, tasan ko a jirgin sama zata baza ta isa kafin lokacin ba amma duk da haka za ta yi iya yinta.

Addu'a ta ringa yi Allah yasa ta samu koda mashin ne ta hau don tsakanin gidana su da babban titi akwai dan tazara ga shi layin ƴan gayu ba'a cika samun abin hawa ba.


Haka ta ringa zuba sauri Kamar zata tashi sama, daga bayanta taji mota yana mata horn da sauri ta juya tare da kaucewa duk da tasan ba akan hanya take ba, maimakon ya wuce sai,matsowa yayi kusa da ita yayi parking tare da sauke glass matashi ne, kyakkyawa, duka bazai wuce tsaran su salman ba, murmushi ya sakar mata tare da cewa "sister school kika yi ne." Ido ta zuba mashi tana son gano inda ta san shi, bai jira jin amsar ta ba yace "OK dama ina ce school zaki in ce ki shigo mu tafi don nima can na nufa." Ta ce "kaima ɗalibin p.u.t, ne." Ya ce "yes." Jin haka yasa ta bude motar ta shiga da zuciya ɗaya. 


Tunda suka fara tafiya saurayin nan bai ƙara ce mata kala ba sai zuba tukin shi yake cike da kwarewa. Har gaban department ɗinsu ya kaita, ta sauka tana ta zuba mashi godiya.


Koda ta ƙarasa a waje ta samu da yawan yan class ɗin su, wurin class captain data hango ta nufa, shima yana ganin ta, ya tare ta, da cewa "A'isha kin makara yanzu ya gama fita, ya kuma ce bazai sake amsar na wani ba ko dan uban wanene?" Zaro ido tayi tace "shi kenan zan fadi a subject ɗin, dama ranar da a ka yi text bana nan, yau kuma gashi an yi submitting assignment ɗin da nake da yaƙinin zai taimaka min na yi passing."  wata daga cikin su ne tace "ki bi shi office ki roke shi ƙila ya karba."


Ta fi mintuna ashirin a bakin office ɗin kafin a bata izinin shigowa, daga gefe ta tsaya ta ce "gud morning Sir," sai da ya gama shan kamshin shi ya ɗago ya mata kallon sama da ƙasa sannan yace "morning! meke tafe dake." Cikin in'ina ta buɗe baki zata fara bada hakuri, wayar shi ta fara ringing dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu, ya yi picking call ɗin tare da karawa a kunne, bata san mai aka gaya mai ta ɗaya bangaren ba zumbur ta ga ya miƙe, yana cin gaba da waya can kuma taga ya nufi hanyar fita, da hannu ya mata alamar ta jirashi yana zuwa ya fice da sauri.


Tayi tsayuwa a cikin office ɗin sir Bala ya kusa na 30 minute bai dawo ba, ita ba abin ta wuce ba, ji tayi ciwon da kanta keyi ya fara karuwa ga wani  jiri jiri da  ya fara diban ta, idanu ta lumshe tare da jingina da wall ɗin office ɗin.

Ƙaran buɗe kofar ne yasa da sauri ta bude lumsassun  idanunta da suka fara rinewa zuwa launin jaa.


Wani irin zabura ta yi lokacin da idanunta ya sauka akan fuskar shi, duk da cikin shigar shi ta 6adda kama yake hakan bai hanata gane  shi ba  zuciyata ce ta hau dakan uku uku, yayinda ta nemi miyau a bakinta ta rasa............



Diyar Nalado ce😍
***